JALILA CHAPTER 5

JALILA CHAPTER 5
A kofar asibitin Dady yai parking sannan sukai shiru a cikin motar, Jalila tasa hannu. zata bude kofar Dady yace "Jalilah!" komawa tai ta zauna tana kallansa tare da amsawa. Dady ya juyo yace "Fatima dan bamu guri." kallansa tai kamar zatai magana sai naga ta fasa, kofar ta bude ta fita sannan ta nufi cikin asibitin. Jalila ta kalleshi sai dai gani take kamar shiryawa sukai, Dady ya kalleta sannan yace "Habiba, na tabbatar kina ganin kamar ban damu dake ba wanda a gaskiyar magana ba haka bane, a duk inda uba yake to lalai tabbas ne yaso abinda ya haifa, kallan mamaki tamai dan tabbas da ace Goggo ba ta bata labarin yanda tai rayuwa dashi ba tabbas zata yarda yana santa sannan zata iya tunanin wani abun akamai daya hanashi nuna mata so. Dady ya kara kallanta yace " kinajin haushi na ko?" kanta na kasa batace komai ba, yace " Jalila wannan auran da za'a miki ba wai rayuwar mahaifiyarki kadai zai taimaka ba, ni kaina kin ceci ni sannan kin taimaki rayuwar yan uwanki."+ Dagowa tai ta kalleshi cikin rashin fahimta tace " Dady ba aure ne tsakaninku da Goggo?" kallanta yai yace "me kike tunani?" Tace " amsar da zaka bani ita zata bani ikon ajiye komai dake raina." Shiru yai yana kallanta yace "Jalila yanzu ba zancen wani aure da rashinsa bane a gabanmu, inhar kinason Inna ta taimaki mahaifiyarki dolene sai kin amince da auran nan, sannan in fada miki gaskiya ko ki yarda ko karki yarda Inna sai ta aura miki yaran nan." Idanunta ne suka fara zubar da kwalla tace "Dady kaine mahaifina ko Inna?" Cikin fada yace "Wai meke damunki ne?yaushe kika fara gardama haka? kina tunanin lalabakin da nakeyi zai baki damar bijirema abinda mukesanki dashi ne? inhar kinasan farincikin uwar data sha wahalarki, kina neman lafiyarta to kibi abinda muka ce miki sannan karki kuskura ki fada mata zancen nan." Kallansa kawai take tana zubarda hawaye, faduwar da Goggo tai kenan su riba suka samu da rashin lafiyarta? tunda batasan dame zasuyi threatening dinta ba. Dady ne yace "muje." A hankali ta tura kofar ta fito, jitai kafafunta na rawa hakan yasa ta rike kofar motar. Haka suka shiga cikin asibitin yana gaba tana baya. ******** A cikin asibitin kuwa Goggo ce tana kwance tana tunanin Jalila da bata dawo ba,Mumy ta turo kofar dakin. Goggo ta kalleta sannan ta gaidata, dan dama tunda sukazo gidan haka suka saba, Goggo ce ke gaidata. Mumy ta zauna a kan kujera sannan ta kalleta tace "Ya jikin?" Goggo tace "Da sauki, tare kuke da Jalila ne?" Mumy tace "eh suna tare da mahaifinta ne yanzu zata shigo." Da sauri Goggo ta canza fuska tace "me yake ce mata? ba dai zance........." Mumy ce ta katseta tana murmushi tace "Kai maman Jalila, ba wannan zancen bane, ai wannan maganar an ajiyeta sai kin samu lafiya, mun isa mu yanke hukunci ne mahaifiyar yarinya na asibiti?" Goggo ta mata kallan zargi, Mumy tace "duk rashin kirkirnmu ai bamu isa yi mata aure dai kina asibiti ba, sannan mahaifinta ma har fada mukai akan zancen nan, ya hana a kara tada shi." Jin hakan ne yasa Goggo tadan saki jiki har tace "mun gode kuna ta dawainiya." Mumy a ranta tace "Yarki dai nayi. Amma a fili tace " Karki damu, ke dai ki kwantar da hankalinki ki samu lafiya, kinga dai irin kudin da ake narkarwa a asibitin nan." Turo kofar da Dady yai ne yasa ta dan canza fuska wai ita a dole fishi takeyi. Jalila ta shigo ta tafi kusa da Goggo ta zauna. Dady fuskarnan a hade yace "Ya jiki?" Tace "Alhamdulila."2 Kusa da ita ya matso ya ajiye mata kudi sannan ya juya. Mumy ce ta mike tace "Sai an kawo abincin dare." Goggo tace "Angode." Haka suka fita, Jalila ta kwanta a kafadarta. Goggo tace "Menene?" Jalila ta kara gyarawa tace " Kawai dumin Goggona nakesan ji." Goggo tai murmushi tace "wani abun ya faru ne?" Tace " me zai faru? Ni fa bangarenmu naje na kwanta, hardasu barci." Goggo tace "kin kyauta, ki dinga zuwa kema kina hutawa, zaman asibiti ba dadi sannan na kula bakya samun barci sosai." Jalila ta daga kai tana murmushi. Goggo ta miko mata duka kudin da Dady ya ajiye tace "irga." Jalila ta irga tace "ni Goggo dubu ashirinn nake gani." Goggo cikin mamaki tace "dubu ashirin? Me zamuyi da kudi haka? Sannan ni tunda nake a rayuwata ban taba rike kudi mai yawa haka ba." Jalila a ranta tace " gashi kin rike yau tunda suna san saida farincikin yarki." Goggo tai shiru aranta tana mamaki........ *********** A can gidansu Hassan kuwa, Sagir sai karya yai akan sunje sannan shima yayan ya ganta. Ummy duk ta matso dasan jin labari tace "Sagir kana tunanin ta mai?" Yace "kinsan halin yaya baice komai ba amma ga dukan alamu ta kwantamai." Ummy tai murmushi tace "ni kaina nasan zata kwantamai dan wannan inaji a jikina alheri ne atattare da ita." Abba yai dariya yace "Ah Alhamdulila lalai yau hankalinmu ya kwanta." Hassan sai wajen magrib ya dawo, yana shigowa Ummy ta fito cikin farinciki tace "Hassan ka dawo?" Kai ya daga kawai ya nufi sama. Yana shiga daki, kafin kofar ta rufo Sagir ya shigo, yace "Yaya dan Allah me ka aikata dazu? Ta ya zaka tafi ka barmu a gidan yarinya?" Hassan bai tanka mai ba sai rigarsa da ya cire dan dama ya gaji da ita. Sagir yace "Amma Yaya wlh ba dadi, bakaji yanda na ji kunya ba, gashi an hada maka abinci kala kala. Hassan ya juyo ya kalleshi, Sagir yace "Ya Hassan." Hassan ya matso kusa dashi yace " Sry." Ya juya yaja towel ya shiga toilet. Sagir ya bishi da kallo sannan yai ajiyar zuciya. Juyawa yai ya koma d'aki, dan shi yau abin duniya shima ya dameshi. Baiga Jalila a makaranta ba daya koma sannan duk yanda ya sake kiranta a waya sai acemai a kashe take. *£*£*£££** Ta kowani bangare shirin aure sukeyi, Sagir ya dawo kasa an kara gyara musu saman, sai dai duk yanda ake shirin auren nan Amarya da Ango ko a tsikar jikinsu, dan ita tana asibiti gun mahaifiyarta, yanzu ko gidan ma bata zuwa, kayanta kala uku data taho dasu shi take ta sawa. Sam batasan auran sati biyu aka saba itadai kawai tasan batasan zuwa gidan ne ma bare a mata zancen. Kudin da Dady ya basu shi suke dan kwalam dinsu, sai abinci da ake aiko musu, kaf gidan ba wanda ya sake zuwa duba Goggo sai Sultan da yake zuwa duk bayan kwana biyu, sannan ita ko lefen ma da aka kawo basu nuna mata ba, ita kuwa dama ba wannan bane a gabanta, bakincikinta inda zataga Ya Sagir. Zuwanta makarantarsu uku amma ba ta taba dakar sa'ar ganinsa ba, har ta hakura. A yau da yazone wanda kwananta 10 kenan da zuwa gida wanda yai daidai da kwana 11 da kawo lefe. Yau saura kwana uku kenan bikin ta amma bata sani ba. Tana zaune bayan sunci abincin safe Sultan yazo shi da wata yarinya wacce batakai Jalila ba, gaida Goggo yai. Jalila ta kalleshi tace "Sultan wannan fa?" Yace "itace zata dinga tayaki zama, mai kula da Goggo." Gabanta ne ya fadi dan tabbas ta fahimci me hakan yake nufi, yace "sannan Dady yanasan ganinki yanzu." Jalila tai yake tana kallan Goggo, Goggo cikin mamaki tace "Allah sarki angode, kinga yanzu sai ki taimaka inkinje gida ki huta ki bari sai gobe ko jibi kya dawo tunda kinga jikin nawa ai da sauki sosai, ni da zasu sallamemu ma da naji dadi." Jalila ta mike jiki a sanyaye, yarinyar ta gaida Goggo, Goggo ta amsa fuska a sake tace "ya sunanki?" Zulai yarinyar ta fada. Jalila ta matso kusa da Goggo ta rike hannunnta idanunta suna neman canzawa tace "Goggo sai na dawo." Goggo ta jinjina kai tace "ki bari sai gobe ko jibi." Tace to. Haka suka fito ta shiga mota. Suna fara tafiya ta kalli Sultan tace "Sultan wani abin ya faru ne?" Yace "ban sani ba sai dai na tabbatar an kusa auranki tunda yanzu ma gidan da mutane, sannan naji Mumy na cewa an turo wai yau kanin Ango zaizo dan kuyi magana, tun jiya yaso zuwa to sai sukai tafiya, bandai san maganar da zakuyi ba." Gaban Jalila ne ya shiga faduwa, a hankali hawaye suka fara zubo mata, kanin ango? Zancen me? Ankusa bikinta? Da wa? Wad'an nan sune suka sake ingizata ta shiga zubar da hawaye. Suna isa gidan ta fara gaida bakin dake gidan, duk yan uwan Mumy ne dan dama a iya tsayin rayuwarta bata taba ganin dangin mahaifiyarta ba, dan duk yawansu ba mai nemansu, sannan shima Dadyn baya kuma san su nemeshin. Shikuwa danginsa dama Mahaifinsa ya dade da rasuwa, sai mahaifiyarsa wacce dama ita kam bata san auransa da Goggo sai Mumy, takanzo lokaci zuwa lokaci, abinda zai baka mamaki shine, ita kadai take zuwa sai kanwarsa wacce dama ita fitsarariyace. Ko sau d'aya Mahaifiyarsa bata taba cewa Innan Goggo tazo suje muhalin yarta ba, Jalila na shekara 10 Allah ya d'auki ran mahaifiyar Dadyn. Shikadai yaje, dan sai daya dawo daga gaisuwa ya aiko mata da tsintsiya, kuka da gyada wai inji babarta sannan tasan yaje, sai Jalila data jiyo gun Safeena akan mahaifiyar Dady ta rasu.