ZEHRA CHAPTER 7 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZEHRA CHAPTER 7

ZEHRA CHAPTER 7

- - Post a Comment
ZEHRA CHAPTER 7
EM-ZEE KITCHEN AND CATERING SERVICE Kwance take a kan kujerar tana ta kuka yayinda Hidaya take ta bata haquri.+ Sossai Hidaya take mamakin irin soyayyar dake tsakanin qawarta da Mustapha. A rayuwarta bata taba ganin dedication a soyayya irin nasu ba. Ji nayi Hidaya tace “Babes wannan tafiyar da zai yi ba wai yana nufin ya rabu da ke bane fa, you know cewar he is yours, why are you this bothered??” Cikin kuka Zehra tace “Babes wallahi ni kaina na rasa dalilin da ya sa na kasa samun natsuwa, kawai ina feeling kamar I am about to lose him” Hidaya wadda ta tausaya ma halin da take ciki tace “please calm down my friend, the guy is yours and yours alone, Insha Allah zai dawo zuwa gare ki in no time” Da haka dai ta cigaba da lallashinta tare da fadi mata kalamai masu sanyaya zuciya har ta haqura. ♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Ko da Mustapha ya iso gida a gurguje ya qarasa sashen shi yayi wanka sannan ya shirya cikin wata tsadaddar shadda sky blue mai kyan gaske wadda aka yi ma dinkin zamani. Hular kanshi kamar kullum mai kyau matching colour. Yana sanya cufflinks ne Muhammad ya kira shi a waya. Gani nayi ya dauki wayar ya duba yayinda yayi murmushi. Ko da ya amsa ji nayi yace “Bros gani nan har na shirya, kana ina?” Yace “ina sashen Daddy” Yace “gani nan zuwa” Bayan ya kashe wayar ne ya dauki turaruka ya feshe kanshi da su, aikuwa nan da nan dakin ya dauki qamshi. A yadda yayi kyau kuwa babbar riga kawai zai dora a ce shine angon ma. hehehehe...2 Ko da Mustapha ya isa sashen Daddy a falon shi ya tarar da su tare da baqi wadanda kuwa suke ta haramar tafiya daurin aure wanda za’a yi a Central Mosque bayan sallan Juma’a. Cike da girmamawa ya qarasa wurin mahaifin shi ya miqa mishi hannu suka yi musabaha. Haka duk ya bi abokanen Daddy sukayi musabaha sannan ya koma kusa da Daddy ya zauna a qasa. Gani nayi sun kalli juna shi da Muhammad suka yi murmushi. Yawancin abokanen Daddy ne suke ta tsokanar shi na rashin son shiga mutane yayinda Muhammad yake ta qoqarin kare shi. Mustapha ne ya dan yi gyaran murya yace “Daddy dama ina so in fadi maka immediately after daurin auren Dee zan yi tafiya. I am going to Maiduguri” Daddy yace “A yau dinnan Mustapha?? Emergency ne hala?” Daya daga cikin abokanen Daddy mai suna Alhaji Tukur Abdallah ne yace “hala dai akan rigimar da ake yi ne wanda na ji mun yi asarar sojojin mu dayawa??” Da sauri Muhammad yace “a’a ba wannan issue din bane, he already has a course da zai je. kawai wani routine check ne zasu je” Ya kalli Mustapha yace "right bro??" Mustapha wanda yake kallon Muhammad sai gani nayi yana murmushi a ranshi yace "How on earth can I not call you My guardian Angel..." A fili kuwa yace "haka ne" STORY CONTINUES BELOW Daddy yace “toh ai shikenan, Allah ya kai ka lafiya ya dawo mana da kai lafiya” Murmushi yayi yace “ameen Daddy” Mustapha da Mohammad suka kalli juna yayinda suka yi ma juna murmushi wanda kuwa a hakan sunyi communicating da juna without even talking to eachother. Daddy yace “kayi ma Mummyn ka sallama ko?” Yace “yanzu zan shiga in sanar da ita Daddy” Ya Kalli Muhammad yace “bros mu je” daga nan Muhammad ya miqe yace “Daddy sai mun hadu a masallacin” daga nan suka yi musu sallama suka fita yayinda Daddy ya bi su da kallo cike da so da qaunar yaran nashi. ********* Ko da suka shiga sashen Mummy gaba daya sai aka fara yi musu guda kamar su ne angwayen. Sossai Mustapha yake ta tsare gida domin kuwa shi dama asali ba mai fara’a bane. Zehra kadai take sa shi dariya wanda baya ma sanin yana yi. Muhammad kuwa sai biye musu yake yi yayinda yake ta gaisawa da su. Cikin sallama suka shiga dakin Mummy wadda ta cika da farin cikin ganin su. Sossai take son yaran ta. gani nayi ta bude hannuwan ta suka qarasa suka rungume ta. Kiss tayi musu bibbiyu a kumatu sannan tace “har kun shirya zuwa daurin auren ne?” Muhammad yace “Yes Mummy” Tana kallon su tace “masha Allah kunyi kyau sossai, Allah ya tsare mun ku” Suka amsa da “ameen” Daga nan ne Mustapha yace “uhm Mummy dama zan yi miki sallama ne, I am going to Maiduguri immediately after Dee’s wedding fatiha” Cike da damuwa tace “Maiduguri Mustapha?? Ni fa bana son Maidugurin nan. cikin ‘yan kwanakin nan na ji abubuwan da suke ta faruwa na rashin zaman lafiya” Da sauri ya katse ta yace “I am just going to review something ne Mummy, ba wurin rigimar zan je ba. Just give me your blessings” Ta rungume shi tare da fadin “Allah ya tsare mun kai Mustapaha na” Ta janyo Muhammad shima tace “Allah yayi muku albarka gaba daya” Suka amsa da “ameen” Matan