AL,ADUN WASU CHAPTER 9

AL,ADUN WASU CHAPTER 9
Bakin kofar Izzatu taje ta riko hannun Zuhra suka shigo cikin dakin. A gefen gado ta zaunar da ita, mugun kallon da Hamza ya watsa mata yasa tayi saurin zamewa kasa, dama a darare ta zauna. Wasu yan siraran hawaye Izzatu ta soma yi tace Zuhra don Allah ki yafeni. I played a cruel joke on you. Zuhra tace eyye...play kuma? Kawar da kai Hamza ya yi yayi dan murmushi. Yana ganin da kyar idan Zuhra ta fahimci abinda Izzatu ta fada saboda yadda ta soma yaken karfi da yaji. Izzatu ta cigaba da magana, nasan ban kyauta ba amma don Allah ki yafe min.+ Babu komai Zuhra tace idanunta na cikowa da kwalla. Ta dai yafe amma bata jin zata taba manta irin dariyar da Izzatu tayi mata a gaban mutane. Tashi ma tayi zata koma nata dakin Izzatu ta dan taba Hamza, baka bata hakuri ba. Ni kuma??? A wani dalili? Dan marairaicewa Izzatu tayi, shi kuma yana kallon Zuhra da ta tsare shi da ido. Dena kallona ya fada yana harararta. Kanta ta sunkuyar dama tasan bazai bata hakurin ba. Izzatu dai da fara'arta tace ni na baki hakuri a madadinsa. Kai Zuhra ta gyada kawai, Izzatu tace to tunda kin hakura ina fata zaki amince ya SAKE ki. Ta juya ga Hamza, daga shi har Zuhra kallon mamaki suke mata. Zuhra tace dama abinda kike so kenan shine kika rinka yi min kirki dazu? Duk abin Izzatu sai da taji kunya. Hannuwan Zuhra ta rike, nasan kema auren nan dole ake yi miki kamar yadda aka yi mana. Ki amince ya sakeki ki koma gida ki auri miji daidai da ke wanda zai so ki. Nasan idan da bakinki kika fadawa Alhaji ke kika nemi sakin bazai ga laifin Sweetyna ba. Sai ta kalli Hamza ta kalli Zuhra duk tunani suke yi. Dan gyaran murya Hamza yayi duka suka mayar da hankulansu gareshi. Idan kin amince da sakin bazan sake ki yanzu ba sai nan da kamar wata shida ko shekara daya saboda Alhaji bazai taba yarda ke kika nema ba. Izzatu ta bata fuska habaaaa Hamza, wata shida is too long. Hankalinsa yana ga Zuhra yana karantar yanayinta saboda ta zurfafa a tunani. Zaman gidan nan ba nata bane saboda babu mai kaunarta. Itama kuma ba son mijin take ba, son kyautatawa iyayenta da nunawa Izzatu kurenta yasa tun farko ta amince. To yanzu idan aka saketa yaya Baba da Umma zasu ji? Waye zai yarda ya aureta idan aka ji aurenta ya mutu bayan wata shida. A sanyaye ta dago kanta suka hada ido da Hamza, saurin kawar da kanta tayi kamar ba itace mai tsare mutane da ido ba. Na yarda amma don Allah kada ku bata min suna idan anyi sakin saboda iyayena....hawaye ne suka zubo mata tayi saurin rufe fuskarta da mayafinta ta fita. Tana jiyo ihun murnar Izzatu ta sake danewa jikin Hamza. Shima duk jikinsa yayi sanyi don baiyi tunanin zata amince da wuri haka ba. Dole ya sami dalilin da zai fadawa iyayensu yadda baza'a ga laifin kowa cikinsu ba. Izzatu yaji tana kokarin cire masa riga yasa hannu biyu ya rike abarsa. Meye haka? Dazu kinzo kinyi hugging dina a gaban yarinya. To meye ta fada tana jan rigarsa. Ai tasan abinda yafi haka ma munayi. Tana dariya tace Baby we need to celebrate bari na samo mana juice mai sanyi da cups muyi toasting. Duk da wata shida is a long time amma ba komai. Fita ta sake yi ta barshi yana tunani. Kamata yayi ya yi murna da amincewar Zuhra sai dai a kasan zuciyarsa yasan abinda suke niyar yi bai kamata ba. Ba jimawa ta dawo da apple juice a wata roba mai kyau ta tsiyaya musu a glass cups. Hamza zai kai nashi baki ta rike hannun, I said lets toast ta kashe masa ido. Tare suka dan buga cups din suka yi yar kara. Izzatu tace TO FREEDOM. 37 Kwanaki biyu a tsakani Zuhra na zaune a falo don yanzu Izzatu tace ta rinka zama tana sakewa. Hatta su Khalifa tana bari su zauna da ita. Wurin karfe biyar na yamma Hamza ya shigo maigadi ya biyo shi da ledoji. Kofar inda ya kamata ya zama kitchen din Zuhra yace ya ajiye masa. Su Junior da Izzatu suna ta yi masa sannu da zuwa Zuhra ta mayar da idanunta ga kallon tv. Ita yanzu da tasan matsayinta a gidan tana ganin yi masa sannu da zuwa kamar shishshigi ne. Shima a nasa bangaren bai kulata ba suka tafi dakinsa shi da Izzatu. Ba jimawa ya fito da shirt mara nauyi da dogon wando, da gani wanka yayi. Abinci ya zauna ci suna ta hira da Izzatu. Sai da ya gama ya tashi ya bude kitchen din Zuhra sannan yace ke zo. Da farko tayi niyar sharewa sai Izzatu tace mata jeki mana Zuhra kayan miya ya siyo miki. A hankali take tafiyar har sai da yaji haushi. Ya nuna mata kayan da hannu alamun ta dauko. Wato kace na dauka da bakinka ne kake ganin asara....Allah Ya sauwake ta fada a ranta. Dauka tayi gabadaya hudun ta shigar dasu kitchen din. Kallon mamakin da yayi mata yasa ta tuna maganarsu dasu Anas da suka ce mata maza basa son mata masu karfi. Sai kuma ta tunawa kanta ai Hamza ba mijin da zasu so juna bane. STORY CONTINUES BELOW  Kwalin gas cooker dinta ya farke ya sake fita. Bai dade ba ya shigo dauke da karamar cylinder. Daga can gefe ya ajiyeta sannan ya hada mata gas din. Ya koma kan fridge din shima dan madaidaici ya jona mata. Ita dai tana gefe tana binsa da ido. Sai da ya gama tsaf yace ga kayan miya nan da nama sai ki saka a fridge kada su lalace. Daga yau ki rinka dafa iya abincin da zaki ci. Idan akwai abinda babu a cikin kayanki sai ki fada a siyo. Tsananin farinciki da taji yasa ta washe baki da gaske kake don Allah....daure fuska yayi, na taba wasa dake ne? Nagode, nagode, nagode ta rinka fada tana bude ledojin. Ji tayi yace kuma ki kula kada ki bata wurin nan kinga tun asali ba kitchen bane. Ya nuna mata sink shi kadai zan iya sawa idan kin tafi sai a cire amma bazan miki wani kitchen kabinet ba. Duk da haka ma nagode ta fada cike da murna. Yau zata dafa abinci son ranta