-->
olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

UMMI CHAPTER 14

UMMI CHAPTER 14
MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Abu dai kamar wasa Ummi ta qi yarda MK ya matso kusa da ita tun jiya da daddare.. Tun da jiri ya kwasheta ta fadi a jikin shi ya dauke ta ya kai ta dakin ta ne ta kore shi. Ya so ya san yadda take ji idan da akwai taimakon da zai iya yi mata amma sam ta qi sauraron shi.. Kukan da take ta yi shine yake tayar mishi da hankali matuqa... haka nan ba don ya so ba ya qyale ta tunda abinda take so kenan. A yau da safe ma da ya shiga dakin nata qin sauraron shi tayi... dukda bata bari ya matsa kusa da ita ba ya fahimci cewar akwai zazzabi a jikinta don haka ne ya kira Dr. Zeenat. Da qyar Ummi ta amince Dr. Zeenat ta duba jikinta.. sossai likitar tayi mamaki domin kuwa babu wata matsala mai tsanani, ta kula dai Ummi raki gareta sai kuma shagwaba sannan kuma qila harda yarinta. Da qyar ta lallabata ta sake gasa jikinta a ruwan zafi sannan ta sha magani da fresh milk. Likitar dai ta tabbatar ma MK cewar babu wata matsala don haka ya kwantar da hankalin shi. A haka tayi mishi sallama ta tafi. ************* Kusan minti talatin kenan da Dr. Zeenat ta bar gidan. MK wanda yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya ne ya nufi sashen Ummi. Yana bude qofar dakinta na ga ya zaro idanuwa cike da mamaki a dalilin ganinta da yayi tana shiri... da alama dai fita zata yi. toh fa.. Da sauri ya qarasa shiga cikin dakin ya nufi wurinta ya kamo hannunta yace "Baby meye haka?? ina zaki je??" Fizge hannun ta tayi ba tare da ta kalle shi ba tace "gidan Goggo zan tafi.. zan roqe ta mu koma Rugange.."12 Ni kuwa nace Kamar fa ta san hanyar gidan Goggon..🤣 Wannan maganar ta so ta bashi dariya amma ya matse.. Gani nayi ya qara riqo hannunta ya janyo ta suka zauna kan gadonta sannan yace "Haba Baby.. kiyi haquri mana.. Hamma bazai qara ba, kin ga fa ba laifi na bane.. ai ke ce kika nemi mu cigaba kuma fa da amincewar ki.."2 Kai tsaye tace "toh ni ban san cewar abinda zaka yi mun kenan ba... yanzu ka ji mun ciwo ka sa ina ta jin zafi.. shikenan ka lalata mun rayuwa..."4 Wannan karon dai fashewa yayi da dariya yayinda ta danna mishi harara. Da sauri ya natsu tare da fadin "don Allah kiyi haquri Baby.. nima ban so na baki wahala ba.. ke ce kika ruda ni gaba daya" Ya qara matsawa daf da ita yayinda yake riqe da hannun ta ya cigaba da fadin "kin ga fa abinda muka yi jiya ba laifi bane.. ko manzon Allah yace.." Fizge hannunta tayi ta miqe tare da fadin "toh ai bai ce kayi mun mai zafi ba.."1 Janyo gyalenta tayi tace "ni tafiya zanyi.." Da sauri ya miqe ya tare ta yace "don Allah kar ki tafi... wallahi Baby idan kika tafi zan mutu"2 Jin haka kuma sai tayi saurin kallon shi cikin ido yayinda jikinta yayi mugun sanyi.. A wannan lokacin sai ta ji lallai bazata iya tafiya ba toh amma kuma azabar da ya gana mata fa?? Tana turo baki tace "idan na tsaya zakayi mun alqawari cewar bazaka qara matsowa kusa da ni ba.. ka amince??"3 STORY CONTINUES BELOW Zaro idanuwa yayi yace "what??" Toh ai bazai iya ba... shi a yadda yake kallonta haka ma ji yake yi kamar su cigaba daga inda ya tsaya jiya domin kuwa sam bata ishe shi ba sannan ga wata muguwar sha'awar ta da take taso mishi... but for now idan har amincewar shi zata sa ta kwantar da hankalinta it will be the best option for him!! Gani nayi ya shafa kan shi da hannuwan shi biyu sannan yace "shikenan na amince Baby... bazan matso kusa da ke ba har sai idan ke ce kika matso inda nake" Daga nan ya zare gyalen da ta yafa a kanta ya shiga closet dinta ya ajiye. Ko da ya fito wuce ta yayi tare da fadin "nagode baby na" Tana kallon shi ya fita yayinda ta koma kan gado ta fashe da kuka.. Ji nayi tace "haka kawai muna zaman mu lafiya ka bata.."4 Ni kuwa nace ya gyara dai... ah toh!!🤣 *************** Yinin ranar kuwa Ummi a daki ta yi shi cikin qunci da haushin MK... Ko da ya kira ta a waya qin answering tayi... gashi ya san ko ya tura mata text ba iya karantawa zata yi ba tunda dai bata iya karatu ba.3 MK dai bai yi niyyar fita ba amma a dalilin Kiran gaggawa da aka yi mishi a office ne ya fita. Ummi ta so kiran Goggo ta fadi mata abinda MK yayi mata toh amma kuma tana jin kunyar fadi mata abinda ya faru.. sannan ta tuna da cewar Goggo tayi mata gargadi akan ta daina tona asirin abinda ke tsakanin ta da mijinta don haka ne ta fasa kiran ta yayinda ta cigaba da quncin ta. Haka gidan ya kasance shiru.. Ita Maleeka dama tun da safe ta bar gidan cikin qunan rai. Bata so ko alama ta zauna a gidan don kar ta ga abun baqin ciki..2 Gaba daya ji take yi bazata iya zama under thesame roof ba da Ummi a matsayin kishiya.. A yanzu kuwa gidan ya zame mata tamkar ba nata ba.. ta zama tamkar baquwa a cikin gidan..9 ***************** Wuraren qarfe hudu na yamma ne Fatima ta shigo gidan.. dayake tayi ta kiran Ummi a waya bata yi picking ba gashi bata je islamiyya ba don haka ne ta zo gidan don duba ta. Fatima ta tarar da Ummi ta idar da sallar la'asar kenan yayinda take qoqarin ninke hijabinta. Tana ganin ta kuwa ta saki hijabin hannunta ta qarasa wurinta ta rungume ta ta fara kuka. Fatima cike da mamaki tace "babyn Hamma meye haka??? me Maleeka tayi miki??" Cikin kuka tace "toh ba gwara abinda Adda zata yi mun ba akan abinda Hamma yayi mun?" Fatima tace "Hamma kuma?? me yayi miki??" Anan kuma tayi shiru ta kasa magana. Fatima ta janyo ta suka zauna a bisa gadonta sannan tace "fadi mun mana Babyn Hamma.." Ummi wadda take share hawayenta ne tace "kin ga fa jiya da daddare.. toh fa ni ya ji mun ciwo kuma.." Fatima wadda take kallonta ce ta fashe da dariya yayinda ta girgiza kai.. tuni ta fahimci abinda yake faruwa. Ummi wadda take kallon Fatima cike da mamaki ce tace "Haba Adda meye na yin dariya?.. wallahi Hamma mugu ne kuma ni bana son shi. kin san fa na so in bar gidan amma kuma yace wai idan na tafi zai mutu.."4 Daga nan ta dan yi shiru sai kuma ta cigaba da fadin "toh ni fa dukda muguntar da yayi mun bana so ya mutu saboda..." Shiru tayi tana wasa da yatsun hannuwan ta. STORY CONTINUES BELOW Fatima wadda take ta kallon Ummi sossai take bata dariya amma ta matse.. lallai har yanzu akwai yarinta a tattare da yarinyar. Gani nayi Fatima ta cire hijabin da ke jikinta yayinda ta gyara zama tace "Babyn Hamma kina so Allah yayi fushi da ke?" Ta girgiza kai alamar a'a Tace "kina so ki saka ma Hamma da alkhairi akan dukkanin taimakon da yayi miki a rayuwar ki?? Ta girgiza kai alamar eh Tace "kina so ki haifa ma Hamma Baby?" Ta girgiza kai alamar eh Daga nan Fatima ta riqo hannunta sannan tace "wannan abin da kika ce yayi miki ba wani abu bane, Allah ya halarta ma mata da miji yin shi sannan yin hakan ai raya sunnan manzo ne.. na san kin sani cewa ta wannan hanyar ce zaku samar ma kanku Baby.." Ran Ummi a bace tace "toh Adda akwai zafi fa..." Fatima ta girgiza kai tace "kar ki damu daga wannan bazaki qara jin zafi ba... ina roqon ki don Allah ki dinga bashi hadin kai duk lokacin da ya nemi kuyi..." Da sauri tace "ai ma yace bazai qara ba Adda.. yayi mun alqawari bazai qara zuwa kusa da ni ba.. shiyasa ma na fasa tafiya" Fatima tana dariya tace "ai kuwa ya zama dole ke ki je kusa da shi idan ba kin fasa haifa mishi babyn ba ne.." Zaro idanuwa Ummi tayi tace "tab.. gaskiya bazan iya ba Adda" Fatima tana dariya tace "zaki iya... bari in fadi miki yadda zaki yi...."2 Da kyau ta Fahad!!👍8 ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK dai tunda ya isa office ya tarar da wani report na security glitch da aka samu a ma'aikatar NCC na nan Abuja wanda yake buqatar urgent rectification. Security Program Design yana daga cikin courses din MK yayi wadanda ya qware a kai.. wannan ne ya sanya akayi calling attention din shi. Tunda suka hau wannan aikin da shi da abokin shi Fahad suka duqufa. Banda Sallah babu abinda yake fitar da su daga ofis din.. Wasa-wasa dai har dare suna abu daya. Basu bar ofis din ba sai kusan qarfe goma sha biyu na dare.. shima ba wai don sun gama ba. Ko da MK ya dawo gidan a gajiye yake don haka babu bata lokaci ya shige dakin shi yayi shirin wanka ya fada bathroom.. Ko da ya fito yayi shirin bacci sai da ya fita ya leqa dakin Ummi ya ganta kwance a kan gado cikin Duvet rungume da teddy dinta tana bacci.. Qarasawa yayi har gefen gadon nata yayi mata light kiss a goshi sannan ya juya ya fita. Komawa yayi dakin shi ya haye kan gado domin kuwa he was so exhausted. Washegari kuwa tun da safe wuraren qarfe bakwai ya fice. Tun safe suka duqufa.. Cikin ikon Allah kuwa daf da sallar Magrib ne suka shawo kan matsalar. Basu bar ofis din ba sai da suka yi modifying security codes din ma'aikatar. *************** MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Wuraren qarfe tara na dare ne ya shigo gidan. Kamar kullum dai gidan shiru. Zaka rantse babu kowa a ciki.. MK dai dukda ya leqa Ummi jiya sossai yake missing dinta.. dukda aikin da ya dauke mishi hankali tana nan maqale a zuciyar shi, daidai da second daya bata fita daga tunanin shi ba musamman after what happened between them a wannan daren. STORY CONTINUES BELOW Har zai wuce sashen shi sai kuma ya dawo ya nufi sashen ta.. Ya qwanqwaso qofar ya ji shiru don haka ne ya bude tare da yin sallama ya shiga. Bai ganta a dakin ba amma ya ji motsi a bathroom wanda ya tabbatar mishi da tana ciki. Wucewa yayi ya fita.. Fitar MK ba da dadewa bane Ummi ta fito daure da towel yayinda na ga ta tsaya cak a dalilin jin qamshin turaren nan da take bala'in so.. turaren MK. Cike da mamaki na ji tace "Ya shigo dakin nan ne ko dai ni ce nake kewar shi??"3 Gani nayi tayi murmushi yayinda ta nufi vanity table dinta. Zama tayi akan stool ta fara shafa mayyukan ta masu qamshin gaske.. daga nan kuma ta shafa turarruka sannan ta fesa sprays.. nan da nan dakin ya dauki qamshi. Miqewa tayi ta nufi closet dinta... straight wurin kayan baccinta ta nufa, ta dade tana neman wadda zata sa.. Gani nayi ta janyo wata gajerar Babydoll nightie yayinda ta qura mata idanuwa. Ji nayi tace "toh ni yanzu ma zan iya sa wannan kuwa??" Da ta tuno maganganun Fatima ne sai ta saki ajiyar zuciya yayinda ta nufi gaban dressing mirror ta zura nightie din. qare ma kanta kallo take yi yayinda tayi masifar kyau. Gani nayi tayi murmushi sannan ta fita. Gaban Vanity Mirror ta koma ta dauki comb ta fara taje gashin kanta wanda yake ta zuba qamshi.. sakin gashin tayi a haka ba tare da ta daure shi ba.. Wasu turarukan ta qara dauka ta fesa sannan ta janyo hijabin sallanta ta fita. ************ Qirjinta yana ta dukan uku-uku har ta qaraso qofar dakin shi. A hankali ta qwanqwaso qofar sannan ta shiga. MK wanda yake zaune a kan gadon shi yana latsa wayar shi yayinda yake shan Cappucino ne yayi saurin dago kai ya ga Ummi tsaye a bakin qofa. Sossai ya cika da mamaki. Murmushi ta sakar mishi wanda yayi saurin mayar da idanuwan shi kan wayar shi ba tare da ya mayar mata da murmushin ba.4 Ummi wadda take tsaye zuciyarta ce ta buga a dalilin ganin yadda MK ya basar da ita. Jikinta a sanyaye ta qarasa shigowa dakin yayinda ta nufi wurin shi. Gefen shi ta tsugunna har qasa yayinda tace "Hamma don Allah kayi haquri.." MK dai mamaki ne ya cika shi yayinda ya ji wani irin sanyi a zuciyar shi.. dukda haka kuwa bai nuna ba... Miqewa tayi tsaye ta cire hijabin da ke jikinta ta jefar sannan ta duqo ta qwace wayar hannun shi ta jefar a gefe ta haye bisa cinyar shi tace "Please Hamma... I am sorry"5 Cike da mamaki MK yake kallonta.. first time da Ummi take yi mishi turanci straight up. it came out from her mouth fluently.. how beautiful!! Babydoll nightie din da ta sanya sossai tayi mata kyau.. Ga wani asirtaccen qamshi da take yi. Idanuwan shi da suka sauka akan qirjinta kuwa kasa cire su yayi domin kuwa rigar tayi revealing cleavage dinta.. Bai ankara ba ya ji tace "Hamma I love you.."1 Zaro idanuwa yayi yayinda na ga kuma yayi murmushi... Kafin yayi magana ne ya ga ta matso daf da shi tana shirin yi mishi kiss... Gani nayi yayi saurin kaucewa yayinda ya tura ta baya. Cike da mamaki tace "Hamma baka haqura ba?" STORY CONTINUES BELOW Ji tayi yace "bude bakin ki in gani" Cikin rashin fahimta ta bude yayinda yake ta leqa cikin bakin nata kamar me neman wani abu. Daga nan kuma ya kamo hannuwan ta guda biyu yana inspecting finger nails dinta.. Tana kallon shi tace "Hamma me kake nema??" Yace "ina qoqarin tabbatar da ke din ba vampire bace"3 Cikin rashin fahimta tace "meye Vampire?" Yace "wasu halittu ne masu tsinin haqora da dogayen qumba.. idan suka cije ka sai ka sha wahala. kin ga haka kika dinga cizo na ranan duk kin ji mun ciwo" Sagala hannuwan ta tayi a wuyan shi tana dariya tace "ni ba vampire bace Hamma.. don Allah kayi haquri ka ji?" Bata jira komai ba ta hada bakin ta da nashi yayinda ta fara isar mishi da saqonnin da suka birkita shi gaba daya. Tuni ya matse ta a jikin shi yayinda ya karbi saqon nata cike da farin ciki.1 A hankali ta tura shi ya kwanta a kan gado wanda ta haye shi amma kuma yayi saurin dakatar da ita yace "Baby wait... kin ga fa kar in zo in qara yi miki irin na shekaran jiya ki ce na ji miki ciwo zaki tafi ki bar ni... dagaske idan kika tafi kika bar ni mutuwa zanyi" Ummi wadda ta cire nightie din jikinta ce ta kwanto jikinshi tare da fadin "Hamma don Allah mu