Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUCIYA CHAPTER 19

ZUCIYA CHAPTER 19

- - Post a Comment
ZUCIYA CHAPTER 19
Nan Dady yai ta jansa da hira shima yana biyemai kafin daga bisani yamai sallama, Habib yace "muje ka gaida Mum."+ Ashraf ya dafashi yace " next time kanina." Murmushi sukai a tare Ashraf ya kira Dan Litti suka dau hanya, suna hawa kan titi dan litti ya kalli Ashraf yace " Ashe ma kasan 'yan gidan." Ashraf yai murmushin takaici yace " Gidan yayan mahaifiyata ne " Dan litti yasa dariya yace " ohh shiyasa yazo nan?" Murmushi kawai Ashraf yai ya bud'e window tare da kurama titi ido, suna isa gida ya fito jiki a sanyaye yai b'angarensa. Nafi kam harta gaji da jiran dawowarsa gashi ta mai abinci, ganin anyi sallar isha'i yasa tai tunanin dubawa ko ya dawo. Da yake yanzu tanada makulli bayan ta kwankwasa taji shiru sai ta bud'e kofar, duk wutan bangaren a kashe yake da alama ba mutum a ciki, ta d'an d'aga gira tare da yin ajiyar zuciya tace " bai dawo ba." Tayi nufin juyawa sai taji ringing din waya, ita kuma ba tata bace dan tata na gida, cikin tsoro ta fara yin sanda tana bin inda takejin karar gashi a bin mamaki ba'a d'aga wayar ba. D'akinsa taji karar na fitowa a hankali ta murd'a tare da yin addu'oi a ranta, kwan wuta ta kuna da sauri tana tsoron kafin a maketa gwara taga waye. A binda ta gani ne yasa gaba d'aya jikinta ya mutu, tsayawa tai cak tana kallan Ashraf wanda ke zaune a kasa ya hada kai da gwiwa, ga kuma wayarsa nan a hanunsa yanaji ana kira bai dauka ba, sai dai ta kula ba wayarsa bace da yake amfani da ita. Ganin haske ya kewaye d'akin ne yasa ya d'ago ya kalleta da idanunsa wadanda sukai jaa, a hankali yace " Nafisa can u please get out?" Kallansa tai cikin tsananin mamakin halin data ganshi cikin rawar murya tace " Ya Ashraf?" Idanu ya runtse yace " please can u get out, banasan ki ganni cikin wannan halin....." ya karasa maganar cikin wata irin murya, sakon da aka turo mai yana kokarin bud'e kofa ne yasashi cikin wannan halin. Kawu ne yai reply kamar haka "Max na d'auka kunyi da Yaya akan bazaka kara nemana ba? To shi yace kaje yana nemanka." wannan sako ya d'agama Ashraf hankali, a iya saninsa Kawu mahaifin Habib kawai yake cema Yaya, sai dai tayaya za'ace da hannun yayan mahaifiyarsa????? Ganin bai maida reply ba yasa Kawu ke ta kiransa. Kashe wutar Nafi tai sannan a hankali ta taka zuwa inda yake, ta tsugunna tare da rungumoshi jikinta, idanunta sun cika taf da kwalla tun da take bata taba ganin Ashraf a irin wannan yanayin ba, hawaye ne ya ziraro mata a hankali tace " taya zan iya tafiya na barka cikin wannan yanayin?" Ashraf ya d'an zare jikinsa kadan yace " Nafisa please......" Hannu tasa ta rufe bakinsa sannan ta kara kankameshi hawaye suka fara zirya a idanunta cikin kuka tace " Yaya can u please share ur burden with me? Zuciyata tana zafi idan na duba naga bansan abinda ke faruwa dakai ba, bansan a wani hali kake ciki ba, Yaya ka taimaka ka sanar dani damuwar ka dan Allah...." Kuka take sosai wanda yasa jikinsa yin sanyi, kankameta yai sosai a hankali yaji hawaye ya gangaro ta idanunsa, yace " Nafisa ya zanyi? Ya zanyi da rayuwata, duk wanda nake tunanin yana sona sai na duba sai inga makiyi na ne, duk wanda nake tunanin yadamu dani sai in