Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MRS AMIDUD   CHAPTER 1

MRS AMIDUD CHAPTER 1

- - Post a Comment
MRS AMIDUD CHAPTER 1
Hey Durling! Kyale wancan village girl d'incan Ni da nake dake me zanyi da Mahaukaciya." Rike habb'a nayi cike da jin haushi nace. "Duk wanda ya kuma zagina da Yaren da bana wa ba, mey hinsif ya zaga.😏" "Kaiii....Jan Pari me kuma i go fass a he." Dariya na saka cikin jin dad'i nace. "Nusent a dey tali yu, duk cikin bini nu bodi fass min ingilse" 😂😹 Kina wuta Jin yadda suka rud'e da ihu nayi murmushin jin dadi abinka da kauyawa. Nace. "Ef i taili yu, de hawus d'in da muke, ibi laki tangaran, gahi da fanfu, jummalo yo mu ba taliya muke kiran, sufa acan bini sofageti suke ce mihi: "Wayyo Allah na shiga uku, Ke Pari wannan mugun alkaba'in da kike fa, duk a zuwa binin kika koyo" Tura baki nayi gaba cikin kunkuni nace . "kaka Iya, waiti konse yu, she bi a de sifiki ingilise." Kuka tasaka sosai. A rud'e nace "Iya wata de firobilan!?" Kuka ta kuma sakawa tace. "Yanzun abinda Muhmood zai min kenan ya kaiki aljanun nasara sun shigeki: Cikin gafara da nuna Ni naje bini Nace. "Jummalo. I suwai ef i kachi Aaira, i go fass a hedi" 😂😹🙆🏾‍♀️ : "Ya Amidud!" Wani kallon banza yayi min. Kallon kwandon hannuna nayi naci Pilisi. "A go Cross yi hedi da baskit d'in" 🤦🏽‍♂️ Safe goshinsa yayi cikin, baki cikin sabida Aashiq Ali da Aarzam suna tare da shi su kansu kwashewa sukayi da dariya😹😂 turanci, Gyad'a kaina nayi cikin gamsuwa da abinda Aashiq Ali yace, sannan nace "Bat wai kike kafa foo min" Rike baki Aarzam yayi, n kuma cewa. "Bi kos i sifiki ingilise beri wey" A fusace Ya Amidud ya Mike nayi wurgo da baskit d'in😂 : Gyad'a musu kai nayi, Sannan nace musu. "Aunty Lamisah ce tace ita tsani ses, bata son Ya Amidud yana mata ses" Dauke wutaaaa sukayi dan sun fahimci language din: A can sakonni naji Aunty lamisah tana cewa ai ita ta tsani wani kalma wanda yake bani wahalar fada. Ses dan haka na shiga d'akin Mamie suna hira da su Ya Amidud. Nace " Mamie meye ake nufi da ses!?" "Ses!!??" Duk suka juyo da idanunsu kaina, 😂😹🙆🏾‍♀️ "kee Get out banziya kawai ansaki turancin dole ne" Ya daka min tsawa, Murguda baki na nayi sannan nace. "Nu bodi fafet" Hannu Aashiq Ali ya daura akai yace. "Ya Salam no body perfect"😹 [3/13, 4:58 PM] Jan Pari✨: 😳 Zaro ido Ya Amidud yayi yana jin abinda matar shi take cewa. "Honey aljanun ne da ita shi yasa take surutu" Dake yana tsoron aljanun yace. "Dole ma mu maida ita gidan Mamie"5 Cike da bakin ciki nace. "Nu bodi kan tak me go gidan Mamie," [3/13, 9:24 PM] Jan Pari✨: Tafiya nake wai Ni yan mata, ina kareraya, Yana gani na yace. "Ke! Zo nan" Tab'e baki nayi sannan nace. "Mi no go fi cam"🙄 [3/13, 9:25 PM] Jan Pari✨: MRS AMIDUD Kuruciyar JAN PARIH... [3/13, 9:28 PM] Jan Pari✨: Dafe kirjina nayi tare da zare ido nace "aljanun zaku ci kaniyarku" Ihu na fasa tare da kakkafewa, na murgud'a bakina gefe. Nace. "Heehuuuuu! Mu muke ganinsu baku kuke ganins mu ba," yau sai na dauki ribanta" [3/13, 10:01 PM] Jan Pari✨: "Wayyo Allah na, Dole na kaiki gurin, gidan tafisu me bori ta kad'e miki wannan