taci ta koshi. Hango kanta take da kwano ba ma plate ba shake da abinci. Wannan irin farinciki da take yi yasa shi jindadi. Ko ba komai yana ganin ya tsira daga laifin tauye mata hakki a ganinsa. Zuhra tana susar kai tace uhmmm....yes ya amsa don yasan akwai abinda take son fada. Dama...dama... gajiya yayi da inda indarta yace dama me? Uhmm nace shi gas din ya zan rinka kunnawa? Au dama baki iya kunnawa ba aka kawo ki dashi. Turo masa baki tayi to mu a gida ba da itace muke yi ba ko risho. Ganin ya daga hannu tasan a bakinta zai sauke shi tayi saurin ja da baya. Nufi na fa ban saba dashi ba amma cikin kayana akwai risho din sai na fito dashi. Hannu ya daga yana nunata, ki fito da me? Wallahi kada kuskura ki kunna min risho a wurin nan in ba so kike ki sake min sabon fenti ba. Kinji ko! Gyada kai ta rinka yi kamar kadangaruwa da taji ya fara daga murya. Sai kuma yace matso ki gani..kunnawa yayi sannan ya gwada ragewa da kashewa duk tana gani. Idan kin kasa ki kira Tala ta nuna miki don naga alama kin fita kauyanci. Ni ba yar kauye bace ta fada tana kara turo bakin nan nata. Biyota Hamza yayi zaiyi maganin rashin kunya ta juya da gudu. A bakin kofa suka ga Izzatu tana dariya. Ai tunda naji kana daga murya nasan kun fara fada shine nazo kallo. Ta kalli Zuhra bai dake ba ko...babu wanda ya bata amsa ta cigaba da dariyarta ta kama hannun Hamza suka fita. Tuwo Zuhra tayi niyar yi Izzatu tace kada tayi girki an riga anyi abincin dare da ita. Har ranta bata ji dadi ba amma haka ta daure taci abincin. Inuwa sakatare yana ta hada wasu files zai kaiwa Hamza saboda meeting din da zasu yi sai gashi ya fito daga office dinsa rike da waya da makullin mota. Inuwa yace ranka ya dade fita zaka yi ne? Akwai meeting fa biyu da rabi. Ba jimawa zanyi ba Inuwa in sha Allah. Zanje banki ne tun friday kaga yau alhamis banji alert ba na kudin da ka ciro. Inuwa yace to Allah Ya kiyaye adawo lafiya. Amma ranka ya dade yaushe Oscar yace zai dawo ne muna bukatar sa hannunsa a wasu takardu. Hamza yace nima duk na damu ko jikin mahaifiyar tasa ne sai dai ban same shi a waya ba. Bari nayi sauri na dawo sai muyi maganar dai. Koda ya fita jikin Inuwa sakatare yayi sanyi....Allah Yasa abinda zuciyarsa take kitsa masa ba gaskiya bane. Manyan architects yau da kanka a office dina. Manaja ke magana yana tashi tsaye suka gaisa da Hamza. Kowa fuskarsa dauke da murmushi suka tambayi juna iyali. Manaja yace sai kuma naji kayi aure ba labari. Kai Hamza ya dan sosa yana tunanin yadda zance ke yawo a gari..kayi hakuri abin ne yazo a gaggauce. Babu komai Allah Ya sanya alkhairi. Yanzu dai how can I help you? Tashi Hamza yayi kada ka damu shigowa nayi mu gaisa na riga na sanar dasu a costumer care alert ne bana ji tun last friday. Kuma har a atm da na cire kudi still banji ba. Manaja yayi dariya ai dole ka damu ku masu harka da manyan kudi. Suna magana text ya shigowa Hamza. Yayi murmushi dadina da bankin nan saurin gyara abu. Gashi har alerts din sun shigo. Yanayin fuskarsa ne ya soma canjawa a take. Manaja ya naga alert na an cire ten million har sau biyu a ranar friday din? Manaja ma dena murmushi yayi ai sau biyun ne Architect. Ka turo sakatare dinka sannan ga mamakina ka turo wani Mr..Mr....mtsw na manta sunan amma dai na kira nayi confirming a wurinka kafin a sakar masa kudin. Jiri ne ya soma dibar Hamza daga tsaye yayi saurin dafa tebur din manaja ya zauna. Da kyar ya iya cewa Mr Oscar? Eh shi kuwa manajan ya amsa. Ka tuna na kira na tambayeka kace eh kaine ka turo shi. Tabbas manaja ya kira amma a lokacin Izzatu ke faman daga murya tana masifa sai ya saki Zuhra baiji abinda manajan yace ba ya amsa masa. Wato shiyasa Oscar yace mamansa ba lafiya ya tafi garinsu gashi an kusa sati babu mai samunsa a waya. Allahumma ajirni fi musibati wa akhlufni khairan minha. 38 A rikice manaja ya fara tambayar Hamza ko sunyi kuskure ne. Numfashin Hamza da kyar yake fita ya dago idanunsa da suka yi nauyi lokaci guda yace babu abinda kayi manaja. Matsalar daga bangarena ne. Sau biyu yana yunkurin tashi amma kafafunsa sun kasa daukarsa. Manajan sai bashi baki yake yana rokonsa ya zauna har zuciyarsa ta daidaita amma sam yaki zama. Ko da ya shiga mota rasa wurin zuwa yayi. Gidansa zai tafi ko office zai koma. Yafi rabin awa a motar kafin ya tayar ya dauki hanya. Lokacin da ya shiga gidan babu kowa sai Kande mai aikinsu. Da fara'arta ta tare shi tana masa sannu da zuwa. Jikinsa duk a sanyaye yake yace ina mutan gidan ne naji shiru. Nura yana daki su Adabiyya kuma sun tafi makatanta. Hajiya da Mama kuma sunje unguwa. To din ma da kyar ya iya fada sai ya tashi ya tafi dakin Hajiya. Babu abinda yake a lokacin kamar yaga mahaifiyasa. Yaji dadi a bude ta barshi kamar tasan zai zo. Gadonta ya nufa ya kwanta abinda ya dade baiyi ba. Yana rufe ido sai wasu zafafan hawaye suka sauko masa. Ji yake kamar komai nashi ya tsaya cak. Cheque din da Mr Oscar ya dauka hade da sauran da suke office dinsa idan an hada miliyan arbain kenan zai hada ya bawa su Mr Peter ya kawo karshen contract dinsu. A dalilin hada wannan kudin gabadaya maaikatansa suka amince da karban rabin albashinsu a wannan watan don kawai su tseratar da kamfanin. Yanzu gashi miliyan goma ta tafi a kudin bai san ta ina zai samu su ba. Ginin gidansa yaci kudi ba na wasa ba. Idan kuma ya tattara kudaden account dinsa tare da sayar da filayensa zai iya biyan kudin to amma rike iyalinsa zai zama da matsala domin kuwa akalla kafin kudin ayyukan da yake su fito zai dan dauki lokaci. Yana wannan tunanin bacci ya dauke shi. Hajiya ta kira Mama ko sun taho daukarta daga tata unguwar Mama tace tun dazu nake kiranki