ZUCIYA CHAPTER7 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUCIYA CHAPTER7

ZUCIYA CHAPTER7

- - Post a Comment
ZUCIYA CHAPTER 7
Shiru Ashraf yai a mota bayan sun fito daga Asibiti, tunani yake mai zurfi ina zai sa Nafi a makaranta? A kalaa dai shekarunsu d'aya da Little banbancinsu dai Little nada d'an jiki sai dai Nafi siririyace sosai sai tsayi, ko alphabet bata iya ba. Ya d'an juya kai, ina zai sata? Yarinyar nan dai bamai ansarta ko Js1 ne to a hakan ma Js1 ya mata kankanta saboda ita ba yarinya bace, yai d'an karamin tsaki lalai Malam dama wahala ya d'auramai. Sam baiji sanda Driver yake ta cemai Oga ina zamu? Can bayan ya gama tunani ya kalli Adamu yace "Adamu me muke jira kuma? " Adamu ya dan saki fuska yace " tun d'azu nake tambayar inda zamu banji kace komai ba. " Tsaki ya kara ja sannan yace "Mu tafi gida, tunani ne suka min yawa. " A gida kam kan kace me kowa yasan abinda Ashraf yama Aneesa akan wasiyyar da za'a bata, duk ta yad'ashi tana fadama mutane tana kukan sakalci, anyi carko carko a waje kowa nata fada'an albarkacin bakinsa, sai dai kaf Ashraf suke bama laifi gani suke ai ta cancanci abata ta gani, dan ankusa d'aura musu aure. Mumy kam tana d'aki abin duniya ya dameta itakam ba abinda ta tsana irin taji ance Ashraf yayi abu. Tun da suka shigo Ashraf ya fuskanci da matsala sai dai har sukai parking ya fito bai nuna komai ba, ba kuma yasan ya san meke faruwa, direct hanyar banharensa ya nufa, suna daga tsaye ko kallan inda suke baiyi ba, Ga Aneesa da su Umma suma daga d'an gefe. Asim ne cikin kuluwa yace " Ashraf bakaga dan kai muke tsaye ba? " Kallansu yai ya saki wani mugun smiling na rainin hankali yace " Da alama tsayuwar domin ni tana muku dadi ne. " Ya ci gaba da tafiyarsa, a xabure Asim da kannansa suka matso inda Ashraf yake, Asim ya tafi a zuciye zai shake Ashraf, saura kiris ya karaso Ashraf yace " D'an daba muka samu a gidan? Ka tabbatar kasan me kake shirin yi kafin a samu matsala. " Jin haka yasa kannensa sukai saurin tare Asim d'in shikam sai hucci yake, ya nuna Ashraf yace " Dan kut........ Kai har ka isa kasa kanwata kuka?" Kallan inda su Umma suke yai sai a lokacin ma ya kula da su, cikin zuciyarshi kwarai takaici ya lulube shi sai dai murmushi ya sake saki yace " Kanwarka? Sai kai azama ka bata hakuri sannan kai gaggawar yi mata kashedi akan zubar da hawaye akan wani bare. " Ran Asim ne ya kara dugunzuma, yanzu kam har kannansa abin ya kular dasu, Aneesa ta matso, Ashraf ya d'an buga mata wani kallo sannan ya kalli Asim fuskarsa a sake sosai kamar ba'amai komai ba yace " Ya? Gatannan sai ka tambayeta me baren nan ya mata. " Asim ya kalli Ashraf cikin masifa yace " kai dan rashin mutunci baza ka bata wasiyyar mahaifinka ba? Ko dan tsabar mugunta rikewa zakai? Oh andaiji jiki uba ya mutu ya bar wasiyya amma d'a ya kasa......" Kasa karasawa yai saboda ganin Ashraf yana murmushi harr hakoransa suka fito, cikin tsananin takaici ya kalli Ashraf yace " kut! Dariya ma na baka? " Ashraf ya juya kai tare da shafar kasan kansa da hannun da baya mai ciwo yace " Uba? Sai kuma ka manta wannan Uban nawa ne ko? Sannan banaji a wasiyyarsa yace inba matar da ban aura ba ko? " Aneesa ta matso kusa dashi tace " Yaya?" Matsawa yai daga kusa da ita baice musu komai ba ya juya ya fara tafiya, sai dai abin mamaki kasa cemai komai sukai sai Aneesa