Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUCIYA CHAPTER 21

ZUCIYA CHAPTER 21

- - Post a Comment
ZUCIYA CHAPTER 21
Nafi ganin tana ta kiran number Ashraf amma shiru yasa ta mike tai hanyar waje da sauri, Little ta bita da kallan mamak, me ke damun Feenah? + Kitchen ta nufa da kanta ta shiga shiryama Ashraf abincin safe tana gamawa ta juye sannan ta fito tai bangarensu, wanka tai ta zura wata doguwar rigar abaya ash color anyi kwalliya da stones kalar silver a jiki, tayi kyau sosai. Little kam mamaki take tace " ina zaki wai?" Nafi tace " dan Allah so nake in zaki fita skul yanzu mu tafi tare ki ajiyeni a gun aikin yaya." Idanu Little ta zaro tace " kije kiyi me?" Tace " gun mijina zanje, hankali na bazai taba dawowa daidai ba sai naga halin da yake ciki." Little ta rike baki cikin mamaki tace " lalai Feenah kinyi nisa bakyajin kira, amma kina gani yayan bazai fada ba in kika je?ki kirashi a waya tukunna." Nafi tai ajiyar zuciya tace " da na sameshi a waya ai hankali na bazai tashi haka ba, sannan in ma yamin fadan zuwan ai dai a kalla na ganshi, bazanji haushi ba." Little ta jinjina kai tace " lalai Feenah wai a 'yan kwanakin nan ne kika mato haka akan san yaya ko kuwa dama can b'oyewa kike?" Nafi ta mike tare da rataya jaka karama mai dogon hannu tace " Little muje please kafin hankali na ya nemi goshewa." Tare suka fito Nafi ta d'auko abincin daga kitchen suka tafi. A hanya ko magana batayi fatanta kawai ta samu Ashraf lafiya, ganin batasan magana yasa Little ma tai shiru. A bakin company din ta ajiye ta tace " ko inzo in rakaki?" Nafi ta girgiza kai alamar a'a tace " zanyi tambaya." Nan Little tai gaba ita kuma ta nufi kofar shiga. Taje shiga taga wani wanda ba tantama tasan fuskar sai dai a ina?? Shi kam Dan litti kallanta yai sam amma bai ganeta ba, to dama ta ina zai gane Nafi kucaka da wannan? Tambayar sa tai tace " bawan Allah." Dan litti har yayi gaba ya dawo, tace " dan Allah office din Ashraf nake nema." Kallan mamaki ya mata lalai gata kamar mutuniyar arzuki ashe neman mijin wata tazo yi, ya had'e rai yace " ban sani ba, sannan yarinya karama bai dace da ke ba irin wannan rayuwar." Ya juya yai gaba, kallan mamaki ta bishi dashi bai dace da ita ba kamar ya? Shiga ciki tai ta sami wani security ta tambayeshi, nan ya mata kwatancen office din Ashraf. A hankai ta murda kofar ta shiga ta gaida secretary din sannan tace " gun yaya nazo." Kallan mamaki ya mata yace " yaya wanne kenan?" Tace " ya Ashraf kace mai kanwarsa ce." Secretary ya mike tare da knocking din kofar Ashraf, daga ciki Ashraf yace " ka manta nace banasan ganin wani in ba urgent bane?" Yace " yallabai kanwarka ce tazo." Ashraf cikin mamaki yace " Little?ba dai wani abun bane ya faru." STORY CONTINUES BELOW Da sauri yace " ta shigo." Nan Nafi ta karasa tare da murda kofar ta shiga. Sannan ta maida kofar ta rufe tare da jingina jikinta jikin kofar. Wani nannauyan ajiyar zuciya ta saki, ganin Ashraf a zaune lafiya kalau. Kallan kallo suka shiga yi mamaki yake dama Nafisa ce? Sansanyar murmushi ta saki sannan a hankali ta fara takowa zuwa inda yake. Kallanta kawai yakeyi yanajin wani sanyi naratsa shi. Nafi sai datazo kusa da inda yake kadan sannan ta ajiye abincin akan center table cikin shagwaba tace " Nasan ba farin ciki