ban samu ba. Gamu a garejin makanike ban je inda zani ba. Amma na fasa ana gamawa zamu biyo. Hajiya tace babu komai bari na bi adaidaita sahu kaina ke ciwo. To ki kira Nura mana yazo ya dauke ki. Hajiya tace babu komai shima yau da mura ya tashi. Sai kun dawo ni zan wuce gida. Tana gama wayar suka yi sallama da kawarta da taje dubawa ta fita ta hau adaidaita sahu. Gabanta yayi mummunan faduwa ganin mutum a kwance a kan gadonta. Alhaji yana Kumo kuma ko shine da wuya ya kwanta a dakinta. Nura kuma sai da ta leka dakinsa ta dubashi sannan ta taho nata. Babu inda baya rawa a jikinta ta ja kafa ta je gefen gadon inda zata ga fuskar mai baccin. Sai da ta dan ja baya saboda wanda bata taba tsammani ba ta gani. A tsorace tace Yaya....shima kansa ke masifar ciwo ya bude idanunsa da kyar. Hawaye ne bushe a fuskarshi Hajiya ta matsa ta taba shi. Bakinta har rawa yake saboda tsoron abinda zai ce tace Yaya me ya faru? Tashi yayi ya gyara rigarsa da ta yamutse sannan ya mayar da hularsa. Yana dan murmushi yace Hajiya babu komai. Zuwa nayi mu gaisa duk bakwa gidan. Bari na koma office sai anjima. Hannunsa ta rike. Itama hawayen take yi....haba Yaya duk duniya idan akwai wanda zaka boyewa damuwarka kasan banda ni ko. Bar ganin ban fiye shiga harkarka ba duk yanayin da ka shiga nakan gane na farinciki ne ko akasinsa. Dawowa yayi yasa mata kuka kamar karamin yaro. Kai bakace Hamza bane dan shekara talatin da takwas mijin Izzatu da Zuhra. Akan kujera ta zauna tana rike da hannunsa ya zauna a gabanta. Kansa ta dora akan cinyarta yayi kukansa mai isarsa. Rabonsa da yi mata irin kukan nan tun ranar da zai tafi Canada. Duk ranar da yayi irinsa to ba karamar damuwa yake ciki ba. Babu wanda yasan yana yi sai ita mahaifiyarsa. Cike da tausayawa irin ta uwa ta rinka shafa kansa har yayi shiru. Ko da ya dago kansa murmushi ne a fuskarsa yace Hajiya na dade banyi miki kuka ba ko. Yau ma sha'awarsa nayi shine na taso daga office. Bari na koma ana jirana meeting karfe biyu da rabi. Lokacin biyu saura kwata. Tunaninsa bai wuce yadda ya mori kudinsa ba lokacin da yake dasu shi kadai. Sai da matsala ta tashi zaizo ya tayarwa da mahaifiyarsa rai. Ya santa bata da magana sosai, ba lallai ko Alhaji ta fadawa amma zata shiga damuwa. Hajiya tace tunda baka son fada min damuwarka zan tayaka addua kamar kullum. Allah Ya kawo sauki cikin dukkan al'amuranka. Ka yawaita ambaton Allah hakan yana yaye damuwa da bacin rai, sannan kayi kokarin sauke hakkin wadanda ke kanka Allah Yayi maka albarka. Wani hawayen ne ya sauko masa yayi saurin gogewa. Amin Hajiya nagode. Tana kallo ya fita ta shiga toilet tayi alwala. Tasan da kansa zaizo ya fada mata matsalar amma abinda yafi dacewa yanzu tayi zata masa. Addua ta dukufa yi masa sannan ta saka dukkan kannensa da iyalansu. Waya yayiwa Inuwa meeting sai gobe baya jindadin jikinsa. Tunani ne fal a zuciyarsa. Sai yanzu yake tunawa cewa Allah SWT Ya na jarabtar bayinsa ta hanyoyi da dama. A irin rayuwar sakaci da addini da yayi ai dole watarana ya fuskanci irin wannan. Sai yanzu ya sake nadamar abubuwan da yayi a baya da wanda yake kanyi yanzu wato sake da hakkokin matarsa don a zahiri suna damunsa. Sonta kawai baya yi. Zaiyi kokarin kyautata alakarsa da Mahaliccinsa da sauran mutane. Itama Zuhra zaiyi kokari ya sake da ita zuwa lokacin da zai saketa. Tunda basa son juna rabuwar ce zata fi. ta yadda bazai cigaba da daukan hakkinta ba. Zai bari sai komai ya lafa masa a wurin aiki sai ya sanar da Alhaji zai saketa saboda gudun kada Allah Ya kamashi. A lokaci daya duk sai ya zama abin tausayi. Karo na biyar kenan da Zuhra ke dandana ruwan miyarta. Yawunta duk ya tsinke saboda yadda kamshin daddawa ke tashi. Nana na biye da ita a kitchen din har ta gama. Tuwon shinkafa tayi malmala biyar yadda zai isheta taci da rana, da daddare sannan ta sami na dumame da safe. Plate ta dauko mai dan fadi da zurfi ta saka malmalar da tafi kowacce girma da miyar kukarta duk a hade. Manshanu kadan ta zuba ta goya Nana a bayanta ba zani ta dauki plate din da hannu biyu ta tafi falo. Tana tafiya tana cewa Nana rike wuyana sosai fa. Ita kuwa Nana sai murna take tace toh.+ Sai da ta shimfida tabarma kusa ta dinning table sannan ta zauna cin tuwo. Loma take kaiwa kamar za'a kwace. Tana ci tana bawa Nana a baki. Sun kusa cin rabi Izzatu ta sauko...idanunta kan Zuhra tana bawa yarta tuwo a baki. Har da nan gudunta tayi saurin zuwa inda suke ta dauke Nana tana ta warin kuka da daddawa. Zuhra ya zaki bata abincinki ke da aka ce ki dafa naki ke kadai? Ni ban saba bata abinci da hannu ba kuma bama tuwo sosai saboda yayi mata nauyi. Bata nuna jin haushi ba tace kiyi hakuri ban sani ba. Ganin Izzatu tayi hanyar kitchen yasa Nana ihu tana cewa Mummy sauketa, sauketa abinci. Izzatu tace naji yunwa kike ji bari na wanke miki baki na zuba miki couscous. Bata ankara ba Nana ta galla mata cizo a kafada. Ba shiri ta sauketa tana sosa wurin. Ita kuwa da gudu ta koma gaban kwanon Zuhra. Hannu biyu tasa tana ci bata jira Zuhra ta bata ba. Sake komawa Izzatu tayi zata dauketa sai taji muryar Hamza yana sallama. Yana shigowa Zuhra ta kai wata shirgegiyar loma bakinta. Ido suka hada ai kuwa ta kware saboda kunya. Ji yayi nauyin zuciyarsa ya ragu saboda yadda yaga tana cin tuwon cike da nishadi. Izzatu tace sweety kaga rigimar Nana wai sai taci abincin Zuhra. To ki kyaleta mana ya fada tare da wucewa sama. Ita kanta Zuhra tayi mamakin amsarsa. Bayansa Izzatu tabi tana masa sannu da zuwa. Zuhra ji tayi jikinta yayi sanyi saboda yanayin da taga Hamza. Da gani yana cikin damuwa Allah Yasa ba wani laifin tayi masa ba. Plate din tuwo kuwa sai da suka