+ Kaf gidan yan uwan Mumy ne, sai ita kanwar Dadyn ita kadai. Abin mamaki shine taya akai tasan ana taro? Kuma me yasa itama in zata zo sai dai ta taho ita kadai? Kana ganin hakan kasan Dady ne ke sanar da ita. Jalila itakam gaishesu kawai takeyi, tana gamawa ta mike zatai gun Mumy wacce ta leko tana mata alama da hannu akan tazo. Jalila ta mike zata wuce taji an tawo mata hijab saura kadan ta fadi, kallanta tai zatai magana sai kuma ta fasa tace "Aunty?" Kanwar Dady wato Aunty Adama tace "Ke dama bakida tarbiya, in ba haka ba ki gaida kowa baki ko kalleni ba?" Jalila ta tsuguna tace "Aunty kema kinsan ban ganki bane." Tace "eh ni da nake a kauye ai bazaki ganni ba, tunda kaf falon nan akaina idan naki ya makance." Jalila zatai magana, Mumy tace "Jalila!" Kallan Mumy tai sannan ta amsa, ta kalli Adama kafin tai magana ma tace "tashi kije ana kiranki." Jalila ta mike ta wuce. Tana shiga d'akin Mumy ta rufe kofa sannan ta riko hannunta. Gefen gado ta zaunar da ita ta rike hannunta duka biyun tace "Jalila? Kinji abu kwatsam ko?" Jalila ta kalleta idanunta sun canza kala tace "Mumy ban fahimci abinda ke faruwa ba." Mumy ta rungumeta cikin murya mai rauni tace "Jalila nikaina abin nan na rasa ta ina zan fara sanar miki, dangin mijin ne suka ce suna san auran cikin gaggawa, yanzu nan da kwana uku za'a........." Yanda ta ture Mumyn daga jikinta ne yasa Mumyn yin shiru, Jalila bakinta na rawa tace "kwana uku?" Mumy tace "kiyi hakuri Jalila, sadaukarwa ce kikayi don ceto mahaifiyarki, kinfi kowa sanin Inna inhar bakiyi abinda tace ba, tabbas zata daina biya ma Goggo kudin asibiti ne, sannan zata iya korarku daga gidan nan, kinsan dai ba lafiya ne da ita ba, kar kuje garin wahala ciwon ya cita har azo ana dana sani...." Wasu zafaffan hawaye ne suka zuboma Jalila, ta kara maimaitawa kwana uku? Mumy tace " karki damu, mahaifinki ya yanke hukunci inhar akai auran kikaga ana cutar dake to ki sanar dashi shidakansa zai sa a raba auran." Wayyo yarinta da rashin tunani mai zurfi yasa Jalila tace "Haka yace ?" Mumy tace "sosai, kina tunanin zai bari a cutar dake ne?" Shiru tai tana kallan Mumy, Mumy ta mike ta bude drawer ta d'auko mata wani dankararen material mai duwatsu, tace " ki tashi ki shirya, kaninsa zaizo yanzu, insha Allah Jalila ba abinda zai faru dake, kidinga sa mahaifiyarki agaban komai." Jalila bakinta ma rawa tama kasa magana, Mumy ta mikar da ita tace "kiyi hakuri ki saka Jalila, dan tundazu akace ya taho." Haka ta hau saka kaya tana kuka, tana gamawa Mumy ta mata kwalliya da kanta, ta fesa mata turare sannan ta d'aura mata d'ankwali.2 Jalila tana zaune agaban madubi akai knocking, mai aikinsu ce tace mata wai yana falon baki. Mumy ta kalleta tace "Jalila!" Kallanta tai sannan tace "Mumy?" Mumy ta kara rungumeta tace "Jalila ki yafemin wahalar da na baki a da, ni kaina ina dana sanin yin hakan, kishi ne yasani yin komai."1 Da yake yarinyace mai kishiriwar nuna mata kulawa, jitai gaba daya jikinta yayi sanyi balle dataga Mumy na matse kwalla. Haka Jalila ta fito daga d'akin fa nufi falon bakin. ******** Sagir na zaune yana waya da Abba, yace "Abba nifa kasan bansan me ake cewa ba?" Abba yace "kai dai Sagir sai a hankali, to inkungaisa sai kai introducing din kanka, inkundan yi hira kadan sai ka bata kudin kace na kwalliya ne da wasu hidindimo, dama ai laifinkune da baku bata ba da wuri, sannan laifin yayanka ne da bashida aboki ko d'aya a duniyar nan." Sagir yai murmushi yace "Abba bye na fara jiyo kamshin Amaryar mu." Dariya sukai a tare ya juyo yana cewa "Abba sai.........." Kallan da yake mata ne yasa ya kasa karasawa, Abba ya kashe waya yana murmushi. A hankali ta shigo falon kanta a kasa, kusa dashi taje ta ajiye tiren dake hannunta. Sannan ta dago dan gaidashi. Sagir cikin mamaki yace "Jalila?" Da sauri ta karasa dago da fuskarta tace "Uncle?" Kallan juna sukai kawai sai sukai dariya a tare, yace "Jalila ta!" Kanta ta sunkuyar sannan ta kalleshi tana murmushi tace "Uncle kaine dama? Ya akai kasan gidanmu?"1 Yace "woah da alama we are made for each other, kinsan ban taba tunanin ganinki ba?" Samun kanta tai da zama a kasan gun, fuskarta dauke da tsantsar farinciki tace "Uncle ni kaina nayi mamakin ganinka." Yace "wai ina kika shiga ne? Ko fishin ne yasa aka kashemin waya?" Tace "Uncle wata matsala ce ta hanani magana dakai." Shiru yai yana kallanta, yanayin fuskarsa ne ya canza, ido ya kura