kai da ganina ba, dama lafiyarka nazo dubawa, tunda na gani bari na juya." Ta fada tare da juyawa, da sauri Ashraf ya taso ya kamo hannunta ya jawota jikinsa ya rungume tsam, sannan ya saki ajiyar zuciya yace " Ban kawo araina zan ganki bane sam." Tace " A wani hali kake tunanin zaka barni bayan ka amsa waya kamar numfashinka zai fita? Sannan daga baya ka kashe wayar ma gaba daya?" Ashraf ya dagota tare da rike kafadunta yace " Sry Baby nasan zaki damu in ban daga ba sannan dana daga kuma sai naga kamar zan fi tada miki hankali inkikaji yanayin da nake ciki." Cikin damuwa tace "mai ya faru wai?" Murmushi ya mata sannan ya kara jawota jikinsa yace " karki damu ba wani....." Kwace jikinta tai tace cikin dan zafin rai kadan " yaya baka yarda dani ba ko?" Jawota ya sake yi ya rungume yace " kema kinsan ba haka bane, kece mutum ta farko dana yarda da ita a duniyan nan." Har kasan ranta taji dadin kalamansa. Sake ta yai ya zauna tare da jawo kular abincin yace " Ahhh bari inga mai matata ta shiryamin." Tai murmushi sannan ta kamar zata zauna a dan nesa dashi. Harararta yai sannan ya bubuga kusa dashi da hannu yace " nan." Kallansa tai tace " in wani ya shigo fa?" Ta fada tare da matsawa inda yake. Hannu yasa ya jawota ta fada kan cinyarsa yace " anaso ana kaiwa kasuwa." Baki tadan turo tace " yaushe nace inaso?" Wani murmushi yai yace " gashi nan waya d'aya ta tada hankalinki gaba daya har kika tsiri kunyar fulani kika biyo mijinki." Idanu ta dan murza tace " yaya wani abu ya shiga idona." Dariya yadan yi yace " ko? Bari in duba miki." Neman mikewa tai tana rurufe ido, hannu yasa ya riko kugunta sukasa dariya a tare. Kan desk dinshi ta kalla taga take-away kallansa tai tace " wancan fa?" Yai murmushi yace " wlh abokina ko ince abokinmu ni da ke shine ya damu wai yaga alama banci abinci ba ya kawo min." Kallan mamaki tamai tace " abokin mu? Ni banda wani aboki namiji." Yai dariya yace " nima ba wai ina nufin abokinki ba na abota abokinmu dai na aure." Kallan mamaki ta sake mai, zatai magana ya matso saitin kunnenta yace " ya? Muyi skipping din aikin yau ne?" Hannu tasa ta rufe mai baki tace " aikin fa?" Yadan sosa kai kadan yace " yau so nake nai spending din whole day din dake." Tai kasa dakai tace " kar mu tafi azo nemanka." Yace " karki damu muje kawai." Abincin ya dauka da kansa ta kwace tace " barshi ni zan dauka." Yai murmushi shi ya fara fitowa ya kalli Secretary dinsa baisan mai zaice dan bai iya karya ba, ganin yana sosa kai yasa Nafi tai murmushi tace " zamuje dubiya bazamu dade ba." Yace " okay sir adawo lafiya." Ashraf ya kalleta sannan yai gaba, tabi bayansa, gudun ma kar asan inda zasu yasa suka tari mai adaidaita. Ta kalleshi tace " ka taba shiga?" Kallanta yai yace " ke dai muje." Ita ta fara shiga sannan ya shiga ya kalli mai adaidaita yace " Shagari Quarters." Kallansa tai mai alamar tambaya yadan matso bakinsa yace " akwai gidana acan na Abba." Kai ta jinjina sannan sukai gaba. Kafin su isa ya kira mai gadi ya sanar dashi zuwansa. *********** Yau Datti ya tashi cikin tsantsar farin ciki saboda jiya da yamma Mairo ta kawo mai shinkafa da miya abinda rabon dayaci shinkafa har ya manta, ga shi harda kaza a ciki, ya gama sannan ta bashi lemo mai dadi ya sha. Sai dai fa tundaga shan lemon nan bai