-->
 • Jelajahi

  ;ƁATACCEN YANAYI COMPLETE (1) A DALILIN MATAR UBA COMPLETE (1) A DUNIYARMU COMPLETE (2) A GIDANA COMPLETE DOC (1) A TUNANINA COMPLETE DOC (1) ABBAS COMPLETE (20) ABDULKADIR COMPLETE (4) ABDULLKADIR COMPLETE (6) ABOKIN MIJINA COMPLETE (1) ADIYYA COMPLETE (2) ADIYYAH COMPLETE (1) ADUN WASU COMPLETE (1) AGOLA COMPLETE (1) AHUMAGGAH COMPLETE (17) AJALIN SO COMPLETE (19) AKAN SO COMPLETE (1) AL (2) AL-AMARIN ZUCI COMPLETE (4) AL'KALAMINE SILA COMPLETE (2) ALMAJIRA COMPLETE DOC (2) ALMAJIRATA COMPLETE (1) AMAL COMPLETE (8) AMAREN BANA COMPLETE (8) AMARIN ZUCI COMPLETE (1) AMININ MAHAIFINA COMPLETE (17) AMJAD COMPLETE (2) ARZIQI RABO COMPLETE (3) ASHE KECE COMPLETE (1) AUREN SIRRI COMPLETE (1) AUREN SOJA COMPLETE (1) BA SONTA NAKE BA COMPLETE (16) BABBAN GIDA CHAPTER 3 MP3 (1) BABBAN GIDA COMPLETE MP3 (23) BABBAN KUSKURE COMPLETE (1) BAGIDAJIYA COMPLETE MP3 (4) BAKAR MACE COMPLETE MP3 (27) BAKIN DARE COMPLETE (5) BAƘIN DARE COMPLETE (15) BANSAN LAIFINA BA COMPLETE (2) BARIKI IYAWA COMPLETE (1) BARIKI NA FITO COMPLETE (48) BARRISTER ASAAD COMPLETE (1) BATACCEN YANAYI COMPLETE (3) BATUUL COMPLETE (24) BAYAN RAI COMPLETE DOC (1) BINTU COMPLETE DOC (1) ƁATACCEN YANAYI COMPLETE (11) CAPTAIN BILAL COMPLETE DOC (1) CIWON IDANUNA COMPLETE (1) COMPLETE (1) COMPLETE DOCUMENTS (10) CONEL AHMARD COMPLETE (6) DA'IMAN COMPLETE (1) DAMATA COMPLETE MP3 (24) DAN ADAM COMPLETE (37) DAN FASHI 🔫 COMPLETE (1) DAN MINISTER COMPLETE (1) DAWUUD CHAPTER 1 (1) DAWUUD COMPLETE (10) DIYAM COMPLETE (20) DR SALEEM COMPLETE (7) DR SAMEER AMEER COMPLETE (2) EL-MUSTAPHA COMPLETE (13) FARA YAR SHEHU COMPLETE (4) FARHA COMPLETE (21) FETTA COMPLETE (31) FIRGITA SAMARI COMPLETE (1) GAMAYYAH COMPLETE (14) GANGAR JIKINSA NA AURA COMPLETE (1) GIDAN SARAUTA COMPLETE (14) GIDAN UNCLE COMPLETE (1) GIMBIYA SA (3) GIMBIYA SA'ADIYA COMPLETE (44) GWARMAYA complete (1) H novels birnin gayu (29) HAFSAT COMPLETE (3) HARSASHEN SO COMPLETE (37) HASKE COMPLETE (27) Hausa novels (35) HIKIMA COMPLETE (10) HUTU COMPLETE (13) IGIYAR RAYUWA COMPLETE (1) IN SO YAKI NE COMPLETE (21) IT IS PART OF THE GIFT COMPLETE (6) Ita (1) ITACE QADDARATA COMPLETE (14) JALILA COMPLETE (13) JAWAHEER COMPLETE (7) JINI DAYA COMPLETE (1) JINNUL AASHIQUE COMPLETE (1) JUYIN RAYUWA COMPLETE (3) K'ADDARACE COMPLETE (14) K'ANWAR MIJINA COMPLETE (1) KADDARA KO SAKACI COMPLETE (3) KAINUWA COMPLETE (9) kANDALA COMPLETE (10) KANO TA JIDDAH COMPLETE (1) KARUWA CE COMPLETE (1) KAWU NANE COMPLETE (1) KAWUNA COMPLETE (8) KE NAKESO COMPLETE (6) KIBIYAR KADDARA COMPLETE (2) KINA RAINA COMPLETE (10) KISHIYOYINA COMPLETE (2) KIYAYYAR ZUCI COMPLETE (3) KOMA KAN MASHEKIYA COMPLETE (3) KOMAI NISAN JIFA COMPLETE (3) KUDIRI COMPLETE (9) kula da kaya (1) LOVE HER SOFTLY COMPLETE (14) MABRUKA COMPLETE DOC (1) MAEESHA COMPLETE (3) MAIRO COMPLETE (5) makaranta duniya (31) MAKIRCI KO ASIRI COMPLETE (4) MAKOTAN JUNA COMPLETE (10) MARWAN COMPLETE (3) MATACCIYAR RAYUWA COMPLETE (36) MATAR SHEIKH COMPLETE (1) MAZA {ALLURAR GUBA}💉 COMPLETE (1) MEYE ILLAR YAYA MATA COMPLETE (24) MIJIN BUZUWA COMPLETE (2) MIJIN HANEEFAH COMPLETE DOC (1) MIJIN YARINYA COMPLETE (2) MRS AMIDUD COMPLETE (12) MRS GURAJE (4) MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE (43) NANNY COMPLETE (3) NAUFAL COMPLETE (2) NAYI GUDUN GARA COMPLETE (39) NI DA PRINCE COMPLETE (19) QADDARAR SUMAYYAH COMPLETE (32) QADDARAR SUMAYYAH COMPLETE MP3 (66) RABO AJALI COMPLETE (8) RAI BIYU COMPLETE (21) RAMUWAR GAYYAH COMPLETE (6) RANA DAYA COMPLETE (3) RANAR NADAMA COMPLETE (2) RAYUWAR ASMAU COMPLETE (14) RIBAR BIYAYYAH COMPLETE (1) RIKICIN WANI GIDA COMPLETE (11) RUDI NE KO BURI COMPLETE MP3 (2) RUDINE KO BURI COMPLETE MP3 (12) RUKAYYAH YAR ALBARKA COMPLETE DOC (1) SAKAMAKO COMPLETE (10) SAMU COMPLETE (7) SAMU YAFI IYAWA COMPLETE (6) SAWUN BARAWO COMPLETE (11) SHIMFIDAR MIJINA COMPLETE (1) SILAR AJALI COMPLETE (3) SILAR GIDAN AIKI COMPLETE (30) SOORAJ COMPLETE (5) soyayyah (1) SOYAYYAH CHAPTER COMPLETE (1) SOYAYYAH COMPLETE (12) SOYAYYAR MU COMPLETE (5) TAGWAYE COMPLETE (36) TAMBARIN TALAKA COMPLETE (1) TANTIRIN NAMIJI COMPLETE (7) TARKO COMPLETE DOC (1) TARKO COMPLETE MP3 (3) TATTALINTA COMPLETE (12) TAZARAR DAKE TSAKANINMU COMPLETE (13) THE BLIND'S MONEY COMPLETE (11) THE CITY COMPLETE (6) TSANANI COMPLETE (20) TSANGAYAR MATI COMPLETE (8) TUN KAFIN AURE COMPLETE (1) TUNTUBEN HARSHE COMPLETE (4) UMARNIN SAURAYI COMPLETE (2) UMMI COMPLETE (15) UNTIL I RELLY DO COMPLETE (14) UZTAZIYA KO YAR DUNIYA COMPLETE (1) WANENE SHI COMPLETE (14) WANI AURE COMPLETE (34) Wata (1) WATA BAKWAI COMPLETE M (17) WATA FUSKA COMPLETE (15) WATA SHARI'A COMPLETE (21) YANAYIN RAYUWA COMPLETE (14) YANKAR KAUNA COMPLETE (2) YAR ALMAJIRA COMPLETE (4) YAR FULANI COMPLETE (2) YAR GWA (1) YAR MAKIYAYA CHAPTER 1 (2) YAR MAKIYAYA COMPLETE (19) YAR SADAKA COMPLETE (2) YAR SHUGABA COMPLETE (42) YAR TALLAH COMPLE (1) YARE BIYU COMPLETE DOC (1) YARIMA ASHMAN (1) YARIMA KHALEED COMPLETE (7) YARIMA SUHAIL COMPLETE DOC (1) YAZEED COMPLETE (3) ZABIN SAMHA COMPLETE (6) ZAMAN HOSTEL COMPLETE (1) ZEENAT YAR JARIDAH COMPLETE (16) ZEHRA COMPLETE (15) ZUCIYA COMPLETE (27)
  Copyright © HAUSA NOVELS
  Best Viral Premium Blogger Templates

  Iklan

  JALILA CHAPTER 3

  Thursday, 3 December 2020, 12/03/2020 05:08:00 am WIB Last Updated 2020-12-17T03:37:37Z
  masukkan script iklan disini
  masukkan script iklan disini
  JALILA CHAPTER 3
