Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZEHRA CHAPTER 1

ZEHRA CHAPTER 1

- - Post a Comment
ZEHRA CHAPTER 1
YEAR 2014 MAITAMA ABUJA ABU-YAZEED RESIDENCE+ Tsaye take a kicin din gidan yayinda take ta qoqarin kammala Chicken Salad din da take hadawa. Abinci ne kala kala ta dafa yayinda gidan gaba daya ya kaure da qamshin girkin nata. Tana qoqarin janyo napkin daga wani drawer ne ta ji an rufe mata idanuwa daga ta baya. Ji nayi ta kwalla ihu tare da fadin "oh My God, Dee" Da sauri Fadeela ta zare hannuwan ta tare da fadin "you are a witch Zee, ta ya kika gane ni ce??" Zehra wadda ta fashe da dariya tace "for crying out loud why wouldn't I?? your Urbanist perfume as usual.." Da sauri ta rungume ta tare da fadin "how I missed you Dee, yaushe kika dawo?? You didn't even call to tell me...I am sure Ya Zain ya sani" Fadeela tana dariya tace "I am sorry love, I just wanted to surprise you ne, and Yes I asked him not to tell you. Kawai muna dawowa nace I have to come see you. I really missed you. How I wish we went together..." Zehra tace "yeah me too, but I didn't want to miss my cooking classes and the competition" Fadeela wadda ta juyo ta kalli kalolin abincin da Zehra tayi ne tace "uhmm, you and your passion for cooking. Well I am glad you won the competition. Insha Allah one of these days zamu gan ki a Masterchef Australia" Daga hannu sama Zehra tayi cike da jin dadi tace "Ameen Dee" Fadeela ta nufi wurin wani lafiyayyen Crunchy Chicken ta dauka daya tace "na ga kinyi abinci kala kala, what's the occasion?? I know for a fact that this isn't just a normal dinner" Zehra wadda ta dauko napkin daga cikin drawer tana dariya tace "wallahi Papa ne zai dawo yau so I decided to prepare something special for him" Ta kai Crunchy Chicken din bakin ta tare da lumshe idanuwa tace "oh my friend, this is delicious. Gaskiya dole ma in kwana gidan nan yau. Papa will have to share" Zehra tana ta dariya yayinda Fadeela ta janyo kujerar Kitchen island ta zauna ta cigaba da fadin "you will have to come and assist us wurin shirya ma Ya Musty idan zai dawo, na ji Mummy tana fadin wai sai tayi hiring Chefs" Da sauri Zehra ta juyo ta kalle ta tace "whoa... Dagaske??? finally one of the brothers is coming back. I will get to meet him.." Fadeela ta fashe da dariya tare da fadin "trust me babes you don't wanna meet this one... gwara dai Ya Moha don shine mutumin arziki" Zehra wadda ta cika da tsananin mamaki kamar kullum idan suka dauko zancen shi ce tace "haba babes, why are you saying this??" Fadeela ta girgiza kai tace "I swear I don't understand the guy, rayuwar shi is so dark that no one can see through. He lives in his space with no one in it.." Zehra ta saki ajiyar zuciya tare da fadin "wai why do you keep talking about him as if he were a monster" Girgiza kai tayi tace "dagaske he is... he is not at all my fav" Zehra tace "well I still wanna meet him, yaushe zai dawo??" Kafin Fadeela ta amsa ne Khadeeja ta shigo kicin din riqe da wayar Zehra wadda take ringing tace "Anty Zee your phone"6 Bayan Zehra ta karbi wayar ne Khadeeja ta nufi wurin Fadeela tace "welcome back Anty Dee, how was your trip?" Fadeela tana murmushi tace "thanks deejah, it was fine. Yanzu na tambayi Anty ke and she told me kina sama, ya school?" STORY CONTINUES BELOW Tace "fine Anty" daga nan ta wuce ta fita. Zehra wadda take waya da Hidaya ce tace "I am fine bestie, I just had to stay back ne saboda Papa zai dawo yau kuma ina shirya mishi special dinner" ta dan yi shiru sannan tayi murmushi tace "not at all bestie, I am absolutely fine" Fadeela wadda ta sa mata idanuwa ce ta dalla mata harara yayinda ita kuma ta kashe mata ido daya. Ji nayi tace "thank you very much Hidaya, I really appreciate you calling to check on me. Sai mun hadu gobe. Bye"3 Bayan ta kashe wayar ne ta ga Fadeela ta miqe tare da juyawa zata bar kicin din. Da sauri ta nufi wurinta tare da