yi... nima fa idan na tafi na barka wallahi mutuwa zanyi. Bala'in sonka nake yi Hamma don haka bazan taba tafiya in bar ka ba.."7 Aikuwa daga nan suka fara hidima da juna... soyayya ce mai zafi suka gurza, Ummi dai sossai ta ji dadin abinda ya wakana a tsakanin su ba kamar shekaran jiya ba.. Sun haukata juna sossai.. albarka dai Ummi ta kwasa babu adadi.. Babban burin Ummi shine ta ga ta faranta ma MK, Sossai ta ji dadin yadda ta sanya shi farin ciki marar misaltuwa.. Rungume da juna suka yi bacci mai dadin gaske a yau... Har aka yi kiran sallar asuba basu farka ba... sai wuraren qarfe shida na safe ne suka farka.. tare sukayi wanka suka dauro alwala... Bayan sun shirya ne suka yi sallah sannan suka koma kan gado maqale da juna. A haka har bacci ya kwashe su. A yau dai through out suna maqale da juna.. hatta ofis MK bai je ba tunda dama yayi overworking kanshi already the previous days. Haka suka dinga kwasar soyayya iri-iri. ************ Wuraren qarfe tara na dare tana zaune a kan kicin island riqe da robar ice cream tana ta sha. A yadda take sha da sauri sauri zaka rantse satar shi tayi bata so a kama ta. Sanye take cikin wata Red baby doll nighty wadda ta bala'in yi mata kyau.. gaba daya cleavage dinta a bayyane yake.. Gashin kanta wanda ya sha gyara ya kwanta a bayan ta... sai baza qamshi take yi. Tayi nisa a shan ice cream din ne ya shigo kicin din.. Ganinta zaune bisa Island din ya bashi mamaki matuqa.. why is she not sitting on one of the chairs?? must she climb on top of the Island?? how weird .. he thought!! Gani nayi ya dan bata rai yayinda yayi gyaran murya wanda hakan ya razana ta... Kadan ya rage ta saki robar ice cream din saboda tsoro. In a confused state tace "Hamma don Allah kayi haquri... wannan shine na qarshe" A yau dai Ummi ta sha ice cream ya kai roba biyar kenan.. A yanzu haka ya hana ta sha ne saboda mura shine ta shigo kicin tana sha a boye.. Qarasowa yayi wurinta ya zauna a kujerar da take kusa da ita tare da fadin "Ni dai babu ruwana idan mura ta kama ki likita kawai zan kira yayi ta zabga miki allura" STORY CONTINUES BELOW Kashe mishi ido daya tayi yayinda ta matsa daf da shi ta duqo tayi mishi kiss a kumatu tare da shafa fuskar shi tace "I love you Hamma.." Hararar ta yayi yace "ni zakiyi ma siyasa?? da kike fadin I love you dinnan ma kin san ma'anar shi??"1 Tana murmushi tace "Ina son ka ko???" Zaro idanuwa yayi yace "wa ya fadi miki??" Ta dago cokalin ice cream ta kai saitin bakin shi tace "babu kowa Hamma... zaka sha?" Girgiza kai yayi alamar a'a Turo baki tayi tace "please...." Murmushi yayi yayinda ya bude baki ta sa mishi. A haka ta cigaba da sha sannan tana bashi a baki shima. Ji nayi yace "toh yanzu meyasa kika zauna a nan sama bayan ga kujeru.." Tana murmushi tace "haka kawai Hamma" Ta dauko spoon din Ice cream zata kai bakin shi ne na ga ta kalli kofa inda ta hango Maleeka tsaye ran ta a bace yayinda take ta cika tana batsewa. Bayan ta bashi ta mayar da cokalin cikin robar zata debo wani ne na ga ta kalli MK sannan ta kalli robar ice cream din.. Kalaman da Maleeka ta taba yi mata ne ta tuno inda tace "Haka kawai bazan bari ka hada jiki da rainon qazantar qauye sannan ka hada naka da nawa ba..." Ban ankara ba na ga Ummi ta debo ice cream din wanda a maimakon ta kai bakinta sai kawai ta saki cokalin a bisa cleavage dinta yayinda tayi saurin fadin "ouch"8 MK wanda yayi saurin miqewa ne yace "ya haka Baby.." Har ya kai hannu zai goge mata sai kuma ya kai bakin shi kan cleavage dinta ya sa harshe ya fara lashewa. She was happy da MK ya qarasa gyara mata plan dinta.. she didn't expect he'd do that!! Wata 'yar qara ta saki cike da jin dadi abinda yake yi mata yayinda ta rungume kan shi ta dora hannunta bisa gashin shi tana ta birkitawa... Idanuwan ta a lumshe tana ta sauke numfashi. MK wanda yayi nisa kuwa tuni ya canza salo yayinda Ummi ta fara haukacewa.. tuni ta manta cewar wata wai ita Maleeka tana kallon su..4 Gani nayi Maleeka ta koma da baya yayinda ta bar wurin da sauri ta nufi sashen ta. Dakinta ta shigo cike da tsananin tashin hankali.. Zuciyarta ce take ta zafi yayinda wani mugun kishi yake addabarta.. A yau ma kukan ya qi zuwa kwata-kwata.. duk yadda ta so ta zubar da hawaye ta kasa.. Abinda take gudun gani a gidan shine ta gani.. the question is why does she always appear duk lokacin da suke tare???2 Gani nayi tana ta kai da komowa a dakin kamar mahaukaciya yayinda na ji tana fadin "I cant stand this anymore... wallahi bazan iya ba.."2 Komawa tayi bisa ottoman din gadonta ta zauna tare da dafe kai. Kamar wadda akayi ma shocking sai gani nayi ta miqe da sauri ta nufi Closet dinta ta dauko akwati ta fara zuba kayan ta a ciki. Ji nayi tace "I am not staying here anymore.. I have to leave this house yanzun nan.. dolen shi ne ya biyo ni"11 really???🤔 Daga nan kuwa sai na ji ta fashe da kuka... Irin kukan nan marar sauti wanda ake yin shi yayinda zuciya take azabar quna..1 A haka ta hada akwatinta ta bar gidan.. ♧♧♧♧♧♧♧♧ ALIYU SODANGI RESIDENCE MAITAMA Zaune suke a falon Daddy suna hira a lokacin da ta shigo a hargitse. Gaba dayan su sun cika da mamakin ganin ta. Mummy tayi saurin miqewa ta riqo ta tare da fadin "Maleeka lafiya? ya haka? ina MK din??" Cikin kuka tace "Mummy wallahi bazan iya zama a gidan ba.." Daddy wanda yake kallon ta ne yace "akan wane dalili??" Mummy ta janyo ta suka zauna yayinda Maleeka tace "Daddy wallahi Honey baya so na kuma.. kullum yana maqale da yarinyar nan, wulaqanci suke yi mun. Kullum yana cikin masifa da zagi na sannan har mari na yayi saboda yarinyar.. yanzu haka hatta kwana na duk ya bata"1 Nikuwa nace what??10 Tunda ta fara magana suke kallon ta. Daga Daddy har Mummy basu gamsu da zancen Maleeka ba.. musamman Mummy wadda ta san mugun kishin Maleeka... ita ta ma ga qoqarin ta da ta zauna tsawon lokaci ba'a jiyo wata rigima ba. Daddy yayi gyaran murya yace "yanzu kina nufin dan uwanki MK ne yayi miki haka??" Cikin kuka tace "eh Daddy.." Kai tsaye Daddy yace "tashi ki tafi sashen ki" Cike da jin dadin response din Daddy ta miqe ta wuce sashen ta yayinda suka bi ta da idanuwa. Bayan ta shige ne Mummy tace "wallahi yarinyar nan bata jin magana... yanzu fa daga jin wannan bayanin nata ka san qarya take yi" Daddy ma dariya yayi yace "Allah yasa ba wata muguntar tayi ma yarinyar ba ta gudo.. " Ya kalli agogo sannan yace "Allah ya kai mu gobe MK din yazo mu ji abinda ke faruwa tunda dare yayi yanzu" ♧♧♧♧♧♧♧♧ Washegari!! Zaune suke a falon yayinda yake sauraron Mummy wadda ta fadi dukkanin abinda Maleeka ta fada jiya. Tunda Mummy ta fara magana MK yake kallon Maleeka cike da mamaki. Bayan Mummy ta gama magana ne MK wanda yake kallon Maleeka yace "abinda ya faru kenan??" Dago kai tayi tana kallon shi yayinda hankalinta yake a tashe.. ita fa ta san qarya tayi toh amma what was she supposed to do?? Gani suka yi ta fashe da kuka yayinda ta matsa kusa da shi tace "Don Allah honey ka saki yarinyar nan.." Mummy ta kalli Daddy wanda shima ita yake kallo. Ban ankara ba na ga Daddy ya miqe yayinda ya nufi wurin Maleeka zai zabga mata mari amma kuma MK yayi saurin kare ta yace "Daddy don Allah kayi haquri.." Tuni Maleeka ta firgice yayinda take ta rusa kuka. Cikin masifa Daddy ya nuna ta da yatsa yace "dan ubanki mu zaki raina ma wayau?? tun jiya da kika yi mana bayanin mun sani sarai qarya kike yi.." Ya nuna MK yace "kin ga wannan?? Dan uwanki ne wanda yake son ki tsakani da Allah.. nayi imani da Allah bazai taba cutar da ke ba.. da kike fadin ya saki matar shi ke meyasa bazai sake ki ba? wannan rashin mutuncin naki ya isa haka nan.. wallahi idan kika cigaba da wannan iskancin zan raba auren ku.. Gidan shi kuma idan kin ga dama kar ki koma, ki cigaba da zama a nan din. Daga ni har Mummyn ki bazamu qara sa bakin mu a al'amarin ki ba.."7 STORY CONTINUES BELOW Ya kalli MK yace "kai kuma idan ka gaji da auren ka aiko mata takardar sakinta.. ni na baka wannan damar" Zuciyar Maleeka ce ta buga da jin wannan zancen.. A yadda take bala'in son MK idan ya sake ta ai sai ta mutu. Jikinta yana rawa cikin kuka tace "Daddy please.." Dakatar da ita yayi yace "just leave my sight Maleeka.." Tana kuka ta tashi ta bar falon yayinda Mummy ta dinga zabga mata harara cike da takaici. MK dai sossai Maleeka ta bashi haushi.. after all she has done, ya haqura sannan ya buqaci su cigaba da zama lafiya amma ta qi. Tabbas zai iya yin komai just to make her happy.. She wants Ummi out of his life but it's not possible.. Miqewa yayi ya bi bayan Maleeka ba tare da yace ma su Mummy komai ba. Bayan ya bar falon ne Mummy ta kalli Daddy tace "ka ga fa yanzu haka bin ta yayi don ya lallashe ta... ni wallahi da zai biye mun ya fita batun ta idan ta gaji zata koma da kanta" Daddy yana dariya yace "baki ga yadda hankalinta ya tashi ba da ta ji nace ya aiko mata da takardar saki idan ya gaji?" Mummy tana dariya tace "ai Maleeka bala'in kishi ne da ita.. ga taurin kai na bala'i kamar sauran mutanen zamanin farko" Haka dai suka cigaba da hirar su like nothing serious is happening to their daughter.2 toh kuma dai dagaske nothing serious is happening to her.. or is there???4 ************ Kwance take a kan gado tana kuka a lokacin da ya turo qofar dakinta ya shigo. Qarasowa yayi gefen ta a kan gadon ya zauna yana kallonta. He just don't know what to do about her anymore.. for crying out loud he is still very much in love with her.. Me yasa bazata gane hakan ba ta kwantar da hankalinta su cigaba da zaman lafiya?? Ajiyar zuciya ya saki sannan yace "Babe what you did was very wrong.. coming to your parents and telling them lies was very wrong.. kin sa iyayen ki sunyi fushi suna ta yi miki fada.. why?? fisabilillah have I ever lay a hand on you?? ni na hana miki kwanan ki na ba Ummi? ba ke da kanki kika ce baki so ba? was I suppose to force you to sleep with me?? Na sani cewar ba kya son Ummi, ba kya son Ummi saboda kina kallonta a matsayin low class, ba kya son Ummi saboda na aure ta, Ba kya son Ummi saboda ina son ta.. kiyi haquri life turned out this way. Ni kaina I never thought zan iya rayuwa da wata macen da ba ke ba amma the circumstances were such that.."2 Tashi tayi zaune cikin kuka tace "don Allah Honey ka manta da wasu circumstances.. ba na baka haquri ba? wallahi zan gyara hali na.. na shirya haifa maka Babies ko nawa kake so.. kawai ka taimaka mun ka sake ta.." Girgiza kai yayi cikin fada yace "just quit this childish attitude of yours and face reality already... na fadi miki bazan iya rabuwa da Ummi ba.. I love her.."2 Ankara yayi da tone din da yayi using yayinda na ga ya saki ajiyar zuciya ya riqo hannun ta yace "I love you too my Babe.. please ki tashi mu koma gida, kiyi haquri ki kwantar da hankalin ki.. you dont even need to do anything against your wish, I still and will forever love you for who you are.. I assure you komai will be okay"2 Qwace hannun ta tayi daga nashi tace "I am not coming back... just leave me alone" yayinda ta koma ta kwanta tana kuka.5 Miqewa yayi yace "fine.. idan haka kike so shikenan.. kamar yadda na fadi miki a baya I will be there whenever you need me.. you know where to find me.. ni na tafi"3 Daga nan ya fice abinshi.3 ♧♧♧♧♧♧♧♧ Tun daga wannan ranar MK bai qara bi ta kan Maleeka ba. Wasa-wasa kuma ta qi komawa gidan shi.. tana nan akan lallai bazata koma ba har sai ya saki Ummi. STORY CONTINUES BELOW Abba da Mamy sun yi qoqarin sasanta al'amarin amma Daddy yayi dismissing case din.. a cewar shi a qyale ta a ga iyakar gudun ruwan ta.. Maleeka is just the type that needs to learn the hard way.. ya tabbatar bazata taba iya rabuwa da MK ba domin bala'in son shi take, idan ta gaji da zama a gidan zata koma gidan mijinta da kanta. Haka take zaune a gidan cikin tsananin damuwa.. Kullum tana cikin tunanin MK yana can tare da yarinyar, tana picturing kalolin soyayyar da suke sha yayinda take qara shiga tashin hankali. Tabbas hasashen Maleeka dagaske ne.. MK yana can shi da Ummin shi suna ta kwasar soyayya iri-iri. A kullum qara shiga ran shi take yi... Sossai take kyautata mishi, Duk wani abu ita take yi mishi.. ta mayar da shi kamar wani qaramin yaro.. Rabon da Migraine din MK ya tashi har ya manta domin kuwa kullum ya dawo daga ofis sai ta yi mishi massage wanda yake bashi soothing relief tare da cire mishi gajiya gaba daya. Ita dai Ummi ta san cewar Maleeka bata gidan kuma bata yi tambayan ta ba.. ita kam babban abinda ya dame ta a rayuwa shine MK kuma tana tare da shi.. any other thing to her is insignificant.. Tuni MK ya kai Goggo gidan Abban shi sun gaisa... sossai Goggo ta dinga yi musu godiya na hidimar da MK... sun qulla zumunci mai qarfi a tsakanin su tunda dai they are in-laws. Ummi dai ta zama 'yar gaban goshin Mamy da Abba.. Sun kula da irin kyautatawar da take yi ma dan su wanda da ka gan shi kasan hankalin shi kwance yake unlike kafin yayi aure da lokacin da yake auren Maleeka. Albarka kuwa tana shan ta lodi-lodi. Tuni Ummi ta waye ta zama babbar yarinya.. Fatima ta gyara ta gaba daya. A yanzu haka idan ka ga Ummi zaka rantse wata 'yar gidan shugaban qasa ce saboda bala'in canzawa da tayi. da ka ganta ka san lallai tana hutawa. ♧♧♧♧♧♧ Weeks later!! LANESBOROUGH HOTEL LONDON-ENGLAND A yau kusan watan su daya da zuwa London. MK dai ya zo