da suka fara shigowa dakin ne yasa suka fita. Ko da suka fito kuwa Muhammad ya cigaba da gasiawa da 'yan uwa tare da tsokanan ‘yan dattijan cikin su ana ta dariya. Shi kam Mustapha gaba daya ma hankalin shi baya kan su. Ganin Muhammad ya tsaya hira da wata ‘yar uwar su ne Mustapha yace mishi “bros let me go say bye to Dee kafin ku gama, ina zuwa” ********* A lokacin da ya nufi sashen Fadeela kuwa cike da ‘yan mata. Tunda ya shiga suke ta kallon shi yayinda suke ta maganar shi. Sossai sun qyasa yayinda kowacce take yaba kyan tsarin shi suna ta wishing ace saurayin ta ne.2 hattara babes... this one is taken!! Ah toh4 Gani nayi Mustapha ya tsaya yayinda ya dan kalli daya daga cikin su yace “where is Dee?” Yusra wadda ta sa mishi ido bata ma ji abinda yace ba. Gaba daya hankalin ta yayi nisa a kallon shi. Hauwa wadda ta fito daga dakin Fadeela ce ta ganshi. Da sauri tace “Ya Musty ina wuni” Shi kam bai ma san ya akayi ta san sunan shi ba amma kuma he is glad ya samu wadda zata bashi amsar tambayar shi because from all indication wadda ya tambaya da farko kurma ce. STORY CONTINUES BELOW abinda yayi tunani kenan3 Ji nayi yace “Lafiya, please call Dee” Tace “ka shiga, Make up ake yi mata” Bai ce komai ba ya shiga dakin. Yusra wadda take ta kallon shi ce ta lumshe idanuwa tace ma Hauwa “ke waye wannan Handsome din?” Hauwa tana dariya tace “Yayan Fadeela ne kuma saurayin Zehra don haka stay away” Yusra tace “kut, wai dama wannan handsome din ne Babyn Zehra din da suke maqale a waya kullum? Gaskiya Zehra tayi sa’a. Allah ya bani mai koda rabin kyan shi ne” Gaba daya suka fashe da dariya. Fadeela wadda take zaune a gaban Millie Mamza ce ta ga Mustapha ya shigo. Zaro idanuwa tayi tace “Ya Musty what are you doing here?? Zehra bata nan ai” Murmushi yayi yace “I know Dee, I came to see you” Ji nayi tace ma Millie “excuse me please” Aikuwa tana miqewa na ga Mustapha ya zaro idanuwa tare da dan matsawa baya yace “what the hell Dee, kin ga fuskar ki kuwa?? I swear you have ruined your face” Millie Mamza da team dinta ne suka fashe da dariya tare da mamakin reaction dinshi kamar ya ga ghost. Fadeela wadda take dariya tace “Ya Musty ai ba’a gama ba, duk za’a yi blending din foundation din and..” Dakatar da ita yayi yace “all the best Dee” Tana murmushi tace “why are you here??” Yace “I came to say good bye, zan yi tafiya zuwa Maiduguri immediately after your wedding fatiha” Gani nayi ta bata rai tare da fadin "Haba Ya Musty, zaka yi tafiya on my wedding day?? not fair" Yace "I am so sorry Dee, tafiyar ta taso ne kawai" Gani nayi ta matsa kusa da shi zata rungume shi yayinda yayi saurin ja baya yace “What the hell, kina so ki bata mun riga na ne da wannan fentin?” Sossai su Millie suke ta kwasar dariya. Fadeela wadda ta qara bin shi tace “wallahi sai nayi hugging dinka, kawai ka tsaya yadda bazan yi staining maka kayan ka ba” Akan dole kuwa ya tsaya tayi hugging dinshi tare da fadin “Allah ya tsare Big bro, Allah ya dawo da kai lafiya” Yace “ameen Amarya, Congratulations to you. Allah ya sanya alkhairi. dont forget to go through the Du'a I gave you” Tace “thank you, Insha Allah bazan manta ba” Bayan sunyi breaking hug dinne tace “ka sallami Angel din taka dai ko??” Yana murmushi yace “we have been together ai tun da safe” Ya riqe hannuwan ta yace “dukda na san you are the bride and will be extremely busy please I want you to take care of her, Calm her down idan ta shiga damuwa because I didn’t like the way I left her” Fadeela tana murmushi tace “don’t worry Bro, she will be fine Insha Allah” Kiran Muhammad ne ya shigo wayar shi yayinda ya daga mata wayar yace “Moha yana jira na let me go, we don’t wanna miss our Baby Dee’s wedding fatiha right?” Fashewa tayi da dariya yayinda ya juya yana fadin “sai munyi waya” ita kuma tace “Allah ya tsare”  STORY CONTINUES BELOW CENTRAL MOSQUE ABUJA Bayan sallar Juma’a ne aka daura auren Zain da Fadeela akan sadaki naira dubu dari. Sossai wannan biki ya samu halartar manyan baqi daga jihohi da daman a qasar mu. Dayake dai Papa da daddy manyan mutane ne sossai abokanen su sunyi musu kara. Bayan daurin auren ne suka dinga gaisawa da mutane yayinda Ahmed Zol ya dinga daukar hotuna. Su Col. Y M Bamanga kuwa bayan sun gagaisa da su Daddy ne suka ce ma Mustapha su zasu wuce Barrack inda zasu fara shiri kafin ya qaraso. Shi dai Muhammad dama dayake sarkin son jama’a ne ko ina ka hange shi zaka ga fuskar shi kamar gonar auduga sabanin Mustapha wanda da an qyale shi ma tafiyar shi zai yi. two different personalities🤣 Tuni aka fara tafiya Reception a Guest house din Daddy wanda kuwa ma’aikatan Zehra sun gama shirya abinci kala kala don tarbar baqin. Muhammad shine ya tafi da Mustapha Barrack inda zai hadu da colleaques din shi don su tafi. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤  Fadeela da Zain👆 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ LUNGI MAITAMA BARRACKS ABUJA A lokacin da Muhammad ya kawo shi Barrack din straight Gidan shi na Barrack din suka nufa inda zai shirya kafin su tafi. Tare suka shiga gidan yayinda Muhammad yake fadin “Your Backman is really keeping the house clean Musty, ka ga gida spotless??” Mustapha yayi murmushi yace “gaskiya babu laifi the guy is trying, Ka san fa ban taba kwana anan ba” Muhammad yace “haba? Why? dukda wannan elegant decor din da kayi ma gidan?? the place is cool ai” Mustapha wanda yayi displaying mamaki yace “cool a ina bros?? don Allah ka bari” Yana murmushi ya girgiza kai tare da fadin “hmm, kai da principles dinka. I really want to see the kinda house da zaka gina” Mustapha yana dariya yace “idan na dawo ma zaka zana mun please, zan dinga yi maka bayani kana zanawa” Muhammad yace “anya zan iya kuwa?? Kasan fa kai komai naka daban ne” Mustapha yace “zaka iya bro” Wayar Muhammad ce tayi ringing. Ko da ya duba sunan Daddy ya gani yayinda ya amsa da sauri harda russunawa kamar yana gaban shi. yaran Daddy very obedient I tell you.. Muryar Daddy ya ji yana fadin “kana ina ne? baka sauke Mustaphan bane??” Yace “na sauke shi Daddy gani nan” Bayan ya kashe ne yace “toh Brother I guess this is our goodbye” STORY CONTINUES BELOW Mustapha ya miqe tare da qaraswa wurin shi ya rungume shi yayinda yace “I am going to miss you bro, You just returned and we couldn’t even have time to discuss about things that happenend in our lives” Muhammad wanda yake shafa bayan shi yace “don’t worry bro, idan ka dawo we will have more than enough time for that. I pray Allah protects you as you embark on this mission” Yace “thanks a lot bro, take care of everyone, I love you” Muhammad yace “Love you too bro and all the very best” Muhammad kuwa yana ta jira Mustapha yayi breaking hug din amma ya qi. Ji nayi yace “hey, can I go??” Mustapha ya sake shi tare da fadin “I am sorry, go ahead” Tare suka fashe da dariya yayinda Muhammad yace “Okay na tafi, sai mun yi waya” Bayan ya fita ne na ga Mustapha a tsaye inda ya bar shi yayinda yayi zurfi a tunani. Ajiyar zuciya ya saki tare da fadin “why do I feel like something is about to go wrong??” Da ya kasa ba kanshi amsa ne na ga ya nufi hanyar dakin shi don canza kaya. ********* Bayan ya gama shirin shi tsab ne ya ji wayar shi ta fara ringing. Ganin sunan ta ne na ga ya girgiza kai yana murmushi yayinda ya zauna a kan gadon dakin sannan ya amsa. Muryar ta very low ya ji tana fadin “Baby ka tafi ne??” Yace “nope, amma dai any moment” Ji yayi tayi shiru yayinda yace “hey are you on the line?” tace “yes” Yace “me kike yi?” Tace “Ina kwance ne a daki, ana yinin biki and everyone is outside” Yace “ke why are you not with them??” Kai tsaye tace “because I am sad Baby, wallahi bana so ka tafi” Shiru ya dan yi sannan yace “yi haquri Angel, I will be back before you know it” Turo baki tayi tace “yanzu babu abinda zan iya yi da zan hana ka tafiya??” Murmushi yayi yace “akwai abubuwa dayawa da zaki iya yi ki hana ni tafiya but please my Angel don't" Murmushi tayi sannan tace "I won't, ban ga gayun da kayi na daurin aure ba, ka dauki hoto?” Yana murmushi yace “yes My angel, na san baki gani ba shiyasa na dauka. Bari idan mun gama waya zan aiko miki” Haka dai suka cigaba da hira wadda yawanci ta lallashi ce. Da qyar ta qyale shi suka yi sallama. Bayan ya kashe wayar ne kuwa ya tura mata hoton. ********** A lokacin da saqon hoton ya shiga wayar ta kuwa da sauri ta bude yayinda na ga tayi shiru tana qare mishi kallo.  Dafa qirjin ta tayi tace “Ya salaam, I really cant survive without you My Charming prince” Gani nayi ta kai bakin ta kan wayar tayi kissing din hoton yayinda tace “I will surely miss you my Baby, Allah ya dawo mun da kai lafiya” Ni kuwa nace “ameen” Haka nan ta cigaba da kallon hotunan shi a waya. Yinin biki kuwa har sai da aka kusa gamawa sannan ta fita. Shima sai da amaryar tayi aike har ta gaji. Khadeeja ce tayi nasarar fitar da ita. ♤♤♤♤♤♤♤. ZAIN ABU-YAZEED RESIDENCE Tuni an kawo amarya fadeela gidan ta wanda yake cikin Maitama.