hugging dinta ta baya tace "Dee..." Cikin fushi Fadeela ta juyo tace "leave me alone Zee" Zehra tana murmushi ta ja kumatun ta tare da fadin "why?? What have i done again??" Cike da masifa Fadeela tace "why the hell were you calling her your bestie?" Zehra tayi murmushi tare da rungume ta tace "I am sorry Dee. Hidaya is just a girl at school da muke shiri. She likes me a lot and I have no choice but to like her back, tana da kirki sossai. she is just a friend but trust me you are my best friend and sister. We are and will continue to be the Inseparables Insha Allah" Fadeela wadda tayi murmushi tace "I love you Zee" Zehra tana murmushi tace "I love you more Dee" ********** Zaune suke a kan dinning suna dinner. Papa ne ya kalli Zehra yace "my Baby abincin nan yayi dadi, Allah ya kawo miki miji nagari kiyi ta dafa mishi irin su" Murmushi tayi tare da rufe fuska yayinda su Anty suka amsa da "Ameen" Zain wanda yake zaune yana fuskantar Fadeela ne na ga yana latsa wayar shi ya tura mata saqo kamar haka: "you are looking soo beautiful My love, its like the weather in Dubai is just so perfect for your skin" Fadeela wadda ta ji qarar saqo tayi saurin daukar wayarta ta duba. Gani nayi tayi murmushi tare da dagowa ta kalle shi sannan tayi typing message kamar haka: "thanks sweetheart, I love you" Ko da ya duba murmushi yayi tare da kashe mata ido daya sannan ya rubuta saqo kamar haka: "cant wait to have you in my house.." Papa da Anty dai sai kallon ikon Allah suke yi yayinda Zehra da Khadeeja suke ta qoqarin boye dariyar su. Muryar Papa suka ji yace "kuyi haquri ku gama cin abincin mana, its getting cold" Zain da Fadeela suka dago kai cike da tsananin kunya da mamaki suka kalli Papa yayinda su Zehra suka fashe da dariya. Fadeela dai miqewa tayi ta bar dinning din a guje yayinda Papa ya cigaba da fadin "I think yakamata mu zauna ayi maganar sa ranar bikin nan naku.." Kafin ya qarasa Zain yace "are you being serious Papa???" Cike da mamaki Anty tace "whoa..." Papa wanda yake murmushi yace "yes son, zanyi ma Daddy Magana sai mu shirya lokaci" Zain ya miqe cike da murna ya rungume shi tare da fadin "thank you so much Papa, I love you" Zehra ta miqe da sauri ta zagaya wurin su itama ta rungume Papa tace "no I love him More" Khadeeja wadda take zaune itama ta miqe tare da zuwa wurinsu itama ta rungume shi tace "no, I love him more than all of you" Papa wanda yake cike da farin cikin yadda yaran suke nuna mishi so da qauna a kullum ne yace "I love you all my babies, Allah yayi muku albarka" gaba daya suka amsa da "ameen" Anty ta kalli Zehra tace "Zee I think yakamata ki daukar ma Fadeela abincin ta ki kai mata tunda dai ta kasa zama a nan din" Zehra tace "ok Ma" ta bugi kafadar Zain tace "congrats bro, can't wait for the day" ya kashe mata ido daya tare da fadin "thanks little Zee, can't wait too" Anty tace "yau an shiga uku, babu ko kunya Zain??" Yana dariya yace "bazaki gane bane Anty, I am head over heels for Dee" ya kalli Papa ya dan sosa kai yace "thanks again Papa, I am going back to the hospital akwai patient din da zan duba" sannan ya wuce ya fita yayinda suka dinga yi mishi dariya. ********** Kwance take a kan gadon Zehra tana ta chatting da Zain wanda yawanci hirar maganar sa ranar bikin su suke yi. Zehra ce ta shigo dakin riqe da cup na Popcorn ta zauna yayinda ta sa ma Fadeela ido. Gani nayi ta sa hannu ta qwace wayar sannan tace "its okay mana, I am jealous fa" Fadeela tana dariya tace "don't be my dear, ke ma kin kusa haduwa da prince charming dinki Insha Allah" Zehra ta lumshe idanuwa tace "can't wait Dee, I really want to fall in love. I want to fall in love with the most handsome guy on earth, the most sweetest and coolest guy, someone that will love me alone and no one else, someone that will stand by me through rough times, someone that can sacrifice everything for me, someone that can die for me, someone that..." Fadeela