Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NI DA PRINCE CHAPTER 14

NI DA PRINCE CHAPTER 14

- - Post a Comment
NI DA PRINCE CHAPTER 14
Bayan sunyi magrib, salma tai kitchen, salman ya kalleta tare da zama akan kujera, salma ta matso inda yake tare da mikamai remote tace ai kallo, ni zanyi girki, ya riko hannunta yace ummm sai yau zanci abincin matata kenan? Salma tace umm da alamu, sukai murmushi a tare salma tai hanyar kitchen,har lokacin d'ingishi take, salman yakalleta tausayi ya kamashi,ya taso yazo kusa da ita yace beauty na hakura, tace da me? Yace da abincin, kawai ki dafa mana indomie gobe kya mana girkin, tace me yasa😳? Yace kinga dare ne banacin abu mai nauyi kinsani, tai shiru, can tace to shikenan, ya shafa gefen kanta sannan yai murmushi ya juya.+ Salma tai murmushi itama, tare da karasawa kitchen d'in, tafara had'a kayan hadin dazata dafa indomie d'in. Salman na zaune yana kallo, najib ya kirashi, ya d'aga tare da cewa najib ya? Najib yace ina kuka gudu kai da amarya? Salman yace to d'an sa ido, waya fad'ama? Najib yace yanzu nazo ganinka naga farha ta fito ranta a b'ace ko kulani batai ba shine na tambayi bayin gun sukace bakannan, salman yai tsaki yace to tunda ka gama sa idan sai ka koma d'akinka ai, najib yai dariya yace oh ni prince wato yanzu soyayya ta rufe ma ido bama kunya abun? Salman yace oho dai kawai an wani kawo ma mutum bayi b'angare sam an hana mutum yasamu nashi privacy d'in, najib yace ummm da alama abin yafi karfina lalai salma taciri tuta, salman yace inkaji haushi kayi aure, yanakainan ya kashe wayar, najib yai murmushi yace naji dadi. Salma ce ta jera had'adiyar indomie datasha vegetables ta ajiye lemo akan dinning sannan ta karaso inda salman yake, ta mikamai hannu,ya kalleta yai murmushi yace kanshi duk ya cikamin hanci🙂 tace um um fa banda kwad'I🤔 ya mike tare da dafo kafad'arta yace muje sai a tantance, sun karasa salman ya zauna tare da nuna ma salman kusa dashi, tai murmushi tare da zama, ta zubamai sannan tad'au plate zatasa nata, hannunta ya rike yace kisa spoon d'inki muci tare, ta kalleshi ya d'aga mata gira ta sa spoon d'inta nan, nan suka faracin abincin, salman na kai lomar farko ya d'ago ya kalleta tare da👍🏼 ta kalleshi yana had'iyewa yace wow delicious, ta d'an harareshi batace komai ba, aranta tace nikam prince yama surprising d'ina da hallayensa da da ban sansu ba, jitai yace what are u thinking? Takalleshi sannan tai murmushi, salman yaci indomien sosai, sannan sukasha lemo suka mike, salman ya rungumeta yace thanks 4 d meal, ta d'ago tace toh😳, yace ahh yakamata in rage ko? Da sauri tace me? Yace my charm, ta d'ago tasa dariya, yace da alama kina mamaki, wannan salman ne? Anya kuwa? Ta kalleshi tace ni? Inji wa? Yasa hannu daidai zuciyarta yace nan? Tace ni dai banji sanda ya fad'a ba, salman yace dama bake aka fad'awa ba sakon dama ni aka fad'ama, ta kalleshi sannan ta saki wani murmushi. Kallanta yai yace kada ki kuskura kima wani irin murmushin nan kuma, tace wani murmushi? Yace irin wanda kikai yanzu, tai murmushi tare da kama hannunsa tace muyi sallah mu kwanta, salman ya kalleta sannan suka wuce. Sunyi sallah sannan suka shiga d'aki, nan fa aka fara kalan kalo, can salma ta daure tare da daukan kayan bacci tai toilet, salman ya bita da kallo, tana fitowa ta kwanta akan karamin carpet d'in dakin, salman ya kalleta sannan yatuna kalaman daya mata randa aka kaita, murmushi yai sannan ya karaso inda take, baice komai ba kawai hannu yasa ya d'agota, gaba d'aya ya d'agata takalleshi tace *my prince*😳 ya kashe mata ido sannan yai kan gado da ita, ya ajiyeta a hankali, ya matso saitin kunnenta yace banace munzama d'aya ba? Salma tad'an turo baki tace ba....bakishi taji a nata, a hankali ta lumshe ido, sannan ya saketa yace beauty munzama d'aya kuma ni yanzu bana tunanin zan iya bacci banjiki a kusa dani ba😉, kallanshi tai tare da murmushi wani sanyi ne ke ratsata, salman ganin tayi shiru yasa yad'an mike dan cire kaya, hannunsa ta jawo,yana tsaye ya