Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NI DA PRINCE CHAPTER 3

NI DA PRINCE CHAPTER 3

- - Post a Comment
NI DA PRINCE CHAPTER 3
Salma kwance akan gado sam ta kasa barci sai juyi take rashin mutuncin da prince ya mata ne ke dawowa kwakwalwarta dasauri ta mike zaune tare dayin kwafa tace a fili yaron nan da ace nasanshi dasai na rama rashin mutuncin dayamin😠wata zuciyar tace kinsan shi mana sai dai in tsoro kike😀, dasauri ta tashi tsaye tace tsoro? Nidin? Inji tsoron wannan banzan? Alla ya sauwake🤔, haka tai ta shirme a d'aki sai 12 tasamu tai bacci. + Waziri ne zaune agaban sarki yace ranka ya dade daga gun malam nake anyi istihara akan al'amarin nan ba shakka wannan auran alheri zai jawoma salman mai yawa, sannan maganar yarinyar kawai dai 'yar talakace amma halinta kaf 'yan unguwar sun shaida kyan halinta. Sarki yai shiru can yai murmushi yace Alhamdulila, waziri yace ga kyau dan 'yan unguwar sunce kyanta dayanda maza ke binta yasa take saka nikaf, sarki yace naji dadin binciken nan zancen talauci kuma ai ba wanI abu bane da talaka da mai kud'I duk daya suke agun Allah. Waziri ya kara tsugunawa yace Allah yajada ran mai martaba, yanzu insanar dashi?sarki yace a'a kasan halin salman taurin kai, kafiya in har yaji to da matsala, waziri yace ai halinku d'aya ranka ya dade yafad'a yana murmushi, sarki yai gyaran murya hakan yasa waziri yace tuba nake ranka ya dade. Sarki yace yanzu kuje kai da yayana kusamu mahaufinta kuji ko an mata miji, waziri yace bamu zamu kirashi ba? Sarki yace a'a ai mu muke nema, waziri yace angama rnka ya dade yafad'a tare da mikewa. Sarki yai murmushi shi kanshi yakosa yaga salman ya nutsu, haka kawai yakejin farin cikin zancen auran nan. Waziri yasa asanar da Amadu zasu shigo da yamma, duk da Abba baisan meke faruwa ba jin ance wai wani mutumi kesan ganinsa akan wata muhimmiyar magana, haka kawai Abba yasamu kanshi da fad'awa d'an aikin in ba damuwa su hadu a sharad'a inda yayansa yake cike da mamaki d'an aiken yace ba damuwa. Nan Abba ya koma gida yaI wanka yasa manyan kaya, umma takalleshi tace meke faruwa? Yace nikaina bansani ba amma kibari inje indawo nikainan bansan menene ba kawai dai naji dan aiken yace mutumin kamar yanada hadi da gidan sarauta, tai shiru tace to Allah yasa alkairi ne yace Ameen Basira bata dawoba? Tace eh yace salma fa? Najita shiru, umma takauda kai tace inazan sani? Yai tsaki yace sai kiyi tayi ai hakan jiya 'yarnan fuskarta duk ta canza amma wai bakisan menene ba? Yai waje cikin fishi. Dakin salma ya shiga tana zaune rike da hoton yaya kamal tanajin salamar Abba tai saurin boye hoton yakalleta cike da tausayi yace zan fita tace to Abba d'aurin aure? Yacs a'a tace adawo lafiya yacs amin tare dayin waje, yana tausayinta sosai dan jiya ya duba yaga adadin kiran datama kamal amma bai kira ba shikam dan dai bayanda zaiyi ne amma shikanshi yanaso 'yarsa tai aure. Yayan Amadu wato Mustapha jin sakon kaninsa yasa aka gyara falon baki tare da siyo lemuka, bayan Amadu ya isone bada dade wa ba kira ta shigo wayar Amadu ya amsa jiyai ance bakin dazasu zone muna sharada gidan wa zamuce? Nan Amadu yashiga kwatanta