duba inga ashe amfani yake dani a b'oye, na d'auka i am smart sai dai yanzu na tabbatar i am the biggest foolish in the world, me yasa Allah ya d'auke Abbana ya barni? Meyasa....." Kuka take sosai ta sa hannu ta toshe bakinsa tana girgiza mai kai" Yaya ka daina fadar haka, Allah na tare da kai sannan duk wanda ya zalunceka Allah bazai barshi ba ko shi wanene." Idanu Ashraf ya runtse wasu zafafan hawaye suka zubo mai yace " me ya kaini binciken abinda ya riga ya shud'e, why???" Nafi ta kankameshi tana girgiza kai tace " laifinane yaya ko ma menene laifina ne, please ka yafemin, da ban sanar dakai ba banaji zakai binciken nan, yaya ka yafemin Laifinane, nice na ja maka shiga wannan halin." Ashraf ya sa hannu ya shafi bayanta yace " ba laifinki bane, na dade ina bincikena, iya kace ke taimakamin kikai, karki sake cewa laifinki ne." Nafi shasheka kawai takeyi, bata san me ya jiyo ba amma ta tabbata abin ya shafi danginsa. Sunyi shiru suna manne da juna cikin duhu, Ashraf can cikin wata sansanyar murya taji yace " Thank u Nafisa." D'agowa tai cikin mamaki duk da ba haske ba ganinsa take ba sai dai mamaki karara ya bayyana a fuskarta, wannan itace rana ta farko data tabajin Ashraf yayi godiya bama ga ita ba, a'a bata tabajin yace ma wani bama. Murmushi taji yayi ya d'an ja numfashi kadan yace " kina mamaki ko? Ni kaina rabon danaji na fadi wannan kalma ba naji zan iya tunawa." Hannayenta tasa akan fuskarsa sannan ta hada goshinsu tace " Yaya in kamin godiya akan me kenan? Ni kuma ince me kenan, yarinyar datake yar kauye ka..........." Hannu yasa ya d'an turo kanta bakinsa yakai cikin nata, wani irin salon soyayya suke ma juna wanda kana gani kasan son da sukema junansu lalai a bayyana yake, sun dade suna sumbatar juna kafin a hankali bakin Ashraf ya sauko kan wuyanta, wani irin yarr taji a jikinta wanda yasata yin numfashi, Ashraf sam ya manta da zancen sai ta aminta dashi, sarafata ya shiga yi sai dai itama duk da batasan kan abun ba haka kawai taji lalai tabbas tanasan ba Ashraf dinta farin cikin da yake nema. Soyayya mai karfi suke nuna ma juna sam bata san sanda ya zuge zip din rigarta ba sai jitai yabrabata da rigarta, ba shakka tsoro da fargaba ne ke damunta sai dai bataji duk wani wahala da ake fada zata iya bijirema Ashraf. Ya gama fita daga hayyacinsa haka itama a daidai wannan lokacin mai afkuwa ta amfku............Nikam ganin haka yasa na fito ga duhu wanda yasa ni yin tuntube da kujera😭 ************ A kauye kuwa Datti yau ya dawo ya taradda matarsa Mairo ta yimasa tuwo miyar kubewa bushashiya sai dai da zabuwa akai miyar, mamaki ya kamashi ya kalleta yace "mairo badai da zab......" Katseshi tai cikin salonta na jan hankali tace " Haba Datti bada zabuwarka bane, zabuwa ta ce data kasa na yanka mana ita." Baki taga ya washe yace " kai Mairo Allah ya miki albarka kinsan darajar dan adam." Nan ya yanko malmalar tuwo ya zuba nama sosai da miya ya hau ci, sai uban santi yake zubawa. Itakam sai murmushi takemai. Yaci yai hani'an ya tauna kasusuwa sannan ya kalleta yace " kai Mairo Allah ya barmin ke " Tace " Amin Datti." Ya kara washe baki yace "rabon dana kai nama bakina har na manta sai dai in gani a kwanon wani." Tai dan fari tace " ai banga laifinka ba, yanzu ba gashinan kafi kowa dukiyar