AL,ADUN WASU CHAPTER 7

AL,ADUN WASU CHAPTER 7
Gidan kanwar Mamanta inda suka yi masauki Izzatu ta tafi. Ko rufe motar bata yi ba ta shiga cikin gidan tana ta rusa kuka. Ana ta tambayarta abinda ya faru taki bada amsa. Sai da kanwar Maman tasu tayi mata tsawa sannan tana shesshekar kuka tace Alhaji ne yace Hamza sai ya auri yarinyar da nayiwa April fool jiya. Anti Larai kanwar Raliya tace kai amma Allah Ya sakawa Alh Nasiru da alheri. Ni dama kinsan duk wannan shirmen naki ba zuwa nake yi ba saboda na rasa wace irin rayuwa kuke yi ke da mijinki. Tun jiya da aka bani labarin abinda kika yi raina ke kuna. Ta mayar da kallonta ga Raliya...Wallahi duk laifinku ne Yaya Raliya. Rayuwar turai ai ba hauka bane. Yara kusan shekara tara da dawowarku kasar nan amma sunki yarda su yar da al'adun da ba nasu ba. Yanzu wa gari ya waya. Raliya ta sunkuyar da kanta kasa. Tasan tabbas gaskiya kanwarta take fada. Ta kalli Izzatu da take ta kuka...sai ki rungumi kaddara tunda ke kika jawowa kanki. Ni bazan shiga zancen nan ba kuma daddynku ma zan fada masa babu ruwansa. Allah Ya baku zaman lafiya. Izzatu tace haba Mum haka ma zaki ce. Raliya tace to ai tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ke duka. Daki Zeenatu ta Izzatu tana rarrashi. Kinga Izzatu kiyi hakuri yayi auren nan tunda dama yan gidansu basa kaunarki. Idan kika nuna bakya son auren suna iya sawa ya rabu dake. The way I see it wannan yarinyar bazata kai ko'ina a gidan ba zai saketa. Da haka tayi ta rarrashin Izzatu har ta hakura ta dauki wayar Hamza da yake ta kiranta ta fada masa inda take sannan ta kusa dawowa gida. Bayan ta koma ne suka yanke shawarar yaje gidan su Zuhra kamar yadda Alhaji ya bukata. Maganar auren tasa fushin da yake da Izzatu akan matsalar kamfaninsa ta ragu. Wani light blue din yadi ya saka da aka yiwa dinki mai kyau amma simple style ba ado da yawa. Yasa hula mai ruwan madara da light blue. Yayi kyau sosai don ma bai fiye sa manyan kaya ba. Ya sha turare sannan Izzatu ta daura masa links a hannun rigar da agogo. Yana saka takalmi tace cikin shagwaba ni gaskiya kayi kyau da yawa kamar kada ka fita. Murmushi yayi mata. Kada ki damu bazan dade ba. Da tambaya ya iso gidan domin zuwan su na dare ga ransa a bace ko kallon hanya baiyi ba. Yaro ya tura yayi masa sallama da Zuhra. Yaron na tafiya yabi bayansa ya tsaya a soron inda suka zauna da Baba. Yaron na sallama Zuhra ta amsa. Ita kadai ce a gidan Umma ana la'asar suka tafi kai garar Hajara. Baba ma ya fita tun safe bai dawo ba. Tana gaban murhu zata fara tuka tuwo. Da murmushinta tace Isuhu daga ina haka? Isuhu yace wani mutum ne a waje wai Hamza yace kizo. Wallahi baki ga yadda ya hadu ba Zuhra, motarsa ma abin kallo ce. Ga wani kamshi dan ubansu yana fitarwa. Tunda Isuhu ya fara magana gabanta ya fadi. Ba yadda za'ayi ta yarda da auren nan. Rokonsa kawai zata yi su fadawa iyayensu basa son auren. Ina ita ina wannan mutumim, ita tsoronsa take ji. Isuhu ta kalla kace masa ina zuwa tuwo zan tuka na kwashe. Babu kowa ne a gidan. Duk maganar da sukeyi Hamza na jinsu. Bashi da niyar dadewa a gidan saboda haka dan aiken nasa na fitowa naira hamsin ya bashi shi kuma yayi sallama ya dan shiga daga cikin tsakar gidan. Zuhra bata gama tantance sallamar waye ba taga mutum ya soma shigowa. Gashi ta zuba garin alkama ta fara tuka tuwon. Da sauri ta fara cewa kai dakata kada ka shigo mana. Wani tsohon zani ne a jikinta da koriyar t-shirt sai dankwalin zanin da ta daure kanta tamau dashi. Hamza bai kula ta ba ya shigo har tsakiyar tsakar gidan tana ta kokawa da dankwalinta tana son bude shi ta rufe jikinta. Wani irin kallo ya bita dashi mai wuyar fassara. Kinga yi aikinki ni ba zama nazo yi ba. Magana nake so muyi ina sauri ne. Fuskarta a turbune tace don kana sauri ko sallamarka ban amsa ba ka fado mana cikin