  Gabanta ya dawo yace " Me kike tunani kuma?" Kai ta girgiza tace "ba komai." Ya dan canza fuska yace " inata farin ciki zamu hadu yau amma ke naga kamar har yanzu hankalinki baya kaina." Jalila ta sunkuyar da kanta kasa tace "Uncle wlh ba haka bane." Yace " to menene?" Murmushi ta shiga yi tana sunkuyar da kanta, yace "Murmushi?" Tace " a'a." Yace "ni to gaskiya a sanar dani" Kasa ta kara yi dakai tana wasa da hannunta, yace "Ahhh na kula dai dan ina malaminki ne yasa ake kunyata haka, gaskiya zansa a canzamin gun service yanda zanzo har gida kinga lokacin sai a cire kunyar." D'agowa tai ta kalleshi tace "a'a gaskiya." Yace " bakyasan in canza?" Tace "eh." Ya da n yi kasa da murya yace " kinfisan ki dinga ganina kullum?" Kunya ce ta kamata dan kuwa abinda take nufi kenan, bata kula ba ashe motarsu har tazo, horn taji anyi, kallan motar tai sannan ta kalleshi tace "Uncle zan tafi." Ta fada cikin sauri tare da fara tafiya, juyowa yai yana kallanta dan kar ga farga har ta bude mota. Safeena tunda ta hangosu a tsaye ta hade fuska, Jalila na shigowa ta kara kallan Sagir wanda har a lokacin idansa na kallan motar sai da suka wuce. Safeena ta kalleta tace "na fada nace iskanci kike zama yi a makaranta kin nemi karyatani yanzu me zakice? Zance da mai mata?" Jalila tace "Zance kikace ai ba a d'aki kika ganmu ba, a iya sanina kuma shine mijin auren ba ni ba."2 Safeena ta kulu tai kwafa tace "wlh zaki fadama Mumy uban me kikeyi a makaranta." Jalila ta juya kai tanama Yasmeen wasa. Suna shiga gida da gudu Safeena ta je tana kaima Mumy gulma, Mumy ta ce "ya isheni menene damuwarki dan tayi zance a makaranta?" Safeena tace "Mumy?" "Banasan gulma, karki kuskura ki kara kawon gulmar Jalila ba yayarki bace?" Mamaki ya kama Safeena, me Mumy take nufi?1 Ita kuwa Jalila tana cire kaya tana leke ko za'azo a mata duka ko aci mutuncinta, sai dai har ta gama cire kaya bataga Mumy ba. Goggo ce ta fito daga bandaki ta zauna da kyar tace "Jalila kin dawo?" Jalila tace "na dawo kina bandaki." "Wlh cikina ke mirdamin tun jiya, da alama yanayin cin abincin da muka samu ne yasa cikina ya hargitse." Jalila cikin kulawa tace "Goggo in anso miki magani ne?" Goggo tace "barshi kawai." Hijab ta zara tadau dari biyun da Mumy tabata dazu tai waje da sauri. Tana zuwa ta sai mata magani ta fito, a hanya taga mai d'ata shima ta siyi na hamsin, tana shiga gida Dady na shigowa. Sai data jira yai parking ta karasa ta gaisheshi. Leda taga ya miko mata yace "Gashi." Kallan mamaki tamai tace "ciki za'a shiga dashi?" Yace "a'a naki ne." Kallan mamaki ta mai tace "nawa?" Baice komai ba ya fito yai ciki. Mamaki ne ya kamata ta bude ledar, doguwar rigace a ciki da mayafinta, sai kayan kwalliya da turare.1 Kallan Dady ta sakeyi wanda yai nisa, mamaki ya kara kamata, me kenan? Haka ta shiga bangarensu tana mamaki, tana shiga ta mikama Goggo magani sannan ta ce kinga. Kayan Goggo ta amsa tace "daga ina?" Jalila tace "Dady ne ya bani." Shiru Goggo tai tana tunani, tabbas tafi kowa sanin halin mutumin nan, tunda aka haifi yarinyar nan ya bata dan kayan jarirai daga nan bai sake bata ko da da falan atamfa ba, sai sallah ne Mumy zata jefeta da atamfa mai arha, sai kuma wani sa'in in kayan Safeena sun tsufa sai a bata, meke faruwa?" Yanda Jalila taga Mumy ta nustu tana tunani yasa tace " Goggo in maida?" "Ba haka bane Jalila, kawai dai ina mamaki ne." Jalila tace "Goggo ni kaina mamaki abinda ke faruwa nakeyi, kinga an hanani yin aikin gida, sannan jiya Mumy tace wai tabada dinkuna a dinkamin, sannan Inna ma yanzu sakemin fuska take, yanzu kuma Dady, bansan me hakan yake nufi ba" Goggo dan kar Jalila ta damu sai tace mata "kila sun duba sunga yanda kike musu ne yasa suka sauko." Jalila tace "ko?" Tace "sosai ma." Murmushi sukai Jalila ta mike ta wanko musu d'ata suka fara ci, basu gama cinyewa ba aka kawomusu abinci mai rai da lafiya. Wannan sabbabin al'amari haka sukai ta faruwa a kwanan nan, Mumy da kanta tasa aka kwashe tsofaffin kayan Jalila aka sa mata sababbi, sannan tace ta dinga zuwa cikin gida tana kallo, sannan kafin su nemi abu an aiko musu. Itakam Goggo haryanzu bata daina mamakin wannan al'amarin ba, itakuwa Jalila hankalinta a kwance sai soyayya mai karfi da take kara shiga tsakaninta da Sagir.2 Kullum da daddare sai ta ba Goggo labarinsa. Shikansa Sagir ji yake a yanzu babban burinsa bai wuce ya ganshi da Jalila ba. ********** Yau Juma'a tun safe Mumy ta aika Jalila tazo, tare sukaje gun wanke kai aka wanke mata, sannan suka taho a hanya sai wani janta da hira takeyi, cikin hirar ne ta riko mata hannu tace "Jalila!" Jalila ta maida hankalinta kan Mumy. Mumy tace "Jalila kiyi hakuri abubuwan da muka muku a baya, bamu kyauta ba na nuna banbanci tsakaninki da Safeena da mukeyi, ke ce babba sai dai zuciya tasa mun tauye miki hakkinki, mun maidake kamar mai aikin gida." Ta kara raunana murya tace "kiyi hakuri Jalila." Jalila jikinta ne yai sanyi tace "ba komai Mumy sannan ni bakumin komai ba, Goggo itace za'a ba hakuri, ni dama 'yace a gunku kome kuka min dama hakkinane na 'ya inyi abinda kuka sa ni." A ran mumy tace 'Ya? Amma a fili tace "Nagode Jalila, sannan zan ba Goggon hakuri itama, inaso ki cigaba da nuna matsayinki na babba a gidan nan, karki nunama kowa ke din ba 'yata bace, da ke da Safeena duk daya kuke a gurina."2 Jalila tace "nagode Mumy." Haka suka isa gida cikin farin ciki. Goggo kuwa bayan sun fita ta fito da kanta ta kwankwasa kofar falon cikin gida, Yasmeen ce ta bude kofar. Goggo tana dan dingisa kafarta da take mata ciwo, tace "Yasmeen Dadynku na nan?" Tace eh, sannan tai ciki da gudu tana kwallamai kira, dady ne yadan fito ba da dadewa ba. Goggo ta kalleshi sannan ta gaisheshi. Mamaki tai dataga ya amsa, tace magana nakesan muyi. Yace ina jinki. Sai datai dan shiru kafin tace "meke faruwa?" Yace "name fa?" Tace "na canzama Jalila da kukai kai da zuri'arka, nasanka nasan bazaka taba canzawa dan kanka ba sai dai in dakwai abinda kake nufi damu, domin kai da kanka kasanar dani hakan." Yace "ban ganeba?" Tace "ka manta da bakinka kacemi kai a rayuwarka ba so, in har kuwa naga kanasan abu to lalai akwai abinda zai kareka ne." Dady yace " kema kinsan wannan zancene na da, sannan me ya kawo wannan maganar da yar cikina?" Kallan zargi tamai tace" tuni nazo na maka dan baxan taba tafema ba in har ka cutarmin da 'ya ta." Ta juya ba tare da ta nemi amsarsa ba, ko ajikinsa ya juyawarsa ciki. ******** Yau tun safe ake hidima a cikin gida,Mumy ta aika aka kira mata Jalila, tare dukansu suka hadu a kitchen sukai ta aiki, Safeena kuwa tana gidan Kanin Inna a cikin gari, suna gamawa Mumy tace ma Jalila tace tai wanka a toilet din Safeena. Wani had'ad'en material ta dauko mata ta saka, Jalila kam yau tayi mamakin kyan da tai, dan tayi kyau sosai, Mumy da kanta ta daura mata dankwali sannan ta sa mata turare. Wajen azahar motar Taura tai parking a gida. Ummy ce ta fara futowa sannan shikuma ya kashe motar ya fito. Kallo d'aya