Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NI DA PRINCE     CHAPTER 6

NI DA PRINCE CHAPTER 6

- - Post a Comment
NI DA PRINCE CHAPTER 6
Mayafin kalar kayan tad'auko sannan tasa takalmi flat ta fito falon, salman na zaune a dinning kuyangi na tsaye a bayansa, ta karasa gun cikin nutsuwa. + Kuyangin ne suka gaisheta a tare ta amsa tare da zama a falon, salman yai gyaran murya da alama magana yakesan yi salma ta mannamai, yasake yi hakan yasa tad'an dago yamata alama da fuska akan tazo taci abinci, ta juya kai tace nakoshi in ka gama mu wuce, ya d'aga kafad'a alamar ruwanta sannan ya kammala tare da mikewa yai hanyar waje, salma ta mike tare dayin tsaki tace mutum sai girman kai ai yacemin in taso😠, ta mike hanne da wata baiwar nabinta a baya salman tagani tsaye a waje takarasa nan bayi maza suka rufo musu baya, salman yad'aga kai sama mutane na gaisheshi amma ga mamaki salma ko amsawa bayayi. Sai da suka kusa isa fadar sarki, salman ya matso daf da ita yace u have to be careful dan karki kuskura ki bari wani a cikin gidan nan yasan irin zaman da muke, mark my word. Salma ta d'ago ta kalleshi gabanta ne ke fad'uwa tadaure tace sai ka fad'amin😗? Bai bata amsa ba ya cigaba da tafiya, sun isa fadar nan aka musu iso, bayan sun shiga salman ya tsuguna itama ta tsugunna nan suka gaida sarki ya amsa cikin farin ciki, nan 'yan fada suka fita suka barsu, sarki yakalli salma yai murmushi lalai yama d'anshi zabi mai kyau dan yarinyar ta kwantamai, yamaida idansa kan salman yace salman ina tsananin farin cikin wannan auran dan Allah ka rike yarinyarnan amana, kaji? Salman yai kasa dakai yace insha Allahu Abba, salma ta kalleshi ta gefen ido tace sai kace gaske ji yanda yakoma innocent😏. Sarki yace jeka waje salman inasan magana da sirikata salman ya d'ago tare da kallan salma sannan ya mike yai waje, sarki ya kalli salma yace 'yata matso, cikin kunya salma ta matsa kad'an sarki yace salma agaskiya ba yaba da yanda kike Allah yasa abinda nagani hakan yake, tai kasa dakai batare datace komai ba, yace salma dan Allah ki rike yaron can da mutunci ki kula dashi, yaro ne maraya he is so lonely, salma tad'an dago idanta maraya? Ta maimaita aranta yace eh salma maraya ne mamaki ya kamata ya akai yasan abinda ke ranta? Sarki yakatse tunaninta dacewa Allah yabaku zaman lafiya tai kasa da kai batace komai ba, yace jeki salma ta mike tare damai sallama. Tana fita ta saki ajiyar zuciya tare da dubawa ko zataga salman, sai dai ba alamarsa, hannece ta karaso tace ranki ya dade muje inkin gama, salma har zatai magana sai kuma ta fasa tace muje. Part dinta suka koma hanne tace sai gobe zaku gaidasu fulani tace to tare da shiga ciki, daki ta koma ga mamakinta salman taganI zaune yasa earphone a kunnensa haushi yakamata ko kallansa batai ba ta karasa kan karamar kujerar d'akin ta zauna tare da kifa kanta ajikin kujerar, tunanin rayuwarsu da kamal tafara, yanda yasota yakuma kula da ita, dashi ta aura tasan da sunanan suna diga luv💖 amma gata yau ta auri wanda kallansa batasan yi shima haka. Tunaninta yayi zurfi batasan sanda hawaye yafara zubo mata ba, muryar salman taji da alama waya yake, jitai yace kai fa dan iska ne najib ni kakema zancen wata amarya? Bataji mai akaceba sai jiganI tai yad'an kalleta sannan yace kai har kana tunanin akwai wata 'ya mace daxanyi lokacin ta? Ni ai a tarihin rayuwata ba mace kaima kasani, ganin yanda salman yai shiru daga ji magana ake sai jitai yace banda lokacinka sannan zancen lokaci kuma mu zuba mugani, yana kainan ya katse wayar sannan yakalli salma yace ke kuma meye na kallona ina magana? Tace mezan kalla? Yace banasan kallo gwara ki sani, haushi ya isheta dama a wuya take tace malam nifa nagaji da bakaken