halartar wani taro ne na manyan software engineers wadanda suka zo daga qasashe daban-daban. Tare da Ummi yayi tafiyar domin kuwa a yanzu haka MK baya iya yin nisa da ita na tsawon lokaci... Yayi mugun sabawa da Ummi domin kuwa komai ita take yi mishi. Taron yayi lasting for three days.. bayan an gama kuwa suka yi zaman su don su huta. Wannan shi ya kasance first time da Ummi ta zo qasar waje.. bata taba tunanin zata je qasar waje ba a rayuwarta sai gata a cikin turawa birjik. Sossai ta cika da murna.. MK ya kai Ummi wurare dayawa a qasar.. tayi murna sossai... tambayoyi kuwa ya sha su babu adadi... Sunyi shopping dayawa.. Ummi dai a kullum mamakin yawan kudaden da MK yake da su take yi, har magana tayi mishi ganin yadda yake kashe kudi amma inaaa.. kamar ma qara ziga shi take yi ya kashe su. Wuraren qarfe takwas da rabi na safe suna kwance a kan gadon dakin su na hotel din suna bacci. Kwance suke a kan pillow daya yayinda suke fuskantar juna.. sun rufa a cikin wani lallausar Duvet. Ummi ce ta farka tare da yin addu'ar tashi daga bacci. Ajiyar zuciya ta saki yayinda na ga ta sanya mishi idanuwa tayi murmushi.. Rayuwarta na baya take tunowa har zuwa yanzu yayinda take qara gode ma Allah kamar kullum na yadda ya sauya mata rayuwa daga kalar wahala zuwa wannan wadda take ciki. Haka ta cigaba da yi MK addu'a shima kamar kullum domin kuwa gaba daya duniyan nan bata da tamkar shi. STORY CONTINUES BELOW Gani nayi ta qara matsawa daf da shi ta sa hannunta tana shafa gashin kan shi zuwa sajen shi zuwa gemun shi tana da wasa da su.. Motsi ya dan yi ba tare da ya bude idanuwan shi ba yace "Baby kin fara ko??" Murmushi tayi sannan tace "yi haquri Hamma.." Ummi dai a kullum idan tana kusa da shi zaka ga tana wasa da gashin shi.. A dalilin bala'in son wasa da gashin shi ne ya sa bata gajiya da yi mishi massage. Ji tayi yace "idan mun fita anjima zan je a aske mun gashi na duka sai in huta" Cikin shagwaba tace "Hamma don Allah kayi haquri kar ka aske.." Har yanzu idanuwan shi a rufe yana murmushi yace "wasa nake Babyn Hamma" Bude idanuwan shi yayi yana kallonta yace "Baby ina so in tambaye ki.. akwai sana'ar da kike buri kiyi a rayuwar ki??" Cikin rashin fahimta tace "Hamma kamar me??" Yace "kamar komai ma.. irin shopping mall- wurin sayar da kayan ciye ciye da sauran su, eatery- kamar gidan abinci, makaranta, Asibiti da koma menene" Tana murmushi tace "bana son komai Hamma.. ni fa kai kadai nake so"1 Kumatun ta ya ja sannan yace "Kin gama samu na Baby amma baki isa ba.. dole ne sai kin fadi mun abinda kike sha'awar mallaka a rayuwar ki.. ki fadi mun ko ma meye.." Shiru ta dan yi sannan tace "Hamma ka ga a rayuwa ta ina so in ga ina tallafa ma Yara marayu da kuma yara wadanda iyayen su basu da qarfin ciyar da su.. toh amma ka ga wannan kashe kudi ne wanda babu riba ba kamar sana'a ba ko??" MK dai gani nayi yana ta murmushi yayinda yayi shiru yana kallonta. Gashin gaban goshinta ne ya shafa sannan yace "kin san meyasa nake qara son ki?" Ta girgiza kai alamar a'a. Yace "saboda kina da zuciya mai kyau, kina da hankali sannan kina da tunani.." Tana murmushi tace "nagode Hamma" Yace "kar ki damu insha Allah zan cika miki burin ki.. Zaki mallaki Charity foundation naki na kanki wanda zai dinga taimaka ma yara marassa galihu.. riba kuma itace ladar da zaki samu daga wurin Allah" Cike da mamaki da kuma tsananin murna tace "dagaske Hamma??" Ya rungume ta yace "yes my Baby" Lumshe idanuwa tayi sannan tace "nagode sossai Hamma.. Allah ya qara budi, Allah kuma ya saka maka da gidan aljannah.." Gani nayi ya tura kan shi cikin duvet din da suka rufa.. Ban ankara ba na ji Ummi tace "Ouch Hamma.." daga nan kuma ta fara dariya yayinda itama ta tura kanta cikin duvet din. ************* Sai da su Mk suka qara sati biyu a Ingila sannan suka fara shirin dawowa gida. A ranar da zasu tafi kuwa bayan sun gama shirin su tsab sukayi checking out of the hotel yayinda suka wuce Airport straight. ************* HEATHROW AIRPORT LONDON MK ne tsaye yayinda yake rungume da Ummi yana magana da wani bature. Ummi dai tun kwana biyu da suka wuce take jin jikinta babu dadi amma a dalilin bala'in tsoron allura sai ta qi fadi ma MK.. sannan ga guntun baccin da take yawan yi.6 Shi kanshi ya kula da yawan baccin nata.. ko da yayi mata magana sai cewa tayi laifin shi ne da yake hana ta yin bacci cikin dare. Tabbas ya sani yana hana ta bacci cikin dare don haka sai ya dinga bata haquri. STORY CONTINUES BELOW A yanzu haka da suke tsaye wani irin bacci take ji shiyasa ma take maqale a jikin shi. Bayan sun gama magana da baturen ne ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace "Baby ya na ji kamar duk kinyi laushi ne?" Idanuwan ta a lumshe tace "Hamma sai yaushe zamu tafi? ni fa bacci nake ji" Cike da mamaki yace "bacci kuma Baby?? ba yanzu kika tashi daga bacci ba shine muka fito?? anya lafiyar ki kuwa?" Da sauri tace "lafiya na lau Hamma" Janyo ta yayi yace "mu je toh mu zauna kafin su gama cike documents din" Suna daf da qarasowa wurin wasu kujeru ne ta hango su. Jameela wadda tayi turus tana kallon MK da Ummi sossai tayi mamakin ganin su. Mamaki take sossai na yadda Ummi tayi masifar canzawa, tayi qara haske tayi kyau.. idan ka kalle ta zaka rantse balarabiya ce. Da sauri ta qaraso wurin su yayinda tace "Ya MK ina wuni" MK ya kalli Jameela yace "whoa.. Jay ya kike?" Ummi wadda take maqale a jikin shi ce ta dago da sauri ta kalli Jameela wadda tace "lafiya lau" Ta kalli Ummi tana murmushi tace "amaryar mu" Ummi ta dan russuna tace "Adda ina wuni" Jameela wadda take ta murmushi ce tace "ki rufa mun asiri ki daina russunawa Ummi.. ni kam ai kin fi qarfin yin hakan yanzu.." MK wanda yake murmushi yace "tell me, what are you doing here?" Jameela tace "wallahi gida zan tafi.. ka san na gama course dina ai. I am going back home ne gashi kuma wai na ji ance za'ayi delaying flight din mu sai zuwa da daddare" MK yace "oh wow.. congrats" Tace "thank you" Yace "well, mu yanzu zamu tafi, why not ki bi mu tunda a jet dina muka zo.. yanzu haka muna jira ne pilot dina ya gama signing wasu documents ne sai mu tafi" Cike da murna Jameela tace "aikuwa nagode Ya MK" ********** A cikin jirgin dai MK yana rungume da Ummi kwance a jikin shi tana ta bacci.. wannan ne ya sanya ya kwantar da seat din to a comfortable position yadda zata ji dadin baccin. Jameela da take zaune nesa da su kadan tana kallo wani Movie.. amma fa lokaci-lokaci takan dago kanta ta kalli su MK. Sossai Jameela ta tausaya ma qawarta tare da yin tir da halinta na ko in kula da take yi ma MK.. she would have been the one with him right now... she would have been his only wife at the moment.. she would have been the one to fulfil his biggest dream a rayuwar nan- Give him a child!! Bata ankara ba ta ga MK ya miqe riqe da Ummi a hannun shi yayinda ya kai ta one of the rooms na jet din. Kwantar da ita yayi bisa gado sannan ya rufe ta da Duvet. Ko da ya fito komawa yayi kusa da Jameela ya zauna yayinda suka fara hira. A cikin hirar ne Jameela tace "amma ni kam sai na ga kamar Ummi bata da lafiya ko?" MK wanda shima a yanzu ya fara tunanin lallai batada lafiya ne yace "I think so honestly.. though when I asked her she said she is fine" Ya dan yi murmushi yace "kin san matsoraciyar allura ce" Jameela tayi murmushi yayinda tace "ai Allura bata da dadi Ya MK.. Allah dai ya qara mana lafiya" Yace "ameen" STORY CONTINUES BELOW Jameela tace "ashe an matso da bikin Hafsah sooner than yadda akayi scheduling.." MK yace "Yeah.. yanzu saura 5 weeks.. Sadiq, mijin da zata aura ne zai je Switzerland yin wani course tsawon 3 years so shine ya roqi alfarmar ayi bikin kawai su tafi tare" Jameela tace "Allah sarki.. Allah ya kai mu rai da lafiya" Yace "ameen" Daga nan ne suka dan yi shiru na lokaci. Jameela tayi gyaran murya yace "hey I heard my friend is at her parent's house ko??" Girgiza kai yayi yace "yeah Jay......." ♧♧♧♧♧ Washegari!! ALIYU SODANGI RESIDENCE MAITAMA Kwance take a kan cinyar Jameela yayinda take ta kuka tana sauraron ta. Jameela dai jiya sunyi maganganu sossai da MK akan Maleeka.. Almost through out the journey Ummi bacci take yi.. ko da ta farka ma bata fito daga dakin ba.. Kwanciyarta tayi a kan gadon yayinda ta cigaba da buga game a wayar ta. Daga baya ne MK ya baro Jameela a lounge na jirgin yayinda ya dawo wuri Ummi suka yi cuddling suna hira har suka iso Nigeria. Har gida suka sauke Jameela sannan suka tafi. Ji nayi Jameela tace "Wallahi Leek Ya MK still loves you.. I am surprised ma da na ji son da yake yi miki is still intact.. tabbas soyayyar ki a cikin jinin shi take domin kuwa babu wanda za'a yi ma irin laifin da kika yi mishi sannan ya cigaba da son ki har haka..." Shiru ta dan yi sannan ta cigaba da fadin "...kin sani cewar baya ganin laifin ki a dukkanin abubuwan da kika yi mishi?? do you know that the poor soul still blames himself for everything that is happening?.." Tana shafa gashin Maleeka tace "...we both know cewar it was never his fault.. Allah ma ya sani Ya MK yayi qoqarin zama tare da ke da hanlin ki.. You are supposed to be a good person Leek, Maganar gaskiya you are a good person.. Babban matsalar ki shine Girman kai da gadara, kina da principles.. You are just like a hard rock that is so difficult to crack. Well, from what we discussed yesterday da shi i have deducted that you still have a chance with him.. kawai..." Da sauri Maleeka ta tashi zaune tace "Jay wallahi wannan baqauyar yarinyar ta mallake shi.. Idan kin ga irin soyayyar da suke yi zaki sha mamaki.. she has taken over him completely, baya gani na da mutunci ko alama" Jameela ta girgiza kai tace "Leek ba mallake shi tayi ba.. Kyautatawar da take yi mishi shine ya sanya shi yake ji da ita da har kike kallon hakan a matsayin an ci mutuncin ki..." Ta dan yi tsaki tace "for crying out loud Leek I know what your problem is, kina so ya rabu da yarinyar ne saboda baqin kishin ki.. ba kya so kiyi sharing duk wani abu naki a duniyar nan. ba tun yau ba kin sani bazai rabu da ita ba tunda dai yace yana son ta.. ba ma sai ya fada ba wallahi, it's obvious he loves her.. kuskure dai kin riga kin yi shi don haka kamar yadda nake fadi miki kullum dole ne kiyi haquri ki rungumi qaddarar ki a yadda ta zo miki" Jameela ta harare ta tare da fadin "ni na kula ma kamar yarinyar ciki ne da ita.. gaba daya tayi laushi ga bacci da na ga tana ta yi. Da alama ma bai sani ba"1 Zuciyar Maleeka ce ta buga da jin maganar qawarta..1 Jameela ta girgiza kai sannan ta cigaba da fadin "..finally she might just be the one to make his dream come true.." Gani nayi Maleeka ta sauka daga kan gadon ta ruga ta shiga bathroom tana kuka. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO Tsaye yake a gaban Vanity mirror na dakin shi yana qarasa shiryawa don zuwa office. A yau kwana biyu kenan da dawowar su daga qasar Ingila. Ummi ce kwance a kan gado cikin Duvet tana ta kallon shi.+ Bayan ya gama shirin shi tsab na ga ya juyo ya kalle ta yana murmushi ya nufi wurinta bisa gadon ya kwanta a gefenta. Gani nayi ya sa hannu ya shafa gashin gaban goshinta sannan yayi mata kiss a baki yace "yi haquri na tada ki" Tana murmushi tace "kar ka damu Hamma na.. har ka gama shiri?" Yace "yes Baby.." Ta yunqura zata tashi zaune tace "mu je in baka abu ka ci kafin ka tafi toh.." Da sauri ya dakatar da ita tare da mayar da ita ya kwantar da ita sannan yace "kar ki damu.. zan hada Cappuccino in sha.." Tace "Haba Hamma.. Cappuccino kawai?? wurin aiki fa zaka je" Ya ja kumatunta tare da fadin "ai bazan dade ba zan dawo... da na gama meeting din zan dawo Insha Allah" Murmushi tayi tare da janyo shi ya kwanto a jikinta ta fara baza mishi kisses masu dauke da salo na soyayya.. A hankali suka dinga smooching juna. Ganin MK ya yaye Duvet din da ta rufa da shi yayinda yayi nisa ne ta yi saurin riqe hannuwan shi. Zare bakinta tayi daga nashi tace "Hamma.. ka manta fita zaka yi??" Ajiyar zuciya ya saki sannan yace "Baby toh ko in fasa ne??" Tana dariya tace "babu ruwana.. ka je ka dawo dai, ina nan ina jiran ka" Da qyar fa MK ya haqura ya qyale Ummi suka yi sallama ya tafi. Ko da ya bar dakin juyawa yayi zata fara wani baccin. A yanzu dai Ummi ta fara damuwa da yawan baccin da take yi.. Ga wata muguwar kasala da take saukar mata... she has become lazy da har yawanci abubuwan da take yi a baya bata iya yin su yanzu. Misali MK ya gama shirin shi tsab ya fita amma bata iya taimaka mishi ba kamar kullum sannan hatta breakfast din ta kasa hada mishi.. da wannan tunanin ne har baccin ya kwashe ta. ************ Wuraren qarfe Goma sha daya saura ne ta farka. Bayan tayi addu'ar tashi daga bacci ne ta tashi zaune a bisa gadon. Gani nayi ta dafe qirjinta yayinda ta rufe bakinta.. Zuciyarta ce take masifar tashi. Ummi dai a yanzu ta tabbatar akwai matsala.. gaba daya jikinta bata jin dadi. Da qyar ta sauko da qafafuwanta daga kan gadon ta miqe tsaye.. Ta taka qafarta kenan jiri ya kwasheta ta zame ta fadi a qasa... toh fa!! ************ Wuraren qarfe goma sha biyu ya shigo gidan.. Da ganin fuskar shi ka san hankalin shi a tashe ne.. Bayan ya fito daga meeting yayi ta kiran ta a waya amma bata yi picking ba wannan ne ya sanya ya baro ofis din ASAP ba tare da ya jira sunyi reviewing abinda akayi