-->
olNGIb4NkK5r2x7x4oG3GpEzizVpnY6KNCck9cym

ZEHRA CHAPTER 15 KARSHE

ZEHRA CHAPTER 15 KARSHE
MUSTAPHA OMAR TAFIDA RESIDENCE Wuraren qarfe goma da rabi na safe kwance take a kan gadon yayinda yake maqale da ita. Kanshi a bisa qirjinta yana ta bacci yayinda take rungume da shi kamar wadda take tsoron kar a sace mata shi.. Kusan mintuna talatin kenan da Zehra ta farka amma a dalilin bata so tayi interrupting baccin nashi ne ta qyale shi. Bata ankara ba ta ji ya dan motsa, da alama ya farka ne. Jin yayi shiru ne tace “Baby??” Yace “na’am” Tace “ka tashi ne?” Kai tsaye yace “a’a” Fashewa tayi da dariya tace “baka tashi ba?? Toh da wa nake Magana??” Muryar shi qasa-qasa yace “My Angel bana so in tashi ne, duk tsawon rayuwa ta ban taba yin bacci mai dadin wannan ba, I feel kamar in cigaba da bacci a jikin ki har abada” Zehra wadda ta qara matse shi a jikinta tace “Baby my body is all yours, so duk yadda kake so kayi da shi zaka yi... anytime! amma yanzu kayi haquri muyi wanka sai mu yi breakfast.. Ka ji??” Kai tsaye yace “bana jin yunwa” Tace “wallahi baka isa ba, kawai ka tashi ko inyi fushi” Da sauri ya tashi zaune yayinda yace “My angel idan kika yi fushi da ni sai na shiga uku a rayuwar nan” Tashi tayi zaune tana dariya yayinda ta janyo shi ta dinga aika mishi soft kisses ta ko ina sannan tace “I love you” Fuskar ta ya shafa yace “hey I forgot to ask you, hope jikin ki baya yi miki ciwo?? Do you need…” Gemun shi ta ja sannan tace “ba sossai ba, you were being gentle all through ai…” ta goga hancin ta da nashi tace “you are so sweet my Colonel” Murmushi yayi yace “thanks My Angel” Tare suka shiga bathroom don yin wanka wanda kuwa sunyi ya kusa awa daya a ciki. Dariyar su kawai na dinga ji tare da qarar ruwa da alama wasa suke yi da ruwan. Sai da suka bata lokaci a ciki sannan suka fito. Ko da suka fito bayan ya shirya cikin three quarter Capripant da T-shirt ne ya nufi dakinta ya dauko mata nata kayan. Wata sleeveless free gown marar nauyi ya dauko mata yayinda ya zauna yana ta kallonta har ta shirya tsab. Kallon shi tayi tace “mu je ka raka ni Kicin” Ko kafin ta daga qafafuwanta sai gani tayi ya duqo ya dauke ta yace “okay my Queen” ************ Ko da suka shigo kicin din sai da ya bata full glass cup na fresh milk ta shanye sannan ta fara hada breakfast din. A cewar shi she needed something to give her strength domin kuwa ya sani sarai ya gajiyar da ita sossai a daren jiyan. Zaune yake a kan kujerar Kitchen Island yayinda yake ta snapping dinta hotuna tana aikinta. Ji nayi tace “Baby dagaske wadanda basu yi kyau ba zaka yi deleting” Murmushi yayi yace “My Angel I have told you before, ko kuka kike yi kina kyau… you are a natural beauty” Gani nayi ta zagayo ta bayan shi ta kwanta yayinda ta rungume shi tace “thank you very much my Baby” STORY CONTINUES BELOW Wayar shi ce tayi ringing inda ya ga sunan Fadeela. Bayan yayi answering ne ya sa a speaker phone. Aikuwa ji suka yi tace “Romeo ka tashi lafiya??” Mustapha wanda yake dariya yace “Dee wallahi kin raina ni, toh zan baki amsar da kike son ji… Na tashi lafiya and I had the best time of my life...” Da sauri ta dakatar da shi tana dariya tace “Yi haquri Ya Musty, dama fa yamsen ce take so tayi Magana da kai, tun jiya take ta takura” Yana murmushi yace “okay give her the phone” Aikuwa muryar ta suka ji tace “Abbu please come”2 Mustapha yana shirin yin Magana ne Zehra ta kai bakinta saitin kunnen shi tace “please kar ka dauko ta” toh fa... Murmushi yayi yace “Zan zo My princess” Tace “yau??” Yace “not today, Abbu zai je wani wuri kuma idan bai je ba za’a zane shi da bulala” Kamar kullum kuwa tana jin bulala ta rude. Ji nayi yace “kina so a zane Abbu??” Kai tsaye tace “no Abbu” Haka dai suka cigaba da hira har suka yi sallama. A lokacin kuwa Zehra ta gama hada breakfast ta ajiye a gaban shi ta zauna. 1 Ya kalli plate din sannan ya kalle ta cike da tausayawa yace “My Angel this looks good, sannu da aiki.. duk kin gaji ko??” Dariya tayi yayinda tace “wanne gajiya Baby, ai girki babu wahala especially if its meant for your loved ones” Murmushi yayi yace “can i??” Tace “nope, ni zan baka” Ko da ta bashi bite din farko gani nayi ya lumshe idanuwa yayinda yace “wooow.. My angel this tastes superb. Ya sunan abincin?” Kai tsaye tace “Moha’a recipe”4 Cikin confusion yace “as in?? ban gane ba..” Dariya tayi tace “Yaaya ne ya koya mun, when I asked him sunan dish din sai yace shima bai sani ba, he ended up naming it Moha’s recipe” Mustapha ya girgiza kai yace “Allah sarki Muhammad, I missed him A lot, Ubangiji Allah ya jiqan shi” Tace “ameen” Yana kallonta yace “I guess you understood what I meant when I told you he was a great person” Murmushi tayi tace “yes I do, he was surely a great person, the problem was that I loved and still love only one person duk duniyan nan… YOU my Baby” STORY CONTINUES BELOW Murmushi yayi yace “I am grateful for that My Angel” Tana kallon shi tace “Ni kam I am glad I have achieved my greatest dream a duniyar nan… becoming Mrs M Tafida” Yana murmushi yace “speaking of dreams my Angel, I promised you our honeymoon in Dubai dukda dai kin karya shi jiya but we will still go… what say??” Cike da murna tace “I say yes my Baby” Yace “mu tafi gobe??” Zaro idanuwa tayi tace “whoa.. Gobe My Baby??” Yace “yeah, kin san na kusa komawa aiki gwara muyi utilizing hutun nawa” *************** Bayan sun gama breakfast din ne ta raka shi Gym din shi na nan gidan don ya dan yi working out, shi kam Mustapha a kullum dole ne sai yayi exercise domin kuwa ya saba. Ita dai Zehra tayi mamakin ganin qaton Gym a cikin gidan. Ko da ta tamabaye shi dalilin da ya sa yake zuwa Gym when he has one at home sai cewa yayi ya fi sabawa da na can din ne shiyasa. A ranar kuwa suka yi booking flight suka yi reserving masaukin su a can Dubai din. Da yamma ne suka shirya don zuwa gidan iyayen nasu suyi musu sallama. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Mummy ce zaune a falonta tana kallon tashar BBC a lokacin da suka yi sallama. Sossai Mummy ta ji dadin ganin su. Zehra wadda ta qarasa wurinta kuwa har qasa ta duqa ta gaishe ta yayinda tayi saurin riqo hannunta ta zaunar da ita gefen ta tace “yaushe muka fara haka da ke Zehra?? zo ki zauna kusa da ni. Ya gida?” Zehra wadda take murmushi tace “lafiya lau Mummy” Ta kalli Mustapha tace “ya jikin naka? Ka dai warware babu inda yake yi maka ciwo ko??” Yana murmushi yace “Alhamdulillah Mummy, I am good. Daddy bai dawo ba??” Tace “munyi waya da shi anjima kadan zai iso insha Allah. Ina Yasmeen??” Yace “tana gidan Dee tun jiya, dama fa mun zo muyi muku sallama ne.. zamu je Dubai honeymoon dinmu idan Allah ya kaimu gobe….”3 Muryar Zehra suka ji tace “na shiga uku Baby???” Zehra wadda ta zaro idanuwa tana kallon shi sossai ta cika da mamakin yadda yayi maganar ba tare da jin kunyar Mummy ba. Yana kallon ta ne yace “My angel what??” Mummy ce ta fashe da dariya yayinda Zehra ta miqe cike da kunya ta bar falon. Mustapha wanda yake kallon Mummy cike da mamaki yace “did I say something wrong??” Mummy tana dariya tace “kunya ta ji don kace zaku je Honeymoon”3 Girgiza kai yayi yana murmushi yace “ooooh.. that?” A haka dai suka cigaba da hirar su har Daddy ya dawo. Zehra ta je har falon shi ta gaishe shi. *********** Lokacin Dinner ne Zehra ta shiga kitchen din don taya su Larai dafa abinci wanda kuwa a qarshe ma sallamar su tayi ta shiga girkin da kanta. Bayan sallan Isha’I tana tsaye a kitchen din tana qoqarin kammala shirya abincin ne ta ji an rungumeta ta baya. STORY CONTINUES BELOW Ajiyar zuciya ta saki yayinda tace “Baby… ka dai san ba gidan mu bane ko?? Idan Mummy ta shi…” Bata qarasa maganar ta ba na ji tana sauke numfashi