musu har suka gane. Su Amadu na zaune da yayansa suna hira suka dingajin hayaniya a waje cikin mamaki mustapha ya mike ya fito Amadu na bayanshi. Mamakine yakamasu ganin motoci guda 6 sun jeru a kofar gidansa ga fadawa a tsatsaye Mustapha yace hala wani taro nasarauta za'ayi Amadu yace ko kuma hawa ba? Naga in gidan sarauta zasuyi aure suna hawa, nan sukai murmushi tare da juyawa ji sukai ance banan ne gidan Mustafa ba yayan Amadu? Atare suka juyo suka kalli bafaden dayai maganar, Amadu yadaure yace nan amma meke faruwa? Ahankali aka bude motoci biyun tsakiya kowace waziri da yayan sarki Modibo suka fito. Mustafa da Amadu sukai kuri suna kallo ga kutane sun cika gun, jisukai wani bafade yace a waje zaku barsu? Dasauri Mustafa yace ahhhh ku ku shigo. Waziri da Modibo suka nufi gidan shikam Amadu jiyai kamar yayi mutuwar tsaye tunaninsa d'aya laifi yayi kawai. Sun zauna su kuma su Abba sun tsugunna suna kwasar gaisuwa,modibo yaI murmushi yace haka ake neman aure a tsugunne? Cikin sauri mustafa da Amadu suka d'ago ido? Tare da kallan juna sukace aure?Waziri yace kuzauna mana, nan suka zame suka zauna, modibo yace muna namawa Salman d'an gidan sarki auren 'yarku salma, cikin kidima Abba yace eye? Waziri yace eh muna neman alfarma, sai dai in kun mata miji to fa wannan ba yanda zamuyi, Abba yai shiru zufa tashiga keto mai, yakali mustafa shima zufar yake, Abba yadaure yace salma? Waziri yace ita fa, Abba yace ku gafarceni ranku ya dade amma....dasauri mustafa ya katseshi yace mun baku indai Salma ce😬 waziri yace amma kuwa muna godiya, yace a'a ai mune da godiya, Modibo yace to *Alhamdulila* munji dadi sosai sai dai munada magana, Nan su Abba suka d'ago, Modibo yacee bamasan auran ya wuce wata d'aya Abba yace wata 1? Waziri yace eh sannan munaso ku taimakemu karku mata komai nakayan d'aki mustafa yace amma ina ake haka? Modibo yace wannan gudumawar sarkine na amsawa dakukai zaku bamu 'yarku, mustafa yace toh😳. Nan modibo ya ciro bandir din dubo d'aya guda 3 ya ajiye yace wannan kudin mun gani muna so ne kenan kudin gaisuwa cike da tsoro Abba yakalli kudin zaiyi magana mustafa yarigashi yace mun gode amma kudin nan yayi yawa, guda d'aya zamu d'auka sannan inkun tsaida ranar auran sai a turo afad'amin nan sukaita godiya suka mike. Abba ya zube a gun yace yaya yazamuyi da kamal? Mustafa yace kamal basan auran salma yake ba tunda haryakai wannan lokacin batare daya dawo ba bayan nasan yagama karatu, Abba yace salma fa? Datake tsananin sansa? Yace intai aure zataso mijinta kasan zuciyar mace ai. Abba tare suka taho da mustafa dakuma matarsa, salma na kwance a kasa inda tai sallah batasan sanda bacci ya dauketa ba. + Mafarki take mai dadi, wai gata rike da hannun wani sai dai bataga fuskarshi ba sun je bakin ruwa sun zauna, yasa hannunsa a kafad'arta tare da kwantar da kanta a jikin kafad'arsa murmushi take sosai, tareda jin wani sanyin shaukin kauna na ratsata, a cikin bacci taji anacewa ke! Ke firgigit ta mike tare da kallan umma dake tsaye akanta, umma tace tashi ku gaisa da baffanki tace to tare da mikewa. A falo tagansu ta gaishesu suka amsa cikin farin ciki mustafa yakaleta yace