mata wanda haryasata tsarguwa, tace " ka ganni kamar bani ba ko?" Idanunsa na kanta sai yanayin fuskarsa dake kara canzawa, a hankali yace "Jalila nan ina ne?" Tace "Gidanmu ne mana." Wani mugun faduwa gabansa yai ya kara kallanta, itama yanzu jikinta yayi wani irin sanyi a hankali tace "bakasani ba?" Bakinsa na rawa yace " ina Amar Amaryar?" Jalila gabanta ne yai wani faduwa hannu tasa tadan tura jikinta tai baya kadan sannan ta kalleshi idanunta sun ciciko. Sagir ya fara girgiza kai yana cewa "U are not the one ko? Na tabbatar ba ke bace ba ko?"2 Hawaye ne suka fara zubo mata, idanunta na kansa, gaba d'aya jiyai wani irin zufa na keto mai yace "will you please tell me?" Jalila ta runtse ido wasu hawaye suka zubo mata tace "Uncle i am sorry." Sauko wa yai ya zauna a kasa sannan ya sa hannayensa ya shafi fuskarsa, kallanta yai cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa yace "Jalila kinsan waye Angon?" Kai ta girgiza tana hawaye tace "bansashi ba kuma bana sha'awar saninsa Uncle, kai nake so kai kadai nakeso Uncle na rasa yanda zanyi, rayuwar........." Tana kokarin sanar dashi rayuwar Goggonta, sai jitai yace "Yayana ne fa."2 A firgice ta bude idanunta, tace "me kace?" Idanunsa ya rufe sannan ya bude yace "Jalila he is my brother." Mikewa tai tana kallansa tace "brother? Ha kana nufin yayanka ne gidanku d'aya? Kenan zuwanka gidan nan a matsayin kaninsa kazo?" Sagir ya rufe idanunsa cikin takaicin abinda ke faruwa? Meke faruwa? Yau me takeji haka? Mikewa tai da sauri zata fita. Jitai yace "He is someone whom i love alot." Tsayawa tai cak ba tare da ta juyo ba, idanunsa ne suka zubo da wasu kwalla yace "He is someone whom I respect alot." Yacigaba "He is someone whom I can't compare to anyone, i can sacrifice everything for his happiness." Jalila ta juyo da sauri tace "me kake so kace?" Idanu ya rufe wasu hawaye suka zubomai yace "Jalila bazan iya fad'a miko komai ba ayanzu, sai dai a hankali zaki fahimci abinda nake nufi ba sai dai bazan taba zama dalilin da zai zama silar bakincikin zuri'ar mu ba." Kallan mamaki Jalila takemai, sai hawaye dake ta gudu a idanunta tace " Kana san kaima kace inyi hakuri da auran kenan?" Sagir ya taso a hankali yazo inda take, kallanta ya shiga yi hakan yasa ta rufe idanunta tana hawaye. Jin batajin motsinsa ne yasa ta bude idanunta a hankali, me zata gani? Sagir ta gani gwiwowinsa a kasa. Da sauri ta ja baya tace "Uncle me kenan?" Sagir yace "That is how much he means to me." Jalila kallan tsoro ta fara mai, tama kasa magana sam, sai kai da take girgizawa a ranta tana cewa "banda kai Uncle, Please banda kai, ko kowa zai fada Please banda kai, Please ku tasheni daga baccin da nakeyi." Sagir a ransa yana hango abinda zai faru inhar ya nemi bin zuciyarsa, yanzu ma da ya ya yayan nasa ya yarda? Sannan inya tuno da tashin hankalin da iyayensa ke ciki da abinda Hassan yamai a rayuwa bayaji akwai wani abu a cikin duniyar nan da zai kasa barmai, inya tuno da rashin lafiyarsa kuwa tabbas mace kamar Jalila itace best choice, sai dai kai fa?" Abinda zuciyarsa ke fadamai kenan, muryar Jalila yaji tace "Uncle have you ever love me?" Kallanta yai yana murmushin takaici, tace " me yasa kowa baya tunani na? Me yasa kowa yake san tsaramin rayuwata? Me yasa kowa yakesan ya zama nice mai sadaukarwa? Me yasa kowa yakesan yin amfani da ni?" Tsugunawa tai a gun kawai tasa kuka. Gana daya ya rasa yanda zaiyi, harcikin zuciyarsa yakejin kukanta. Baice mata komai ba sai tafasa da tasa zuciyar takeyi. D'agowa tai ta share hawayenta kawai ta meke zata fita. Sagir har ya kai hannu zai riko mayafinta sai ya fasa. Cewa yai "Jalila!" Kallansa tai sannan tace "zan shiga ciki." Yace " bamu gama magana ba." Tace " na fahimci me kakeso kacemin." Yace "Akwai sakon dana kawo miki." Cikin mamaki ta kalleshi, tana kallansa ya mike yaje inda yake a zaune dazu ya d'auko wata yar karamai jaka ta kwali sannan ya mika mata. Hannu tasa ta amsa sannan ta kalleshi, bai saki jakar ba yace "Jalila Please." Kallansa tai bakinta na rawa tace " zan shiga ciki." Sakin jakar tai, hakan yasa yai saurin mika mata yace "Yaya yace inkawo miki na hidindimo sannan yace kiyi hakuri bai samu zuwa ba rannan, da kuma yau." Jalila ta kalleshi kawai dan tama kasa magana. Juyawa yai da sauri, kallan bayansa tai sannan ta fita. Tana tsaye har ya fita daga falon, jitai