+ Gidan Fadeela dai lafiyayyan Duplex ne wanda ya qawatu da kayan zamani. Idan ka shiga gidan ma mantawa zaka yi da cewar qasar mu Nigeria kake domin kuwa tsarin gida ne kamar a turai. Tsaye take a gaban madubin dakin Fadeela sanye cikin wani Royal Blue Material mai shegen kyau wanda Hudayya ta dinka mata. Kallon kanta take yi yayinda take yaba kwalliyan da Fati Mamza tayi mata. Ji nayi tace “As simple as I want it, thank you so much Fati” Fati Mamza tace “its okay dear, looking forward to glamming you up on your wedding day” Zehra ta dan yi murmushi tace “Oh Allah, Har kin sa na tuno shi. I am missing him badly I swear” Ta dafa Vanity table din tace “why does he have to go today?” Fadeela wadda Dazeita take ta qoqarin kammala mata make up din ta ne tace “relax Angel din Baby, you will see him soon” Zehra tayi murmushi tare da matsowa kusa da Fadeela ta tsaya. Ji nayi tace “wooow, look at my Sister inlaw looking all beautiful. I swear yayana yayi sa’ar mata” Gaba daya aka fashe da dariya yayinda Dazeita tace “all done Ma’am” Haka qawayen ta ma suka dinga yaba kyan da tayi. Fadeela wadda ta miqe tsaye tace “Thanks Millie” Kallon kanta tayi a madubi tace “whoa… Good job Millie” aikuwa daga nan su Zehra suka fara kashe mata hotuna yayinda suka cigaba da yaba kyan da tayi. Fadeela dai sanye take cikin wani tsadaden material tan colour wanda Kathyanthony ta dinka mata. Basu ankara bane suka ji ance motocin kwasar amarya da qawayen ta sun iso don haka ne aka fara haraman tafiya Dinner. Zehra dai motar Amarya da Ango ta bi wanda kuwa ta dinga yi musu tsiya a hanya. Fadeela ce tace “Allah ya kaimu ranar bikin ki da Ya Musty ki ga yadda zanyi miki" GOLDENBIRD MARQUEE AND EVENT CENTER Wurin cike yake da manyan baqi yayinda kowa yayi shiga ta alfarma. Sossai décor din wurin yayi masifar kyau. A lokacin da motar amarya ta iso kuwa MC ya fara sanarwa yayinda yake ta yi musu kirari. Wannan Dinner din kuwa harda su Papa da abokanen su don haka ne hall din ya cika sossai. Kamar dai kowanne biki haka qawayen amarya da abokanen ango suka bi trail suka shigo. Sossai suka birge mutane. Tunda suka shigo shahararren mai daukar hoton nan wato Ahmad Zol yake ta kashe musu hotuna. George okoro ma ba’a bar shi a baya ba. Bayan sun qarasa wurin zaman su ne na ga qawayen amarya da abokanen ango ma sun juya sun nufi wurin zaman da aka tanadar musu.  STORY CONTINUES BELOW Zehra wadda take shirin zama kan kujerarta ce ta ji ance “excuse me Ma’am, can I give you a shot please?” Juyowan da tayi ne ta ga George Okoro a bayan ta yana murmushi. Zehra tana murmushi tace “oh my God, George how are you?” Yana murmushi yace “fine dear, you look beautiful” Tana murmushi tace “thank you” daga nan kuwa tayi posing ya bata wasu shots masu zafin gaske. 7 Tuni MC ya fara aikin shi. Bayan Anty ta bude taron da addu’a ne aka cigaba da gabatar da shirin. Zehra tana zaune gani nayi ta riqe wayar ta tana ta typing message yayinda take murmushi. Ko da na leqa gani nayi ta tura saqo kamar haka: “Yes Baby, me kake yi??” Reply na ga ya aiko kamar haka: “Nothing My Angel, yanzu muka gama meeting and here I am on the bed missing you terribly” Gani nayi tayi murmushi ta tura mishi da message kamar haka: “nima ina ta missing dinka Baby na, gaba daya ma bikin Dee baya yi mun dadi” Ya turo Mata reply kamar haka: “Kar ki damu, I will try and finish up everything in dawo gida, gobe zamu je qauyen idan mun gama binciken da wuri within the week ma zan dawo” Gani nayi ta bata rai sannan ta tura mishi message kamar haka: “wallahi bana so in ji kayi maganan qauyen nan, please be careful and try as much as possible not to fall ill” Tana jiran reply dinshi ne ta ji MC yace “I would like to call on stage the bride’s best friend and sister to the groom in person of Zehra Abu-Yazeed to please come and say something about them” Gaba daya hall din aka fara tafi yayinda Zehra ta miqe riqe da wayar ta tana karanta saqon Mustapha inda yace: “I will my angel, don’t forget to send me a picture of you, I wanna see how beautiful you looked tonight” Tana tafe na ga tayi typing mishi message kamar haka: “I will My Baby, gotta go give my speech…just wait for me please” *********** Zaune yake tare da abokanen shi yayinda suke hirar bayan rabuwa. Jin an kira sunan Zehra ne na ga ya mayar da hankalin shi kan stage din yayinda yake ta jiran ganin mai muryar da take yawo a cikin qwalwar shi wadda ta hana shi sukuni tun lokacin da ya ji ta.4 Ni kuwa nace babbar magana🤣🤣 A lokacin da Zehra ta qarasa wurin MC din ne yace “takawar ki lafiya sarauniyar mata” ya miqa mata Mic din yayinda yace “over to you” STORY CONTINUES BELOW Juyowar da Zehra tayi yayi daidai da bugawar zuciyar shi. Gani nayi ya dafe qirjin shi yayinda yace “hasbunallahu wani’imal wakeel” Daya daga cikin abokanen shi mai suna Bash ne yace “Moha ya akayi ne?” Muhammad wanda ya kafe Zehra da idanuwa ne yace “nothing” Bai ankara ba muryarta ta daki kunnuwan shi inda tace “Asalamu’alaikum everyone, My name is Zehra Abu-Yazeed, a sister to the groom and best friend to the bride. Funny right?” Gaba daya aka fashe da dariya yayinda