[Advertisements⬇️]

ZEHRA CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Mon. Sep 26th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ZEHRA CHAPTER 5

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ABU-YAZEED RESIDENCE Zaune yake a kan stool din Vanity table na dakin yayinda ya cika da tsananin damuwa. Kusan awa daya kenan yana nan zaune yana ta kallonta yayinda take ta motsi cikin bargo tana bacci.+ A yau ne Mustapha zai yi tafiya zuwa Lagos har tsawon sati daya. Kamar yadda yayi mata alqawarin zai zo suyi sallama kuwa ya zo amma kuma ya tarar da labarin cewar bata da lafiya tun cikin daren jiya. Babu yadda Mustapha bai yi da Anty a kai ta asibti ba amma kuma sanin abinda yake damunta ne yasa Anty tace kar ya damu zata samu sauqi. Tun kafin Fadeela ta tafi wurin aiki Mustapha ya zo gidan. Har tana yi mishi tsiya wanda he didn’t find funny, mamaki ma ya dinga yi na yadda basu dauki ciwon nata serious ba. Anty ce ta shigo dakin ta same shi zaune ya sa mata ido. Gani nayi tayi dariya tare da matsawa kusa da shi tace “hey, gwara ka tashi ka kama hanya, kar kayi missing flight dinka. Ka dai san na fadi maka she will be fine ko? Trust me she will” Ba tare da ya kalli Anty ba yace “bazan matsa daga nan ba har sai ta tashi ta fadi mun she is okay Anty, I still can’t believe baku dauki ciwon nata serious ba” Anty tana dariya tace “its because ba serious din bane Mustapha, idan ta tashi zata fadi maka da kanta” Bayan Anty ta fita da kusan minti goma sha biyar ne ta farka. Qamshin turaren shi da ta ji ne yasa tayi saurin bude idanuwan ta wadanda suka yi ja. Ji nayi yace “My Angel kin tashi?? Sannu…” Murmushi ta sakar mishi tare da fadin “baka tafi ba Baby??” Yace “I couldn’t My Angel, bazan iya tafiya in bar ki kina rashin lafiya ba” Gyara kwanciyar ta tayi a cikin bargon tace “hey kar ka damu I will be fine” Yace “no My Angel, tashi mu je asibiti” lumshe idanuwa tayi tace “don’t worry My baby, it happens every month and da zarar na qara shan ruwan lipton I will be much better” Cike da mamaki yace “Lipton, yaushe lipton ya zama maganin ciwo?? Hey tell me, what is wrong with you?” Tana kallon shi a ranta tace “what is wrong with this guy? Ta ya yake so in fadi mishi cewar I am having serious cramps ne??” Ji tayi yace “idan baki fadi mun ba I will carry you to the hospital..” Da sauri tace “yi haquri please, idan na fadi maka zaka tafi??” Yace “yeah, idan har ba serious bane kamar yadda kowa yake fadi” Tace “its Menstrual Pain My Baby, haka yake yi mun every month. Its just on the first day though. Ka ga tun cikin dare wuraren 3 ya fara. Da na dan sha Lipton ne cramps din ya dan rage…”5 Cike da tausayawa yace “how I wish I can take away the pain My Angel, its not possible right??” Zehra dai bata san lokacin da ta fashe da dariya ba. STORY CONTINUES BELOW Shima dariya yayi yace “I am sorry, There is no way in hell I can do that ko?” Nikuwa nace tabbas there is no way Mr Romeo🤣5 Zehra wadda take ta dariya tace “Baby I love you, please don’t stop loving me” Yana murmushi yace “I wont My Angel” Tace “toh tashi ka kama hanya, I will be fine” Ya miqe tare da fadin “Okay My Angel, bari in tafi. Please ki kwanta ki huta kin ji?? I will call you idan na isa” Yayi blowing mata kisses yayinda ta kama da hannunta tare da lumshe idanuwa tace “Allah ya kiyaye hanya, I will miss you” yace “me too” hmmmm.. how cute😘😘😘2 ♤♤♤♤♤♤♤ Da daddare Fadeela tana zaune a kan kujerar dakin su tana yin wani aiki a laptop dinta yayinda Zehra take zaune a kan stool na Vanity table daure da towel tana shafa mai. Cikin tsokana Fadeela tace “babes I beg you wankan nan ya isa haka kuma sai gobe” Zehra ta fashe da dariya tace “insha Allah Dee” Ta miqe zata shiga dressing room ne tace “bari in kammala in zo in kira Baby na” Fadeela ta Harare ta tace “toh duka duka yaushe kuka yi magana?? Is it even up to fourty minutes now??” Zehra tace “wallahi Dee missing dinshi nake yi sossai, I just don’t know how I will cope har dawowan shi” Fadeela tana dariya tace “wallahi na masifar jin dadin soyayyar nan taku, ki duba fa ki gani a dalilin ki Ya Musty ya canza kamar ba shi ba, har hira yake zama ayi da shi a cikin gida. God will bless you Zehra” Zehra tayi murmushi ta shige dressing room. Aikuwa tana ciki ne wayarta ta fara ringing. Muryar Fadeela ta ji tana fadin “Toh Angel ki fito ga Babyn ki yana kira” Da sauri ta qarasa sanya rigar baccinta ta fito ta tarar wayar ta tsinke. Hayewa kan gadon tayi tana shirin kiran shi ta ga incoming Video call din shi. Ganin haka ne ta shiga duvet ta rufe jikinta gaba daya, kanta kawai ne ya zama visible. Zehra dai tayi haka ne domin kuwa rigar baccin da ta sa sleeveless ce mai hade da gajeren wando. Asali ma duk kayan baccinta haka suke, gajeru ne sannan sleeveless. A rayuwarta bata son kayan bacci masu nauyi. ko da ta amsa kyakyawar fuskar shi ce ta bayyana yayinda yake kwance a kan gado. Ji tayi yace “hey My Angel how are you? Ya jikin ya warware??” tace “yes My Baby. You look tired” Ya dan lumshe idanuwa yace “wallahi Baby I am so tired and I need to wake up early tomorrow” Tace “ayya, toh ai da kayi baccin ka kawai ka huta” murmushi yayi yace “ai idan ban ji muryar ki sannan na ga fuskar ki ba cikin daren nan akwai matsala..” Kafin ta amsa kuwa ya jiyo muryar Fadeela tana fadin “iyyeh, wai wannan Ya Musty din da na sani ne??” Zehra dai gani tayi