Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NI DA PRINCE CHAPTER 4

NI DA PRINCE CHAPTER 4

- - Post a Comment
NI DA PRINCE CHAPTER 4
Salman zaune a gaban sarki, mai martaba yace za'a kwashe kayan bangarenka a sake wasu ko kana bukatar wani abun? Salman yace a'a duk yanda kuka gani, sarki yace inafatan kaje gun yarinyar kaji ko tana bukatar wani abun na biki? Salman yaji gabansa ya fad'I amma yad'aure yace tace bata bukatar komaI, sarki yace zancen banza kenan kai bakasan kawaici ba? Ko kataba ganin inda amarya tace bata bukatar kudi? Salman yai kasa dakai yace zan aika mata wani abun, sarki yace dakanka zaka koma, salman yadaure yace to Abba. + Lefen da aka kai sai daya tsorata duk yan uwan dasukaje, mamakin irin kayan da aka zuba suke, kamar ba'a talauci a duniya? Kanwar maman salma kam kasa jurewa tai tace kai JAMA'A kayan nan ai sunyi yawa, zainab tace haba hajiya bakomai ai nan kowa yashiga jinjina wa salma lalai kam tagama warkewa, dan gidan sarki? Hmmm. Zeena kam zaune kawai take amma sam ranta badadi yama za'ayi ace salman guda a aura masa yarinyar da iyayenta basufi bayin gidansu ba😡 nan suka ajiye kudin dinkin amarya dana kwalliya, dubu dari biyu mamaki yakama mutane nan aka shiga gulma daga gani Abba saida 'yarsa yai inba haka ba wannan kudi da kaya haka? Shiyasa ma bikin ba'a wani ja shi ba, sudai 'yan kawo lefe nan suka tafi suma suna gulma. A gidan akabar kayan dan kamwar maman salma tace in aka kai kayan can gulma yawa zatai, nan suka debi d'inkakun kaya a karamar jaka suka fita. Salma na kwance zazzabin jikinta yafara raguwar dan bacci ya d'auketa taji guda a saitin kunnenta da sauri ta mike a zabure, dangin mamanta ne suke guda, wata daga cikinsu tace kai yarinya tayi goshi irin wannan al'amura haka? Salma kam kallansu kawai takeyi Asabe kanwar mamansu tace tashi kiyi wanka dalla kinwani zauna kamar wacce za'a kaita gidan marii, salma tace nifa.....Asabe tace so kike kibamu kunya?kin tashi ko sai na miki wanka dakaina? Salma ta mike tare da turo baki tai waje, nan aka shiga guda. Suna zaune ita da kawayenta 'yan uwa, sun sata agaba suna tsokana idanta duk ya cika da kwalla, Asabe tazo tace wai ma taci abinci? Sukace anya kuwa? Nan ta kama hannun salma tai dakin umma da ita tasa aka siyo maltina da madarar ruwa ta juye a kofi tace kafa kai? Salma tace nifa banajin yunwa☹ tace kin kafa kai kosai na mareki? Nan salma ta amsa tana sha tana kuka inta tuno kamal sai taji kamar ta kwalla ihu. Ran Alhamis da safe gida ya cika taf salma na kwance zazzabi yadawo sabo, jin gobe za'a d'aura aure kuma akaita, wank yaro ne yai sallama yace wai ana sallama da salma, Asabe ta shigo d'akin tace tashi kiji inaji angon ne salma ta hade rai takuma ki tashi, asabe tace kin tashi ko kuwa? Salma ta mike ta yayimi hijabin sallarta ta zura tai waje Asabe na kiranta amma ina hartakai kofa, zuciyarta taf take da masifa, sai dai me? Tana zuwa taga wannan bafaden na rannan, yana ganinta ya zube a kasa yashiga jera gaisuwa ita abin ma mamaki ya bata dakyar tace menene hakan? Yana tsugunne ya miko mata envelope takalleshi tace namiye? Yace aikoni akai inkawo miki, tace inji wa fa? Yace mai gidana, tace ina nasanshi?yace wanda zaki aurafa? Sai yanzu ta gane, haushi ya isheta tai tsaki tace kamaidamai kudinsa kace bana bukatar wannan, in yanaso ya birgeni to ya......tunowa tai dakalmar mahaifinta dayace nasani bazaki bani kunya ba, idanta ya ciko da kwalla tace ka maidamai kudinsa bana bukata tana fad'a tai ciki da sauri. Tana shiga