data bishi da sauri, tana kiranshi. Ko Kallanta baiyi ba, ransu Umma ya sake b'aci, yana shiga falonsa ta bishi itama tace "Hubby? " Matsowa ya farayi inda take harta isa jikin bango yasa hannunsa ya matseta har sai datai dan kara, sannan yace " wlh ki shiga hankalinki, inkikai wasa Wlh kinji na rantse duk sanda nake miki sai in ajiye maganar auranki, kinfi kowa sannin ni Ashraf nafi karfin mace ta wulakantani ko ta juyani. " saketa yai sannan yai d'akinsa. STORY CONTINUES BELOW Da kallo ta bishi dashi, wani mugun tsoro ne ya shigeta,A tsorace tai waje. Ashraf kam yana shiga d'aki ya durkushe agun, kafad'arsa har kasan hannunsa banda azabar zafi ba abinda yake ji, d'ayan hannun yasa da niyyar sa magani, sai dai ina jin gun yai ya kara kumbura, ya tuna abinda likita yace mai. "Ashraf a ina ka bugu haka? " Da mamaki yace" ni ban bugu ba kawai da daddare ciwo ya tashi min." Likitan yai shiru can yace " A 'yan kwanakin nan baka bugu ba? " Ashraf ya kalleshi yace " na dai d'an sanu karamin accident to daga nan ina d'anjin gun ba dadi to amma bawai ciwi ya kemin ba. " Likitan yai d'an ajiyar zuciya yace " Ashraf ya akai haka? Me yasa bakazo checkup ba bayan abin? " Ganin bashida niyyar magana yasa ya mik'e ya bashi magunguna, sannan yace " a sa tsuma a ruwan zafi a dinga matsewa ana gasa ma gun, sai a shafa wannan. " Asharf ya amsa, yacigaba "wannan kuma na had'iya ne. " Nan ya bashi kud'inshi Ashraf ya mike, har ya fara tafiya likitan yace " Ashraf ka tabbatar an gasa ma sannan karkai amfani da jikinka sosai. " Nan yai gaba, ta ina zai iya gasa gun da kansa? Gashi sunyi fada da waccan yarinyar, shikuma kaf mazan gidan bayaji akwai wanda zai iya kira. Wayarsa ya d'aga ya dannan number Little yana fatan Allah yasa ta dawo. Daga can b'angaren Little wacce ke kwance batajin dadi ta daga, bayan tagaisheshi bai amsa ba kawai yace "little kizo yanzu. " Abinda ya fada kenan ya kashe, little wacce da alama ciwon mara take ganin yanda take a durkushe sai dai ita batasan meke damunta ba, ta kalli Nafi wacce ke xaune kusa da ita duk ta rikice kamar ita take ciwo. Tace "Nafi dan Allah jeki yayane ke kirana nikuma kinga cikina murd'amin yake. " Nafi ta kalleta daa idanunta da sukai raurau tace " taya zan tafi in barki? " Little tace " naji muryar yayan ma kamar......" Ai Nafi da sauri ta mike batama jira karashen zancen ba tai waje da sauri, ganin saurin bai mata ba ga ba mutane agun yasa tadan sa gudu, tabbas ciwonsa ne ya motsa abinda kawai tasa a ranta kenan. Sam bata kula da Asim ba wanda ke kokarin shawo kwana ita kuma zata mike, dayake gudu takeyi iya karfinta kuwa ta bangaje shi, Asim ya juyo cikin tsananin mamaki ganin wani kwararen ne? Nafi kam jikinta ya fara tsuma ta kalleshi a tsorace tace " Yahkuri yaya dan Allah. " Asim ya d'ago da niyyar masifa, sai dai me? Can ya ganta ta mai nisa sai sauri take, ta sani bazai kyaleta ba sai dai yanzu abu d'aya ne a gabanta ba kuma taji akwai abinda zai tsayar da ita. Tana murd'a kofar tajishi a bud'e nan ta shiga ta fara sallama, jin shiru cikin tsoro kawai ta dannu ciki, baya falo hakan yasa ta wuce d'akin shi. A zaune yake a kasa ya kifa kansa akan gado, ba riga a jikinsa sai dogon wando hakan yasa Nafi ta juya baya da sauri, a hankali tace "Yaya ga...... " Yanda yakeji yasa bai bari ta karasa ba ya katseta "Little yi sauri ki d'au roba a