Mustapha ya bata rai yayinda yace “wallahi Dee zan mare ki, me zai sa ki dinga shiga hirar masoya. Tashi ki bar dakin” Fashewa tayi da dariya tace “sorry bros bazan qara intruding ba amma please a bar ni nima inyi course..” Zehra wadda take ta dariya tace “baby don’t mind her” Daga nan kuwa suka cigaba da hirar su ta soyayya wadda kuwa basu gajiya. Wasa wasa dai da qyar ma Zehra ta roqe shi su yi sallama don ya samu bacci mai yawa ya huta. STORY CONTINUES BELOW ♤♤♤♤♤♤♤ Haka dai suka cigaba da gudanar da soyayyar su. Kusan kodayaushe idan Mustapha is not busy with work toh yana waya da Zehra. A haka kuwa har sati daya ta wuce ya dawo. Ranar da ya dawo kuwa murna a wurin Zehra abin ba’a magana. Abinci kala kala ta dafa a gidan ranar har su Daddy suna ta tsokanar ta a dalilin Mustapha sun ci special abinci mai dadi. A yanzu dai su Daddy sun gano cewar akwai soyayya a tsakanin yaran nasu. Sossai sun ji dadi musamman da suka ga canji a tare da Mustapha duk a dalilin Zehra. Har sun fara shawarar ba da jimawa ba kawai za’a fara maganar auren su suma. Anty har mamaki take yi yadda Mustapha yake shiga gidan su ya zauna ayi ta hira da shi. Dukda ta kasance qanwar mahaifin shi baya wani relating da ita amma kuma a dalilin Zehra yanzu relationship dinsu yayi improving sossai. Sun amince lallai Zehra ta taka rawar gani babba wurin canza shi wanda kuwa hakan ya tabbatar musu da lallai ba qaramin so yake yi mata ba. ♤♤♤♤♤♤ A yau ne ake bikin yayan Hidaya wanda kuwa ta gayyaci Zehra. Har ankon bikin sai da tayi. A yau ne ake yin bikin reception a The glam Hall.3 Zehra ta so ace Mustapha ne zai kai ta amma kuma yana da meeting a ofis wanda kuwa tun safe suka shiga. Lokacin ma da zata tafi reception din text message ta tura mishi ta sanar mishi. Ya turo mata da reply akan ta fadi mishi venue din idan ya gama abinda yake yi zai zo ya dauke ta. Ta masifar jin dadin hakan kuwa. THE GLAM HALL Bayan an tashi kuwa mutane suka fara tafiya. Hidaya wadda take ta hada hada da mutane kuwa sai da ta tabbatar kowa ya samu motar tafiya gida. Tuni Magrib ta kusa yayinda mutane suka watse sai daidaikon su suka rage. Hidaya wadda take tsaye a gaban motar gidan su ce ta kalli Zehra tace “babes mu je kawai mu sauke ki gida, kin ga dare yana yi” Zehra wadda ta kalli wayar ta tace “kar ki damu Babes, Baby just called me, he said gashi nan zuwa” Hidaya tace “are you sure you will be fine??” tace “yes dear, besides ai ga sauran mutane nan” Bayan sunyi sallama ne ta samu wata kujerar shaqatawa ta zauna tana jiran shi. Zehra bata ankara ba ta ga wasu samari guda biyu a gaban ta. kauda kanta tayi yayinda ta fara jero addu’o’I a ranta. Daya daga cikin su ne yace “gimbiya muna lafiya?” Zehra kuwa ko kallon su bata yi ba balle ta yi musu Magana. Dayan ne yace “ke kar ki raina mana wayau mana, ana yi miki Magana kina wani share mu. An gaya miki bamu san dalilin ki na zama anan din bane??” Jin haka kuwa ya sa Zehra ta miqe zata bar musu wurin. Ta daga qafarta kenan daya daga cikin su ya janyo veil dinta wanda har ta kusa faduwa. Tuni ta shiga rudani yayinda qwalla suka taru a idanuwan ta amma don kar ta nuna musu ta tsorata sai ta matse. A daidai wannan lokacin ne Mustapha ya qaraso harabar wurin. Yana shirin kiran ta a waya ne ya hango ta tsaye tare da wadannan samarin. Sossai zuciyar shi take tafasa ganin ta tsaye da samarin. Runtse idanuwan shi yayi sannan ya bude yace “Control Mustapha” Da saurin gaske ya nufi wurin su. Ko Kafin ya qarasa ne ya ji daya daga cikin su yana fadin “idan baki yi mana Magana ba sai na farfasa miki mari a nan” STORY CONTINUES BELOW Daga bayan su suka ji muryar shi yana fadin “ai gata nan a gaban ku, ku mare ta” Zehra dai tana jin muryar Mustapha ta saki ajiyar zuciya tare da komawa bayan shi ta tsaya yayinda tace “thank God you came” Cike da rainin wayau daya daga cikin samarin yace “kai kuma who are you?” Mustapha a ranshi yace “these boys are lucky sai da na je gida na cire Khaki na, but then zasu gane who they are messing with” Ya juya ya kalli Zehra wadda take tsaye a bayan shi ya miqa mata makullin motar yace “go sit in the car My Angel” Ko da ta karba tana tafe tana waige don ganin abinda Mustapha zai yi. Mustapha wanda ya kalle su yace “ina sauraron ku, me kuke cewa??” Dariya suka yi yayinda daya yace “ka kuwa san ko mu su waye a garin Abuja?? Kai har ka isa ka raina mana wayau??” Mustapha yayi murmushi yace “interesting” Ita dai Zehra tana daga cikin mota ta hango shi ya zauna a kan kujera har tana mamaki. Mustapha wanda yake zaune cike da curiosity yace “ku bani labari” Daya daga cikin su yace “ka je ka tambaya waye Alhaji Habibu Mayana a garin Abuja, wallahi Allah ya so ka Daddy baya nan da sai ya sa an kama ka” Mustapha ya Dan zaro idanuwa tace “you don’t say… Alhaji Habibu Mayana?? tsohon Chairman?? ah lallai ku manyan yara ne” Gani suka yi Mustapha ya latsa wayar shi ya kai kunnen shi yace “yes please, come to the glam hall right now” Bayan ya kashe wayar ne yace “Na ji ko ku su waye. You guys are indeed big boys, nima bari in fahimtar da ku ko ni waye” A tunanin Mustapha zasu ji tsoro su tafi amma inaa ji yayi ma daya daga cikin su yana fadin “ai yau zamu ga qarshen rainin wayau” Zehra ce ta kira shi a waya tace “Baby ka zo mu tafi mana” murmushi yayi yace “ina zuwa My Angel, let me just settle a little issue with these boys” Suna nan tsaye suka ga