ta cigaba da fadin “Well, I am supposed to say something about these lovebirds but what can I say?? I believe each and every one of us won’t be here if we really don’t know them, right??” Ta cigaba da fadin “Both of them are a definition of greatness…” Ta juya ta kalli su Fadeela tace “I am sure you will be more than glad you chose each other as companions. I pray Allah bless your union and as you embark on this journey of marriage, may it stand the test of time and may you be blessed with beautiful kids… Ameen”2 Ai kuwa tana gamawa aka dinga yi mata tafi yayinda MC ya karbi Mic din yace “thank you very much for this wonderful speech Miss Zehra the CEO of EM-ZEE kitchen and catering service..” Muhammad wanda yake zaune kuwa gaba daya Zehra ta gama birge shi. A zuciyar shi ne yace “Its definately love at first sight”3 oh oh oh...🙄🙄3 Haka dai aka cigaba da bikin yayinda aka yi rawa aka ci aka sha. Sossai aka dinga yaba kalolin abincin da aka yi serving. (courtesy of EM-ZEE Kitchen and catering service) Rawar Ango Zain da Fadeela amarya kuwa sossai tayi kyau. Wani slow music aka sa musu yayinda suka fito suka taka cike da so da qaunar juna. MC kuwa sai kirari yake yi musu. sai da suka taka son ran su sannan aka bada damar mutane suyi joining dinsu 4 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Gaba daya tunda Muhammad ya ga Zehra idanuwan shi suna kanta, duk inda ta nufa sai ya bi ta da kallo. Zuciyar shi kuwa gaba daya ta karkata gareta. Muryar ta kawai ke yawo a cikin qwalwar shi. He has never felt this before, could it be that he has found the One??4 Zehra dai tana nan zaune a kan kujerarta tana ta chatting da Mustapha. A lokacin ne ta aika mishi da hoton gayun da tayi. Tana jiran Reply dinshi ne ta ga kiran shi ya shigo. Gani nayi tayi murmushi sannan ta miqe da sauri ta fita daga hall din. STORY CONTINUES BELOW Muhammad wanda idanuwan shi suke kan ta gani nayi ya miqe tare da fadi ma abokanen shi “Guys ina zuwa” where the hell is he going to??11 ♤♤♤♤♤♤♤ Zaune take a harabar wurin wanda babu hayaniya. Tana ta murmushi yayinda take sauraron shi yana fadin “kin yi kyau sossai my Angel. Gaskiya I am jealous don nasan guys suna ta kallon ki. Oh my God”1 A daidai wannan lokacin ne Muhammad ya qaraso wurin. Gani nayi ya tsaya yayinda ya ji ta fashe da dariya tace “Kar ka damu, Zehra taka ce kai kadai insha Allah. I swear Baby ban taba missing dinka kamar wannan tafiyar da kayi ba. Da safen nan fa muka rabu amma wallahi ji nake kamar mun shekara bamu ga juna ba. Kai ma haka kake ji ko dai ni kadai ce??” Fashewa yayi da dariya yace “the feeling is mutual My Angel, A yadda nake jin ki fa ko mutuwa nayi kina nan cikin zuciya ta, wannan fact ne” Cike da farin ciki tace “ni kuwa wane abin kirki nayi a duniyan nan da Allah ya bani kai??” Yana dariya yace “nothing My Angel, I guess our match was made right from heaven” Bata rai tayi tace “Gashi duk tsarin da muka yi na zuwa bikin nan tare ya zama shattered” A dayan bangaren ne Mustapha yace “don’t worry my Angel, haka Allah ya tsara” Ji yayi tace “toh Allah yasa a cikin tsarin akwai auren mu tare da kasancewa da juna har abada” Sossai wannan maganar kuwa ta bashi dariya yace “My angel you are crazy and the more reason why I love you” Tace “I love you too my Baby, Allah ya kaimu ranar da zan gan ni a cikin gidan ka a matsayin matar ka, can’t wait to sleep and wake up by your side every blessed day” Shi dai Mustapha dariya kawai yake yi yayinda yace “cant wait to have you by my side too, to hug you tight, kiss you all over and show you how much I really love you.. My Angel, you are simply my life” Cike da kunya ta rufe idanuwan ta yayinda tace “oooh Allah, amma dai kasan zan dinga hana ka fita ko?? Wallahi Baby kawai retire yakamata kayi, I promise to do everything for you” Yana dariya yace “not again my angel, idan nayi retire ta ya zan kula da ke da yaran namu??” Cikin shagwaba tace “toh ba ga Catering service dina ba?? We will survive Baby” Mustapha dai yana ta kwasar dariya. A yadda tayi maganar ya tabbatar da gaske take yi. Ji tayi yace “honestly My Angel I wouldn’t want that, I want to give my family a luxurious life. Ina so ku zama contented yadda bazaku taba neman komai a rayuwa ba. Addu’a nake yi Allah ya bani arzikin da zan iya baku duk wani abu na jin dadin rayuwa wanda kuka nema da wanda ma baku nema ba” Tana murmushi tace “Ya Allah, Baby wallahi idan na rasa ka ban san wane hali zan shiga ba. I am sure there is no one better than you a fadin duniyan nan. I love you sooo very much” Ji tayi yace “but wait, kamar kin ce idan nayi retire zakiyi mun komai?? Like everything??” Tana dariya tace “wallahi komai My baby, zan dafa