farka ba sai yanzu, agoggon hannunsa ya kalla yaga wai karfe 9 na safe. A firgice ya mike zaune yace tun hudu da rabi na yamma nake bacci?" Mikewa tsaye yai yana kwalla ma Mairo kira, sai dai me? Shiru yaji kamar ba kowa ma agidan. Nan ya fito waje yana kiranta, babu ita ba alamarta. Da sauri ya shiga nemanta sai dai ina sam batannan. Yai dariya yace " da alama wata kazar aka tafi siyomin yau ma zansha dage dage." Garkensa ya nufa da niyyar ganin halin da dabobinsa suke ciki. Idanu ya zaro ganin kofar a bud'e. A tsorace ya karasa ciki.... Jama'a mai Datti zai gani?????? Kaf an kwashe komai dake cikin garken ba komau a ciki sai kashin dabobbi. Wani irin kara ya kwalla da karfi.... Wanda ya razanani yasa na yarda biro na. Datti kam daga wannan ihu shikenan ya zube ya zauna a gun kamar gunki, sam ya kasa ko da magana na ne.+ Gashi a bayan gari suke hakan yasa ba wand ya shigo, sai can wajen azahar yayansa ya biyo dan yanasan datti yazo ya duba mahaifiyarsu dake kwance ba lafiya. Can ya ganshi zaune, yai tsaki yace " kaji asara wlh kazo kasa dabobbi a gaba kana kallo, ni can na bazama ina nemanka kai ko jina ma bakai ba." Ya karasa maganar tare da karasowa inda Datti yake. Ganin kamar baima san me yake cewa ba yasa yayan ya tabashi da hannu tare da kallan garken. Shikanshi tsorata yai, ya kalli Datti cikin tsananin firgici yace " Datti ina dabobbin?" Datti kam ba magana yai dif kawai sai kallan turkensa yakeyi. Ganin kamar ba a hayyacinsa yake ba yasa yayan ya d'agashi dakyar yai waje dashi, a taburma ya zaunar dashi sannan ya shiga mai fifita. Datti kam haryanzu baya hayyacinsa ganin haka yasa yayan yai waje da sauri dan neman mai magani kafin matsala ta afku. ************* A b'angaren Ashraf kuwa sun isa gidan suka sauka daga kan adaidaita nan ya bada kudi suka nufi gidan. Mai gadi ya bud'e tare da gaidasu. Suna shiga falon Ashraf ya rungume Nafi ta baya yace " ahhh finally we are alone." Ta zare hannunsa daga kugunta sannan ta kama hannun ta zaunar dashi kan kujerar dinning sannan ta ajiye kular tai kitchen ta dauko plate da spoon. Kallo kawai yake binta dashi yana murmushi, ta kawo ta ajiye mai sannan ta bud'e abincin wani daddadan kamshi ne ya daki hancin Ashraf ya lumshe ido tare da kallanta. Dankalin turawa ne aka mai hadi cikin kifi da vegetable ta zubamai a plate sannan ta mikamai spoon tace " a taimaka a ba cikina abinci." Kallanta yai cikin tsananin so yace " nima ko ba'a fadaba nasan nawa cikin yana bukatar abinci." Tai murmushi sannan tace " to ya za'ai kenan? Nima nina zubama nawa cikin abinci baka ganin kaima aikinka ne ka kula da naka?" Murmushi ya saki wanda har fararen hakoransa suka fito, hannunsa ya nuna mata alamar tazo. Ta dan turo baki ya kara nuna mata hannunsa, nan ta mike cikin shagwaba ta karaso gunsa kujerar kusa dashi ya jawo mata ta zauna ya kalleta sannan ya matso cikin rada yace " muci tare gwara na tabbatar da yawan abincin da zakici dan inaji a jikina nayi a jiya a cikina." Kallansa tai cikin mamaki sai dai bata gane mai yake nufi ba, tace " ajiya?tame kenan?" Yai murmushi tare da sa yatsarsa akan bakinsa yace " sirrine." Harararsa tadanyi sannan ta d'auko spoon suka fara cin abinci a plate daya. Suna gamawa ta kwashe kwanukan tai kitchen dasu, cikin tsautsayi garin ajiye cup