kowa ya shiga kallanta ana tsokana, wato dan rashin hakuri shida za'a kaimasa ke gobe shine sai daya aiko aga lafiyarki?haushi ya kamata ko kulasu batai ba tai d'aki ta shiga bargo tasaki kuka. Salma kam hidimarsa yake kamar ba aurensa za'ayi ba su Amir ma abakin mannir sukaji zancen auren. Yau juma'a tun safe gida ya cika makil, salma kam tana d'akin goggo a kwance, Abba ne ya shigo tana kwance idanta duk ya kumbura, ahankali yakalleta tare da zama kusa da ita. Idanunta ta bude ganin Abba yasa ta kakaro murmushi tace Abba, tafad'a ta a kokarin mikewa hannu yasa a kafad'arta yace yi kwanciyarki salma, ta kwanta tare da yin shiru, yace salma ni najamiki ciwon nan ko? Tace a'a Abba, yace nasani salma kiyi hakuri laifinane dana bari yaya ya amsa tun farkon maganar, dasauri tace haba Abba ai nasan dan kun isa danine yasa kuka amsa, yace to meya saki zazzabi? Aranta tace ko mijin fa bansani ba? Nadaisan yana da hadi da gidan saraura tunda taji 'yan uwa nazancen, sai kuma bafaden nan data gani, amma afili tace cutace kawai, Abba yace salma Allah yamiki Albarka, da izinin Allab bazakiyi danasanin wannan auran ba, tai murmushi tare da cewa yaya kamal ya sani? Abba yace ai kamal sam ko babansa yakirashi baya d'agawa bamusan me yake tunani ba, tai shiru..... Abba yace da daddare za'a kaiki nasani ke yarinyace tagari amma gidan dazaki sai kinyi hakuri, tace wani iri ne? Yacr gidan sarauta tad'an juya kai kodai d'an gidan waziri zata aura? Abba dakanshi yasa aka kawo mata koko da kosai taci. Auren in anyi sallar juma'a ne hakan yasa Massallacin gidan sarki ya cika taf da mutane, manyan mutane na sarauta da kuma na milki. Salman na kwance a d'aki yana sharar baccinsa, sai nemanshi akeyi, najib ne ya shigo dakin kamar wasa dan baiyi tunanin zai ganshi anan ba,mamaki ya kamashi ganin salman daI_dai akan gado yana bacci karasawa yai kusa dashi tare da tabashi, cikin abin bacci salman ya bude ido, Najib yace prince me kakeyi hakan? Salman yace don't u see? Najib yace anacan ana nemanka amma kana nan kana bacci😳? Salman yace oh!!! Lokacin auran nasu yayi ne? Yafad'a tare da duba agoggon bango na d'akin, najib yace auransu ko auranka? Salman yai tsaki yace ni wannan shirman auran badamuna yai ba yarinyarce koma wacece kawai ina tausayinta, sannan ina tausayin kaina dan za'asani sharing din daki da wata kucaka😡 ko dayake servant zansamu, Najib yace salman kasan me kake fad'a kuwa? Yace malam kyaleni, najib yace naji amma tashi ka shirya kafin ran mai martaba ya baci, salman ya mike yasaki kwafa irin ta muguntarnan. Haka salman yashirya cikin dakakun kayan sarauta da Mai martaba ya aikomai dashi, shi kanshi yasan yayi kyau najib sai kodashi yake, yai dan karamin tsaki yace I wish wannan auran da budurwar danakeso akeyi,amma meye amfanin kwalliyar? Najib yace zaka fara ko? Dan Allah kazo mu wuce, turarensa ya fesa sannan yasa hula da takalmi ya fito cikin kasaitarsa. + Tunda ya fito bayi da 'yan uwa kemai sannu da Allah yasanya alkairi amma kasaita da jin kai irin na salman ba wanda ya amsawa sai najib ne yashiga amsawa. Yana zuwa hanyar fada wasu bayi sukazo suka kewayeshi yace kun fara ko? Najib yace wad'annan fa? Salman yace ai aiki yaganka dan hakannan zasuyi tabinmu har agama, najib yace lalai kace alamace ta ango ya taho, salman ya juya kai ba tare dayai magana ba. Guri yacika sosai su Abba kam suna wani guri da aka ware musu, tsoro ya fara kama Abba shikanshi yafara tunanin kodai saida 'yarsa yai?. Salman haka yai ta ratsawa cikin manyan mutane suna gaisawa, basu dade ba aka shiga huduba ta sallar juma'a, bayan anyi sallah ne aka d'aura auran *SALMAN DA SALMA* akan sadaki dubu hamsin, dan Abba yace sadaki kad'an yafi daraja a aure duk yanda sukaso ko dari abada amma yaki yace hamsin ya isa hakan yasa aka hakura aka bada hamsin. 