juyo ya kalleta, ta lumshe ido tace thanks 4 saying that, ya lankwasar da kansa sannan ya saki murmushi har fararen hakoransa suka fito, salma ta kalleshi aranta tace niya kamata in hana wannan murmushin ai, salman taga ya sunkuyo yaja hancinta yace bari inzo, tace to, salman yakalleta sannan ya kalli hannunsa, sai a lokacin takalli hannunta, dasauri ta sakeshi tare da rufe ido, ya kara sunkuyowa dai dai kunnenta cikin rad'a yace da alama matarnan batasan mijinta ya matsa, salma tai sauri ta murgina, yai murmushi sannan ya bude jaka, anan ya cire kayansa, salma dai dama tunda ta rufe ido bata juyo ba. Salman na gama shiryawa ya hau kan gado tare da jawo salma jikinsa, harta fara bacci, ya kura mata ido shikad'ai yasan me yake tunani a hankali yakai hannunsa gefen fuskarta ya shafa sannan ya sumbaci goshinta, shima ya kwanta, zuciyarshi sai kwad'aita mishi sha'awar salma ya daure ya tuno wahalar dasha, ahankali ya rufe ido,yana tunani baisan sanda bacci yai gaba dashi.+ Sai asuba salma ta bude ido, tare da kallan salman, murmushi tasake tare da mikewa, balaifi taji saukin jikin ba kamar jiya ba,tai alwala tana fitowa salman ya bude ido cikin kalar bacci, takaraso inda yake ahankali tace ka tashi? Lumshe mata ido yai alamar eh, tace amma kamar ba masallaci a kusa ko? Naga ba gidaje, ya kalleta sannan yakara lumshe ido alamar eh, tai murmushi tace to ka tashe sai muyi sallar? Yai shiru kawai yana kallanta, ta sunkuyo tace kanaji na? Rigarta ya jawo ta fad'a jikinsa, ahankali yace a taimaken a d'agani nakasa tashi, mikewa tai tace ohh pretending? Yai shiru tare da d'aga mata gira, ta mike tare da kamo hannunsa, ahankali ya d'ago ta taimakamai ya tashi, yana mikewa yace tnx beauty☺, tace oh zaka iya tafiyar ashe, ya kalleta sannan yai murmushi yai toilet ta kalleshi tare da tada sallar nafila, tare sukai sallah sunyi adduo'I sannan salma ta kalli salman tace yaushe zamu tafi? Yace ina? Kin kosa ne? Dasauri tace a'a, yasa dariya yace baki kosa ba? Ta mike tare da kwanciya tace nidai yau inaji tsetse fly ne ya cijeni bacci nakeji, salman ya mike yazo ya kwanta kusa da ita, salma ta kamo hannunsa ta rike tare da kwanciya akan kafadarsa, bacci mai dadi ne yai gaba dasu. Farha kam tun jiya tashiga d'aki bakin ciki ya hanata fitowa, da safe fulani taje d'akin tace wai farha meye hakan? Farha tace bafa sannan☹fulani tace an fad'amin to shine me? Farha ta kalleta da mamaki tace fulank kinfa san......fulani takatseta tace farha kidaina bani kunya mana, zan miki abu d'aya, zansan yanda zanyi salman yadawo yau ke kuma sai kisan yanda zakiyi ki aureshi. Farha ta mike tace fulani salman nawa ne tun ina yarinya nasan da haka, ko saurayi nai bana kawo auransa araina salman kawai nake hange, fulani tai murmushin mugunta da alama tasamu wacce zatasa amaida salman kasar waje batare da tayi komai ba. Salma karfe 9 ta tashi, a hankali ta zare jikinta daga jikin salman tai kitchen, dankali ta fara ferewa nan ta fara had'a kayan potato omelette d'in datake san yi, tana gamawa ta sa tafashen naman da suka siyo na sa, bayan ya tafasa tayanka sirara ta hada da karas da tarugu da albasa tai pepper meat. Babu abinda kakeji a gidan sai kanshi, ruwan tea ta dafa ta ajiye a dinning,ta gama ta wanke hannu ta wuce toilet, tana fitowa sanye da towel, salman ya bud'e ido, cikin tsoro ta kalleshi😳, tunanin jiya ne ya fad'o mata, salman yai murmushi sarai ya gane, wata sha'awa ce ta tasomai, yq daure bai ce mata komai ba yai toilet, tabishi da kallo sannan tai ajiyar zuciya. Kaya tasa doguwar rigar material ce ta mata kyau sosai ta tufke kanta bata d'aura d'ankwali ba, salman ne ya fito, ta kalleshi tace muje muyi break, tafad'a tare da matsowa kusa dashi, hannunsa yasa a nata yace harkin had'a mana? Tace eh, yace wooo I think shI yasa naji kanshi a cikin bacci na😎 takalleshi tasa dariya tace ko? Ya maze tace kamar kuma ba haka ba😏, ta turo baki ta kalli gefe, murmushi yai tare da janta, suna zuwa dinning ta bude potato omelette d'in salman yace wow not