dabobi ba duk yankin nan." Ya sake washe baki yace " Zabina guda 20 ne kaji guda 30 banda raguna, saniyoyi da akuya." Ta matso kusa dashi tace " yaushe za ka nunamin ne nima in gansu." Dariya ya kwashe dashi yace " karki damu gobe da kaina zan kaiki ki gansu." Tace to Datti Allah yabarmu tare. Yace Amin Mairoro ta.... Nace inma Maikoko ce...Lol masu suna Mairo tuba nake🤢Tana kallo Datti washegari ya d'aga rigarsa ya zuge wani zip ya zaro yar karamar wuka sannan yaje kusa da tirken ya d'an barzo wani gini sai ga makulli ya fito, da sauri ta koma jikin bango ta labe, ya kara le lekawa sai daya tabbatar ba kowa sannan ya bud'e turken.+ Kwalla mata kira yai sai ga Mairo ta taho hannunta duk gari tace " Datti ya akai? Ina tankade ne banji kiranka ba." Ya washe baki yace " zo kiga tirken." Tai murmushi tare da cewa ai har na saduda na dauka ma ka manta ko baxaka nunin ba." "Ah haba yanzu dai shigo ki gani " Nanta shiga ciki mamaki ya hanata magana, wannan wani irin arziki gareshi??? Yi tai kamar abin bai bata tsoro ba ganin yawan dukiyarsa tace " Allah ya kara amfa nawa, na gani bari na koma na karasa tankad'en." Dadi ya kama Datti ganin bata rude da ganin dukiyarsa ba lalai baza ta ci amanarsa ba.1 *********** A b'angaren su Nafi kuwa bayan komai ya wakana, itakam bacci ne yai gaba da ita, Ashraf ya mike tare da kunna fitilar gefen gado ya d'auketa ya d'aurata kan gado tare da lulube mata jiki, ya sani dolene tasha wahala tunda na farkon ta ne. Ya gyara kasan da suka b'ata sannan ya shiga wanka. Bayan ya fito ya zauna a gefenta tare da kura mata ido, wani irin shaukin santa ne ke kara ratsashi, lalai ba shakka zuciyarsa na tsananin san Nafisa. Hannu yasa yana shafar gashin kanta a hankali ya sumbaci goshinta cikin tsananin kauna yace " Nagode Nafisa, da kika jure wulakancin da na miki a baya baki takura na baki takardarki ba, lalai da nayi takaicin rayuwata na kuma yi rashi babba." Kwanciya yai tare da jawota jikinsa ya rungume yanajin dadin dumin jikinta, wannan rana ya manta sam da abinda ya faru dashi domin kuwa farincikin da ya keji ya kawar da waccan damuwar. Nafi kam bacci take sosai, sai asubahi motsin Ashraf ya farkar da ita. Tana bud'e ido kuwa suka hada ido da shi da sauri ta rufe idanta yai murmushi sannan yace " ki jirani yanzu zan dawo in taimaka miki sai kiyi sallah. Bata amsa mai ba wai ita a dole bacci take. Ya fita yana murmushi. Ana idar da sallah ya fito ya dawo b'angarensa ta lulube har kanta da bedsheets din daya rufeta dashi. Yai murmushi sannan ya wuce toilet. Gurin wanka ya toshe sannan ya kunna ruwan dumi, sai da ya taru sosai sannan ya dawo d'aki ya zauna kusa da ita yace " Hajiya Amarya zaki iya bud'e fuskarki." Tana jinshi amma kunya ya hanata bud'ewa hannu yasa ya d'agota cak daga ita har bedsheets din yai toilet dasu. Nafi sai dan motsi takeyi alamar wai bataso. Shikam yana shiga toilet din ya fara kokarin ajiyeta, ganin za'a ajiyeta a kasa yasa tai saurin bud'ewa dan batasan inda suke ba. Ashraf yai dariya yace " why? Kina tsoron kar in yarda ke ne?" Ta juya kanta da sauri, hannu yasa ya kama bedsheets din ya fara kokarin jawota baya tai da sauri wanda hakan yai sanadiyar yayewar zanin gadon sakamakon juyin datai. Idanu ta zaro ganin ba komai a jikinta da sauri