maka abinci in baka a baki sannan zan sa ka bacci zan kuma tashe ka. Again, zan..” Ji tayi yace “zaki dinga yi mun wanka??..” Kafin ya qarasa maganar shi kuwa tace “whaaat?? Wanka Baby??” Fashewa yayi da dariya yace “yes” Cike da kunya tace “ah, gaskiya bazan iya ba” Kai tsaye yace “no deal” Da sauri tace “idan na amince zan dinga yi maka zaka yi retire dagaske??” Shi kam sossai dariya Zehra take bashi yayinda yace “nope My Angel, bazan yi retire ba kuma zakiyi mun trust me” Turo baki tayi ba tare da tace komai ba. Bata ankara ba ta ji hayaniyar mutane wanda kuwa hakan ya tabbatar mata da lallai an gama dinner din ne. Tashi tayi tsaye tace “na shiga uku Baby, an tashi daga dinner ina nan. Nasan Dee zata ci qaniya na” Murmushi yayi yace “don’t worry she won’t scold you” Tana tafe zata koma ciki ne tace “I swear i am going to be in trouble, kai baka nan sannan Dee is going tomorrow. I am so going to miss you guys” Yace “I am sorry My Angel, Zan dawo as soon as possible insha Allah. Wanne country zasu je?” Tace “London sannan zasu je Umra before coming back” Yace “hmm, Interesting” Haka dai suka cigaba da hira har ta koma ta shiga hall din. Wait, Muhammad??? Shin yana ina?? Ba yana tsaye a wurin ba??21 Har ga Allah na manta da shi... I was carried away by our lovebird's Conversation..☹☹15 yana ina?? ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ oh oh oh... MUHAMMAD OMAR TAFIDA RESIDENCE Zaune yake a tangamemen falon gidan shi wanda ya qawatu da kayan zamani. Sossai gidan Muhammad ya hadu, tsarin turawa ne sak sannan everything to his taste.+ (abinka da mai zanen gida da kanshi) Idan kana cikin wannan gida mantawa kake da komai domin kuwa gida ne kamar aljannar duniya. Tunda ya bar venue din da aka yi dinner din Fadeela ne ya nufi gidan shi domin kuwa sossai zuciyar shi take tafasa. Gani nayi ya zame daga kan kujerar yayinda ya kwanta a kan lafiyayyen Chinese rug din da yake falon.7 Sossai kalaman ta suke amsa kowa a cikin qwalwar shi. "Kar ka damu, Zehra taka ce kai kadai insha Allah. I swear Baby ban taba missing dinka kamar wannan tafiyar da kayi ba. Da safen nan fa muka rabu amma wallahi ji nake kamar mun shekara bamu ga juna ba. Kai ma haka kake ji ko dai ni kadai ce??" "I love you too my Baby, Allah ya kaimu ranar da zan gan ni a cikin gidan ka a matsayin matar ka, can't wait to sleep and wake up by your side every blessed day" "oooh Allah, amma dai kasan zan dinga hana ka fita ko?? Wallahi Baby kawai retire yakamata kayi, I promise to do everything for you" "toh ba ga Catering service dina ba?? We will survive Baby" "Ya Allah, Baby wallahi idan na rasa ka ban san wane hali zan shiga ba. I am sure there is no one better than you a fadin duniyan nan. I love you sooo very much" Idanuwan shi a rufe yayinda na ji yace "ko ma waye wannan yayi sa'ar samun true love.. she is definately into him and babu abinda zan iya yi da ya wuce inyi haquri"9 Can kuma yayi tsaki yace "why didn't I met her earlier??" Tashi yayi ya koma kan kujera ya zauna yayinda ya dafa kai yace "Oh Muhammad, can you deal with this??" Ya shafa kan shi sannan yace "dole in cire ta daga zuciya ta before I fail.."3 fail???🤔🤔🤔 Daga nan kuwa gani nayi ya dafe qirjin shi daidai saitin da zuciyar shi take yayinda ya kwantar da kanshi a kujera ya fara addu'a kamar haka: "bis-mil-lah" sau uku Sannan ya cigaba da fadin: "a'udhu billahi waqudratihi min sharri maa Ajidu wa uhaadhir" har wurin sau bakwai. Da alama abu ne da ya saba yi.. hmmmm.. ZAIN ABU-YAZEED RESIDENCE Da safe gaba daya qawayen amarya suna falon ta suna breakfast suna ta hira sannan suna ta kallon TV. Kwance take a kan gadon dakin Fadeela yayinda take ta kallon hotunan shi a waya. Sossai take missing dinshi. Ta kira wayar shi amma a kashe. Gaba daya babu abinda yake yi mata dadi a rayuwa. Babu wanda take son gani idan ba shi ba. STORY CONTINUES BELOW A yanzu da babu halin ganin shi kuwa she can manage listening to his voice amma hakan ma ya faskara. Gashi bata samu wani baccin kirki ba jiya. This is just one day she thought.. Gani nayi ta fashe da kuka yayinda take fadin "na shiga uku, Baby what have you done to me??" A daidai wannan lokacin ne Fadeela ta fito daga bathroom daure da towel. Da alama daga wanka ta fito. Ganin Zehra kwance a kan gado tana ta share hawaye ne tayi mamaki matuqa. Da sauri ta qarasa ta haye kan gadon ta dafa ta tare da fadin "Zee what is it?? Tunanin shi kike yi ko?" Zehra wadda ta tashi zaune tace "Wallahi Dee ina missing din shi sossai, it's just one day but I swear its feeling like a year" Ta dafa qirjinta daidai saitin inda zuciyar ta take tace "my heart is seriously aching. Yanzu haka muryar shi kawai nake so in