ZUCIYA CHAPTER 6 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUCIYA  CHAPTER 6

ZUCIYA CHAPTER 6

- - Post a Comment
ZUCIYA CHAPTER 6
Kwanaki sun d'an tafi yau kwanar Nafi 10 sai dai abubuwa dayawa sun canza, sam yanzu Ashraf yadaina mata magana tundaga wannan ranar ko gaisheshi tai kai kawai yake d'agawa, tana zuwa gyaramai d'aki duk bayan kwana biyu sai dai daga ta shiga yake fitowa, wannan abu na damun Nafi iya tsanani, gida ya mata zafi ga Little yanzu suna jarabawa ba zaman gida take ba, sannan cikin gida kowa zancen biki ne a gabansa, shiyasa yanzu zamanta yafi yawa a kitchen, sosai ta fara iya abinci dan yanzu tana nata iya kokarin. + Kamar yanda ta saba yau ma a ka'ida zataje ta gyara b'angaren Ashraf suna gama aiki a kitchen tai wanka ta d'au abincinsa tai gaba, ya bata makuli saboda wani sa'in in bayannan hakan yasa data kwankwasa taji shiru kawai tasa makuli ta bud'e, karfe goma ne shiyasa kanta tsaye tai d'aki ta d'auka ya fita, me zata gani? Ashraf ta gani kwance ya dukunkune jikinsa da bargo, lekawa tai cikin tsoro idanunsa a rufe suke hakan yasa ta karasa kusa dashi, numfarfashi yake fitarwa sama sama, Nafi ta tsuguna saitin fuskarsa, hucin da yake fitowa daga bakinsa yasa tasan yanajin jiki, kuramai ido tai kawai hawaye ne suke zubo mata wanda ita kanta batasan tanayi ba, a hankali yad'an bud'e ido ganin Nafi yasa ya ciro hannunsa da niyyar yi mata bayani, itakam ganin yana miko hannu tai saurin rike hannun, ya kara daurewa ya bud'e ido, yayi mamakin ganin yanda take zubar da hawaye sai dai abinda yakeji yasa ya d'aure yace " rub zaki mikon." Mikewa tai da sauri ta shiga dube dube, hannunsa ya sa ya nuna mata inda yake, da sauri ta d'auko ta mikamai, nuna mata kafad'ar hagunsa yai ya d'aure da kyar yace shafamin anan. " Kallan mamaki tamai sai dai gani tai idanunsa a rufe suke, mikewa tai a hankali ta rasa ta ina zata fara, ganin yanda yake hucci yasa ta d'aure a hankali ta d'an yaye bargon daga b'angaren sa na haggu. Vest ne a jikinshi shiyasa tana iya ganin gun, mamaki ne ya kamata ganin gun ya kumbura, da alama bigewa yai ko kuma wani abun lalai wannan ciwon ne ya sa mai zazzab'i, kallansa tai cikin tsananin tausayi wanda bata tab'a ji ba, yau ce rana ta farko da takeji inama ciwon ya dawo jikinta, a hankali ta d'ebi rub d'in ta fara kokarin shafawa, sai dai daga takai hannunta kan jikinsa sai tai sauri ta d'auke, tasan magani ne da alama kuma yanda takeji maganin zafi zai mai. Cikin wani yanayi wanda Ita kanta bata sani ba tace " Yaya baka ganin zaiyi xafi? " A hankali yace " Nafeesa samin ba zaiyi ba. " Idanu ta rufe kamkam kamar ita za'a sawa a haka ta samai, sam batasan hawayenta na d'iga akan gun ba, Ashraf kam ido ya rufe dan akwai zafi sai dai jin hawayen nafi agun ciwon yasa jikinsa yai sanyi, meyasa? Menene dalilinta? Wata zuciyar tace kasan Nafi da tausayi. Tana gamamai ta maida bargon ta rufe shi sannan ta share hawayenta wanda ita kanta tana mamakin yanda suke zuba haka, cikin sanyin murya tace " Yaya ka tashi ko wani abin kaci. " Kai ya girgiza mata alamar a'a, idanunta suka kara cicikowa tace "Yaya dan Allah, in kumaa da wani abu da kakeso sai in maka yanzu. " Idanu ya bud'e a hankali ya kakaro murmushi sannan yace " me kika iya?" Da sauri tace "duk abinda kakeso na