ce ta fashe da dariya tace "not again with this fantasy of yours Zee, come back to reality already. ke kam just pray you get a nice guy not a sadist irin su Ya Musty.." Zehra ta harare ta tare da fadin "haba Dee, ki daina fadin irin wadannan maganganun akan Yayan ki mana. Wai is he that bad??" Tana dariya tace "very bad my dear.." Zehra wadda ta watsa popcorn a bakinta ce ta gyara zama sannan tace "ni Kuwa ina so in hadu da shi..." Fadeela tana kallonta tace "hmm.. trust me Zee, that your Psychology abi Sociology won't help you understand the guy, he is just so outta this planet and on top of it all he decided to join the Army...huh" Zehra ta matsa kusa da Fadeela tace "Please Dee just do me a favour ki dan bani labarin shi, I really wanna know about him. You know very well cewar I like knowing about people and hey, this time you have to tell me everything" Fadeela tace "What do I tell you Zee?? abinda na sani dai shine Ya Musty is self-sufficient, reserved, yana enjoying alone time, he is a deep thinker, keeps opinion to himself but then I must admit that he is calm and collected" Ta dan girgiza kai yayinda ta cigaba da fadin "amma fa idan ka takura ma rayuwar shi, hmmmm you are so in trouble....shiyasa ma ni babu ruwana da shi" Ta gyara kwanciya sannan ta ja bargo tace "i guess it's all I know. he is my brother but how weird I don't even know much about him, funny right???" Zehra wadda ta cika da mamaki ce tace "whoa... dama irin wadannan mutanen suna existing a reality??? OMG, I really can't wait for a new experience..." ♤♤♤♤♤♤ Haduwar Omar Tafida da Abu-Yazeed tun suna yara. Sun kasance aminan juna tun zamanin quruciyar su.+ Haifaffun cikin garin Katsina. Iyayen su Katsinawa ne gaba da baya. Tare suka yi makarantar primary da secondary wanda bayan sun kammala ne iyayen su suka tura su qasar Switzerland suka cigaba da karatun su. Omar Tafida ya karanci Law yayinda Abu- Yazeed ya karanci Engineering. Suna gab da zasu kammala karatun su ne Mahaifin Omar ya hada shi aure da wata diyar abokin shi mai suna Nafisa. Tun kafin a hada su aure kuwa Omar ya kasance yana son Nafisa domin kuwa mace ce mai hankali sossai. duk tarin dukiyar da iyayen ta suka mallaka bata kasance mutuniyar banza ba. Asali ma mace ce kamila mai kamun kai, ga ilimi na addini harda boko. A lokacin da Nafisa ta kammala secondary dinta ne aka yi auren su wanda kuwa ya tafi da ita qasar Switzerland inda ta cigaba da karatun ta. Ko da suka kammala karatun su kuwa Omar ya tattaro ya dawo Nigeria inda ya samu aiki a Federal high court a cikin garin Abuja. Shi kuwa Abu-Yazeed a qasar Switzerland aka riqe shi inda ya samu aiki da wani kamfani. A qasar Switzerland ne Abu-Yazeed ya hadu da wata yarinya mai suna Aesha. Aesha dai asalinta mutimiyar qasar Lebanon ce. Kyakyawa fara sol. Iyayenta suna zaune a nan qasar Switzerland din ne wadanda aiki ya kai su zama can a wannan lokacin. Tuni suka qulla soyayya a tsakanin su. Iyayen Aesha suna son Abu-Yazeed sossai domin kuwa sun kula yana da hankali. A lokacin da suka hadu kuwa Aesha bata iya Hausa ba ko alama. Asali ma da turanci suke Magana ko kuma da larabci dukda kuwa shi Abu-Yazeed ba wani iya larabcin yayi ba. zama tare ne yasa Abu-Yazeed ya koya mata hausa wanda kuwa tayi picking ahankali har ta iya. Wasa wasa dai ganin shaquwar su tayi yawa ne yasa iyayen su suka shiga zancen su inda aka daura musu aure. A nan qasar Switzerland din suka cigaba da zama. Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya inda suka cigaba da zumunci dukda kuwa zumuncin ya fi qarfi ta waya. Ko da suka haihu yaran su suka taso basu san juna ba sossai a dalilin rashin haduwa. Yaran Omar sun kasance su Uku. Muhammad shine babba sai Mustapha sannan auta Fadeela. Shi kuwa Abu-Yazeed yaran shi biyu Zain da Zehra wanda kuwa a lokacin da Zehra take shekara goma ne mahaifiyarsu ta rasu a sanadiyar hatsarin mota. Mutuwar Aesha kuwa ya jijjiga Abu-Yazeed da yaran shi a wannan lokacin. A kan ikon Allah kuwa dole sukayi haquri suka dauki dangana. Bayan rasuwar mahaifiyar su zehra ne da shekara daya Omar yayi ma abokin nashi tayin qanwar shi mai suna Fatima. Ko da aka yi auren su da farko Abu-Yazeed ya qi sakin jiki da ita domin kuwa baya tunanin zai so wata mace kamar yadda ya so Mahaifiyar 'ya'yan shi amma kuma daga baya sai gashi ta maye gurbin ta. STORY CONTINUES BELOW Sossai su Zain sun ji dadin zama da ita domin kuwa ta kasance musu uwa ta gari. Al'amuran su kaf tana kula da su don haka ne suke bala'in sonta tare da girmama ta. Shekara daya da auren su ne ta haifi 'yarta kyakyawa wadda ta ci suna Khadeejah. ZEHRA Zehra ta taso cikin gata na iyaye . Yarinya fara sol kyakyawa. Kirki da son mutane. yarinya mai farin jinin gaske. Babu yadda za'a yi Zehra ta shiga wani wuri bata fita da tarin masoya ba. kowa sonta yake yi. Zehra tana shekara goma ne mahaifiyarta ta rasu a dalilin hatsarin mota da tayi. Wannan hatsarin kuwa ya faru ne a wata rana da suka je gidan iyayen ta tare da Zehra. A kan hanyar su ta dawowa ne birkin motar ya kufce mata inda ta daki wani dakali. Abin mamaki kuwa banda kanta da ya bugu a stirring babu wani injury din da tayi sustaining. Dayake dai dan Adam baya wuce lokacin shi ko kafin a kai ta asibiti ta rasu. Wani ikon Allah kuwa zehra ko ciwo bata ji ba a wannan lokacin saidai kuma wannan al'amari ya tsaya mata a rai wanda har gobe idan ta tuno abinda ya faru sai tayi ta rusa kuka. Tun daga wannan lokacin da mahaifiyarta ta rasu ne ta tsani mota a rayuwarta. Da girman ta ma kwata kwata ta qi yarda ta koyi tuqi saidai a tuqa ta. Tun da Zehra ta taso take qaunar son sanin halayyar mutane daban daban. Tana da son jin labarin mutane da experiences din su na rayuwa. Wannan ne yasa tayi taking up sociology as a course of study. Ta karanci litattafan psychology da dama. Da farko mahaifinta wanda suke kira da Papa bai so ta karanci wannan course din ba amma kuwa ganin cewar passion dinta ne ya haqura. Zehra dai a yanzu ba sai ta tambaye ka abinda yake damun ka ba, da ta karance ka zata fahimci halin da kake ciki shiyasa kuwa idan ma har ta tambaye ka abu kayi mata qarya tana ganewa. Zehra dai tun tana qarama take bala'in qaunar dafa abinci. Anty tayi fama da ita lokacin tana qarama da yadda take bata mata kicin. Tun tana qoqarin hana ta har ta fahimci cewar abinda take so ne with passion. Don haka ne ta sa ta a gaba ta dinga koya mata. Wasa wasa kuwa duka chefs din gidan an sallame su a dalilin zehra ta dauki responsibility na dafa abinci a gidan. Saboda tsananin son girki duk wata tasha da ake dafa abinci Zehra ta sani. Best tashar ta kuwa Food network. Idan dai tana gida toh fa Food network ne. Su Papa dai kullum sai sun ci sabon abinci. Babban Burin Zehra bai wuci na son bude qaton Restaurant ba. A lokacin da Zehra ta gama secondary school zata shiga jami'a ne Fadeela diyar aminin Papa wato Omar Tafida ta samu gurbi a University of Zurich. Fadeela dai a gidan su Zehra ta zauna. Sossai shaquwa ta shiga tsakanin ta da Zehra domin kuwa halin su kusan daya ne. tare suke zuwa makaranta sannan duk wata hidimar rayuwar su tare suke yi. Sun kasance aminan juna, babu sirrin junan su da basu sani ba. kaf duniyan nan babu mai shiga tsakanin su, idan ma ka shiga kai zaka sha kunya. Ko fada suka yi kuwa kafin wani ya ji su sun shirya tsakanin su, wannan ne yasa suke kiran kan su THE INSEPARABLES. Fadeela takan ba Zehra labarin 'yan gidan su wanda yawancin hirar bata wuce na Daddynta da Mummynta sai kuma na Yayan ta Muhammad. Dayan yayan nata Mustapha kuwa ko cikin hira ta kira sunan shi sai ta bata rai. Duk yadda Zehra taso ta ji labarin Mustapha abu ya gagara domin kuwa Fadeela ta gwada mata cewar babu abinda ta sani a game da rayuwar shi. Asali ma cewa take yi tunda ta taso ta gan shi a gidan da baqin hali yake. Ita kuwa Zehra addu'a