toilet ki taro ruwan zafi ki sa tsuma a ciki kizo ki dinga matsewa kina gasamin gun nan. " Nafi ta juyo a hankali tana san cemai ba little bace tace " Ya.... " "Little wuce mana" Jiki a sanyaye Nafi ta wuce toilet yanzu ta iya kunna famfo ta kuma san inda ruwan sanyi dana zafi yake, nan ta tara a roba ta saka towel karami dake rataye a ban d'akin ta fito, ganin yanda ya kifa kansa ko d'agowa baiyi ba yasa tasan yanajin zafin gurin, kallan gun tai taga ya kara tashi ba kamar da safe ba, idanunta ne suka fara cicikowa, ta karasa a hankali tai kneel down ta bayansa ta fara matsewa tana gasa mai gun, dun sanda tasa sai taga ya d'an motsa kad'an. Kamar a jikinta takejin ciwo nan, intaga ya motsa sai ta runtse ido. Asim kam wanda ransa yakai kololuwar tashi ya tsaya ya d'auka yanzu zata dawo yaci mutuncinta, jin shiru yasa yabi bayanta a kufule. Bud'e kofar yai a zuciye yai ciki, me zai gani????? Me kuma idanunsa suke gane mai??????? Tofah! Babbar magana........ ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ A b'angaren su Datti kam haka sukai ta yawo suna neman taimako, kayan da maman hanne tazo dasu suma sai siyarwa tai. Da kyar suka hada kudin mota suka koma Gwaram..... ¤¤¤¤¤¤¤ Shikam d'an litti ya musu bayani har ya gaji amma ina... Sunce dole sai ya fada musu wanda ya sani yazo yayi bailing shi. D'an litti yace " ku nemo min Ashraf. " Officer yace " Ashraf wa? A ina yake? Meye number wayarsa? " To fa! Da masifa D'an litti yace " nidai ba na fada muku ba? Sunanshi Ashraf a kuma kano yake. " Officer yace " me kake nufi to? So kake mu shiga kano mu fara neman masu suna Ashraf ko me? " D'an litti takaici ya kamashi ya zauna a cell d'in kamar yasa ihu, gashi sunce inya sake musu turancin nan nasa sai sun fasamai kai........ A tsorace Nafi ta mike gabanta sai fad'uwa yake, shikam gogan ko mikewa baiyi ba sai cewa dayai "Little mikomin rigata a kan gado. "+ Nafi ta mikomai sannan ta fito daga d'akin da sauri tare da ja mai kofar, dan ta kula kamar bayasan asan bashida lafiya. Tana fita falo Asim ya karaso tare da jan hannunta da karfin tsiya, Nafi ta d'an turje sai hawaye da takeyi. Asim ya haska mata wani wawan mari yace " banza karuwa, a ido kamar bakauyiya ashe kinfi karuwai iya iskanci. " Nafi ta shiga girgiza kai hawaye na zubo mata. Kofa aka bud'e, mamaki ne ya kama Ashraf ganin Nafi, sai dai bai bari mamakin ya fito fili ba cikin isa ya karaso ya sa hannu ya rike hannun da Asim ya rike. Asim ne ya kalleshi cikin masifa yace " Me kenan? Kazo karema karuwarka ne? " Nafi kam kanta na kasa, kunyar Ashraf duk ta gama rufeta ta sani sarai bai san ita bace sai yanzu. Ashraf ya kalli Asim yace " Saketa ko? " Nafi kam hannunta sai zugi yake yi, Asim yace " bazan saketa ba sai munje gaban kawu ta sanar mai abinda kai da ita kuke aikatawa. " Ashraf yai wani murmushi ya kalli agogo karfe 6 na yamma, sannan ya kalli Asim yace " ai banaji sai ta bika wajen isar da sakon kai kad'ai ma ya wadatar kaje ka sanar. " Asim ya kara cika baki da takaici yace " Me kake nufi? " Ashraf ya kalli Asim ya mai alama da ya sakar mata hannu, cikin takaici Asim ya saketa, Ashraf ya kalleta yace " wuce ko? " Nafi ta kalleshi idanunta sun cika da kwalla tanasan bashi hakuri sai dai bataga fuska ba, da kai ya mata alama ta wuce mana, jiki a sanyaye tai gaba tana yi tana waigensa. Tana fita Ashraf