discussing a meeting din ba kamar dai kullum. A lokacin da ya bude qofar dakin shi ya shigo ne na ga ya tsaya cak cike da tsananin tashin hankali. Ummi ce kwance a qasa tana ta kuka yayinda take ta juyi tana jero addu'o'i iri-iri. STORY CONTINUES BELOW A guje ya qarasa wurinta ya dago ta yana fadin "Baby lafiya?? me ya.." Kafin ya qarasa maganar shi kuwa ta wanke shi da amai.. Ji nayi yace "subhanalillah.. Baby baki da lafiya shine baki fadi mun ba??" Ummi dai sai kakarin amai take yi yayinda jikinta ya bi ya saki. A rude MK ya kwashe ta sai bathroom.. Sai da ya kimtsa ta ya kimtsa kanshi sannan ya dawo da ita ya kwantar a kan gadon. Da sauri ya dauki wayar shi ya kira Dr. Zeenat. Bayan ya kashe wayar ne ya koma wurin Ummi yayi hugging dinta yace "Baby sannu kin ji.. bari likita ta zo ta duba ki" Idanuwan ta a rufe yayinda hawaye ke ta bin fuskarta tace "nagode Hamma.." ************* hours later... Kwance take a kan gadon dakin tana bacci.. hannunta dauke da cannula ana qara mata ruwa... da ganin yadda take numfashi ka san tana jin jiki. MK ne zaune a gefenta cike da tsananin damuwa yayinda yake riqe da hannun ta.. Idanuwan shi sunyi jajawur, ba sai an fada ba yana cikin tsananin tashin hankali ganin halin da Ummi take ciki. Mamy, Hafsah da Goggo suna nan zaune a dakin cike da damuwa.. Gaba dayan su babu mai iya yi ma wani magana.. banda addu'o'i babu abinda suke yi ma Ummi. Ummi dai har suma tayi kafin likita ta zo. Tana zuwa ta ga halin da take ciki ne tayi setting dinta up. A yanzu haka ta debi jinin Ummi ne yayinda ta koma asibiti don running tests.. Kusan mintuna arba'in kenan da tafiyar Dr. Zeenat amma MK ya kira ta a waya ya fi sau goma. A yanzu haka da ya kira ta ce mishi tayi gata nan zuwa. Bayan ya kashe wayar ne ya jefar tare da yin tsaki yace "I wonder why she is taking this long" Matsawa yayi daf da Ummi ya kwanta a gefenta yana shafa kanta yayinda na ji yana fadin "Ummi don Allah ki dan bude idanuwanki ki fadi mun abinda ke damun ki.." Goggo ce tace "Kabiru kayi haquri mu jira likitar ta dawo sai mu ji.." Hafsah ce tace "matsalar ma yadda har yanzu bata farfado ba.. wannan wane irin ciwo ne haka" Mamy ce tace "Allah dai ya bata lafiya" Gaba dayan su suka ce "Ameen" *********** Dr. Zeenat ce ta shigo. Cikin girmamawa ta gaida su Mamy yayinda ta qarasa wurin Ummi tana duba yanayin jikin ta. MK yana kallon Dr. Zeenat ne yace "hey is the test result ready?? me ke damun Baby na??" Dr. Zeenat tana dan murmushi ta ciro wata envelope daga cikin Jakarta sannan ta miqa mishi tace "congratulations Sir" MK wanda ya karbi envelope din miqewa yayi tare da fadin "what are you saying??? my wife is sick and you are congratulating me? are you...." "She is pregnant.." maganar da ta sa shi yin shiru kenan.2 Gani nayi yayi freezing yayinda ya sa ma Dr. Zeenat idanuwa. She is pregnant!!2 Sakin envelope din hannun shi yayi tare da fadin "wait what??" Dr. Zeenat tana murmushi tace "Your wife is six weeks pregnant Mr. Kabeer" Gani nayi ya zame qasa yayinda ya daga hannuwan shi biyu sama yace "Alhamdulillah... Alhamdulillah.. Subhaanallaahi wa bihamdihi 'Adada khalqihi, wa ridhaa nafsihi, wa zinata 'arshihi wa midaada kalimaatihi.. Subhaana thil-jabaruti, walmalakuti, walkibriyaa'i, wal'adhamati.. finally my dream came true... Ya Allah thank you very much for this gift.."4 STORY CONTINUES BELOW Muryoyin su Mamy na ji suna ta murna yayinda suke ta jero nasu addu'o'in. MK cike da tsananin murna na ga ya tashi ya rungume Mamy yayinda na ji yana fadin "Mamy my dream just came true.. I am going to be a father, Ya salaam, Mamy I am so happy"3 Mamy wadda take rungume da dan nata tace "Allah ya sanya albarka MK, Allah kuma ya bata lafiya ya raba lafiya.. I am so happy zan ga grand child dina" Hafsah wadda take cikin murna ce tace "Congratulations Bro.. finally" Da sauri ya rungume ta itama yayinda suka cigaba da rejoicing. Da ganin yadda MK ya cika da tsananin murna ka san cewar surely this means alot to him. Goggo dai harda hawaye na farin ciki.. yau Umminta ta samu ciki zata haifa ma Hardo (Allah ya jiqan shi) jika. Dr. Zeenat wadda ta duba jikin Ummi ce ta kalli MK tace "She is doing fine... Da zarar ta farka she will feel better" Ya girgiza kai tare da fadin "thank you doc" Dr. Zeenat ta kalli ledar ruwan da ke rataye ta ga ya kusa qarewa.. Kallon MK tayi tace "Can I have a word with you in private sir?" Yace "sure" *************** Zaune suke a falon shi yayinda yake sauraron Dr. Zeenat. Gyara glasses din idanuwan ta tayi sannan tace "How old is your wife?". Kai tsaye yace "seventeen plus..." Ta dan yi murmushi sannan tace "that explains it all.." Cikin rashin fahimta MK yace "is there a problem??" Ta girgiza kai tare da fadin "not really Mr. Kabir.. the thing is matarka is still very young sannan body system dinta is very much fragile.. normally mata suna samun matsala sossai a first trimester dinsu toh amma case dinta might be worse..." MK wanda hankalinshi ya tashi ne yace "ban gane ba.. kina nufin Ummi zata samu matsala a dalilin cikin??" Dr. Zeenat ta girgiza kai tare da fadin "Calm down Mr Kabir.... idan an kula da ita sossai insha Allah both her and her baby will be fine" Runtse idanuwan shi yayi sannan ya bude yace "what do I have to do??" Dr. Zeenat ta gyara zama sannan tace "Matarka tana buqatar hutu sossai... idan da son samu ne kar tayi aiki ko ya yake kuwa. from time to time zan dinga sa ta a bed rest and you will have to ensure she comply... tana buqatar abinci masu gina jiki- proteinous food, again tana buqatar plenty of fruits and vegetables. For now zata rage shan kayan zaqi irin su Ice cream, chocolates da sauran su. Most importantly ayi qoqari a guji duk wani abinda zai bata mata rai ko kuma wanda zai tayar mata da hankali..." MK ne yace "okay, I will make sure of that doc.." Dr. Zeenat tace "and yes.. you should try not to go hard on her in bed because we wouldn't want anything happening to the baby right?" Murmushi kawai MK yayi tare da girgiza kai yace "Its okay doc.. thank you very much... thanks for giving me such a great news.. it is surely the best news I have received all through my life" Dr. Zeenat tana murmushi tace "I could tell from your expression sir" Ta miqe tare da fadin "Bari in duba in gani ko ruwan ya qare sai a cire mata.. Insha Allah anjima zan dawo in duba ta but please take care of her" Yana murmushi yace "I will... thanks again, I am gonna send you a little something later" Ita dai Dr. Zeenat ta san me yake nufi.. kudi ne zai tura mata don haka ne ta dinga zabga godiya. STORY CONTINUES BELOW Hakanan a banza ma MK yana basu kudade masu yawan gaske ita da Dr. Davis a matsayin su na family doctor dinsu balle yanzu da tayi mishi albishir da zancen cikin nan. ************* Bayan sallar la'asar ne Ummi ta farka.. A wannan lokacin kuwa MK ne kadai a dakin.. Su Mamy duk suna falo. MK wanda yake rungume da ita ne yace "Baby kin tashi???" Yana gyara mata gashinta da ya rufe mata fuskarta yace "sorry kin ji??" Gani nayi ta fara yunqurin tashi zaune muryarta qasa-qasa tace "Hamma me ya faru??" Da sauri ya riqe ta tare da fadin "Relax Baby, ya janyo ta jikin shi ya rungume ta yace "kinyi rashin lafiya ne.. yanzu ina ne yake yi miki ciwo??" Ummi wadda ta gyara kwanciyar ta a jikin shi ce tace "Hamma duka jikina bana jin dadi.. ciki na yana ciwo" Kallon hannunta da aka cire ma Cannula tayi sannan tace "ka ga hannu na ma yana yi mun ciwo..." Ya matse ta a jikin shi tare da shafa bayanta yace "yi haquri duk zasu daina.." Dayake dai jikinta babu qwari sai tayi kwanciyarta a jikinshi yayinda ta lumshe idanuwa.. A duk duniyan nan babu wurin da Ummi take jin dadin kasancewa irin tare da MK... A yanzu bata qi su kasance a haka ba har abada. Bayan dan lokaci ne na ji yace "Baby me zaki ci??" Cikin shagwaba tace "Hamma babu komai.. kawai mu tsaya a haka" Murmushi yayi sannan ya gyara mata kwanciya a jikin shi. Hafsah ce ta qwanqwaso qofar dakin ta shigo... tsayawa tayi turus yayinda take murmushi tace "ashe Babyn Hamma ta farka.." bata jira komai ba na ga ta koma. Gani nayi sun shigo dakin cike da murna.. Ummi wadda ta jiyo muryar su Mamy ce ta bude idanuwan ta yayinda ta cika da mamaki.. Ko kafin tayi magana sai ji tayi suna ta yi mata sannu da jiki.. ita dai bin su ta dinga yi tana ta amsawa dukda bata gama gane me ya same ta ba. Su Mamy basu wani dade ba suka yi ma MK sallama... An so a bar Hafsah amma MK yace kar su damu shi zai kula da Ummi... Goggo ce tace "toh ko za'a aiko miki da tuwo ne?" Ummi tace "kar ki damu Goggo.. idan ina jin yunwa zan dafa abinci" Da sauri MK yace "a'a Baby... bazaki shiga kicin ba" Ya kalli Goggo yace "ki aiko mata da tuwon Goggo" Mamy ce tace "don Allah Ummi ki dinga qoqari kina cin abinci yadda yakamata ko don abinda ke cikin ki" Cike da mamaki Ummi ta kalli MK tace "Hamma meye a ciki na?" Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Goggo tace "au.. ashe baka fadi mata ba kenan" Mamy da Hafsah suna dariya ne suka yi musu sallama suka yi tafiyar su.. Aikuwa suna fita Ummi ta janye daga jikin MK ta tashi zaune tana kallon shi tace "Hamma wai me ke faruwa ne?? bani da lafiya shine kuke boye mun ko?? mutuwa zan yi??" Da sauri ya toshe bakinta yace "sssshhhh... Baby lafiyar ki qalau" Gani nayi ya dora hannun shi a kan cikinta yana shafawa yace "ina da Baby a nan ciki.." Zaro idanuwa tayi tace "a ina Hamma??" Ta dora hannunta a bisa nashi tace "kana nufin ina da ciki???" Yana murmushi ya girgiza kai alamar 'eh' Jikinta ne yayi mugun sanyi yayinda ta kasa motsi.. da alama she is confused. STORY CONTINUES BELOW Yana kallonta yace "Baby kin bani babbar kyauta wanda ban taba samun irin shi ba.. babban buri na a duniya in ga dan da zan haifa sai gashi yau kin bani, nagode sossai Babyna, Ubangiji Allah ya saka miki da gidan aljannah, Allah yayi miki albarka...." Ummi dai kallon shi take yi tana ta mamakin yadda ya bi ya cika da murna da yadda yake ta yi mata godiya.. bata taba ganin farin ciki irin wannan a tare da shi ba... Lumshe idanuwa tayi sannan ta rungume shi very tight tace "Hamma don Allah ka daina yi mun godiya.. ni yakamata inyi maka godiya, Ni din da ba kowa ba ka aure ni ka bani dukkan wani abun jin dadi na rayuwa, ka so ni tsakani da Allah.." Da sauri yayi breaking hug din yace "sssshhh Baby.. kar ki qara fadin ke ba kowa bace.." Cupping fuskar ta yayi da hannuwan shi biyu yace "Baby ke ce hasken rayuwata gaba daya.. MK bazai iya yin komai ba idan babu ke.. I love you so very much" Daga nan ya hada bakin shi da nata ya fara kissing dinta... irin kiss din da ke haukata Ummi.. Lumshe idanuwa tayi yayinda ta shiga mayar mishi da salon nata itama wadanda suke birkita shi. Sai da suka yi mai isar su sannan suka natsu. Daga nan fa ya shiga yi mata hirar Babyn da ke cikinta... Ummi kuwa sossai ta cika da mamakin jin labarai kala-kala a wurin MK na abubuwan da zasuyi tare da Babyn bayan ta haihu. Babu abinda take yi banda gode ma Allah da ya bata ikon cika mishi burin shi a duniyan nan. *********** Da daddare ko da Goggo ta aiko musu da Tuwo shi ya bata a baki da kanshi sannan shima ya ci. Duk wani abinda Ummi take so shine yayi mata.. har mamaki take yi na yadda ya hana ta ko tafiya, sai dai shine yake daukar ta ta kai ta duk inda take so. Da ta tambaye shi sai cewa tayi baya so Babyn su yayi ciwo a cikin ta... sossai hakan ya bata dariya. ********** Wuraren qarfe Goma na dare ne ya fito daga bathroom dinshi riqe da ita a hannun shi... Ahankali ya zaunar da ita bisa vanity mirror ya fara shafa mata mai.. bayan ya gama ne ya shiga closet ya dauko mata wata gajerar nightie marar nauyi ya fito ya zame towel din jikinta sannan ya sanya mata. Ummi dai sai kallon ikon Allah take yi yayinda take ta mamaki... a ganinta wahalar da kanshi yake yi tunda dai duk wadannan abubuwan da yake yi mata zata iya yi da kanta. Bayan ya dora ta kan gado ne ya duqo yayi mata kiss a kumatu sannan yace "yanzu me kike so?" Gashin kan shi ta birkita tana murmushi tace "kai nake so Hamma.." Gani nayi yana gyara gashin nashi yana murmushi yace "kin gama samun Hamma.. Ni naki ne Baby, sai yadda kika yi da ni" Ya miqa mata wayar ta yace "buga game dinki kafin inyi wanka in zo" Ta karbi wayar sannan tace "ina nan ina jiran ka" Haka ta bi shi da kallo har ya shige dressing room. Gani nayi tana murmushi yayinda ta shafa cikinta tace "Allah ya bani ikon haifo maka Babyn ka Hamma"15 Nikuwa nace ameen..2 Tana ta buga game har MK ya fito daga wanka.. bayan ya gama abinda zai yi a gaban Vanity mirror ne ya wuce ya shiga dressing room. Bayan dan lokaci na gan shi ya fito sanye cikin three quarter sweatpant da T-shirt... Hannun shi riqe da wani jewelry box mai masifar kyau. Hayewa yayi kan gadon ya qwace wayar hannunta yace "time up" STORY CONTINUES BELOW Turo baki tayi tace "Hamma ban gama ba fa.." Ya ajiye wayar kan bed side drawer sannan ya miqa mata jewelry box din ba tare da yace komai ba. Gani nayi ta karba tare da sanya ma box din idanuwa... sossai ya birge ta. Tana kallon shi tace "Hamma na waye?" Yace "naki ne.. bude ki gani" Da sauri ta bude yayinda wani lafiyayyen zoben diamond ya haske ta.. Zaro idanuwa tayi harda baki yayinda na ga tayi saurin kallon shi tace "Hamma??" Yana murmushi ya