take yi Allah ya kawo ranar da zata hadu da Mustapha ta ga asali wane irin mutum ne. Duk haduwa da take yi da mutane bata taba cin karo da mai irin halin shi ba. she became very interested in knowing more about him. Fadeela dai tunda ta zo gidan ta hadu da Zain yayan Zehra ne suka qulla soyayya. Zain dai a wannan lokacin yana gab da qarasa karatun shi na Medecine. Zain kuwa tuni ya fadi ma Papa cewar yana son Fadeela akan ya nemar mishi izini wurin Daddy ya amince mishi. Ko da Daddy ya ji labari kuwa yayi murna sossai domin kuwa hakan yana nufin qara danqon zumunci a tsakanin families din guda biyu. A lokacin da su Zehra suka kammala karatun Masters din su ne Papa ya samu appointment a Headquarter ta ma'aikatar NNPC a Nigeria. Don haka ne kuwa suka tattara suka dawo Nigeria inda ya mallaki gidan shi a unguwar Maitama a Abuja. Zain ma transfer ya name ya dawo National Hospital na Abuja inda ya kasance daya daga cikin manyan likitocin da ake ji da su. A lokacin da suka dawo kuwa Fadeela ta samu aiki a FIRS a nan cikin garin Abuja yayinda Zehra ta qi neman aiki. Makarantar koyon girki ta shiga domin kuwa burinta bai wuci ta zama independent entrepreneur ba. Tun lokacin da su Zehra suka dawo Nigeria kuwa suka koma kwana gidajen juna for one week. Idan Zehra ta kwana a gidan su Fadeela wannan satin toh next week fadeela zata kwana a gidan su Zehra. Rabin kayan su suna gidajen juna. Dakin Zehra ya kasance dakin Fadeela haka dakin Fadeela ya kasance na Zehra. Sossai amintakar su take birge iyayen su. Zehra dai ta kula tunda suka dawo bata ga yayyen Fadeela ba. ko da ta tambaye ta sai cewa tayi Muhammad wanda ya kasance Archietect yana London. Shi kuma Mustapha bata san inda yake ba, abinda ta sani shine he is an army officer, she doesn't even know wane rank yake balle his whereabouts... Zehra dai a kullum qara mamakin Fadeela take yi da yadda take yawan fadin bad about Mustapha. All she wants is to meet him so she can confirm what her friend is saying about him... The question here is what will she do if she does?????4 ♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE A yau Public Holiday suna gida. Zehra ce ta fito daga bathroom daure da towel yayinda tayi daurin turban da wani towel din a kanta. Fadeela wadda take kwance cikin bargo ce tace "sarkin tsabta yau din ma da babu inda zaki je sai kin buga sammako wurin wanka" Tana dariya tace "Dee, it is rightly said that cleanliness is next to Godliness" Fadeela ta Harare ta tare da fadin "shiyasa kike wanka more than five times a day??" Zehra ta qara fashewa da dariya tace "haba Dee, abin harda sharri?? Idan dai ina period ne nake yin wanka sau dayawa shima fa baya kai five times" Fadeela wadda ta gyara kwanciyar ta cikin bargo tace "uhm, I hear you" Zehra ta warware towel din kanta yayinda gashinta ya sauka a bayan ta da kafadun ta. Gani nayi ta janyo comb ta fara taje gashin nata sannan tace "Dee please in shirya in zo kiyi mun kalba?? Wallahi gashin nan ya dame ni a haka" Fadeela ta turo baki tace "gaskiya manya zanyi miki because this your full hair is something else" Zehra tana dariya tace "na amince Dee, idan dai zaki kitsa mun shi kin kyauta. Again cikin gashi na da naki wanne ya fi cika??" Fadeela tace "eh na sani cewar nawa ya fi cika amma ai naki ya fi tsawo" Haka dai suka cigaba da hira har Zehra ta shirya cikin wani pencil jeans da wata 'yar qaramar T-shirt. Suna cikin yin kitson ne Mummy ta qwanqwaso qofa ta shigo dakin. Bayan sun gaishe ta ne ta qarasa wurin su tace "ashe kitso kuke yi" Zehra tace "eh Mummy" Mummy ta zauna a kan stool din Vanity table din dakin tace "dama ina so ku fara shirya abubuwan da za'a buqata na tarban yayanku. Mun yi waya dazu yace ranar Saturday zai dawo" Fadeela ce tace "toh wai Mummy me zamu shirya mishi? Kin fi kowa sanin halin Ya Musty. Yanzu duk sai mun gama wahalar shirya mishi sai ya dawo ya gwasale mu. Ni kam Mummy wani