ya kalli Asim yace " D'an sako mai kake jira? " "d'an sako? Nine d'an sakon? " Ashraf yai wani murmushi yace " Au na d'auka danace kaje ka sanar ai zaka wuce da sauri ka gurfana agaban kawu ka sanar mai. " A zuciye Asim ya kama wuyan Ashraf cikin masifa yace " Ni kake fada ma haka? " Ashraf yad'an juya ido kad'an yace " inmu uku ne to dana ukun nake." Ya ja jikinsa ya koma d'aki dan yin alwala. Asim ya naushi iska cikin tsananin takaici yai waje jiyake kamar ya lumama Ashraf wuka hankalinsa ya kwanta. Ashraf kam alwala yai sannan ya fito waje. Nafi kam d'aki tai tana kuka, Little ta gani ta fito daga wanka, da sauri Little ta karaso tace " Nafi menene? Wani abin ya miki? Laifi kikama yayan? " Kai kawai Nafi take girgizawa, Little tace " to menene?" Nafi ta kalleta tace" me karuwa yake nufi dan Allah? " Little da mamaki ta kalleta tace " Yayan ne ya fada miki hakan? " Kai ta girgiza alamar a'a sannan tai hanyar ban d'aki da sauri, da alama kalmar bata da dad'i ganin yanda fuskar Little ta canza. Little ta bita da kallo, sannan ta d'au always d'in da Mumy ta kawo mata ta sa, zama tai jiki a sanyaye, waye yacema Nafi karuwa? Asim kam ana idar da sallah ya tari kawu acikin masallacin ma ya fad'amai, ran kawu yayi dubu gurin b'aci, ganin haka yasa Asim ya saki wani murmushin mugunta. STORY CONTINUES BELOW Kawu ya fito cikin tsananin masifa nan yace Ashraf ya biyoshi, duk da kasan zuciyarsa yaji ba dadi sai dai bai nuna ba, nan Asim yabi bayan kawu. A falo Mumy, Umma, Asim da Ashraf ne a zaune sai kawu. Cikin fada kawu ya kalli Ashraf yace " Ashraf meke faruwa? Wani banzan labari nake ji haka? " Ashraf ya kallesu kaf sai dai kafin yai magana Aneesa ta shigo cikin tsananin kishi ta karaso kusa da Ashraf tace " Yaya me kenan? Ni zakaci amana? " Mumy wacce jikinta duk ya mutu dan ta taba ganinta ta fito daga d'akin, tai shiru yau kam batada halin kare Ashraf. Kawu ya daka mata tsawa yace " Aneesa bakida hankali ne? " Ta kalli kawu cikin tsananin takaici tace " Amma Abba..... " Hannu ya d'aga mata hakan yasa Umma ta zaunar da ita a kusa da ita. Ashraf wanda ke zaune sai dai duk masifar mutum bazai tab'a gane meke yawo a ransa ba, sam babu b'acin rai ko farin ciki a tattare dashi. Kawu yace " Asim fad'i me ka gani. " Hankalin Asim a kwance ya sanar da abinda ya gani har da karin cewa wai suna ganinshi suka tura kofar d'akin suka rufe, sai daya dade kafin su fito. Mumy ta runtse ido zuciyarta na wani irin zafi, Umma ta shiga tafa hannu tana salati, itakam Aneesa kafe Ashraf kawai tai da ido jitake kamar zata mutu dan tsananin kishi. Kawu ya kalli Ashraf rai a b'ace yace " Wani irin iskanci ne hakan Ashraf? " Ashraf ya mike daga zaunan da yake ya kallesu ga mamakinsu Murmushi sukaga ya saki, ya jinjina kai sannan yace" tunda maganar Asim itace gaskiya banaji inada abin cewa. " Yana kai nan ya nemi hanyar fita, Umma cikin kuluwa tace "lalai kuwa Alhaji yarinyar nan dole ne ta bar gidan nan, inshi ba'a isa dashi ba ai ita kam karya take. " Ashraf ya juyo ya kalleta sannan ya kalli Aneesa da ta ke zaune kamar gunki ya bud'e baki zaiyi magana yaji Mumy tace " Gaskiya nima Alhaji yarinyar nan bata kwanta min ba." Fuskar Ashraf ce ta canza, yanzu kam ransa ya b'aci sosai, bai damu inkowa ya mai abu ba amma ya tsani yaga mahaifiyarsa na goyon bayan masu mai abu. Kawu ya kalli Asim yace "Ai