zakama Ummy kasan macece mai class ba wani shigar karya tai ba sai dai kana ganinta kasan matar manya ce. Taura ya matso sannan ya nuna mata hanyar. Dady ne ya fito ya shigar dasu falon baki, sai wani washe baki yakeyi, Inna ta sauko suka gaisa, nan suka dan tattaba magana akan harkar business, Mumy ta mike ta shigo dakin Safeena inda Jalila take a zaune,tace "Jalila zo ki kai musu abinsha." Jalila ta mike tana cewa "Mumy kunya nake." Mumy ta yafa mata mayafi tana cewa "abokana Dadynki ne gaisawa kawai zakuyi." Haka ta fito ta amshi tiren ta nufi falon, ta rasa me yasa gabanta ke faduwa, yaye labulen tai ta shiga da sallama. Ummy tana shigowa ta kura mata ido, haka kawai taji yarinyar ta shiga ranta, yanayin nutsuwarta ne ya kara burgeta, Jalila ta ajiye tiren kanta na kasa dan ji take kamar kallanta akeyi. Kanta na kasa ta gaishesu, Ummy ta fara amsawa sannan Taura ya amsa ya daura da cewa " Ya karatu?" Tace "Alhamdulila." Yace "ance kun kusa fara jarabawa sai a dage ko?" Tace "insha Allah." Ganin yanda take tsugunne a gun yasa Ummy tace "tashi kije." Nan Jalila ta mike ta fita. Inna ta kalli Ummy tace "kun ganta?" Ummy tace " Mun ganta sai fatan Allah ya kaimu lokacin, sannan muna fatan bazaku mata maganar auren ba har sai ta gama karatunta kamar yanda aka tsara." Inna tace "dama hakan shine daidai." Ummy tai shiru kafin can tace "sai dai ni banasan auren dole, a matsayina na mace banasan tauye hakkin mace yar uwata, kar muje akwai wanda takeso." Mumy tace "in dai wannan ne ba matsala dan Jalila ba ruwanta da kula kowa, ita kunya ma bazata barta ta kula saurayi ba." Ummy ta jinjina kai na gamsuwa, haka suka sa hannu a takarda na yarjejeniya....... Sannan sukai sallama. Nace uhm hmm.......... Ummy har ta sa hannu zata kwankwasa kofar Hassan sai kuma naga ta sauke hannunta sannan ta bi kofar da kallo, juyawa tai jiki a sanyaye tana neman sauka. Sagir ne ya fito daga dakinsa, kallan Ummy yai sannan ya matso gunta, yace "Ummy menene?" Tace " Sagir ashe kana ciki?" Ya kalli shima kofar Hassan sannan yace "Ummy in koma dakin yaya ta karfi?" Harararsa tai na wasa tace "kana tunanin zai barka ne?" Yace "sai in zauna ta karfi ince bazan fita ba." Ummy tai murmushi tace "karka damu insha Allah na kusa samun mai tayashi kwana." Cikin zumudi yace "haba?wanene?" Ummy ta fara sauka daga matatakalar tana cewa " watace." Sagir cikin mamaki yace " Aure?" Nan ta shiga bashi labarin abinda ke faruwa sannan ta daura da cewa " Sagir ni na rasa me yasa tunda na ga yarinyar nan nakeji kamar akwai alamun tauye hakki acikin wannan lamarin."+ Sagir yace "ba wani tauye hakki Ummy, na farko Yaya ba mahaukaci bane, ba kuma nakasashe bane, sannan a zamanin da ai mace ma ance ba sanin wanda zata aura take ba har sai anyi mata auren."2 Kallansa tai tace " hakane nima dan Abbanku sai da aka gama komai na ganshi." Tana fada tana dariya. Yace "kinji ma ko? Wow Ummy harna kosa naga yarinyar, tunda ta kwanta miki ma tabbatar yarinyar ta gaske ce." Ummy tace "kai sai yaushe zaka nunamin taka budurwar?" Yace "nan gaba kadan nafisan ne sai mun rabu ta gama makaranta sai na fara zuwa gidansu a matsayin saurayinta ba malami ba, kinga sai na kawo miki ita kiganta."5 Ummy tai murmushi tace "babban burina a duniyarnan bai wuce abubuwa uku ba Sagir, na farko naga yayanka ya warke ya dawo kamar da, na biyu naga ya samu macen da zata kula dashi na uku kuma na ganka kaima da matar da kakeso kuna rayuwar farin ciki." Sagir yai murmushin jin dadi yace "insha Allah Ummy duka burikan nan naki zasu cika ba da dadewa ba." Haka suka sauko kasa suna hira. ***** Kansa yaji yamai gingirin gim, gaba daya dakin yamai zafi, mikewa yai ya fito daga d'akin ya sauko kasa. Yana jin muryar Ummy dasu Ameera a kitchen, waje yai ya fada motarsa yai waje........... Wani irin farinciki kwanan nan takeji, ga gida yanzu ana santa sosai, ga tsananin soyayya dake kara shiga tsakaninta da Sagir, jiya suka gama waec zasu fara neco, shine yau ta fita da kanta ta hau mota tace gidansu Zarah ta amso aran wasu litattafanta. Tana zaune cikin adaidaita tana murmushi suka dan tsaya saboda dan karamin go slow dake gun, gefenta ta kalla motarsa ce a gun, kallan motar tai sannan tai dan tsaki tace " irin motar wannan dan iskan." Kallan motar ta sakeyi sannan, da yake motar mai tint ce sannan bata ganshi ba a wancan ranar shiyasa bazata iya ganewa ba.3 Sa'a akai ya juyo da fuskarsa inda take, kawai ya hangota tana murguda baki da hararar motar, mamaki ya kamashi dan ya tabbatar bata ganinsa bare tace wani abin ya mata. Har ya dauke idanunsa sai ya kara juyawa, baki ta kara tabewa sannan ta juya kanta tana yan guna guni, kai ya girgiza sannan ya juya fuskarsa. Jalila tana dan masifa tana cewa ai indai na kama mutumin nan ko ban mai komai ba sai na harareshi irin taimakon nan ma bai iya ba, ba kunya ranar ya mata rashin mutunci. Hassan kam gaba yai ya tafi can inda ya saba zama, ya kashe motar sannan ya kwantar da kansa a jikin kujera tare da kunna karatun al-qur'ani, kira'ar Malam Abdullahi Abba ne ya zagaye cikin motar. Jalila an samu jin dadi, yanzu kayanta kala kala, sannan haka zata zauna wani sa'in a falo itafa Yasmeen suyi ta kallansu, duk sanda suke kallan india in ana soyayya itada Sagir dinta kawai take hangowa, ba shakka bata san sanda san Sagir yai nisa a zuciyarta ba. Goggo najin dadin yanda Jalila yanzu ta murmure duk da ba kiba tai ba amma inka ganta zakaga ba wahala a jikinta. A kasan zuciyar Goggo har yau hankalinta ya kasa kwanciya da yanda su Mumy da Dady ke jan Jalila a jiki, sai dai duk sanda Goggo ta nemi Jalila data rage zuwa gunsu Jalila sai tace "Goggo Allah ba abinda sukemin sai mutunci." Jalila an dage sosai ana ta karatun Neco saboda Sagir yace tai karatu sosai dan yanasan yaga matarsa ta cigaba da karatu. Duk sanda yai wannan maganar sai Jalila ta sunkuyar da kai wai ita kunya, sai dai a kasan ranta wani dadi take ji. Goggo har ta gaji da labarin Sagir dan kusan kullum sai ta mata tadin shi. Su kuwa a bangaren su Inner company ya kara habaka saboda sun samu kudi sosai a gun Taura, yanzu company din ma yafi da karfi. Su uku suke tsara abin biki dan har kayan daki sun fara siya, Safeena