gida. Kuma ko lullubi babu a jikina. Dan karamin tsaki yayi, kwantar da hankalinki baki da abinda zai daga min hankali don na ganki ba mayafi. Maganar ta bata haushi sai ta danne tace ina wuni? Kafin ya amsa ta cigaba da tuka tuwonta. Kallo ya bita dashi yadda take zaune gaban murhu zafin baya damunta. Bazaki bani wurin zama ba? Ko juyowa bata yi ba tace na dauka ba zama kazo yi ba. Can gefe ya sake matsawa saboda wutar ta fara hayaki. Ita kanta Zuhran yana damunta ta fara hawaye da majina. Tasa gefen dankwalinta ta goge fuskar ta cigaba da aiki. Da kyar ya hadiyi yawu saboda gabadaya kyankyaminta ne ya kamashi. Gara yayi abinda ya kawo shi ya fita kafin zuciyarsa ta fara tashi. Ji tayi yace Ke,wai baki da saurayi ne?....ta murguda baki duk da ta juya masa baya ni ba sunana ke ba. Kuma ina ruwanka da samarina. What ever taji ya fada da turanci. A ranta tace ban yafe ba idan ka zagen. Alhaji yace yana so na zo wurinki atleast sau uku kafin a kawo kudi. Za'a tambayeki kafin ranar idan kin amince da auren, ina so kice ba kya sona. Mun gama magana da Izzatu tace kina da saukin kai zaki amince. Izzatu da ya fada ya kara bata haushi. Ko kadan bata son sake jin sunan matar. Kinga ni bana sonki kuma idan kika aureni wahala zaki sha. A tsarina mace daya ta isheni. Tunda bana jin kina da saurayi akwai sakatare na Inuwa zanyi mishi tayinki. Idan ya amince kinga shikenan. Ko ba komai na taimaka miki. Kuma nayi alkawarin yi miki kayan daki idan kin tashi aure. Murmushi kawai Zuhra keyi ta gama tuka tuwon ta rufe tukunyar sannan ta gyara wutar. Wato mutumin nan ya raina mata hankali. Shi iyayensa su yabe shi ita kuma ace bata da kunya. Wai har cewa yake zaiyiwa wani tayinta. Ko na sati ne sai ta aure shi ta bata masa rai daga shi har masoyiyar tasa Izzatu. Da wannan shawarar ta dago kanta amma bata hada ido dashi ba. Tace shikenan abinda ya kawoka? Hamza yace eh ko kudi kike so zan iya biya kice ba kya sona kinji. Wannan karon tamkar mai magiya yake magana. hanyar dan karamin falonsu ta kama. Zanyi tunani a kan maganar, ka gaida gida. Shigewa tayi ta barshi nan a tsaye yana mamakin wai itama ta iya jan aji. Ya kada kansa ya fice daga gidan. Washegari Hamza ya koma gidansu Zuhra. Soro ta fito ta same shi. Yau zama yayi yana lissafa mata irin mawuyacin halin da zata iya shiga muddin ta yarda aka yi auren. Kanta a kasa har ya gama bayaninsa ya juya ya tafi. A waje ya hadu da Baba yana dawowa gida. Yara ne sunfi goma suke biye dashi yana rarraba musu alawa. Hakan ya bawa Hamza sha'awa. Karasawa yayi suka gaisa da Baba cikin ladabi sannan ya tafi. Yau dai ya karewa hannun Baba kallo ya kula yankewa aka yi ba kuturta bace ta cinye yatsun.+ Saboda matsalar office dinsa sai bayan kwana biyu ya sake komawa. Umma tasa tayi kwalliya irin wadda ta saba yi tana ta yabon kyan tilon yarta. Zuhra tace don ma banyi wanka ba Umma ai da sai nafi haka kyau. Umma tace to sakarai sai kin fada da karfi yaji yasan cewa ke kazama ce ko. Bata rai tayi haba Umma ki dena ce min kazama. Baba yace na kile. Ai fa naga alama, to wuce ki tafi kin barshi yana jiranki. Tabarma ta dauka ta fita soron. Kamshin turarensa ya cika wurin. Yau suit ce a jikinsa ruwan toka. Zuhra ta gaishe shi ta sami wuri ta zauna don baya zama akan tabarmar. To yau nayi zuwa uku ina fata kina rike da dukkan abinda nake fada miki. Ya dan jima yana magana sannan ya lura ba saurarensa take ba. Shi ta kurawa ido....ke, keee, KE lafiyarki? Bata dawo hayyacinta ba sai da ya dan tafa hannuwansa a gaban fuskarta. Ajiyar zuciya tayi sannan tace yanzu don Allah kana iya numfashi? Ni bansan haka ake saka abinnan a zahiri ba sai yau. Waige ya fara yi don bai gane kan zancen ba. Tace neck tayil dinka nake nufi. Naga ya shake maka wuya kamar mai shirin rataye kansa. Yanayin maganarta yasa shi yin murmushi. Necktie