iya kaji. " Ganin baiyi magana ba yasa tace "Dankali aka soyama da farfesun kayan ciki, xaka iya ci? " Kallanta ya sakeyi sannan yace "eh" Da sauri ta mike tai falo ta dan zubo a plate, tazo kusa dashi, kallanta yai baice komai ba. Itama tsayawa tai rike da abinci batasan ya zatai ba. Suna nan a haka har bacci yai gaba dashi, kuramai ido tai a hankali tace "Kayi bacci sau biyu kenan Ina tsaye. " Tai murmushi sannan tace "sai dai duk banajin haushin hakan. " Falo ta fito ta maida abincin sannan ta shiga gyara, har ta gama bai farka ba, itakam zuciyarta na raya mata taje ta sanar da mumy halin da Ashraf ke ciki, sai dai tana tsoro dan kuwa tasan halinsa, ta kuma kula kamar ba wani shakuwa sukai ba. Gashi ta gama aiki kuma sam batasan ta fita tabarshi shi kad'ai, kuma tana tsoron kar azo a ganta matsala ta sake faruwa wanda ita kuma bataso. Haka tanaji tana gani tai waje tana waiwayen d'akin. _Kauye_ Yau tun safe su maman Hanne suka shirya ita da Datti akan lalai yau ya kamata suje ganin muhalin Nafi saboda ai dama bai kamata suje daga farko ba. Sun fito suka tarar da D'an Litti a inda sukai zai jirasu, Kowa ya kalli D'an litti sai ya kara saboda tsananin gayun dayasha, riga ce ta shadda mai dogon hannu yasa wando jeans ya tutura rigar a cikin wandan sannan ya kwama takalmi sau ciki ba safa, ya kawo hula irin tamu ta hausa ya saka, sannan ya kwama glass dinsa, gefen aljihun wandon kuwa ya ajiye wata zargab'ebiyar wuka. Tsayawa yai ya wani karkace, su Datti suka karasa, maman Hanne na rike da gari yai zafi, wanda 'yan uwan Nafi suka harhad'a mata tarkace su fura ne, kayan mata ne, gayayyaki na magani, su daddawa ne, kub'ewa busassa da sauransu. Datti ya kalli D'an litti yace " kai amma wannan yaron kana burgeni, ni kam dama kaine ka auri Nafi ba wannan ba. " Dan Litti ya juyo cikin gayunsa yace "Haba Malam ni ai nafi karfin Nafi sannan ni abinda yasa nake san zuwa rakiyar nan ba komai bane ila I want me to see Ashaf. " Datti ya juya kai tare da tab'e baki yace " mu tafi nikam ba turanci ne a gabana ba. " Sun isa Gwaram suka samu wata bus anata lodi masu zuwa kano nan suka shige, Datti yai dariya yace " Ashe ma abin ba wuya." Me ruwa ne ta leko tana asai ruwa, Dan Litti ya kobare cikin salonsa yace " ke me ruwa Me too want water one. " Ta kalleshi tace " Dan boko banajin turanci. " Maman Hanne tace "Kayi mata da hausa D'an litti kasan ba iyawa tai ba " Yai murmushin kasaita yace " okay, bani ruwa d'aya. " Nan ta bashi, Datti yace "lalai yaro muna zaune dan rashin d'a'a sai ka sai ruwa kai kad'ai ba tare da ka sanmana ba? " Dan litti ya kara gyara zaman glass d'in sa yace "gatannan ka siya kaima." Datti ganin inya siya sai ya saima maman Hanne hakan yasa ya gwara shima ya hakura. Nan mota ta tashi suka fara tafiya.......... _Gida_ Kawu ne ya kalli Mumy wacce ke zaune cikin damuwa, yace "Hajiya lafiya kuwa? " Kallansa tai cikin kulawa tace " Tunani nake yaushe ya kamata asa lawyer d'in mahaifin Ashraf ya kawo sakon wasiyyar nan? " Kawu ya mike zaune tare da dafata yace "Hajiya karki damu da wannan, ai shima Yayan cewa yai abama wacce Ashraf ya fara aura, sai mu bari sai anyi auren kenan ko? " Tai d'an dariya tace "I am really curious akan me ya ajiyema Matar Ashraf wanda ba wanda ya sani sai shi daya tafi. " Kawu yai