ciro zoben yace "bani hannunki" Cike da murna ta miqa mishi yayinda ya sanya mata sannan ya kai hannunta saitin bakin shi yayi mata kiss yace "I love you Umm Aimaan.. ina bala'in sonki.. ki kasance sanye da zoben nan har abada" Ya shafa cikinta tare da fadin "nagode sossai da kika bani wannan kyautar" Ummi tana kallon yadda zoben ya zauna a hannunta yayinda ta lumshe idanuwa. Kallonshi tayi tace "zo nan" yayinda ta ware hannuwanta. Matsawa yayi ya shige jikinta suka yi hugging juna... A kunnen shi ta rada mishi "nagode sossai Hamma... I love you" Daga nan ta hura mishi iska kamar yadda yake yi mata yayinda yayi saurin cafko bakinta da nashi ya fara aika mata da saqon kisses. ************* Bayan sati daya!! ALIYU SODANGI RESIDENCE MAITAMA Zaune take a kan stool na Vanity mirror din dakinta yayinda take riqe da body spray... da alama ta dauko ne don ta fesa amma dayake hankalinta yayi nisa a tunani ta manta da abinda yake hannunta. Maleeka dai gaba daya bata jin dadin rayuwarta.. sossai take missing dinshi. Babu abinda take so irin ta ji ta maqale a jikin shi.. tayi qoqarin accepting reality amma ta kasa.. bazata taba iya sharing MK da wata ba, watan ma 'yar aiki, baqauya, marar ilimi..4 Gani nayi hawaye na bin fuskarta.. da alama bata ma san tana yi ba. Jameela ce ta shigo dakin cikin sallama amma kuma har ta qaraso wurin qawarta bata san ta shigo ba. Gani nayi Jameela ta girgiza kai cike da tausayin ta. Taurin kai da girman kai su ne suka sanya ta cikin wannan halin da take ciki. Matsawa tayi ta dan taba ta.. Zabura tayi tare da dago kanta tana kallon qawarta. Jameela ta sa hannu ta share mata hawayen fuskarta yayinda tace "for how long Leek? for how long are you gonna keep torturing yourself?? don Allah Leek kiyi haquri ki koma gidan mijinki.. kiyi haquri ki tausa zuciyarki ki karbi qaddara kamar yadda ta zo..."2 Maleeka ta miqe tsaye tare da girgiza kai tace "wallahi Jay bazan iya ba... wai bazaku gane cewar bana son kowacce mace a kusa da shi bayan ni? bazan iya zama da shi tare da wata ba.. ya taimaka mun ya saki yarinyar nan.. wallahi I am ready to do whatever he wants idan har ya rabu da ita" Jameela ta girgiza kai tare da fadin "toh Leek.. sai ki jira ranar da zai sake ta sannan ki koma.."3 Ta haye kan gado ta cigaba da fadin "...ni kam na zo in fadi miki cewar next week za'a zo sa ranar bikina" Zaro idanuwa Leek tayi tace "what?? oh my God Jay, finally kin kusa zama ta Suleiman Yusuf Mayana" Jameela ta fashe da dariya tace "Suleiman fa kika ce" Maleeka ta koma kusa da qawarta kan gado cike da mamaki tace "ban gane ba.. kar ki ce mun.." Jameela tana murmushi tace "oh yes my friend.. its Engr. Umar Farouq Danbatta" Maleeka tana kallon qawarta cike da mamaki tace "you must be joking right?? haba qawata.. yanzu fisabilillah me zakiyi da Engr.?? the guy has a wife fa?? ga saurayi son kowa.. handsome, rich and..." Jameela tana dariya tace "Suleiman is a spoilt brat.. yayi depending solely akan kudin mahaifin shi, he is very lazy and bana son auren namiji irin shi.." Maleeka tace "toh yanzu ke kin gwammace ki auri mai mata??? kishiya fa ba abun qauna bace.. zaki je kiyi ta sharing dinshi da wata??" Jameela ta fashe da dariya tare da fadin "Ke kika damu da wannan qawata.. shiyasa kika kasa komawa gidan mijin ki. I love him kuma I dont care about his wife.. harkar ta daban kuma tawa daban..." Kafin Maleeka tayi magana ne aka qwanqwaso qofar dakin.. Daya daga cikin house help din gidan mai suna Zakiyya ce ta shigo (replacement din Ummi) Cike da girmamawa ta duqa har qasa ta gaishe su. Jameela ce ta amsa cikin fara'a as usual. Maleeka wadda ta kalle ta ne tace "me kike yi anan?" Tace "dama na zo in gyara miki dakin ne..." Da sauri Maleeka tace "ban gane ba.. ina tsohuwar da take yi mun aiki??" Inno take nufi.. Asali dai tunda ta dawo gidan Inno ce tayi taking over na kula da al'amuran Maleeka. Zakiyya tace "ai tun jiya ta bar nan gidan... ta koma gidan Uncle MK" Cike da mamaki tace "what??" Wayarta ta janyo tana qoqarin dialing number din Mummy yayinda take fadin "Akan wanne dalili zata bar nan gidan bayan ni take yi ma aiki.." A daidai lokacin ne Mummy ta amsa wayar yayinda tace "hello" Maleeka tace "Mummy wai me nake ji ance tsohuwar da take yi mun aiki ta koma gidan Honey.. akan wane dalili?" Mummy cikin rashin damuwa ne tace "au.. aikuwa na manta ban fadi miki ba, Inno ta koma gidan MK tun jiya saboda Ummi babu lafiya.. Cikinta yana bata wahala kuma.."7 Gani nayi wayar ta zame daga hannunta yayinda na ga ta dafe kanta tace "inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un.. She is pregnant?? yanzu shikenan ta qwace mun komai nawa??" Jameela wadda take kallon qawarta ce tace "calm down Leek.." Cike da mamaki hawaye na bin fuskarta tace"Calm down? how?" Miqewa tayi tsaye yace "wallahi bata isa ba..I have had enough already.. I will make her return everything she stole away from me.."3 Nikuwa nace how?? ♧♧♧♧♧♧♧♧ A yanzu dai bikin Hafsah ya matso don haka sossai shirye shirye ake yi. Ummi dai cikinta yana bata wahala.. yau lafiya gobe babu lafiya.. Kullum Dr. Zeenat sai ta je gida ta duba ta. Kamar dai yadda ta bada shawara Ummi tana buqatar hutu da kulawa sossai domin kuwa a stage din da take any slight thing could bring problem to the pregnancy. Wannan ne ya sanya hankalin MK gaba daya ya koma kan ta. A yanzu haka kusan ma za'a ce shine yake rainon cikin don kuwa babu abinda yake bari tayi da kanta no matter how little..+ Sossai yake ji da cikin nan nata. A dalilin yawan rashin lafiyar Ummi ne ya daina zuwa ofis idan ba wani important abu bane ya taso wanda yake buqatar attention dinshi.. hatta meetings ma daga gida yake zama suyi ta video conference call. Dayake Fahad yana nan shine yake kula da komai kamar yadda ya saba idan MK baya nan. A duk lokacin da MK zai je ofis a dalilin emergency kuwa ya dinga yi ma Inno bayanin abubuwan da zata yi ma Ummi wanda duk ta sani.. Al'amarin MK har dariya yake bata. Ko da ya tafi ofis din ya dinga kiran waya kenan don jin lafiyar Ummi. Ummi dai tun yana bata dariya har ya koma bata tausayi domin kuwa sossai yake shiga damuwa.. shiyasa lokutta da dama take qoqarin matsewa idan bata jin dadi saboda kar ya tayar da hankalin shi. Kusan kullum sai Goggo ta aiko Lado ya kawo ma Ummi abinci don yanzu haka idan ba Goggo ta dafa abinci ba bata ci.. shima abincin Tuwo. Toh har gwara ma wani lokaci idan Inno ta dafa tana ci. Da qarfi da yaji MK ya hana ta shan ice-cream da sauran kayan zaqi.. Daga fruits, vegetables sai kuma plenty of body building foods kamar yadda likita ta bada shawara. Haka ya hana ta yin azumin da suke yi mondays and Thursdays.. Ummi dai dukda tana fama da ciwo yau, lafiya gobe tayi fresh ta qara haske amma dai bata yi qiba ba.. ta qara kyau sai glowing take yi.. Tuni MK ya nema mata hutu a islamiyya.. hakan yana nufin zata yi differing session din wanda Ummi ta dinga qorafi amma ya qi sauraren ta. A kan dole ta haqura ganin dagaske dai baya so ta wahala ko alama. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Weeks later! MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO A yau saura sati daya bikin Hafsah. Da safe tana kwance a kan gadon dakin shi cikin Duvet tana ta kallon shi yayinda yake qarasa shirin tafiya ofis.. A yadda yake shirin kuwa zaka gane cewar sauri yake yi, da alama dai jiran shi ake yi. Ko da ya feshe kanshi da turaruka ya juyo ya kalleta sai gani yayi ta bata rai.. Ummi dai a 'yan kwanakin nan bata so ko alama MK yayi nisa da ita.. gani take yi kamar idan baya nan wani abu zai cutar da ita. She feels insecured without him close to her.. ko meyasa?? oho Murmushi yayi yace "Baby don Allah kar ki hana ni fita.. wallahi ana jira na ne" Turo baki tayi tace "toh ni kawai ka dan zo..." Gani nayi ya girgiza kai sannan ya nufi wurinta ya kwanta gefenta a kan gadon yace "toh Baby ga ni" STORY CONTINUES BELOW Matsawa tayi ta kwanta a jikin shi. Cikin shagwaba tace "don Allah kar ka fita.. ka ga idan ka tafi ciki na zai yi ciwo" Fashewa yayi da dariya yace "kin san abinda kike nema kiyi mun kuwa Baby?? emotional blackmail ne fa" Muryarta qasa-qasa tace "Hamma koma dai menene please..." Bai ankara ba ya ji ta hada fuskar ta da nashi yayinda ta shiga zuba mishi kisses babu sassautawa... Tuni MK ya biye mata. Gaba daya baya iya resisting din Ummi domin kuwa she is super sweet- the whole of her. A hankali dai sai ga Ummi ta fara balle buttons din shirt din shi.. cike da salo mai rikitarwa ta jefa shi wata duniyar.. duniya mai dadi wadda idan da hali zasu yi zaman su a cikinta har abada.3 Duk yadda Ummi take birkita mishi qwalwa yana tabbatar da ya bi ta ahankali kamar yadda likita ta bashi shawara. Bayan sun kwashi soyayya sun sarara ne suka shiga hira.. As usual hirar Babyn su idan ya fado duniya.. Wayar MK ce tayi ringing.. ko da ya duba gani nayi ya rufe idanuwan shi sannan ya bude. Yana answering ne na ji yace "Fahad please I am sorry.. bazan samu zuwa ba, you guys should just carry on.." Shiru ya dan yi sannan yace "yeah dont worry kawai ka tura mun a mail dina I will review it.." Murmushi yayi yayinda ya shafa gashin kanta yace "gata nan... jikin Alhamdulillah" daga nan kuma yace "toh Ameen abokina.. nagode" Bayan ya kashe wayar ne yace "Baby kin ga kin hana ni attending meeting ko?" Ummi wadda kanta ke bisa qirjin shi ce ta qara langwabewa a jikin shi tace "yi haquri Hamma.. ni fa kawai bana so kayi nisa ka barni ni daya ne..." Wrapping hannun shi yayi around her yace "toh yanzu bacci zamuyi ko kuma mu je muyi wanka?" Da sauri tace "mu yi bacci.. idan mun tashi sai mu yi wanka.. ka ga dama yau Hudayya zata kawo mun dinkunan kayan da zan sa a bikin Hafsah, zaka taya ni gani ko sunyi kyau ko basu yi ba ko?" Girgiza kai yayi yace "duk abinda kike so zan yi miki Babyna.. ko rijiya kika ce in fada zan fada.." Tana dariya tace "thank you Hamma" A haka dai suka cigaba da hira har bacci ya kwashe su. ♧♧♧♧♧♧♧ One week later!! Tuni an shigo satin bikin Hafsah.. Sossai ake shiri na musamman.. Hafsah dai ta kasance 'yar gata gaba da baya. Sossai ake ta kashe kudi na shirye-shiryen bikin. Kayan lefen ta kuwa dayake ita ta hada kayanta abun ba'a cewa komai... duk wani abu na cikin kayan na gani na fada ne. ♧♧♧♧♧♧♧ MUHAMMAD SODANGI RESIDENCE MAITAMA A yau ranar qunshi... tun da safe gidan ya cika da qawayen ta. Dayake dai Hafsah tana da qawaye dayawa gaba daya sashenta a cike yake. Team din Henna temple aka gayyato don yi ma amarya da qawayenta qunshi. ********** MK ne da Ummi zaune cikin mota a tsakar gidan. Dayake ya hana ta yin komai shine ya kawo ta da kan shi wanda idan ta gama shine zai zo ya dauke ta. Kamar kullum dai MK yana ta tambayan ta inda yake yi mata ciwo yayinda take gwada mishi babu ko ina.. STORY CONTINUES BELOW Asali dai yau kusan sati daya kenan da Ummi bata jin dadin jikinta toh amma tunda bai kai ta ga kwanciya ba sai ta daure. Gashi bata son ganin yadda MK yake shiga damuwa idan bata jin dadi... sossai yake bata tausayi. Gani nayi ya fito daga motar ya zagaya sannan ya bude mata. Hannunta ya riqo ya taimaka mata ta fito. Ummi dai sossai tayi kyau. Sanye take cikin wani tsadaden lace mai laushin gaske wanda aka yi ma dinkin doguwar riga.. Fuskarta babu kwalliya domin kuwa dai ita din ba ma'abociya kwalliya bace.. Amma fa dukda haka idan ka kalle ta dole ne ka yaba domin kuwa Ummi kyakyawar bafillatana ce sannan ga wani asirtaccen kyau da ta qara yi tana ta qyalli. Ummi dai ko da ta fito tana qoqarin gyara gyalen da ta yafa ne MK ya taimaka mata.. Gani nayi ya jingina ta jikin motar yayinda ya duqo da fuskar shi saitin fuskarta yace "idan kin ji jikin ki babu dadi ki kira ni.. kin ji??" Tana murmushi tace "toh Hamma" Ya dan shafa fuskarta yace "Ina sonki sossai Babyna.." Ta ja gemun shi tace "nima ina bala'in sonka Hamma na.. yanzu dagaske bazaka shigo ba??" Yace "gaskiya bazan shiga ba.. na san duk mata sun cika gidan, ki gaida mun Mamy da Hafsah kawai.." A daidai wannan lokacin ne motar Jameela ta shigo gidan.. Maleeka ce zaune a gefenta. Suna hira ne Maleeka ta dauke wuta a dalilin hango su da tayi tsaye jikin motar shi. Bata ankara ba ta ga sun rungume juna sannan kuma suka saki juna.. Wata magana yayi mata yayinda ta fashe da dariya.. daga nan kuma sai ta janyo shi tayi mishi kiss a kumatu sannan kuma tayi mishi a baki. Jameela wadda itama ta hango su girgiza kai kawai tayi ba tare da tace komai ba. Bayan ta samu wuri tayi parking ne tace "Leek mu je ko? Cikin qunar rai Maleeka tace "ki bari sai ya tafi.. bana son ganin shi da wancan 'yar iskan yarinyar" Jameela tace "Leek ba fa 'yar iska bace.. matar shi ce" Maleeka wadda ta sa musu idanuwa gani tayi ya ba Ummi side hug yayinda suka fara tafiya. Da suka isa gaban porch din gidan ne kuma suka tsaya suna fuskantar juna riqe da hannuwan juna suna magana. Daga nan Ummi tayi hugging dinshi sannan ya duqo yayi mata Kiss a kumatu ya kai bakin shi saitin kunnen ta ya fadi mata wata magana.. ita kuma ta fashe da dariya. Daga mishi hannu tayi alamar bye bye yayinda shima ya daga mata sannan ya juya. MK dai ko da ya shiga motar shi qin tafiya yayi sai da ya ga matar shi ta shige gidan ne ya tayar da motar ya tafi. Sai da ya fita daga gidan sannan Maleeka ta fito daga