ta fara kokarin komawa ta nade cikin zanin gadon, sai dai kafin nan Ashraf ya fizge zanin gadon da karfinsa. STORY CONTINUES BELOW Nafi tasa hannu ta kankame jikinta. Kusa da ita ya matso ya d'agata ya sata a cikin wannan ruwan dumi mai dan zafi sai dai ba zafin dazai kona mutun ba. Yar kara tai sakamakon zafin dataji a gabanta, Ashraf ya sunkuyo tare da zama a gefen gun yace " raguwa kawai." Kallansa tai tace " yaya mai kake kai kuma anan?" Yai murmushi yace " baki gani ba? Matata zan taimakama tai wanka." Idanu ta dan zaro tace " zan iya da kaina." Yace " na sani sai dai banaji zan iya tafiya na barki." Kanta ta kawar gefe batai auni ba kawai taji soso a bayanta da sauri ta juyo ta kalleshi sai dai ta kasa magana. Gira ya d'aga mata yace " kina farin ciki ko? Allah ya baki namiji mai kulawa ko?" Ta d'an yi murmushi kadan a ranta tace " dama yaya....." Bata karasa fadar abinda zata fada a ranta ba taji hannunsa yana wanke mata wuyanta. Kallansa tai a hankali tasa hannu ta rike masa hannunsa,wani irin kallo ya mata mai sagar da gababuwan jiki, a hankali ta zare hannunta. Da kashi ya cud'ata sai daya gama sannan ya mike ya ce kiyi wankan tsarki. Ya juya ya fita. Kallo ta bishi dashi, a hankali murmushi ya bayyana a fuskarta. Shikansa yana fita ya saki murmushi sannan ya kalli kansa a madubin d'akin yace " wai da gaske nine kuwa???" Zama yai a bakin gado sai a lokacin tunanin Dadyn Habib ya fado mai, idanu ya runtse cikin kunar zuci yace " wani kuma abin mamakin zan gani nan gaba??? Ya Allah gani gareka." Motsin Nafi dayajine yasa ya mike ya sa hannu a kugunta ganin tana d'an dingisa kafa kadan, yana kallanta tai sallah bayan ta idar ta dade tana addu'oi sai dai gaba d'aya addu'oin ta akan mijinta takeyi bayan ta shafa ne ta juyo ta kalleshi cikin shagwaba tace " Yaya mai zancema Little?" Cikin rashin kulawa da abin yace " akan me kenan?" Tace " na kwana anan mana." Kallanta yai yace " kice mata kin kwana a gun mijinki, menene a ciki? Ni inaji ma kin dawo nan kenan." Idanu ta zaro tace "bangane na dawo nan kenan ba?" Ya hade rai tamau yace " kwarai, nima inasan matata a kusa dani." Kallansa tai cikin mamaki tace " Sai muzo mu zauna nida yaya nisa ko me?" Yace " Nisa?" sam yama sha'afa da ita. Kallan Nafi yai yace " to sai me?" Baki dan turo tace " ni dai ban yarda ba kabarni a can gaskiya." Ya mike yace " shikenan da alama zanje bikon matata." Gani tai ya mike, da sauri ta riko shi. Juyowa yai ya kalleta ta shagwabe mai fuska ba tare da tace komai ba. Kallanta yai shima fuska a hade bai ce komai ba, sun dade a haka kafin tace " ni fa ba haka nake nufi ba." Ya kunshe dariyarsa yace " then?" Fuskar ta tadan sosa tana kallansa, ya zauna a kusa da ita tarecda jawota jikinsa yace " what are u afraid of?" A hankali tace " Yaya Mumy ba ta....." Yace " wannan ba uzuri bane a guna." Tace " 'yan gidan nan duk......" Yace shima ba uzuri bane a guna." Tace " amma...." Katseta ya sakeyi yace " we have already become one, ya kamata ko menene yanzu mu ajiyeshi a gefe." Kara kwantawa tai a jikinsa tare da d'agamai kai... Tare suka koma bacci lokacin tashinsa nayi ya mike ya shiga wanka, farkawa tai a hankali take tafiya ta shiga kitchen, tayi mamaki ganin ba komai a ciki na kayan abinci sai kawai kayan