bad😉 ta hararreshi tare da rufewa, yace to in nace ya burgeni ko da gani zai dadi sai ki kushe shiyasa nima nace haka, tace amma ai.....yace naji amma a bani abinci inaci sai muyi maganar, yafad'a tare da budewa, wuka tasa ta yanka ta d'auramai a plate, yace kai abinnan ya burgeni, naman ta mikomai sannan ta had'amai tea, yace oh karfa dad'I yamin yawa mukoma ince nisai abincin matata🤔, tace nikam bazamu iya zama anan ba? Ya kalleta tare da sa abinci abakinsa yace tun kafin nai aure naso nabar gidan sarauta sai dai bansan meyasa Abba yake hanani ba, salma tai murmushi tace hala yafisan yaganka a kusa dashi ne, kallanta yai bai magana ba kawai ya cigaba dacin abincinsa, itama shirun tai. STORY CONTINUES BELOW Sun gama ta kwashe kwanuka ta wanke sannan ta taho falo, salman na gamawa wanka ya shiga, salma na zaune a falo tanajinshi yana waya batadai san me yake cewa ba, salman na fitowa ya kalleta rai a b'ace yace ki shirya mu koma, da sauri ta mike tazo inda yake tace my prince😳? Bam gane ba? Ya dafata da hannayensa biyu yace wai fulani ce ba lafiya, salma tace naam? Yai murmushin yake yasan rainin hankali ne in bata da lafiyan bakowa a kusa da ita ne? Wai amma waziri ke cemai fulani nata cigiyarsa😠, salma tasan baiji dadi ba tarasa mai zatace mai itama, can ta daure tace bakomai ai zamu iya zuwa wata rana, salman ya rungumeta sosai yace nafisan inganni daga ni sai ke banasan bayin nan, tad'ago a hankali ta kalleshi tace yazamuyi? Salman a hankali yakai bakinshi nata wani salo yake mata wanda yasa ita kanta ta rikice, batasan sanda tafara maidamai ba, cikin d'akin suka shiga sosai, kai da gani kasan basa hayaccinsu. Nikam ganin haka yasa nai baya, kar salman ya makomin harara, kofa na rufe musu......🚶🏻🚶🏻🚶🏻3 Ishaq ne zaune kusa da fulani yace umma me kike shirin had'awa? Ta kaleshi tace name? Yace kinzo kin kwanta kina wani kiran salman nk banfahimceki ba, ta kalleshi ta nunamai ya kori bayin, nan ya korasu ta mike tace kaifa kanka baya ja, ishaq yace zaki fara ko umma? Fulani tace so nake ya dawo, kasan sunyi tafiya da salma? Dasauri ya mike yace what? Umma yazakumin haka?yazaku bar salman yai ta.....fulani tace ai kajika, to ni so nake ya dawo, akwai shirin damuke da farha, ishaq yace dafatan shirin bai shafi salma ta ba? Tace salmar ka? A ina taxama taka? Yace nidai nasan tawace ba kuma abinda yadameni da wani shirinku,nikaina inasan a kori salman amma kar abin yashafi salmata, fulani ta mike rai a b'ace har zatai masifa sai kuma ta tuna yanzu inta mai fad'a kila yaki bata had'in kai hakan yasa tace to in farha ta auri salman ba sai tasa yasaki salma ba kaikuma kaga ai kasamu chance, ishaq ya washe baki yace kumafa hakane, tace kokaifa? Nace zancen kuke so😏aikin kawai😗. Salma kam batasha wahala sosai kamar jiya ba, yau kam tare sukai wanka sannan suka shirya, salma na tsaye jikin madubi tana gyara gashinta, salman yazo tabayanta ya tsaya, takalleshi tacikin madubin tai murmushi a hankali yace sannu beauty, murmushi tai batace komai ba, gashinta ya shafa yace beauty tace naam? Tare da juyowa, yace zan tada mota inzo, tace kacema mai gadi yazo ya fita da sauran kayan abincin da muka siya tunda bamusan ranar dawowar mu ba yace ok👌🏻. Ya fita a ransa shikad'ai yasan irin bakar maganar daya shirya fad'ama fulani zatai dana sanin sashi ya dawo, yasani sarai munafurcine amma bayasan su waziri susan basa shiri. Salma ta gama komai sannan ta rufo gidan tare da karasowa gun motarsu, salman na zaune tunda ta fito ya kura mata ido yana kallo, haryanzu a hankali take tafiya, shikam yana mamaki yanda yake jin shaukin san salma, nai tab'a tunanin akwai maccen dazaiji ta a ransa kamar haka ba.