sude shi tas ita da yarta Nana sannan aka tashi aka wanke hannu. Bayan yayi wanka Izzatu ke tambayarsa ya aiki. A hankali yake magana yace Alhamdulillah. Tana zaune akan kujera tana masa kallon tuhuma tace Hamza ko ka fara sonta ne? Bangane ba shima a zaunen yake don baya jin zai iya cin abinci. Banda damuwar da yake ciki hannun Zuhra yake hangowa miya na binsa ta gefe tana kai lomar tuwo. Yarinyar ta fiye kazanta. Izzatu ta dan sha kunu Zuhra nake nufi. Lokacin da ka shigo ita ka fara kallo kuma ka danyi murmushi. Izzatu kenan,yanzu baki bani komai nasa a baki ba kike tuhumata. To idan naso ta laifi ne? Matata ce fa. Sosai ta daure fuska bana so, Hamza bana son irin wannan wasan. Nan da wata shida zata koma gidan iyayenta mu cigaba da zamanmu yadda muka saba. Daga nan sai kuma ta soma murmushi baka ga yadda take cin abinci ba dazu. Baka ce dan bakin nan tana zai dauki abinda take tura masa ba. Idan ka fita yau pizza zaka siyo mana Baby a matsayin dinner. Ko sau daya bata damu da rashin walwalarsa ba. Hmmm kina bani mamaki Izzy...me kuma nayi Babyna? Murmushi take masa tana kashe ido. Fada mata ma bata lokaci ne don karshenta ta fadi abinda zai kara bata masa rai. Babu komai bari na dan kwanta kaina na ciwo. Tashi tayi to bari na kawo maka magani. Amma kafin nan ga wannan....ta dauko cards har kala hudu na biki. Ni duk matsalar Zuhra yasa na manta next week za'a fara bikin Mardiya cousin dina ta kaduna. Yar Uncle Jibril kanin Dad dinmu. Wai matar da miji ya fadawa yana ciwon kai kenan. Ga naka na daurin aure, ni a son raina ranar saturday na tafi kadunan saboda muna da shirye shirye a gabanmu. Kasan dani suka dogara tunda na zauna a Canada suna son ayi abin da tsari sosai. Kije Allah Ya kiyaye hanya ya fada a takaice....bargo yaja ya rufa har kansa. Bashi da kwarin yi mata fada ko fada mata abinda ya kamata. Sai da ta gama yi masa lissafin kudin da take bukata sannan ta dauko masa magani da ruwa. Sai la'asar ya tashi jikinsa ya danyi kwari sannan kan ya dena ciwo. Masallacin kusa da gidansa yaje yayi sallah ya dawo yaci abinci. Yana gama cin abincin ya dauki key din mota....Izzy ni zan fita ki fadawa yarinyar nan kada tayi abincin dare zan taho muku da pizza din in sha Allah. Duk maganar a sanyaye yake yinta, wani salihanci yake ji tunda Oscar ya dibga masa sata. Tace harda Zuhra kuma? Ba kayi mata siyayyar kayan abinci ba. Yace nasan nayi amma as long as tana gidan nan zanyi kokarin sauke nauyinta. Tabe baki Izzatu tayi to shikenan sai ka dawo. Har bakin mota ta rakashi ya tafi gidansu. Nan ya zauna suka sha hira da kannensa kamar bashi ba. Hajiya taji dadin ganin ya sake ba kamar dazu ba Takwas da rabi a gida tayi masa ya shigo da ledar pizza har hudu manya. Ya riga ya kudurce a ransa daga yau siyayyar abincin alhamis ta kare sai lokaci lokaci kuma. Itama Izzatu zai bata kudi taje bikin ta dawo sannan ya sanar da ita halin da yake ciki tunda bata tambaya da kanta ba. Ita da yara suna ta murna da ya dawo ta karba ta rarraba. Yanka biyu ta sakawa Zuhra a plate Hamza yace ta kara mata daya saboda big size ce. Tala ta kirawo ta kaiwa Zuhra daki saboda tun bayan magriba bata sauko ba. Tala ta fito daga kitchen hannunta duk kumfa tana gogewa da tsumma. Hamza ya mika hannu bari na kai mata saman zani. Plate din ta mika masa tana tambayarsa a ina zai ci tasa yace ta kai masa falonsa yau baya son hayaniya. Zuhra na kwance akan doguwar kujerarta tana kallon wani film din Hausa na marigayi Rabilu Musa dan ibro tana ta dariya. Tun daga bakin kofar dakin Hamza yake jin dariyarta. Yarinyar nan bata da kamun kai ya fada a ransa. Ji yadda take dariya kamar ba mace ba. Sallama yayi ta tashi da gudu ta dora hijab a jikinta. Plate din kawai ya mika mata zai fita sai yaji tace ina wuni? Tunawa tayi dazu tana cin tuwo bata gaishe shi ba. Jiya kuwa dama basu hadu ba. Da ya juyo ya amsa sai yaga plate din take karewa kallo. Ta dan kalle shi....shi kuma wannan menene? Pizza ce, baki taba ganinta bane? Tace eh, Allah Yasa da dadi dai. Sai da yayi murmushi sannan yace ci ki ji mana. Yanka daya ta dauko gashi da girma ta dan lankwasa shi biyu ta tura a baki ta gutsiri rabi. Sai da Hamza yasa hannu a bakinsa don mamaki....tabdi! Ke bakinki zai iya yagewa idan kina katuwar loma haka. Dan gayun nan na mata ma baki iya ba. Wani irin dandano taji da bata taba ji ba. Abin dai bazata iya kwatantashi ba. Bata san lokacin da ta furzar da na cikin bakinta ba, wanda bai sauka a ko'ina ba sai kafar Hamza. Wayyo Allah, Wayyo Allah, Wayyo Allah shine abinda yake ta nanatawa ya dage kafar tare da kawar da kansa gefe. Idan ya kalli kafarsa yasan dole ne yayi amai. Kamar yayi kuka saboda da takaici. Yana girgiza kai yace ke kuwa me nayi miki zaki tofa min abin baki. A tsorace ta dago kai zata bashi hakuri. Sauran ya gani a gefen bakinta da habarta. Dan danne fushin da yake yi ne ya gagara ya daka mata tsawa....Goge bakinki mana. Da hijab dinta tayi saurin gogewa sannan ta sake cewa kayi hakuri, shi kuwa sake hade fuska yayi yana ta yatsina hanci....kai so disgusting yace yana rike hanci. Irin kallon bangane ba tayi masa sannan tace SO kuma? Ni yaushe kaji nace so? Ba cewa nayi ina sonka ba hakuri nake baka. A wane dalilin zan ce ina sonka? Mamaki ta bashi ya rasa daga ina taji kalmar. Sai daga baya ya tuna yace SO DISGUSTING. Dariya sosai abin ya bashi, yace anya kin taba shiga aji kuwa? Sosai ma kuwa, har SS3 na kai a sakandire. Tana magana ta durkusa zata goge masa na kafar tasa da hannunta. Saurin jan kafar yayi tare da yin tsaki...kazama da hannu kuma zaki goge, ni bani tissue. Eyye me kace? Ya sake maimaimatawa. Dan murmushi tayi na