ba sai anja da tsauri ba, yanzu nan za'a kirata tabar gidan nan. " Ashraf ya had'iyi wani abu sannan ya d'auke idansa daga kan Mumy ya maidashi kan kawu, ya kalli Kawu yace " Kawu banasan abu yaji da zafi sai dai in aka kaini bango banajin kowa zaiji da dadi a gidan nan. " Yana kai nan yai waje, Mumy ta dafa kanta, tanaji Umma na cewa " Allah wadaran nakaa ya lalace, sam yaran nan yafi karfin kowa a gidan nan? " Kawu yai shiru shikansa ya kasa magana. Ashraf kam yana fita ya kira number Habib, bugu biyu Habib ya d'aga yace " Buddy yau kuma soyayyarce ta tashi? " Ashraf yai tsaki yace " Habib dan Allah makarantar Abbanka wace iri ce? " Da mamaki Habib yace "lalai Ashraf kana nufin bakama san me Abbana yake ba? " Ashraf yace " Malam dole ne sai na sani? Ba gashi ina tambayarka baa yanzu? " Habib wanda baiji dadin kalaman Ashraf ba yace " Primaryce da secondary." Ashraf yace " day ce ko boarding?" Day ce mana. Ashraf yad'an shafi kansa sannan yace " Habib boarding school nakesan asa Nafisa gashi kasan tayi girma ba ilimi na rasa ya zanyi. " Habib yai shiru can yace " karka damu Aminin Abba matarsa itace principal ta makarantar kwana dake nan minjibir, sai a d'an yi mata ciwa ciwa ko Js3 ne a sakata. " Ashraf ya d'an saki fuska yace "yauwa Habib hakan yayi." Habib yai dariya yace " bazaka gode min ba? " Ashraf yace " in komai ya kammala zan gode ma, but please ka tambayi Abban yanzu dan inasan ta tafi a satin nan. " Habib yace Shikenan. Yana kashe wayar yai ajiyar zuciya sannan ya makama inda ya fito wani mugun kallo na takaici, yai gaba. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Su kam a ciki sai tada zancen suke yi, mumy kam duk ranta ya gama da gulewa rai b'ace ta fito daga falon tai b'angaren su Little. A zaune taga Little a kan gado ta zuba tagumi, Nafi kuma ta ra kub'e a gefen gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta, abu d'aya ke yawo a ranta tajama Ashraf fada ita abinda ke damunta kenan. Muryar Mumy ce tasata ga d'ago, mumy ta tsaya a kusa da Little tace " Nafi ta fadamiki abinda ya faru? " Jikin little a sanyaye tace " Mumy bakisan Nafi bane, kome ke damunta bazata taba fad'amin ba. " Mumy cikin fada tace " ai kuwa yau dole ta fada tunda gashi can ta jama Ashraf cin mutunci. " Nafi wacce jin hakan yasa ta mike cikin tsoro ta matso kusa da Mumy ta tsugunna a gabanta tace " wlh Mumy ba abinda Yaya ya sani, bai ma san nice naje d'akin ba. " Mumy tace " mene? " Nan little ta fad'a mata ita yace taje ita kuma batada lafiya shine Nafi taje, jikin mumy ne yai sanyi ta kalli Nafi tace " to akace kina d'akinsa? " Nafi ta share kwalla tace "Mumy bashida lafiya fa? " Idanu mumy ta zaro ta kalli Nafi jiki a sanyaye, Nafi wacce idanta ya rufe dasan kare Ashraf tacigaba " Mumy wlh tun safe bashida lafiya kuma wlh yana jin jiki, ni a ganina bai kamata ma ace kaf gidan nan ba wanda yasan halin da yake ciki ba........" Hannu tasa ta rufe bakinta, me take fada? A ranta tace " amma ai Anisa ta sani. Mumy tai shiru a hankali ta juya tai waje batace komai ba, little ta kalleta tace " lalai Nafi dama kin iya zakewa haka? " Nafi ta kalleta tace " Maryam bakisan halin da yaya yake ciki bane sannan ace dake kanwarsa da mahaifiyarsa ba wanda ya sani? Na d'auka in bashida lafiya Mumy ya kamata ya fara sanarwa? " Little tai wani sansanyan murmushi tace " Nafi