maganganunka salman nifa nasan nafika san rashin auren nan dan ni inada wanda nake so kaifa? Bana tunanin kasan me kalmar so take nufi, sannan.....dasauri ya katseta yace kinada magana ne? Tace ai maganar nakeyi yanzu😡 yace banjiba ko zaki maimaita😏? Bakin ciki ne yazoma salma wuya tarasa mema zatace kawai ta harareshi tare da cewa haka maraya yake?I thought mara uwa ba haka suke ba? Cikin hanzari taga salman ya sauko idanunsa ya kad'a yai jaa yakaraso inda take ya fizgota daga kan kujera sannan ya matseta a jikin bango, idanta ta runtse da karfi, ko miyau takasa yad'iya salman cikin zafin rai da wata irin murya yace *WHAT DO U KNOW*? Jikin salma yafara rawa, salman ya kara matse mata hannu har saidatai karamin kara yace *HOW DARE U TALK TO ME LIKE THAT?* I can tolerate anything but don't u dare to say something like that😡.. Salma kam jikinta rawa kawai yake yana gama fad'ar haka ya saketa tare da d'aukan makullin mota yabar dakin, idanta na rufe sai dataji ya bugo kofa da karfi sannan ta bude ido a hankali jikinta har a lokacin bai daina rawa ba ta kalli hannunta dake mata zafi, ganin guntai yayi jaa dakyar ta furzar da wata iska sannan ta tsugunna tare da rike kanta, tace me nace da ranshi ya b'aci haka? Ahankali hawaye yafara zubo mata tace yaya kamal yazanyi? Salman yana fita mota ya fad'a yai hanyar Buk, tafiya yake amma ransa duk a b'ace, inda najib yake ya nufa, a kusa da makarantar Buk yake da zama, najib bad'an kano bane daga bauchi yake, karatune yakawoshi nan.+ Salman yai parking din mota ya fito ya nufi d'akin najib, knocking yai najib dake zaune yana kallo yataso ya budemai, cike da mamaki yake kallan salman sai dai kafin ya firta wata kalma salman ya ture hannunsa dake jikin kofa ya wuce cikin d'akin, najib yakalleshi yace Ango? Ya haka? Salman ya fad'a gado tare da d'aukar remote yace waye angon? Najib ya rufe kofar tare da karasowa yace salman bai kamatafa aganka a wajeba yau🤔salman yace tunda kaine ubana ba? Najib yace Allah yabaka hakuri dagaji ranka a b'ace yake, salman yai tsaki tare da canza tasha yace nifa banajin zan iya sati 1 da waccen 'yar rainin hankalin a d'aki d'aya😏 najib yace haba salman meyasa kake hakane? Kasani sarai su ishaq dasaninsu suka tinguno zancen auren nan, plz ka jure mubasu kunya. Salman yace yarinyarce kanta na rawa tagama rainani, sai kace ni din sa'an tane😠. Najib yace salman yarinyar nan fa batada laifi ina ganin yanda kake mata, ni naji dad.....salman yakatseshi yace kasan wacece ma wai? Najib yace naji dai Amir yace 'yar skul din mu ce, salman yace kyale banza shi baisan me ake ciki ba sai yaje yana yad'a maganarsu mannir, wannan 'yar rainin hankalin nan cefa mai *Ninja*😏najib yace ninja? Salman yace kaifa banza ne ninja mana basune suke rufe fuskarsu da wani bakin kyalleba? Najib ya kwashe da dariya yace amma prince sai a hankali nikaf din ne ninja? Yace to yarinyar cefa? Najib yace badai wacce nakusan bigewa ina koyon nan ba? Salman ya juya kai yakalli gefe sannan ya ceji baki yace ita fa, najib yace ita😳? To dama ka santa ne? Salman yace dalla malam inazansan wannan kucakar?nifa an cucenI wlh, najib yace amma ta hadu akwai kyau😁. Ran salman ya b'aci yad'au pillow ya makamai yace cemaka akai kyai shine komai?nan dai sukaita musunsu nikam naja jiki nabar gun😒. 