a dalilin wasu zafafan kisses da ta ji yana sakar mata. Zehra dai tuni ya jefa ta wata duniyar yayinda ta juyo ta fuskance shi tare da sagala hannuwan ta a wuyan shi ta tura bakinta cikin nashi yayinda suka fara kissing juna. Gaba daya sunyi nisa a romancing juna ne suka ji muryar Mummy tana fadin “A kitchen dina za’a fara honeymoon din kenan??”3 Zehra wadda ta cika da tsananin kunya kuwa gani nayi ta runtse idanuwan ta yayinda ta boye fuskar ta a qirjin shi. Mustapha ya dan sosa kai ya juyo ya kalli Mummy yayinda yace “Yi haquri Mummy, wallahi I just couldn’t help it ne… I swear bala’in son matar nan tawa nake yi” Zehra wadda ta ji kamar ta nitse a qasa don kunya kuwa sossai jikinta yayi sanyi. Mummy dai dariya tayi tana girgiza kai tayi tace “Allah ya shirye ka Mustapha” sannan ta juya ta bar kicin din” Mummy tana fita kuwa Zehra ta ture shi yayinda tace “baby wallahi ka cuce ni, Yanzu Mummy zata ce banda kunya” Fashewa yayi da dariya yace “on the contrary she is happy that we are happy” Ko da suka zauna dinner Zehra dai cike da kunya ta dinga cin abinci wanda Mummy ta kula da hakan. Ita kam murna take yi a dalilin soyayyar ta dan nata ya canza gaba daya to a better person. Babu abinda take yi banda sa ma Zehra albarka. ************ Bayan sun bar gidan daddy ne suka wuce gidan Papa don yi musu sallama. Basu bar gidan ba sai wuraren qarfe goma wanda kuwa straight gidan su Fadeela suka je. A lokacin da suka je gidan kuwa sun tabbatar Yasmeen tayi bacci don haka kuwa hankalin su a kwance suka sha hira sannan sukayi sallama.3 Washegari kuwa suka hau jirgi sai Dubai. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ BURJ-AL-ARAB, DUBAI Sun sauka a shahararren masaukin baqin nan na Dubai wato Bur-al-arab. Wani lafiyayyen Honeymoon Suite suka sauka wanda kuwa ya hadu iya haduwa. Tunda suka iso kuwa babu abinda sukeyi banda soyayya, sossai Zehra da Mustapha suke gurzar soyayya. Sai da suka yi kwana uku suna indoors sannan suka fara fita yawo. Sun zagaya wurare da dama sannan ya kashe kudi sossai kamar ba neman su akeyi ba. Wata irin rayuwa mai dadin gaske suke yi a wannan qasar. ************ A yau kwanan su shidda da zuwa Dubai. Da safe Zehra tana tsaye gaban dressing mirror yayinda take qoqarin gyara handle din bra din da ta sanya wadda ta murde. Bata ankara ba ta gan shi a bayan ta. Ji tayi ya balle hook na bra din yayinda ya rungume ta. Zaro idanuwa tayi tace “Baby ya haka??” Yana qoqarin zare shi daga jikinta ne yace “I swear I don’t like this thing, wai dole ne sai an sa shi?” Fashewa tayi da dariya tace “toh me yayi maka??” Ya jefar da shi sannan ya fara wasa da boobs dinta yace “yana hana easy access, don Allah My angel tunda dai ba dole bane ki daina sa shi..” STORY CONTINUES BELOW Girgiza kai tayi sannan ta juyo ta fuskance shi tare da fadin “Yadda kake so haka zanyi My baby” Kissing dinta ya shiga yi ta ko ina yayinda yake ta romancing dinta. Idanuwan ta a lumshe tace “ina ka je tun dazu ina ta neman ka??” Muryar shi qasa-qasa yace “na je Gym ne, kiyi haquri lokacin da na tashi kina bacci and I didn’t want to disturb” Zehra wadda take ta karbar saqonnin da yake aika mata tuni ya jefa ta wata duniyar. Tana maqale a jikin shi ne ta ji yana neman zarcewa yayinda tayi saurin fadin “don Allah Baby kayi haquri, yanzu fa nayi wanka…” Ji tayi yace “sai mu je mu qara yin wani My Angel” Cikin shagwaba tace “Baby please..” Numfashi ya sauke sannan yace “okay My Angel..” Ya janyo rigar ta ya zura mata yayinda yace “ki duba lounge I dropped something for you on the table… hoping you’d like it” Tace “what is it Baby??” Yace “just go and see for yourself... bari inyi wanka in zo” Ko da ta iso Lounge din gani nayi ta tsaya cak yayinda ta hango wasu roses neatly arranged a cikin wani heart shaped package.  Da sauri ta qarasa wurin table din yayinda ta duqa ta kai hancinta kusa da roses din tana shaqar qamshin su mai dadin gaske. Lumshe idanuwa tayi tare da fadin "hmmm... how sweet" Wani card da yake gefe ne ta janyo ta bude. Rubutu ta gani kamar haka: “if I did anything right in my life, it was when I gave my heart to you. I love you for all that you are, all that you have been and all that you will be My Angel. A very happy Valentine’s day to you” Zehra ta karanta wannan message din ya fi sau goma. Gani nayi ta rungume card din yayinda ta runtse idanuwan ta. Bata san yawan lokacin da ta bata a tsaye ba sai ta ji ya rungumeta ta baya yayinda yace “hey my angel hope you liked…” Bai qarasa rufe bakin shi ba ne ya ji sheshekar kukanta. Cikin tsananin tashin hankali ya juyo ta da sauri yayinda ya ga hawaye suna bin fuskar ta. A rude yace “subhanalillah, my angel ya haka kuma??” Gani nayi yayi saurin karbar card din daga hannun ta yana fadin “baki son abinda na rubuta ne?? bari a yaga…” Da sauri Zehra ta karbi card din tare da rungume shi tightly. Muryar ta qasa-qasa tace “Baby this means a lot to me, I cant thank you enough for the love you have shown me. I will forever be grateful for everything.. bani da kamar ka a duniyar nan” STORY CONTINUES BELOW Murmushi yayi yace “huh... thank God. Nima haka my Angel, without you I am useless...” Ture shi tayi tace “tell me, ya aka yi kasan yau Valentine??...” tayi mishi wani irin kallo yayinda ta cigaba da fadin “....kana celebrating da wata kenan before ko??” Fashewa yayi da dariya yace “I swear ban taba ba, wani ne muka hadu a gym shine muke hira da shi, toh anan ne ya fadi mun and he took me to a shop just across the street. He bought something for his girl and I decided to get you this” Turo baki tayi tace “I didn’t even know today's date, thanks to you. Wai meyasa ka boye mun waya na?” Kumatun ta ya ja sannan yace “just… mu je muyi breakfast sai mu fita yawo. Ko bazaki je ba??” Da sauri tace “zan je Baby” Daga nan suka nufi wurin breakfast din da tayi musu ordering yayinda na ji tana fadin “Baby zamu qara komawa Palm Jumeirah please, I forgot to take pictures” Yana murmushi yace “anything for you my Angel” ************ Tsawon sati uku sukayi a qasar Dubai. Sun yi yawo sossai sannan sun huta don kuwa har a jikin su hutun ya nuna musamman Zehra wadda ta samu kwanciyar hankali. Dubai surely held some memories that they will forever remember and cherish. ************ Ana gobe zasu bar qasar daddare Mustapha yana zaune a kan kujera riqe da laptop yana wani abu very important ne ta fito daga bathroom daure da towel, da alama wanka tayi. Daga kai yayi ya kalle ta yayinda ta kashe mishi ido daya. Murmushi yayi tare da blowing mata kiss yace “I love you” Tayi mishi gwalo tare da fadin “say something I don’t know” Dariya kawai yayi ya cigaba da abinda yake yi wanda kuwa jefi-jefi yana daga kai yana kallonta yayinda soyayyarta take yawo a jinin jikin shi. Yana kallonta ta gama ‘yan shafe shafen ta sannan ta miqe ta nufi dressing room don shiryawa. Gani yayi ta fito sanye cikin wata sexy Baby doll nightie Pink wadda ta bayyana sirrin jikinta. Lumshe idanuwa yayi yayinda yace “Ya salaam, Allah nagode maka da ka bani wannan kyakyawar a matsayin mata” Fashewa tayi da dariya yayinda ta fara approaching dinshi. Ko kafin ta qaraso sai gani nayi ya canza page din da yake. 