ta gane zancen. Toli fefa kake nufi, wallahi bani da ita. Jin kafarsa yake kamar ya yanke ta yace to dauko min ta toilet dinki da sauri. Ya dan kalli kafar....Oh God I hate this. Gani yayi bata tafi ba ya dan daga murya nace ki dauko ta toilet kin tsaya kina kallona. Baya ta dan sake matsawa na fada maka babu. Iko sai Allah, yanzu ko a toilet babu? To da me kike amfani. Dariya ya bata ji wata irin tambaya.... tace da tawul mana, ni bansan ana goge jiki da toli fefa ba. Jin bata fahimce shi ba ya kara bashi haushi. Ni ba cewa nayi a goge jiki ba. Shiru yayi saboda kunyar abinda zai fada. Da kyar yace kafin kiyi tsarki nake nufi. Kanta ta dan juyar a kunyace tace tsarki da toli fefa kuma kamar wata arniya. Yarinyar nan duka take so...kwafa yayi sannan yace ke a kazantarki idan kin gama abinda kike a toilet hannu kike sawa? Shi kam Izzatu ta cuce shi da tayi sanadin auren nan. Gaskiya ke kazama ce ta karshe ya fada yana toshe hanci. Hanyar toilet dinta yabi zai wanke kafarsa sai wata zuciyar ta hanashi. Karshenta yaga wani kayan kazantar. Da jan kafa ya fita daga dakin ya tafi nasa. Ya shiga toilet ya sakarwa kafar ruwa. Sai da yaga babu komai a kafar sannan yayi wanka ya fito. STORY CONTINUES BELOW  Ita kuma Zuhra gyara wurin da abin pizzar ya bata tayi ta sauka da sauran a plate. Izzatu ta kaiwa suna cin nasu dasu Khalifa tace bazan iya cin wannan abin ba. Izzatu tayi dariya dama shi ya dage sai ya baki. Tana karba ta bude plate din da ta saka masa nasa ta kara da sauran biyun na Zuhra. Tana kallo Zuhra ta wuce kitchen dinta ta dumama tuwo ta haye sama zata ci. A bakin bene suka hadu yace mhmmm haka kika iya, ki cika kwano da tuwo. Bata amsa ba ta bashi wuri ya sauka. Izzatu ta biyoshi falonsa da nasa abincin. Biyun saman wanda aka yi da naman kaza ya cinye yace ya koshi. Izzatu tace kuma kai na ajiyewa mai beef(naman saniya) din don nasan shi kafi so. Ruwa ya dauka a cup yana sha tace ashe rabonka ne mai chicken din da Zuhra ta dawo dashi wai bata.......kwarewa yayi sosai tun kafin ta gama maganar ya soma kakarin amai. Idanunsa har ja suka yi saboda wahala yace yanzu Izzy ragowar yarinyar nan kika bani. Tace to meye ai bata ci ba, hannu tasa tana shafa masa baya. Sannu kaji my darling shiyasa ba'a son magana idan an cin abinci. 41 Washegari meeting din gaggawa ya kira da dukkan maaikatansa. A nan yake sanar dasu abinda Mr Oscar yayi. Inuwa sakatare yace shi yayi mamaki da ya ganshi a banki amma tunda manaja yace da yardar Hamza aka saki kudin shiyasa bai tayar da zancen ba. Maaikatan suka tambayi Hamza garin yaya haka ta faru yace matsalace ta taso daga gida a lokacin. Yana kujerar tsakaya a conference room din yadda kowa zai iya ganinshi a katon zagayayyen table dinsu yace kada ku damu in sha Allah bazan bari kwazonku ya tashi a banza ba. Sauran cheques din ya nuna musu Allah Yasa na rarraba da guda daya ne Oscar ya dauka ba karamar matsala zamu shiga ba. In Allah Ya yarda zan san yadda nayi na fito da wata miliyan goman da zamu hada musu. Next zuwan Mr Peter kasar nan zamu hada musu kudinsu. Ayyukan gabanmu kuma kunga manyan projects ne. Ina rokon kuwa dage ayi ingantaccen aiki. Sannan ina neman afuwarku na kasancewata shugaba mai sakaci da aiki. Muryoyi ne suka rinka tashi suna fada masa babu komai. Wani yace yallabai irin haka shine yake sa bawa ya kara jajicewa da imani. Ba karamin dadi yaji ba da yadda suka yi masa uzuri. Bayan sun gama tattaunawa addua suka yi aka rufe taron. Shima sai ya sake samun kwarin gwiwa tare da yiwa kansa alkawarin bazai sake basu kunya ba. Kafin ya koma Izzatu ta gama hada duk kayan da zata bukata na tafiyar. Idan ta tafi sai lahadi ta sama zata dawo. Sannan ta sanar da Zuhra zatayi tafiya. Tala ma ta hada nata kayan dana yara. Suna zaune a falo daga Zuhra sai Izzatu tace idan mun tafi basai kinyi girki da Sweetyna ba. Zai rinka siyan abincinsa, da zaki yarda ma kawai ki tafi gidanku ki kwana biyu kafin na dawo. Zuhra tace a ranta lallai Izzatun nan ma, daga aure sai tafiya gida a kwana? Wannan ai sai mutane su gane lallai auren babu lafiya. Izzatu tace kinyi shiru ko ba kya son zuwa gida. Nasan dole zaki fi jindadi da sakewa a nan to amma....Zuhra taji haushin maganar tace ba haka bane, su Baba zasu yi tunanin ko akwai matsala. Kinga idan akayi sakin laifinsa zasu gani. Izzatu tayi dan tunani eh haka ne fa. To ki zauna amma ko da wasa kada ki shiga harkarsa nasan shima bazai shiga taki ba don ba sonki yake ba. Murmushi Zuhra tayi tana jin yadda Izzatu ke fada mata bakaken maganganu. Dubu dari Hamza ya bawa Izzatu kafin su kwanta. Tayi murna amma fuskarta ta nuna ba haka taso ba. Yana daga kwance yace ya akayi ne? Juya kudin take yi a hannu babu komai, nayi tunanin zaka karamin ne saboda yara. Ga Tala zan tafi da ita don ta kula dasu. Tashi yayi zaune ba shiri, da Tala zaki tafi amma baki fada min ba? Tunaninsa bai wuce zaman da zaiyi da Zuhra shi kadai ba na kwana takwas. Izzatu tace da bakinka kace ko unguwa zani na dade na rinka tafiya da ita. To zan sami karin kudin? No, yace tare da sake kwanciya. Bani dasu. Idan kin dawo akwai maganar da nake so muyi. Ta tashi ta saka kudin a jaka. Indai ba Zuhra ka fara so ba ko meye babu damuwa. Hamza ya girgiza kansa kawai ya kwanta, halin Izzatu sai ita. Wato gara duk abinda zai faru ya faru akan ta zauna da kishiya. Washegari da wuri suka shirya kafin goma duk kayansu suna mota. Suna gama breakfast dreban da yake kai su Khalifa makaranta ya iso. Tare zasu tafi ya dawo a motar haya ya barwa Izzatu motar. Idan sun tashi dawowa ya koma ya dauko su. Har bakin mota Zuhra ta rako su. Hamza ya rungume 'ya'yansa sannan suka