na tangaran ya fadi kasa. Ashraf dake falo jin kara yasa yace " Baby menene?" Idanu ta zaro duk ta rikice batasan ko kadan ta jawo abinda zai batama Ashraf rai, tana kokarin matsawa dan ta bashi amsa sai jiyai ta dan yi kara. STORY CONTINUES BELOW Da sauri ya mike ya nufi kitchen din a rikice. A zaune ya ganta ta rike kafarta ga jini sai zubowa yakeyi a tafin kafarta. Cikin rudewa ya karaso tare da kallan cup din daya fashe. Ya zagayo inda take ya d'aga cak yai falo da ita. Kan kujera ya zaunar da ita ya kalleta da niyyar yi mata fada akan rashin kulan da takeyi sai dai ganin yanda tai raurau da ido yasa yai shiru. Hannu tasa ta dan rike kunnenta tace " Yahkuri." Kallanta yai tare da rufe ido sannan ya kalli kafarta, mikewa yai ya dauko tissue ya ciro kwalbar sannan ya goge jini, sai dai yana gogewa wani na zubowa. Kallanta ya kumayi yace " sai dai mujibko chemist ne." Tace " ta yaya? A adaidaita fa muka zo." Ya kalleta cikin fada yace " Akan me ma tun farko bazaki dinga kula ba? Abu ya fashi kuma kin gani, mai zai sa bazakibi a hankali ba ki zagaye gun?" Yar kara ta saki tace " Yaya zafi." Ya sani sarai ta fadane saboda ya daina mata fada. Mikewa yai ya sungumeta yai toilet da ita. Ruwan dumi ya tara a dan roba sannan ya zuba dettol ya fara wanke mata. Rike rigarshi tai tana dan rakinta, bayan ya gama ya kalleta yace " zaki iya tashi?" Kai ta girgiza alamar a'a, yadan yi murmushi kadan yace " to yanzu ya za'ayi?" Ta dan kara shagwabewa tace " kadaukeni irin na d'azu." Baisan sanda yai dariya ba yace " naki, tunda bazaki dinga kula da kanki ba." Rigarsa ta rike, ya juyo ya kalleta tadan karkatar dakai cikin shagwaba tace " in nai kuka fa?" Kallanta yai batare da ya bata amsa ba, tace " Allah zanyi kuka, bakasan zafin da nakeji ba." Murmushi ya karayi sannan ya d'agata, d'aki ya kaita ya ajiyeta a kan gado sannan ya zauna a gefenta yana kallan yanda take murmushi kasa kasa, ya kura mata ido yace " me kike saka wa?" Mazewa tai ta kalleshi sannan cikin sanyin murya kalar tausayi tace " ruwa nakesan sha kuma bansan ya zan ba." Kallanta yai yace " ruwa?" Kai ta daga da sauri, ya mike yai waje, tabi bayansa da kallo, yana fita tadanyi dariya. Bai dadeba sai gashi da ruwa ya bata ta amsa ta sha, yace " ni danazo dan karamin honeymoon kin maidani mai kula da mara lafiya." Kasa tai dakai tace " ya hkuri yaya nima ba asan raina naji ciwon ba." Ajiyar zuciya yai sannan ya matso kusa da ita, cinyarta ta nunamai tace " kwanta anan." Harararta yai yace " salan anjima kizo kice na sagar miki da kafa?" Baki ta turo tace " tayaya zan fadi haka?" Kwanciya yai akan cinyarta tasa hannu tana shafa kan sumarsa. Idanunsa ya lumshe ba tare da ya bud'e idanunsa ba yace " Mu gudu mubar garin nan gaba d'aya?" Kallan mamaki tamai tace " Yaya." Idanunsa a lumshe yai murmushi yace " mu bar komai a yanda yake in daukeki mu bar garin nan?" Kanta ta sunkuyo ta daura fuskarta kan goshinsa tace " duk inda kake so muje in dai har da kaine bana shakka sai dai ka tabbatar zaka iya hakura da komai? Iyayenka? Kannenka? Company din da mahaifinka ya gina da guminsa?" A hankali ya bud'e idansa ya kalleta yace " Nafisa i am really scared." D'agowa tai cikin mamaki ta kalleshi tace " Yaya!" cikin raunanniyar murya. Idanu ya dan runtse kadan yace " Ina