motar sojoji ta shigo harabar wurin yayinda ta qaraso wurin da suke.10 Gani nayi gayun sun dan sha jinin jikin su amma suka basar. Officer Usman ne ya fito tare da yaran shi suka qaraso wurin Mustapha suke ce “Sir” Ji nayi yace “take these guys with you and deal with them..” Zehra wadda ta hango wannan al’amari kuwa duk ta bi ta rude. Ji yayi gayun suna ta fadin “wai me muka yi da zaka sa a tafi da mu?” Mustapha yana murmushi yace “you disrespected an army officer and messed with his girl, that’s what you did” Ganin dagaske dai tafiya za’a yi da su ne suka ce “don Allah don annabi kayi haquri, wallahi bamu san cewar kai soja bane” Tuni aka ingiza su cikin motar yayinda sauran mutanen da suka rage a harabar wurin da securities din wurin suke ta kallon ikon Allah. ♤♤♤♤♤♤ Ko da suka kamo hanya hankalin Zehra a tashe yayinda ta kalli Mustapha tace “Baby ina za’a kai su??” Murmushi yayi yace “gida za’a kai su My Angel, just forget about it. How was the programme?? Hope you enjoyed yourself??” Aikuwa daga nan ta fara bashi labarin abubuwan da suka faru yayinda tace “wallahi baby at a point in time ina ta imagining ranar auren mu and how happy i will be” Yana dariya yace “I really can’t wait for that day honestly, kalan farin cikin da zan shiga only God knows” haka dai suka cigaba da hirar su ta soyayya wadda bata qarewa. ♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Ko da suka iso gida ana ta kiran Sallan magrib don haka ba tare da bata lokaci ba yayi parking ta shige gida yayinda ya wuce masallaci. Zaune suke a falon sama suna hira yayinda Zehra take basu labarin abinda ya faru. Bayan ta gama ne Mummy tace “wai kina nufin an tafi da su??” tace “eh Mummy, amma dai na tambayi Baby yace wai gida za’a kai su” Fadeela ce ta fashe da dariya tace “what?? Wallahi ba gaskiya bane, Ya Musy fa Barrack ya sa a kai su. wallahi dukan tsiya za’a yi musu” Zehra ta zaro idanuwa tace “dagaske Dee??” Mummy wadda take dariya tace “ina kika taba ganin an kawo sojoji an kwashi mutane ba’a kai su Barrack an duke su ba..” Fadeela ce tace “wallahi Zehra zaki sa Ya Musty yayi ta sa ana kama mutane a dalilin ki” Aikuwa gani suka yi ta miqe a guje ta wuce dakin su yayinda ta dauki wayarta ta kira shi. A lokacin kuwa yana duba wani aiki a laptop dinshi ne kiran ta ya shigo. Ko da ya amsa kafin yayi Magana ya ji tace “don Allah Baby ka sa a saki wadannan mutanen, Dee tace wai ba gida za’a kai su ba. Barrack za’a kai su ayi musu duka” Murmushi yayi yace “Hey relax, za’a dan koya musu hankali ne. They messed up with you and they deserve to be thought some lesson” Tace “idan dai don ta ni ce wallahi na yafe musu please ka sa ayi releasing din su” Girgiza kai yayi yace “Unfortunately My Angel it’s about me, bana so in gani ko da wasa wani yayi approaching dinki talk more of harassing you, I promise you nan da three days za’a sake su” Ji yayi ta fashe da kuka wanda hakan kuwa yayi sanadin tashin hankalin shi. Aikuwa nan da nan yace “hey stop crying, zan sa a sake su yanzun nan I promise. Duk abinda kike so inyi shi zan yi miki. I love you so much” Tana share hawayen ta tace “thank you My Baby, ina jiran ka kazo muyi dinner, kowa ya ci abinci amma ni ban ci ba. kai nake jira” Murmushi yayi yace “My Angel I am not hungry” Cikin shagwaba tace “Idan baka zo ka ci ba nima bazan ci ba kuma haka zan kwana da yunwa” Da sauri yace “please don’t, I am on my way” Kamar kuwa yadda yayi mata alqawari yana gama waya da ita ya kira ya sa a saki gayun with strict warning akan kar su qara. ♤♤♤♤♤♤♤ hmmmm… ABU-YAZEED RESIDENCE Zaune suke a falon gidan suna hira. Bisa single seaters din da suke hade da juna suke zaune.+ Zehra wadda take ta kallon shi ce tace “Baby wallahi zanyi missing din ka, if not because kayan Dee za’a je siyowa da babu inda zan je” Shafa kan shi yayi yace “I will miss you more My Angel, you have become a part of me. Tunanin ki kawai makes my day, you can imagine how being with you feels” Zehra wadda ta ji dadin kalaman shi ce tace “toh ka zo mu je tare mana” Murmushi yayi yace “I can’t, If I am not on a mission sannan ba course nake yi ba I have to go to the office everyday just like normal civilians. Abinda yasa ma kika ga bayan na dawo ban je ba its because an bani hutu ne” Bata rai tayi tace “toh wai dama banda field work kuna yin admin ne??” Dariya yayi yace “har classes muna shiga My Angel, I have an office in the Barrack here, Abuja is my base. Duk lokacin da akwai mission ne ko peace keeping or course shine ake posting dinmu” Tace “yanzu dai wato dole inyi haquri kenan??” Yana murmushi yace “I am sorry My Angel” Ganin ta bata rai ne yace “hey baki tura mun hotunan ki da kika yi mun alqawari ba” ya miqa mata wayar shi yace “please” Ta karbi wayar ta fara turawa yayinda take ta turo baki. Shi kam duk bai ji dadi ba, tunani yake yi yadda zai yi da ita. Bayan ta gama ne ya ga ta miqo mishi wayar ba tare da tace komai ba. Gyaran murya yayi yace “hey tashi mu je mu siyo ice cream, ko bazaki sha ba?” Murmushi tayi tace “zan sha” Da sauri ta miqe tace “ina zuwa” yace “don Allah kar ki dade” tace “just thirty minutes” ya zaro idanuwa yace “what??” tana dariya tace “just kidding” A dalilin wannan fitar da suka yi kuwa ta sassauta fushin da tayi. Ita dai Zehra duk wani moment da tayi spending da Mustapha tana masifar valuing dinshi. Ita kam Mustapha baya laifi a wurinta. Duk