🤔🤔🤔🤔 Gefen shi ta zauna tace “wai me kake yi ne?? ka zo mu je muyi bacci” Kiss yayi mata a goshi yace “I am just trying to finish up some work My Angel, je ki kwanta and I will be right behind you” Turo baki tayi cikin shagwaba tace “amma fa you said there won't be work all through..” Kafin ta qarasa maganarta ne ya janyo ta jikin shi sannan ya fara kashe mata jiki da sweet kisses dinshi yace “yi haquri my Angel, this is kinda important ne kuma I swear idan kina nan bazan iya qarasawa ba” Miqewa tayi ranta a bace tace “yeah because I am a distraction..” Daga nan ta wuce ta haye gado tare da shigewa duvet ta juya mishi baya. Mustapha dai ya sani sarai ta ji haushi ne but he needed to finish what he was doing. Komawa yayi page din da ya rufe yayinda ya cigaba da latse-latsen shi. STORY CONTINUES BELOW Bayan kusan minti goma sha biyar ne ya gama sannan ya kashe. Kai tsaye kan gadon ya haye yayinda ya shige duvet din ya matsa jikinta ya dora kan shi a kan kafadarta yana ta shaqar qamshinta. Ji yayi tace “leave me alone, go and touch your laptop” Fashewa yayi da dariya yace “yi haquri my angel..” daga nan ya zura hannun shi a cikin nighty dinta yayinda ya dinga sarrafata kamar yadda yasan yana haukata ta. Nan da nan tayi laushi tana ta sakin numfashi. Juyowa tayi ta rungume shi gam yayinda suka fada wata duniyar. Duniyar da suke bala’in so, duniyar da ta fi musu komai dadi, duniyar da idan suka shiga basu so su fito, duniyar da suke fata su kasance a cikinta har abada. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Washegari ko da suka shirya barin Dubai Zehra ta ga ticket dinsu wanda ta zama confused. Ji nayi tace “Baby Greece?? Why?” Murmushi yayi yace “because akwai abinda zamuyi a can, just for a few days” what could it be???🤔 Ita kuwa dadi ta ji don ko babu komai ta san cewar they will get to spend more time together. Ita dai bata qi su je koma ina bane as long as they are together.3 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ KIVOTOS HOTEL AND VILLAS SANTORINI, GREECE One of the best places with a beautiful location a qasar. Zehra dai tunda suka iso ta rude gaba daya. She was so happy especially yadda yanayin wurin yake kamar ba reality ba. It looked more like a fantasy land. 1 Kwanan su biyu a wannan wurin basu fita ko ina ba, soyayya lafiyayya suke gudanarwa. Kashe wayar shi ma yayi gaba daya domin ko da wasa baya son interruption. ************* A ranar da suka cika kwana uku da daddare Zehra tana tsaye a gaban mirror tana ta taje gashin kanta. Sanye take cikin wata lafiyayyar black nighty yayinda hankalinta yayi nisa. Bata ankara ba ta ji ya rungume ta so tightly ta baya yayinda yake ta shaqar qamshinta as usual. Murmushi tayi tace “Baby tun dazu ina ta jiran ka, ina ka je?” Yace “wani wuri na je My angel” Juyo ta yayi sannan ya sa mata idanuwa yana murmushi. Wayar shi ya fitar ya dinga snapping dinta hotuna yayinda yace “toh yanzu da kika yi wanka ni kuma fa??” Murmushi tayi tace “haquri zaka yi ka je kayi babu ni…” Cikin irin shagwabar da take yi mishi ne yace “gaskiya bazan iya ba, kawai ki zo mu je kiyi mun” STORY CONTINUES BELOW Kallon rashin yarda tayi mishi tace “zan je only if you promise me cewar you won’t do anything to me…” Girgiza kai yayi yace “I will try but gaskiya banyi alqawari ba” Fashewa tayi da dariya sannan tace "ya zanyi da kai??" Haka dai babu shiri ta bi shi bathroom din wanda kuwa kamar kullum sai jin dariyar su nake yi yayinda suka jefa juna duniyar su ta masoya. Ko da suka fito maqale take a jikin shi yayinda suka fada gado suka cigaba da kwasar soyayyar. ************** Washegari da safe wuraren qarfe tara da rabi na safe Zehra tana cikin Duvet tana ta bacci. Gani nayi ta dan motsa yayinda ta bude idanuwan ta ahankali. Ganin shi tayi zaune a gaban ta yana kallonta yayinda yake murmushi. Itama murmushin tayi yayinda tace “Good morning my handsome Colonel” Yana murmushi ya ja kumatun ta tare da fadin “and HAPPY BIRTHDAY to you my Angel” Zaro idanuwa tayi tace “whaaaaaaat??” Da sauri ta tashi zaune tace “Baby today is my birthday??? Like seriously??” Yana dariya yace “yes My angel..” Ji yayi tace “ya akayi ban tuna ba??” Ta Harare shi tace “duk laifin ka ne” ta qara zaro idanuwa tace “oooooohhhhh, shiyasa dama ka qwace mun waya ka boye tun a Dubai don kar in tuna??” Dariya yayi tare da kashe mata ido daya yace “that’s the whole idea my Angel… to surprise you” Bata ankara ba ta ga ya miqa mata wani dan qaramin gift box yace “here, open it” Ko da Zehra ta karba ta bude wani lafiyayyen Diamond necklace ne ya haske fuskar ta. Zaro idanuwa tayi sannan tace “wooow, Baby??” Yana kallonta yace “you like it??” Cikin ihu da murna tace “I love it” Rungume shi tayi tace “Baby thank you very much, you always find a way to make my birthday special, I love you very much” Yana murmushi yace “I love you too my Angel.. kawo in sa miki” Ta miqa mishi tare da juyawa ta dage gashin kanta yadda zai ji dadin sanya mata. Bayan ya sanya mata ne ya juyo da ita ta fuskance shi yayinda ya shafa pendant din yace “its beautiful but you made it more beautiful my Angel” Tana murmushi tace “thank you” yayinda ta haye bisa cinyar shi ta fara jefa mishi kisses irin wadanda suke haukata shi. Sun dade suna romancing juna ne yace “hey, tashi mu shirya muyi celebrating.. it’s the reason why we are in Greece, Your Birthday” Zaro idanuwa tayi tace “are you serious??” yace “yes dear, You are my angel, kin cancanci fiye da hakan” Gani nayi ta tsaya tana ta kallon shi yayinda take gode ma Allah da ya bata Mustapha. Wani mugun son shi take yi. Fingers dinshi yayi snapping a saitin fuskarta yayinda ta saki ajiyar zuciya tace "Allah ya bar mun kai my Baby" yana dariya yace "Ameen my angel" *********** Zehra dai bata san inda zasu je ba. Ko da sukayi wanka abinda ya bata mamaki shine kayan da ya zabar mata wanda ta zaro idanuwa tace “Baby ya za’a yi in fita da wannan?” STORY CONTINUES BELOW Yana murmushi yace “sssshhhh, just wear it” Aikuwa tana sanya kayan ya sa mata idanuwa babu qyaftawa. Wata V-neck strap mini dress red colour ya zabar mata. Curves dinta sun fita a rigar gwanin ban sha'awa. Gashin kanta kuwa daure shi tayi a tsakiya yayinda tayi kamar wata barbie doll. Rungume ta yayi yace “wallahi My angel zaki kashe ni da kyan nan naki…” tana murmushi tace “ka fi ni kyau Baby” Ya girgiza kai yace “lets not go there” Ta fashe da dariya. Zehra dai gani tayi ya bude wata qofa wadda ta sada su da wani open space. Wani table ta hango dauke da wasu beautiful cakes guda hudu. Ko da suka qarasa wurin tace “four cakes….” ta kalle shi sannan tace “Oh my God... for my birthdays da kayi missing” Ya girgiza mata kai alamar 'eh' yayinda yake murmushi. Rungume shi tayi tace “Oh my God, Baby ni kam na rasa wane irin so nake yi maka.... I pray we continue to celebrate my birthday together..” yana murmushi yace “har jikokin mu Insha Allah” ta fashe da dariya. Tana qoqarin yanko cake din ne yace “hey, eat a little because there is more..." Zehra wadda ta yanko cake juyowa tayi tace "open your mouth" Ko da ya bude sanya Cake din tayi bakinta sannan ta hada da bakin shi suka cinye cake din tare yayinda suka cigaba da smooching juna. Sai da suka yi mai isan su sannan suka sassauta yayinda ya janyo hannunta suka cigaba da tafiya. Gani nayi Zehra ta tsaya cak tare da zaro idanuwa. Ihu ta saki tare da fadin "Baby??????? Is this for real??” Sakin hannun shi tayi ta ruga a guje tana qare ma wannan wurin kallo. Ni kaina na rude domin kuwa wani lafiyayyen breakfast table ne Wanda aka shirya in a romantic setting. Wannan table din dai yana daf da wani heart shaped pool ne. Abinda ya fi birge ni kuwa shine lafiyayyen view na ocean wanda ya qara ma wurin kyau da tsaruwa. 