kuma suna ta shirye shiryen kaita Egypt wai ta cigaba da karatunta. Sai dai ni nasan suna kokarin fita da ita ne dan karma a san da zamanta har sai anyi auren. A can gidan su Ummy kuwa, suma ita da Ameera da Aina'u suna zuwa siyayyar kayan lefe, sanda Aunty nana taji zancen nan har gida tazo tacema Ummy wai tayi dabara ai gwara da suka nemarmai mata ta kudi wai sai yafi daraja. Sanda tai maganar nan Ummy bata tanka ba dan haryau kalaman Aunty Nana na mata ciwo. Yau suke zane paper karshe ta neco, suna fitowa suka hau ihon gama makaranta. Jalila ma zaune itada Zarah a can gefe, Zarah tace "Jalila ni tun jiya nakesan fada miki wani abu." Jalila tace "menene? Fada kukai da Nasir?" Zarah ta juyo saitin Jalila sosai tace "Jalila tsoron abinda na aikata nakeyi." Jalila ta mata kallan tuhuma. Zarah tace "Jalila jiya Nasir ya sani yin abinda na ke ta tsoro." Jalila tace " me ya saki yi?" Idanun Zarah ne suka canza suka ciciko da kwalla tace "Jalila jiya muna tare da Nasir kinsan in zaizo kasan layinmu yake tsayawa sai ni kuma naje saboda tsoron kar yayana ya ganmu, jiya sai na ganshi a mota sai yake cemin motar babansa ce aka aikeshi, bayan mun gama hirarmu a cikin mota zai tafi sai cemin yai wai sai na mai kiss." Jalila cikin tsantsar mamaki tace "kiss?" Zarah ta runtse ido cikin dana sani tace "Jalila kinsan yanda nake tsananin san Nasir ganin ransa ya baci dana tsaya ina tunani yasa na matso kusa dashi na sumbaceshi a kunci, shine yace shi sai na mai a baki, nan na kai bakina saitin bakinsa shine ya rikoni ya dinga tsotsar leb'ena bansan sanda na bude mai cikin bakina ba, Jalila bansan ya akai ba na kasa kwacewa sai bashi hadin kai danai, dakyar na kwavi zuciyata na fizge jikina da sauri na fito daga motar nai gida da gudu........." Kuka ne ya zo mata wanda yasa ta kasa karasa abinda takesan fada, Jalila kam sam tama kasa magana sai inalilahi kawai da take cewa........ Ganin yanda Zarah ke kuka yasa Jalila ta riko hannunta tace "Zarah it's okay! Kinyi laifi babba ma kuwa sai dai tunda harkin fahimci kinyi laifi sai ki nemi yafiya a gun Allah ki kuma kiyayi aikata makamancin abinda kika aikata." Zarah ta rungume Jalila tana kuka, Jalila tace "Sai dai magana daya zan fada miki gaskiya ki bincike san da Nasir yake miki, so ne ko sha'awa, in so ne sai ku tuba ga Allah ku nemi kariya daga shedan in kusa sha'awa ne sai kisan zaman da zakiyi dashi." (_Gareku 'yan mata da samari masu irin wannan soyayyar, sai kaga saurayi yazo gun budurwa in zai tafi sai yace sai ta mai kiss ko sai ya rungumeta, ko kuma ya nemi tamai abinda bai kamata ba, wanda ke da kike aikatawa kinsan haramun ne, sannan shi da yake saki shima yasan haramun ne._ _Dan Allah mu guji fadawa halaka saboda wani buri na zuciyar mu, Allah ya mana tsari ya kare mu daga sharrin zuciya_Ameen suma Ameen) Jalila na zaune itada Zarah tana kara mata fada aka aiko tazo inji Uncle Sagir. Kallan Zarah tai tace "Zarah ina zuwa." Zarah tace " Ba sai kin dawo ba dan na san ba ganinki zanyi yanzu ba." Jalila ta kalleta tace " har kin dago?" Zarah ta harareta tace " yanda kike nunawa ta ya ya zan kasa ganewa? Ba ni ba na tabbatar yawancin mutane sun sani." Jalila ta matso tace "da gaske? Ina nunawa a fili?" Zarah tai dariya tace gashi nan kin rubuta a goshinki da jan biro." Jalila ta dan daket tace "bansan iskanci." Zarah tace "daga ke har shi ai kun gama sanar ma mutane dan ni a bakin mutane ma na fara ji." Jalila ta dan shagwabe fuska tace " kice kowa kallona kawai yakeyi?" Zarah tace "ah to mu ai yan kallo ne." Jalila ta rufe fuskarta tace "bari in rufe fuska ta inje a haka." Zarah tai dariya tana cewa " u are so Naive." Jalila tana ta wani nuku nuku a haka har ta fita dan dama jiya ma a waje suka hadu gaban makarantarsu kadan, wani dan lungu. Sai data dan laleka kafin ta gangara wai ita a dole batasan a ganta. Sagir na kallanta yana murmushi har ta karaso, yace " me kike ta lekawa?" Tace "Uncle ya zamuyi? Duk fa ansan menene tsakanin mu." Yace "to sai akai ya?" Tace "qx Yace "nace sai akai ya?" Tace "hmm hmm" Murmushi yai yace " kin manta kin gama skul? Sannan ba yaudara ko wasa muke ba balle muce bamasan a sani, ya zakiyi in sukazo auranmu? Ko gidan mu?" Idanu ta zaro sai kuma ta rufe idanta da sauri, yace "oh ni wai sai yaushe ne za'a daina min kunyar nan?" Sauke hannu tai tace "ni in kai wata maganar ne sai naji kunya ta kamani." Yace "to da alama zan tattara maganganun dake cina sai munyi aure." Murmushi tai, sun dade tare kafin tace zata tafi, dan yau ita kadai za'azo dauka tunda Safeena tana gidan kanin Inner tun last week tacan take zuwa makaranta. ******** Abba ne ya kalli Ummy yace " ya kamata yau na sanar ma Hassan abinda ke faruwa." Ummy tace " ni kam tsoro nake kar abin nashi ya dawo." Abba yace " sai yaushe ne zaki bari a fadamai? Tun wancan satin kike sani nake jan lokaci ko so kike sai abin ya zo zai sani?" Tace"shikenan ka fadamai yau." Abba ya mike yai sama........... Hassan na sa kaya yaji Abba na knocking, da sauri ya karasa sa rigarsa sannan ya murda makullin ya bude dakin. Abba ya matsawa ya shiga cikin dakin, kallan dakin Abba ya shiga yi yana jinjina kai, gashi dau duk lalurar dake damun Hassan amma bazaka taba ganin dakinsa da datti ba, yadan murmusa dan tabbas bai manta lokacin yana yaro ba kafin abin nan ya sameshi Hassan mutum ne mai tsafta da tsantsani, sai dai dakin bai musu karami ba? Ko sagir zai maida kasa? Dan dama saboda Hassan ne ya dawo nan kusa da dakinsa.