1 Salman kam baimasan an d'aura auran ba yana waje suna hira da Amir da Najib sai dayaji masu busa da kirari sun matso kusa dashi sunayi nan fa mutane suka zagayeshi, haushi duk ya isheshi jin wai sunan matar salma, wato salman da salma kenan😡? Inama ace wacce yakeso ne take da wannan sunan kuma sukai aure? Da baisan irin kyautar dazaiyi ba yau. Najib ne yaja hannun salman yakaishi gunsu Abba, har kasa salman ya tsugunna yagaidasu, Mustafa yace ikon Allah sai yau mukaga sirikin namu, salman yai kasa dakai, Abba yadaure yace salman ko? Nan prince yace eh, Abba yace kada kamanta amana muka baka😊 salman aranshi yace amana🤔? Amma afili sai ya d'aga kai Abba yakaraji yaran ya birgeshi yace Allah yabaku aman lafiya, Najib cikin murna yace Amin. Salma na tsugunne tana alwala dan baccine ya d'auketa sai da aka tasheta, jin busa a waje da kid'an kalangu yasa mutanen gidan suka shiga sa mayafi suna fita kallo, salma kam abin dake faruwa a gidan sam haushi yake bata, da gudu taga mutane sun shigo suna guda sun tsaya akanta, takarasa d'auraye kafa ta d'ago jitai sunce Alhamdulila an d'aura auran *SALMAH DA SALMAN* jitai gabanta ya yenke ya fad'I cikin rawar murya tace ma naau gud'ar kud'an matsa in wuce, jitai an rungumeta idanta ta rufe kwalla ta zubo mata Asabe tace Alhamdulila salma naji dadi, Allah yakareki daga sharrin makiya. Ahankali hawaye suka shiga zubo mata ta d'aure tace Aunty sallah zanyi, Asabe tace muje in kaiki nan gida ya kara kaurewa da murna zee ma ta iso, sai dai ganin kawarta a wannan hali yasa jikinta yai sanyi. Wajen karfe 6 na yamma Asabe da goggo sun zauna sai gyara amarya sukeyi, dakyar suka lalabata tai shiru har zee tasamu damar yi mata kwalliya, motocin d'aukar amarya suna waje, dan wasu yan zumudin harsun shige. Lifaya ce aka nad'a mata wacce Matar mustafa dakanta ta siyo mata mai tsadar gaske tayi kyau sosai acikin orange din lifayar, ga zee ta mata kwalliya, tasha sarka da d'ankunne silver hakama takalmin kafarta. Sai kamshin humra da turaren wuta takeyi. Bayan sun gamane suka kaita d'akin Abba Tana zaune kusa dashi, Abba yace salma? Tace naam yace kiyi hakuri kinji? Tace Abba kadaina bani hakuri, yace naga salman a gaskiya ya kwantamin tai murmushin yake yace kuje mutane na jira gashi naji ance jarfe 8 akwaI abinda za'ayi acan tace umm... Nan suka mike ta kalli umma datai kasa dakai, kusa da ita taje tare da cewa Umma natafi d'agowa umma tai idanta yai jaa tace Allah yabada zaman lafiya salma bata amsa ba tai waje da sauri jin kuka zai kubce mata. Zee ce a gefenta sai Asabe dake kusa da ita sunzo fita kofa salma tasa kai shima yasa kai aikam suka gwari juna, zee tace sannu sannan ta d'ago tace malam la.......cikin wata irin murya salma taji ance mekuke nufi da nad'e mata kai? Dasauri ta yaye mayafin da aka rufeta tad'ago jikinta ne yashiga rawa ahankali tafara ja da baya tana girgiza kai wasu hawayen bakin ciki na zubo mata. Asabe ta d'aure tace meye hakan kuma? Tafad'a tana kallan mai maganar? Yace Aunty ni... Asabe ta katseshi bamu hanya nace? Yace Aunty.. Takara katseshi tace ka bamu hanya ko? Ahankali ya matsa idanshi taf kwalla Asabe ta fizgo hannun salma da karfi tafara janta sun zo fita kawai ya kama d'ayan