1 Salma kam ta dade kafin tadawo normal nan ta gyara d'akin dan taga falon har an gyara kafin su fito ankuma sa turaren wuta, bayan tagamane 'yan uwa sukaita zuwa yi mata sallama sai azahar tasamu nutsuwa tai alwala tai sallah, so take ta zaga taga gidan sai dai kunyar hakan takeyi, hakan yasa kawai tazauna a d'aki ganin qur'anI yasa tad'auka tafara karantawa, jitai cikinta na kara tasanI yunwace amma fitina irinta salma taki fita taci. sai karfe 2;30 hanne ta kwankwasa salma ta bude, tace ranki ya dade ankawo abincin rana tace to tare da mikewa nan tazauna a dinning ganin abinci kala_kala yasa tace hanne abincin ai yai yawa🤔 hanne tacs haka ake kawowa sai dai inkungama sai akwashe, salma ta girgiza kai tace oh nan tafara cin abinci, taci sosai sannan tasha lemo ta koma d'aki. Hartai isha'I salman bai dawoba hakan yasa ta kwanta a gado ta shige bargo, dan sanyi akeyi, jiya data kwanta a kasa sanyi ya ratsata ga ba bargo, da ciwon jiki ta tash. Jinta mike akan had'aden gadon d'akin yasa tasaki ajiyar zuciya, takwanta tashiha tunanin masoyinta, da ace tanada waya dako Abba takira taji lafiyar kamal😞 tana tunani bacci mai karfi yai gaba da ita. Salman sai 11 ya dawo ya shigo, ganin d'akin dulim ba wuta yasa ya kunna, mamaki ne yakamashi ganin salma tai dai_dai akan gadonshi, yakarasa cikin bacin rai yad'au sandarshi ya zunguro ta ta farka cikin razana tare da rike gun, ganin salman yasa ta hade rai tace malam banasan haka, nafad'ama kadaina zungurata salman yai murmurshI 😏yace kinfisan in tab'aki? Dasauri tace karka kuskura ehe😗 yace to mike mai guri yazo ai kin mori gadon, salma kam taji dadin bacci akan gado tace ina zani? Yace inazaki? Inda kike kwana mana🤔tace tab aikam yau bazan yarda ba sai dai kanani pillow da bargo😕salman yace bakya ganewa ko? Yafad'a yana nuna kansa, tace oho ko mezakace baxan yadda insake kwana a kasa ba😠. Salma yace matsalarkice wannan sannan yad'au rigar dayake bacci da ita ya wuce toilet ta murguda baki tace ai naga alama sai nima nadinga zakewa😠. Ai naga yanada d'an manner nasan yanda zanyi yaban bargo, Hijab din sallarta tad'auko tasa a tsakiyar gadon, yana fitowa ya kalleta yace baki sauka ba? Tace oho gashinan na raba mana ni nan bangaren kai nan, salman yai wata dariya yace what? Gadon nawa kika raba harda wani ni nan ke nan? Tace eh sannan kar wanda ya kuskura ya gangaro bangaren d'an uwansa😏 salman yace lalai kin girma dayawa tace da nid'in yarinya ce? Yace kin cire hijab dinnan kin sauko ko kuwa? Tace kazabi d'ayan uku, ko in koma falo na kwanta, ko kaban bargo ko kuma mu kwana a haka😏 salman yakalleta yace in zaba? Tace eh u have to choose a'a bama haka ba u most choose😎.... Salman yai ajiyar zuciya yace ke karki kuskura kib'atamin rai a daren nan dan zakisha mamaki, salma tad'an juyakai batare datayi magana ba, salman yace kwanta!in so kike mu kwana tare😏 dasauri ta juyo tace na'am? Yace eh ba haka kike son jiba? Ta mike daga kan gadon tace yaza'ayi mukwana tare😳? Salman ya matso inda take yasa hannunshi a kugunta ya janyota jikinshi, da sauri ta runtse ido, yai wani murmushin mugunta yace ba haka kike so ba? Ta d'aure tazare jikinta tace a'a ka kwanta😞.+ Salman yace a'a mukwana taren ko? Dasauri ta girgiza kai tace a'a nabarma bargon da pillow d'in yaI kwafa aranshi yace kin d'aukan bansan burga zakimin ba? . Kwanciya yai tare da jefo maya pillow din, ta amsa tarr da kallanshi☹, sunyi shiru dukansu kowa da abinda yake sakawa,can tad'aure tace sorry cikin sanyin murya, shima cikin magana mai sanyi yace 4 what? Tace maganar dana fad'a dazu I think bai kamata nafad'a ba, salman yad'anyi juyi yace at least kinsani, tace eh amma kaima u overreacted yace so kike nima in baki hakuri? Tace in mutum yai abinda bai daceba hakuri yake badawa ai, yace in hakane I can't zatai magana yace karki damen bacci nakeji🤔 aranta tace kamar nadamu muyi maganar😒. Karfe 4 ta tashi tai alwala ta fara nafila batai minti goma da tashi ba salman ya mike ganin tana sallah kwarai yaji dadi aransa, mikewa yai yashiga toilet shima yad'auro alwala ya fita, harya dawo tana zaune tana karatun qur'ani sai dai a zuciyarta takeyi. Wucewa yai ya hau