+ Salma ta bude motar ta shiga, kallansa tai tare da matsowa ta hura masa ido, salman ya kalleta tace tunanin me kake? Ya lumshe ido yace shine ai, tunanin me nake? Tai murmushi tace muje? Ya kalleta tare da tada jan motar. Sun d'au hanya, wayar salma tai kara, salman ya kalleta tare da kallan wayar dake hannunta, numberce salma ta kalleshi itakam ta gane number dan number kamal ne, a hankali ta d'aga tace yaya kamal? Kamal daga can yace salma ya kke? Salma ta kalli salman tace lafiya, kamal yace to ya gidan? Zatai magana taga salman ya miko mata hannu, alamar ta bashi wayarta, mikamai tai batare da tayi musu ba duk da a ranta batasan yacima kamal mutunci, salman ya kai wayar kumnensa daidai sana kamal yakara cewa salma ya gidan? Kinyi shiru ko dai......salman ne ya katseshi yace d'an rakiya? Kai ne? Haushi ya kama kamal yace malam kanwaa nake nema ba kaiba😠, salman yai murmushi yace d'an rakiya a ina kasamu number matata? A iya sanina baka da ita, kamal ya cije lebe yace meya dameka? Salma dai kanwatace, salman yai dariya yace okay tunda haka ne bari na kira Abba nasanar dashi irin so da kulawar dakake ba kanwarka kaga sai a maka kyauta😏, kamal yace cemaka nai ka fad'amai? Yafad'a tare da saurin kashe wayar, salman yabi wayar da kallo sannan ya cillama salma wayar. STORY CONTINUES BELOW Ta kalleshi tace ka kware a gun iya fad'ar bakar magana, salman yakalleta yace haushi kikaji? Dasauri tace ni? A'a, yace warning namai at least nasan he is smart zai gane mai nake nufi, salma ta murmushi ba shakka yanzu tasan salman na kishinta sosai. Farha, fulani da ishaq zaune a kilisar fulani, farha na zaune a kasa itada ishaq, ta kalli fulani tace fulani sun taho? Fulani tace hb nasan sun taho tunda tun d'azu akama salman d'in magana, da alama yakamata inshiga d'aki in kwanta, farha tace yaya ishaq dan Allah so nake ka nemomin maganin bacci mai karfi, ishaq yace dafatan ba salma zaki ba ba? Tace haba yaya ina na isa? Yace zan turo akawo miki yanzu, ta kalli fulani sukai murmushi. Suna isa gida sukai b'angarensu, bayi nata gaidasu, salman na shiga ya wuce toilet, ya watsa ruwa tare da d'auro alwala, yana fitowa itama tashiga tai wanka tai alwala, hanne ce tai knocking tasanar dasu an kawo abinci, salma dake tsaye ta kalli salman, ya jawo ta jikinsa ya rungumeta tana daga tsaye, salma tace abinci? Yace not now, ni abinda naci d'azu mai dadi bai bar cikina ba, salma tai murmushi, salman ya kamo hannunta ya zaunar da ita, sannan ya kwanta akan cinyarta, ta shafa kansa tace bacci? Yace eh beauty, tace tunda ka yi sallah, salman yace beauty? Tace naam? Yace bana tunanin zan iya bacci ba'akusa dake ba, salma ta kara shafa kansa sannan tazo daidai saitin kunnensa tace naji dadi, murmushi yai tare da lumshe ido, ita kuma tana shafa sumar kansa a hankali. Salman bacci yake sosai, salma ta kura mai ido tana kallanshi, itakanta tasan sanda takema salma yamata yawa, tana zaune tana tunane_tunane har itama tafara bacci, sai wajen 5 salman ya mike tare da kallan salma data jingina da gado tana bacci, mikewa yai ya gyara mata kwanciya, tare da rufa mata bargo sannan ya fita. Salman kam yana fitowa, yaga wasu fadawa biyu a kofarsa, suna ganinshi suka taho da sauri, suka gaidashi, yace menene? Sukace fulani ce tace musanar dakai tana jira, kallansu yai yace kuce ta jira inada uzuri tukun zan shigo😏, yai hanyar mota ya barsu anan, suma suka juya dan kai sako, fulani ta kwanta a gado ta daddage tana kakaro numfashi irin wacce takejin jiki d'in nan, tad'auka zataga salman, sai dai jitai ance wai yanada uzuri, bakin ciki ya isheta ta tashi zaune tare dayin kwafa, lalai itama ta kosa ai maganin d'an iskan yarancan. Salman dama da saninsa ya fita daga gidan, gidan najib yaje Amir ma na gidan, nan suka shiga tsokanarshi wai ya honeymoon d'in nasa? Salman kam murmushi yai yace matsalarku duk jin kwakwaf d'inku yau sai dai ku hakura dan bazakuji komai ba🤔. Salma bayan ta tashi,ta fita falo taci abinci sannan takira salman, ringing uku ya d'aga tace prince ka fita bakaci abinci ba? Ya kalle najib da Amir da suka matso kusa dashi dan jin kwakwaf, dasauri yace zan kiraki anjima ya katse wayar, salma tabi wayar da kallo tare da mamaki. salman kam kallansu yai yace da alama nakusa daina zuwa nan tunda kun koma 'yan sa ido, dariya sukai sukace yarima kaga yanda kafara canza wa kuwa? Salman yace