abinda yayi daidai ne. Sossai take qaunar shi. ♤♤♤♤♤♤ Washe gari da zasu tafi kuwa har kuka ta dinga yi saboda zata rabu da Masoyinta. Haka ya dinga lallashin ta kamar wata qaramar yarinya yayinda ake ta yi musu dariya. Babu yadda Zehra bata roqi Fadeela akan tayi haquri su tafi su barta ba amma sam Fadeela ta qi. Haka dai akan dole ta haqura ta bi su wanda kuwa duk bai ji dadi ba. Wannan tafiyar dai tare da Anty da Khadeja suka yi ta. Sun sauka a daya daga cikin shahararren wurin saukar baqin nan na qasar Dubai wato Burj-al-khalifa. Ko da suka isa dai kasa gane kan Zehra suka yi don haka ma tsawon kwana biyu da suka yi ba tare da ita ake fita shopping ba. kullum tana daki tana faman tunanin shi. idan ka gan ta cikin walwala toh suna waya ne. Fadeela kuwa tayi masifa har ta gaji.Cewa ma tayi da su Papa sun sani kawai da an hada bikin su tare su je su cinye juna kowa ma ya huta.7 🤣🤣🤣🤣 STORY CONTINUES BELOW ♤♤♤♤♤♤ BURJ-AL-KHALIFA, DUBAI A yau Saturday duk sun tafi Shopping as usual Wanda kuwa Fadeela ta dinga masifa akan yadda Zehra ta qi bin su bayan duk plans dinsu tare suka yi. Anty ce take bata haquri akan ta qyale ta tunda dai hankalinta baya tare da ita. Zehra tana zaune a kusa da window na dakin Suite din su yayinda take ta hangen masoya suna ta kai da komowa a harabar wurin. Sossai take ta imagining dinta da Mustapha a cikin wannan yanayin. Gani nayi tayi murmushi tace “I really love him, Ya Allah ina roqon ka kar ka dauki raina ban kasance matar shi ba” Bata ankara ba ta ji wayar ta tana ringing. Unknown number ta gani don haka ne ta Bata rai tace “waye wannan kuma?” Tana amsawa kuwa ta ji muryar shi yana fadin “My Angel ba kya so ki amsa wayar Babyn ki ne??” Cike da mamaki na ga ta tashi tsaye tace “Baby?? Na ga lambar Dubai?? How comes??” Murmushi yayi yace “yes My Angel, its because I am in Dubai” Ji yayi ta saki ihu yayinda tayi tsalle wanda har sai da ya toshe kunnuwan shi. Tace “wallahi Baby I am so happy, kana ina ne?? gani nan zuwa…” yana dariya yace “I am outside across the street, maybe if you look through the window you might even see me” Aikuwa gani nayi ta leqa window yayinda ta hango shi a tsaye in black, P-cap ne a kan shi yayinda yake riqe da sun glasses din shi a hannun shi. Ajiyar zuciya tayi tace “na shiga uku, ya zanyi da son shi??” Gani nayi ta dauko wata green flowery kimono ta dora akan English wears na Jeans trouser da sleeveless top din da ke jikinta. Bayan ta yafa gyalen a kanta ne ta dauko qaramar hand bag dinta ta fita. Mustapha dai ba’a yi five minutes da suka yi Magana a waya ba sai ganin ta yayi a gaban shi.5 Cike da mamaki yace “like seriously?? You came this fast?? Haka kika yi missing dina??” Dayake ta gane abinda yake nufi ne ta fashe da dariya tace “I swear Baby I needed to see you badly, how was your trip?? Ya akayi ka zo?? Kayi kyau sossai” Dariya yayi yace “kema kinyi kyau My Angel, my trip was fine. Kin san yau Saturday ai, I just decided to come see you shine na biyo flight jiya da dare and here I am” Tana murmushi tace “wallahi na ji dadi, ban taba tunanin zaka zo ba” yana murmushi yace “I can do anything to make my Angel happy” Hannuwan shi ya sa a aljihu yace “so what do we do now??” Tana murmushi tace “yanzu dai mu je kayi breakfast don na San baka ci wani abun kirki ba” Murmushi yayi yace “I can’t say no right??” tana dariya tace “nope” Dariya yayi yace “mu je toh” Cike da farin ciki suka nufi wurin cin abinci a nan Burj-al-khalifa. Bayan sun gama cin abinci ne suka yi deciding su kira su Fadeela don su hadu a kasuwar because Fadeela tana ta kiran shi tun yana Nigeria tana qorafi akan Zehra ta qi raka su kasuwa. THE DUBAI MALL Sossai su Anty suka yi mamakin ganin Mustapha. Fadeela tace “gaskiya wannan soyayyar taku ba ‘yar qarama bace, ni fa har kuna sani ina tuhumar kaina anya soyayyar da nake yi ma sweetheart is deep enough kuwa??” STORY CONTINUES BELOW Fashewa suka yi da dariya yayinda Mustapha yace “ke ko??” Fadeela tana dariya tace “hmm, ni kam na ji dadin zuwan ka domin kuwa wallahi na rasa gane kan Angel dinnan taka, Anya ya Musty baka yi mata asiri ba kuwa??” Anty tace “ko kuma ita tayi mishi ba?” Yana dariya yace “ai dama zata yi mun asirin da ta taimake ni wallahi..” Wannan maganar kuwa ta su dariya sossai. Haka dai suka cigaba da siyayya. Shi dai Mustapha duk wani abinda ya gani da yayi mishi kyau sai ya siya ma Zehra. Su Anty kuwa kallon ikon Allah kawai suke ta yi. A lokacin da suka je Jewelry shop kuwa suka dinga zabar sarqoqin da za’a zuba a kayan lefen Fadeela. Mustapha wanda yake zaune a gefe ne ya hango wasu zobuna hade da juna. Da ganin yadda aka ajiye su kasan zasu ja kudi. they looked simple but elegant. Sossai suka yi mishi kyau. Ji nayi ya kira daya daga sales reps din shagon yayinda ya sa shi ya dauko mishi. Mustapha wanda ya riqe Zobunan gani nayi yayi murmushi yace “beautiful” Mutumin yace “they are precious too, unique and elegant” Ji nayi yace “My Angel” Zehra wadda suke ta faman zaben Sarqoqi ce ta juyo da sauri tace “Yes Baby” Yace “please come” Da sauri ta je wurin shi tace “ga ni” Yace “bani hanuun ki” Ta miqa mishi cike da mamaki. Gani nayi ya dauki zoben ya sanya mata. Sossai yayi fitting dinta yayinda ta zaro idanuwa tace “wow, Baby this is beautiful. I love it very much” Yana murmushi ta ga ya dauki dayan zai sa a hannun shi. Da sauri ta karba tace “ni zan sa