tsoron abinda zan binciko, bansan wani abu mai rikitarwa zan kara cin karo dashi ba." Hannunta tasa cikin tafin hannunsa idanunta suka ciciko tace " bayan kawu akwai wasu ne?" Cikin mamaki ya kalleta yace " ya akai kikasan....." Murmushi tai tace " yaya kenan, da alama da a birni na taso lawyer zan zama ko inzama Agent." Yai murmushi tare da maida kansa saitin cikinta yace " i am always impressed yanda kwakwalwarki ke saurin daukan abu." Murmushi tai tace " naji ance Abba kasheshi akai, to abun ai ba mai wuya bane, waye yafi amfanuwa da mutuwarsa? Duk ta inda aka duba kawu ne, kaga kuwa wannan binciken mai sauki ne na gaske." Dagowa yai kadan ya kalleta yace " whoa! Lalai na yarda matar nan tawa tana ja." Idanu ta rufe yai murmushi sannan ya maida kansa saitin cikin ta, yace " mai kike tunani gama da Mumy?" Cikin mamaki ta kalleshi, tare da tsayawa daga shafamai kan da take, tace " yaya ni fa har yanzu......." Kasa karasawa tai jin bakinsa akan cibiyarta, numfashinta ne taji ya dan dauke, a hankali ya shiga sarrafa ta cikin salon soyayya wanda itama ba'a barta a baya ba............ Ganin yanda suka fita hayyacinsu yasa na jawo kofar ina dariya nace " ko ina ciwon🤔???" ************ Dakyar aka samu kan Datti sai dai tun da ya fara magana zancenshi daya " Mairo Allah ya isa." Abinda yake ta fada kenan, ganin haka yasa yayansa ya taimakamai suka tafi rigarsu dashi. Duk yan uwansa ba wanda ya tausayamai da jin abinda ya faru, kowa Allah ya kara yakeyi wasu kuwa suce dama ai ance in bakai sharar masallaci ba kayi ta kasuwa, bai har matarsa? Yarsa?iyayensa da yan uwansa sunci arzikinsa ba ai gashinan wata katuwa can ta yasheshi." Yayansa yaje kauyen su Mairo sai dai iyeyenta sun sanar dashi suma basu ganta ba yanzu haka 'yayanta ma ake nema. Nam yayam ya gane dama can sun gama tsarawa. Amma Datti yana me? Ala fitar da dabbobi haka masu uban yawa???Kwance yake akan gado ita kuma tana kan cikinsa ya kalli agoggon bangon d'akin azahar tayi yace " tashi muyi wanka muyi sallah."+ D'agowa tai ta kalleshi tace " yaya sai dai ka kaini toilet kasan kafata ciwo take." Baisan sanda dariya ta kamashi ba yace " au dama haryanzu kafar tana ciwo? Sai naga d'azu kamar kin ma manta da ita." Fuska ta had'e tace " bafa mantawa nai ba kawai daurewa nai." Murgina wa yai daga inda yake ya koma gefen gado yace " hmm na fahimta yanzu." Nan ya sauka tare da d'aura towel sannan ya d'agata sukai toilet. Sunyi wanka sukai sallah, yana zaune kan sallaya yaji wayarsa nata neman agaji. Nan ya mike yai falo, ganin Dan litti ne yasa ya d'aga da sauri yace " mutumin ya an dubo?" Dan litti yace " Yallabai munje makarantar da yake da ita ni da officer din sai dai a can mukaji makarantar shekararta 30 da ginawa." Ashraf yace " 30?" Dan litti yace eh, sannan karamin asibiti din dayake dashi shima haka. Ashraf yace "gidajen hayansa fa?" Dan litti yace " su din ne bamu gama nemo su ba." Ashraf yai shiru can yace " is ok ma hakan, nagode, sannan ina shagari quaters ka kawomin mota please, zan turoma address." Yace " okay." Yana kashe wayar ya zauna tare da kurama wani guri ido yana tunani, wato tun Abba nada rai kenan makarantar take da asibitin. Kan kujera ya kwantar da kansa ya d'aura hannunsa akan goshinsa tunani yakeyi sosai, so yake ya hada puzzle