kanta yayi wani irin sarawa kawai ta zube agun ta zauna, yanzu kam hawayen ma sun kame, sam ta kasa yinkukan, batasan sanda Mumy ta shigo falon ba. Sai jinta tai tana cewa "Dubu d'ari da Hamsin!" Lalai mutanen nan. Kallanta tai sannan ta kalli kudin hannunta, jakar da Uncle ya mika mata ne, har yaushe Mumy ta shigo ta amshi jakar? Mikewa tai dakyar sannan ta fita itama ta baya tana layi, Mumy ko ta kanta batai ba ta fita falo, ta haura sama. Bangarensu ta nufa kawai ta zube a kasa ta kwanta, me ke faruwa da ita? Uncle? Dady? Mumy? Inna? Me yasa kowa yake san tsara mata abinda yaga dama? Me yas ba wanda yake tunanin farincikin ta?" Wasu zafaffan kwalla ne suka gangaro mata, tana nan azaune sam batasan sanda bacci yai gaba da ita ba.+ ********** Sagir kam tana fita daya shiga mota ya ja ta da gudu, gaba daya ya rasa tunanin me ya kamata yai, ta ina zai fara iya zama gida d'aya da Jalila? Sannan amatsayin matar yayansa? Wani irin burki yaja, ya gangara gefen titi sannan ya kashe motar. Kansa ya kifa akan sityarin motar yana tunano kalaman Jalila, idanunsa ya runtse cikin tsananin damuwa, yace a fili "Am sorry, i am really sorry Jalilah."1 Kiran Ummy ne yasa ya d'ago, sannan ya daga wayar, Ummy daga can bangaren tace "My son ya kukai?" Ya kakaro murmushi yace "komai ya tafi daidai Ummy, sannan na tabbatar yarinyar nan zata kula da Yaya sosai." Tai dariya cikin jin dadi tace "kai ma ka gano hakan ko?" Yace "sosai Ummy, she is really kind, innocent and honest, yaya zaiji dadin zama da ita." Ummy tace "Na gode sosai Sagir, sai mumai fatan amincewa da ita." Sagir ya daure yace "sosai ma kuwa Ummy." Tace "Ka taho ne?" "Ina hanya zan dan tsaya wani gun ne." Yace "ba matsala, ka gama abinda kakeyi, sai na ganka." Nan ta kashe wayar tana murmushin jin dadi. Aunty Nana ta kalla wacce ke ce mata, wai da gaske a birni take? Tace "wai ke haryanzu baki yarda ba? Kindauka a kauye take?" Aunty Nana tace "ba wai haka bane." "Ko kina tunanin ba mai bawa Hassan yarsa ne ya aura?" Aunty Nana tace "ni ba haka nake nufi ba, inadai mamaki ne." Ummy ta kalleta cikin mamaki tace "indai har ke yar uwata kika fadi haka ai banaji akwai wanda zai fadi haka naji haushi." Ta mike ta fito daga dakin tanajinta tana cewa "ke dai bakya san gaskiya......" Ummy ta janyo kofar ta fito dan kara duba sama, dan sunce gobe zasuzo jere, ba wani taro zasuyi ba saboda halin da ake ciki, dan sunsan ko sunce zasuyi Hassan bazai taba zuwa ba, aure kawai za'a daura a kawota da daddare.3 Bangaren ya gyaru sosai, tura kofar Hassan tai dan tasan yana ciki. Jin kofar a rufe yasa ta dan yi knocking, Hassan ya mike ya bude kofar. Ummy ce ta kalleshi sannan ta shiga. Hassan ya maida kofar ya rufe sannan ya tako ya zauna abakin gado. Kallan d'akin tai tace "Hassan baka tunanin ya kamata mu canza gado?" Kallanta yai baice komai ba, tacigaba " wannan sofar ma ta tsufa ya kamata mu sa wani, sannan carpet din nan shima ya kamata mu canza shi, Hassan mai kake gani?" Hassan bai kalleta ba yace "Ummy Please ki bari." Tace "me? Bakaso a canza?" Yace "na rasa me yasa kike zumudin auran nan, Ummy bakya tsoron abinda zaije ya dawo?" Kallansa tai cikin mamaki tace "me kake nufi?" Yace "Ummy kinfi kowa sanin me nake nufi." Ummy yanayin fuskarta ya canza tace "Hassan please ka dingama kanka fatan alkairi, sannan ka dinga sa salama a cikin zuciyarka." Kallanta yai kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya rasa me yasa duk basa gane abinda shi yake nufi. Ummy tai shiru, jiki a sanyaye ta fita daga d'akin, kallan kofar yai sannan ya runtse idanunsa dan jiya ma sam baiyi bacci sosai ba saboda matsalarsa data tashi, ta ina zai iya zama da mace a haka? Ya tabbatar daga randa ta ganshi cikin wannan halin zata gudu. ********* Jalila haka ta kwana a bangarensu ita kadai, abinda zai baka mamaki ba wanda yabi ta kanta sai abincin dare da aka kawo mata, sannan taje fita da safe mai gadinsu yace ai ance karta sake fita. Haka tanaji tana gani ta dawo ciki. Wanka kawai tai Mumy tazo ta d'auketa sukaje gun salon, a can ne ma ta daure ta tambayeta inda Safeena take. Nan Mumy tace mata tana gidan kanin Inna har yanzu, bayan alokacin ma tana Abuja gidan babban d'an Alhaji Sanusin wato kanin Inna. Jalila bata ce komai ba, haka aka fara mata gyaran jiki, Mumy ta barta agun suka tafi gidan Taura yin jere. Shikam Hassan