maka” Yana murmushi ya miqa mata ta karba sannan ta sa mishi. Ji suka yi gaba daya shagon ana ta tafi harda su Fadeela. Cike da mamaki suka juya suna kallon all eyes on them yayinda suka fashe da dariya. Mustapha wanda ya daga musu hannu alamar godiya ne ya kalle ta tare da kashe mata ido daya yace “guess we just got engaged”8 Whoa…😘😘 Zehra kuwa kamar ta zuba ruwa a qasa ta sha don murna. Mai shagon kuwa yana ta murna za’a yi musu ciniki. Addu’a yake ta yi Allah yasa Mustapha ya siya domin kuwa zobunan suna da masifar tsada wanda kuwa tsadan su ne yake hana mutane siya. Mustapha yana kallon mutumin yace “Price please” Kai tsaye yace “40,500 Dirham Sir” Gani nayi Zehra ta zaro idanuwa yayinda Mustapha ya fiddo credit card dinshi zai miqa ma mutumin. Da sauri ta qwace katin tace “what are you doing?? Ka san nawa ya ce kuwa?? roughly 4m fa Nigerian currency” Mustapha wanda yake kallon ta yace “I heard my Angel, its okay ai considering the uniqueness” Gani yayi Zehra tana qoqarin zare zoben daga hannunta yayinda tace “wallahi sun yi tsada Baby, zobe ne fa…” Da sauri ya riqe hannun ta yace “hey stop it, I can spend my money to the last kobo for you My angel. You are my precious Jewel and I love you very much” STORY CONTINUES BELOW Ya gyara ma zoben zama a yatsar ta yace “now give him the card” Murmushi tayi mishi sannan ta juya ta kalli mutumin tare da daure fuska tace “hey, but hope you know these are too expensive right??” Mutumin yayi murmushi yace “it’s the best you can get across the world Ma’am. Congratulations on your engagement. You really are lucky to have him” Mustapha wanda yake kallon Zehra yace “I am the lucky one here. She is an Angel sent directly from heaven”4 Awwwnn😘😘😘 Su Anty dai suna nan tsaye suna ta mamakin yadda wadannan masoyan suke ta faman zabga soyayya a cikin shago. Sossai suka dinga yi musu tsiya amma ko a jikin su. A dalilin wannan cinikin da Mustapha yayi ma masu shagon kuwa suka yi ma Fadeela discount sossai akan kayan da ta siya. Har extra set na sarqa suka ba Khadeeja kyauta. BURJ-AL-KHALIFA Ko da suka dawo Masaukin su Zehra ta kalli Mustapha tace “Baby ina ka sauka??” Yana murmushi yace “I am going back tonight My Angel” Gani yayi ta bata rai yayinda su Fadeela suka dinga yi mata dariya. Fadeela ce tace “yanzu Ya Musty kana nufin you came all the way just to see her?? Oh my God, I swear this love is breathtakingly beautiful” Hararar ta yayi tare da kallon Anty yace “wallahi Anty yakamata ki hukunta yarinyar nan, whats her problem ne?? gaba daya ta gama raina ni” Anty ce tace “toh ai abun mamaki ne wannan, ni ban taba ganin irin wannan soyayyar ba” Mustapha dai ganin sun sa shi a gaba ne ya qyale su ya dawo da hankalin shi wurin Zehra wadda take ta fushi yace “tashi mu je yawo, lets spend more time together my Angel. Ko kin gaji ne??” Zaraf suka ga ta miqe tace “mu je” Mustapha wanda shima ya miqe ne yace “sai mun dawo” Fadeela tana kallon Zehra tace “toh Angel a dawo lafiya” Bayan sun fita ne Fadeela tace “wallahi I am so happy for them, especially my friend. Sossai dream dinta came true. Ya Musty is the kind of man she has always wanted and I pray they continue to be together” Su Anty suka ce “ameen” Nima nace Ameeeeeeeen… Ah toh2 ♤♤♤♤♤♤♤ BURJ-AL-KHALIFA PARK, DUBAI Zaune suke a park din yayinda Zehra take wasa da wata tattabara. Mustapha kuwa kallon ta kawai yake yi yayinda take birge shi. Shi kam ya rasa wane irin so yake yi ma Zehra. Burin shi bai wuce ya mallake ta ba a matsayin matar aure, he just can’t wait to show her how much he really loves her. Gani nayi ya dan bata rai yayinda wata zuciya take tuna mishi tafiyar da zai yi zuwa Italy. Ajiyar zuciya ya saki wanda hakan ya sa tayi saurin waigowa ta kalle shi tare da fadin “whats wrong??” kai tsaye yace “I love you” Tana murmushi tace “say something I don’t know” Shima murmushi yayi tare da kamo hannun ta wanda yake sanye da zoben da ya sanya mata yace “promise me bazaki taba cire wannan zoben daga hannun ki ba and the day you do, it will mean that babu ni a cikin zuciyar ki…” Ya dan yi murmushi yace “but I don’t pray for that to happen anyway” Matse hannun shi tayi a cikin nata tace “I promise you my love, kaima promise me” Yace “it will remain with me till I die my Angel” Cike da murna tace “kayi mun wani alqawari kuma” Yace “what is it??” Tace “promise me that idan muka yi aure zaka kawo ni nan qasar, I want to spend a beautiful moment with you here, I just love the country” Yana murmushi yace “I promise you my Angel, idan muka yi aure a nan qasar zamuyi Honeymoon dinmu” Gani yayi ta sa hannu ta rufe idnuwan ta yayinda ya fashe da dariya. Suna nan suna ta hirar soyayya ne ta hango mai sayar da Popcorn. Ji nayi tace “Baby zan ci popcorn” Girgiza kai yayi yace “You and Popcorn..” Dariya tayi yayinda yace “if I can remember, Popcorn was involved during our first encounter..” Gani nayi ya dafe kai yace “Oh my God, I even slapped you..” Bata Ankara ba ta ga ya sauka tare da duqawa har qasa yace “please forgive me for slapping you a lokacin.. Guess I was a fool for not realising the beautiful face I…” Fashewa tayi da dariya tare da riqe hannun shi tace “don Allah ka tashi Baby, ni kam i never took it to heart.. I love you” Yana murmushi ya miqe tare da fadin “thanks My angel, let me get you your popcorn” Tana kallon shi ya nufi wurin mai Popcorn din yayinda ta bude Jakarta ta ciro shades dinta ta Sanya saboda rana. Mustapha Wanda yake gaban mai popcorn din yana jiran turn dinshi gani nayi ya juyo ya kalle ta yayinda yayi murmushi yace “How I love you my beautiful Zehra” Daga nan kuwa ya fiddo wayar shi yayi zooming dinta yayinda ya dinga daukar ta hotuna.  ♤♤♤♤♤♤ Da dare ne suka raka shi Airport ya tafi. Dukda kuwa tayi missing dinshi wannan karon bata nuna damuwa ba. Tare da ita aka cigaba da hidimar siyayyan kayan auren Fadeela amma fa motsi kadan zaka gan ta riqe da waya tana hira da Mustapha. ABU-YAZEED RESIDENCE Satin su uku da dawowa daga Dubai.+ Sossai kayan da suka siyo sunyi kyau. Tuni har an kai kayan lefen wanda kuwa amaryar dai ita ta hado kayan ta don haka komai na cikin akwatunan to her taste ne. Kudaden Zain sunyi kuka don kuwa komai first class ne. Harda Makullin dalleliyar mota qirar Audi A4 aka sa a kayan. ♤♤♤♤♤♤♤ A yau wuraren qarfe goma sha daya da kwata (11:15pm) na dare Zehra tana zaune a kan kujerar dakin su yayinda take ta gyangyadi. Fadeela wadda ta gama shan hirar soyayya da masoyin ta a waya ce ta kalle ta tare da fashewa da dariya tace “babe zo ki kwanta kiyi bacci, he is going to send you your birthday message, gobe da safe kya karanta” Zehra ta girgiza kai alamar a’a sannan tace “I want to read it as soon as he sends it, maybe ma kirana zai yi” Fadeela wadda ta gyara duvet din da ta rufe ce tace “toh shikenan Angel din Baby, ni dai sai da safe and happy birthday in advance” ********** Qarfe goma sha biyu na dare daidai Zehra tana riqe da waya amma shiru. Bata ankara ba ta ji qarar shigowar text message. Cike da murna na ji tace “yesss…” tana dubawa na ga ta bata rai tare da fadin “its not him” toh fa🙄 Haka ta qara jin shigowar wani saqon ta duba, nan ma haka ba shi bane. Sossai hankalin Zehra ya baci. A yadda suke da Mustapha presently ta sa a ranta shine first person da zai yi wishing dinta. what could be wrong???3 🤔🤔🤔🤔 Tun tana zaune tana jira har ta koma kan gado ta kwanta yayinda take ta duba duk wani saqon da ya shigo wayarta. Abin mamaki wasu messages din ma ta manta wadanda suka aiko mata su, wasu ma batada number din su. Yawanci irin mutanen nan ne da aka Dade ba’a yi having contact da su ba. Haka dai ta cigaba da qunci har bacci barawo ya sace ta. ************ Tun da asuba da ta farka kuwa wayarta ta fara janyowa ta duba amma har ta gama dubawa babu saqon Mustapha. Fadeela wadda ta fito daga bathroom ce ta qaraso wurinta tana yi mata waqar Happy birthday amma kuma abin mamaki sai ta ganta tana ta rusa kuka. Tsayawa tayi turus cike da mamaki tace “Zee lafiya??” Cikin kuka tace “Baby ya manta da ni, he has not wished me up til now” Fadeela wadda tayi mamakin haka kuwa tace “anya Babyn ki zai manta da ke kuwa?? We even talked about your birthday da shi fa jiya” Ta hau gadon tare da hugging dinta tace “daina kuka, give him time I am sure he will wish you. Kin dai san Sojoji dama komai nasu daban ne maybe he didn’t realise cewar tun 12am yakamata yayi wishing dinki” Ta dan shafa bayan ta tare da fadin “je kiyi alwala ki zo kiyi sallah” Ni kuwa nace hmmmm, what is wrong with baby Musty??🤔 STORY CONTINUES BELOW ************ Wasa wasa dai har qarfe goma sha biyun rana shiru Babu Mustapha babu kiran waya. Abinda ya fi ba Zehra haushi kuma yau Saturday, ta sani sarai he is not busy don kuwa banda Gym babu inda yake zuwa on Saturdays da Sundays. Haka duk ta bi ta birkice musu a gidan. Anty ma har kiran Mustaphan ta so yi amma Zehra ta hana domin kuwa tayi fushi da shi. Its her birthday, its supposed to be one of her best days amma kuma it turned out to be the worst. Ayyah… poor Zehra!! I am feeling for her☹2 Anty dai da abun ya dame ta kuwa ta neme shi a waya amma kuma abin mamaki wayar shi a kashe. Da aka tambayi Mummy ma cewa tayi tun safe da ya fita bai dawo ba. Haka ta yini a daki tana ta rusa kuka. Har zazzabi ya saukar mata wanda kuwa anyi da ita ta sha magani amma ta qi. A cewar ta tunda Mustapha baya sonta gwara ciwon son shi ya kashe ta.5 Oh oh oh… how emotional😥3 ♤♤♤♤♤♤ Bayan sallan Isha’I Anty tana zaune a falo tare da Khadeeja da Fadeela suna ta hirar halin da Zehra take ciki tare da mamakin inda Mustapha ya shiga yinin ranar ba’a san inda yake ba. Fadeela ce tace “gaskiya Ya Musty bai kyauta ba, kuma ma fa abin mamaki he is nowhere to be found. I have never seen my friend this worried” Anty tace “ni zazzabin ma da ya saukar mata ne matsala na sannan ga rashin cin abinci” Sallamar shi suka ji wanda ya sa su duka suka yi saurin kallon qofar. Cike da mamaki Fadeela ta miqe tace “Ya Musty, where have you been?? Ka san halin da ka jefa qawa ta kuwa?” Maimakon ya nuna damuwa da hakan sai gani suka yi yana murmushi yace “wallahi Dee I have been busy ne, where is my Birthday girl??” Cike da mamaki suke kallon shi yayinda Anty tace “au, ashe ma ba mantawa kayi ba, kenan da gangan ka qi wishing dinta” Gani suka yi yayi dariya yace “bazaku gane bane” Fadeela ce tace “hmmm, this kind love self. Tana daki batada lafiya, she didn’t eat since morning kuma ta qi shan magani” Gani suka yi ya nufi hanyar dakin yayinda yake fadin “thanks Dee, I will handle it from here” Haka kuwa ya tafi ya bar su cike da mamaki. *********** Kwance take cikin duvet yayinda take ta kuka. Qwanqwaso qofar yayi sannan ya shiga. Tsayawa yayi kusa da gadon yana ta kallonta yayinda yake murmushi. A ran shi