+ Ganin Abba na ta dubs dube yasa hassan ya koma kan sofa ya zauna. Abba ya kalleshi sannan ya koma kusa dashi shima ya zauna., Matsawa kadan Hassan yai dan Abba ya zauna daf dashi. Abba yai murmushi yace " Hassan yada matsawa?" Bai tanka ba dan dama Abban yasan ba tankawar zaiyi ba. Sunyi shiru sai karar fanka dake kadawa a cikin dakin, sai sanyin A.C, Abba ya rasa ta ina zai fara, can ya daure ya maida hankalinsa kan Hassan yace "Hassan!" Kallansa yadanyi baice komai ba. Sai daya dan kara yin shiru kafin yace "Hassan ke kake tunani game da aure?" "Aure? Aure kamar ya?" Abba yace "baka tunanin aure?" Cikin rashin fahimta yace "ban fahimci aure ga mara lafiya?" Abba ya danyi shiru kafin yace " Hassan mubar zancen lafiya da rashinsa, kafi kowa sanin halin da mahaifiyarka take ciki a kanka, ka kuma san yanda tasha wahala akan rashin dan uwan............" Kallan sa Hassan yai idanunsa har sun kada, bakinsa ne ya fara rawa, hannunsa ya sa a wuyansa yana dan kakari, cikin lokaci kankani Hassan ya rikede, hankalin Abba ya tashi sosai rungumeshi kawai yai dan ya rasa ma mai zai mai. Da kyar numfashinsa ya daidaita sai dai zufa da ta keto masa, Abba jikinsa ya kara yin sanyi tsananin tausayi dan nasa ya kara kamashi. Ya dade sosai kafin ya dawo daidai, Abba ya mike zai fita, Har yakai kofa Hassan yace "Wani abu ya samu Ummy ne?" Abba ya juyo daga inda yake a tsaye cikin raraunar murya yace " Hassan in har ka damu da halin da muke ciki ka amince ka auri yarinyar da mukesanka da ita." Mamaki me ya kara kamashi yace" tambayar abinda ya samu Ummy......." Yanzu Abba ya canza muryarsa daga alamar tausasawa zuwa dan bacin rai, yace " akwai wani abu dake damunta ne a duniya daya wuce matsalar da kake ciki? In har kanasan hankalinta da nawa ya kwanta ka yarda da auren da muke kokarin yi maka." Hassan shima cikin dan zafi abinda rabon da yai magana mai tsayi haka harya manta yace " Taya zaku nemi min aure bayan kunsan halin da nake ciki? Sannan ni a rayuwata kunfi kowa sanin banasan zama inba ni kadai ba, ya zakuyi kuyi tunanin hadani da wata? Bayan kunsan daga ita har ni hakkin mu zaku shiga?" Abba ya dan matso yace "wannan halin da kake ciki shine yasa muke tunanin ma auren kota wani hali, halin zama kai kadai, halin kin fadar in baka da lafiya, halin nunkufarci da rashin fadar matsalar ka, halin kin yima kowa magana, halin rashin kula da kanka, wannan kadan ne daga cikin dalilan dayasa mukesan ma aure." Hassan har zaiyi magana yaji kansa yayi gingirin gim dan gaba daya dama baya iya magana mai tsayi, mikewa yai ya shige cikin toilet ya rufo kofar. Abba ya juya ya fita, Ummy na tsaye a falo a kasa sai zagaye takeyi tana ganinsa ta matso tace ya kukai? Yace "kema kinsan bazai yarda ba daga bugu daya ba." Tace haka ne, yace "ke zaki mai magana gobe, dan inyaga kin damu kema kinsan zai yarda." Tace "amfani dani da tsauyi da kaunar da yakemin zamuyi?" Abba yace "ba haka nake nufina, hakan dai shi kadai ne haya." Shiru tai batace komai ba. Jalila kuwa tana zaune kusa da goggo suna dan cin abinci duk ta dameta da labarin film din India data kalla mai suna Vivah tana ta fada mata yanda saurayin ciki da budurwar ke san juna can tace "Goggo kinsan abin mamaki? Matarfa ranar auransu ta kone a jikinta amma saurayin nan dan tsabar san da yake mata ya nuna shi wannan ba komai bane, Goggo a asibitin fa ya aureta......" Goggo tace " nikan Jalila sai yaushe ne zaki kyalemu muci abinci shiru? Bafa asan mutum na cin abinci na magana, sannan ni na rasa me yasa baki da aiki sai zancen soyayya, wani irin so kikema Sagir din nan dayasa kika koma haka?" Jalila tai dariya tace "Goggo karki damu yanzu tunda muka gama makaranta zaki ganshi tunda kinga gobe za'ai taron yaye mu, kinga kuwa kila ma jibi ki ganshi dan bazai iya dadewa bai ganni ba." Goggo ta girgiza kai cikin mamaki tace "yaran zamani wato ba kunya, sannan ya san gidan nan ne?" Tace "gobe zan kwatantamai." Goggo ta tabe baki tace " da alama dai kinfi sanshi ma." Jalila tau dariya tace " tab Goggo ai ni bansan wayafi san wani a tsakanin mu ba." Ya isheni haka nan. Ta fada tare da tsame hannunta dan ta rasa me yasa takejin kirjinta na mata nauyi sosai sannan sai tafi kanta na sarawa. Jalila tace " Goggo ki bari kawai na kusa daukeki mu koma gidan aurena." Harararta Goggo tai tace " to sannu, nidai na fada miki ki kiyayi kanki karkije ba shine mijinki ba." Jalila tai dariya tace "tab lalai Goggo kina tunanin zan kara san wani bayan Uncle? Ai nni har mafarki nayi na auranmu." Goggo tace "to uwar surutu ya isheni haka nan, ba wanda yasan mijinki a duniya sai Allah sai dai a koda yaushe ina miki fatan miji na gari wanda zai soki kamar ransa ya kuma kula dake kulawar da baki samu ba a rayuwarki." Jalila batace komai ba sai cigaba da cin abincinta datai tana murmushi dan itakam tasan mai so da kula da ita ba kowa bane sai Uncle dinta. ******** Abba ne ya kira Sagir ya tambayeshi labarin jarabawa dan shi ba sanin abinda ake ciki yai ba, nan Sagir ya sanar mai ai an gama Neco. Yana kashe wa ya kira Inna, bayan sun gaisa ne yace mata "Inna yara sun gama jarabawa ko?" Tace "eh sun kammala nima dama ina jiran kiranka." Abba yace " sai mu hanzarta ko?" Tace "ba laifi ai ku muke jira." Yace " To Alhamdulila insha Allah jibi sai mata su kawo lefe." Tace "hakan yayi , Allah ya kaimu." Nan sukai sallama, kallan Mumy tai tace " yaushe kike tunanin ya kamata asanar mata?" Mumy tace " duk sanda ya dace kinsan bata isa bijirema maganar mu ba tunda tasan Uwarta a karkashinmu take, sannan in muka mata barazana da rayuwar ta ba shiri zata aminta da duk abinda muka gindaya mata." Inna ta jinjina kai tace " hakan yayi, yanzu mu bari sai jibinbin ankawo lefe dan na tabbatar bazai wuce sati biyu ba bikin dan da alama Taura ya kosa." Mumy tace "mu ko yau yake so menene damuwar mu? Shiyasa ma nace Safeena ta cigaba da zama a gidan kawu daga nan ta wuce Egypt hankali a kwance." Inna tace " da nace kibi mijinki Abuja yau kin binsa kikai ko?" Tace "Inna dan Allah ki kyale Abbakar, sai yaushe ne zaki barshi yai aikinsa cikin nutsuwa?" Inna ta girgiza kai tace "haryanzu baki da hankali, ke wai a naki haukar har yanzu kina tunani tsabar so ne yasa yake kula dake haka? Yake kuma wulakanta matarcan?" Mumy tace "Hajiya." Inna tai tsaki tace "Ke kika sani, ni dai company din ku bazan taba yarda na barmai gaba daya ba dan kina kallan idanunsa da yanda yake aiki zakisan akwai tsantsar greediness." Mumy ta mike tace " Zan sauka." Inna ta kalleta ta girgiza kai, tace ba da dan ina nuna mai matsayinsa ba kina tunanin zai ci. A da darajaki ne?" Mumy tai shiru, Inna tace "jeki ke kika sani." Mumy ta sauko ranta ba dadi. ******* Ummy ce ta turo kofarsa dan tajita ba a kulle ba, yana zaune a kasa yayi shiru sai ma ka rasa me yakeyi shi kadai kullum a zaune, ta shiga ta ajiye tiren abincin sannan ta zauna gefensa kadan tace "tunani