lokaci ma gani nake kamar ba dan gidan nan ba wallahi" Ta dan yi dariya tace "anya ke kika haife shi kuwa??" Zehra ce tace "what the hell Dee..." yayinda Mummy wadda take dariya tace "qyale ta Zehra, tsinto shi nayi kuma haka zaku cigaba da zama a gida daya har lokacin da zakiyi aure ki bar mun gida na" Fadeela wadda take dariya tace "aikuwa gwara in tafi in bar ki da ke da shi, mutum kamar mai aljanu" Mummy tana dariya tace "idan kika ja tsiya ya dawo sai na fadi mishi maganganun da kike fadi akan shi" Da sauri Fadeela ta sauka a guje ta tsugunna gaban Mummy tare da riqe hannun ta tace "sorry Mummy please don't tell him, wallahi mugun tsoron shi nake yi. Har yau idan na tuno marin da yayi mun lokacin da na fasa mishi waya mistakenly sai hankali na ya tashi" Mummy da Zehra kuwa me zasuyi banda dariya. ********** A ranar kuwa su zehra suka fara shirye shiryen tarbar Mustapha. Sossai ake ta hidima kamar wadanda suke shirin tarbar shugaban qasa. Ana yi kuwa Fadeela tana ta qorafi yayinda Zehra ta shige gaba wurin hidimar. Duk yadda Zehra ta so ta san taste din Musty akan abubuwa ta kasa domin kuwa ba Fadeela ba hatta Mummy bata san abinda yake so da wanda baya so ba. STORY CONTINUES BELOW Hakan kuwa ya tabbatar mata da lallai Mustapha murdadden mutum ne. Ko da suka shiga kasuwa yin siyayya gaba daya favourite stuff din Zehra suka kwaso. Kwata kwata bata damu da cewar abu for men bane ko for women. A cewar ta tunda baya da choice he will have to go with hers. Ita dai Fadeela kallon ikon Allah kawai take yi domin kuwa ta ga yadda Zehra ta dage abin ba'a cewa komai. ********** Riqe take da makullin sashen shi yayinda ta kira masu aikin gidan don su je su gyara mishi. Zehra dai tunda ta doshi sashen shi ne ta ji bugun zuciyar ta ya qaru. Gani nayi ta dafe qirjin ta yayinda tace "relax Zehra, are you scared already?? The guy is not even around and..." Muryar daya daga cikin masu aikin ta ji tana fadin "Anty Zee, lafiya kike Magana ke kadai??" Da qyar ta saita murya tace "I am good Mairo" Ko da ta murda key din ta bude qofar ta shiga gani nayi ta tsaya cak yayinda ta sa ma falon ido. Ji nayi tace "wooow, how breathtakenly beautiful" Masu aikin suka yi dariya yayinda daya daga cikin su mai suna Furera tace "hmmm, ai Anty Zee sashen Uncle musty ya hadu. Ya fi na kowa kyau a gidan nan" Zehra dai lumshe idanuwa tayi tace "tabbas na amince da hakan" gani nayi tana waige waige tare da mamakin yadda sashen nashi yake tsab tsab kamar dama akwai mutum a ciki. Kallon su tayi tace "amma ya na ga kamar komai a tsabtace? Ba ance ya kusa shekara daya bai zo ba??" Mairo tace "hmm, ai Anty duk sati sai mun shigo mun share ko ina amma banda dakin shi. kin san fa Uncle Musty baya son datti ko alama. dama sai idan zai dawo ne Anty Dee take gyara mishi dakin shi" Kafin Zehra tayi Magana ne Fadeela ta shigo riqe da makullin dakin shi. A lokacin kuwa tuni Furera ta fara yaye cover din da aka rurrufe kujerun falon. Cike da mamaki Zehra ta zaro idanuwa tace "white???" Fadeela ta fashe da dariya tace "yes dear, White everything. I think its his fav color" Tuni dai masu aikin sun fara aikin su yayinda Fadeela ta janye Zehra zuwa dakin shi. Sossai Zehra tayi mamakin ganin lafiyayyen daki irin na Mustapha. A yanzu kuwa ta tabbatar cewar he has a high taste. Sannan kuma wani ikon Allah dukda rabon shi da gidan kusan shekara daya amma dakin yana ta baza qamshi. How weird she thought. Qamshin ya masifar yi ma Zehra dadi har tana fadin "I love the smell of his perfume Dee" Fadeela ta fashe da dariya tace "babes you are not serious" Sossai Zehra ta zage tana gyaran bedroom din. Suna cikin gyaran ne Zain ya kira Fadeela a waya yayinda Zehra tayi mata sign akan ta je ta amsa wayar ta kawai. Tunda kuwa Fadeela ta tafi bata dawo ba. Zehra kuwa tana gyare gyare tana yaba ma tsarin rayuwar shi. ita dai gaba daya abubuwan shi sun birge ta. tana cikin gyare gyare