bansan iskanci, ba wani canzawa, Amir yace ga hasken Amarci nan😃 salman ya girgiza kai tare da mikewa yace mu fita ko? Sukace kai ya kamata dama an dade. Salma kam duk gidan ba dadi haka tai tajinta, takosa salman ya dawo, waya tad'auka kamar ta kirashi sai kuma ta fasa tunda shi yace zai kirata. Salman kam sunje yawo sai 9 sannan ya kamo hanya, waya ya d'aga yakira salma, da sauri ta d'aga, salman yace kinjini shiru ko?tace ina kashiga? Yace ina tare dasu najib ne sun takuramin, tai murmushi tace ka taho? Yace eh ganinan, kinyi missing d'inane?tai shiru, yace ohh da alama dai, tace kaje dubiyar? Nima inasan shiga amma bansan zuwa ni kad'ai, salman yai wani murmushi yace nakusa isowa nan da 5 mins ki fito sai mu shiga tare tace to sai ka iso, nan sukai sallama ta mike tare da d'an gyara fuskarta ta yafa mayafi ta fito. Daga nesa ta hangoshi shima haka tun daga nesa sukema juna murmushi a hankali suka karaso kusa da juna, salman ya kalli salma, sannan ya kalli bayin dake biye da ita ya d'an sukunyo kad'an yace har naji relief dana ganki, murmushi tamai mai kashe zuciya, shima murmushin ya mata suka karasa b'angaren fulani. STORY CONTINUES BELOW Farha ta had'a juice d'in abarba ta zuba maganin bacci tun d'azu suna jiran salman sai dai salman shiru hakan yasa tasa a fridge, tai d'aki tana kokoni. Jin sallamar salman yasa ta fito da sauri, sai dai tai turus, ganin salman da salma a kilisar fulani su biyu, salman yasa hannunsa a kugun salma tana ture hannun tana cewa prince a b'angaren fulani muke fa🙊? Salman yace to sai me? Ya matso daf da ita yace u are my wife, farha ta cika tai fam, tayi gyaran murya tare da karasowa, atare suka kalli gun salma ta had'e rai ganin farha, shima salman d'in fuska ya d'aure, farha kam aranta tace kyalesu,kin manta...hakan yasa ta saki murmushi takaraso tace yayana? Ina kashiga? Salman ya kalleta yace farha dama kinanan? Tad'an bata rai tace yaya yazaka cemin haka🙁? So kake intafi? Salman yace ba haka nake nufi ba, ina umma? Takalli salma tace sannu in_law, sannan tace yaya muje tana d'akinta, salman ya kalli salma yace beauty muje ko? Salma tai murmushi tare da d'aga kai, farha ta maimaita beauty? Tasan beyi karya ba amma kishi duk ya kara cika ta. Suna shiga d'aki sukaga fulani a kwance cikin bargo, dama tunda taji sallamar salman tai saurin rufuwa, salman yakaraso kusa da ita da sauri, yace umma? Jikin ne? Fulani ta saki numfashi tare da d'aga kai, salman yace ayya sannu, har magana bakya iyayi? Ta kasa dakai, salman zai magana yaji muryar ishaq yana cewa umma kina d'aki ne? Yafad'a tare da bankad'a labulen d'akin,ganin salman da masoyiyarsa yasa ya had'iye maganar dayake shirin yi, yakalli salman yace ashe ka iso? Umma sai nemanka take, salman kam ba shakka yasan pretending ne daga yanda yaji ishaq yai magana daya shigo, amma a fili yai murmushi yace ba dole in dawo ba tunda umma ta matso tanasan ta ganni, da alama dai tafisan taganni akanka, ishaq yacd ban gane ba? Salman yace ni danake wani garin? Tunda tasa akirani ai kaga ta kosa ta gannine, ishaq ya d'aure fuska, salman ya kalli ishaq yace umma najin jiki yaya, ishaq yace sosai ma, salman yace ayya, dama haka ne, in mutum ya dade bai yi cuta ba ai da alama sai ya duba ibadunsa, ishaq yace bangane ba, salman ya kalli fulani sannan yace dama ba kowa bane zai gane😏, ran fulani dake kwance ya b'aci wato da ita yake ko wa? Abinciki ibadunsa? Sannan ta matsu ta ganshi? Salman ya kalli ishaq yace yaya ka kula da umma plz kar mu sake wani rashin😞 salma kam kallan salman kawai take tana mamaki mutum irinshi, sai magana cikin magana yake kwaba musu kuma fuskarsa d'auke da murmushi. Farha ce tad'an taba fulani, salma na kallanta, salma sai ji tai fulani cikin dakucewar murya tace salman inasan magana dakai, salman ya kalleta sannan ya nuna kansa yace ni? Ta d'aga kai, farha da sauri takalli salma tace mu basu guri ko? Salma tace eh tafad'a tare dayin waje, farha tai murmushi. Salma na fita ta kalli farha sam batasan zama da ita hakan yasa