ake cewa sannan bai shake ni ba. Amma dai baka sakewa ko? Dauri irin wannan akwai ganganci a cikinsa. Dole Izzatu tace yarinyar nan tana da shirme. Yace ni zan tafi ina tunanin jibi Alhaji zai zo. Ki kiyaye abinda na fada miki. Har ya juya sai ya dawo...by the way nayiwa Inuwa maganarki sai dai mun makara. An kusa kai kudin aurensa. Zuhra tace babu komai. Nagode.....yadda yaga kamar ta nutsu yasa ya kwantar da hankalinsa. Dubu goma ya dauko yan dari dari sababbi ya mika mata. Ga wannan ki rike. Nagode ta sake cewa sai kawai ta nade tabarmarta ta shige ciki. Mayar da kudinsa yayi aljihu yana mamaki da bata karba ba.3 Bayan Isha Baba ya kira Zuhra da Umma. Wani katon littafi ya dauko mai hotunan kayan daki irinsu gado, kujeru da kitchen cabinet masu tsada. Kunsan aikina ba wai ina yin kayan daki na masu kudi bane sosai. To amma na sami wani ya bani aron littafinsa nake son kwaikwayon duk wanda kika zaba zanyi kokari na kwatanta miki irinsa uwata. Atine gashi ki tayata zabe. Hawaye ne mai zafi ya saukowa Zuhra. Tabbas iyaye sun cancanci dukkan girmamawa daga 'ya'yansu. Allah Ka sakawa iyayenmu da alkhairi. Baba ne ya fara gani yace meye haka uwata ta kaina? Da yake Umma ma akwai rauni sai kawai suka hadu suna kuka maimakon ta rarrasheta. Baba ma dai ta maza yayi ya fara musu fadan su dena yi masa kuka. Burina Zuhra tayi aure ta sami mai kula da ita. Sai da shekaru suka zo mana muka haifeki dole nayi murna idan na sami wanda zai tayani kula da Fatima kyauta daga Allah. Zuhra fadawa tayi jikin Baba tana kuka. Ni bazanyi aure ba. Saurin tashe mata baki yayi...kul na sake jin irin haka. Aure ai shine rufin asirin kowa. Zaki yi aure cikin gidan mutumci kuma in Allah Ya yarda zaki kawo min jikoki su zo in basu labarin tabara irin ta babarsu. dariya ta rinka yi. Daga baya suka zabi gado da kujeru ita da Umma. Sai da ta kwanta ne a kan dan gadonta maganar Hamza ta rinka dawo mata. Tabbas da niyarta ta aureshi ta kuntata masa. Don duk zancen da yake mata jinsa kawai take yi. Sun dauketa wata gaula daga shi har matar tasa. To amma maganar Baba ta tsaya mata a rai. Duk shirmenta tana kaunar iyayenta kuma bata son bata musu suna. In Allah Ya yarda bazata wasta musu kasa a ido ba. Idan har baayi auren ba sai dai idan Hamza da bakinsa yace baya so. 27 Bayan kwana biyu Umma ta sanar da Zuhra yau iyayen Hamza zasu zo. Mamansu Hajara ta shigo tayata aiki. Kaji hudu suka soya, Anti Faiza sarkin flour tayi musu cake, meatpie da doughnut. Zuhra ta wanke tsakar gidansu tas dama irin fasassun tiles dinnan ne. Nan da nan wurin ya hau sheki. Bayan ta gama aikin ta hau magiyar a barta taje gidan Hajara. Tunda akayi biki Baba ya kafa mata dokar sai tayi sati baya son yawon gulma. Anti Faiza tace ke da zasu ji ta bakinki ai bai kamata ki fita ba. Kannen Umma biyu suma suna ta zolayarta da matar kanin Baba. Sai bayan la'asar suka watse aka bar Maman Hajara da Umma. Baba ya shigo tare da Malam yace su bakin zasu shigo. Kaninsa da yake aikin masinja ma yazo tunda Alh Nasiru yace indai ta amince to a lokacin zasu bada kudi asa rana. Su Umma daki suka koma bayan an jerawa baki kayan motsa baki. Sai da suka gama barkwancinsu sannan Alh Nasiru ya bukaci ganin Zuhra domin yaji amsarta. Dan karamin falonsu ya shiga tare da Baba. Kanta a kasa ta gaishe shi ya amsa yana mai yabon halayenta. Sannan ya tambayeta domin baya son matsa mata ta auri wanda bata so. Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kai. Ganin haka ya mike suka koma tsakar gida. Ya dubi sauran jamaar wurin. Shirun budurwa alama ce ta amincewarta saboda haka idan duk kun amince ina so asa rana nan da sati hudu. Kowa yayi naam da hakan harda Baba. A take suka bada kudin aure dubu dari aka yi addua taro ya watse. Ranar murna a wurin Baba da Umma ba'a cewa komai. Kudin da aka bayar Baba yace zai ajiye mata zuwa lokacin biki. Kinga ko mijinki bai yarda ki cigaba da saka ba kina da dan abin hannunki. Sannan ku shirya karshen sati zamu je Ajingi. Nan Zuhra ta hau murna zata je wurin Inna. Yinin ranar Hamza suna ta meeting da maaikatansa akan yadda zasu samu su karasa biyan kudin da turawan ke binsu kamfanin ya dawo mallakin Hamza shi kadai. Ya sanar dasu dole su zage damtse ayi aiki sosai domin su fitar da kudin kafin watanni shidan da aka basu su cika. Suna fitowa gidansu ya tafi saboda amsa kiran Alhaji. Yasan zancen bazai wuce Zuhra taki amincewa ba ayi masa fadan bai yi abinda ya dace wurin jan raayinta ba. Mama bata gida lokacin da yaje sun fita da Nura. Da Hajiya suka gaisa kafin ya karasa wurin Alhaji. Fuskarsa a sake ya amsa gaisuwar Hamza sannan yace ya kamata ka fara shiri tunda sati hudu kawai aka sa rana. Idan baka son hadasu gida daya sai ka gyara mata tsohon gidanka. A dan daburce Hamza yace wa zan gyarawa? Alh Nasiru yayi murmushi amaryarka mana. Yadda gabansa ya fadi bai san lokacin da yace amincewa tayi??? Alhaji yace ba haka kaso ba ko. Ai nasani Babana. To sai ka dau hakuri yarinya tana neman albarkar iyaye. Hamza yace Alhaji nima ina nema. Don Allah a janye zancen nan. Ko Nura ka aurawa ita. Dariya Alhaji yayi shi kuwa Hamza kamar yayi kuka yace yarinya ce karama. Ya za'ayi na zauna da ita? Alhaji ya gyara zamansa. Kaga ba jan zance nake so muyi ba. Aure ne sai an daura in sha Allah. Ni ban dora maka nauyin komai ba sai sadaki. Tunda na fika son ayi auren na dauke maka duk wata hidima da zata taso. Rasa bakin magana yayi yana kallon mahaifinsa. Mama ce ta shigo tare da Nura da su Hamida suna rike da wasu jakunkuna masu kyau. Seti ne guda shida, tace Alhaji kaga wadanda muka samu. Sai ta kalli Hamza, a'a kaga babban dana angon Zuhra. Ta tura masa daya daga cikin jakankunan. Kaga wannan sunyi kyau? Yanayin fuskarsa bazai fasaltu ba yace Mama harda ke? Nice ma kan gaba ta bashi amsa. Uhm Alhaji gobe da safe zamu je da su Jidda kasuwar, kasan hada lefe akwai cin lokaci. Yana shan furarsa yace Allah Ya kaimu. Share Hamza suka yi tamkar baya wurin. Tunaninsa daya yadda zai fadawa Izzatu plan dinsu bai karbu ba. Washegari Hamza ya koma gidansu Zuhra. Soro ta fito ta same shi. Yau zama yayi yana lissafa mata irin mawuyacin halin da zata iya shiga muddin ta yarda aka yi auren. Kanta a kasa har ya gama bayaninsa ya juya ya tafi. A waje ya hadu da Baba yana dawowa gida. Yara ne sunfi goma suke biye dashi yana rarraba musu alawa. Hakan ya bawa Hamza sha'awa. Karasawa yayi suka gaisa da Baba cikin ladabi sannan ya tafi. Yau dai ya karewa hannun Baba kallo ya kula yankewa aka yi ba kuturta bace ta cinye yatsun. Saboda matsalar office dinsa sai bayan kwana biyu ya sake komawa. Umma tasa tayi kwalliya irin wadda ta saba yi tana ta yabon kyan tilon yarta. Zuhra tace don ma banyi wanka ba Umma ai da sai nafi haka kyau. Umma tace to sakarai sai kin fada da karfi yaji yasan cewa ke kazama ce ko. Bata rai tayi haba Umma ki dena ce min kazama. Baba yace na kile. Ai fa naga alama, to wuce ki tafi kin barshi yana jiranki. Tabarma ta dauka ta fita soron. Kamshin turarensa ya cika wurin. Yau suit ce a jikinsa ruwan toka. Zuhra ta gaishe shi ta sami wuri ta zauna don baya zama akan tabarmar. To yau nayi zuwa uku ina fata kina rike da dukkan abinda nake fada miki. Ya dan jima yana magana sannan ya lura ba saurarensa take ba. Shi ta kurawa ido....ke, keee, KE lafiyarki? Bata dawo hayyacinta ba sai da ya dan tafa hannuwansa a gaban fuskarta. Ajiyar zuciya tayi sannan tace yanzu don Allah kana iya numfashi? Ni bansan haka ake saka abinnan a zahiri ba sai yau. Waige ya fara yi don bai gane kan zancen ba. Tace neck tayil dinka nake nufi. Naga ya shake maka wuya kamar mai shirin rataye kansa. Yanayin maganarta yasa