kake?" Kallanta yai bai ce komai ba, tace "Dazu Abbanka yama magana ko?" Yanzun ma baice komai ba, tace "Hassan mu iyayenka ne wandanda duk duniya duk wani mai sanka sai dai ya biyo bayanmu, ka fi kowa sanin bazamu zabama abinda zai cutar dakai ba, bazan kuma nemi takura maka ba, sai dai abu daya zan fadama wannan auran ni na fara amincewa akai sannan shine babban burina wanda nakesan ka taimaka ka cikamin shi." Ta danyi shiru kafin ta mike tai waje. Da kallo yabi bayanta sannan ya runtse idanunsa, Ummy ya takeso yai? A rayuwar Jalila indai tana gaban Goggo jinta takeyi kamar yarinyar goye, shiyasa duk wata tabata da shirme juyema Goggo takeyi, suna kwance zasuyi bacci duk ta isheta da neman sanin asalin labarinta. Goggo tace "to ya isheni haka nan yanzu sai ki kwanta ko kin manta gobe kunada taro a makaranta?" Jalila ta juyo inda Goggo take tace "Goggo kinsan yanzu addu'ar da nake yi yanzu?" Goggo tace "ya wuce shirmen soyayyarki?" Jalila ta girgiza kai tace "A'a addu'a nake Allah ya kara miki lafiya da tsawan kwana muyi rayuwa tare, banaji zan iya kwana d'aya a duniya in bakyanan."1 Goggo ta hade rai tace "Jalila nikam sai yaushe ne zaki girma? Na dauka in mutum ya tashi cikin wahala yana hankali amma wani sa'in in kikai wani abun sai inta mamakin ki." Jalila tai murmushi tace "Goggo a koda yaushe in ina tare dake ji na nake kamar yarinyar goye, kece kawata, mahaifiyata, mahaifina, sannan kuma yar uwata, Goggo yanda bana boye miki komai dan Allah kema kidinga sanar dani komai na rayuwarki." Kallan tausayawa ta mata dan tabbas tana ji a jikinta wani babban ciwo na cinta domin wasu sababbin canjin da take fuskata a jikinta tasan da matsala,, sai dai fatan Allah yasa abin ba babba bane. Jalila tace "Goggo!" Goggo tace "shikenan Jalila na miki alkawari a daren gobe zan sanar dake komai na kafin a haifeki, yanzu dai ki kwanta." Tace "yauwa Goggona, saida safe." Goggo ta daga kai, sannan ta zuba mata ido, kankace me Jalila ta tafi bacci. Goggo a dade tana kallanta har batasan sanda hawaye suka gangaro mata ba, hannu tasa ta share sannan ta gyara mata bargo ta juya ta fara bacci. Da safe bayan ta gama gyara bangarensu ta fada wanka, an dade ana saba jiki kai kace fatar tata zata canza, ta fito ta bude drawer dinta ta saka kayan makaranta sannan ta shiga duba sababbin dinkin da aka mata, nan ta zabi wani lace mai an karan kyau yasha duwatsu, ta fara kokarin sawa a jakar hannunta da aka sai mata. Goggo ta bude labule tana kokarin shigowa, kallan Jalila tai tace "ke da zaki makaranta me zakiyi da kayan gida?" Ta karasa shigowa da kyar ta samu ta zauna. Jalila tai murmushi tace "Goggo yau fa ake yaye mu." Tace "to sai akai ya?" Jalila tace "Ana gama taran ai zamu kwabe mu shiga kayan gida ai shagali." Goggo ta tabe baki cikin rashin gamsuwa tace " Wai yaushe aka fara haka a makarantar Gomnati ma?" Jalila tai dariya tace " ina kike fita balle ki sani?" Goggo tace "Hmm amma ai kyaci abinci ko?" Jalila tace " Ni bana jin yunwa sannan za'a kawo abin saidawa a makaran........." Kallan da Goggo ta matane yasa ta zauna da sauri tare da bude kular abincin, tea ne da bread da farfesun naman kai." Jalila ta dade kafin ta bude bread din, har goggo tace "menene?" Jalila tai yake tace "rayuwa kawai nake tunani Goggo, wai yanzu mune ake bamu abinci ba tare da munyi musu aiki ba, Goggo kin manta sanda muke musu wanki? Mu musu komai na gidan?" Goggo tace " rayuwa kenan Jalila, insha Allah wahala ta kare miki a rayuwa." Jalila tai murmushi sannan ta fara cin abincin, bazata cemata iyaye suna zuwa ba dan ta tabbbar zataji ba dadi, gashi ita ba lafiyar kafa ba." Tana gamaci ta fito, Sultan ta gani yana kokarin shiga mota, tace "Sultan?" Tsayawa yai har ta iso, tace "ina zaka?" Ta dauka cemai akai ya rakata saboda gama makaranta da zasuyi. Jitai Yace "In an kaiki makaranta ne zan wuce gidan kawu in amso sako." Sakon me? Yace " kamar wai lefe za'a kawo." Jalila cikin mamaki tace "lefe? Lefen wa za'a kawo?" Yace "ina na sani?" Ya fada tare da shiga motar. Jalila ta shiga tana mamaki, bikin Safeena za'ai? Amma bataji labari ba, to ko amsar kayan za'ai kawai a gidan?" Ganin batada amsa yasa ta share. Yau yan mate dinsu Jalila ansha uban kwalliya, sai iyayi akeyi. Haka aka fara programs kowa iyayensa da yan uwansa sai zuwa sukeyi, Jalila tana zaune dan tasan ba wanda zata gani. Zarah ce ta tabata tace "Jalila Yaya yazo dasu Umma." Nan sukaje suka gaishesu, Jalila tana zaune daga inda take tana hango Uncle Sagir, insuka hada ido sai suyi ma juna murmushi. Ganin Uncle ne ma yasa ta cire komai a ranta har aka gama programs. Nan sukaje suka canza kaya kowa yasa kayan gida suka dau kwalliya, masu waya sunata yin hotuna, Zahra ma ta zo musu da waya sai hoto ake tayi. Wata monitor din Jss3 ce ta shigo ajin nasu, nan ta nemi inda Jalila take ta tabata. Jalila ta kalleta tace " Hadiza ya akai?" Mika mata wata yar karamar jaka ta kwalli tai tace "gashi inji Uncle Sagir." Jalila ta amsa tana bude jakar. Kwalli ta gani ta jawo,Zahrace ta matso ta fizgi kwallin tana cewa " me muka sa......" Ganin waya yasa ta kalli Jalila tace " yeee!" Jalila ta harareta sannan ta fizge wayar tace " muga." Ganin Wayar ne ya sa ta kallan Zahra, hannu tasa cikin jakar ta zaro wani karamin card. Bude shi tai taga ansa _To u my dear!