4 Mustapha dai tsayawa yayi yana kallon yadda take ta tsalle tana zagaya wurin. Shi kam burin shi a duniya bai wuce ya ga Zehra tana cikin farin ciki ba. His happiness surely lies in her's.... Juyowa tayi cike da murna ta rugo ta rungume shi so tight wanda har sai da yace "ouch" Ji nayi tace “woow Baby I love this place, I love the suprise, the gift, everything..." Ta fara jefa mishi kisses ta ko ina tana fadin "I love you, I love you, I love you soooo much” Cike da jin dadi yace “I am glad you liked everything my angel, I love you to the moon and back” Sun dade a nan tsaye suna jaddada ma junan su irin son da suke yi ma juna yayinda suka dinga romancing juna. Da qyar suka haqura suka nufi table din don yin breakfast. Bisa cinyar shi ta zauna. Duk abinda ta dauko ta sa a bakinta kuwa sai ta hada da bakinshi su cinye tare. A haka suka cigaba da cin abincin yayinda suke ta kwasar soyayya suna daukar selfies kala kala. Zehra dai farin cikin da Mustapha ya sanya ta marar misaltuwa. Ta ji dadin suprise birthday din da yayi mata, ta ji dadin rayuwar da suka yi a Santorini Greece. She surely had the best time of her life. They shared beautiful moments together, they got much more closer to each other, they created alot of beautiful memories together. They lived THE DREAM... the kind of life they always wanted to have.2 ♤♤♤♤♤♤♤♤ Bayan sun dawo Nigeria kuwa tuni Mustapha ya koma aiki wanda a kullum da safe tare suke fita su ajiye Yasmeen a school sannan ya ajiye ta a ofis dinta daga nan ya tafi barrack.+ A wurin aikin nasu kuwa da sunyi kewar juna zaka ji suna hira a waya... Hirar su ta soyayya wadda bata qarewa. Wani lokacin ma idan Mustapha baya da wani aiki mai yawa guduwa yake yi ya tafi office dinta su rufe qofa su kwashi hirar soyayyar su. Watarana ma janye ta yake yi su wuce gida. ♤♤♤♤♤♤♤♤ MUSTAPHA OMAR TAFIDA RESIDENCE A yau Saturday, satin su biyu da dawowa daga honeymoon dinsu. Zehra ce ta gayyaci Fadeela da Hidaya tare da mazajen su lunch a gidan su. Tsaye take a kicin yayinda Hidaya take zaune a kan kujerar Kitchen Island. A yanzu kuwa cikin Hidaya ya kai wata shidda.2 Fadeela ce tsaye tana taya Zehra kammala lunch din yayinda suke ta hira. Zehra wadda ta nufi wurin Kazar ta da take grilling sai gani nayi tayi pause yayinda ta dafe kanta. Gani suka yi ta tafi zata fadi. Fadeela wadda take kusa da ita ne tayi saurin riqe ta tare da fadin “Subhanalillah... Zee ya haka??” Hidaya ma tuni ta miqe ta qaraso wurin su a rude. Muryar ta qasa-qasa tace “wallahi Dee wani jiri ne ya debe ni yanzun nan” Janyo kujera sukayi sannan suka zaunar da ita. Gani nayi ta dafe qirjinta yayinda zuciyarta take ta tashi. Hidaya wadda take kallon Zehra tace “Babe you need to take a pregnancy test, da alama you are pregnant…” Fadeela wadda take kallon Hidaya tace “hey, kuma fa haka ne” Ta kalli Zehra tace “ni fa dama nace wannan glowing din da kike yi akwai wani abu... I am sure yaya na yana da ajiya a cikin nan naki” Zehra wadda take kallon su gani nayi tayi murmushi tace “kuna ganin ciki gareni dagaske??” Fadeela ta Harare ta tace “eh mana, yaushe rabon ki da ganin nightmare din naki?” Zehra shiru tayi tana tunani sannan tace “wallahi nayi losing count, gaba daya Baby ya dauke mun hankali… I think about nothing but him” Hidaya tana dariya tace “aikuwa ga result ya fito... try and take the test or just go to the hospital to confirm” Zehra tana murmushi tace “Allah yasa I am pregnant wallahi, Can't wait to see our child.. na tabbatar he will be so happy to hear the news” Fadeela tace “Yes dear... na ga Ya Musty yana son yara gaskiya... ki ga fa yadda yake wasa da su Yasmeen” Haka dai suka cigaba da hira yayinda suke ta yi mata fatan Allah yasa akwai cikin. Wasa wasa dai Fadeela ce ta qarasa girkin. Fadeela dai har yau bata samu ciki ba. Da alama ta dauko gene din Mummy ne tunda kuwa tsakaninta da Mustapha ma shekara takwas wanda kuwa daga ita din bata sake haihuwa ba. STORY CONTINUES BELOW ************* Ko da suka zauna Dinning gaba dayan su suna zaune gefen mazajen su yayinda suke ba junan su abincin. Da alama dai tradition din su kenan ko a gidajen su. Mustapha wanda ya fara ba Zehra kuwa ya kai cokali na uku bakinta sai ta girgiza kai alamar ta qoshi. Zuciyarta ce take ta tashi yayinda take ta qoqarin dannewa. Qawayen nata dai sai kallonta suke yi yayinda suke ta matse dariyar su. Shi kam Mustapha yayi mamakin yadda ta qi cin abincin... ya kula ma yanayinta ya canza. Ji suka yi yace “hey My angel come here” ya nuna mata cinyar shi yayinda Al-ameen da Zain suka kalli juna suna murmushi, Fadeela da Hidaya suka fashe da dariya. Tashi tayi ta koma bisa cinyar shi ta zauna yayinda ya rungume ta ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “what’s wrong with you? Are you okay?” Cikin shagwaba tace “I am fine Baby, gajiya ce” Yace “toh meyasa kika daina cin abincin??” Tace “bana jin yunwa ne, anjima zan ci” Muryar Fadeela suka ji tace “Ya Musty muna nan fa bamu tafi ba tukun” Yace “na sani ai Dee, shiyasa muke magana cikin sirri don kar ku jiyo mu” Gaba dayan su suka fashe da dariya. Ita dai Zehra gyara kwanciyarta tayi a jikin shi yayinda ta binne fuskar ta a wuyan shi tana ta shaqar qamshin shi wanda ya taimaka wurin kwantar mata da tashin da zuciyarta take yi. Zain ne yace "Zee ko baki da lafiya ne?? should I examine you?" Da sauri tace "No Ya Zain, I am fine" Hidaya ce tace "qila shagwaba ce kawai.." yayinda suka yi dariya. Haka dai suka dinga yi musu tsiya har suka kammala lunch din. Shi kam Mustapha gaba daya hankalin shi baya tare da su. Sossai ya shiga damuwa na ganin yadda Angel dinshi tayi sanyi. Ko da suka koma falo tana nan maqale da shi yayinda suka cigaba da hira. Motsi kadan kuwa sai ya kai bakin shi saitin kunnen ta ya tambaye ta if she is okay yayinda take ta bashi positive response. Wasa wasa dai Zehra bacci tayi a bisa cinyar shi wanda har su Fadeela suka tafi bata sani ba. Shi kuma ganin baccin nata yayi nisa ne bai tada ta ba, haka ya dinga shafa kanta yayinda yake tunanin what could be wrong. ************** Bayan sallar la’asar ne na ga sun fito riqe da hannun juna, Da alama fita zai yi. Tana maqale a jikin shi ne na ji yana fadin “My angel you don’t look good, as in you look sick.. kin tabbata lafiyar ki kuwa??” tace “I am fine my baby, kar ka damu” Ita dai Zehra ta qi ta fadi mishi komai because she wants to confirm first before breaking the news to him.. Daya daga cikin drivers din gidan ne ya qaraso wurin su cikin ladabi yace “Sir” tare da miqa mishi key din mota. Jikin shi har rawa yake yi wanda kuwa Zehra ta kula da hakan. Cike da girmamawa ya kalleta yace “good day Ma” tana murmushi tace “good day how are you?” yace “fine Ma” Mustapha wanda ya karbi Makullin motar fuskar shi a murtuke yace “have you done what I asked you to do??” da sauri yace “almost done Sir” Girgiza kai yayi sannan ya daga mishi hannu alamar ya tafi. STORY CONTINUES BELOW Bayan ya tafi ne Zehra tace “Baby wallahi ma’aikatan gidan nan bala’in tsoronka suke ji, har kyarma fa suke yi idan kana yi musu magana” Ta dan ja kumatun shi tace “ka dinga yi musu fara’a ka ji baby na??” Murmushi yayi sannan yace “toh my angel, I will try. Duk abinda kike so dole in yi even though wannan din is gonna be difficult” Ko da suka nufi Parking lot sai da suka bata lokaci suna ta soyayya sannan ya tafi. Mustapha dai daga Gym dinshi aka Kira shi aka sanar da shi cewar anyi delivering Cable Biceps bar din da yayi ordering don haka ne zai je ya gani. Bayan ya tafi kuwa straight dakinta ta wuce inda na ga ta bude wata drawer ta fiddo Pregnancy test strip ta nufi bathroom. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Wuraren qarfe goma na dare yana tsaye a kusa da window na dakinshi yayinda yake Magana da Col. M Fahad a waya. Hankalin shi yayi nisa a hirar da suke yi ne ya ji ta rungume shi ta baya tare da kwantar da kanta a bayan shi. A hankali kuma ta zagayo ta gaban shi yayinda ta fara balle buttons din shirt dinshi ta binne fuskar ta a qirjin shi tana shaqar qamshin shi. Tuni hankalin shi ya koma kanta wanda kuwa tun yana gane abinda Col. M Fahad yake fadi har ya daina ganewa. Daga baya ma ji nayi yace “Uhm Fahad lets talk more tomorrow” Can kuma yace “Okay Good night” Yana kashe wayar ya shafa kanta tare da fadin “hey..” Muryar ta qasa qasa tace “yi haquri na sa ka yanke wayar ka..” Zagaye hannun shi yayi a bayan ta yace “you are more important my Angel” tace “thanks my Baby” Ji nayi tace "Baby ka canza spray ne??" Yace "nope, it has always been and will continue to be my favorite Tom ford... kin ji yayi daban ne??" Tace "yes Baby, na ji na qara son shi ne..." Kai tsaye yace "ni ba'a qara sona ba???" ta qara mannewa a jikin shi tana murmushi tace "na fi sonka fiye da komai a duniya nan My baby" Murmushi yayi yace "Godiya nake yi gimbiya ta" Kusan minti goma suna nan a tsaye tana ta shaqar qamshin nashi har yana mamaki amma bai ce komai ba. Dago kanta tayi tace “Baby zo mu je dakina in nuna maka wani abu” ta janyo hannun shi suka fita. Zaunar da shi tayi kan gadonta sannan ta juya ta nufi bathroom dinta yayinda ya bi ta da idanuwa cike da sonta. Yana nan zaune ta fito riqe da pregnancy test strip din ta qaraso wurin shi ta zauna a kan cinyar shi tace “Baby ka san ko meye wannan??” Gani nayi ya kai hannu zai karba yace “let me see” Tana murmushi tace “hmmm, its obvious you don’t” Ko da ya karba gani nayi yana ta juya shi yayinda ya ji tace “it’s a pregnancy test strip” Da sauri ya dago kai ya kalle ta yayinda yake jiran abinda zata fadi next. Sagala hannunta tayi a wuyan shi yayinda tace “ka ga wannan lines din guda biyu?” Ya kalli strip din tare da fadin “yes My angel” tace “it confirms that I am pregnant..” Cike da tsananin murna yace “what???? Dagaske??” STORY CONTINUES BELOW Daga nan kuwa sai ji tayi ya daga ta sama yayinda ya rungume ta so tight yana fadin "Alhamdulillaahil-lathee faddalanaa ‘alaa katheerin min ‘ibaadihil-mumineen... Alhamdulillah.. Allah nagode maka I am going to be a father.. we are going to have a baby” Yana twirling dinta yace “My angel you just gave me the best news and the best gift ever, thank you very much and I love you very very much” Zehra wadda take cike da farin ciki kuwa ji tayi yana ta baza mata kisses ta ko ina yayinda yake ta maganganu kala kala na farin ciki. Gani nayi ya zaunar da ita a kan gadon very gently yayinda ya tsugunna a gaban ta yace “My angel fadi mun duk abinda kike so zan baki shi, koma meye just name it” Birkita gashin kanshi tayi tace “abu daya nake so Baby..” Kai tsaye yace “tell me” Ta sa hannun ta a kan qirjin shi saitin da zuciyar shi take sannan tace “your heart” Murmushi yayi tare da dora hannun shi a kan nata yace “it has always been yours my Angel, you are free to do whatever you want with it.. You control it” Lumshe idanuwa tayi yayinda tace “nagode sossai my Baby” Daga nan ya rungumo ta tare da zura hannun shi ta cikin rigarta yana shafa flat tummy dinta yana fadin “Yanzu my Angel you mean akwai little baby anan??” Tana dariya tace "yes my Baby" Yace "toh ya kike ji?? as in akwai zafi??" Tana dariya ta ja kumatun shi tare da fadin "No my Baby... for now I am okay. kawai dai zuciya ta ce take tashi amma kana da maganin.." Cike da mamaki yace "ban gane ba.." Tana shaqar qamshin spray din shi tace "your favorite Tom Ford" Ya girgiza kai yace "zan baki su dayawa..." Tace "no... I want it only a jikin ka. Just promise me you will always be there when I need it" Kai tsaye yace "i promise you... duk abinda kike so kin samu. I love you so much" A haka dai suka cigaba da hirar cikin yayinda take bashi labarin stages din har yana tausaya mata. Gaba daya jikin shi yayi sanyi har yana Gode ma Allah da ya sa shi din ba mace bane. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Mustapha dai tuni yayi breaking ma family news din cikin Zehra wanda kuwa aka yi murna sossai. Ko da suka je asibiti Dr. Haleema ta tabbatar musu da lallai akwai ciki na tsawon sati bakwai sannan tayi musu bayanin abubuwan da za’a kiyaye da kuma abubuwan da Zehra zata dinga buqata wanda yawanci ita Zehran ta sani tunda dai ba cikinta na farko bane. A yanzu dai Mustapha ya hana ta yin komai, duk abinda take so shi yake yi mata. Office din ma ba kullum take zuwa ba domin kuwa yace baya so tana stressing kanta. Zehra dai cikinta kamar na Yasmeen ba mai laulayi bane sossai domin kuwa har mantawa ma take yi da tana da ciki amma shi Mustapha gani yake yi kamar tana wahala. Motsi kadan sai ya dinga tambayar ta inda yake yi mata ciwo, gaba daya ya tada hankalin shi akanta wanda kuwa a kullum tana cikin gwada mishi she is fine. Sossai yake bata tausayi yadda duk yake bi yana shiga damuwa. Mustapha yayi qoqarin ya koyi girki saboda yayi relieving dinta amma ya kasa. Its not just his thing.. Ita kuwa ta gwada mishi yin girkin ba abu bane mai wahala don haka ne ta roqe shi akan ya qyaleta ta dinga yi. he had no choice but to let her.. A kullum kuwa tare suke shiga wanda yake dan taya ta yin wasu abubuwa. STORY CONTINUES BELOW Abinci kadai take dafawa, daga wannan kuwa babu abinda take yi. Sossai ya shagwaba ta domin kuwa komai shine yake yi mata. A kullum zaka ganta maqale da shi tana shaqar qamshin Tom Ford body spray dinshi. Idan ya tafi ofis kuwa ta dinga kiran shi a waya kenan. Lokutta da dama saidai ya bar abinda yake yi a ofis din ya dawo. Ita kam Yasmeen jin cewar akwai Baby a cikin Amminta kullum labarin ta bai wuce na sabon Baby ba. Haka zata zauna tayi ta basu labarin kalolin wasan da zasu dinga yi idan Babyn ya zo. Sossai suke shan dariya. Tuni Hidaya ta haihu inda ta haifi 'yarta mace wadda ta ci sunan mahaifiyar Al'ameen wato Asma'u. Sossai Zehra ta kashe ma Babyn kudade domin kuwa Hidaya has been nothing but a true friend.. she is like a sister to her. ************* A lokacin da cikin Zehra ya kai wata shidda ne Mustapha ya roqi Anty akan Khadeeja ta dawo zama a gidan. Khadeeja kuwa tuni an sa ranar bikinta wanda saura wata bakwai. Zata auri wani saurayin ta mai suna Imraan Bashir Sodangi, dan gidan Ambassador Bashir Sodangi. Imraan dai engineer ne Wanda a yanzu haka yana London yana wani course. Bayan bikin nasu ma tafiya zaiyi da amaryar shi can har sai ya gama course din sannan su dawo. ♤♤♤♤♤♤♤ Months later... A yanzu dai EDD din Zehra is very close. Sossai take zabga mishi shagwaba don kuwa yanzu hatta tafiya idan ta ga dama sai tace mishi bazata iya ba. Shi yake daukar ta yana kai ta duk inda take so. Bala'in tausayin ta yake ji. Inda suka yi sa’a kuwa tunda Zehra ta samu ciki Ba’a yi posting Mustapha outside Abuja ba, dukda anyi missions wadanda ya so ya je don ya taimaka amma sam Zehra ta hana. Dayake yana bada gudumuwar shi ta wurin hada strategy plan sossai ake samun nassara a missions din. ♤♤♤♤♤♤♤♤ MUSTAPHA OMAR TAFIDA RESIDENCE Kwance take a kan gadon dakin shi da daddare yayinda take kallon shi daure da towel yana tsaye a gaban vanity mirror. Hango ta yayi ta mirror din ta sa mishi idanuwa babu ko qyaftawa. Murmushi yayi yace “hey, why are you staring at me??” Lumshe idanuwa tayi tana murmushi tace “I love you” Dariya yayi yace “I know that” Tace “I love your physique” Ya kashe mata ido daya ta mirror yace “I know that too” Tana murmushi tace “I am jealous” Juyowa yayi yana kallonta yace “Jealous of what????” Turo baki tayi tace “I swear Baby kullum qara zama yaro kake yi, idan an gan ka fa za’a yi tunanin you are not even up to thirty” Fashewa yayi da dariya yace "it's all thanks to you my beautiful queen, kula da ni kike yi sossai shiyasa..." Ya feshe kanshi da favorite spray dinta sannan ya qaraso wurinta kan gadon ya janyo ta jikin shi yayinda ta binne fuskarta a qirjin shi tana ta shaqar qamshin shi. Ya shafa gashin kanta yace “bari in sa kaya in zo inyi miki wanka” Da sauri ta dago kanta ta kalle shi sannan tace “nace maka fa bazan yi ba” STORY CONTINUES BELOW Yana kallonta yace “My angel yau fa sau daya kika yi wanka shima fa da qyar, yanzu haka zaki yi bacci? Little Moha fa zai yi fushi..” Dayake scan result yayi confirming its going to be a boy… Cikin shagwaba tace “ai kawai haquri zai yi” Hararar ta yayi ya tashi tare da fadin “dirty girl” Gwalo tayi mishi sannan tace “eh din, a haka dai kake so na” Dariya yayi sannan yace “sossai ma kuwa My angel, Mustapha is useless without Zehra” Ya wuce dressing room dinshi yayinda take dariya. Wayar shi ta janyo yayinda ta shiga gallery tana ta kallon hotunan da yake yawan snapping dinta. Hotunan Zehra da ke wayar Mustapha a yanzu sun kusa dubu, wasu ma bata sanin lokacin da yake snapping dinsu saidai kawai ta gani a wayar shi. Akwai wani da ya mayar da shi black and white sossai yayi mata kyau. Gani nayi ta dade tana kallon hoton.  