shayi. Tace " 'yan gidan nan sun saba da a aiko musu da abinci kawai." Ruwan zafi ta hada tayi tunanin fita taje kitchen sai dai tana tsoron kartaje kafin ta dawo Ashraf ya fita. Nan ta jera kayan shayin akan dinning yana fitowa ya ganta a falo. Yai murmushi ya tuna sanda Anisa nanan har ya fitama bata sani ba tana baccinta. Karasowa yai gunta yace " Me yasa kika tashi bayan jikinki ba kwari?" Hannunta tasa cikin nasa sannan ta mike tace " muje kasha ko tea ne naga ba kayan abinci a kitchen din." Yai murmushi sannan suka karasa. Tea ta hadamai mai kauri a hankali yake kurba idanunsa na kanta. Bayan ya gama ne, ya sunkuyo ya sumbaceta sannan ya dau jakarsa yai waje. Kallo ta bishi dashi harya fita. Ashraf yana fita suka hadu da Dan litti nan sukai gun mota. A tsaye sukaga Asim yana ta danna waya da alamar wani yake nema bai sameshi ba. Ashraf ya dauke kai kamar bai ganshi ba, Asim yace " Lala Ashraf wuyanka ya isa yanka dan an karama matsayi shine har zaka iya ganina ka wuce ni?" Kallansa Ashraf yai ya saki murmushi yace " Ai ban kula da mutum anan ba, ya dafatan ka fara sabawa da inda aka maida ka Assistant director." Asim ya kumburo fuska yace " kana tunanin zan yarda da wannan karamin office din?" Ashraf ya kalli Kawu wanda ya taho ta bayan Asim yai murmushi sannan yace " Ayya gashi banaji Kawu zai daukeka daga nan yanzu." Asim cikin masifa yace " kana tunanin Abban ya isa ya barni anan?" Ashraf ya kalli Kawu wanda kalaman Asim suka dakarmai kunne. Asim ya cigaba " in ma kana tunanin Abban ya isa ne to gwara......." "ni kake fadama haka Asim? Kawu yai maganar cikin zafin rai. A tsorace Asim ya juya yace " Abba!" Ashraf ya saki wani murmushin ya hade hannayensa biyu yace " Nabarku lafiya da alama akwai maganar da zakuyi." Yana kaiwa nan ya wuce mota Dan litti yana dariya shima ya shiga sukai gaba. Kawu ya kalli Asim cikin kunar rai, da sauri Asim ya matso yace " Abba abinda ya faru shine....." Wuceshi kawu yai ya shiga mota shima yai gaba. Asim a zuciye ya naushi iska da hannunsa..... Nafi kam yana fita ta gyara d'akin sannan ta fito kamar munafuka ta nufi bangarensu, a hankali take tafiya taje kwanar da zata shiga part dinsu taji ance " kan bala'i daga ina kike?"+ Gabanta ne ya fadi ta juyo a hankali cikin tsananin tsoro, Umma ta karaso cikin huci tasa hannu ta fizgota Nafi ta fadi a kasa. Umma ta kalleta tace " daga gidan ubanwa kike da safen nan???" Nafi ta kalleta tace " ba daga inda nake kawai dai na fito ne." Umma ta nunata da yatsa tace " ke na miki kama da sususu??" Cikin mamaki Nafi tace " Sususu??" Umma ta kara hasala tace " badai a bangaren Ashraf kika kwana ba?" Kasa Nafi tai da kanta da sauri. Cikin tsananin fishi umma tasa hannu ta mangareta da karfinta tace " 'yata tana can ta kasa bacci tabar mijinta saboda ke, ke kuma kinsamu wannan damar kina neman maye gurbinta." Nafi ta d'ago ta kalleta, Umma tace "me? Zaki ramane?? Uban me kikaje yi a bangaren 'yata?" Nafi ta ki dauke ido daga kanta bata kuma bata amsa ba, a zahiri bazata juri dukan nan ba haka kawai ba gaira ba dalili. Umma ta rike haba tace " ke ni kikema wannan kallon??" Nafi tai shiru. Umma ta sa hannu ta kara mangareta tace " dauke idanunki daga kaina." Nafi kam ko gizau idanun nan nakan Umma. Takaici ya kara rufe