ne yace “Ya Allah nagode maka da ka bani wadda take bala’in sona” Zehra wadda take kwance ta san mutum ya shigo dakin amma a dalilin kanta yana cikin duvet bata san ko waye ba. she doesn’t even care domin kuwa hankalinta baya ma tare da ita. Jin muryar shi tayi yana fadin “My Angel zafi ake yi fa, AC yakamata ki kunna and not cover yourself like this” Can kuma sai yace “or are you ill??” Ya sani sarai bazata amsa shi ba don haka ne ya dan duqo ya yaye duvet din. Da sauri ta tashi tare da sauka daga kan gadon zata shige bathroom domin kuwa ko ganin shi bata son yi. Ai kuwa ko kafin ta daga qafafuwan ta yayi saurin riqe hannun ta. Cikin masifa tace “ka qyale ni, I hate you..” STORY CONTINUES BELOW Yana murmushi yace “and I love you My Angel” Murmushin da yayi kuwa ya qara bata haushi yayinda ta dinga qoqarin fizge hannun ta. Ji tayi yace “kin dai san bazaki iya qwacewa ba ko?? Just relax and listen to me” Zehra dai ganin tabbas bazata iya qwacewa bane yasa ta natsu yayinda hawaye suka cigaba da gangarowa daga idanuwan ta. Zaunar da ita yayi a kan gadon sannan ya janyo stool na Vanity table din dakin ya zauna. Yana kallonta yace “I am sorry..” Dago kai tayi tana kallon shi tace “I am sorry?? Abinda kadai zaka ce kenan?? Ka san abinda kayi mun kuwa?? You broke my Heart Baby..” Ji tayi yace “I swear I will mend it right away, I just need a favour from you” Ya dan shafa kan shi sannan yace “please je ki wanke fuskarki ki zo mu je..” Kafin ya qarasa maganar shi tace “babu inda zan je da kai” Miqewa yayi fuskar shi a murtuke yace “idan baki tashi ba zan dauke ki da kai na” Ganin yanayin fuskar shi ne yasa ta tashi ta shiga bathroom. Ko da ta fito wurin madubi ta nufa wanda kuwa yayi saurin dakatar da ita yace “don Allah kiyi haquri, you look beautiful even as you are all messed up. Just grab your Hijab lets go” Zehra wadda ta dan yi mamaki kuwa a ranta tace “ni fa sakarya ce, wai ko resisiting dinshi bazan iya ba?? gaskiya soyayya ta cuce ni”2 hahahaha… na today?? Gani nayi ta wuce ta dauko Hijab dinta ta sanya sannan suka fito. ************ Su Anty dai suna zaune suka ga fitowar su. Tana tafe yayinda yake biye da ita. Sossai suka cika da mamaki. Fadeela wadda ta miqe ce tace “like seriously??” Anty tace “yau na ga ikon Allah, Lallai soyayya shegiyar abu ce. Tun da safe ana fama da ke ki tashi ko abinci ne ki ci amma kika qi shine daga zuwan shi har ya lallabo ki..” Mustapha wanda yake biye da ita ne yayi musu sign da hannu akan suyi haquri su qyale ta yayinda ya kashe musu ido daya yace “Anty sai mun dawo” Fadeela da Khadeeja kuwa me zasu yi banda dariya. Ita kuwa Zehra daure fuska tayi ba tare da ta kalle su ba ta fice. *********** Tafe suke a kan hanya amma fa fuskar ta a murtuke. Ko kallon gefen shi bata yi. Duk maganar da yake ta yi mata ta qi responding. UNKNOWN PLACE🤔 Bata ankara ba ta ji yayi horn a gaban wani wuri wanda bata gama tantance ko ina bane.2 Securities din wurin ne suka gaishe shi cike da girmamawa yayinda suka bude gate din wurin. Tunda suka shiga kuwa na ga Zehra tana kalle kalle. Abinda dai ta sani shine lallai wurin yana da alaqa da gidan abinci.. more like kitchen, eatery or even catering service amma kuma da alama babu activity a ciki domin kuwa wurin sabon wuri ne. Yawancin abubuwan da ta gani a rufe suke alamar wurin bai riga ya fara functioning ba. Da sauri ta daga kai don ganin sunan wurin amma shima a rufe. Ginin bene ne wanda ya qawatu sossai. A ranta ne take fadin “Allah ya bani ikon mallakar irin wannan wata rana…” Bata kammala tunaninta bane ta ji ya bude mata qofar mota yace “lets go” STORY CONTINUES BELOW Bayan ta fito ne ya rufe qofar yayinda ma’aikatan wurin suka dinga kawo musu gaisuwa. Zehra dai ta yi mamakin ganin yadda suke ta girmama su. Da ta kasa jurewa ne tace “why are they greeting us this way??” Murmushi yayi yace “Probably because they feel its the right thing to do” Ko da suka iso bakin qofar shiga wurin tsayawa yayi yace “My Angel shiga, let me just answer a call” Zehra wadda ta qagara ta shiga don ta ba idanuwan ta abinci kuwa bata ma saurare shi ba ta shige cikin wurin. Tana shiga kuwa aka kunna wasu spotlights yayinda ta ga wani irin classy décor na 3D reflection wanda yayi displaying rubutu kamar haka “HAPPY 22ND BIRTHDAY MY ANGEL” Bata ankara ba ta ga an saki wasu red and white balloons daga sama. Sossai wannan Abu ya birge ta. Idanuwan ta a lumshe na ga ta daga kanta sama yayinda tayi stretching hannuwan ta. Ji nayi tana fadin “Oh my God, this is beautiful..” Gani nayi ta ruga a guje cikin wurin tana bin ko ina da kallo cike da tsananin mamaki. Ihu ta dinga yi tana fadin “Wooow..” yayinda take ta zagaye ko ina. Sossai Zehra tayi murna domin kuwa decor din ya birge ta matuqa. Everything so Classy. Qarasawa tayi wurin jerin wasu kyawawan Cakes dayawa ta fara qirgawa. Tana yi yayinda take ta zaro idanuwa. Ni dai ji nayi ta ce “22 Cakes??” Muryar shi ta ji a bayan ta yana fadin “I am sorry my Angel for ruining your day, Happy Birthday to you” Da sauri ta juyo ta gan shi tsaye yayinda ya riqe kunnuwan shi alamar neman afuwa. Girgiza kai tayi tana murmushi tace “Oh my Baby, you did all these for me?? Thank you very much, wallahi I am so happy” Matsawa tayi kusa da shi tace “I am sorry, I never thought you had plans for my birthday, I swear I have never had a birthday suprise like this one all through