tace ni nayi gaba bansan how long hirar tasu zata kaiba, farha tace to in law, dama haka suke so, salma ta juya tanajin farha tad'anyi wani shewa itadai tai gaba. Salman na zaune farha ta kawojuice, salman ya kalleta sannan ya kalli fulani yace ya akai? Fulani takalleshi tace salman kayi hakuri nasan kaji haushi danasa ka dawo,salman yace haushi? Wa? Ni? Fulani ta tsani rainin hankalin nan, tadaure tace to kasha lemon mana ko kana tunanin nasa ma wani abu ne? Salman yace wai umma meke damunki? Ban gane kinsa wai abu ba? Fulani ta zubo da kwalla, tace salman na sani bana kyautamaka kayi hakuri dan Allah, salman ya kalleta tare da kallan farha data zuba mai juice d'in tace yaya nina had'ama special, ya amsa tare da kurbar kad'an yace farha bansanki da haka ba shine kika ki d'aukowa tun matata tananan? Tace laa wlh mantawa nai, akwai dayawa inzaka tafi zan bada akaimata ko ibika dakaina in kaimata, salman yace gwara ki hada d'in dai bawai ki bini ba, yafad'a tare da shanye na cup d'in. Farha ta kalli ishaq sukai wani murmushi salman ya kalleta yace meye.....sai dai ganin dishi_dishin daya fara yasa yai shiru, ai bai kara magana ba ya tun tsere agun, farha tasaki dariya suma haka, nan ishaq ya taimakama farha suka kai salman d'akim farhan suka kwantar. Salma kam tana d'aki a tsaye, ganin har 11 shuru ba salman tsoro ya fara kamata kawai ganin text tai a waya, "am sry beauty, zanyi dare ki kwanta". STORY CONTINUES BELOW Da mamaki takara maimaita text din, hartayi cilli da wayar sai kuma ta d'auko, tare da kara karanta text d'in, zanyi dare? Ki kwanta? Salman d'in? Nan rayuwarsu ta jiya da yau tashuga fad'o mata, ta tuna a yanda tasan salman ba abinda zai zaunar dashi acan,tuno sanda farha ta taba fulani tai sannan shewar dataji farha tayi, dasauri ta jawo mayafita wajen 11:30 tai waje, su hanne basu masan tafita ba. Farha kam tanacan tana murna harta hango an fad'ama sarki salman ya kwana da ita, ai ba makawa sai aure. Nikam dariya ma taban dasauri nabi salma ganin tana zuba sauri. Salma na zuwa tai hanyar d'akin fulani, bayin suka tambayeta,salma ta kallesu yace farha fa? Suka nuna mata hanyar d'akinta, salma ta kallesu sannan tai d'akin farhan, batasan meyasa jikinta ke bata farha ce ke shirya wani abu, salma takarasa jikin kofar tare da knocking, farha da ke kwance kusa da salman ta kalleshi sannan ta mike, tace waye? Salma bata amsa ba, hakan yasa farha tai tunanin ko fulani ce, farha ta bude kofar.+ Ganin salma yasa ta zaro ido tare da janyo kofar, sai dai kafin takarasa rufewa salma ta hankad'a kofar da karfinta,😰😳 ganin salman a kwance ya baje yasa jikinta ya d'au rawa, gashi an cire mai riga an barshi da vest, wani mugun kishi ne ya taso mata, ta shiga d'akin rai a b'ace, farha kam jikinta sai b'ari yakeyi tai hanyar kofa da alama so take ta fita, salma na ganin haka tasa gudu ta rigata zuwa kofar ta datse da makulle sannan ta zare makullin, ta watsama farha wani kallo sannan takarasa gun salman. Cikin kishi ya tabashi tace malam mike, tana fad'a hawaye na zubo mata, jin salman yayi shiru yakuma cigaba da baccinsa yasa haushi ya kamata ta jijigashi da karfinta kamar mahaukaciya tace malam ka tashi nace, sai dai salman taga ya koma duk abinnan datake wai bacci yake, tsoro ya kamata kardai mutuwa yai, kallan farha tai dake rakube a jikin bango tana tunanin abinyi, salma ta karaso gunta tana zuwa ta kalleta tace me ya sameshi😠? Farha ta hadI'ye wani yawo tace me yasameshi kuwa banda soyayyarmu da muka tuno? Batai auni ba taji salma ta kifa mata mari, farha ta rike kuncinta tace are u crazy? How dare yo.....salma ta kara mata wani ta d'aya kuncin, farfa ta zabura itama takai hannu, salma tai caraf ta rike hannun, tace baki kai matsayin marina ba, farha tace what? Salma ta kalleta tace farha karkiyi tunanin abinda kike yi tsorone yasa nake kyaleka a'a tausayin ki nake akan kina san maso wani, kuma bari in fad'a miki salman nawa ne wannan kalmar ki ajiyeta a cikin zuciyarki, farha kam jitake kamar ta mutu, salma ta kalli salman sannan ta kalleta tace magani kika samai ko? Farha ta fizge hannunta tace babu wani namiji dayakai matsayin insamai magani,sannan salman shi yakawo kanshi d'akin nan saboda ni, zancen salman nake ne wannan hasasshenki ne kawai, kuma kiyi gaggawar barmin d'aki yanzun nan. Salma ta kalleta tasa dariya tace farha yanda naga alama kamar kanki ba d'aya ba, kinaso kicemin salman neman mata yake ko me? Sannan ke da ake nema kece idanki biyu shikuma mai neman har ya gama biyan bukatarsa ya kwanta? 