hannun salma yace salma haka alkawari yace? Dama akwai ranar dazaki wuce gidan wani namiji bani ba? Takalleshi a zabure hawaye yakeyi shima runtse idanta tai dakarfe batasan sanda kuka ya kufce mata ba, yace isowata kenan ko gidan banjeba nace dan taxi yakawoni infara ganinki amma me? Sai infara ganin motoci, sannan in ganki kinfito da sufar amarya wacce za'a kai gidan wani? Salma mekeke shirin aikatawa rayuwar mu? Girgiza kai kawai take cikin matsanancin kuka tace Yaya *KAMAL* na shiga uku........yaxanyi? Asabe kam da sauri ta juya tai d'akin Abba dan sanar me. Kamal yakaraso da sauri ya rungumeta kuka take sosai yace salma bazai yiwu ba, u are mine, muje gunsu Abban susan yanda......jin muryar mustafa sukai cikin zafin rai yace wani irin sabon iskanci ne wannan kamal😡? Dasauri salma ta janye jikinta, ya cigaba baka da hankaline? Matar wani kake rungumewa? Kamal yace Dady wai me kake fad'a haka? Yaza'ayi salma tazama matar wani bayan ni?dai_dai nan su Abba da goggo da Asabe suka karaso gun, mustafa yace bayan kai? Kai wa? Cike da mamaki kamal yakalli dadynsa zaiyi magana mustafa ya katse shi dacewa, kad'auka mudun shashashu ne? Tun yaushe ka gama karatu? Kamal yakalli salma sannan ya kalli Abban salma ya maida idanshi kan dady yace dady amma...... Mustafa yace banasan iskancin banza, dan kaga yarinya nasanka shine kadinga raina mata hankali daga kace saura 3wks ku gama sai ka kara cemata 2wks itakuma saboda shirme da yarda dakai yasa take d'auka, to bari kaji nasani sarai kafi 8month dagama makaranta dan wa'inda kwankwaso ya biya muku tare tuni suka dawo, ko sai kai kad'ane karage? Kamal yakalli salma zaiyi magana, tsugunawa tai da sauri tace wayyo ni😭 Mustafa yakalleta sannan yakalli Abba yace Amadu dagata dakanka ka kaita mota dan 'yan daukarta sun gaji da jira yakalli kamal sannan yace to yaya, tare da karasowa ya d'agata. Idanta ya rufe da kuka kawai sa kafa takeyi, dasauri kamal ya karaso kusa da ita yai kneel down yace salma please😥 mustafa yace Amadu ku wuce nace, cikin sanyin jiki da tausayin kamal Abba ya wuce da salma mota. Motocine guda 20 tata tana tsakiya nan akasata mutane harda makota ganin motar bilis yasa suka shiga😜. Salma kam zaune take a cikin mota tai kasa dakai banda kuka ba abinda takeyi zee ma kukan take dan tasan yanda salma kesan kamal, Asabe kam rungume salma tai tafara lallashi sai dai kamar zigata take. Sun isa gidan sarki salma batamasan ina sukeyi ba tadai ji sun yi parking. 'Yan uwa na gidan sarki sun fito taryarsu, nan aka yan Rakiyar bangaren salma, ita kuma su zainab suka riketa sukai bangaren fulani da ita, zee da Asabe na biye dasu. Sai da suka kaita duka bangaren matan sannan suka maidata bangarenta, yan rakiya sun rikice da kallo ganin irin dukiyar da aka zuba a bangaren, falone kato da kofofi uku, d'aya daki ne a cikinsa da bandaki a d'akin nan ne master bedroom, sai kuma dayar kofar da kuma daki ne da toilet aciki, sai d'ayan kitchen ne kato duk da bawani girki sukeyi ba amma anyishi ko akwai abinda zaisa ai girki aciki. Baban dakin aka kaita tanaji mutane nata wasa kayan gidan amma ita ko kallan dakin ma batai ba bare, hawaye sai gudu suke a fuskarta, wata baiwa ce ta shigo tace wai ance duk ku fito za'a wuce, sukace amarya bata shirya ba ai, baiwar tace eh ita yanzu za'a shirya ta zasu taho dashi. Nan suka fara fita, akabar salma ita kad'ai, kifa kanta tai tana kuka yanzu shikenan an rabata da yaya kamal? Wacce irin rayuwa zatai?jin sallama tai dasauri ta zauna tare da gyara mayafinta