Bata ankara ba ta ga kira ya shigo wayar wanda na ga ta zabura tare da jefar da wayar. Cikinta kuwa sai da ya motsa yayinda ta dafa shi. Ji nayi tace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un… SAREENAH???”5 🙄🙄🙄 Tana dafe da cikinta yayinda hankalinta yayi mugun tashi, zuciyarta tana ta tafasa da zafin kishi yayinda jikinta yake ta kyarma. Ban ankara ba sai ganin hawaye nayi yana zuba a fuskarta kamar an saki famfo. Mustapha wanda ya fito sanye cikin three quarter sweat da t-shirt kuwa ganinta yayi tana ta rusa kuka. Hankalin shi a tashe ya nufo wurin ta yana fadin “hey, why are you crying? cikin ne??” Ture shi tayi da hannuwan ta biyu cikin kuka tace “Allah ya isa tsakani na da kai, duk soyayyar da nake yi maka da abinda zaka saka mun da shi kenan??” Mustapha dai cike da tsananin confusion gani nayi ya qara matsowa kusa da ita yayinda yake fadin “My angel, why are you saying this? Me nayi?? we were just fine before I went into that dressing room..” Da sauri tace "just shut up... I hate you" Yatsarta ta dago ta nuna shi tana kuka tace “stay away from me, dama ance duk wanda ya mayar da namiji maraya zai mutu uba…”2 Shiru ta dan yi sannan tace “wait... ba daidai bane ko??” Girgiza kai yayi yace “Yes My angel, it's the other way round… wanda ya mayar da namiji uba zai mutu maraya” Kai tsaye tace “yauwa… exactly” Da sauri yace “wallahi My Angel hausa ce kawai wannan… ni kam bazan taba bari ki mutu marainiya ba” Yayi saurin hugging dinta tare da fadin “Please calm down and talk to me…..” Ture shi tayi yayinda ta juya zata bar mishi dakin. Tana daga qafafuwanta kuwa cikin ta yayi wani irin murdawa yayinda marar ta tayi nauyi. Gani nayi ta dafe cikinta tace “ouch… wayyo Allah ciki na”2 Da sauri ya riqo ta a rude yace “subhanalillah, what happened?? EDD dinki saura 4 days ai” Yana qoqarin shafa cikin nata ne ta bige hannun shi cikin masifa tace “EDD is just an estimation.. I think the Baby wants to come sooner..." Ta danna mishi harara tace "all thanks to you.." Ya matso kusa da ita hankali a tashe wanda ko kafin ya taba ta tace "stay away from..” Bata qarasa maganar ba na ga ta duqe tare da fadin “Ouch Baby cikina… please help me zan mutu... take me to the hospital”2 Mustapha wanda duk ya bi ya rude gani nayi ya qara riqe ta yayinda yake qoqarin daukar ta yana fadin "sorry my Angel..." Cike da masifa tace "don't touch me.. duk kai ka ja mun wannan matsalar, ni kar ka dauke ni” Cike da tsananin mamaki yace “hey wai me nayi miki ne??” yayinda ya dauke ta cak ya fita da ita. Shi kam Mustapha this is the first time that he didn't find her MASIFA funny... Yana tunanin lallai zafin ciwo ne yake sanya ta maganganu marassa kai. Ji yayi ta kai mishi duka a kafada cikin kuka tace “Ni wallahi sai ka fadi mun abinda kuke yi da Sareenah da har take kiran wayar ka da daddare.." Zaro idanuwa yayi yace “What???” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ BAYAN SHEKARA DAYA MUSTAPHA OMAR TAFIDA RESIDENCE Zaune yake a cikin motar shi yayinda Yasmeen da Ameer suke zaune a gefen shi. Yasmeen da Ameer kuwa a kullum sai sunyi drama akan zaman gaban... babu mai son ya zama shine zai zauna a baya don haka ne zaka gansu su biyun a gaba. Zehra ce tsaye yayinda ta duqo jikin window na motar suna ta hira. Asali dai yawo zasu je wanda kuwa daga nan zasu mayar da Ameer gida. Ji nayi tace “Baby please kar ka manta mun da saqona wurin Dee” Yana kallonta yace “bazan manta ba my Angel, ko na manta dole zan koma” In a serious tone tace “banda dogon yawo don nasan yaran nan idan suka ja ka har sai kun zagaya shagunan garin nan baku sani ba” Murmushi yayi yace “okay Ma” Shafa fuskar shi tayi sannan tace “Baby kai kam kullum qara zama yaro kake yi, dagaske fa I am jealous” Fashewa yayi da dariya yace “Yi haquri my Angel” Itama dariyar tayi tare da dago wayarta ta fara snapping dinshi kamar dai yadda yake yi mata itama.. Ganin haka ne su Yasmeen suka ce “Ammi harda mu” Tace “okay… 1, 2, Go” tayi clicking. 2 Tana shirin clicking wani ne wayarta tayi ringing. Gani nayi tayi murmushi tana kallon Mustapha tace “one minute please” Girgiza kai yayi yace “go ahead my Angel” Ji nayi tace “qawa how far” Ta dan yi shiru sannan tace “ki dauko mun Gold din tunda babu red” Dariya tayi sannan tace “marar jin Magana kamar Abbun shi… Yana nan lafiya bacci ma yake yi” Can kuma tace “gasu nan zasu fita yawo” Tana kallon Mustapha tace “zasu ji insha Allah, next week din zaki dawo??” Tayi murmushi tace “toh shikenan, take care bye” Bayan ta kashe wayar ne tace “that was SAREENAH, tace in gaishe ka”2 Ni kuwa nace whaaaat??? Girgiza kai yayi yace “meye na ji kina fadin a dauko miki gold??” Hararar shi tayi tace “eavesdropper...” STORY CONTINUES BELOW Dariya yayi yace “Allah ya baki haquri.. Well, Mu bari mu tafi” Tana murmushi tace “nima bari in dubo Khaleefa don na san qila ya tashi har ya fara wata barnar” Turo baki tayi ta cigaba da fadin “....wallahi Khaleefa yayi gadon rashin ji a wurin ka sossai… Just 2 weeks to his first birthday amma yana buga irin wannan rashin jin, idan ya qara girma fa akwai matsala” Mustapha wanda yake dariya yace “yi haquri My Angel, zai daina” Ya nuna kumatun shi yace “my kiss” Ta duqo tayi mishi kiss tace “I love you my handsome Colonel” Ya shafa fuskar ta sannan yace “I love you more my angel, take care” tace “you too my baby” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Flash back… NATIONAL HOSPITAL ABUJA Zehra a cikin labour room riqe take da hannun shi gam ta qi saki yayinda take ihu tana yi mishi masifa. Gaba daya ta qi barin shi yayi Magana, gashi hankalin shi a matuqar tashe ganin yadda take murqususu idan ciwo ya tsungule ta. Dr. Haleema da nurses dinta dai sai kallon drama suke yi wanda har dariya suna yi jefi-jefi. Mustapha dai ya sha duka. Cike da damuwa ne yace “My angel listen to me, ki bani minti daya inyi miki bayani” Cikin masifa tace “qarya zaka yi mun” Bata Ankara ba ta ji yace “she is getting married next month” Da sauri ta kalle shi tace “whaaat??” Zama yayi kan gadon yayi hugging dinta yace “Yes My Angel, ta aiko mun invitation na auren ne shine na kira inyi congratulating dinta and unfortunately she missed my call… and then she called back sai kika gani” Zehra dai dukda azabar da take ji sai da ta ji wani sanyi a ranta. Kusan ma dama zafin kishi ne yayi adding to pains din da take ji. Ji tayi ya cigaba da fadin “My angel you are my life and I love you very much..” Tana maqale da shi tace “My Baby I am sorry please… I was confused…” Kafin ta qarasa maganar tayi ihu yayinda ta matse hannun shi gam tana fadin “Baby na shiga uku, cikina… Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un... baya na…” yayinda take ta rusa kuka. Mustapha dai ganin yadda Angel dinshi take fama da azaba sai kawai hawaye suka fara bin fuskar shi. Dr Haleema kuwa sai ta koma lallashi yayinda Nurses suke ta matse dariyar su. Zehra dai saida ta sha wahala sannan haihuwar ta zo mata gadan gadan. Cikin ikon Allah ta haifi yaronta namiji fari sol kyakyawa. Masu karatu ba sai na baku labarin kalan murnar da Mustapha yayi ba, tuni yayi ma yaron huduba da suna Muhammad. Zehra kuwa kwanan su biyu a asibiti aka sallame su inda aka wuce da su gidan Papa. ********** Zehra dai ta kwantar da hankalinta jin cewar Sareenah aure zata yi. Abin mamaki sai ga su har sun qulla qawance mai qarfi wanda ita dama Sareenah ta so suyi zumunci tuntuni amma ganin Zehra bata sonta ne ta haqura. STORY CONTINUES BELOW Tare da ita akayi hidimar suna sannan Zehra tana cikin wadanda suka taya ta shirya bikinta. Sareenah dai wani Dan uwanta ta aura mai suna Muhammad Kabeer Modibbo. Shahararren pilot ne a qasar nan. Suna nan zaune a cikin danqararren gidan su a Abuja. A yanzu haka ta je Ingila ne don siyo kayan jarirai domin kuwa tana dauke da cikinta wata biyar. End of flashback... ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ After two weeks…. MUSTAPHA OMAR TAFIDA RESIDENCE A yau Saturday, a yau ne Khaleefa yake cika shekara daya a duniya. Zehra ta shirya mishi birthday party wanda za'a yi da yamma. Kwance yake a kan gadon shi da safe yana ta bacci, as usual dakin yayi duhu kamar tsakiyar dare. Sanyin AC ne yake ratsawa a dakin wanda ya gauraye da wani asirtaccen qamshi ya bada yanayi mai dadin gaske. Zehra ce ta turo qofar dakin riqe da Khaleefa yayinda ta kunna wuta. Hango shi tayi cikin Duvet yana ta baccin shi cikin kwanciyar hankali. Girgiza kai tayi tana murmushi yayinda ta qarasa wurin shi. Gani nayi ta sauke Khaleefa wanda tuni dama ya fara tafiya kadan kadan sannan ta ajiye wayar ta akan bed side drawer din shi. Hawa tayi kan gadon yayinda ta haye kan shi ta kwanto tana baza mishi kisses. A hankali ya bude idanuwan shi yana kallonta. Tana murmushi tare da goga hancinta da nashi tace “Baby its time to wake up, yi haquri nasan jiya kana aiki baka kwanta da wuri ba..” Shi kam tunda ya bude idanuwan shi ya ganta yake ta kallonta. What would have become of him idan bai samu wannan pretty lady din a rayuwar shi ba?? Har duniya ta nade bazai taba son wata mace kamar yadda yake son Zehra ba, she completes him gaba daya. Bai ankara ba ya ji muryarta tana fadin “hey, why are you staring at me??” Hancin ta ya dan ja yace “because I love you my Angel, I love you so very much that I don’t know how to express in words..” Lumshe idanuwa tayi yayinda tace “if there is one legit thing I believe a duk fadin duniyar nan, its your love for me My Baby…. Thank you very much for loving me unconditionally” Yace “No thank you for coming into my life” Daga nan kuwa ta tura bakinta cikin nashi suka fara kissing juna.. Qarar da suka ji ne ya dawo da hankalin su kan Khaleefa wanda yake tsaye a gefe. Da sauri suka tashi zaune yayinda suka hango wayar Zehra a qasa. Gani nayi ta sauko da sauri ta dauki wayar tana dubawa. Waya dai screen yayi kaca-kaca domin kuwa bata sa screen protector ba daman.. Saboda haushi ma kasa magana tayi yayinda na ga tana kallon yaron. Mustapha wanda yayi saurin saukowa ya janyo Khaleefa ya rungume ne ya kalli Zehra yace “Please kiyi haquri...” Cikin masifa tace “its my iphone 11 fa Baby… yanzu fisabilillah abinda yaron nan yake yi yana kyautawa?? Komai na gidan nan sai ya fasa shi??” Shi kam Mustapha ya sani sarai tana bala'in ji da wayar domin kuwa a yadda ya ji daga wurinta it's the latest iphone.... Ji nayi yace “Don Allah kiyi haquri, bari in sa a kawo miki wata...” STORY CONTINUES BELOW Hararar shi tayi tace “ai dama dole ka dinga kare mishi tunda halin ku daya..” Fashewa yayi da dariya yace “gaskiya wannan ya fi ni bala’i, ni banyi haka ba... again ni na daina ai” Tace “hmmm.... ka dai rage amma wallahi har yanzu baka jin Magana” Ta kalli khaleefa wanda yake ta kallonta tace “look at him, kamar babu ruwanshi” Mustapha yana dariya yace “ni duk ba wannan ba, rashin fara'ar shi ce matsala ta, ni fa ban taba ganin yana dariya ba… duk wasan da nake yi mishi baya dariya ko alama” Fashewa tayi da dariya tace “laifin wa?? Ai wallahi Baby kai ya biyo har ya zarce” Girgiza kai yayi yace “Oh Mustapha you are in trouble” Yayi ma Khaleefa kiss a kumatu yace “hey little Moha please kayi qoqari ka canza hali ka ji??” Zehra dai dariya ta dinga yi musu. Ji suka yi an qwanqwaso qofar yayinda Zehra tace “yes, come in” Yasmeen ce ta shigo a guje ta nufi wurin Mustapha tana fadin “Abbu Good morning” Itama daukar ta yayi yace “Morning my princess” Kiss tayi mishi a kumatu sannan ta sagala hannunta a wuyan shi tace "Abbu zaka zo dakina ka ga gift din da zan ba Khaleefa??" Mustapha ya girgiza kai tace "yes my princess" Muryar Zehra suka ji tana fadin "ni kam da nasan zai fasa mun waya da ban kashe kudina na hada mishi birthday din ba..." Mustapha wanda yake dariya yace "Haba Ammi.. kiyi mana haquri bazamu qara ba" Murmushi tayi tace "please My Baby try and make it to the party... I need you to be there" Yace "insha Allah my Angel.. meeting din is going to be brief" Daga nan fa Yasmeen ta fara zubo mishi hirar ta wadda bata qarewa, shi kuwa biye mata yayi suna ta yi. Zehra wadda ta ga hirar ta qi qarewa ce tace “Breakfast is ready fa, oya ku tashi mu je dinning” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ THE TENT, RED SPARROW EVENT CENTRE MAITAMA, ABUJA Wurin cike yake da iyaye da yara kai ka ce bikin aure ake yi. Decor din da aka yi kuwa shine zai tabbatar maka da harkar ta yara ce. Kayan wasan yara da aka baza a wurin kamar Children's park... Sossai wurin ya qawatu. Mummy da Anty suma sun halarci wannan party din. Papa da Daddy dai basu samu zuwa ba. Zain da Al-ameen mijin Hidaya ma sun zo, Mijin Sareenah wanda shima ana zumunci da shi bai samu zuwa ba saboda yayi tafiya. Khadeeja kuwa tana London tare da mijin ta Imraan wanda aka yi auren su watannin da suka wuce. Mummy wadda take zaune tare da su Anty da wasu qawayenta ce tace "wannan party dai banda kayan wasan yaran nan da suka baza ai sai ayi tunanin bikin aure ne" Anty tana dariya tace "The funny part kuma wai birthday din shekara daya... Mu kam mun dai zo re-union kawai" Sossai yara suke ta watayawa suna wasan su yayinda wani funny MC yake ta basu dariya. Zehra kuwa wuri suka samu ita da Fadeela, Hidaya da Sareenah suka dinga hira.. Zehra ce tace "wai yanzu Dee daga next week shikenan??" Fadeela tana murmushi tace "wallahi kuwa Zee, zanyi missing dinku sossai" STORY CONTINUES BELOW Hidaya tace "five years gaskiya da tsawo" Sareenah tace "toh yanzu kinyi quitting aikin ki kenan?" Fadeela tana dariya tace "inaaa... leave without pay na nema... har ma sunyi approving" Zehra tace "Gaskiya zamu yi missing dinku" Fadeela dai Germany zasu tafi, Zain ne aka tura wani course har tsawon shekara biyar wanda zai tafi da family dinshi tunda dai shekarun akwai yawa. Haka dai suka cigaba da hira har suka jiyo MC yana tambayar birthday boy. Gani nayi Zehra ta juya tana qoqarin neman Khaleefa amma bata gan shi ba. Tashi tayi yayinda tace "wannan yaro kuma ina ya shiga ne??" Fadeela tana dariya tace "hala ya koma can wani lungu shi kadai yana wasan shi... halin Ya Musty sak wallahi" Su Sareenah suna ta dariya yayinda suka tashi don taya ta neman shi. Aikuwa dai sun dade suna neman shi a cikin cunkoson yara. Ganin shi suka yi zaune a can wani gefe yana ta wasa da toys. Zehra ta girgiza kai tace "na shiga uku da yaron nan... kai komai naka daban...." Fadeela tana dariya tace "One of the prices you have to pay for being Mrs M. Tafida hajiya... Yaro dai baban shi ya biyo... Allah ya baki wani introvert din" Sareenah tace "don ma tayi sa'a ta gyara baban ai da yanzu sun zama mata biyu.. " Suka fashe da dariya. ************* MC dai sa Khaleefa yayi a gaba ana ta yin games da yaran Wanda suka dinga cinye kyaututuka. Daga baya ne aka fara daukar hotuna afterwards ayi wishing dinshi sannan ya yanka cake din (tare da iyayen shi).1 Ko da aka ajiye Khaleefa kusa da cake din ana yi mishi hoto gaba daya hankalin shi ya tafi ga kallon cake din.  