aljanun nasaran" Tura baki nayi cikin kuka nace. "Kaka Iya iz but lai daya, babu aljanus a kaina, na oli Ingilishi" "Wayyo Allah na shiga uku meye kuma ledas Parih aljanun ashe ba d'aya bane har dasu ledas"🙆🏾‍♀️ [3/13, 10:07 PM] Jan Pari✨: Cancaba kwalliya nayi Yaron me gari zai zo min dan tun da na dawo daga bini samarika ke damuna, Ina fitowa na tsaya. Cikin Mugun turancin kare dangi nace. "Barka da zuwa my suwetin hat, kasan weya tugeda" 🙄 Mu yan Bauchi ne, amma karamar hukumar misau, a misau d'in ma can wani ƙauye da ake kira da dabji, Iyayena da Kakanni na duk Fulanin can ne, sai dai Ni mareniya ce, amma me gata da galihu. Iyayena sun rasa rayukansu ne a wata tafiya da suka yi daga bauchi zuwa misau. Inda suka yi hatsarin yar kurkuro wanda iya ke kira da yar kurkuro, a taki suka mutu Ni kad'ai ce na rayu. Kasancewar Mahaifiyata itace auta sai soyayyarta ya dawo kaina, inda Kakata ta roka aka bata Ni, amma da sharad'in da zaran na cika shekara biyu zasu zo daukata. Rimi rimi ta amince, abin dariya sai da nacika shekara biyu ta tubure tace. "Wallahi bani kuma sake na rasa Jan PARIH, kamar yadda na rasa mahaifiyar ta, kuje amma ba zan baku ita ku sanyata a yar kurkura ba dan banza ana, shi kad'ai yana tafiya sai motsi yake." Duk yadda Yaranta da suke bini suka so daukata taki firr, ita tana tsoron kar su sanya ni a yar kurkuro. Tun tasowata *Kaka Iya* take bani labarin hatsarin dake tare da yar kurkuro.+ Yau ma kamar shekaru shida baya, dan duk shekara sai anzo gaban hakimin Dabji, naci kwalliya. Dan na ɗauki aniyar yau zan bar garin dabji ko Iya tana so ko bata so, nima zanje binni na kece reni, Aairah ta daina min feleke ita tana da dangi a can,😏🙄 A yanzun shekarata goma sha daya cif a duniya, naci ace ina makarantar Finramari amma Iya ta hanani wai kar yarda dan makaranta nasara sune suka kirkiri yar kurkuro, ta kashe min iyayena. Zaka sha mamaki dan garin mu yar kurkuro bata shigowa, sai dai a fidda kai da keken shanuwa. Sai ko keke da kuma keke me numfashi, yo naji shima suna kiran shi da wai babur, ranar da aka kawo mana shi, duk yan garinmu sai da muka b'oya. Ina dalilin ina dan mafari, ai kuwa lokacin muna can dandali aka shigo mana dashi, kowa sai da yayi mamakin babbar keke, haka lallai nasara sai dai abar shi inda yake, kuma ba kowa bane yayi wannan tsiyar sai Ilu dan gidan liman dake yana wai daukar mutane zuwa wasu unguwar suna biyan shi. Shine mara mutumci ya kawo mana, Babur me rai, wato da ya buga wata abu na jikinta, ai sai muka ji tace. "Nanananana! Bammmmmm!" Kafin tace. "Burburburbur!" Ai da muka dafe keya take aka shiga gudun fanfalalaki, domin bamu tab'a ganin wannan iftila'in ba, keke me numfashi,, kan kace me tuni dandali ya watsa, sai yan tsirara wanda suka san da abin sai dariya suke, Allah ya kiyashe mu da rayuwar duhun kai.. ..... Yau ma mun same liman da wakilin hakimi kasancewar shi ba mazaunin Dabji bane. Rike kunnena tayi na kuwa saka mata kara, tace. "Yar bante uba! Ko sun ce zasu tafi dake karki bisu, dan yan binni kashe mutane kauye suke, sannan kina ji kina gani za ayi cinikinki na dai