my life” Ta kalli cakes din tace “22 Cakes?? Baby why??” Yana murmushi yace “…..for each and every birthday of yours that I missed”17 Gani yayi ta fashe da dariya yayinda tace “you are crazy” Shima yana dariya yace “Crazily in love with you My Angel” Cike da mamaki tace “but Baby, why do we have to come here?? Who has this place??” Ji tayi yace “sssshhhhhh, come” Zehra dai bin shi tayi yayinda suka haura sama. Tayi masifar rudewa domin kuwa saman wurin sossai ya hadu. bata yi tunanin wurin ya kai girman haka ba. Abinda ya birge ta shine tsarin interior decor din kaman a turai. Wani office ya bude sannan ya matsa mata yace “after you” Zehra kuwa tana shiga na ga ta zaro idanuwa tace “Oh my… Oh my… OMG, Baby??” Da sauri ta qarasa shiga cikin wurin yayinda ta dinga zagayawa tace “everything here is to my taste.. don Allah waye wannan da…” Yana dariya ya nuna mata executive chair na office din yace “Sit here” Zata yi Magana yace “Ssshhhh, just don’t say anything and sit” Zehra ta zauna yayinda ya dauko wani file ya miqa mata yace “congratulations to you Zehra Abu-Yazeed, The CEO of EM-ZEE KITCHEN AND CATERING SERVICE..” STORY CONTINUES BELOW Zaraf ta miqe cike da mamaki yayinda tayi ihu tace “whaaaaat???” Yace “yes my angel, a small birthday gift from your Baby…”2 Zaro idanuwa tayi tace “like seriously?? you call this small??? Baby you know what you just did?? you just fulfilled my biggest dream aside aure na da kai ofcourse..” tare da kashe mishi ido daya. Dariya yayi yace “I am glad you like the gift” Tana riqe da file din ta matsa kusa da shi ta nuna mishi rubutun sunnan wurin yayinda tace “this is the part I love the most” Ta dago kai ta kalle shi tare da fadin “EM-ZEE.. EM for Mustapha and ZEE for Zehra..” Ta ajiye file din akan table tace “I pray it will always be me and you my Baby” Yana murmushi yace “Ameen my Angel.. its EM-ZEE but actually 100% ZEE’s” Tana dariya tace “it’s EM’s too my Baby” Kallonta kawai yake yana murmushi yayinda ta cigaba da fadin “amma dai ka san if not because babu kyau I would have given you a tight hug ko?” Fashewa yayi da dariya yace “yeah lokaci ya kusa zuwa for that” ya shafa kai yace “Oh Allah, can’t wait” yayinda ta fashe da dariya.4 Gani yayi ta zabura tace “na shiga uku, I don’t even know where to start from. Baby this is my dream come true fa..” yana dariya yace “I know” Tana ta zagaya wurin kamar mahaukaciya ne ya riqo hannun ta yace “hey relax, zo ki zauna akwai maganar da nake so mu yi” 🤔🤔🤔🤔 Da sauri ta koma ta zauna yayinda tace “ina jin ka Baby” shima zama yayi yana fuskantar ta yace “I think few months after bikin Dee zan tafi Italy, akwai wani course da zamu yi a can har kusan tsawon four years..” Kafin ya rufe bakin shi ta dafe qirji tare da miqewa tace “whaaaat?? Wallahi Baby ban yarda ba..” Tuni hawaye sun fara wanke fuskar ta yayinda hankalin shi ya tashi. Hannun ta ya riqe yace “daina kuka My angel, please sit down and listen to me” Zehra dai zama tayi yayinda ta cigaba da zubar da hawaye. Ji tayi yace “I can’t go without you My Angel shiyasa nake so inyi ma su Daddy Maganar auren mu. Let’s get married sai mu tafi tare” Da sauri ta dago kai ta kalle shi tace “dagaske kake yi??” yana murmushi yace “ko bazaki aure ni bane??” Tana share hawayen fuskar ta ne tace “ai bani da burin da ya wuce in ga na zama matar ka Baby, I want to spend the rest of my life with you. In haifo maka yara masu kama da kai..” Dariya yayi yace “guda ashirin kawai nake so duka mata masu irin idanuwan ki…My angel eyes” Zaro idanuwa tayi tace “whaaat?? Wallahi bazan iya ba. baka san an ce haihuwa akwai wahala ba?” Dariya yayi yace “just kidding My Angel, duk yadda kike so haka za’a yi. Your every wish will always be my command. I love you very much” Tana murmushi tace “I love you too and thank you very much for this special gift” Wayar shi ce tayi ringing inda aka sanar da shi anyi setting musu dinner just as he requested. Bayan ya kashe wayar ne yace “mu je mu ci abinci, na ji ance rabon ki da abinci tun jiya” Miqewa tayi cikin shagwaba tace “toh ba laifin ka bane??” Yace “yi haquri, Baby ba zai qara ba” tayi dariya. Suna tafe ne tace “toh wai yanzu how do I start running this big place?” Yace “everything is taken care of, I have hired the best people to assist you in running it, ofcourse with the help of your cooking school chef. You will get to meet them” Cike da mamaki tace “you mean even Chef Laura ta sani??” Yace “yes, tace saura 2 weeks ma kuyi graduating ai ko??” Tana murmushi tace “yes” Yace “again, she told me you are her best student and that she doesn’t even know why you are there learning when you know and can do everything” Dariya tayi tace “don’t mind her, babu wani abinda na iya” Yana dariya yace “Liar, ai muma mun shaida. You are very good” Lumshe idanuwa tayi tace “thanks Baby, wallahi gani nake yi kamar a mafarki, I still can’t believe this is for me” yayinda take nuna wurin. Hannun ta ya riqo ya dunqule a cikin nashi yace “My Angel, soyayyarki a cikin jini na take. I really love you which means I can do anything for you. My happiness lies in yours” Cike da farin ciki tace “thank you My Baby” Daga nan suka qarasa wurin table din da aka shirya musu abinci kala kala suka zauna don yin dinner. ♤♤♤♤♤♤♤ hmmm hmmmm hmmmmmm…. What a birthday special for her😘😘

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]