wani manne da juna shi da Izzatu ana kiss a gaban mutane. Kunya duk ta ishe Zuhra. Ita kuwa Tala dama ta saba gani. Nan suka tsaya har motar ta fita maigadi ya rufe gate. STORY CONTINUES BELOW  Ajiyar zuciya Zuhra tayi tana tausayawa kanta yadda zata zauna ita kadai a gidan. Kasancewar Hamza ba tafiya zaiyi ba bai dameta ba tunda ba harkar juna suke shiga ba. Ciki ta koma zata tafi dakinta Hamza ya shigo yace ki shirya bayan azahar zamu fita. A sanyaye ta dan juyo gida zaka mayar dani? Na fada mata zan zauna a nan saboda kada a zargi wani abu a gida. Hamza yace Izzatu tace ki koma gida ne? Wai ita zai nunawa bai sani ba. Tace eh jiya ta fada min. Dan guntun tsaki yayi. Izzy ta fiye rigima itama. Ki shirya zamu je ki gaisa dasu Baba sannan muje gidanmu. Wani tsalle tayi da yasa ya matsa gefe kada ta bige shi. Alhamdulillah ta fada ta haye sama cike da murna. Wani lokacin sai ya ganta kamar mai hankali, idan abin ya motsa kuma ba kanta. Daga murya yayi yace idan na dawo daga masallaci baki shirya ba an fasa. A hankali tace zaka sha mamaki. Ai kuwa yasha mamakin domin yana dawowa daga masallacin ya ganta zaune kwam a falo ta gama shirinta. Tuna masa tayi da ranar da ya fara ganinta har ya kusa bigeta da mota. Duk zafin da ake a gari fuskarta sai kyallin foundation take. Tabi girarta da pink din jagira ta gyarata, da yake kayan jikinta akwai green sosai har mayafin haka ta saka green din eyeshadow. Sai yan labbanta da ta zanawa bakin lining sannan ta saka jan janbaki da ya fito sosai. Abin bai bashi dariya ba ma, wannan wace irin kwalliya ce. Mtswwww Da taji yayi tsaki ga wani kallo da yake binta dashi sai jikinta yayi sanyi. Shi dama bai ma gama shiri ba don jallabiyace a jikinsa. Muje yace da ita yana shirin hawa bene. A tsorace tace ina???? Sama ya nuna mata da hannu. Kawai gani yayi ta durkusa gwiwoyi a kasa idanunta sun ciko da hawaye don Allah kada mu fasa zuwa. Don Allah ka kaini naga Ummana da Babana. Yayi yar dariya au gorin iyaye zaki min? Girgiza kai tayi da sauri a'a Ummanmu da Babanmu nake nufi. Yace to naji tashi muje yana murmushi. Da gaske sama taga zai hau sai ta dan ja baya. Hannunta kawai ya kama ya ja ta suka hau saman tana ta tirjewa. Wani abu yaji ya soki zuciyarsa da ya kama mata hannu. 42 Iyakar karfinta tasa tana neman kwace hannunta amma rikon da yayi mata ba na wasa bane. A haka ya jata suka je dakinsa ya dauko kwalin tissue sannan suka koma nata dakin. Iyakar tsurewa Zuhra ta gama don bata san abinda zaiyi mata ba sai magiya take yayi hakuri. Yana jinta ya share, sai da suka zo gaban dressing mirror dinta ya jawo stool din ya zaunar da ita. Numfashinta har wani sama sama yake don fargaba. Har tausayi ta bashi sai ya dan sassauta murya tare da daidaita fuskarsa da tata har suna jin numfashin juna...ke, rufe idonki. Ji tayi kamar zuciyarta zata ballo kirjinta ta fito, ba dai hada bakin da ya gama da Izzatu zaiyi da ita ba. Ita ko a litattafan hausa idan tana karantawa ta tsani ace anyi kiss. Turawa dai marasa kunya suyi abinsu amma ita duk yar kazantarta kyankyamin haden bakin nan take yi. Kokarin tashi tayi ya rike kafadunta ya sake zaunar da ita. Kawai sai ta saka masa kuka...don Allah kada kaci amanar matarka. Kamar yau ne zata dawo kuyi abinku. Tissue yake zarowa daga kwali yace me zamuyi? Kanta a kasa tace sumba mana. Bai san lokacin da ya soma dariya ba. Kece sumbar ai....ya nuna bakinta Allah Ya kiyaye nayi kissing wannan dan bakin. Ina miki kallon saliha ashe kema idonki ya bude kinsan kiss. Hannuwanta tasa ta rufe fuskarta don kunya yasa hannu ya sauke su. Rufe ido nace. Ba musu ta rufe...tissue ya ninke ya soma goge mata girarta. Yana yi yana kallon yadda ta bata rai harda turo baki. Bai bar abinda yake ba yana yi yana kallonta. Ya gama da girar ya koma saman idanunta da lips dinta. Takaici duk ya isheta kwalliyar rabin awa an goge mata ita. Hannunta ya sake kamawa ya kaita kofar toilet. Jeki kisa sabulu ki wanke fuskarki. A tsiwace tace bayan duk ka goge min kwalliyata. Daga hannu yayi zai dalle mata baki ta tafi da sauri. Ke dawo ki ajiye mayafin kada ya jike. Kamar bata ji me yace ba sai da ya maimaita da dan fada fada. A hankali ta warware shi. Idanunsa a kanta, dole ta rufe jiki da katon mayafi irin wannan matsatsiyar riga. Doguwar riga ce mai kyau duk ta fito da surar Zuhra. Ta wuyan rigar kirjinta ya dan fito. Tana daga hannu ta ajiye ya hango hammatarta......fal gashi.1 Saurin kawar da kansa yayi. Yaso shagala da kallon jikinta sai gashin da ya gani ya dawo dashi. Gaskiya lamarin Zuhra akwai gyara. A inda ta barshi ta dawo ta same shi yace ta sake zama a kan stool din. Wani lotion mai kamshi yasa kadan a hannunsa saboda zafin gari ya shafa mata a fuska. Daga shi har ita wani yanayi suka shiga yadda yake shafa mata fuskar. Bayan ya gama ya dauko hoda ya shafa mata. Sai ya duba lip gloss light brown ya sa mata a baki. Har abin taje gira yasa ya kwantar mata da gashin girar sosai. Ita kanta sai taga tafi dazu kyau duk da tana son saka janbaki da eyeshadow. Kallonsa take yadda ya iya sarrafa kayan kwalliyar mata. Da ya gama mikewa yayi yana dan sosa bayansa da ya kage saboda ya jima a duke. Hararta yayi saura kice min dan daudu, kuma ko kice kinyi kyau bare kuma godiya. Murmushi tayi tace nagode. Shareta yayi ganin ta fara dariyar shakiyanci bari naje na shirya ki canja kayan nan kafin na fito ki saka mai zani. Wata atampa mai adon pink da fari ta saka wrapper skirt da riga. Duk Hajara ke kai musu dinki kuma sunyi sa'ar tela. Pink din mayafi ta saka da farin takalmi da yar jaka fara mai kyau. Sake kallon kanta tayi a mudubi tayi murmushi. Mutumin min nan yana da