gado sai dai ba bacci yai ba waya ya d'auko yana dannawa. Wajen 7 ta kwanta yana kallanta sannan shima ya kwanta, basu tashiba sai da hanne tai musu knocking, salma ta mike tare da bude kofar, hanne tace ranki ya dade ku shirya zaku gaisuwa gun matan gidan, tace to nagode, hanne tace aikin nane ai. Salma takoma ciki tare da kallan salman tace zamu gaisuwa, yai tsaki tare da juya mata baya ta makamai harara aranta tace so rude. Kaya ta d'auka ta wuce toilet tai wanka ta goge jikinta tasa kayan, tana fitowa ya shiga ta kalleshi tace mutum sai isa🤔? Yace I can hear u dasauri ta rufe bakinta, ta shafa mai tare da murza hoda, ta zura kwalli tayi kyau dan dama mai kyan ce. Mayafi tad'auka tare da cewa dole insa akawomin Abba yad'inkon hijabai ko biyu ne ta yafa mayafin tai falo, shayi ta had'a ko kulolin bata budeba, ta kurba ruwan tea din jin daxafi yasa ta ajiye tashiga tunani, ko ina yaya kamal? Wai ahaka zata kare rayuwarta a gidan nan? Kwakwalwarta ta cunkushe da wannan tunanin da basu da amsa, batasan salman harya fito ya zauna a kujerar gefenta ta d'ayan bangaren, jin motsin bude kula ne yasata ta d'ago wata baiwa ce ke bude kwanukan tana tambayarshi abinda yakeso? Salma takalleshi ta tabe baki, a ranta tace abincin ma sai an budema? Ko kallanta baiyiba itama tad'auke kai tashanye shayinta ta mike da sauri hanne ta karaso tace ranki ya dade bakici abinciba ai😞? Salma tace banajin ci ne hanne karki damu, hanne tace jiyamafa bakice na safe ba, salma tace nakoshi ne, hanne zatai magana salman yace kin min shiru ko kuwa? Batace ta koshi ba? Hanne tai kasa tace yahkri ranka ya dade, salma ta kalleshi ranta in yayi dubu ya b'aci ta koma falo ta zauna a kujera batare datace komai ba. Salman harya gama sannan, ya mike tare da kallanta dasauri hanne takarasa gunta tace ki taso, salma ta d'ago ganin salman na kalleta ta harareshi tare da d'auke kai, ya ce taso mana? Ta mike fuskarnan a hade suka fito a jere ya matso yace kin manta abinda nace miki ko? Karki bari wasu susan halin da muke ciki ta kalleshi tace kaikuma fa? Yace ni me? Tace shikenan. Ya juya kai nan suka wuce bayi nata gaisuwa, salma na amsawa ya matso yace kidaina amsawa ki wuce kawai tace amm...yace bansan musu tad'an turo baki batarr datayI magana ba haka suka karasa bangaren hajiya karama tana zaune a kilisarta sun shiga sun gaisheta ta amsa tare da tambayar salma yazaman bakunta, daganan bata sake magana ba shima salman haka, nan suka taso sukai hanyar bangaren hajiya babba itama sun gaisa tad'an tambayi salma koda abinda takeso? Tace a'a nan ma taga sunyi shiru har suka taso, mamaki ya isheta haka ake rayuwa a gidan bad'an hirar rayuwa da shakuwa? Sun isa bangaren fulani zasu shiha ishaq ya taho shida mannir tundaga nesa ishaq kebin salma da kallo har karkata kai yake, suna isowa kofa ya kura mata ido sam yamanta da salman, sai da mannir ya kula yadan tabashi sannan, itakam salma duk ta tsargu ganin irin kallan dayake mata, ishaq ya had'eyi yawo tare da cewa Ango kasha kanshi😁 salman yaI murmushi tare da cewa muje ciki ishaq ya kalli salma yace Amarya muje😁, takalleshi tareda yin murmushi ai jiyai kamar ya fad'I har salma ta shige ciki itada salman ishaq bai kula ba sai da mannir ya matso yace yaya me kake kitsimawa? Ishaq yace mannir waccen yarinyarce matar salman? Mannir yace eh mana dan ma baka ganta agun dinner ba🤔 ishaq yai ajiyar zuciya yace amma na cuci kaina ai dani ta dace gaskiya da sake😠. Mannir yace sai hakuri dan tazama matar kanninka, haushi ya ishi ishaq yace bazan yarda ba kasan irin wannan matar nake dreaming arayuwata? Najib yace yaya mai kake shirin yi? Yace I have to think amma bazan bari ta kubcemin ba😕

Post a Comment for "NI DA PRINCE CHAPTER 6"