motar. A yadda zuciyarta take zafi ma ji tayi kamar su fasa halartar bikin qunshin su koma gida. Jameela dai ta kula da halin da take ciki don haka ne ma bata yi mata magana ba. Ummi dai ko da ta shiga gidan sashen Mamy ta wuce abinta. Sai da tayi kusan awa daya a wurin Mamy sannan ta nufi sashen Hafsah. ******** Suna zaune a falon ne Ummi ta shigo cikin sallama.. Gaba dayan su da suke zaune a falon suka juyo don ganin me sweet voice din.. Maleeka wadda take zaune tare da qawarta Jameela sai da zuciyarta ta buga a dalilin ganin Ummi. Ganin ta very closely da tayi a yanzu ne ta hango yadda ta canza gaba daya.. tayi masifar kyau.. kamarninta sun koma kamar na larabawa.. STORY CONTINUES BELOW Muryar Hafsah suka ji tace "oyoyo oyoyo.. Babyn yaaya na ta iso" Ummi wadda tayi murmushi ce ta qaraso wurin Hafsah yayinda take ta gaisawa da mutanen da suke falon. A dalilin yadda kowa ke ta bin ta da idanuwa ne bata wani kalle su ba balle ta ga su Maleeka wadanda suke zaune a kan kujera daga dan nesa kadan. Ummi dai samun wuri tayi kusa da Hafsah ta zauna. Hafsah ce tace "Babyn Hamma sannu da zuwa.. Ya gida?? ya qarfin jiki??" Ummi tace "lafiya lau.. Alhamdulillah" Cikin tsokana Hafsah tace "ai nayi zaton Ya MK bazai bari ki fito ba don na ga tunda kika samu cikin nan ya hana ki motsi.." Maleeka wadda take sauraron maganganun Hafsah sossai ranta ya baci.. ji tayi kamar ta mutu don baqin ciki Ummi wadda tayi murmushi tace "ya za'ayi in kasa zuwa bikin ki Hafsah..." A haka dai aka cigaba da random hira yayinda team din Henna temple suke ta zirara ma amarya da qawayenta lalle gwanin ban sha'awa. Bayan an gama ma Hafsah nata ne gaba daya falon aka dinga yabawa.. ita kanta ta yaba qwarai, sossai ta ji dadi don kuwa Allah ya sani Hafsah bata so wani abu ya je wrong a bikin ta. She wants everything to be perfect.. Labiba CEO ta Henna temple din da kanta ce tayi ma Hafsah... ko da ta gama ma Hafsah ne ta kalli Ummi tace "matar Yaaya bisimillah.." Ummi wadda take kallon ta ce tayi murmushi tare da fadin "ai ni bazan yi ba.." Da sauri Hafsah tace "kamar ya bazakiyi ba?" Ummi tace "dagske Hafsah ban ma taba yi ba fa" Nafisatu qawar Hafsah ce tace "don Allah kiyi haquri ayi miki... wallahi zaiyi miki kyau sossai" Hafsah ta kalli Labiba tace "kiyi mata Red mai kyau" Ta kalli Ummi tace "Dan kadan zata yi miki.. zai yi kyau" Akan dole dai Ummi ta miqa hannunta yayinda na ji tace "a hannu kawai zakiyi mun" Labiba tana murmushi tace "toh Matar Yaaya" Tana shirin farawa ne tace "toh ko zaki cire zoben nan.." Da sauri Ummi tace "a'a bazan cire ba.." Labiba tace "toh ya za'ayi lallen?" Ummi tace "kawai ki tsallake shi.." Hafsah wadda take hira da qawayenta ne ta jiyo su.. Gani nayi ta kalli Zoben da yake hannun Ummi yayinda na ga ta zaro idanuwa. Da sauri ta kalli Labiba tace "don Allah ki rufa mun asiri kiyi mata lallen ba sai ta cire zoben nan ba.." Cike da tsokana ta cigaba da fadin "...ai wannan zoben alqawari ne na soyayya.. idan ta cire shi ba ke kadai ba hatta ni sai na ga fushin Ya MK. bazan taba mantawa ba last year da muka je Dubai ya siyo shi.. it was the most unique and expensive ring in the market. Na so ya bani amma ya qi.. ashe specially ya sa aka yi mishi designing wanda a wannan zuwan da muka yi ne ya karba. He told me that bazan gan shi a hannun kowa ba sai a hannun mother of his child.."1 Kafin Hafsah ta gama magana ne suka ji Maleeka cikin fada tana fadin "nace ki cire shi haka nan... ya ishe ni" Daga nan kuma sai gani suka yi ta buga tsaki ta fizge hannunta daga hannun daya daga cikin masu lallen ta miqe ta bar falon cike da tashin hankali. Jameela wadda ta san halin qawarta ce ta miqe ta bi bayan ta da sauri. Gaba daya hankalin kowa ne ya dawo kansu yayinda mai lallen ta tsaya galala cike da mamaki.. STORY CONTINUES BELOW Hafsah wadda ta ankara da barnar da tayi ce ta runtse idanuwa ta bude yayinda na ji tace "Subhanalillah... what have I done?" Har ga Allah Hafsah ta manta cewar Maleeka tana wurin tayi maganar... kuma ma bata sa ran tana sauraron maganar su ba tunda dai they are a bit faraway from her sannan 'yan mata suna ta hayaniya a falon.. Ji nayi Labiba tace "Maryam me ya faru?" Ko kafin Maryam din tayi magana ne Hafsah tace "kar ki damu.. ba laifin ta bane" Ita dai Ummi gaba daya ma ji tayi dama bata zo ba.. da ba'a fara yi mata lallen ba da ta bar gidan domin kuwa a yanzu haka kawai gaban ta yake faduwa tunda ta ga Maleeka.. Gashi dama ba wani dadi jikinta yake yi mata ba. Har aka gama yi ma Ummi lallen ta ya bushe Maleeka bata dawo ba.. Gaba daya jikinta a sanyaye yake. Aikuwa bayan an gama ta wuce sashen Mamy ta shige dakinta ta kwanta abinta.. Mamy kuwa ganin yanayin Ummi sai ta shiga damuwa yayinda take ta tambayarta ko cikin ne yake ciwo amma sai ta gwada kawai tana so tayi bacci ne. Da baccin ya gagare ta ma sai kawai ta dauki wayarta ta kira MK akan ya zo ya kai ta gida.. Hankalin Ummi dai bai kwanta ba a ranar sai da ta koma gida.. Ita kanta ta rasa dalilin da ya sanya duk ta bi ta damu kanta akan dan abinda ya faru.. ************* Wasa-wasa dai sai da Ummi ta kwanta jinya a gida.. harda qarin ruwa aka yi mata.. MK duk ya bi ya rude. Dr. Zeenat ce ta dinga calming din shi down tare da yi mishi bayanin situation din wanda is under control. Dama dai yawanci ana dan shan wahala a first trimester balle kuma ga yanayin body system din Ummi and considering how fragile she is. Tunda ta kwanta kuwa bai qara fita ba.. Duk wani aikin ofis daga gida yake yin shi. Gaba daya 'yan biki kuma sai aka koma ana zuwa dubiya. A haka dai aka gama bikin Hafsah Ummi tana kwance. Ko kafin Su Hafsah su bar qasar sai da suka je suka duba jikin Ummi. ♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO A yau kwana uku kenan da aka gama bikin Hafsah. Babu laifi Ummi ta qara samun sauqi amma kuma jikin ta very weak. Zaune take a kan gadon dakin shi rungume da teddy bear dinta yayinda yake bata cornflakes a baki. Tana sha suna hira as usual. Wayar shi ce tayi ringing yayinda ya ajiye bowl din da ke hannun shi. Ko da yayi answering ji nayi yace "abokina ya akayi ne??" Can kuma yace "today??" Bata rai yayi yace "cant you handle it??" Kanshi ya shafa sannan yace "okay my friend.. it had better be brief don wallahi bana son barin Baby ita kadai for long" Gani nayi yayi murmushi yace "gata nan.. she is fine" Daga nan yace "toh sai na zo" Yana kashe wayar ne ya kalli Ummi wadda take kallon shi yace "Baby zan dan je ofis akwai wasu baqi da muka yi daga China zamu dan tattauna" Turo baki tayi tace "toh don Allah ka dawo da wuri ka ji Hamma??" Ya ja kumatun ta yace "I will my love" Sai da ya gama bata cornflakes din sannan ya miqe ya nufi dressing room don shiryawa. Ko da ya gama shirin shi tsab ya fito kiran Inno yayi ta wayar intercom. STORY CONTINUES BELOW Cikin sallama ta shigo dakin inda ta tarar da su zaune a kan gado. Bayan sun gaisa ne MK yace "don Allah ki zauna ki kula mun da ita kafin in dawo.. kar ki bari tayi komai please.." Inno tana ta murmushi yayinda Ummi take dariya tace "Hamma kar ka damu babu abinda zanyi.." Matsawa yayi daf da ita yayi mata kiss sannan yace "idan kina buqatar wani abu ki kira ni a waya kin ji??" tace "toh Hamma" Gani nayi yana shafa wuyanta da goshin ta yace "babu inda ke yi miki ciwo??" Tana murmushi ta girgiza kai tace "babu" Ya shafa cikinta yace "okay toh bari in tafi.. ba zan dade ba zan dawo" Tace "toh Hamma" Hugging dinta yayi tare da yi mata kiss yace "I love you" Ita dai Inno tana nan tsaye tana kallon ikon Allah.. da abun ya nemi fin qarfinta ne ta kauda kai. Ji nayi Ummi tace "mu je in raka ka" Da sauri yace "No baby.. yi zaman ki. bana son ki da wahala" Murmushi kawai tayi yayinda ya sauka daga kan gadon. Ji nayi yana ta qara repeating ma Inno abubuwan da zata yi ma Ummi wadanda ta riga ta sani. Bayan MK ya tafi ne Inno ta matsa kusa da Ummi tace "ke kam kin more a rayuwar ki wallahi Ummi.. irin wannan kulawa da yake nuna miki kamar 'yar gwal?? Ubangiji Allah ya bar ku tare" Ummi tana murmushi tace "Ameen Daada" Inno tace "Hajiya qarama dai tayi asara wallahi.. na rasa me take zaman yi a gida" Ummi dai jin maganar Maleeka sai da gaban ta ya fadi amma ta matse.. she seems to be having weird feelings about her lately, why??? Anan Inno ta dauke bowl din cornflakes din da Ummi ta sha ta mayar kicin sannan ta dawo ta zauna a dakin suka shiga hira. A haka har bacci ya kwashe Ummi. Inno dai dukda Ummi tayi bacci bata bar dakin ba.. tana nan zaune har ta farka. Inno tace "ya jikin??" Tace "Alhamdulillah Daada.. kawai dai bana jin qarfi a jikina ne" Inno tace "toh ko zaki watsa ruwa ne ko kya dan ji dama-dama?" Ummi tace "toh Daada" Daga nan Inno ta miqe ta nufi bathroom don hada mata ruwan wanka. Bayan Ummi ta fito daga wanka ta shirya cikin wata doguwar sleeveless material gown sannan ta koma kan gado ta kwanta. Inno ce tace "Ummi me zaki ci in je in dafa miki?" Girgiza kai tayi tace "babu komai Daada.." Inno tace "ai bazai yiwu ki zauna da yunwa ba, don Allah fadi mun abinda kike sha'awar ci sai in dafa miki" Shiru ta dan yi sannan tace "Daada da zan samu tuwo da miyan ayayo.." Inno ta miqe tare da fadin "toh Ummi, amma dai sai na je kasuwa na siyo ayayo.." Ummi tayi saurin fadin "babu damuwa Daada.. ki je kawai" Inno tace "anya Ummi.. kar maigidan ki ya dawo ya ga na bar ki ke kadai kuma yayi fada" Ummi ta fashe da dariya tace "haba dai Daada.. kar ki damu don Allah.. zan yi mishi bayani" Ko kafin Inno ta tafi sai da ta tabbatar Ummi bata buqatar komai sannan. STORY CONTINUES BELOW *********** Ummi ce ta fito daga daki maqale da waya a kunne tana hira da Fatima matar Fahad... A hankali take tafiya a dalilin jikinta that is weak. Ko da ta sauko zama tayi a falon qasa suna ta hira tsawon lokaci.. daga baya kuma suka yi sallama. Har ta miqe zata wuce kicin ne wayar tayi ringing.. tana dubawa ta ga Video call daga MK. Murmushi tayi sannan tayi answering.. Yana kallon fuskarta yace "Maman Baby how are you??" Tana murmushi tace "Fine Baban baby" Wani lafiyayyen murmushi ya saki tare da lumshe idanuwa sannan yace "Allah ya sani na ji dadin sunan nan da kika kira ni da shi- Baban Baby" Turo baki tayi cikin shagwaba tace "anya idan na haifo Babyn nan bazaka juya mun baya ba kuwa?" Zaro idanuwa yayi yace "Ni??? rufa mun asiri.. ai kin fi mun komai muhimmanci a rayuwar nan Ummi.. kinyi mun abubuwan da har in mutu bazan manta ba.. Allah ya sani ina bala'in son ki kuma ina fata ki kasance mata ta ba a nan duniyar kawai ba, har a gidan Aljannah. I love you so much" Shiru tayi tana kallon fuskar shi yayinda take murmushi.. Lumshe idanuwa tayi tace "nagode sossai mijina.. nima ina sonka sossai" Yana kallon background din da take ne yace "hey, me kike yi a falo?? ba nace ki kwanta ki huta ba?? you are supposed to be in bed rest.. Ina Inno take?" Ummi wadda take kallon shi tace "yi haquri Hamma.. baki na ne babu dadi shine zan je kicin in dan ci wani abu.. Daada kuma ta tafi kasuwa zata siyo mun ayayo" Shiru ya dan yi sannan yace "meye wannan??". Fashewa tayi da dariya tace "kai fa dan birni ne na manta.. wani ganye ne da ake yin miya da shi. ko zaka ci ne??" Kai tsaye yace "Baby idan dai ke zaki ci nima zan ci.. duk abinda kike so nima ina so" Tana murmushi tace "toh yaushe zaka dawo?? ina kewar ka sossai" Yace "yanzun nan.. mun gama meeting din. da zarar nayi signing wasu takardu zan dawo" tana kallon shi tace "toh Hamma na.. ina nan ina jiran ka" Yace "toh masoyiya ta.. bye" Da sauri tace "dan tsaya" yace "me ya faru??" Tace "ina sonka Hamma" Murmushi yayi yace "nima ina son ki sossai babyn Hamma.. in kashe??" Ta dan yi shiru tana kallon shi sannan tayi blowing mishi kisses tace "I love you" Lumshe idanuwa yayi yana murmushi ya kama kisses din da ta huro mishi ya shafa a kan chest dinshi daidai saitin da zuciyar shi take yace "I love you more.. sai na dawo" Bayan ta kashe wayar ta miqe tsaye ne gabanta yayi mummunar faduwa a dalilin ganinta da tayi. Maleeka!!!13 What is she doing here??? Gani nayi Ummi ta dafe qirjinta yayinda ta saki ajiyar zuciya sannan tace "sannu Adda" daga nan ta raba ta gefenta zata wuce kicin. Ji tayi Maleeka ta fizgo ta da qarfi wanda har ta kusa faduwa.. dafe cikinta tayi wanda ya juya a dalilin wujijiga ta da Maleeka tayi. Gani nayi Ummi ta ja jikinta zata koma daki amma Maleeka tayi saurin shiga gabanta. Da sauri ta hada ta da bango tare da fadin "Dan ubanki tsaya.. magana zamuyi" Ummi wadda gaba daya jikinta yake rawa ce tace "don Allah Adda ki qyale ni... bana jin dadi. ki bari idan.." STORY CONTINUES BELOW Wata muguwar shaqa Maleeka ta kai mata a wuya wanda ya sanya Ummi ta fara kakarin amai. Maleeka tana kallon fuskarta yayinda ta qi sakin wuyan ta tace "me kike so in baki ki fita daga rayuwar miji na??" Ummi wadda take kakarin amai ce ta kufce daga riqon da Maleeka tayi mata yayinda ta riqe wuyanta wanda tuni yayi ja. Cikin muryar kuka tace "ni bana son komai.." Maleeka tayi murmushin takaici tace "duk duniya babu wanda nake so sama da dan uwa na.. babu wanda nake kishi sama da shi.. ko alama bana so in ga wata mace ta rabe shi sai gashi daga sama kin shiga rayuwar shi.. na kore ki a karo na farko amma ya bi ki ya auro ki ya kawo ki cikin gidana... har kina hada