kirki idan yaso. Amma banda wayon ya tabani meye zai goge min fuska da kansa. Tana zancen zuci taji wani kamshin turare mai dadi. Hamza ne sanye da yadi ruwan madara mara nauyi. Ya gyara fuskarsa ya rage gemu da gashin baki. Sai ya kara haske da yi mata kyau. Shima kallonta yayi ta canja kayan yace better...Zuhra tace best. Ta dan daga gira...nima fa na iya turancin nan. Good, better, best waye bai iya ba. Dariya ta bashi ita kuwa ko a jikinta tabi bayansa suka fita.2 Da kansa ya bude mata gaban motar ta zauna ya rufe. Yana tayar da motar ya kunna AC, ko minti biyar basu yi da fara tafiya ba ta soma gyangyadi. Dan bugun kujerarta yayi, kinji sanyin AC ko, to idan kika yi min bacci jefar dake zanyi a titi na huta. Gyara zamanta tayi tace amma dai wasa kake yi ko? Gabansa yake kallo ki yi baccin sai mu gani wasa ne ko gaske. Waje ta koma kallo. Da shirun ya isheta tace Allah Sarki su Nana suna hanya ko. Kaduna babu nisa sosai tun dazu suka isa ya bata amsa. Daga nan motar tayi tsit ko rediyo bai kunna ba. Motar na shiga layinsu Zuhra yara suka fara binsu ana ga Zuhran baban yara. Hannu bibbiyu ta rinka daga musu. Har su Anas da Sani kowa ta gani sai ta daga hannu. Haka kawai Hamza sai abin bai masa dadi ba. Tana dagawa Munkaila mai shagon kusa da gidansu hannu Hamza yace kika kara daga hannu sai na dalle miki baki. A islamiyya ba'a koya muku kamun kai bane. Turo baki tayi to kuma sai ka hanani zumunci da mutane. Rai a bace ya juyo sai dai ko motar bata jira ya kashe ba ta fice da gudu. Umma na kwance a falo taji an fado mata a jiki. Tana kokarin tashi Zuhra ta soma kuka. Umma tace to meye haka kuma. zuciyarta cike take da farincikin ganin yarta. Baba da ke daki fitowa yayi da jin muryar Zuhra. Shima makale shi tayi tana kuka. Umma tace wai kukan na meye ne? Hamza ne ya shigo dauke da manyan ledoji guda biyu yace kukan shagwaba take yi Umma. Baba ya tarbe shi, har kasa ya durkusa ya gaishesu tare da ajiye ledojin a gaban Baba. Umma tace kai kuwa baka gajiya da wahala. Duk zuwa sai kayi dawainiya. Dan sunkuyar da kansa yayi albarkarku muke nema Umma. Zuhra mamaki tayi wai dama yana zuwa gidansu. Kawai sai taji ya kara girma a idonta. Zata yi kokarin dena yi masa rashin kunya. Hira sosai suka yi da Baba ita kuma suka shige daki da Umma. Duk dadi ya kama Umma taga kamar Zuhra ta nutsu. Zuhra tace sai bayan hutu zaki dauko Safara'u ne? Umma tace eh ance sun kusa fara jarabawa. Zuhra tace yace daga nan gidansu zamu je. To me zaki kaiwa surukan naki? Sai a lokacin tayi tunani ya kamata ace ta kai wani abu tunda yana yiwa nata iyayen. Umma bata jirata ba ta fita kitchen. Kayan kamshi da kayan kadin da kanwarta ta aiko mata da yawa ta zuba a leda ta bata. Da zasu tafi bayan sunyi sallar laasar Baba ya bata wani turare mai kyau yace ta kaiwa Alh Nasiru. Har suka isa gidan babu wanda yayi magana a motar. Ficewarsa ma yayi daga motar ya shiga gidan ya barta. Kwafa tayi sannan ta fito da ledarta a hannu. Hanyar da yabi itama ta bi. Sai ta ganshi a bakin kofa yana tsaye...kinji yadda naji dazu da kika fita baki jirani ba. Bude baki tayi....lahhh wai haushi kaji. Sai kuma yaji haushin kansa meye zai biye mata harda ramawa. Gyaran murya yayi shi a dole a ba wasa. Shige muje ya nuna mata hanya.+ Dakin Mama suka fara zuwa bata ciki. A hanyarsu ta zuwa dakin Hajiya suka hadu da Adabiyya. Wani ihu ta saki tare da kankame Zuhra. Oyoyo Anti Zuhra....Hamida naji ita ma ta fito daga dakinsu suna ta ihun murna Zuhra na murmushi. Hamza yace lallai yaran nan. Kirikiri kun nuna min bakwa son uwar 'ya'yana. Hamida tace to Yaya ai itama ba sonmu take ba. Tana fada ta shige daki da gudu don tasan muguntar dallin bakin da yake mata. Adabiyya ta gaishe shi sannan taja hannun Zuhra suka tafi kitchen. Hajiya na dora ruwan tuwo suna hira da Mama. Adabiyya na shiga Hajiya tace wato don kada kuyi aiki kunce zakuyi karatun jarabawa sai gashi kun cika mana gida da ihu. Adabiyya tana dariya ta turo Zuhra da ke makale jikin kofa kinga bakuwar da muka yi. Mama ta taso itama tana mata sannu da zuwa. Kasa Zuhra tayi duk ta gaishesu. Ina Yayan naku Mama ta tambayi Adabiyya. Yana wajen dakinku. Fita Mama tayi tace Adabiyya kaita dakinku zata fi sakewa ki kai mata abinci. Idon Zuhra na kan Hajiya tana bare albasa zata hada ruwan miya. Gabanta ta karasa a kunyace tace Hajiya kawo na yanka miki. Itama Hajiyan ta rasa dalilin da yasa taji kunyar Zuhra kamar yanzu Yaya ya fara aure. Barshi kuje daki da Adabiyya idan na gama zanzo mu sake gaisawa. Adabiyya ta gama hada cup da lemo a tray tace zo muje Antinmu. Zuhra ta mika hannu don Allah Hajiya ki kawo na tayaki. Me zaki dafa nayi miki? Na iya girki fa. Hajiya tayi murmushi tana kallon Zuhra. Mayafinta ta cire ta jefa saman kofar kitchen din. Adabiyya tace don Allah kizo muje idan kika sha ruwa sai mu dawo. Ki tayani zama a nan kawai muyi girki. Ta karbi albasar Hajiya kije ki huta. Sosai Hajiya taji dadi sai dai kuma girkin saboda Alhaji da zai dawo daga Kumo yau take yi. Amma yadda Zuhra ta langabe mata kai yasa ta hakura ta fada mata tuwon semovita zata yi da miyar danyar kubewa wadda tuni Hamida ta gurza. Tana fita Adabiyya tace gaskiya ina taya Yaya murna yanzu yayi aure. Zuhra bata ce komai ba sai dariya tace ta bata roba zata yi rude. Sai ga Hamida da littafi a hannu tace ayi hirar da ita. Sunso sa mata hannu tace ita dai su tayata zama. Komai ta nema zasu nuna mata haka tayi tuwonta wanda ya tuku sosai yayi kauri. A leda ta kulle sannan ta bar ruwan miyar wajen awa daya yana dahuwa wutar kasa kasa yadda Umma ke yi. Hamida tace ita kamshi ya dameta a kada miyar yau tuwo zata ci ba indomie