salma inaso kisan duk abinda yafaru dake to ba shakka mukaddarine sannan mahaifinki dani masu sanki ne bazamu yanke hukunci akan abinda mukasan bazai taimakeki ba tace hakane baffa, Abba yace ungo nan ya mika mata d'ari 500 yace kije kisiyoma baffanki lemon fata da ayaba tace to tare da fita, taxo fita taga goggo tadawo nan tagaisheta ta wuce. Haka ta tafi tana murmushi haka kawai tunda tai mafarki takejin farinciki. Can bakin titi taje tana tafe cikin nikaf tana murmushi. Mustafa shi dakanshi yazaunar da umma da goggo da matarshi dake ciki time din batasan meke faruwa ba ya musu bayanin halin da'ake ciki, Goggo kam tayi murna ta kuma yi bakinciki. Tana murna salma zatai aure sai dai tana kishin auran d'an sarkin dazatai sai dai yaxatayi? Tunda batada 'da. Hafsa matar mustafa tace amma kamal.....dasauri mustafa ya katseta yace inhar kamal yadamu da salma da tuni ya dawo sannan daya dinga nemanta ta hanyoyi daban daban amma ina sane baya nemanta, umma kam batace komai ba. Abba yace kada kowa yafad'ama salma halin da ake ciki yanzu harsai bikin yazo kusa gudun kar sanda takema kamal yaja mata matsala sukace to. Salma tadawo gida tawuce d'aki tare da d'aukan hoton kamal tace yaya inaji ajikina munkusa fara rayuwa tare ganin irin mafarkin danai. Nace toh fa🤔 anya kuwa?. 4 Fulani dakanta ta kira Zainab da Zeena 'ya'yanta manya masu aure kuma sune kesan salman nagaskiya, nan ta sanar dazu umarnin sarki na lefem salman da zasu hado, murna sosak sukai, fulank tace sai dai yarinyar yar talakawa ce dan haka kusan irin kayan dazaku hado? Cike da mamaki zeena tace bangane ba? Dan zai auri talaka sai akace ita ba mutum bace? Zainab tace mudai zamuyi abinda muka saba, fulani tace kukuka sani😠 sannan ance kar wanda yama salman zancen auran. Zainab tace bangane ba?baya santa ne ko me? Tace nidai nafad'a muku umarnin mahaifinku ne. Suka kalli juna cikin mamaki. Shirye shiryen biki ake sosai agidan sarki an tsaida lokaci nan da 3weeks, salman kam yafahimci akwai shirin biki da ake a gidan sai dai ganin ba wanda yamai maganar yasa shima ya basar ya nuna baisan me sukeyi ba. Haka gidansu salma ita ba makaranta take zuwa ba sai dai itakanta batasan shiga da fitar da ake a gidan ba gashi kullum goggo sai ta kawo mata abu a kofi tace tasha intai magana sai tace bayam inakallan yanda kikeyi da jiki gabadaya shawara da basir sun kamaki, shiyasa ko makaranta bakya iya zuwa tace hmmm. Yau saura sati 1 biki haka kuma yau ne sarki ya kira salman da daddare suka zauna a turakarsa, sunyi shiru na wasu lokutan sannan sarki ya nisa yace salman menene matsayina agunka? Salman ya d'ago da mamaki yace Abba yazaka tambayi 'da matsayin uba a gareshi? yacigaba Abba bani da kamarka aduniya, sarki yai shiru can yace nasani salman sai dai inasan intunatar dakaine yanda kakejin matsayin na agunka nima haka nakejin matsayinka aguna. Salman yai kasa dakai idansa ya kad'a yai jaa, Sarki yacigaba salman na maka mata ina fatan kuma zakamin biyaya a matsayina na wanda bakada kamarsa, cikin kid'ima salman yad'ago ya kalli sarki yace Abba mekake nufi da mata? Sarki yace eh salman wannan shine my first and last request to u