kenan, bakisan komai ba a kan harkar rayuwar gidan nan. " Nafi ta mata kallan mamaki, little tace " karki damu zan sajar dake komai gobe, in kikaje zaki gane dalilin dayasa Yaya baya shiga harkar Mumy. " Nafi tai shiru batace komai ba.... Mumy ta fito jiki a sanyaye kanta sai sara mata yake yi, a waje ta hango Aneesa ta taho kamar zaki rike da wata zungureriyar waya tana tafe Umma na mata magana amma da alama bata ma jin me ake cemata, Mumy tana tsaye a kofar su Little har Aneesa ta karaso, idanunta sun canza. + Da mamaki Mumy ta kalleta tace " Neesah meye hakan? " Aneesa wacce sai hucci take ta kasa magana sai neman cusa kanta ciki take, Mumy tasa hannu ta riketa tace " Neesa meye hakan wai? " Umma ce ta karaso cikin kinibibi tace" Yauwa gwara da kika riketa wai Nafi zataje ta zane. " Mumy takaici ya kamata tace " in kuma Ashraf d'in yajiki kice me? " kallan Mumy tai kamar mai shirin kuka tace" Mumy amma kina ganin..... " Mumy tace " Laifinkine, in har Nafi ta fiki sanin meke damun Ashraf, ke da zai zama mijinki amma ace ba kece ke kula da shi ba. " Umma tace " wace irin magana kikeyi haka? Haba Amina ya zakisa yarinya a gaba wacce ranta yake a b'ace ki kara b'ata mata." Mumy ta kalli Umma sai dai takaicin abinda yake faruwa yasa ta kasa tanka mata. Umma ta juya kai tace " haba Amina _wace irin zuciya gareki?_ace ke kawai d'anki kika sani? " Mumy ta juya batare da ta sake magana ba. Aneesa ta kara zuwa wuya gani take kamar saboda Nafi itama Mumyn take mata haka. Hannunta ta fizge daga gun Umma tai ciki a zuciye. Nafi kam ta d'auro alwala isha'i kenan, ta zauna a bakin gado ta rasa abinda ke mata dadi, taji an banko kofa da karfi kamar za'a b'ala, da sauri ta kalli kofar. Little dake zaune akan kujera ma ta d'ago da sauri. Aneesa a zuciya ta shigo d'akin, Nafi dake tsaye ta shiga kallanta cikin tsananin tsoro, Little ta mike tace " Ya Neesa meye kuma hakan? " Aneesa ta buga mata wata muguwar harara sannan ta nufi kan Nafi gadan gadan Umma kuma ko kunya tana tsaye a baya. Da karfi Little tace " Wlh Ya Neesa kika daketa sai na fadaki da Yaya. " Cikin kuluwa Aneesa ta wurga mata kallo, Little ta kalleta tare da d'aukan wayarta tace " Wlh kika daketa yanzu zan kirashi." Aneesa kam ta kulu fam kamar zata fashe, Umma ta matso ta gaurama Nafi mari iya karfinta sannan ta kalli Little tace" ni ki tabbatar kin fadamai inyaso ya zo ya rama mata. " Tana kai nan ta fizgi hannun Aneesa tai gaba. Nafi kam ko kuka batai ba dan ganin zabgegiyar bulalar dake hannun Aneesa yasa batama ji zafin marin sosai ba. ¤¤¤¤¤ Mumy kam ana idar da sallah tai b'angaren Ashraf, a hanya suka had'u da Mumy baice mata komai ba sai dai yasan gunsa tazo, nan ya bud'e ya shiga tare da kunna kwan wuta. A bud'e ya bar kofar hakan yasa Mumy ta shiga. Shikam d'aki kawai ya wuce, ya d'au ruwan da Nafi ta gasa mai gun ciwon ya zubar a toilett, sannan ya matse towel d'in ya shanya sannan ya fito. Mumy na zaune hakan yasa yaje d'an nesa kadan da ita ya zauna a kasa, Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tace " Ashraf abinda ya faru d'azu kayi hakuri....." D'agowa yai ya kalleta idanunsa sunyi jaa jikinta ya kara yin sanyi, cikin wata irin murya wanda mai sauraro shi kad'ai zai fahimci abinda ke zuciyar me maganar Ashraf yace " Kin taba yadda dani Mumy? Ko me aka fada a kaina tun ina karami kin taba yin bincike