ba. Suna ta barkwancinsu har ta gama hada miyar kitchen din yana ta kamshi. Mama da Hamza suna daki suna hira. Da suka gama yace zai fita sai bayan sallar isha zai dawo. Dakin Hajiya taje tace mu leka yarinyar nan ko? Hajiya tace tana kitchen da yan uwanta wai ita zata yi tuwon. Farincikin Mama bazai misaltu ba tace Hajiya kinga ikon Allah ko. Kina ganin Zuhra kinsan yarinya ce mai tarbiya. Hajiyan ma murmushi take, sai wani koda surika kike a gabana ko kunya babu. Bari nawa dan Nura yayi aure kisha mamaki. Haka suka sha hirarsu gwanin sha'awa har suka ji shigowar motar Alhaji. Ana magariba Hamida ta zuba musu tuwon a katon faranti. Suna ci yan matan na zuba mata santi. Ita duk kunyarsu take ji ta kasa sakin jiki taci sosai. Bayan sun gama Mama tace su rakata falon Alhaji ta gaishe shi. Tuna ranar da ta fara zuwa gidan tayi kunya ta kamata ta rufa katon mayafinta ko fuskarta baa gani. Tana durkusawa ta gaisheshi ya fara miko mata rafar kudi dubu goma. Tayi saurin daga kanta yayi mata murmushi wannan tukwicin ciyar da dan tsoho ne. Itama murmushin tayi Hamida tace Alhaji mun tayata fa. Yayi dariya kin tayata hira dai. Daga shi har Hajiya da Mama duk sun mata karba mai kyau suna ta yabon iya girkinta. Wannan kuwa a wurin Ummanta ta koya. Da zasu koma dakinsu Adabiyya ta dauko turaren ta mika masa gashi inji Baba. Allah Sarki mal Bashir harda wata wahala banda 'ya da ya bani. Ina fata babu wata matsala dai tsakaninki da Yaya da Izzatu. Tace babu komai nagode. Ledar kayan da Umma ta bata ta bawa Adabiyya ta kaiwa su Mama. Tasha addua sosai a wurinsu. Da Hamza ya dawo falon Alhaji yaje. Suna hira ya bude food flask din yaga akwai sauran tuwo a ciki. plate din Alhajin ya jawo ya zuba yaci harda karawa. Alhaji yace Kaltume kiyiwa danki magana ya bar min na dumame. Hamza na dariya yace yau tuwon yayi dadi amma ba jagwalgwalon su Adabiyya bane ko. Mama tace me ka mayar min da 'ya'ya ne. Don kasan matarka ce ta dafa kake mana santi. Cak ya tsaya da shan miyar da yake da cokali yana kallon Mama. Hajiya tace yau kowa yasan sabon hannu yayi mana girki sai yabonta ake yi. To Hamza, ga abinci da dadi ga kyankyamin Zuhra da yake. Amma dole ya yaba mata don ba karya ta iya girki. Da zasu tafi Mama atampa Super Exclusive ta bata mai kyau, Hajiya kuma ta bata dubu biyar. Sai godiya take musu kamar ta ari baki. Su Adabiyya suka yi mata alkawarin zuwa su kwana biyu da weekend don duk cikin satin zasu gama jarabawa. Adabiyya na level two Hamida na level one a jamia. Hamza sai mamakinsu yake basa son zuwa gidansa a iya saninsa. Ba karamin dadi taji ba yadda suka karbeta a gidan. Suna isa gida ya rufe ko'ina yace mata sai da safe. Yana son yaba mata yadda ta kyautatawa iyayensa amma wata zuciyar ta hana shi. Abinda su Hajiya suka bata ta nuna masa yace to Allah Ya saka da alkhairi. Kema an fada min abinda kika kai musu nagode. Taji dadin godiyar tasa ta tafi dakinta zuciyarta fes. Da sassafe ta farka ta gyara wake ta bawa maigadi ya kai mata markade. Haka kawai taji kosai take son yi. Waken ba dayawa ta hada ba tunda nata ne ita kadai amma tayi yadda maigadin zai samu don tana ta tunanin me yaci jiya da rana da kuma dare. Tafi kowa sanin yunwa ba dadi. Kunu ta dama da tsamiya ta dan saka lemon tsami sannan ta soya musu kosan. A dan karamin jug din roba ta zubawa maigadi nasa kunun sannan ta sami wata robar ta zuba masa kosai da yaji. Nata kuma ta kwashe daga mai ra barshi ya tsane kafin ta kaiwa maigadin. Tana juyowa taga Hamza har sai da taji tsoro. Ya gama shirinsa zai tafi wurin aiki. Gaisheshi tayi tace zan mikawa maigadi abinci. Hanya ya bata ta wuce ya tsaya yana kallon kosan. Yana jin yunwa amma bazai ce tayi abinci dashi ba duk da jiya yaci kuma ya yaba. Kamar ya fita daga kitchen din sai ya dawo bari yaci yaji ko ta iya kosan. Izzatu bata yi tace abincin talakawa ne. Daya ya jefa a baki yaji dadi harda dan kurbar kununta dake cikin kofi. Gaskiya da dadi, a hankali ya dawo ya dan leka falon yaga bata taho ba. Da sauri yazo ya dauki wani harda saka yajin da ke wata yar roba ya kuma sawa a baki duk da akwai zafi sannan ya dauki biyu a hannu. Ko taunawa bai fara ba Zuhra ta dawo tayi mamakin ganinsa a kitchen din tace ashe baka tafi ba. A ransa yace me zaisa ta dawo yanzu. Gimtse baki yayi yace uhmm. Kallon rashin yarda tayi masa ko akwai abinda kake so? Uhmm uhmm ya amsa bakin nan a rufe. Ya rasa yadda zaiyi da kosan bakinsa. Daukar plate tayi ta juye kosan ta dauki kofin kunun tace to adawo lafiya ta fice ta barshi a tsaye. Sai a lokacin ya saki numfashi sannan ya sami damar tauna da hadiye kosan bakinsa. Ficewa yayi ya shiga mota ya cinye sauran biyun sannan ya goge hannu ta tissue. A mudubin motar ya kalli kansa....Hamza kaji jiki, satar kosai a cikin gidanka. Murmushi yayi ya ja motarsa. Missing page. Assalam alaikum wa rahmatullah. Afuwan masu karatu. Wasu pages din na labarin nan sun bace min saboda ya dan jima. Dalilin ma da na kawo shi nan kenan saboda bacewar da yake neman yi. A halin yanzu pages wurin uku ne bani dasu ciki harda wannan. Idan akwai wadda ta samu don Allah turo min ta wannan num din Nagode Abinda zan iya tunawa ya faru a shafin shi ne, Hamza zai cigaba da diban abincin Zuhra idan ta dafa a boye saboda yana masa dadi. Ita kuma da ta gane shi ne sai take mayar da abin tsokana. Tayi girki ta ajiye inda zai gani. Yana zuwa ya diba zai ci ta fito sai ya mayar da spoon din ya ajiye. Shi ne take soma kukan karya wai akwai aljanu a gidan suna satat mata abinci. Hankalinsa ya tashi yana son yi mata bayani ta kara da cewa ta fadawa maigadi ya kirowa malami ayi karatu a gidan domin korarsu.

0 Comments