shi yin murmushi. Necktie ake cewa sannan bai shake ni ba. Amma dai baka sakewa ko? Dauri irin wannan akwai ganganci a cikinsa. Dole Izzatu tace yarinyar nan tana da shirme. Yace ni zan tafi ina tunanin jibi Alhaji zai zo. Ki kiyaye abinda na fada miki. Har ya juya sai ya dawo...by the way nayiwa Inuwa maganarki sai dai mun makara. An kusa kai kudin aurensa. Zuhra tace babu komai. Nagode.....yadda yaga kamar ta nutsu yasa ya kwantar da hankalinsa. Dubu goma ya dauko yan dari dari sababbi ya mika mata. Ga wannan ki rike. Nagode ta sake cewa sai kawai ta nade tabarmarta ta shige ciki. Mayar da kudinsa yayi aljihu yana mamaki da bata karba ba.3 Bayan Isha Baba ya kira Zuhra da Umma. Wani katon littafi ya dauko mai hotunan kayan daki irinsu gado, kujeru da kitchen cabinet masu tsada. Kunsan aikina ba wai ina yin kayan daki na masu kudi bane sosai. To amma na sami wani ya bani aron littafinsa nake son kwaikwayon duk wanda kika zaba zanyi kokari na kwatanta miki irinsa uwata. Atine gashi ki tayata zabe. Hawaye ne mai zafi ya saukowa Zuhra. Tabbas iyaye sun cancanci dukkan girmamawa daga 'ya'yansu. Allah Ka sakawa iyayenmu da alkhairi. Baba ne ya fara gani yace meye haka uwata ta kaina? Da yake Umma ma akwai rauni sai kawai suka hadu suna kuka maimakon ta rarrasheta. Baba ma dai ta maza yayi ya fara musu fadan su dena yi masa kuka. Burina Zuhra tayi aure ta sami mai kula da ita. Sai da shekaru suka zo mana muka haifeki dole nayi murna idan na sami wanda zai tayani kula da Fatima kyauta daga Allah. Zuhra fadawa tayi jikin Baba tana kuka. Ni bazanyi aure ba. Saurin tashe mata baki yayi...kul na sake jin irin haka. Aure ai shine rufin asirin kowa. Zaki yi aure cikin gidan mutumci kuma in Allah Ya yarda zaki kawo min jikoki su zo in basu labarin tabara irin ta babarsu. dariya ta rinka yi. Daga baya suka zabi gado da kujeru ita da Umma. Sai da ta kwanta ne a kan dan gadonta maganar Hamza ta rinka dawo mata. Tabbas da niyarta ta aureshi ta kuntata masa. Don duk zancen da yake mata jinsa kawai take yi. Sun dauketa wata gaula daga shi har matar tasa. To amma maganar Baba ta tsaya mata a rai. Duk shirmenta tana kaunar iyayenta kuma bata son bata musu suna. In Allah Ya yarda bazata wasta musu kasa a ido ba. Idan har baayi auren ba sai dai idan Hamza da bakinsa yace baya so. 27 Bayan kwana biyu Umma ta sanar da Zuhra yau iyayen Hamza zasu zo. Mamansu Hajara ta shigo tayata aiki. Kaji hudu suka soya, Anti Faiza sarkin flour tayi musu cake, meatpie da doughnut. Zuhra ta wanke tsakar gidansu tas dama irin fasassun tiles dinnan ne. Nan da nan wurin ya hau sheki. Bayan ta gama aikin ta hau magiyar a barta taje gidan Hajara. Tunda akayi biki Baba ya kafa mata dokar sai tayi sati baya son yawon gulma. Anti Faiza tace ke da zasu ji ta bakinki ai bai kamata ki fita ba. Kannen Umma biyu suma suna ta zolayarta da matar kanin Baba. Sai bayan la'asar suka watse aka bar Maman Hajara da Umma. Baba ya shigo tare da Malam yace su bakin zasu shigo. Kaninsa da yake aikin masinja ma yazo tunda Alh Nasiru yace indai ta amince to a lokacin zasu bada kudi asa rana. Su Umma daki suka koma bayan an jerawa baki kayan motsa baki. Sai da suka gama barkwancinsu sannan Alh Nasiru ya bukaci ganin Zuhra domin yaji amsarta. Dan karamin falonsu ya shiga tare da Baba. Kanta a kasa ta gaishe shi ya amsa yana mai yabon halayenta. Sannan ya tambayeta domin baya son matsa mata ta auri wanda bata so. Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kai. Ganin haka ya mike suka koma tsakar gida. Ya dubi sauran jamaar wurin. Shirun budurwa alama ce ta amincewarta saboda haka idan duk kun amince ina so asa rana nan da sati hudu. Kowa yayi naam da hakan harda Baba. A take suka bada kudin aure dubu dari aka yi addua taro ya watse. Ranar murna a wurin Baba da Umma ba'a cewa komai. Kudin da aka bayar Baba yace zai ajiye mata zuwa lokacin biki. Kinga ko mijinki bai yarda ki cigaba da saka ba kina da dan abin hannunki. Sannan ku shirya karshen sati zamu je Ajingi. Nan Zuhra ta hau murna zata je wurin Inna. Yinin ranar Hamza suna ta meeting da maaikatansa akan yadda zasu samu su karasa biyan kudin da turawan ke binsu kamfanin ya dawo mallakin Hamza shi kadai. Ya sanar dasu dole su zage damtse ayi aiki sosai domin su fitar da kudin kafin watanni shidan da aka basu su cika. Suna fitowa gidansu ya tafi saboda amsa kiran Alhaji. Yasan zancen bazai wuce Zuhra taki amincewa ba ayi masa fadan bai yi abinda ya dace wurin jan raayinta ba. Mama bata gida lokacin da yaje sun fita da Nura. Da Hajiya suka gaisa kafin ya karasa wurin Alhaji. Fuskarsa a sake ya amsa gaisuwar Hamza sannan yace ya kamata ka fara shiri tunda sati hudu kawai aka sa rana. Idan baka son hadasu gida daya sai ka gyara mata tsohon gidanka. A dan daburce Hamza yace wa zan gyarawa? Alh Nasiru yayi murmushi amaryarka mana. Yadda gabansa ya fadi bai san lokacin da yace amincewa tayi??? Alhaji yace ba haka kaso ba ko. Ai nasani Babana. To sai ka dau hakuri yarinya tana neman albarkar iyaye. Hamza yace Alhaji nima ina nema. Don Allah a janye zancen nan. Ko Nura ka aurawa ita. Dariya Alhaji yayi shi kuwa Hamza kamar yayi kuka yace yarinya ce karama. Ya za'ayi na zauna da ita? Alhaji ya gyara zamansa. Kaga ba jan zance nake so muyi ba. Aure ne sai an daura in sha Allah. Ni ban dora maka nauyin komai ba sai sadaki. Tunda na fika son ayi auren na dauke maka duk wata hidima da zata taso. Rasa bakin magana yayi yana kallon mahaifinsa. Mama ce ta shigo tare da Nura da su Hamida suna rike da wasu jakunkuna masu kyau. Seti ne guda shida, tace Alhaji kaga wadanda muka samu. Sai ta kalli Hamza, a'a kaga babban dana angon Zuhra. Ta tura masa daya daga cikin jakankunan. Kaga wannan sunyi kyau? Yanayin fuskarsa bazai fasaltu ba yace Mama harda ke? Nice ma kan gaba ta bashi amsa. Uhm Alhaji gobe da safe zamu je da su Jidda kasuwar, kasan hada lefe akwai cin lokaci. Yana shan furarsa yace Allah Ya kaimu. Share Hamza suka yi tamkar baya wurin. Tunaninsa daya yadda zai fadawa Izzatu plan dinsu bai karbu ba. Abinda yaji tsoro ne ya faru. Izzatu tayi kuka har ta gaji. Rokon Hamza take yi ya rufa mata asiri kada yayi auren. Tun yana rarrashinta har ransa ya baci da tace duk gidansu babu mai kaunarta. A hasale yake kallonta ke har kina da bakin cewa ba'a sonki Izzy? You caused everything. Lokaci guda kin lalata farincikin gidan nan. Ganin ya soma fada yasa ta rungumeshi. Am sorry baby. Na yarda kayi auren amma bayan lokaci kadan sai mu nemi dalilin da zaisa ka saketa. Jinta kawai yayi. Shi da Alhaji ya kafa masa sharadin indai ba da dalilin da ya sabawa shariah ba bai yarda ya saki Zuhra ba.+ A bangaren su Zuhra kuwa shirye shirye ya kankama. Makota da abokan arziki kowa yana son gwada bajintarsa wurin bikin tilon yar baban yara. Gudunmawar kudi suka rinka bawa Mal Bashir sai da ya tashi da dubu dari biyu da talatin. Shi kanshi ba karamin mamakin wannan karramawa ta mutanen unguwarsu yayi ba. Anas da Sani ma ba'a barsu a baya ba domin kuwa gas cooker karami suka kawo. Baba yayi murna da godiya sosai. Haka Umma ta rinka shiga gida gida tana godiya itama. Zuhra taje gidan Hajara a nan suke nasu tsarin bikin duk da ba damunta yayi ba don tasan wahala zata sha kawai. Hajara tace wato Zuhra da gaske kike da kika ce idan kika tashi aure sai munyi mamaki. Gashi zaki auri dan gayu dan boko. Wallahi ki dage sosai tunda yana da mata. Zuhra tayi dariya wace irin dagewa kuma. Ai kawai indai zasu bani abinci naci na koshi to suje can su karata. Sahabi da yake daki ya fito ba shiri. Amma dai Zuhra wasa kike ko? Tace da akayi me fa? Maganar da kika fada yanzu nake nufi. Yaushe zaki ce