gaya miki mu zauna abinmu ko." Gyad'a mata kai nayi, ina kallon Wan mahaifina, Alhaji Muhmood Dabji. Bud'e min hannu yayi naje na shiga cikin babban rigarshi, na zauna. Bayan an bud'e taro da addu'a, Liman ya kalle Kaka Iya, yace. "Iya shekara sha daya ya cika, ina baki manta ba, kece kika ce a bar Jan PARIH ta cika shekara sha d'aya lokacin tana da shekara biyar. Toh ga Muhmood yazo karb'an yar shi." Kallona tayi taga yadda nake lafe a jikinshi, tabbas tana daukar alhakin Muhmood, dan ita shaida ce wannan karon ne bai zo da iyalin shi ba, amma duk zuwa tare yake zuwa da Iyalinsa, kuma suyiwa PARIH sayayyar ban girma. Karkace kai tayi irin ita bari ta gwada ko xan zab'i binsu. Cikin nuna ta tuna da haka tace. "Yo Allah ya gafarta me rawani Baga Jan din ba, sai kin tambayeta ko tana bukatar zama dasu." Gyara zama wakilin hakimi yayi tare da mai da kallon shi kaina yace. "Jal Parih zaki bi Baffanki ko zaki zauna da Iyarki" Kallon Kaka Iya nayi cikin tausayawa nace. "Iyata kiyi hakuri nabiso ko da kwana d'aya ne sai na dawo nima ina son naje naga binnin nan, kamar." "Ke rufe min baƙi, sakarya toh wallahi santsin da ya kwashe ki ya kai ki can zaki gayawa, ince a binnin kika rasa iyayenki shikenan jeki binnin." Mik'ewa tayi tana kad'e gyalenta muryanta na rawa tace. "Muhmood Ni dai ga mareniya don Allah karka bari a cutar da ita, sannan kasa ido kanta kuje kawai karku zo gidana.". Karku sha mamaki a gidan iya mu yaran kananun mun kai goma sha, soyayyar da take min na dabane, bata tab'a min fad'a ba, sai dai zata tsorarta dani abun me cutarwa ne. Tashi nayi na bi bayanta ina kuka, cikin raunin zuciya ta juyo tare da riko hannuna ta kai Ni gurin Baffana tace. "Ku tafi idan na cigaba da ganinta zan iya karya alkawarin da na dauka" Shi kanshi Baffa dan alkawarin da ya daukawa Iyayena akan zai rike ni yasashi matsawa a bashi ni. Gashi yana yawan mafarkin iyayena, suna matsa mishi yaje ya dauko Ni, ina cikin duhu. Haka ya mike tare da musu alkhairi, sannan yasa aka kaiwa Kaka Iya abubuwan da yake kawo min. Dakyar ta amsa tana kukan zuci. Gefe guda kuwa murna nake raina kal. Zabi binnin da ake min gori akai. Haka nabi dangi na musu bankwana, Iya kam shigewa tayi taki min magana da kuka na bar gidan, tunda na hau keken shanu nake raba idanuna, sai da muka yi tafiyar awa biyu sannan muka fito wata duniya, tun daga nesa nake hango shiftawa wasu ana a guje, jinjina kaina nayi cikin mamaki na kalli Baffana nace. "Baffa! Naga wasu ana suna shiftawa a guje menene su." Kallona yayi cikin murmushi yace. "Ai motocci ne!?" Shiru nayi ina nazarin su, can a tuna ai Iya ta tab'a gaya min dayan sunan Yar kurkuro mato. Wanda yayi ajalin iyayena, "Kutt ba dai hine mato ba!?" Kallona yayi sannan yace. "Mota ake cewa" Hannuna duk biyu na daura a kaina na fasa ihu, ina cewa. "Kwarankwatsa bazan bika ba, dan ina zuwa nima kahe Ni zai yi kaga abu a cure." "Ikon Allah! Jan Parih ki shiga babu abinda zai same ki idan munje gurin motar." Zan bud'e baki nayi zan yi magana sai ga wata yar karamar Y'ar kurkura tazo ta wucce fiiiiiiii, kuka nasa tare da cewa. "Aradun