shimfida da shi..." Hawaye ne suka fara bin fuskarta yayinda ta cigaba da fadin "....abin mamaki.. ke din ba kowa ba, 'yar qauye, talaka, wadda bata je makaranta ba.. iyayena sun hana ni koya miki hankali, sun gina katanga a tsakani na da ke.. kin raba ni da miji na... tsawon watanni baya kula ni..." Ta share hawayen fuskarta yayinda tace "not anymore... Wallahi qaryan ki, ina bala'in son mijina kuma babu wadda ta isa ta raba ni da shi" Ummi wadda take kuka ce tace "Adda ni ban raba ki da shi ba. Nima ai mijina ne kuma ina son shi.." Kafin ta rufe bakin ta ne ta ji saukar mari a kumatun ta.. Ihu ta saki yayinda ta dafe kumatun tana kuka.. Maleeka ce ta nuna ta da yatsa tace "qarya kike yi 'yar iskar yarinya.." Cikin kuka Ummi tace "wallahi ina son shi kuma bazan taba daina son shi ba.." Wani marin ta sake ji a kumatun ta yayinda ta qara fashewa da kuka.. tuni kumatun ta yayi ja..1 Tana kuka tace "Adda ko kashe ni zakiyi bazan fasa fadi miki ba.. ina son mijina kuma babu wanda ya isa ya raba ni da shi a duniyar nan sai Allah.." Daga nan ta raba ta gefenta ta ruga a guje dafe da cikinta wanda yake mata ciwo zata haura sama... Maleeka ta bi bayan ta a guje cike da bacin rai ta fizgo ta da qarfi. Hakan kuwa ya sanya Ummi tayi missing steps dinta. Ihu ta saki yayinda na ga ta fadi a qasa ruf da ciki.. It happened so fast.7 Gani nayi Maleeka tayi freezing a tsaye yayinda zuciyarta ta buga ganin Ummi kwance a qasa bata motsi.. A razane ta sa Hannu a kai yayinda na ji tana fadin "no no no no..." Ta matsa zata taba Ummi kenan ta ga jini na gangarowa daga ta tsakanin qafafuwan ta. Hawaye ne suke ta bin fuskarta kamar an saki famfo.. Ji nayi tace "na shiga uku.. what have I done?"1 Matsawa tayi baya da sauri yayinda ta zama so confused... jikinta ne yake ta rawa, gwiwowinta sunyi mugun sanyi sannan qafafuwanta sun yi nauyi.. Bata taba shiga tashin hankali ba irin na yau. Komawa tayi wurin Ummi ta jijjiga ta tana fadin "don Allah kar ki mutu.. ki tashi Ummi, don Allah Ummi.. please don't die on me.. ki taimaka mun ki bude idanuwan ki please Ummi..." Ganin dai Ummi bata motsi sannan ga jini da yake ta zuba daga jikinta ne ya sanya tayi saurin tashi a rude ta ruga a guje zata bar falon. Har ta kai bakin qofa sai kuma ta juyo tana hango Ummi kwance cikin jini.. At the point in time Maleeka looked so scared, confused and hopeless... sossai ta firgice. Wata zuciya ce take fadi mata ta koma ta tabbatar da halin da Ummi take ciki yayinda dayar take fadi mata ta gudu kawai...5 ♧♧♧♧♧♧♧♧ WILDOT CLINIC ASOKORO-ABUJA Zaune suke a kan kujerun waiting room na ER din da aka shigar da ita. Hankulan su sunyi matuqar tashi musamman MK wanda yake ji kamar zai mutu. Duk yadda ya so ya daure ya kasa... hawaye ne ke ta gangarowa daga idanuwan shi yayinda jikin shi yayi matuqar sanyi. Abba wanda yake riqe da hannun shi ne yake ta lallashin shi tare da qarfafa mishi qwarin gwiwa.+ Mamy da Goggo ma sai zubar da hawaye suke yi.. Mummy wadda itama hankalinta a tashe tana magana da Daddy a waya. He travelled to Spain! Fatima tana maqale a jikin Fahad itama kuka take ta yi.. Haka Lado shima yana gefe yana ta share hawaye. Gaba dayan su dai jikin su yayi sanyi domin kuwa a halin da aka shigar da Ummi chances din ta are very low musamman idan aka yi la'akari da yawan jinin da ta zubar.. Kusan awa uku kenan da aka shigar da Ummi amma har a wannan lokacin shiru... babu wanda ya fito daga Emergency room din balle su san me ake ciki.. Babu abinda MK yake picturing sai halin da ya tarar da Ummi... Kwance cikin jini bata numfashi.. yana rungume da ita yana zubar da hawaye ya kasa yin komai har sai da Inno ta shigo gidan.. A wannan lokacin kawai ya zata Ummi ta rasu ne.. he was so confused that he didn't even know what to do.2 Inno wadda ta shiga tsananin tashin hankali a wannan lokacin itama kukan take ta yi yayinda take ta salati tana ba MK haquri na barin Ummi da tayi ita daya a cikin gida. Ita ce ma tayi qarfin halin ankarar da MK akan a kira asibiti qila bata mutu ba... that was when he called Dr. Davis... Ko da Dr. Davis yayi feeling pulse din Ummi it was very weak. She is alive amma a dalilin jinin da take losing mai yawa babu guarantee na zata rayu... instantly suka janye ta daga jikin MK suka dora ta a kan stretcher sai asibiti. Dr. Davis ne ya fito daga emergency room din. A matsayin shi na family doctor dinsu ne ya zo ya basu update. Gaba dayan su suka miqe tsaye cike da fargaba musamman MK wanda qafafuwan shi suka yi mugun sanyi. Ji nayi Dr. Davis yace "for now the patient is alive but she has lost alot of blood and..." Tun kafin Dr. Davis ya rufe bakin shi ne MK yace "Please take mine, I am a universal donor.." Ya hada hannuwan shi biyu yace "...Please Doctor, you have to do everything necessary to keep her alive... she has to stay alive for me.." Dr. Davis ya girgiza kai tare da fadin "we are doing our best to keep her alive Mr. Kabir.." Nan da nan Dr. Davis ya kira nurses yayinda aka tafi da MK don auna jinin shi. Duk yadda su Abba suka so suyi extracting information akan halin da Ummi take ciki daga wurin Dr. Davis sun kasa.. bai san me zai ce musu ba because even the surgeons that are operating on her have nothing to say a yanzu.. Abinda kadai ya ce musu shine " just be hopeful and prayerful.." ♧♧♧♧♧♧ 2 days later... Wuraren qarfe bakwai da rabi na safe yana zaune a gefen gadonta yayinda ya zuba mata idanuwa. Tsakanin 'yan kwanakin Ummi ta rame sossai tayi haske.. har yanzu na'urar EKG ce maqale da ita wadda take monitoring din yanayin jikin nata. STORY CONTINUES BELOW Tsawon kwana biyu kenan Ummi tana kwance ana sa ran ganin ta farka... though she is doing well, amma bata motsa ba balle ta farka.. Wadannan kwanakin biyu are surely the worst days of his life.. a yanzu haka kuwa he is finding it difficult holding up!! Ko sau daya MK bai bar wurin Ummi ba... Sallah kadai ke tayar da shi daga wurinta. Babu yadda su Abba basu yi ba akan ya je gida ya huta tunda ance she is stable amma sam ya qi. He wants to be there when she wakes up... Tun likitoci suna hana shi shiga dakin Ummi ya zauna ya dade har suka haqura ganin yadda yake ta breaking musu rules. Su Mamy kuwa a kullum nan suke yini sai dare suke komawa gida amma ana barin Lado tare da MK incase he might need him to run an errand for him.. Yana riqe da hannunta ne ya ji ta dan yi motsi yayinda ta bude idanuwan ta ahankali.. mayar da idanuwan tayi ta rufe yayinda na ji muryarta qasa-qasa tana fadin "Hamma... Hamma..." Cike da tsananin murna MK ya matsa daf da ita ya rungume ta tare da fadin "Baby... you are awake? Alhamdulillah..." Ba tare da ta bude idanuwan ta ba ta kai hannunta kan cikinta ta shafa... yanayin yadda ta ji cikin ne ya sanya tayi saurin bude idanuwan ta tace "Hamma.. ciki na..??" Tayi maganar cikin tambaya.. MK wanda yake rungume da ita ne yace "baby relax..." Da sauri tace "Hamma?? wani abu ya samu cikina.." Daga nan ta fara yunqurin tashi zaune yayinda take fadin "bana jin komai a.." Fashewa tayi da kuka yayinda hankalin MK yayi mugun tashi... Hugging dinta yayi very tight yace "Baby ki daina kuka.. Allah ne ya bamu kuma ya karbi kayan shi.. dole ne mu yi imani da qaddarar Allah kamar yadda ta zo mana. kiyi haquri kin ji??"3 Ayyah!! the baby is Gone?? Ya salaam..5 Kuka kawai Ummi take rusawa... MK wanda yake ta goge mata hawaye ne ya dinga lallashin ta tare gaya mata maganganu masu sanyaya zuciya. Lallashinta yake yi amma kamar qara ziga ta yake yi. Da qyar ya shawo kanta ta daina kuka amma fa har a lokacin hawaye na bin fuskarta. Shi kanshi a wannan lokacin he is extremely sad because Allah ya sani ya sanya buri a kan cikin Ummi amma they lost it.. at this point in time he needs to be strong a gaban ta. Dr. Davis ne ya shigo tare da Dr. Zeenat. Ji nayi Dr. Davis yace "finally, Mrs Muhammad Kabir is awake.." Dr. Zeenat ta qarasa wurin Ummi yayinda na ji tana fadin "kiyi haquri ki daina kuka.. Allah zai baki wani kin ji??" MK ne ya dan yi ma Dr. Zeenat murmushi yace "thanks Doc" Gani nayi Dr. Zeenat din ta fara duba yanayin jikin Ummi yayinda Dr. Davis ya nufi wurin EKG machine yana qoqarin disconnecting. Bayan ya gama ne ya dawo gefen Dr. Zeenat ya kalli MK yace "Mr. Kabir while Dr. Zeenat is attending to her, I will like to talk to you in private please.. can you come with me to my office??" Kai tsaye MK yace "is something wrong with my wife??" Murmushi ya dan yi sannan yace "no Mr. Kabir but it's kind of important.." MK ya girgiza mishi kai sannan ya kai bakin shi saitin kunnen Ummi yace "Baby ina zuwa bari in ga likita in dawo kin ji??" Daga mishi kai tayi tare da fadin "toh Hamma.. don Allah kar ka dade" STORY CONTINUES BELOW A hankali ya mayar da kanta kan pillow sannan ya sauka daga kan gadon ya duqo yayi mata kiss a goshi yace "ba zan dade ba.." Ya kalli Dr. Zeenat yace "please dont leave her alone" Tana murmushi tace "I will be here with her Sir.." ♧♧♧♧♧♧ Zaune yake a office din Dr. Davis yana sauraron bayanin likitan kamar haka: "Mr Kabir, I was going through your wife's medical report and I came across something I think you should know.." Gani nayi ya miqa ma MK wani file yayinda ya cigaba da fadin "..your wife was physically assaulted at the time she met with the accident.. infact I think someone tried to harm her.." MK wanda hankalin shi yake a matuqar tashe tuni ya mayar da attention dinshi kan report din Ummi wanda yake nuni da cewar an shaqe ta a wuya sannan an mare ta a kumatu multiple times.. Hakan ya tabbatar da lallai someone was responsible for what happened to his wife and his baby.. Ji yayi Dr. Davis yace "..I suggest you investigate further by asking your wife what really happened because her life may be in danger and you might want to involve the police in..."7 Gani nayi MK ya miqe da sauri yayinda yace "thanks alot Doc... I will handle it from here" Daga nan ya fita da sauri. ************* MK ya shigo dakin hankali a tashe. A lokacin Ummi tana kwance idanuwan ta a rufe, hawaye ne ke ta bin fuskarta yayinda take jin zafin rashin Babyn ta... Dr. Zeenat wadda take zaune a kusa da ita tana ta lallashinta ce ta kalle shi tace "please try and calm her down.. we wouldn't want her blood pressure to be on the high side right now.." MK yace "I will doc... thanks alot" Dr. Zeenat ta miqe tare da daukan file dinta tace "just call me incase you need anything" Yace "thanks" Bayan ta fita ne MK ya haye kan gadon ya janyo Ummi jikinshi yayi hugging dinta. Kusan minti biyar suna a haka wanda tun Ummi tana kuka har ta daina yayinda ta koma sakin ajiyar zuciya. Muryar shi qasa-qasa ne yace "Baby idan na tambaye ki zaki fadi mun gaskiya??" Girgiza mishi kai tayi alamar 'eh' Kai tsaye yace "me ya faru ranar da kika fadi??.." Zuciyar Ummi ce ta buga yayinda take tuno abinda ya faru.. Kalaman Maleeka ne suke ta yawo a qwalwar ta... haka zafin marin da tayi mata da kuma shaqar da ta kai mata.. ta tuno azabar da ta sha lokacin da ta fadi wanda daga nan tayi passing out... Muryar shi ta ji yana fadin "kar ki ji tsoro Baby.. gaya mun abinda ya faru" Muryarta tana rawa tace "Hamma zamewa nayi na fadi... don Allah kayi haquri nayi mana asarar Babyn mu.."3 Daga nan ta fashe da wani sabon kuka.. Da sauri MK yace "ssshhh.. relax ki daina kuka Baby... Kin fi komai muhimmanci a wurina don haka nagode ma Allah da ya bar mun ke a raye babyna.." Haka ya cigaba da lallashin ta yayinda yake tunanin abinda likita ya fadi mishi da kuma abinda ita Ummin ta fadi a yanzu... She is definately hiding something from him and he needs to find out... but how??5 A haka dai suka kasance har lokacin da su Mamy suka dawo.. Tuni likitocin sun bada damar a ba Ummi abinci ta ci amma ba mai nauyi ba.. STORY CONTINUES BELOW Dayake Goggo ta kawo Kunu sai aka fara bata shi ta sha.. Ganin su Mamy sun dawo ne MK yace musu zai je gida ya dawo. The first time he left the hospital tunda aka kawo Ummi... ♧♧♧♧♧♧ MK SODANGI RESIDENCE ASOKORO MK dai ko da ya shiga gidan kai tsaye ya kira Inno ya sanar da ita cewar Ummi ta farka wanda kuwa ta dinga murna tana qara gode ma Allah yayinda ta dinga yi musu fatan samun wani rabon a nan gaba... Ko da tayi mishi tayin abinci ce mata yayi baya jin yunwa.. Kai tsaye sashen shi ya wuce yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya ma three quarter sweat da T-shirt. Gani nayi ya koma kan gadon shi ya kwanta yayinda ya shiga tunani akan what might have happened to Ummi... its obvious she lied to him but why??? Wayar shi ce tayi ringing wanda har ta gama bai yi picking ba... Sake ringing tayi a karo na biyu yayinda yayi stretching hannun shi ya janyo. Ganin sunan abokin shi ne yayi answering tare da fadin "hey my friend.." Fahad a dayan bangaren ne yace "abokina how are you? ashe Ummi ta farfado?? dazu da na kai Fatima asibitin kafin in zo office shine muka tarar da good news... Alhamdulillah, Allah ya qara mata lafiya" Yace "ameen my friend thanks.. how's everything in the office??? thank you very much for taking care of things while I am away" Fahad yace "it's okay abokina.. an ce ka je gida ko?" MK yace "yes" Fahad yace "ai gwara ka dan kwanta ka huta zuwa anjima.. you surely need to rest" Girgiza kai MK yayi yace "how can I rest abokina when I just found