dariya yace "nikaina na k'osa naga menene wannan, da yace lalai matar Ashraf ta farko ya umarta abama. " Nan suka shiga tattaunawa akan al'amarin wanda ba su kad'ai ba kowa ya kosa yaga menene wannan abun...... To nima daban taba ji ba sai yau na k'osa na gani sai dai ina ta tambayar kaina, Wacece matar Ashraf ta farko?????? Duk yanda Nafi taso ta kwantar da hankalinta ta kasa, ganin azahar tayi tai sallah dan yanzu ba laifi Little ta koya mata duk da suratul Iklas kawai ta iya ko hijab d'in datai sallah bata cire ba tai waje da sauri, knocking tai ganin ba'a bud'e ba yasa tasa makuli ta bud'e.+ Ko kofar bata rufe ba ta shiga da sauri tana fatan Allah yasa ba wani abun bane ya sami Ashraf. D'akinsa ta nufa kofar nanan a bud'e kai tsaye tai nufin shiga sai dai me? Aneesa ta gani zaune kusa da Ashraf ta rike plate a hannunta ta d'ebi Faten dankali tana kokarin kai bakinsa, da sauri ta matsa daga kofar ta tsaya a jikin bango, hannu. Ashraf yasa da niyar amsar cokalin ta noke kafad'a tace " ni zan baka Hubby. " Kallan mamaki ya mata, ta kashe mai ido cikin salo tace " daga yau na daina cema Yaya tunda bikinmu ya matso, Hubbyna zan dinga kiranka. " Ashraf baice komai ba sai kula da hijab dayai a bakin kofa, Nafi wacce ke lab'e tad'an leko kad'an jin abinda Aneesa ta fad'a. Idanunsu ne suka had'u juyawa tai da gudu tai waje, baice komai ba haka kuma bai mike ba sai murmushi dayai. Aneesa ta d'auka cemai Hubby datai shiyasa yai murmushi, ta kalleshi cikin kauna tace "ahhh! " Amsar cokalin yai, ta turo baku cikin shagwab'a tace "Hubby ya maganar sakon Abbanka? Sai yaushe za'a bani. " Kallan mamaki ya mata yace "me? " Ta d'an mai hararrar wasa tace " haba Hubby na kagu inga menene. " Fuska Ashraf ya canza, cikin takaici ya kalleta yace " Get out." Mikewa tai cikin mamaki tace "me kuma nai? " Yace "what? Me kikai? Ina kwance ba lafiya amma ki rasa me zaki ce sai zancen wani abu? Fita nace. " Idanu ta fara canzawa zatai alamun kuka, yace "wlh Anisa kika min kuka anan sai kinyi bala'in dana sani. " Ta kalleshi cikin tsoro tace "Tayaya zaka iya abu kai kad'ai bayan kafad'ar ka a kumbure take? " Ya juya kai yace "da sanda kika gani a mace kika ganni? Fita nace ko? " Aneesa ta mike ta fita cikin takaici. Tsaki yai sannan ya tuno sanda Nafi take hawaye sanda taganshi haka da sanda takesamai magani, tsaki yaja kawai. Nafi kam tana fita d'aki ta koma ta rasa me yasa takejin zafin Ashraf, Hubby? A fili tace ko meye hakan oho.... Harta zauna ta mike tai kitchen. _A Mota_ Tunda suka isa birnin kudu aka tsaya aka ajiye mutane sannan aka d'ebi wasu, kowa ya kalli D'an litti wanda ke sanye da wuka a katara sai ya matsa, sai kuma yasha jinin jikinsa, duk mutane sunyi tsit a mota duk tunaninsu d'aya wancan me zaiyi da wuka? " Haka dai akai ta tafiyar kurma shikam yana nan kwame da glass d'iinsa baicewa komai, haushinshi ma su Datti da suka isheshi da zancen wai gaskiya sun gaji har yanzu ba'a iso ba? Wani gida ne kano haka? Sun isa kachako anan kwandasta ya kalli kowa yace "a kawo kud'in mota." D'an litti yace "nawa ne? " "dari 700." A zabure Datti yace "me? Dari 700?hauka kuke? Kunsan ma miye d'ari bakwai? " Wani ne wanda ke gaban d'an Litti ya d'an mike yace "To wlh anmin sata. " Gangarawa mai mota yai, parking yai sannan akace