abinci zaki je ci. Wuri ya samu ya zauna yana karanta mata yadda zata yi a gidan miji. Hajara sai dariya saboda Zuhra rufe kanta tayi da mayafi. Irin wannan bayani na Sahabi yafi karfinta. Shi kuwa ya dauketa kanwarsa ne tunda duk unguwarsu daya. An kawo lefe akwati shida da kit. Komai Alhaji ne ya siya. Makota da yan uwa suna ta san barka. Washegari Baba yayi shatar mota suka dauki kayan suka wuce Ajingi. Nan ma kowa yace Zuhra tayi goshi. Yan uwanta suka shiga hada mata abubuwan da zata gyara kanta. Yi kawai take don kada a gane auren da matsala. Cikin wannan lokacin ko text bai taba hada Hamza da Zuhra ba. Har Umma sai da tace naga kwana biyu shiru yaron nan. Zuhra tayi yake muna waya kullum Umma. Wani aiki ne yake son karasawa kafin bikin. Umma tace to Allah Ya bada saa. Alhaji ya sake tuntubar Hamza inda zai ajiye Zuhra. Takardun tsohon gidansa ya dauko ya mikawa Alhaji yace na riga na gama komai ya zama mallakin Nura. A sabon gidan akwai dakuna sai ta zauna a cikin daya. Alhaji yasa masa albarka sannan ya tura Mama ta gano dakin da za'a bawa Zuhra. Dakina ne babba a kasa da toilet a ciki. Mama tace sam amarya ma a sama zata zauna. Dakunan saman uku ne har an gama jera kayan su Khalifa a ciki. Bisa umarnin Alhaji dole aka dawo dasu kasa ba da son ran Izzatu ba aka sabonta fentin. Katon daki ne kamar na Izzatu da toilet. A ciki aka jerawa Zuhra gadonta daga wani gefe da yayi dan tudu. Dayan gefen kuma kujerunta da su tv. Mama tace kuma lallai ayi kitchen kabinet a daya daga cikin dakunan kasan saboda a raba musu kitchen. An fara biki cikin kwanciyar hankali. Baba yana ta yabon Hamza saboda yana yawan kiransa a waya su gaisa. Hakan yasa suka cigaba da tunanin komai lafiya tsakaninsa da Zuhra. Anti Faiza kuma ta sake ja mata kunne akan tayi shiru da bakinta. Sannan tayi mata nasiha akan kwalliya da tsafta. Ni girar nan da kike ja ce bana so Zuhra. A shagwabe tace nufinki bana yin kyau Anti Faiza. Kinsan ni gaskiya zan fada miki. Bata miki kyau don ba iyawa kika yi ba. Kuma babu ruwanki da Izzatu ki kama kanki kinji ko. Zuhra ta gyada kai. Kinga yadda iyayensa suka tsaya miki sosai. Ina so ki kyautata musu daidai gwargwado. Babu fitsara ba rashin kunya. Nagode Anti Faiza in sha Allah zan kiyaye. Anyi kamun Zuhra a unguwarsu washegari alhamis suka tafi Ajingi. Jumaa bayan masallaci aka daura auren Arch Hamza Nasir Hamza da Fatima Bashir Ajingi. Kai ka dauka auren yar wani maikudi ake yi saboda yadda mutane suka zo. Asabar da safe suka dawo kano aka fara shirin kai amarya. Jikin Zuhra a sanyaye tunda aka daura auren. Shikenan zata bar iyayenta ta zauna da mutumin da babu soyayya a tsakaninsu. Ba'a tashi kuka ba sai da motocin daukar amarya suka zo. Aka rasa yadda zaayi a raba Zuhra da Umma. Gabadayansu kuka suke yi tamkar sun rabo kenan. Baba ya shigo yana fadan sun bar mutane a waje. Sai dai Zuhra na rungumeshi ya soma hawaye. Daki yaja hannunta suka koma. Yana kuka yana mata nasiha....uwata ki rinka tsafta kinji ko, ki rike Allah da ManzonSa SAW komai zaizo miki da sauki. Ki rinka taimakon mijinki. Kuma banda katuwar loma a gaban miji. Murmushi tayi hade da kuka ta sake fadawa jikinsa. Baba wa zaku rinka gani a gidan nan idan na tafi? Umma ce ta bata amsa bayan ta fyace hanci cikin yaran Yaya Shafiu matarsa tace na dauki duk wadda nake so. Baba ya dauko wata leda ya damka mata. Ga wannan dubu hamsin ne. Cikin kudin da na samu ne. Zan ajiye miki sauran. Ki rinka amfani dashi. Allah Yayi miki albarka. Basu fito ba sai da Malam babansu Hajara yazo ya buga kofar. Haka suka tafi tana ta rusa kuka ita da Hajara. Anti Faiza tace gulmammu duk wadda bata son auren sai mu koma da ita. 29 Idan kaga dakin Zuhra baka ce na yar Mal Bashir kafinta bane. Tabbas duk dakunan gidan sunfi nata kaya masu kyau da tsada. To amma itama nata iyayen