ne hannun ta ya kai wani drawer ta bude. Wani dan madaidaicin sketch ne ya fado yayinda tayi saurin sa hannu ta dauka. Gani nayi ta razana tare da zaro idanuwa. Qirjinta kuwa sai bugawa yake yi. Da sauri na ga ta nufi gaban madubi ta kalli idanuwan ta sannan ta kalli sketch din. STORY CONTINUES BELOW Ji nayi tace "hey, these looks like mine" Ni kuwa da na leqa sai na ga zanen idanuwa wadanda kuwa babu tantama idan ka tambaye ni zan ce maka idanuwan Zehra ne.. toh amma how is it possible?? Tana nan tsaye ne Fadeela ta shigo dakin. Qarsawa tayi wurinta tace "hey, what are you doing??" Zehra ta dago sketch din tace "I found this..." kafin ta rufe bakinta ne Fadeela tace "what the... babes this is your eyes. How did you... wait dama Ya Musty ya san ki ne? I mean baku taba haduwa ba, how comes he has a sketch of your eyes??" Zehra ta saki ajiyar zuciya tare da girgiza kai tace "well its possible na budurwar shi ce, its just a sketch after all" Fadeela ta fashe da dariya tace "budurwar shi?? I doubt.. wace mace ce zata yadda ta zama budurwar Ya Musty? ai shi ina kyautata zaton daddy sai ya kai hoton shi masallaci a roqa mishi mata..." Zehra wadda ta fashe da dariya tace "I swear babes baki da kirki, ni kam na qagara ya dawo in gani if at all what you are saying about him is true" Fadeela tana dariya tace "I swear babu exaggeration, trust me zaki ga more than this" Haka dai suka gama gyare mishi ko ina tsab. Wasu turarruka da Zehra ta siyo a kasuwa ta kwaso ta fesa ko ina sannan ta ajiye mishi sabbin turarukan wanka irin wadanda take amfani da su. Haka ta ajiye designer perfumes a kan Vanity table din shi. Fadeela wadda take ta kwasar dariya tace "wallahi Zee babu ruwana, idan ya dawo ya ga wadannan tarkacen naki ya fara fada. Kin kuwa san cewar dukkanin abubuwan da kika ajiye mishi for her ne??" Zehra tana dariya tace "don't worry Dee, nasan ma bazai kula ba" Haka dai suka gama suka bar mishi sashen nashi yayinda qamshi yake ta tashi. ********** Washegari ranar Saturday kuwa tun da safe Zehra ta shiga kicin. Sossai take ta shirye shiryen kalolin abincin da zata dafa. Mummy ta so tayi hiring Chefs amma Zehra ta hana. Haka ta dinga hidimar abinci kala kala, Fadeela wadda ba ma'abociyar girki ba kuwa tana nan zaune tana kallon ikon Allah, lokaci lokaci dai takan taya ta motsa abu a tukunya ko ta taimaka mata wurin yanka abu. Gaba daya gidan ya kaure da qamshin girkin Zehra. Bayan sun kammala ne suka samu Mummy zaune a falonta yayinda take ta yi musu sannu da aiki. Zehra tana kwance kan cinyar Mummy yayinda Fadeela take zaune a gefe tana chatting da Zain a waya. Mummy ce ta shafa kan Zehra tace "ke kam Zehra mijin ki ya huta wallahi, abinci dai sai ya ture" Fadeela tana murmushi tace "abinda yake bani mamaki shine sai ta dafa amma kuma bata wani ci dayawa" Furera ce ta shigo falon cikin sallama yayinda ta qaraso wurin su ta tsugunna har qasa tace "Mummy an kawo kayan wankin Uncle Musty..." Mummy ta kalli Fadeela tace "sai ki je ki shigar mishi da su" Fadeela ta dan turo baki tace "gaskiya Ya Musty yana wahalar da mutane, shiyasa fa na fi son idan Ya Moha zai dawo. Komai nashi simple wallahi" Zehra ce ta miqe tare da fadin "uhm, ni bari in shigar mishi da su Mummy" Ta kalli Fadeela tace "where did you keep the key?" tace "yana kan Vanity Table, thanks love" Ko da ta shiga dakin shi bude wadrobe din nashi tayi yayinda ta dinga jera mishi kayan shi. STORY CONTINUES BELOW Zehra dai ta kula cewar yana son Kaftans domin kuwa kusan duka kayan nashi da aka kawo daga wurin wanki Kaftans ne. Abinda ya bata mamaki kuwa 80% na kaftans din Musty Farare ne. A yanzu kuwa ta amince lallai white is his fav color. Bayan ta gama jera kayan ne ta dauko turarrukan da ta ajiye mishi ta shiga fesawa. Tuni wadrobe din suka dauki qamshi. Ko da ta gama har ta juya zata fita sai kuma na ga ta dawo ta zauna kan stool din vanity table yayinda ta bude wata