Allah bani higa kaga yadda wancan yar kurkuro ta shika a guje, sai kace zata kai sako bangon duniya" Me Nura drive zai yi ban da dariya, muna isa gurin yar kurkuro, na tsaya a bayan Baffa ina kallon inda Yan kurkuro suke tsula gudu, sai kaji sunce shuuuuu kiiiiiiii, kai wannan yar aba akwai shai'dana. Kallon Baffa nayi shima Ni yake kallo yana tunanin yadda zan shiga yar kurkuro. Nuna mishi inda yar kurkuro suke rantawa a guje nayi sannan nace. "Shi wancan gurin taburma da ruwa ce aka shimfida." Kallon gurin yayi sannan ya ce. "Parih ai kwaltace." Wato tsabar ban fahimci maganar shi ba, ban san lokacin da na d'anne shi. Nace. "Wayyo Allah na Kwarankwatsa bani kwantawa wallahi na yafe zuwa binnin" Duk yadda yaso na sauka a jikinshi naki dan gani nayi kamar zai cillani can, Wata doguwar yar kurkuro ce yazo wuccewa cikin mamaki nace. "Baffa a yar kurkuro akwai macizai ne?" 🤣😂 Low laf Parih na tambayar makapolo wai maciji ne Murmushi Baffa yayi sannan yace. "Ai mota ce itama" Shiru nayi domin tun da nake ban tab'a ganin wannan damuwar ba,juyawa nayi zan koma hanyar da muka fito Nura yayi maza ya kwabko Ni, kuka na saka tare cewa. "Aradun Allah na fasa, kome zaku yi sai kuyi." Aikuwa cusani yayi cikin yar kurkura, ihu na saka tare da kame jikina a bisa wani lallausar abu, tsalle nayi sai da kaina ya buga da rumfar yar kurkura, safe kaina nayi tare da fashewa da kuka nace. "Wayyo Allah na dakwalwata"1 Tadda yar kurkura Nura yayi, Naji ta fara numfashi huuuuuuuuuu. "Wayyo Allah na, wallahi Ni ban nime mutuwa ba, gashi yau za a kaini a cikin yar kurkura, wayyo Allah na wallahi ban gama zuwa binnin ba sai gashi yar kurkura zata kaini lahira" Haba me de na zai ban da dariya, shima Baffa dariyar yake. Shiru nayi ina raba idanu, can idanuna ya sauka akan bishiyoyin da muketa wucce su.+ Sake baki nayi na koma jikin tagar motar ina kallon yadda dariya nasaka sannan nace. "Yan banza in ba tsoron ba, ku kara sauri mana" Girgiza Baffa yayi tsabar dariya, juyawa nayi nace. "Baffa! Nikam A ina muke tafiya badai akan taburma da ruwa nan muke sharara uban gudu nan kamar mu kai sautu bangon duniya." Bai ce min komai ba, shigar mu garin misau, na sake baki ina kallon wata yar karamar Y'ar kurkura, me kafa uku. "Baffa wancan yar kurkura me kafa ukun da" "Keke Napep kenan! Wasu suna kiran da adedaita sahu ko kafin babur" Shiru nayi ina nazarin yar kurkura, can da wata banzar tunani yazo min nace. "Aihoo wancan babur me numfashin ya haifi wannan kafin babur din, ayya hi wancan me kafa biyu. Wannan me kafa uku." Ta madubin drvn ya kalle ni. Shiru suka yi har nima, can kuma nace. "Baffa! Wai me yasa bishiyoyin nan suke binmu da gudu." Juyawa yayi cikin gajiya da damuwata yace. "Sabida su cinye bakin matambayi, koma ki kwanta ko kuma su zo su cinye bakin ki." Zaro ido nayi cikin tsoro nace. "Toh su bishiyoyi binnin haka suke dama" Bai kuma bin takaina ba, har muka bar misau muka nufo Bauchi. Tsayawa mukayi a wani gidan me yawan bututu, sai kallon gidan nake, ina ganin me tuka yar kurkura yaje ya sayo min wani abu da ruwan tare da wasu abubuwa ya kawo