da sassafe ya garkame dakinsa ya bar musu gidan, Sagir ma yaso gudu sai dai Ummy ce ta hanashi tace "ya kamata ace da namiji agun. Haka ya zauna cikin tsananin damuwa, yana bin masu jeren da kallo. Sai yamma aka turo aka dauketa, Mumyy ta kama hannunta sukai bangaren Safeena. Jalila tace "Mumy gun Goggo nake san zuwa." Mumy tace "kiyi hakuri Jalila sai dai ki je gunta da mijinki, dan umarnin Inna da Dadynki ne." Tasha kuka ranar sai a lokacin tai dana sanin guduwa da batai ba daga gun salon. Haka ta kwana tana kuka, bacci ma sai zarar ta yai. Abinci kuwa dama turawa kawai takeyi. Ba wanda ya damu da ita bare ya fahimci ranmar da tai a dan kankanin lokacin nan. Yau take asabar, Goggo na zaune akan gado tayi shiru tana tunani, me yasa tun jiya take tunanin Jalila? Ta tabbatar inhar lafiya bazata taba yin kwana uku bata zo ta ganta ba. Shiru tai ta shiga yin addu'a akan Allah yasa lafiya, sannan Allah yasa Sultan yazo ta tambayeshi. Jalila kam yau rufe kofar d'akin Safeena tai dan wani irin zazzabi mai zafi ne ya rufeta sam bata san hayaniya. Gudar da taji ne cikin bacci yasa ta bude idanunta a hankali, ba kowa a d'akin sai ita, sai dai daga falo tana jin ana guda. Mikewa taj da kyar ta sa saitin kunnenta a jikin kufar, duk lab'an bakinta sun bushe. Jitai wata ta sakeyin gudar, sai jitai ance "dalla malama yi mana shiru, sai wani guda kike kamar auran yar gata, da auran Safeena akeyi sai mu jure jin gudar nan amma kinzo kin cikamana kunne." Jalila tai murmushin takaici, har zata juya sai taji ance "Wai ke Fatima kin taba ganin mijin ma kuwa?" Tanajin muryar Mumy tace "inafa na ganshi?" Wacce tai magana tace "tunda ance yana da matsala na tabbatar babba ne, kila fa zaikai shekara 40 ko?" Mumy tai dariya tace "ina na sani? Sai ku bari sai ankai Amarya da daddare sai ku tambayeta." "40?" Gaban Jalila ne ya fadi, matsala? Meke faruwa? Duk da tasan dama bazasu taba mata auran mutunci ba amma batai tsammanin babba bane haka, da alama kenan akwai kanne dayawa tsakanin sa da Uncle?" A can gun d'aurin aure kuwa, Hassan dakyar ya tsaya aka d'aura auran, ana fitowa hoto d'aya ya daure akai dashi, shima wasu manyan mutanen Abba ne da bayanda zaiyi, sannan Abban na rike da hannunsa. Ai kuwa suna gama d'auka yai wuf ya tafi. Sagir kuwa, ba'a magana dan kuwa jiyai kamar an jefamasa katan dutse a sanda yaji sanarwar d'aurin auransu. Dole shi ya tsaya aka dinga gaishe gaishe dashi. Dady sai baza ido yake yaga ango amma bai ganshi ba, Sagir dayazo suka gaisa yake tambayarsa ina Angon? Sagir yace "Yanzun nan ya dan fita, kansa ne ke ciwo." Hassan kuwa yana shiga cikin mota ya rufe, jiyai gumi na keto mai ta ko ina, sam hayaniyar nan tasa gaba d'aya jikinsa ya ji gaba d'aya ba dadi. Idanunsa ne suka canza kala, kansa ya kwantar akan kujera ya rufe idanunsa. Firgigit ya farka dan baisan har yadan yi bacci ba, jiyai numfashinsa na neman d'aukewa, nan yasa hannunsa ya rike wuyansa yana kokarin jawo numfashinsa, gaba d'aya jikinsa ya kame, sai uban zufa dake karyomai, idanunsa sunyi jaa sosai, dakyar ya iya jawo numfashinsa. Nan ya shiga yin numfashi akai akai. Jinai gaba daya jikina yai sanyi, dan tabbas duk wanda yaga Hassan zai dauka ko Aljanu ne dashi ko kuma hankalinsa ba daidai yake ba, Hassan meke damunka? Abinda zuciyata ta shiga tambaya kenan? Nace masu karatu ku taimaka min....... Tana zaune a d'aki wajen azahar Mumy ta fara mata knocking. A kasan kofar take a kwance dan zazzabin dake jikinta mai zafine. Da kyar ta iya mikewa ta bude kofar, Mumy tace "Jalila ko wanka bakiyi ba? Naga tun jiya na ajiye miki kayan da zaki saka?" Jalila ta kalleta bakinta na rawa tace " Mumy....." Ganin yanda idanunta keyi yasa Mumy ta riketa, jitai jikinta ya d'au zafi sosai, tace "Zazzabi kike?" Jalila tai shiru, hannunta ta kamo tace " Muje Inna ke nemanki, in ta gama miki magana sai ki dawo ki sha magani." Nan ta rike hannunta suka fito, kallan banza kowa yake mata dan dama duk yan uwan Mumy ne masu tayata kishi da zuga ta. Haka suka shiga d'akin Inna. Tana zaune tana duba abu a waya suka shiga, sai data gama sannan ta ajiye ta kalli Jalila, sannan tai dialing number a wayarta tana cewa " magana zakuyi da Goggonki, ki sanar da ita baki da lafiya shiyasa ba zakizo ba." Kafin Jalila tai kokarin bada amsa, har Inna ta miko mata wayar sannan tasa hands free. Muryar Sultan taji yana cewa "Inna ina Jalilan? Gani a kusa da Goggon." Jalila ta daure tace "Sultan ni ce." Yace "Jalila Goggo na nemanki." Ya fada tare da mikama Goggon waya.