😅 me kike tunani? Ni yarinyace? Ko kuwa 'yar kauyen dabatasan komai ba? Farha ta ce oho wannan matsalarki ce amma nidai kibarmin d'aki, salma ta riko wuyanta ta kaita bango tace zan buga miki last warning koda wasa kada ki kuskura ki kara had'a mijina da mazinaci, dan wlh I won't tolerate that. Salma na gama fad'ar haka ta sake farha tare da karasawa gun salman, duk yanda ta jijigashi bai mekeba, haka kuma duk yanda taso ta d'agashi ta kasa, hawaye tasa tana jijigashi sai dai ina.....?salman baisan ma tana yi ba, gashi ba damar tanemi taimakon wasu kar a gane. STORY CONTINUES BELOW Salma ta sauko daga daga kan gadon, ta kalli farha tace is not a bad idea hakan da kikai, farha dake tsaye rike da kugu tace what? Salma ta karaso inda take tace canjin gurin kwana, farha tace mekike nufi😡? Salma tace ahhh me nake nufi? Nufina kibar mana d'akin mu kwana, farha tace me kika ce? Salma tace ohhh baki ganeba? Nufina ni da mijina😏 da alama ciwon fulani yasa mijina cikin damuwa shiyasa ya nemi mukwana a b'angarenta, farha tace ke me kike tunanin yi? Salma ta jawo hannunta tace kije ki kwanta ko a kusa da fulani ne mu zamu rufe d'aki🙂. Farha jitai kamar ta shake salma ta kashe wani bakin ciki ne ke yawo akanta, a iya tarihin rayuwarta tana tunanin yaune rana ta farko da aka tab'a ci mata mutunci irin na yau, haka ta fita daga d'akin cikin tsananin bakin ciki. Salma tai ajiyar zuciya tace dama inada zafi haka? Tafad'a tana kallan salman?1 Karasawa tai ta kwanta kusa da salman ta shige jikinsa wasu zafafan hawayene suka zubo mata, ba shakka wannan abun da fulani aka had'a plan d'in amma wannan wace irin tsana ce? Kara shigewa jikisa tai tace *I WILL PROTECT YOU MY PRINCE*. Farha da gudu tai d'akin fulani tana hawaye, fulani kam harta fara bacci, ta mike zaune tace waye wannan?farha ta karasa cikin d'akin, fulani ta kunna fitila, ganin farha yasa tace farha ke kuma menene? Farha kam kuka take, fulani tace meye hakan zakizo kisani a gaba kina min kuka? Farha tace fulani salma ta ruguzamin plan d'ina😭, fulani tace ban gane ba? Wace salman? Farha nan ta shiha zayane mata sai dai bata fad'a salma ta mareta ba😛, ran fulani ya b'aci ta kalli farha bakin ciki da haushin salma yakamata, farha tace yanzu ni da wani idon zan kalli yayana? Fulani ta zuciya tace to ko kin hakura da auransa? Farha tace ban hakura ba, zuwa zanyi gobe infad'ama sarki ya auramin salman ai yayan mahaifinane, fulani tai tsaki tace ke a tunaninki sarki zaiji maganarki yabar ta d'an daya haifa? D'an ma kuma salman? Farha tace fulani yazanyi to? Fulani tace kibari yanzu gobe kiga mai shi salman d'in zai yi, farha tace to, fulani tace ki kwana anan gudun magana tace to.+ Salma kam ta dade batai bacci ba, tunani sun cika mata kwakwalwa, sai can cikin dare batasan yanda akai bacci yai gaba da ita ba, hartai sallah, salman bai farfad'o ba, ta shiga tasbihi, sai 8 sannan salman yai juyi, a hankali ya bud'e idansa tare da sa hannu a kai, jin kan yamai nauyi, salma dake zaune tana tasbihi ta mike da sauri tare da hawa gadon, salman ya mike zaune tare da kallan d'akin, me ya kawoshi nan? Dream ne? muryar salma yaji, ta taba shi tace prince ka tashi? Salman ya kalleta sannan ya kara kallan d'akin, dasauri ya diro daga kan gadon ya kalli salma yace me muke anan? Ta kalleshi ta daure sannan ta kakaro murmushi tace kamanta? Jiya anan muka kwana ai😊salman ya kalleta yace what? Sannan ya ka kalleta yace anan? Tace eh mana yai murmushi yace Do u expect me to believe that? Yafad'a