min, na amsa sai kallon abin nske. Fita suka yi ina zaune Baffa ya shigo kallona yayi sannan yace. " Parih muje kiyi sayi." "Hmm" nace sannan na fito, muna zuwa ya nuna min ban d'akin da bauta karba nayi ina shiga bayin naga wata yar tunkuya me ban sha'awa, tsayawa nayi ina kare mata kallon cikin jimamin nace. "Alkur'ani bazan tab'a ki ba, sayin ma na fasa to tukunya da rufi, waye zai so b'ata ta." Fitowa nayi naga Baffa yana kallon agogon hannun shi, ajiye butar nayi muka wucce. Muna shiga Baffa ya amshi kayan ya buɗe min sannan ya mika mini wata ruwa baka sai kumfa take.2 Kare mata kallo nayi sannan na girgizata, ai kuwa sai ga kumfa fuuuuuuuu. Ai ban san lokacin da nayi wurgi da goran ba na daka uban tsalle jikina na kerrma. "Wayyo ni Parih naga siddabaru! Wallahi bani shan wannan kayan maitar kaga abu hi daya yana kumfa sai kace tsatsamar nono." Juyowa Baffa yayi dan wurgin da nayi da abin ya b'ata mishi kayan shi. "Sannu Jan ai ba haka ake yi ba, duk kin jika mu." "Wallahi Baffa wancan abin kumfa yake " Jinjina kai yayi sannan ya duba goran wani ruwa ya miko min, Mika min yayi, nasa hannun na amsa cike da tsoro na kai bakina naji babu wannan alluran da suka soke min harshena, wasu abubuwa na leka na kasa ci kamar zanyi kuka nace. "Alkur'an bani cin wanga ana" Ajiye musu nayi a gefe ina tura baki. Muna isa soro naga me rogo washe baki nayi sannan nace. "Baffa ga can rogoji, da kosae" Tsayar da me tuka yar kurkura yayi sannan ya mika mishi kudi, can sai ga shi da nikinikin cima, har da barodi. Kashe bakina nayi cikin dariya nace. "Yau zanci cimar binnin." Yana miko min na amsa na yaga ledar, na zabtari barodi, na shiga dangwala da wannan ruwan dadin nan ina ci. Ai ina gama ci na bingire sai barci, leko Ni Baffa yayi yace "arkin tambaye har tayi barci." Karfe biyu muka iso bauchi, dai dai da farkawata. Kallon garin na shiga yi ina mamakin wani gini da muka wucce, me dororo. "Baffa shi wannan abin mutane basu tsoron ya diro musu tsakar ka." "Me fa Parih!?" Ya tambayeta, "Wancan dororon mana da muka wucce." Jingina kai yayi, tabbas fito da fari daga can shine zai taimakawa rayuwarta gurin samun ilimin addini da na boko, "Baffa! Wannan kuma menene? A nan" ta nuna round about, Murmushi yayi sannan yace. "Wannan shine round about." D'aga kai sama cikin tunani, ta kuma leka Baffa sannan tace mishi. "Kace me sunan hi?" "Round about!" "Aihoo na gane sunan hi, randabat toh kenan randa ake ajiyetawa toh kenan idan Yar a kurkura tana jin ƙishirwa ba sai dai su zo su gyata su hai ruwa kenan" "Bala'iiiiiii!" Inji Nura, me ba Dariya ce ta kwacewa Baffanta yanayi ya kumawa, suna cikin tafiya dake sun biyo ta baya wato Maiduguri bypss, sai ya zagayo dasu Army barrack, dai dai, suka bullo tabaya kenan toh nan ma akwai wani round about, ɗin, wanda kana shigowa Bauchi zaka ga angina Giwa da. Karewa gurin kallo tayi sannan tace. "Baffa wannan kuma randabat din da wancan abun na meye"+ Juyawa yayi dan iya gajiya ya gaji da shegen tambayarta. "Ai yana cinye duk me ganin abu ya tambaya ne." Shiru tayi bata kuma magana ba, har suka wucce jifatu. A