a matsayina na mahaifinka, salman bakinsa yashiha rawa kanshi yafara zafi samun kanshi yai dacewa bakomai Abba, sarki ya saki murmushi yace nasank sarai bazaka bani kunya ba. Salman yai kasa dakai, sarki yace gobe ka shirya Mannir ya rakaka yace a'a nikadai zani, sarki yace a'a ko ishaq to kad'auka yacd zanduba, harya mike sarki yace nan da kwana 6 za'a d'aura auren ragowar sha'anin biki sai ta tare za'ayi tunda ba hali garesu ba, haushi yakamashi talakace ma kenan? yace da wuri haka? Abba yace mezamu jira salman? Kannanka fa sunyi aure yai murmushin yake tare da mikewa. Salma kam tanata sharar dakuna dan yau tun safe 'yan gidan suka tafi gidan baffanta, tagama da d'akuna tashiga falon Abba ta share sannan tad'auko tsinma ta fara goge_goge tazo goge gun tv taga invitation Cike da mamaki tad'aga dan ganin auran wa za'ayi? Mamaki ya kamata ganin sunanta daro_daro wai ana gayyatar walimar bikinta ranar juma'a da misalin karfe 4, takalla dakyau basunan namiji, tace mekenan? Badai yaya kamal bane zai dawo akaki fad'amin😬.1 Jitai ana kwamkwasa kofa tafi to dasauri makocinsu ne tagaidashi yace babankine yakirani wai inkawo miki waya zai kira tace to. Basu dadeba Abba yakira tad'aga yace salmah kiyi hakuri naso in nadawo nafad'amiki wata muhimmiyar magana sai dai I am too late, tace na me fa? Abba yace ki shirya zakiyi bako sannan dan Allah inhar kinsan darajata karki wulakantamin bako, da mamaki tace to amma bakon guna zaizo? Yace eh ki tambatar kin shirya sannan karki manta karki wulakantashi indai......ta katseshi da sauri to Abba naji😊. Yace kin yarda dani aiko? Tace in banyarda da Abba na ba dawa zan yarda yace good dan haka kitaimakeni karnaji kunya nida yayana tace Abba karka damu, nan sukai sallama..... Wanka salma ta shiga bayan tagama komai ta shirya cikin less d'inta na sallah haka kawai ta kosa taga bakon da Abbanta yake magana. + Salman ma ya shirya cikin kayansu na sarauta shida bawanshi suka fito dakuma driver, su biyu suna gaba shikuma yana baya rike da waya yana dane_dane, sam bai kula da inda suke shigaba dan driver dashi akazo ganin gidan tun farkon zancen auran, salman jin ana jugub_jugub a mota yasa ya dago kai, cikim tsananin mamaki yake kallan dan lokon da suke shiga, cike da mamaki ya kalli driver nasa yasa mamman ina kake kaini? Yace yalab'ai kayi hakuri mun kusa zuwa, cikin b'acin rai yace Mun kusa zuwa ina😡? Mamman yace gidan matar taka, salman da sauri ya juya baya tacikin glass yana kara kallan unguwar yace anan unguwar take? Yace eh tare dayin parking awani karamin gida salman yace me kenan? Yace an iso ga gidan nan, ya nuna wani karamin gida mai kofa karama salman yashiga yin wata dariya mai karfi, wanda hakan yasa suka razana bawan yace Ranka ya dade menene?salman yace bakuda hankali ne kuka kawoni nan? Mamman yace yallabai ai.....da karfi salman ya katsesu yace kuyi gaggawar fitar dani daga unguwarnan kafin kwalara takamani, mamman yace yallabai bakaga matar taka ba ai, yace wace mata kuma? Nace ku fita dani ko? Bawan yace to yallabai amma bari in ajiye mata sakon da sarki yabada yace aikin banza, ka fita ka kaimata inyaso ka taho daga baya yace