din da yake a rarrabe a kwakwalwarsa. Nafi jin shiru bai dawo ba yasa ta mike tare da dingisa kafa ta fito falo. Ganin yanayin da yake ciki yasa tasan tunani yakeyi, a hankali ta taho kusa da shi ta zauna batace komai ba. Ashraf kam can cikin kwakwalwarsa abu d'aya ke saka masa, wato dady sun hada baki da kawu sun salwantar da rayuwar Abbansa saboda dukiya kenan. Shi kawu yana san dukiyarsa da kuma matarsa, shikuma Dady wato saboda kin taimaka masa da Abba yai da wuri shiyasa yake ganin shine sanadiyar talaucewarsu da kuma rasuwar iyayensa. Wannan dalilin ne yasa suka salwantar da Abba shima dan ya samu nasa kason na dukiyar Abba? Ko kuwa kafin Abban ya rasu ya mallaki dukiyar? Ajiyar zuciya yai tare da sauke hannunsa daga kan goshin sa, jin alamun mutum yasa ya juyar da kansa ba tare da ya d'ago ba. Kallan Nafi yai wacce itama kallansa take. Idanu ya lumshe sannan ya bud'e su a hankali yace " Yaushe kikazo?" Itama kanta ta kwantar a saman kujerar tana kallansa a hankali itana tace " tun dazu." Ya dan murmusa kadan sannan yace " banji motsinki ba." Tai murmushi tace " na kula kana bukatar kasancewa kai kadai ne, ni kuma banasan barinka shiyasa na zauna anan ba tare da saninka ba." Murmushi ya mata sannan ya mata alama da hannu akan ta matso, a hankali ta matsa kusa dashi yasa hannu a kugunta tare da kwantar da kanta akan kafadarsa yace " mu dawo nan da zama?" STORY CONTINUES BELOW Kai ta girgiza alamar a'a tace " yaya meyasa kaketa fadan magana irin haka." Kansa ya dan kwantar akanta yace " yanzu dai kawai jinai inasan inganni daga ni sai ke a gidanmu mu biyu." Tace " mu biyu? Ko uku?" Kallanta yai cikin mamaki zai ce mu uku kuma? Sai ya tuna da Anisa, hakan yasa yai shiru. Kallanshi tai tace " ya kamata in daura mana abinci sai dai naga ba komai a gidan na girki." Yace " hmm kayan abinci ba matsala bane sai dai da alama kin warke, kar anjima azo acemin baza'a iya abincin ba bayan an siyo, a nemi sani a kitchen." Dariya tai sannan tace " ko na saka a kitchen din ai bana tunanin akwai abinda zaka iya dafawa." Yace " akwai abinda zan iya dafawa mana." Cikin zumudi tace " haba? Mene? Fadamin dan Allah." Dariya yai sannan yace " matso in rada miki." Da sauri ta kai kunnenta saitin bakinsa, ya jawo kunnen da hannun harsai da tadanji zafi sannan yace " kinasan ji?" Kai ta daga alamar eh, yace " ruwan zafi." Yana fada ya mike yana dariya. Leb'enta ta ciza tace " YaYa." Ta fada cikin fushi. Dariya yasa mata tare da yimata gwalo. Mikewa tai dasauri tana dingisawa ta bishi kafarta ya nuna yana mata dariya. Nan ta kara sauri dan kamoshi. Dariya sosai yake mata ya shige d'aki, itama ta bishi nan suka fara zagaye gado yana tsokanarta wai Nafisa Cogal, ganin ba yanda zatai ta kamashi gashi ta gama kuluwa yasa tace " wayyo kafata." Ta fada tare da durkusawa. Da sauri ya matso yace " Nafisa menene?" Cafkeshi tai tace " wacce Cogal din?" Dariya yai ya jata suka fada kan gadon, dariya suke sosai dukansu kafin daga bisani su tsagaita. Matsowa tai ta daura hannunta kan kirjinsa tana kallansa tace " yaya inaji farin ciki zaimin yawa, ina tsoro kar ya yankemin lokaci guda." Kallanta yai cikin kauna yace " Baby tun da nake, bandai san kafin Abba ya rasu ba sai dai a iya tarihin rayuwata yanzu ne nasan me ake nufi da farinciki, me