can g.r.a ko nace sir kashim, unguwar suka nufa. Cikin sir Kashim din wani had'ed'en gida suka danna. A hankali motar ta shiga gidan, me mugun kyau da ɗaukar hankali, tun a mota Parih take kallon gidan, har motar ta tsaya sannan Alhaji Muhmood ya fito daga motar, ya buɗe mata sauka tayi tana kallon gidan, tunowa da Labarin da Iya Kaka ta bata yasata ja baya, sakamakon hango gidan karshe, wato dakin generator abinda Iya take gaya mata ba komai bane. _Wato kinga mutanen da kayukan mutane suke kuɗi suna da dakin da yake firinji kudi, dan haka ki raba kanki da binnin nan_ Dafa kafad'arta Baffa yayi ta fasa mishi ihu tare da k'amk'ame shi, tace. "Wallahi Ni ku mai dani gida na fasa zuwa binnin" Mamaki ne ya rufe Nura yace.. "Toh meye kuma?!" "Wallahi Iya kaka tace masu kudin binni da kayukar mutane suke yi." Cikin tsananin takaici Nura yace.. "Aikuwa can dakin gurin Franka zamu wulla ki a wancan daki." Aikuwa ta ware murya ta zuduma musu ihu, bana wasa ba, "Haba Nura!" "Kayi hakuri Alhaji yarinyar ce da ban haushi." Riƙe hannunta yayi har cikin gidan, tana tirjewa yana janta har zuwa cikin gidan. Suna shiga yaran shi suka tawo da gudu suna mishi oyoyo aikuwa Parih ta juya da gudu,, sai da yabi bayanta, ta kasa bud'e kofar, abinda ya koreta kuwa, teddy da taga a hannun Aarib, shine ya sanyata wasan tsare. Komawa bayan Baffa tayi ta boya tana leka teddy. "A'ah Alhaji Barka da hanya, Jal Parih, fito mana." Inji wata babbar mace. Kyakyawa me kyan diri, kana ganinta ka ga bafulatana, a kala shekaru hansin da biyu, ka tasowa tayi tace. "Alhaji lafiya? Ku ke tsaye." "Ki bari kawai Adawiyah, Parih ce ta hanani motsi daga shigowar mu shine ta juya a guje dama kuma kafin mu iso sai da muka Ji jiki da ita." Riko hannunta Hajiya Adawiyah tayi. "Ayya ka tuna lokacin da Amatul Islam tazo kafin aurenta da Absham, ai haka muka yi fama da ita har bayan auren su kafin su tafi Pakistan, haka yayi ta Fama da ita." Cikin jimami yace. "Allah ya jikansu da Rahama Amin, gashi yarinya zata tashi bata sansu ba." "Alhaji Barka da zuwa! A'a Parih ce amma Alhaji kunsha artabu da Iyar Parih " "Ke dai bari," "Daddy me ka kawo mana." Yaran suka tambaya, biyu mata sai na miji a tsakiyarsu, Nuna musu Parih yayi, ita kuma hankalinta na kan tv falon inda yake aiki ya fitota da hannu mutumin cikin tv yayi ta girgiza kai, ya kuma kiranta ta girgiza mishi kai bazata zo ba, aikuwa ya taso da sauri. "Wayyo Allah na na higa uku Alkur'an bazan zo ba" Kafin su an kara Parih tayi wani uban tsalle ta koma bayan kujeran falon ta b'oya jikinta na rawa,(🤣😂) Me zasu yi ban da dariya, tsabar kauyanci zalla. Alhaji Muhmood yake basu labarin yadda sukayi da ita kafin ta shiga motar shi, da irin tambayar da suka sha. "Fito abinki kinji Parihna" Zaro ido tayi waje sannan tace. "Kwarankwatsa idan na hito kama Ni zai yi kinga ji ce min yayi nazo" Had'iye dariyar ta tayi, sannan tace. "Babu abinda zai miki, miki kinji fito." "Hikenan zan hito! Don Allah kice mihi kar ya kuma yahito ni."

Post a Comment for "MRS AMIDUD CHAPTER 1"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...