out that Ummi was physically assaulted and Allah kadai ya sani if it's what led to the accident.." Da sauri Fahad yace "wait what?? are you telling me that someone tried to kill her?? ba ance babu kowa a gidan ba lokacin da abin ya faru?.." MK yace "well lokacin da na shiga gidan babu kowa but according to the doctor's report...." Daga nan ya bashi labarin abinda report din ya fadi da kuma abinda Ummi tace... Shi dai Fahad ko kafin MK ya gama magana yayi suspecting Maleeka. Its logical ai tunda dai bata da wata maqiyar da ta wuce ita!! Ji yayi MK yace "I really dont understand.. ban san ta ya zan gano gaskiya ba.." Kai tsaye Fahad yace "abokina it's simple mana... the CCTV cameras.. ba a kunne suke ba??"5 Gani nayi MK ya zabura ya sauka daga kan gadon da sauri yace "Ya akayi na manta da CCTV cams... hey, zan kira ka anjima" Daga nan ya kashe wayar ya fita. Straight study dinshi ya shiga yayinda ya tafi wurin control na CCTV cameras din gidan. Gani nayi ya kunna na ranar da abin ya faru yayinda ya fara kallo... Tunda ya fara kallo na ga hankalin shi yayi mummunan tashi yayinda na ga ya fara zufa.. Maleeka ya gani ta fito daga sashen ta riqe da file and was on her way going out of the main parlor, ganin Ummi zaune a kan kujera tana video call da shi har tana dariya ne ta dawo and it all happened.. Ji nayi yace "Maleeka???" Runtse idanuwa yayi yayinda yayi relaxing bayan shi a kujerar da yake.. Muryar shi qasa-qasa na ji yace "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un... Maleeka why??? why does it have to be you??"1 STORY CONTINUES BELOW A fusace ya miqe tare da sa hannu ya watsar da tarkacen da ke kan table din.. Gani nayi yana ta naushin table din da hannun shi cike da tsananin bacin rai...1 Ji nayi yace "This is it...." Daga nan na ga ya fita cike da tsananin bacin rai. ♧♧♧♧♧♧♧ ALIYU SODANGI RESIDENCE MAITAMA Zaune take a qasan dakinta yayinda ta jingina bayanta a ottoman din gadonta. Kanta a bisa gwiwowinta yayinda take ta Jan numfashi... da alama dai kuka take yi. Maleeka dai tun ranar da wannan al'amarin ya faru ta shiga tsananin tashin hankali. Babu abinda take yi sai da-na-sanin qin tsayawa taimaka ma Ummi a ranar.. Da ta tsaya wurinta qila da ta rage ma kanta hukuncin da za'a yanke mata na laifin da tayi... da ta rage ma kanta zafin da take ji a yanzu.. haka da tayi facing worst fear dinta tun a lokacin... Tun daga wannan ranar ta birkice gaba daya.. it's been 2 days today and nobody is telling her anything about what happened to Ummi or her unborn child.. Cikin kwanakin nan biyu tayi yunqurin tambayar Mummy halin da ake ciki amma ta ya zata fara?? abu ne da ba fadi mata aka yi ba.. idan har tayi tambaya ya akayi ta sani?? another thing is Mummy ma bata zama gidan kullum.. sai dare take dawowa. Ta tabbatar dai asibiti take zuwa wanda hakan ya tabbatar mata da Ummi is alive.. toh amma meyasa har yanzu bata ji anyi maganar abinda ya faru ba?? Ta sani cewar idan har Ummi ta farfado zata fadi abinda ya faru.. idan har ta farfado ta fadi musu abinda ya faru meyasa har yanzu babu wanda ya tuhume ta?? toh kenan har yanzu bata farfado ba?? kenan Ummi is in a critical condition because of her??? Her greatest fear is reaction din MK idan ya gano abinda ya faru, ta sani sarai idan wani abu ya samu Ummi ko abinda ke cikin ta qarshen zaman su ya zo... kenan sakin ta zai yi!! Zuciyarta ce ta buga yayinda na ji ta fashe da kuka tace "Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un.. na shiga uku.." Bata gama rufe baki ba ta ji an banko qofar dakin ta.. A firgice ta dago kai yayinda ta gan shi cikin yanayin da bata taba ganin shi a ciki ba. Nan da nan cikin ta yayi wani irin qugi yayinda gaba daya jikin ta ya dauki rawa.. A birkice ta miqe tsaye tana kuka yayinda ta fara approaching dinshi tare da hada hannuwanta wuri daya alamar roqo tace "Honey don Allah.." Saukan mugun mari ta ji a kumatun ta wanda ya sa ta saki ihu...1 Cikin kuka ta qara bude bakinta tace "don Allah Honey.." Wannan karon ma bata qarasa magana ba ya sake zabga mata wani marin tare da nuna ta da yatsa yace "one word from you and I swear I'll beat you up" Gaba daya jikinta rawa yake yi yayinda kumatunta suka dauki zugi.. kuka take yi yayinda take ta kallon shi.. A yanzu kuwa ta kasa magana domin ta tabbatar idan tayi magana toh MK sai ya aikata abinda yace... Ganin ya fara approaching dinta cikin yanayi mai ban tsoro ne ta fara komawa da baya.. Da qyar take daga qafafuwanta wadanda suka yi mata mugun nauyi.. Bata ankara ba ta ji ta a jikin bango. MK wanda ya matse ta a bangon gani nayi ya shaqe wuyan ta yayinda na ji yace "why??" Maleeka wadda take kakarin amai ce ta bude baki zata yi magana amma ta kasa... hawaye ne ke ta gangarowa daga idanuwan ta.. Qura mata idanuwa yayi yayinda yake wasu tunani a ranshi.. STORY CONTINUES BELOW this is the first time that he is laying his hand on Maleeka, kai gaba daya ma rayuwar shi bai taba dukan mutum ba sai gashi yau ya mari Maleekar shi- his dearest cousin and beloved wife??!! Yarinyar da ko fada yayi mata ba da son ran shi bane... Ban ankara ba na ga yayi saurin sakinta yayinda ya dan matsa baya a rude.. A wannan lokacin ne ta samu damar yin tari babu kakautawa yayinda ta duqe a qasa... MK yana ta safa da marwa a dakin yayinda yake ta shafa kanshi da hannuwan shi biyu.. Tsayawa tayi cak yace "tunda aka haife ki nake yi miki son da ban taba yi ma wani ba a duniyar nan.. Soyayyar duniyan nan na dauka na dora a kanki Maleeka.. I lived my whole life loving you unconditionally. Tun farko na sani cewar we are two different people with different personalities, We are incompatible in every aspect... halin mu ba daya bane but ban damu da hakan ba because a tunani na soyayyar da ke tsakani na da ke will over power every differences..." Shiru ya dan yi sannan ya cigaba da fadin "...Maleeka I have spent my whole life sacrificing everything for you.. you won't believe me when I tell you I have lost alot of important things in my life for you... I never expected you to do thesame for me saboda duk abinda nayi miki nayi ne don Allah da kuma bala'in son da nake yi miki..." Maleeka wadda ta jingina da bango tana sauraron shi kuwa babu abinda take yi banda kuka... Ji tayi ya cigaba da fadin "..I cared about you alot to the extent that ko sauro idan ina da hali bazan bari ya matso kusa da ke ba balle ya cije ki... kin fi kowa sanin haka but Maleeka you never cared about me... baki damu da al'amura na ba, you dont ask me abubuwan da ke faruwa a rayuwa ta.. idan ciwo na ya tashi you dont even ask me how I am feeling.. the only thing on your mind is yourself and your business. eventhough it hurts, hakan bai sa na rage kulawar da nake nuna miki ba.. infact I loved you just the way you are... I saw your flaws to be so perfect that I never saw any fault in them.. bana taba ganin laifin ki ko da kuwa you are really at fault, afterall you are that little girl I fell in love with.. I was willing to live with you dukda baki shirya cika mun burina ba... it hurts Maleeka, knowing that babban buri na daya a duniyan nan kin qi amincewa ki cika mun shi. You left me for crying out loud and that was when everything changed... SHE came into my life..." Sakin numfashi yayi yace "...ban taba kallon wata mace ba bayan ke.. I dont even have to tell you that because kin sani..." Shafa fuskar shi yayi da hannuwa biyu sannan yace "bazan yi miki qarya ba tabbas tun ranar da na fara jin muryar Ummi nayi feeling wani abu a zuciya ta.. there is this connection that I always feel whenever I hear her voice and then suddenly when I saw her the feeling grew stronger... it was your fault ni da Ummi came close to each other. Laifi kika yi mun Maleeka sannan kika gudu kika bar ni.. She was there for me when I needed you in my life.. You left me all by myself and she took care of me.. UMMI ta kyautata mun in so many good ways da har in mutu I will forever be grateful to her..." Ya kai hannun shi bisa qirjin shi daidai saitin da zuciyar shi take yace "zuciya tana qaunar duk wani mai kyautata mata.. kyautatawar da Ummi take yi mun shi ya sanya ta fara samun mazauni a zuciya ta. She became this special person that I never want to lose in my life.. ta damu da al'amura na.. Cikin lokaci qanqani ta koyi duk wani abinda ta san ina so wanda bata iya ba... hey, it was as if her only mission in this life was to look after me. She was just a maid Maleeka. on the other hand, you are my wife but you never cared. Out of no where kika dawo kika yi mata dukan tsiya kika kore ta.. I was hurt because I lost someone that cared about me alot, maganar gaskiya a lokacin UMMI was my only happiness and I had no choice but to go looking for my happiness. A lokacin da na gano ta kuma abubuwa suka canza.. In order to bring her back with me I had to marry her.." STORY CONTINUES BELOW Yana kallon Maleeka cikin ido yace "ban taba tunanin zan iya kallon wata mace ba balle har in aure ta bayan ke Maleeka.. but what was I supposed to do?? I was not ready to give up my happiness for anything in this life... Yes she was nobody, she had nothing, she was just a maid amma guess what... the maid, UMMI... she gave me everything"1 Hannuwan shi ya sa a cikin aljihun sweatpant din da ke jikin shi yayinda yace "Kar ki manta ina da wani gida a Maitama wanda idan na ga dama zan kai Ummi gidan yadda bazaku taba haduwa ba balle ma har wani abu ya shiga tsakanin ku.. but what will I gain by doing that?? kin sani cewar ni mutum ne da baya son fitina.. even because of my illness I wouldn't want anything that will stress me out but I still feel zaman ku a wuri daya will clear the air, zaku fahimci juna and zamu zauna lafiya.. I wanted to have a beautiful family full of love and happiness.. I wanted you to accept her mu zauna lafiya amma kika qi.. Kin zage ta, kin fadi mata munanan kalamai.. Have you ever sat down to think ya take ji idan kika zage ta kika wulaqanta ta?? kin taba zama kika yi tunanin yadda take ji idan kin zagi iyayenta? Maleeka, Ummi is an orphan.. she has gone through alot a rayuwa. ba laifinta bane don ta tsinci kanta a wurin da ta taso. Ba wai don Allah ya fi son ki bane ya baki gata a rayuwa sannan ya hana mata.. infact you were just lucky to be born into a rich family because da ace hali Allah yake dubawa I doubt if you will fit into the category you belong right now... to HIM we are all equal irrespective of class or whatever. Maleeka a yau idan kika fadi kika mutu you ain't taking all these material things with you.. duk wani abinda kike taqama da shi a nan zaki bar shi.. it shall be thesame piece of white cloth, six feet under, in a normal grave yard. You shall only account for your deeds in the hereafter- Good or bad!!"6 Shiru ya dan yi sannan yace "I told you I was willing to continue living with you on your terms just because I want peace amma kika qi.. she was willing to give me something you didn't want to give me- a child" Muryar shi tana rawa yace "Maleeka, why did you have to destroy my unborn child?? Me nayi miki da har zaki aikata mun hakan?? " A razane Maleeka take kallon shi yayinda take ta rusa kuka... bata taba ganin MK a irin wannan halin ba.. he was heartbroken and very much disturbed.. Muryarta tana rawa ta miqe tsaye tace "wallahi Honey ba da gangan bane.. Na je daukar wasu documents dina ne.. wallahi tsautsayi.." Kafin ta qarasa magana yace "oh just shut up.. tsautsayi akan unborn child dina?? lokacin da kika dauki documents din why didn't you just go? dama opportunity kike nema and you had one.. I swear idan kika qara yin magana I will beat the hell out of you" Maleeka dai jin haka ya sanya tayi shiru yayinda ta cigaba da kuka.. Ji tayi yace "na san kina tunanin Ummi ta fadi mun abinda ya faru ko?? toh guess what?? she didn't, infact qarya tayi mun cewar ta fadi ne.. Yanzu fisabilillah ki fadi mun.. is UMMI a bad person?? even after what you did to her, ta rufa miki asiri. I honestly dont know her reason amma abinda na sani shine Ummi has a good heart which you dont" Jikin Maleeka dai yayi matuqar sanyi.. Tsayuwar ma gagarar ta tayi.. Zamewa tayi a qasa tana ta rusa kuka yayinda kalaman MK suke ta dukan qwalwarta. Bata ankara ba ta ji yace "well dear cousin.. you have succeeded in shattering my dream once again...." Yayi clapping hannuwan shi yace "congratulations to you" Matsowa kusa da ita yayi ya duqo daidai saitin fuskarta yace "ba dai Ummi ba ce damuwar ki?? toh albishirin ki, bazaki sake ganin ta ba" Daga nan ya juya zai bar dakin yayinda hankalinta yayi mugun tashi.. me yake nufi da wannan maganar??? sakin ta zai yi???3 A guje ta bi bayan shi ta riqe qafar shi tana kuka tace "don Allah Honey kayi haquri kar ka.."1 Bai tsaya sauraron ta ba ya fizge qafar shi ya fice ya barta tana ta rusa kuka. Gaba daya ma kasa motsi tayi balle ta bi bayan shi... This is the first time da take regretting dukkanin abubuwan da tayi a rayuwarta.. the first time she wished she could turn back the hands of time idan da hali.. the first time da take wishing she had done things differently because from the looks of it all she has just lost the most precious thing she ever had all through her life... MK!!6 ♧♧♧♧♧♧
Related Posts

Related Posts

Post a Comment