kowa ya fito, wanda akama sata yace wlh an d'auken kudina a dunkule. D'an litti yaja tsaki yace "kudai kawai baku ajiye kudi ba yanda ya kamata zakuzo kuce am d'auke muku. " Nan aka fara hayaniya kwandasta da kansa yake tambayan kowa ko ya d'auka har akazo kan d'an litti yace "Kai Tsakanin ka da Allah kaika d'auka? " "I am the one. "abinda d'an litti ya fad'a kenan cikin gadara da takaici, shi harga Allah ya dauka i am the one yana nufin ba i am not ne. Nan aka shiga zaginsa wasu na cewa dama su basu yadda dashi ba, hannu yasa ganin ana mai hayaniya da jiyar fito musu da aljihun sa akan su tabbatar ba komai a ciki, da sauri Driver ya rike hannun sa ta baya, yace " me kake shirin d'aukowa? " Mamaki ya kama d'an litti zai magana sai ga 'yan sanda, nan suka fad'a musu, su kansu suna kallan yanda d'an litti yasa wuka zargab'ebiya a gefen riga suka tabbatar da lalai da alamar tambaya. Cafkeshi sukai sukace sai sun kaishi office an charge shi, Datti a zabure yace "Aradun Allah baku isa ba rakamu gurin 'yata fa zai. " Kallansa sukai sukace "sai dai ku koma in ya dawo ya rakaku amma wannan dole me ya bimu." Dan litti sai kokawa yake akan a kyaleshi amma ina...ankwa aka garkama mai akai gaba dashi sai ihu yake yana cewa Wallahi Allah bani bane, Allah I am the one. " Su Datti kam abin duniya ya damesu, maman Hanne tace "Yaya aikam dole mu koma ina mukasan zamu? " Mai mota yace sai sun bashi dari 1000 su biyu, da kyar aka laluba datti aka samo dari 500 cikin takaici suka barsu agun sukai gaba. Datti kam duk ya rikice, shida yakesan suje gun Nafi wannan yaran ya d'an bashi kudi dan yaga da alama akwai kudi a jikinsa. Maman hanne ta kalleshi tace " Yaya wlh ba karamin kuskure kai...... " Tsawa ya daka mata dama yana takaicin bai samu wani kudin ba ga nashi ya kare uta ficika ba a d'auka nata ba yace "ke ni gafara bani guri, banza kanwar mai satan saniya duk ba yayarki bace taja duk abinda ya faru? Zaki wani bud'en baki kice wai nayi kuskure? Nayi kuskuren 'yarki ce? " Maman Hanne tace "Allah ya baka hakuri.... " Nima nace Ameen Dakyar Ashraf ya iya watsa ruwa a jikinsa, wajen sa kaya kamar yai ihu, haka dai ya daurw yasa riga, makuli ya d'auka ya nufi hanyar waje da niyyar zuwa asibiti.+ Yaje fita Umma ta kirashi hakan yasa ya karasa gunta, falo suka shiga bayan sun gaisa ya kalleta yace "Umma ya akai? " Ta d'anyi murmushi tace"Dama tun jiya nakesan magana dakai. " Kallanta yai kawai baice komai ba, ganin haka yasa tace " yanzu saura wata d'aya da sati biyu bikinku da Aneesa shiyasa nake tunanin kamar ya cancanta a bata sakon mahaifinka..... " Wani kallo ya mata wanda ita kanta batasan ke yake nufi ba, sannan murmushi ne ya biyo bayan fuskarsa ya kalleta yace " Ashe har na bada sadaki an shaida kenan? " Umma tace "mene? " Yai wani murmushin rainin hankali yace "a iya sanina wanda ya bada wasiyyar nan cewa yai matata ta farko, banaji yace matar dana kusa aura. " Ta kalleshi sannan ta motsa baki zatai magana, mik'ewa yai sannan yace " inada abinyi Umma sai anjima. " Tabishi da kallo cikin maimaita kalamansa, asanda yai maganar sam kwakwalwarta kullewa tai amma yanzu kam datake maimaita kalaman ta fahimci banda tsananin rainin hankali ba abinda Ashraf ya fad'a mata. Shikam cikin tsananin b'acin rai ya shiga mota, yayi tunanin