ake nufi da dariya, me ake nufi da tsokana, me kuma ake nufi da so, Nafisa ban taba tunanin zan yi experiencing wad'annan emotions din ba, sai dai yanzu jina nake kamar yaro dan sha takwas, akanki gani nake zan iya komai." Idanunta ne suka ciciko da kwalla, ya harareta yace " karki soma min kuka please dan banasan kuka ko kadan balle daga wacce nake tsananin kauna." Batasan sanda hawaye ya zubo mata ba, ba shakka bata taba tunanin akwai ranar da zatazo wanda Ashraf zai sota haka ba, kallanta yai tare da kankance ido yace "na dauka nace banasan kukan nan?" Ta share hawayen da hannunta tace " yaya akwai hawayen da suke zubowa in har farinciki ya musu yawa, in har kaga nayi kuka to yanzu akan abu biyo ne, ko dai farin ciki yamin yawa ko kuma kai nakema kukan da zuciyarka ta kasa." Kallanta ya keyi cikin tsananin kauna, kanta ta kwantar akan kirjinsa tace " in har zuciyarka na maka radadi akan wasu al'amuran ni zan ma kukan da zai sanyayata, dan nasan kai bakasan kuka ko kadan." Idanu ya rufe batare da yace komai ba. Tai murmushi itama. Ya bud'e ido a hankali sakamakon wani idea data fado mai, kallanta yai yace " Nafisa duk abinda zan aikata a wadannan lokacin inaso ki kauda kanki, ki kuma yafemin a hankali zan sanar dake dalilin da yasa nai komai, sai dai inaso ki sa a ranki ni Muhammad Ashraf mai san Nafisa ne." D'agowa tai ta kalleshi ba tare da dogon nazarin kalamansa ba ta matso ta sumbaci goshinsa tace " nima inaso kasa a ranka ni Nafisa mai tsananin kaunar Ashraf ce a koda yaushe." Rungumeta yai wani sanyi na ratsa zugakan mutane biyun, sai dai Ashraf yana saka plan dinsa da zai fara gudanar wa. Nace hmmmmmm ************ A b'angaren Mumy kuwa tun bayan tafiyar Nafisa data shiga daki ta dade tana kuka kafin daga bisani ta kwanta. Juyi kawai takeyi san tunani sun taru sun mata yawa akanta. Tana nan a d'aki har yamma kawu ya shigo d'akin ganin bata falo. Kusa da ita ya karaso yana tsaye yace " Hajiya me ya sameki? Naga na dawo bakyanan sannan na shigo banga kin mun sannu da zuwa ba." Ba tare da ta kalleshi ba tace " kaina ke min ciwo." Cikin rud'ewa ya matso tare da cewa kinsha magani? Ko zamuje asibiti?" Kallansa kawai takeyi ba tare da tace komai ba, ya kalleta cikin mamaki yace " menene? Naga kin kuramin ido?" Idanunta ta dauke daga kansa tare da girgiza kai tace "ba komai." Ya karasa kan madubi ya d'auko magani sannan ya fita dan dauko ruwa. Kalli ta bishi dashi wanda ni kaina ban fahimci kallan me take mai ba. Bai dade ba sai gashi nan dauke da ruwa ya nemi d'agata nan tace zata iya tashi, ta mike ta amshi maganin tasha sannan ta kwanta. Yace " bari in fita naga kamar kinasan hutu." Kai ta daga kawai hakan yasa yai waje. Yana fita ta share wasu kwalla da ni kaina ban fahimci kwallar ta menene ba. *********** Datti kam sam ya kasa magana, banda Mairo Allah ya isa ba kalmar da take fitowa daga bakinsa, an kaishi gurin malamai harda yan duba sai dai haryanzu ba sa'a duk hayakin da akemai kuwa, abinci ma sam bayaci sai dai ai ta duramai kunu. Yana zaune kamar gunki sai kalmar Mairo Allah ya isa kawai dayake fada. 'yan gidan ba wanda ya damu dashi banda yayansa guda d'aya. Datti kam duniya ta juyamai baya.......... Mairo ko tana ina??? Abinda ya fado min kenan.

Post a Comment for "ZUCIYA CHAPTER 21"