yahkri yallabai ajiyewa kawai zanyi intaho yace komadai meye to kayi saurin dawowa inka wuce minti 5 tafiya zamuyi dasauri yace to yallabai. Boot din motar ya bude ya dauko manyan jakukuna guda 3 ya nufi gidan ya kwankwasa ciki sauri salma ta bude, sanye take da hijab amma batasa nikaf ba, kallanta tare da sakin baki, tadaure ganin kayan fadawa ajikinsa tace sannu? cikin in_in na yacs yauwa dan Allah hajiya salma nanan? Tadan kalleshi da mamaki tace nice salma tafad'a tare da nuna kanta, yace hmm gashi ance inkawo miki tace ni kuma? Yace eh kiyi hakuri ya shirya zuwa kuma sai wani uzuri yataso mai, tace wafa🤔?Zaiyi magana yaji anmai horn dasauri yajuya yace eh, tabishi da kallo tare da cewa shine bakon Abban? Sai kuma ta d'an daga kafada tare da kallan waje can taga motar ta kulle tad'au jakukunan ta shiga ciki tare da ajiyewa a falon Abba takoma d'aki ta kwanta, tunani take me katin bikin nan yake nufi? Bafaden kam na shiga mota yai ajiyar zuciya tare da cewa kai yallabai kayi sa'a wannan ita kad'ai ma kyanta ai ya isa ka wuni kana kallanta, salman ko kallanshi bai ba asari ma ranshi ne yakara b'aci. Sanda yana yaro mahaifiyarsa ta rasu, matan babansa basanshi sukeba haka 'yan uwansa, sannan yanzu matar dazai aurama maimakon abarshi yasamu wacce zataso shi shima yasota amma sai abashi auran kara buta? Lalai zai d'au mataki bayan auran nan. Salma kam duk abin duniya ya dameta tanajin motsin Abba ta mike da sauri taje ta gaidashi ya amsa tare da cewa kinga bakon? Tace eh wani bafadene yace wanda zaizo din wani uzuri ya hanashi zuwa, Abba yace toh😳? Yaza'ai haka? Tace gashi wanda yazo ya ajiye, Abba yace toh da alama uzurin mai karfine tunda ansanar dani ya fito daga gida, salma tace Abba katin can kamar na biki, Abba yace salma matso nan ta matso kusa dashi tana murmushi yace ki nutsu zan fad'a miki wata magana mai tace to Abba. Yace dani da yayana mun yanke hukunci yi miki aure tad'ago da mamaki tace aure kuma? Yace nasanki salma yarinyace mai biyayya kadaki bani kunya, idanta ya ciko da kwalla tace Abba yaya kamal fa? Yace salma kibar zancen kamal dan mahaifinshine yafara ansar maganar auran, tai shiru zuciyarta sai bigawa take, yace wannan juma'ar za'ayi yini da d'aurin aure da daddare akaiki saidai bansan koda wani abu dazakuyi keda kawayenki ba, tace Abba juma'a?yace eh salma kada ki manta ni mahaifin kene bazan tabayin abinda zai cutar dake ba sannan inaji ajikina auran nan alheri ne. Hawaye take sosai yace salma Allah yamiki albarka ta runtse idanta da karfi meke shirin faruwa da ita? Mafarkin datai dama na rabuwa da kamal ne?😭😭. Abba yace bazaki tambayi sunan mijin ba? Tace basai naji ba Abba tunda kun amince dashi ai shikenan yai murmushi tausayinta yakeji sosai. Mikewa tai tashiga d'aki ta hau kuka, umma najinta amma batako shigo dakin ba ga batare suka dawo da goggo ba ta dawo ba. Yau laraba gida ya fara cika salma kam na kwance ba lafiya sai dai hakan baisa an daina hidima ba, tun safe aka kwashi 'yan uwan umma da Abba suka tafi gidan mustafa acan za'a anshi lefe.

Post a Comment for "NI DA PRINCE CHAPTER 3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...