+ Goggo na amsa tace "Jalila ina kika shiga?" Jalila tace "Goggo zazzabi nakeyi shiyasa baki ganni ba." Tace "ni ai dama cewa nai ki zauna ki huta, amma na rasa meyasa yau hankalina yake a tashe, dafatan ba abinda ya faru?" Jalila tace "mai zai faru Goggo? Ke dai kawai kice ganina kikeso." Goggo tai murmushi dan hankalinta ya kwanta tace "kinsha magani?" "Eh Mumy ta kaini an banni magani." Goggo tace "Ayya! To ki huta sosai, kar ki damu dani." Jalila ta d'aga kai, idanunta suka ciciko a ranta tacce "Goggo ga yarki nan ana mata auran dole, auran fin karfi, auran mugunta, auran san zuciya...." Jin shiru yasa Inna ta kashe wayar sannan ta kalli Jalila, hannunta ta kamo ta rike tace "good girl, karki damu ki kula da mijinki yanda ya kamata, muma zamu kuka da Goggonki yadda ya dace." Jalila ta share hawayenta tace "Inna dan Allah ku kula da ita." Inna tace " karki damu kanki, ai Goggo tamu ce, ke dai kiyi abinda muka saki." Jalila ta d'aga kai alamar to. Nan Mumy ta kamo hannunta suka fito. Innata bisu da kallo, tabbas dolene su kula da Goggo sosai, saboda yanzu ne zasu kara bunkasa company ta hanyar Jalila. Murmushi tai......... Haka Jalila, Mumy tasata tai wanka, tasha magani, ta sa kaya sannan suka fito tare, gefe guda taja ta zauna. Dan bata jin dadi, daga baya ma data kula hankalin kowa baya kanta ta zille tai bangarensu. Kwanciya tai a inda Goggo take kwana, tana tuno rayuwar da sukai a cikin gidan. Kuka ta shiga yi sosai, wanda ya kara sa mata ciwon kan dake damunta, sai yamma likis tana kokarin fita, Dady na turo kofar. Kallanta yai jikinsa ne yai wani sanyi, yace "tundazu nake nemanki shine Mumyn Yasmeen tace kila kina nan." Jalila ta kalleshi bata ce komai ba, kusa da ita ya zauna sannan ya kalli d'akin, yace "kina tuno rayuwa ne?" Itadai batace komai ba, shiru ne yadan ratsa kafin yace "Jalila kiyi hakuri." Kallansa tai cikin mamaki, yace "bazan nemi yafiya akan abubuwan dana aikata ba, domin har yanzu bana dana sanin aikata su, sannan abinda na aikata a baya sune suka sani nazama abinda na zama yanzu, sune kuma suka taimaka suka inganta rayuwar zuri'ata harda ke kanki, sai dai zan baki hakuri akan auran nan da aka miki dan kuwa na san bamu kyauta ba, sai dai ko yanzu aka dawo da hannun agoggo baya tabbas abinda zan sake yankewa kenan."5 Kallansa kawai Jalila take cikin mamaki, dan ta kasa cewa komai, Dady yai shiru kafin yace "ki taso muje a shiryaki sun ce bayan isha'i zasuzo, dazu akaso kiranki nace a barki zuwa anjima." Bata ce komai ba ta mike ta fita kawai, dan itakam bata san me zata cemai ba, tana koma tsoron kar bakincikin dake ranta yasa ta fadamai kalamai marasa dadi. Haka ta wuce bangaren Mumy, wanka aka sata ta sakeyi tai sallah,sannan Mumy ta sata tadan ci abinci wanda cusa wa kawai tai, sannan ta bata magani, kayan da zata saka ta miko mata. Haka Jalila ta saka kayan nan ba tare da tace kala ba. Mumy ta mata kwalliya tai kyau sosai, turaruka ta fesa mata kala kala. Mumy ta fita dan ance motoci sunzo. Sagir na zaune a cikin mota gaba daya yau banda ruwa ba abinda ya shiga cikinsa, wace rayuwa zaiyi da Jalila a matsayin matar yayansa? Gaba d'aya shikam yasan rayuwarsa ta gama hargitsewa. Haka akai ta shiga motoci har aka fito da Jalila aka bude bayan motar da Sagir ya jawo wacce take ta Abba aka saka ta. Kanta na kasa dan a lulube take da mayafi, tunda suka fito yake kallansu. Jalila na zama taji yacema Mumy ina wuni? Gabanta ne ya fadi jin muryar Uncle, shine zai ma kaita? Me yake nufi da ita? Wani sabon takaici ne ya kara kamata, lalai yau ta tabbatar Uncle ba santa yakeyi ba. Haka suka shiga motar aka ja, ita kadai ke kukanta, wanda kukan ke taba cikin zuciyarsa. Haka sukai ta tafiya har suka isa makeken gidan. Gabanta ne ya shiga faduwa sanda akace ta fito, wai yau itace aka ma aure da wanda ko sani batai ba, ko kawayenta su Zahra basu sani ba, ko Mahaifiyarta bata sani ba.2 Haka ta fito, jikinta na kara tsuma wani sabon tsoro da fargabar rayuwarta na kamata.1 Sukam mutane kowa ko a jikinsa, Mumy na rike da ita suka shiga. A gidan kuwa, Ameerra da Aina'u suna zaune a d'akinsu sunyi shiru, Ameera tace "Aina'u inaji ta iso naji guda." Aina'u ta kalleta cikin takaici tace "Ameera me yasa iyayenmu basa duba abinda ya kamata? Kowa yasan tun ina SS1 nakesan Yaya, ni nace bandamu da matsalarsa ba tunda dai nasan ba hauka gareshi ba, me yasa ba wanda ya duba zuciyata? Ba ruwan kowa da damuwa ta?" Ameera tai tsaki tace "nima Allah naji haushi, ita wannan din dame ta fiki daya sa su Ummy mantawa da ke?" Aina'u tai kwafa tace "ni yau ma zan bi Umma mu tafi." Ameera ta ce "haba dai?" Mikewa tai ta shiga toilet dan bata san jin gudar nan." Aunty Nana kam ta baza ido tana san ganin wacece matar Hassan, Ummy ta kalleta tace "Dan Allah karki bude mata fuska sai ta zauna." Aunty Nana tace "ni rikota kawai zanyi bance wani abu ba." Haka akai ta hawa sana ana ganin tsarin gidan, kowa sai ya yaba sai dai dayake bakin ciki suke. Jalila na zaune a kasa, kanta na kasa tana hawaye. Ummy ta d'agota tace "akaita sama. Nan Aunty Nana ta taso da sauri ta riketa, haka ta kaita d'akinta sannan ta bude mata mayafi, shiru tai tana mamaki dan gaskiya bata taba tunani....... Ummy ce ta dafata sannan ta rufema Jalila fuska tace " muje waje." Fita sukai a falo, Aunty Nana ta riko Ummy tace "kun tabbatar dai yarinyar batada wata matsala ko? Ko halayen banza, kinsan wasu yaran a ido baka ganewa amma a fili sai kiga wasu iyayensu ma sun gagaresu ne."1 Unmy takaici ya kamata tace " ba yanzu zaku tafi bane? Naga duk an fara watsewa." Aunty Nana ta tabe baki tace "ba sai kin kuremu ba." Haka ta sauko tana mamaki. Sagir kam yana maidasu gida yai cikin gari. Ummy na zaune sai kiran wayar Hassan takeyi, sai datai ringing har ta katse sau biyu sannan ya d'auka. Ummy tace "Hassan kana ina?" Yace "waje." Tace "ka dawo gida dan Allah, kaga duk an watse sannan an bar yarinya ita kadai tun dazu." Yace " to in ina nan ma me zan mata?" Ummy tace "nidai ka dawo yanzu." Ta katse wayar tana kallan Abba wanda ya shigo yanzu. Hassan na ajiye wayar yau shiru, can ya tada motarsa ya taho gida. Jalila na zaune gurum ba kowa a d'akin, har ta gaji da kukan tayi shiru, sai dai fuskarta a rufe take. Ummy ce ta fito daga daki ta shiga dakinsu Ameera ta kalleta tana assignment, tace "Ameera tashi kije gun Yayarki kafin Hassan ya dawo." Ameera ta turo baki tace "inje in mata me?" Ummy ta hade fuska hakan yasata mikewa ba tare da ta kara cewa komai ba. A zaune take akan gado Ameera ta shiga, sallamarta ta amsa. Ameera ta shiga dakin tana cewa "ki cire mayafin kisha iska tunda ba kowa." Jalila tace " bakomai hakan ma" Ameera ta zauna akan kujera tana latse latse waya. Haka suka zauna shiru kamar ba kowa a dakin. Sai wajen karfe goma da rabi dan har Jalila ta fara gyangyadi, taji karar bude kofar dakin. Ameer ta mie da sauri tace "Yaya." Kallanta yai sannan yai mata murmushi. Mikewa tai ta fita, Ummy ta gani a kasan beni tace "ina ya shiga?" Tace "dakinta." Ummy tai ajiyar zuciya dan sai data mai magana yanzu akan lalai fa dakinta zai shiga ba nashi ba. Zama yai akan kujerar da Ameera ta tashi, sannan ya kalli inda take a zaune, bai damu yasan yanayinta ba, balle kamaninta. Ita kuwa tunda taji Ameera tace "Yaya!"gabanta ke faduwa. Dakin ya sake yin wani shirun, jitai wuyanta yana neman sagewa. Hassan ya kara kallanta, batada niyyar yaye mayafin ne ko me? Ba dai aikinsa bane? Daga inda yake yace " ki zare mayafin ki kwanta inkinyi sallah, in bakiyi ba ki tashi kiyi." Abinda ya fada kenan, ya mike zai fita. Har ya bude kofa zai fita sai idanunsa suka kalli ledar da Abba ya bashi. Kara maida kofar yai ya rufe, ita kuma ta dauka ya fita ne jin rufa kofa sau biyu. Yaye mayafin tai sannan tai wata ajiyar zuciya. Idanunta ne ya sauka a cikin nasa, gabanta ne ya shiga faduwa, sai dai yanda yake kallanta yasa ta kasa dauke idanunta. Kamar yasan fuskar nan, a ina? Idanun Jalila ne suka firfito, juya baya tai da sauri. Hassan ya matso ya d'au ledar ya mika mata. Ganin bata ganinsa yasa ya ajiye a kasa ya juya. Jalila tana jin ya fita ta juyo tare da ajiyar zuciya. Hassan yayi shiru a dakinsa yana tunani, ina ya santa? Wayar Ummy ce ta shigo, kallan wayar yai hartai ringing uku sannan ya d'aga tana neman katsewa. Tace "kana ina?" Yace "Ummy." Tace "in har kanason na samu bacci ka koma gun yarinyar nan, haba Hassan taya zaka bar yarinya ita kadai bako tausayi?" Hassan yace "Ummy kinsan fa bana iya kwana da kowa." Bata ce komai ba ta kashe wayar.3 Kansa ya dafa cikin takaicin wannan abin......