yana nuna kansa, kallansa tai takasa magana, agogon bango dake d'akin ya kalla, 8am? Nan ya tuno shidai yasan an kawomai juice daga nan bazai iya tuna komai ba, dasauri ya matso kusa da salma, ya rike kafad'unta yace beauty? Hawayen datake b'oyewa ne suka zubo, ya kalleta yace me yafaro? Ki fad'an gaskiya, salma ta kalleshi tace ba abinda yafaru, salman ya rungumeta a jikinsa yace bakyaso raina ya b'aci ko? Ta d'aga kai yace amma karki manta nace mu daina b'oyema junanmu komai, salma tai shiru can tace maganin bacci aka sama, dama jikinshi ya bashi yai ajiyar zuciya yace anso amin sharri kenan? Ganina anan ba riga, salma tai shiru, salman ya kara kankameta yace and u protect me ko? Salma dai hawaye ke zubo mata, d'agota yai yasa harshe ya lashe hawayen dake zuba a idanunta, salma kam lumshe ido tai. Salman ya kalleta bayan ya gama yace beauty banason hawaye su dinga zubowa daga kyawawan idanun nan naki, ta bude ido a hankali tana kallanshi, yace don't worry this time I will take care oh them, ya fad'a tare da saketa yace mu fita bazan iya sallah anan ba, salman yad'anyi gaba tare da zura rigarsa, a zahiri ji yake zuciyarsa kamar zata fashe dan bakin ciki, amma yana tunanin in ya nuna gazawarsa ya salma zatai? Wayasan jiya ya tai? Hamdalla yai, lalai shikam yaji dadi samun mata kamar salma sai an tona. STORY CONTINUES BELOW Sun fito harsunyi hanyar fita salman ya kalli salma yace beauty muje muga fulani, ta kalleshi tace da saffen nan? Yai murmushi yace ke kina tunanin jiya sun yi bacci? Tunda kin wargaza musu plan? Kasa tai da kanta, nan sukai d'akin fulani. Ai kam fulani da farha tunda sukai asuba basu samu bacci ba suna zaune suna tunanin me zasu shirya gaba, salman yai knocking fulani tace waye? Salman bai magana ba ya tura kofar, fulani na zane a kan kujera farha na gefenta kad'an, salman yai murmushi ba shakka tare suka had'a, bai taba tunanin farha haka take ba, kallan kofa sukai a tsorace farha take kallan salman amma dayake fulani ta kware tace salman shigo mana, kofa ya kalla tare da cewa beauty ki shigo mana, salma ta shigo d'akin, salman ya kalli fulani yace umma da alama miracle ya faru? Tace name fa? Yai murmushi yace hmm jiya mun kwana anan saboda ke ashe ke kuma sauki har ya iso jikinki😊 fulani ta maimaita kalmar, mun kwana? Lalai yaron nan, salman ya kalli fulani tace baki tambayeni ya kwanan jiya ba? Fulani ta daure tace ya kwanan jiya? Salman yace eh to ba dadi dai, wasu miyagun mutane ne suka kawo min hari? Fulani ta kalleshi da mamaki, salman yai murmushi tare da kama hannun salma yace karki damu umma, ai matata jarumace ita tai yaki dasu, fulani ta makama salma harara, salma ya kula hakan yasa yace zan isar da sako, fulani tace name kuma🙄? Salman yace ki sanar da miyagun mutanen nan in suka kuskura koda wasa suka kara tunanin aikata abinda sukai, sai kuma yai wani murmushi yace umma bansan mezan musu ba dan wlh I won't tolerate it, ba fulani ba, ba farha ba, itakanta salma sai data kalli salman jin yanda ya karara maganar. Ya kalli salma tare da mikewa yace beauty muje ko? Yafad'a tare da mika mata hannu, mikamai hannu tai cikin sanyin jiki ta mike, sun fara tafiya harsun je kofa su farha da fulani sun kafe kamar gunki, salman ya tsaya sannan yace ahhhh, tare da juyowa farka kam zuciyarta tagama tsinkewa, salman yace umma kisanar da mutanen nan duk Wanda ya taba matata sai kuma ya furzar da iskar bakinsa, yai kwafa kawai yai waje, salma suna fita ta rungumshi,salman ya d'agota yace beauty menene? Tace wait...1 min, salman ya dagota yace muje kin manta mijinki baiyi sallah ba? Takalleshi tace wani irin warning ne wannan? Ni wlh kamar ni kakewa, duk na tsorata, yai murmuhsi yace kyalesu muje kinji, tace to. Farha kam da fulani sun dadw ba wanda yai magana fulani sai fila fila take da maganar daya gama dankara mata, itakam har kasan ranta tsoron salman da kwarjininsa take , farha kam jikinta gaba daya ya kame, itakam tad'aukama ta mutu ne. Ohhh *SALMAN*

Post a Comment for "NI DA PRINCE CHAPTER 14"