_ _Congratulation on your graduation, here is my small gift, hope you will accept it._ Zarah ce ta kara amsar wayar ta bude ta, wayace mai tsananin kyau Sumsung Note 5 ce. Kan kice me Zarah ta fara haska Jalila wacce tai tsuru tana kallan ikon Allah. Fitowa tai daga ajin ta shiga nemanshi, can ta hangoshi cikin mutane. Tsayuwa tai dan bata san ya zatai ba, juyowa yai kawai sai hangota yai daga nesa. Yaune rana ta farko da ya ganta cikin shiga haka mai kyau dauke da kwalliya, sannan wannan ne rana ta biyu daya ganta ma da kayan gida a iya zamansu, na farko sanda ya fara ganinta sai kuwa yau. Kasa dauke ido yai daga kanta wanda har hakan yasata tsarguwa. Juyawa tai da sauri ta shiga class din. Zahra ta matso tana nuna mata hotunan da ta mata. Jalila kam bata kula taba dan hankalinta nakan Uncle dake waje. Daina hangoshi tai hakan yasa ta fito daga class din tana lekensa. Zarah ce ta miko mata wayar da sauri tace "Zarah Yours na kiranki." Jalila aji abin banbarakwai, kallan wayar tai a jiki an saka MINE dariya tai sannan ta kalli zahra tace ya ake daga wa?" Mamaki ya kama Zahra sai dai kafin ta farga Jalila tana gwadawa kawai taga yaja hakan yasa Zahra tai tunanin iskanci take mata. Jitai yace "Banga kwalliyar nan ba, tunda ba'a ganni ba sai a taimaka azo inda muke haduwa." Murmushi tai sannan tace "to." Kallan Zahra tai sannan tace "ina zuwa." Nan ta fara tafiya. Yau a kan mota ta ganshi, karasawa tai fuskarta dauke da murmushi da kuma kunya. Tana isa ta gaisheshi, yace "Irin wannan kyau haka ai sai kisa in rasa gane hanya." Kallansa tai tace "Uncle wannan gift din yayi yawa, bana tunanin zan iya amsa, Goggo ma fada zatamin" Yace " to Jalila ya kikeso muyi? Kingama skul nima na gama service a ina kikeso indinga jinki? Ke ba waya ba? Sannan ko zuwa zan dinga yi kina tunanin za'a barni nazo kullum?" Jalila tace kullum? Yace sosai in har bazaki amshi wayar ba sai dai ki amince kullum nazo muyi awa uku tare. Da sauri ta zaro ido dan tasan wannan inaa bazai yiwu ba. Ji tai yace "bazai yiwu ba ko? To kinga kawai ki hakura." Jalila tace "Amma....." Yace "mu bar maganar nan please." Kallansa tai dan batasan me zata ce ba.......... Hira suka shiga yi ta masoya masu tashen soyayya, Kiran wayarsa da akai ne yasa ya kalli wayar mamaki yai dayaga Mine a jiki dan number Jalila ce. Nan ya daga yana cewa wayarki na gun wa? Tace Zahra Zahra na dagawa tace "Uncle wai Jalila tazo anzo daukarta." Uncle ya kalleta yace "wai anzo daukarki." Mamaki ya kamata tace "amma nace sai bayan azahar, gabanta ne ya fadi badai wani abun bane ya samu Goggon ta?" Kallan Uncle tai a tsorace tace "Uncle bari naje gida." Zahra na tsaye kusa da motarsu, wayarta ta mika mata ta bata jakarta, nan Jalila ta sa a cikin jakar ta shiga ciki sukai gaba, addu'a kawai take Allah yasa ba wani abun bane ya samu Goggonta. *£*£********* Goggo tana zaune wajen karfe 12 Yasmeen tazo da gudu wai tazo inji Inna. Tayi mamaki sosai dan tanaji tunda take a gidan Inna bata taba nemanta ba haka kawai. Samun kanta tai da faduwar gaba. Haka ta taso da kyar saboda ciwon kafa ta karasa.1 Tana shiga falon taga Inna, Dady da Mumy a zaune. Faduwar da gabanta ya shiga yi ne kawai ya sa ta shiga yin addu'a dan ta tabbatar ba lafiya ba, shiga tai a hankali. Mumy ta mata nuni da kujerar dake gefe tace "ki zauna anan." Goggo ta zauna sannan ta gaida Inna ta gaida Dady da Mumy. Bayan sun amsa ne falon yai dan shiru. Goggo tace "lafiya?" Inna tace "Gobe za'a kawo kayan lefen Jalila." Abin yazoma Goggo a ba zata wanda yasa tace "lefen Jalila kamar ya kenan? Dan banaji ta taba sanar dani tanada miji." Inna tace " ba sai ta sanar dake tana da saurayi ba, dan kuwa hakkin mahaifi ne ya zaba mata mijin da yaga ya dace da ita, sannan shi Abbakar ya fitar da nasa hakkin na yi mata miji yanzu hakkin 'ya ne tabi umarnin mahaifinta." Goggo ta kalli Dady da sauri tace " Abbakar me kenan?" Yace "hakan da kikaji shine." Cikin daga murya tace "da tunda aka haifeta bakasan da hakkin ta akanka ba sai yanzu? Dama wlh ni jikina yaban mutuncin da kuke mata da wani abin a kasa, ashe aurar da ita zakuyi? Mijin mahaukaci ne ko dan shaye shaye? Ko kuwa barawo ne? Ko kuma nakasasshe? Ko kuma dan fashi ne?" Mumy tace "ya zaki fadi haka, Abbakar fa ubanta ne ta ya za........." Goggo cikin tsawa tace "Ba dake nake ba." Yanda tai maganar ne yasa Mumy tsorata dan bata taba ganin Goggo na fada haka ba. Goggo cikin fada tacigaba " me ka mata a matsayinka na ubanta? Me ka mata?" Dady shim ya kasa magana dan bai taba ganin tana fada haka ba. Goggo fa mike da kyar idanunta sun canza tace " duk abinda kuke ma tunanin ku ajiye dan wlh ba wanda ya isa ya yima Jalila auren dole." Juyawar da zatai taji wani jiri na debanta, kan kace me tayi baya luuuu jikake tim ta fadi a kasa. Da sauri suka mike suna jijigata. Jalila wacce ta shiga bangarensu da gudu taga ba Goggo jakarta ta cilar a dakin sannani ta fito ta nufi bangarensu Mumy dan tambayarsu,ganin Goggo a kasa su Dady da Mumy na kanta yasa ta karasa da gudu jikinta na bari. Dady a rikice ya nufi daki ya dauko key din mota ganin yanda Goggo take a kwance ga Jalila sai wani irin kuka takeyi. Jiyai ance "ABUBAKAR." Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalli Inna, kallansa tai tace "ina zaka?" Yace "Asibiti." Tace "dawo ka zauna." Tsayawa yai yana kallan Goggo sannan ya kalli Inna.+ Mumy ce ta kalli Inna tace "Inna kingafa......" Kallan data mata ne yasa ta yin shiru, Jalila a rikice ta jawo gwiwarta ta iso inda Inna take tace "Inna dan Allah ki bar Dady ya kai Goggo asibiti, duk da bansan me ya hadaku da Goggo ba har take nan bangaren sai dai na rokeki da ki yi hakuri." Hannunta ta hada guri daga tana ta murzasu tana kuka alamar tsantsar neman taimako. Ganin Inna batada niyyar kulata yasa ta ja gwiwa zuwa gun Dady ta rike kafaraa tace "Dady ka taimaka dan Allah, karka manta Goggo matarka ce, sannan mahaifiyatace." Gani tai Dady ya kalli Inna, hankalin Jalila ne ya kara tashi ta matso kusa da Mumy ta rike gwiwowinta tace "Mumy ki taimaka min, bazan sake yima Safeena laifi ba, sannan zan cigaba da yi muku aiki, dan Allah ku taimakeni ku kai Goggo Asibiti." Muryar Inna ce ta katseta da cewa " kinaso a ceci ran mahaifiyarki?" Jalila a rikice tana kuka shabe shabe ta shiga daga kai ba kakautawa, Inna tace " akwai hanya daya mafi sauki, wanda in kika amince da ita bama kaita asibiti ba hatta kula da ita zamu samo wanda zai dinga yi, sannan asibiti duk tsadarsa zamu kaita indai zata samu lafiya." Jalila a rikice tace "ko me kukeso ku fada zanyi dan Allah." Inna tace "ki amince da auran da Mahaifinki zai miki." Gabanta ne ya fadi ta kalli Dady idanunta jagab da hawaye, yana ganin sun hada ido ya juyar da kansa gefe. Jalila tace "ban gane ba Inna." Inna tace "in baki gane ba sai ki bar Goggon taki ta karasa rayuwarta anan." Wani irin fitar da numfashi da Goggo tai shi yasa Jalila rikicewa ta karasa gunta da gudu tana kuka. Inna tace "kina tunani ne akan maganar? Ashe baki dauki ran mahaifiyarki da daraja ba kenan tunda kina tunanin yanda