Umma tasa hannu biyu zata rufe Nafi da duka. Da sauri Nafi ta matsa sannan ta kalleta tace " Umma a matsayina na matar Ashraf banaji zan yarda ki cigaba da dukana kamar wata baiwa." Umma tai sototo tana kallan Nafi, cikin hasala tace " in baki tsaya ba me zakiyi?" Nafi tace " ni dai ki daina dukana, sannan ni ba bangaren 'yarki naje ba bangaren mijina naje, ba kuma naji nayi laifi dan naje can." Tana kaiwa nan ta mike davkyar sakamakon jikinta ta cigaba da dingisawa tai gaba, kallan kafafuwanta Umma tai nan danan ta fahimci komai, tsoro da fargaba suka kamata. Itakam Nafi a hankali ta bud'e kofarsu ta shiga, tana dagowa da niyar ganin Little ko tana bacci, taga Little a tsaye a gabanta daure da towel. Nafi ta zaro ido ta juya da sauri. Little tace " da alama nan gaba kadan zaki gudu daga nan tunda yanzu kunfara dan waken zagaye ke da yaya." ta juya tai toilet." Nafi tadan rufe bakinta sannan ta zauna a gefen gado. Bayan Little ta dawo Nafi ta kalleta tace " kinga sakon ki?" "sakon me kenan?" Nafi ta nuna mata da hannu tace " Ya Habib." Da sauri Little ta mike ta zanyo jakar, ta hau bud'ewa, turaruka ne da wani lace mai masifar kyau, sai dan kunne da sakarsa silver. Little tace " jiya yazo?" Nafi ta daga kai alamar eh sannan tace " do u like him that much?" Little tai murmushi tace " Ni kaina mamakin kaina nakeyi, amma bakya ganin shima yana sona?" STORY CONTINUES BELOW Tausayinta ya kama Nafi, Nafi tai yake tace " kin fadamai tsakanina da yaya?" Little ta girgiza kai, Nafi tace " ki fada mai, kar yaji a gari." a ranta tace mayb inyaji ya shiga hankalinsa. Little ta d'aga kai alamar to sannan ta cigaba da shirin makaranta. *********** Umma kam a zuciye tai bangaren Mumy, ko gaisawa bata bari sunyi ba tace " Ruma hankalinki daya kuwa?" Mumy ta kalleta tace " ban gane wannan banzan zancen ba." Umma ta kara yin hucci tace " wai danki yagama fin karfinki ne? Ko kuwa kin sallamashine yabi duniya?" Mumy wacce kalaman Umma suka bata mata rai tace " wani irin banzan zance ne wannan, taya zakizo har d'akina ki dinga fadar magana irin wannan wacce batada ma'ana." Umma ta tabe baki tace " a ido ne kike nuna mana bakyasan wannan tsinaniyar yarinya ko kuwa har ranki?" Mumy cikin kunar rai tace " har raina mana kema ai kinsani." Umma tacigaba " to in bakiyi wasa ba zaki samu jikar daji, wanda rabin asalinsa ya kasance kidahumin bafulatanin da ko hausa bai sani ba." Mumy tace " banasan kunbiya kunbiya me kike san fada." Umma tace " yarinya ta fara kwana a bangaren Ashraf sannan har jiya ya aikata abinda yakeso, ke wai a sunan uwarsa amma bakisan komai ba sai zaman daki kamar wata gumba." Mumy ta kara hasala tace " inkin gama zaki iya fita ai ko." Umma ta juya cikin takaici tai waje. Zama Mumy tai a bakin gado ta dafa kanta tace " Ashraf!!!!!!" ********* Shikam Ashraf yau ya koma sabon office dinsa a matsayinsa na Chief Director, Kawu dan ya nuna ma mutane yanasan Ashraf da kansa yazo wai zai tayashi murna. Bayan ya shiga ya kalli Ashraf yace " Congratulation d'ana." Ashraf ya kalli Mutanen gun ciki harda Asim sannan shima ya mikamai cikin fara'a, bayan sun gaisa ne Ashraf ya matso kusa dashi yace " thanks but not yet." Kawu ya kalleshi yace " what du u mean?" Ashraf ya sake murmushi sannan ya kara matsowa