kafin kimin fada? " Mumy idanunta suka cicika da kwalla sai dai tsananin tausayin Ashraf dake yawo a ranta. Hannu yasa a bugi inda zuciyarsa take da karfinsa wanda kana iya juyo karar dukan ya cigaba " Kinsan ya nakeji a raina? A duk sanda kika zargeni da abinda banyi ba?....." Kasa karasa kalamansa yai saboda wani rad'ad'i da zuciyarsa take mai, Mumy wacce ganin yanayin d'anta da bata taba gani ba yasa hawayen datake b'oyewa suka zubo ta gefen idanta. Kallansa tai cikin dauriya tace " ba haka bane Ashraf. " Ya kalleta sannan yai wani murmushin takaici yace " Nafi zata tafi makarantar kwana a satin nan insha Allah. " Mumy bata d'auke ido a kanshi ba tace " amma naga kamar ba tada karatu? " Ya sake yin wani murmushin wanda itakam mumy sam batasan taga yayi saboda bata sani me yake nufi yace "eh hanya za'a mata ta shiga Js ko 3 ne inyaso sai a dinga mata lesson kuma a makarantar. " Mumy ta jinjina kai tace " hakan yayi sai dai baka ganin karatun zai mata wahala? " Ashraf ya d'an tab'e baki yace " wannan kuma ruwanta. " Mumy tace " shikenan in makarantar ta fito sai ka fadamin sai muje a mata shopping Allah ya baka lada ya kuma yi albarka. " A cikin ransa yace Ameen, ta mike tace " bari inje. " Bai amsa ba ko ince tasan ma bazai amsa ba, tana fita yabi bayanta da kallo sannan ya koma d'aki ya d'auko diary d'in mahaifin sa wanda wasiya ce kawai ya barmai. Shafin farko wanda a kullum sai ya karantashi yau ma shi ya karanta " _Ashraf kada ka kuskura kabar mutane susan abinda ke zuciyarka,_ _ka dinga kokarin b'oye bakin ciki ko farin cikin dake ranka, kar ka bari wani yasan sirrinka, wannan ita kadai ce hanyar da zaisa ka kare kanka...ko da kuwa 'yan uwanka ne na jini..._" Ashraf ya share zufar data keto mai duk da sanyin AC d'in da ke d'akin, Murmushi yai wanda kana ganin kasan na bakin ciki ne a fili yace " Dad zan iya jure hakan kuwa? I am really lonely." Ya kwantar da kansa kan gado, kafad'ar sa na masa zugi sai dai zugin dake zuciyarsa tafi karfin wannan....... ¤¤¤¤¤¤ Habib kam da kansa ya samu Abbansa ya mai bayani, Abban Habib na tsananin san Ashraf a lokacin ya kira wayar abokinsa ya sanar dashi, sunyi rashin sa'a matar tashi an mata transfer zuwa Rumfa Collage sai dai ya sanar dasu ai kanwarta ma principal ce ta FGC na kazaure, nan ya sanar musu in suna san can d'in to a yanzu zai kira kanwar matar tasa ya fada mata. Nan Habib ya ma Abba alama da a yadda, sunyi sallama akan zai kira anjima. Ba'a dade ba ya kira tare da sanar dasu ba matsala duk sanda suka shirya ko gobe ne su kaita. Nan Habib ya kira Ashraf yamai bayani. ¤¤¤¤¤ A b'angaren D'an litti kuwa yan sanda sun gaji da ajiyarsa gashi abin haushi bashida alamar sanar dasu Inda Ashraf yake, duk kuwa da dukan da sukamai, hakan yasa haushi ya kamasu suka cilloshi waje tare da kwace wukar dake jikinsa. D'an litti ya sha kuka wiwi gashi ko ficika bashida shi, ga wunya datake damunsa. Dakyar ya mike ya dingisa ya shiga gari, yayi sa'a ya sami wani mutum ya bashi naira d'ari. Nan ya gangara yasai wainar gero kan kace me ya cinye, ta gumi ya baza yace " Oh Ni D'an litti haka rayuwata ta koma? Daga boko sai a nemi halakani? Yanzu ni ina zan nufa in nemo Ashaf d'in? " Ya jingins kansa da bango zafin rana na damunsa. Nace wayyo!

Post a Comment for "ZUCIYA CHAPTER7"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...