Decoration din cake din ya fara cirewa Wanda kuwa tun Zehra tana fadin 'Khaleefa bari' har sai suka ga ya ruguzo cake din ya fadi qasa. Aikuwa gaba daya hankulan kowa ya dawo kan shi yayinda wasu suke ta dariya. Zehra dai dafe kai tayi yayinda Fadeela ta nufi wurin shi ta dauke shi tana ta kwasar dariya. Hidaya wadda take dariya tace "yaro ya watse taro.. babu cake ai babu birthday" A daidai lokacin ne Mustapha ya iso wurin. Ganin kowa tsaye anyi cirko-cirko ne ya qarasa wurinsu yayinda ya ji Zehra tana fadin "ni kam ban taba ganin yaro irin wannan ba... yanzu da ya ruguza cake din da me za'a yi wishing dinshi..." Muryar shi ta ji a bayan ta yana fadin "yi haquri Ammi" Fadeela tana dariya tace "ai dama dole ka bada haquri tunda laifin ka ne.." Cike da mamaki yace "how??? I just got here fa.." STORY CONTINUES BELOW Mummy ce tace "halinka ya dauko... ko in tuna maka irin barnar da ka dinga yi ne??" Nan da nan yace "don Allah kiyi haquri Mummy" Yayinda ya karbi yaron shi daga hannun Fadeela yace "Zo mu je in yi maka nasiha ka ji little Moha... you actually need to stop all these" Ya matsa kusa da Zehra yayi mata kiss a kumatu sannan yace "sorry Ammi, we can continue without the cake... trust me" Ranta a bace tace "what's birthday without a cake??" Ya kashe mata ido daya sannan yace "wait and see" Juyowa yayi ya kalli yaran yace "who wants to play???" Gaba dayan su suka ce "me..." Haka aka dinga yi musu dariya. Wasa wasa dai Mustapha duk ya janye yaran suka koma gefe suna ta wasa. A yanzu kuwa Zain da Al-ameen da sauran dads din da suke wurin sunyi joining wasan wanda kuwa aka dinga yi musu dariya. Ga dukkan alamu ma Yaran sun fi enjoying wasan a yanzu don kuwa banda ihu babu abinda suke yi... Gaba daya sun rikita wurin. The kids were definately having a great time with their dads.. Mummy wadda take ta mamaki ce tace "who would have thought cewar Mustapha zai canza haka..." Anty tace "this is all thanks to Zee.." ♤♤♤♤♤♤♤♤ Six months later... ZAIN ABU-YAZEED RESIDENCE FRANKFURT, GERMANY A yau kwana biyu kenan da su Mustapha suka zo Germany. Dayake ana hutun makaranta sannan shima he is kinda free a office. Sossai Yasmeen ta ji dadin ganin dan uwanta Ameer. Sossai suke ta wasa, Shi kuwa Khaleefa kamar koda yaushe yana gefe yana nashi wasan shi kadai. dayake ma ba gane maganar shi ake yi ba su Yasmeen basu sa shi cikin wasan nasu. Fadeela dai ta samu ciki a wannan lokacin. Cikin nata kuwa har ya kai wata uku. Amma fa yana dan bata wahala domin kuwa tuni an hana ta motsi mai qarfi. Dayake Zain din nata likita ne yana kula da ita sossai. *********** Daddare wuraren qarfe Goma suna Lawn din gidan yayinda suke ta hira. Motsi kadan idan Fadeela tayi sai Zain ya dinga tambayar ta yadda take ji. Ita kuwa sai buga mishi shagwaba take yi. Mustapha wanda yake kallon su ne yace "ai na gode ma Allah da ni ba mace bane.. A kullum idan na tuna yadda Angel ta sha wahala wurin haihuwa sai jikina yayi mugun sanyi..." Fashewa suka yi da dariya yayinda Zehra tace "ai wallahi ni kaina na dauka mutuwa zanyi.. ni kam C-section ya fi" Fadeela wadda take kwance a jikin Zain ce tace "sweetheart nima wannan karon C-section kawai zasu yi mun su cire Babyn.. " Murmushi yayi yace "toh sweetheart... Allah ya sauke ki lafiya" Haka suka cigaba da hirar su har Fadeela ta fara hamma. Zain ne yace "sweetheart bacci??" tace "eh.." Tashi yayi tare da daukar ta yace "mu je mu kwanta toh" Zain yana riqe da Fadeela ya kalli su Mustapha yace "mu dai mun shige... Good night" Bayan sun shiga gida ne Zehra wadda take kwance a gefen Mustapha kan wata comfortable resting chair ce tace "Allah sarki Dee.. tana bani tausayi wallahi" STORY CONTINUES BELOW Yace "kuma dama ga raki na bala'i ba.." Zehra tayi dariya. Yana rungume da ita ne yace "hey My angel I forgot to tell you cewar zamu je aikin hajj this year" Cike da murna tace "dagaske?" Yace "Yes... na so mu je last year but kin san aikin nan nawa sai ahankali sannan ke kuma ga Khaleefa" Ya janyota ta kwanta bisa shi yayinda fuskarta take daf ta tashi yace "better we go before you conceive..." Turo baki tayi sannan tace "Baby I don't want to conceive so soon fa... wallahi haihuwa akwai wahala.." Yana murmushi yace "haquri zakiyi ki haifo mun mai kama da ke please my Angel" Yayi kissing dinta sannan ya cigaba da fadin "kyakyawa.. with beautiful eyes... My angel eyes. Daga wannan idan kina so sai a tsaya haka" Murmushi tayi tace "na fi son namiji mai kama da kai..." Zaro idanuwa yayi yace "what?? don Allah ki bari... Another boy??? No... insha Allah it's going to be a girl" Zehra wadda take dariya tace "ka san me??" Yace "tell me" Tace "nayi confirming wani abu.. " Yace "what is that??" Tana murmushi tace "na fi sonka fiye da yadda kake sona..." Da sauri yace "what???? wallahi qarya kike yi.. Son da nake yi miki ko rabin shi ba kya yi mun" Tana dariya tace "I have proof fa" Cike da mamaki ya daga ta suka zauna yayinda yace "like seriously??.." He was looking all serious waiting to hear her so called proof.... Kashe mishi ido daya tayi tare da fadin "Khaleefa.." Cikin rashin fahimta yace "as in??? ban gane ba... what has little Moha got to do with this??" Tace "there is a saying that idan mace ta fara haifo namiji it means tana son mijin fiye da yadda yake sonta..." Zaro idanuwa yayi yace "wanne maqaryacin ya fadi haka???" Da sauri ta sa hannu ta toshe bakin shi sannan tace "ssssshhhh, Yaaya told me" Runtse idanuwa yayi sannan yace "Subhanalillah... na kwafsa" yayinda take ta yi mishi dariya. Ji tayi yace "uhm... I think he misunderstood the saying My Angel.. it might be that idan kika haifo namiji na fi sonki kenan..." Fashewa tayi da dariya tace "dagaske ba haka bane My Baby.." Janyota yayi ta haye kan cinyar shi ya matse ta gam yace "Ni dai wallahi ina bala'in sonki kuma ban yarda naki son ya fi nawa ba" Tana ta dariya tace "Baby nima bala'in sonka nake yi... kuma na fi sonka" Yace "I disagree my Angel.." Tace "nima I disagree.." Haka dai suka dinga cin musu akan wanda ya fi son wani. Daga qarshe ne Mustapha yace "speaking of who loves who more, tashi mu je in nuna miki kadan daga cikin irin son da nake yi miki" Janyo ta yayi suka tashi yayinda na ji tana fadin "Baby don't get me pregnant fa... remember we are going for Hajj" Bata ankara ba ta ji ya dauke ta cak yayinda yace "if I do, we will go next year" Fashewa tayi da dariya. Suna tafe ne na ga ta birkita gashin kanshi cike da tsokana tace "I love you more.." STORY CONTINUES BELOW Yace "Nope... I love you so much more.." Tayi mishi gwalo tace "Khaleefa is my proof..." Yace "Ni yanzu zan nuna miki proof dina practically..." A haka dai suka shige ciki suna ta cin musu akan who loves who more.... ************* Ni kam dakatawa nayi anan saboda tsaro. Da alama idan na bi su zan iya makancewa don kuwa wannan soyayya da za'a kwasa a yau ta daban ce...😏 Tambaya a nan shine from everything that has happened so far, wa kuke tunanin ya fi son dayan a cikin su?? Mustapha ko Zehra?????2 It is rightly said that true love never ends... But then anan zan tsaya da bibiyar wadannan masoyan. Fatan mu Allah ya sa su cigaba da kasancewa tare da juna har abada!! One thing is for sure... their match was one made from heaven ❤❤ Tammat bi-hamdulillah....5 ♤♤♤♤♤♤♤
Related Posts

Related Posts

Post a Comment