yace " in naje office din Chairman na Company din nan at that time zan amshi taya murnar ta ka." Kawu ya zaro ido cikin mamaki, ya kalli Ashraf wanda ya sake hannunsa ya karasa ya cigaba da gaida mutane Kamar ba'ai komai. Asim kam a zuciye yai waje ran nan nasa a b'ace. Shikam Ashraf ko a jikinsa suna fita ya zauna sannan yasa waya ya kira Dan Litti, ba'a dade ba sai ga Dan Litti nan yazo. Ashraf yace " Dan Litti inaso daga yau sunanka ya koma Auwal Max, sannan ka fadama mutane hakan sunanka yake, ni kuma yanzu inka fita inaso kaje inda Kawu yake zansa a kiramin kai." Dan litti yamai kallan mamaki sai dai bai tambaya ba sai yes sir dayace. Ashraf yace sainya kira ka sau uku zaka amsa. Yana fita ya shiga neman kawu can ya gashi a sama sai ya wayance da aiki a gun. Shikuma Ashraf dama dan litti na fita ba dadewa ya tura masingansa akan ya nemomai driver dinsa sunan sa Auwal Max in ya ganshi ya kira sunan da karfi. Nan masingan ya amsa sannan yai waje. Dan Litti yana tsaye, gefe kuma kadan Kawu ne tsaye da Asim. Kawu ya kalli Asim yace " kai wai meke damunka??" Asim yace " da akai me kenan?" Kawu ya hade rai yace " ba nace ka dinga kokarin boye emotion dinka ba? So kake kowa ya gane bakasan matsayin da Ashraf ya samu yanzu?" Asim ya hade rai yace " Abba wai ni haryanzu bakamin bayani ba akan wani dalili ne zaka ba waccan yaron matsayi haka? Baka tsoron abinda zai aikata? Ko kuwa yanzu ka dawo kana bin bayansa ne?" Kawu ya bud'e baki zai magana yaji ance " AUWAL MAX!" Cikin tsananin firgice har da sakin takardun hannunsa ya fara waiwaigawa. Masinja ya kara kwalla kira, Kawu ya rikice yana kalle kalle, Dan litti ya zubamai ido, shikansa Asim sai daya fahimta yace " Abba lafiya?"" Kawu kam sai dudubawa yakeyi baiga alamun wanda yake zargi ba duk ya gama rikicewa, sako ne ya shigo wayar dan litti. Yana dubawa yaga sakon Ashraf akan kar ya amsa yaje kusa da masinja din kawai su taho. Haka kuwa akai, Kawu ya duk ya gama rud'ewa dajin wannan suna shikuma Dan litti yaje yaja hannun masinja sukai gaba. Dan litti ya shiga gun Ashraf ya sanar dashi halin da Kawu ya shiga daga jin sunan. Ashraf yai murmushi yace "jeka na gode." Bayan ya fita Ashraf yai shiru yana tunani kafin ya dauko wayarsa ya danna number Dadyn Habib." Bayan sun gaisa yace " Dadyn nikam dan Allah tambaya, kasan wani Auwal Max?" Gaban Dady ne yai mugun faduwa duk yadda yaso ya daure sai da muryarsa ta canza cikin rawar murya yace "Auwal Max?" Ashraf yai dan dariya yace " eh wlh, jiya ne akamin sako akan wai anasan magana dani wai driver din Abba ne Auwal Max, shine nikuma nake tunani kar inje karya yake sannan ni bangama dalilin haduwar mu ba nace bari na kiraka." Dady yai sauri cewa " Don't meet him." Ashraf yace ' naam?" Dady yace " hmm karka yadda Ashraf ku hadu da mutumin da baka sani ba, wayasa me zai maka? Ko mugu ne??" Ashraf ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan yace " nima abinda nake tunani kenan, shiyasa nace bari na kiraka." Dady yace " yauwa Ashraf kayi tunani mai kyau." Nan sukai sallama, Ashraf ya kankance ido tare da yin hucci yace " How can u do this to me???? Tayaya duk a cikin mutane ace kaii!!! Har da......" Kasa karasawa yai ya sa hannu ya rufe fuskarsa.

Post a Comment for "ZUCIYA CHAPTER 19"