ji ko zan samu in ji sanyi" Fadeela tace "Babes relax, ki kwantar da hankalin ki Insha Allah ko sati daya bazai yi ba na tabbatar zai dawo. I am sure a yanzu haka duk abinda yake yi shima hankalin shi yana kan ki. Honestly Zehra, soyayyar ku tana masifar birge mutane. All my friends are talking about you guys. Allah ya cika muku burin ku" Murmushi Zehra tayi yayinda take share hawayen ta tace "Ameen Dee" Fadeela ta sauka daga kan gadon ta koma wurin Vanity table ta zauna bisa stool yayinda tace "Na San dai auren ku will be very soon tunda dai tafiyar zuwa Italy is very much near" tana murmushi tace "I will be more than happy for that. I swear ban taba sanin cewar zan so wani namiji kamar yadda nake son shi ba. A yadda nake jin baby fa wallahi duk laifin da yayi mun da wanda bai riga yayi mun ba na yafe mishi"3 Fadeela ta zaro idanuwa tace "whaaaat? Ko kishiya yayi miki nan gaba kin yafe??" Murmushi tayi tace "wallahi na yafe Dee, kawai dai zan nuna fushi na amma kuma deep down I will forgive him because I love him unconditionally" Whoa... who would do that?? where are the ladies??🤣🤣9 Fadeela tana dariya tace "aikuwa Ya Musty yayi sa'a, shima fa bala'in son ki yake yi domin kuwa for you he has changed completely" Haka dai suka cigaba da hira wanda duk yawanci na Mustapha ne. Ita dai Fadeela she is only trying to keep her company domin kuwa ta sani sarai she is sad. Da qyar ta lallaba ta tayi breakfast sannan ta koma kan gado tayi bacci. Tuni abokanen ango suka zo suka sallami qawayen amarya. Har aka yi aka gama kuwa Zehra tana ta bacci domin kuwa a gajiye take sossai. ♤♤♤♤♤♤♤ Wuraren qarfe goma sha biyu da rabi ne suka shigo dakin riqe da hannun juna. Kwance take cikin duvet tana ta bacci yayinda gashin kanta duk yayi buzu buzu. Zain wanda yake rungume da Fadeela girgiza kai yayi yace "Ah lallai kam, my sister is completely exhausted" Fadeela tana murmushi tace "I swear at a point in time na dauka ma zata yi breaking down, tunda aka fara bikin nan fa bata zauna ba sannan ga tafiyar Ya Musty kuma duk ya dagula mata lissafi, tana missing dinshi terribly" Zain yace "ayah, na ji Papa yace zasu zauna a sa ranar bikin su ai" Cike da murna tace "dagaske??? Oh I am soo happy" STORY CONTINUES BELOW Gani nayi ya janyo ta ya rungume ta yace "speaking of happiness my sweetheart, I am extremely happy I got you finally" Cikin shagwaba tace "me too" Gani nayi ya dago fuskar ta yana kallon ta cike da so da qauna yayinda yace "I have long been waiting for this moment" cike da confusion tace "what moment??" Yace "this.." daga nan kuwa yayi locking lips dinta da nashi. Fadeela dai zaro idanuwa tayi yayinda ta ji ta a cikin wani planet na daban. Wani yanayi ta shiga mai dadin gaske. Tuni ta saki jiki sukayi intensifying kiss din wanda kuwa bata ankara ba ta ji ya tura ta jikin bango. Zain wanda ya haukace tuni ya fara neman zarcewa kawai sai suka ji muryar ta tana fadin "oh oh oh, Ya Zain a gabana??" Da sauri suka juyo suka ganta zaune a tsakiyar gadon yayinda take kallon screen din wayar ta. Runtse idanuwa yayi yayinda yace "Haba Zee, ki rasa lokacin tashi daga bacci sai yanzu??" Fadeela da Zehra suka fashe da dariya yayinda Zehra tace "yi haquri bros, ni kam bari inyi wanka ma in bar muku gidan tunda dai da alama a nan za'a fara honeymoon din" Da sauri Zain yace "I swear Zee bakya jin Magana" Ya kalli Fadeela yace "zo mu je daki na.." Da sauri ta matsa nesa da shi tace "na qi wayon" yayinda ta kalli Zehra tace "and you are not going anywhere" Yace "please mana" tana murmushi ta koma wurin Zehra kan gado ta zauna tare da fadin "Zamu hadu a London" Zehra wadda take dariya tace "Ya Zain is in trouble" Hararar su yayi sannan ya nuna Fadeela yace "I will catch you" gwalo tayi mishi sannan ya fita. Aikuwa yana fita na ga Fadeela ta lumshe idanuwa tare da shafa lips dinta tace "Ya Allah, it was so sweet" Zehra wadda ta cika da mamaki tace "Iyeeeh, Lallai abun babu sauqi. Toh ko zaki bi shi ne??" Fadeela wadda ta kwanta a kan pillow tace "I would love to do that amma zan daure sai mun tafi London, the new story is supposed to start there" Haka dai suka cigaba da hirar su yayinda Zehra ta dinga tura ma Mustapha messages tana fadi mishi how much she misses him and how very much she loves him dukda kuwa ta san wayar shi a kashe ne tasan duk lokacin da ya kunna zai gani. Ayyaaahh...2 ♤♤♤♤♤♤♤ Da yamma ne su Fadeela suka tafi. Har Airport Zehra ta raka su. Fadeela tayi ta kiran wayar Muhammad don tayi mishi sallama amma har ta gama ringing baya dauka. A tunanin ta qila yana hutawa ne a dalilin gajiyar tafiya don haka ne ta tura mishi text message. Haka suka tafi Zehra tana ta kewar qawarta. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Duk yadda kuke tunanin halin da Zehra zata shiga abin ya wuce nan domin kuwa gaba daya ta daina fita ko ina. A koda yaushe tana dakinta tana tunanin shi. Ta sani cewar a baya Mustapha yana yin tafiya, bata taba shiga tsananin damuwa kamar wannan ba. ta rasa meyasa this time around abin ya zama different. Messages din da ta aika mishi kuwa babu adadi. Lokutta da dama takan zauna tayi ta rusa kuka haka kawai. STORY CONTINUES BELOW Gashi Fadeela da take yawan zama tana yi mata hirar shi bata nan. A koda yaushe Anty da Khadeeja ne masu zaman lallashi.2 OMAR TAFIDA RESIDENCE A yau kwana biyar kenan da Mustapha yayi tafiya. Sai yau ne ragowar baqin da suka zo bikin Fadeela suka tafi gida. Tun safe kuwa ake ta gyaran gidan domin kuwa gaba daya gidan ya birkice. Ma'aikatan gidan dai sun aikatu amma kuma in the end gidan ya koma spotlessly clean. Zaune suke a falon Daddy dadaddare yayinda suke ta hira. Mummy ce tace "ni kuwa yaushe za'a zauna a sa ranar bikin yaran nan ne?? na ga fa ba da dadewa ba Mustapha zai tafi Italy dinnan, ai gwara ayi auren su tafi tare, ko ya ka gani?" Daddy yace "aikuwa haka ne. kin ga gaba daya bikin Fadeela ya dauke mun hankali" Ya janyo wayar shi yayinda yake fadin "bari in kira Papa muyi maganar" Ko da ya kira aminin nashi bayan sun gaisa ne Daddy yace "Maganar sa ranar yaran nan yaushe ne zamu zauna ne?" Papa wanda yake murmushi yace "ai ko gobe ma idan dai kun shirya, ni kam ai tuntuni na ba Mustapha Zehra, wannan din ma don dai formality ne dole mu bi" Daddy yana dariya yace "masha Allah, Insha Allah gobe sai mu zo, Allah ya bar Zumunci" Papa yace "Ameen, ai gwara a yi bikin kowa ma ya huta, gata nan tunda ya tafi an rasa gane kanta. Kullum tana daki ana ta fama da ita" Daddy yana dariya yace "Allah sarki. Gashi ba'a samun shi a waya" Papa yace "Allah dai ya dawo da shi lafiya" Haka dai suka dan taba hira sannan suka yi sallama. Bayan Daddy ya fadi ma Mummy yadda suka yi ne tace "toh masha Allah, Allah ya kaimu" yayinda yace "Ameen" Daddy ne yace "ni kuwa Muhammad fa? Kin ga fa ban fadi mishi zancen ba, ko kin fadi mishi ne?" Mummy tace "wallahi ban sanar da shi ba, ka san hidimar bikin nan gaba daya abubuwa sun yi yawa amma ina kyautata zaton dan uwan nashi ya fadi mishi. Kasan su kamar hanta da jini" aikuwa dai bai fadi mishi ba.. Murmushi Daddy yayi yace "bari dai in kira shi in shaida mishi maganar sa ranar gobe don ya shirya"13 An zo wurin.. Ko da Daddy ya kira wayar Muhammad har ta gama ringing bai amsa ba. Sossai yayi mamaki because its unlike him. Yayi trying kusan sau biyar amma babu response don haka ne ya kira wayar sarkin gidan Muhammad din mai suna Jamilu. Cike da girmamawa Jamilu ya amsa wayar ya gaishe shi. Bayan Daddy ya amsa ne yace "Ina maigidan naka, ina ta kiran shi a waya baya amsawa?" Jamilu ya dan yi shiru sannan yace "uhm, Alhaji dama yau kusan kwana hudu kenan da yace kar wanda ya matsa mishi, toh ban dai sani ba ko akwai matsala ne.." Daddy wanda hankalin shi ya tashi ne yace "shiga gidan ka dubo mun shi yanzun nan" Cike da girmamawa yace "toh Alhaji" Bayan Daddy ya kashe ne ya ba Mummy labarin halin da ake ciki. Mummy wadda hankalin ta ya tashi ce tace "Ni fa wallahi shiyasa ban so Muhammad yayi nisa da mu ba, na so ace sai yayi aure ne zai tare a gidan shi amma ya qi, Allah dai yasa lafiya" Nikuwa nace meyasa ta fadi hakan?? Wayar Daddy ce tayi ringing inda yayi saurin amsawa yayinda ya ji Jamilu wanda muryar shi tana rawa harda sarqewa yace "Alhaji Babu lafiya, da alama ma baya numfashi.."2 Hankalin Daddy a matuqar tashe ya miqe tsaye tare da fadin "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, maza ku kai shi National Hospital, gamu nan zuwa" Mummy wadda tuni itama ta miqe cike da tsananin damuwa tace "me ke faruwa?? ba dai ya samu attack ba?" Daddy wanda yake a rude yace "Ina tunanin hakan" Mummy wadda bata san hawaye sun fara gangarowa daga idanuwan ta ba tace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, me ya faru da har ya janyo mishi shiga wannan halin?? Abinda ya dade bai faru ba??" 🤔🤔 Gani nayi tana neman zubewa qasa yayinda Daddy ya riqo ta tare da rungume ta yace "Hey please calm down, Insha Allah he will be fine. You have to remain strong for him, He is a fighter kuma na tabbatar kamar yadda yayi fighting a baya insha Allah he will this time" Tana kuka tace "Bana so muyi losing dinshi Daddy.." Yace "Sssshhhh, bazamu yi losing dinshi ba. Mu je asibitin mu dubo shi" Haka Iro driver ya ja su suka fita daga gidan hankulan su a tashe. ♤♤♤♤♤♤ Wata sabuwa inji 'yan caca...

Post a Comment for "ZEHRA CHAPTER 7"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...