zakiyi tsakanin lafiyarta da farincikin ki." Jalila ta kalleta tana kuka tace "ko ma dawa zaku hadani na amince ni dai dan Allah ku kai Goggo asibiti." Inna tace "yanzu kikai magana, Abbakar kai Mahaifiyarta asibiti, sannan ki sani gobe za'a kawo lefenki da sa rana." Jalila kam kuka kawai takeyi, haka Dady da Mumy sukasa Goggo a mota Jalila ta shiga baya suka fita. Asibitin Standard sukai parking, Jalila kam banda kuka ba abinda takeyi, ana shiga da Goggo nurse ta nufi office din likita dan sanar da ita halin da Goggo take ciki. Jalila na zaune a kasan beni kuka kawai takeyi tana addu'ar samun lafiya ga mahaifiyarta. Dady na zaune shida Mumy, sunyi shiru suma. Sai da suka samu da taimakon Allah numfashinta ya daidaita sannan suka shiga yi mata gwaje gwaje. Sai da suka gama sannan suka fito aka kira Dady. Likitan ce kalleshi tace "wani maganin hypertension take amfani dashi?" Yace "hypertension?" Tace "kanaso kacemin bakusan tanada shi ba?" Dady ya girgiza kai alamar rashin sani, tace "diabetes fa?" Dady yai shiru nan ma. Tace " menene tsakaninka da ita?" Kunya tasa yace "yar uwatace." Cikin rashin jin dadi tace "wannan wani irin abu ne? Batada miji ne? Ko kuwa neman kasheta yakeyi?"2 Dady yai shiru, tamai bayanin ciwon ta wanda ya riga ya ci jikinta sosai, tace " ta ya za'ayi ku bari diabetes har yai nisa ya ci kafarta?" Dady yace "ai mun dauka ciwon kafa ne na girma." Tace "ko ciwon kafa ne na girma ai kwa gwada zuwa asibiti, da kunzo da wuri ai za'a sanar daku ba shi bane." Sosai ta nuna masa laifinsu sannan ta bashi takardar magunguna tace yaje pharmacy dinsu. Jalila na zaune kusa da Goggo tana kuka, ko mayafi babu a jikinta dan kwalli ne kawai a kanta. Dady sai da ya gama biyan kudin komai sannan ya shigo dakin, Jalila ce ta kalleshi batace komai ba. Dady yace "ya jikin nata?" Kasa amsa mai tai dan gaba daya yau tana tir da kasancewa uba a gareta. Duk wani mutum mai imani bataji zai yiwa matarsa abinda dady ya ma Goggo yau. Dady ganin yanda Jalila ta dauke kai daga kansa yasa ya fito. Mumy ya tadda a zaune yace " mu tafi." Tace ya jikin nata?" Bai bata amsa ba ya wuce mota. Suna shiga ya kalli Mumy yace " yanzu abinda Inna tai dazu ta kyauta?" Mumy ta riko hannunsa tace "nima banji dadi ba sai dai kafi kowa sanin duk abinda Inna takeyi tanayinsa ne saboda mu, na tabbatar ba a san ranta itama tai haka ba." Shiru yai baice komai ba yaja motar sukai gaba. ****** Ummy ce take ta buga mai kofar yanaji sai dai ya kasa mikewa ya bude, yana takure a gefen bandaki ya matse kansa da karfe, zufa nata karyomai, jikinsa sai rawa yakeyi. Ummy ganin ba alamar budewa yasa ta sauka kasa da sauri tana kwallama Sagir kira. Sagir na kwance a falon kasa yasa waya a gaba sai gwada number Jalila yakeyi sai dai tai ringing har ta gaji ba'a daukaba. Jin yanda Ummy ke kiransa yasa ya mike da sauri yana tambayarta Ummy lafiya? Ummy a rikece ta karaso tace "Hassan." Yana jin haka ya hau sama da gudu. Aina'u da Ameera dake zaune suna hira suma suka taso da sauri. Ganin buga kofar bazata kara mai komai ba yasa ya shiga dakinsa da sauri ya dauko spire key ya bude. Hassan na takure jikinsa sai rawa yakeyi ga wani azabbaben ciwon kai dayake damunsa, Sagir ya karasa da sauri ya rungumeshi, Ummy kam zubewa tai a kasa tana maida nimfashi dan ta tsorata ganin yanzu abin da dan sauki zakaga in ka kwankwasa yana budewa, Aina'u da sauri ta karasa kusa da ita. Sagir ya dade yana mai addu'oi samun nutsuwa sannan shima Hassan din ya fara kokarin yi a zuciyarsa. Ameera kam kuka kawai takeyi. Hassan ya kalli Sagir idansa yai ja, kallan Ummy yai da Ameera dake kuka gaba daya tausayinsu ne ya kamashi sai dai bai nuna a fuskarsa ba, mikewa yai ya zari key din motarsa zai fita. Ummy ce ta riko hanunsa dayazo wucewa ta kusa da ita, sannan ta kalli su Ameera ta musu alama da su fita. Suna fita ta kalleshi tace "ina zaka?" Yace "fita kawai zanyi." Tace "Hassan sai yaushene zaka dainafita haka kawai?" Kallanta yai cikin takaicin rayuwarsa yace "To Ummy ya kikeso nai? Nace zan bar garin kin hanani? Sannan ba tun yanzu ba kukasan matsalata sai yaushene zaku daina damuwa in kuka gan ni cikin halin nan? Sai yaushe ne zaku cire abin a ranku ku saba da ganina haka?" Ummy tace "taya kuwa zamu cire abin a ranmu bayan kaidin jinin mu ne? Damuwar ka itace damuwarmu? Rashin lafiyarka itace tamu?" Cikin akaici yace "Ummy please, Please na rokeki da ki cire ni a ranki, Please ki manta dani kiyi rayuwarki yanda kikeyinta da." Tace " kana jin takaicin yanda nake shiga kunci saboda lalurarka?" Kallanta yai baice komai ba, tace "in har kanaso inyi rayuwa yanda kakeso to ka amince da abinda na fada ma." Kallanta yai yace "Ummy wai ta yaya zakuyi tunanin yimin aure cikin wannan halin? Wace macece zata iya zama dani?" Tace " in har ka amince ai zaka ganta, zakaga wace macecen ce haka dazata iya zama dakai?"2 Hassan yai shiru dan kansa har yanzu yana sarawa, yace "naji kiyi duk abinda kike ganin shine daidai." Ya fada tare da fita daga dakin, da kallo ta bishi dashi cikin tausayawa, dan tasan halin zuciyar danta, mutum ne mai saukin kai, sai dai tundaga faruwar al'amarin nan ya rikede ya koma haka. Hassan na fita ya fizge mota yai gaba. Jalila kuwa da daddare Driver ya kawo musu abinci, ganin yunwa zataata lahani ne ya sa ta zuba abincin taci. Goggo ce ta farka daga nannauyan maganin baccin da aka sa mata, kallan Jalila tai sannan ta kalli asibitin, a hankali ta budi baki tace "Jalila!" Tsame hannunta tai da sauri ta isa guda da ita tace "Goggo! Kin ganeni?" Da kyar ta mata murmushi tace "Jalila karki kuskura ki yarda da abinda Mahaifinki ke shirin yi miki." Jalila ta kalli kasa jiki a sanyaye sannan ta kalli Goggo tace "Goggo abinda kikesan cemin kenan daga farfadowarki?" Goggo da kyar tace "Karki yarda Jalila, bazan kara bari su cutar dake ba ta hanyar da bazata kare ba, aure ai ba wasa bane." Jalila tace "to bazan yarda ba yanzu dai ki kwantar da hankalinki kinji?" Goggo ta daga kai a hankali, wani baccin ne ya kara yin gaba da ita.........
  Komentar

  Tampilkan

  No comments:

  Post a Comment

  Terkini

  +
  ?orderby=published&alt=json-in-script&callback=labelthumbs\"><\/script>");