zeena ce da wasu mutane guda 2, zeena ta yaye mata mayafi aranta tace masha Allah sannan tace salma yanaga idanki a haka? Wani irin kuka kikai haka? Salma ta kakaro murmushi tare dayin kasa dakai. wata daga cikin matan tace hb Amarya yanzu ai an daina irin wannan kukan, zeena ta kalli d'ayar tace Meema Yaza'ayi? Tace gata so cute I wish bata b'ata fuskarta haka ba amma ba matsala zeena tace tnx. 1 Nan meema ta matso ta yaye ma salma mayafin gaba daya ta zare d'ankwalin kanta, itakanta zeena sai datai mamakin gashin kanta, ahankali meema tashiga yima salma kwalliya sun d'au lokaci kafin su gama sai dai me? Duk wanda yaga salma to ba karya sai ya kara kallanta tayi kyau na garari.... Zeena ta shiga fasama meema kai, nan suka d'auko wani ratsatsen kaya wanda kyansa ya wuce tunanin mutum, dark blue ne sai kwalliyar jikinta da akai da golden rigar doguwa ce, ta baya jan kasa takeyi, nan aka d'aura mata gwagwaronta dark blue sannan aka yafa mata wani shara_sharan net golden, aka miko mata takalmi mai d'an tsini golden. Salma tayi kyau na karshe sai dai bata farin ciki sam. Zeena tace kai Amaryarmu karfa kisa kanina ya fad'I garin kallanki nan sukai murmushi salma kam ta juya kai. Nan suka ce mu mun wuce yanzu salman Zai zo ku tafi, nan suka fita suna murmushi. Salma na zaune tana tunanin rayuwa ita dake tunanin auranta da kamal sai gata a gidan wani can da bata sani ba, sannan tace a fili wai ahaka suke nufi zanje? Da wannan net din? Tasaki tsaki daidai nan salman yashigo ko salama baiba dan duk ranshi a b'ace yake da akace wai shi zaizo ya d'auketa. A bakin kofa yatsaya yace ke! Salma taki d'agowa yakaracewa ke! Takara kim d'agowa haushi ya isheshi yakaraso kusa da ita tana kallan kafarsa na tahowa duk da a tsorace take amma bazata yarda yace mata ke ba jitai ansa sanda a tabo mata kafad'a da mamaki tad'ago dan ganin wannan rainin hankalin. *tofah*🙄 Nan idanun ma'auratan ya hadu cikin tsananin mamaki mara misaltuwa salma ta mike tace *YOU?* salman yakalleta ba laifi kyanta ya wuce misali sai dai kamar yasanta, jikin salma ya shiga bari? Tad'aure tace me kake anan Prince? Yace oh kinsani dama? Tace ohhh baka ganeni ba? Wace ka cima mutunci a Buk? Me kazoyi nan? Ko nan din ma biyoni kai? Salman yai wata dariya mai karfi wacce tasa zuciyar salma tagama tsinkewa, sai daya gama sannan yace *SALMA*? Da mamaki ta kalleshi tace eh meye? Yakara dariya sannan kuma ya hade rai kamar zaki yace kina nufin kece matar? Ta kalleshi batare data amsa ba yace yar gidan Amadu u are really something, wato sai da kikasan yanda kikai kika aureni ko? Sai dai kuma I really pity you dan tun daga yau zaki fara regretting yar gidan masu gini. Salma tunda taji yace wai auranshi jikinta yafara rawa, zama tai a gadon dabas tace kai ne mijin😳? Yace ke banasan pretending din banza, zatai magana ringing din wayarshi ya katseta yad'aga. Najib ne yace to ango wato anga mata shine aka ahanyani a mota ko? Salman yakalli salma yace u will be really surprise inka ganta, najib yace to please kazo mutafI yaya zainab sai waya take, salman yace ok gamunan. Salma yakalla yace ke taso muje tace amma....ya katseta banasan wani munafirci taso muje, tace munafirci kuma? Yashareta tace wai da wannan mayafin zani? Yai tsaki yace ke bansan iskanci inkinga dama ki fito, yanakai nan yafara tafiya, itama tsakin tai tare da binshi, ya kalleta kawai yai kwafa yaga alama sai ya mata service😜😜😜😜

Post a Comment for "NI DA PRINCE CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...