zai iya tuki sai dai jin zafin da kafad'arsa take yasa ya na driver d'in mumy magana, ba'a dad'e ba ya karaso nan ya jashi suka fita. Kansa ya kwantar akan kujera ya lumshe idanunsa, menene dalilin dayasa mutane suka damu da abinda mahaifinsa ya bari? _Fatiha an d'aura auren Ashraf da Nafisa yar gidan Datti_ Abinda ya fad'o mai a rai kenan, kallan driver yai yace " Adamu kaini wajen malam Yunus " To abinda driver d'in ya fad'a kenan tare da murd'a kan sitiyari, sunyi tafiya sosai kafin su isa wata katuwar makarantar islamiya, nan yai parkin Ashraf ya fita, wani babban office ya nufa ya kwankwasa, daga ciki aka ce shigo, Ashraf ya murd'a kofa ya shiga. Malamin na ganinsa ya mike cikin tsananin farinciki ya karaso kusa da Ashraf tare da mikamai hannu alamar musabaha, shi kanshi Ashraf d'in ya saki fuskarsa sosai, nan shima ya mikamai suka gaisa cikin girmamawa. Nan ya nunama Ashraf guri ya zauna, sunyi gaisuwa tare da tambayan juna bayan rabuwa, dattijon Malami ya kara washe baki yace "Muhammad sam ka daina ziyartata. " Ashraf yai murmushi yace " wlh malam uzuri ne ke hanani zuwa. " Sunjima suna gaishe gaishen su kafin Ashraf yai gyaran murya yace "Malam ina cikin wata 'yar matsala ne wacce duk duniya ba wanda na sanar ma kuma ba wanda zan sanarwa sai kai. " Malam yunus ya kalleshi cikin tsananin kulawa, yace" Inajinka." Ashraf yai shiru, yana tunani. Malam yace "Muhammad karka b'oyemin komai. " Ashraf yai kasa da kai nan ya zayyane mai kaf abinda ya faru sannan ya d'oramai da wasiyyar mahaifinsa. Malam Yunus hankalinsa ya tashi dajin wannan al'amari ya kalli Ashraf yace" Tausayi da Taimako ne yasa ka aureta sai dai Muhammad inasan tunasar dakai aure ko a wasa akayishi indai har anyi auran yanda musulunci yace to fa tabbas wannan auran ya d'auru sannan hakkin matarka na wuyanka. " Kallan Malam yai cikin tsananin damuwa yace " da ina tunanin saki..... " Da sauri Malam yace " kul Muhammad akan me? Ba taimako kakesan yi ba? Meye amfani taimakon kenan? " Ashraf jiki a sanyaye ya kalli Malam yace " me zanyi da ita? A kauye fa take ko ince a riga, yarinyar da banaji sallah cikake ta iya, batasan komai na rayuwa ba, infact shekarunta ma inaji basufi 16 ba Malam me..... " Malam yai murmushi yace " naji duk bata iya komai ba, kamin alkawari d'aya nikuma zan taimaka ma. " Ashraf yace "Name kenan? " Malam Yunus yai murmushi yace " Inaso kasa ta a makaranta inma taa kwana ko ta jeka ka dawo ka kula dacinta da shanta da suturarta har ta kai shekara 20 zuwa da d'aya, inhar aka kai lokacin Bakaji komai a tattare da ita ba inaso ka bata takardarta ita kuma sai ta nemi wani ta aura. " Cikin rashin damuwa Ashraf yace "nama wannan alkawari. " Malam yai murmushi sannan yace " game da wasiyar mahaifinka kuma kasan yanda zakai a rabu lafiya dan kuwa wannan wasiya ta matar daka aurace ba wacce zaka aura ba. " Shiru Ashraf yai yana tunanin lalai akwai chakwakiya inhar yace bazai ba Aneesa wannan wasiyar ba, Malam yaji yace " zaka iya jinkirtawa zuwa sanda ka rabu da matarka." Ashraf yai shiru, sai dai yasan wannan shawarar itace daidai,sunyi Sallama Ashraf ya ajiye mai kud'in talafi na makaranta sannan ya tafi. Mota ya koma nan sukai hanyar Asibiti.

Post a Comment for "ZUCIYA CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...