sunyi kokari sosai. Gida ya cika da yan kawo amarya. Izzatu ita kadai ce a daki dama ita ba mai rakice rakicen kawaye bace. Daga ita sai 'ya'yanta. Duk da tasawa ranta bazata kula Zuhra ko tayi kishinta ba sai da tayi kuka da aka shigo ana guda. Adabiyya da Hamida sunfi kowa rawar kafa Yaya yayi amarya. Hakuri da nasiha aka sake yi mata sannan suka tafi. Hajara da wasu yan uwanta ne karshen tafiya bayan sun sake gyara mata daki. Tashi tayi ta cire mayafin jikinta saboda su hudu ne kawai a dakin. Hajara tayi saurin mayar mata. "Abinda ake son amarya da jan aji. Kin wani cire mayafi, idan wasu suka sake shigowa fa." Sake cire mayafin tayi "ke kyaleni nasha iska. Da zafin gari zanji ko na rabuwa dasu Umma." Tana magana idanunta suka cika da hawaye. Hajara ta ja hannunta suka koma kan gadon. Sake gyara mata dauri tayi aka fesa turare."to mu zamu tafi amarya. Kada ki tashi nasan ango na hanya. Kuma ki dena kukan su Umma haka. Irin haka sai yaga kamar auren dole aka yi muku. A zuciyarta Zuhra tace meye maraba. A zahiri kuwa godiya tayi musu suka tafi. Sai da taji dakin tsit ta tashi tana leka ko ina. Wurin yayi kyau sosai ga kamshin turaren wutar da kanwar Umma ta hada mata. A hankali ta bude kofar toilet ta shiga. Wani murmushu tayi. Irin wannan bandaki kamar a gidan shugaban kasa. Ta mika hannu sink taga ruwa ya fito tun kafin ta kunna famfon. Zabura tayi da gudu zata fita don a zatonta famfon ya lalace ne , kada ace ita ta lalata. Ko da ta juyo sai taga ruwan ya dauke. Gabanta na dukan uku uku ta sake komawa tana mika hannu saman zata kunna sai taga bai sake fitowa ba. Har tayi ajiyar zuciya ta sake saka hannu a wurin fitar ruwa sai gashi ya sake fitowa. Fita kawai tayi ta rufe toilet din. Allah Yasa tayi sallar Isha. Dama nafila take son yi, sai ta hakura. Tun tana jira ko angon nata zai shigo har ta fitar da rai. Dama bata sa a ka ba. Wuri ta samu a tsakiyar gadon tayi kwanciyarta ko kaya bata chanja ba. Bata dade ba bacci mai nauyi yayi gaba da ita. Hamza bai shigo gidan ba sai shadaya da rabi na dare. Tun kayan jikinsa na daurin aure bai dawo gida ba. Babbar rigarsa da hula duk a hannu ya shigo dasu ya hadu da Tala tana ta gyara gidan. Ita kam dole a yaba mata wurin tsafta. A gajiye yake sosai, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya haye sama. Sai da yaji ba dadi da ya kalli kofar dake hagun dakinsa. Wai matarsa ce a ciki. Ko alamar zuwa baiyi ba. Kofar dakin Izzatu ya taba yaji bata rufe ba. Muryarta a shake alamar taci kuka yaji tace "Waye?" Shiga yayi ta taso da sauri ta rungume shi tana kuka. Bai hanata ba sai da tayi shiru don kanta. "Ina su Nana?" Ya tambaya lokacin da yake cire takalmansa. "Suna sabon dakinsu. Tala zata rinka duba min su." Yadda take maganar kasan har yanzu tana bakin cikin canza musu daki da aka yi. Kiss Hamza yayi mata a kumatu." Goodnight Izzy. Kije ki kwanta" Ya juya zai fita. Kansa ke ciwo kamar ya tsage. Yau baici wani abin kirki ba tun safe. Yana son tambayar Izzatu amma yasan idan bata da nutsuwa girki ma baya gabanta. Saurin biyoshi tayi. Ta rike masa hannu" Don't tell me wurin Zuhra zaka kwana". Hannun nata ya saki." No, dakina zani. Na gaji kema ki kwanta haka" Kallon tuhuma take masa." Are you sure?". Kai ya gyada mata. Baya son magana saboda yadda kansa ke sarawa "Ko nazo mu kwana? Ina fargabar ranar da zaka kwana dakin yarinyar nan. Zan iya mutuwa saboda kishi." Ganin baya son magana yasa ta kyale shi. Tasan bazai fadi magana ba yaki cikawa. Bayan ya tafi itama sake gyara jikinta tayi tabi bayansa. Da ya tambayeta abinci tace babu amma bari tayi sauri ta dafa masa wani abin. Jallop din taliya tayi masa. Kafin ta gama yayi wanka. Abinci yaci ya dan zauna ya fada masa. Suka kwanta shi da Izzatunsa. Ba wata hira tsakaninsu domin kuwa akwai abinda ke damunsa.

0 Comments