drawer ta zaro Note pad da pen tayi rubutu a ciki. Gani nayi ta yaga page din sannan ta ajiye a saman note pad din sannan ta dora pen din a bisa. Miqewa tayi tana murmushi ta fita daga dakin. ************ Qarfe tara na dare suna ta jiran isowar Musty amma shiru. Mummy dai tana ta kiran wayar shi amma bata shiga. Zehra duk ta bi ta damu har tana fadin "Allah dai yasa lafiya" Fadeela ce tace "yanzu haka ma don wulaqanci qila ya fasa zuwa ne shine ya bamu wahala" Mummy ce tace "aikuwa ko da muka yi waya da safe yace mun yana airport, the distance from Russia zuwa Nigeria ai ya ci ace ya iso" Fadeela ce tace "oh wai dama Russia yake? me yake yi a can ne wai Mummy??" Mummy tace "course ne suka yi na ten months..." Fadeela tace "uhmm, Allah yasa dai bazai dade ba idan ya zo" Mummy tana dariya tace "aikuwa zaiyi kusan wata uku..." Fadeela ta zaro idanuwa tace what?? ashe kuwa mun shiga uku" Haka dai suka cigaba da hira yayinda Zehra ta shiga tsananin damuwa, Addu'a take ta yi a ranta Allah yasa komai lafiya" ********** Wuraren qarfe goma sha biyu na dare na ji horn. Ko da security ya bude gate din wata farar Mercedes benz E350 ta shigo gidan yayinda na ga security din ya daga hannun shi tare da duqawa, da alama gaisuwa yake miqawa. Qarar horn kawai na ji wanda hakan ya tabbatar mun da cewa mamallakin motar ya amsa gaisuwar security din ne. Ko da motar ta tsaya a parking lot tuni ma'aikatan gidan sun zagaye motar cike da girmamawa yayinda suke jiran fitowar shi. Ni kaina sai da na matsa don ba ma idanuwa na abinci. Bayan kusan minti biyar ne na ga ya bude qofar motar ya fito. Aikuwa ban san lokacin da nace "OMG" ba. Wani kyakyawan saurayi, fari, dogo with a well-built body ne ya fito daga motar. Sanye yake cikin wandon Camo na three quarter da farar T-shirt. Yayi masifar kyau. Cike da girmamawa ma'aikatan suka dinga gaishe shi yayinda ya daga musu hannu, key din motar ya danna yayinda boot din motar ya bude sannan ya jefa ma Iro direba key din ya nufi sashen shi. Yana murda key din sashen shi ya shiga ne na ga ya tsaya cak tare da lumshe idanuwa yayinda yake ta shaqar wani qamshi mai dadi. Har ma'aikatan gidan suka shigo mishi da akwatunan shi yana nan tsaye idanuwan shi a rufe. Muryar Iro direba ce ta dawo da shi inda ya ji yana fadin "ga makullin nan Yallabai, sai da safe" ya fita. Ajiyar zuciya ya saki sannan ya rufe qofar shi. akwatunan nashi ya ja kai tsaye ya wuce bedroom dinshi. A nan ma tsayawa yayi cak a bakin qofa ganin yadda aka gyare ko ina tsab sannan ga wani asirtaccen qamshi da yake tashi. Ji nayi yace "like seriously??" Asali dai ba'a taba gyara ma Mustapha sashen shi ya ji dadi ba kamar wannan karon.. saboda rashin gyaruwa a lokuttan baya idan ya dawo sai ya qara gyarawa da kan shi amma kuma abin mamaki wannan karon ko ina looking spotless. Ko zama bai yi ba ya nufi dressing room dinshi ya tube kayan jikin shi yayi shirin shiga wanka. Mustapha wanda bai cika dadewa wurin wanka ba kuwa a yau sai ya tsinci kanshi da dadewa yayinda yake ta shaqar daddadan qamshin turarrukan wankan da ko duba sunan su bai yi ba. Bayan ya fito ya nufi gaban madubi, turaruka kawai ya fesa sai wani oil da ya shafa a gashin kanshi da sajen shi. bayan ya gama brushing gashin kan nashi ne ya nufi dressing room dinshi. Ni kuwa nace su ma turarrukan bai duba ba balle ya ga irin su. Da alama dai a gajiye yake shiyasa. Ko da ya bude wadrobe din shi wani lafiyayyen qamshi ya bugi hancin shi. Abinda ya birge shi kuma yadda aka jera mishi kayan gwanin ban sha'awa. Cike da mamaki yace "I can't believe she did all these for me.." ♤♤♤♤♤♤ Ghen ghen ghen... Wa yake tunanin tayi mishi wannan gyaran???7 What about the sketch da Zehra ta gani a drawer din Musty??? Zanen idanuwan ta ne ko kuwa?? Shin ya san ta ne dama ko kuwa?? What kinda guy is MUSTAPHA??

Post a Comment for "ZEHRA CHAPTER 1"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...