Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NI DA PRINCE CHAPTER 10

NI DA PRINCE CHAPTER 10

- - Post a Comment
NI DA PRINCE CHAPTER 10
Duk shiru sukai ad'akin ishaq ya mike a zuciye zai fita, salman ya kalleshi yace yaya ishaq sai ina? Ya juyo a zuciye yace duk inda zani sai na sanar dakai? Salman yai murmushi yace maida wukar yaya adawo lafiya, fulani ta cije lebe inama d'anta ne haka? Amma tana bakincikin yanda salman ya ninka d'anta komai.+ Salma ce tai kasa dakai tace fulani ayi hakuri abunda yafaru rannan munyi kuskure😞 tafad'a tare dayin kasa dakai, salman ya maka mata harara ta gefen ido amma a bayyane sai yace umma kinji hakuri take badawa bayan ninai laifin, fulanI aranta tace wato kana nufin kai kafi karfin bada hakuri kenan? Salman ya kalleta yasan metake tunani amma a fili yace umma bari mu wuce ina tunanin zamu d'an fita akwai inda zata rakani, yafad'a yana murmushi, sannan ya kalli salma yace muje dear😉 salma ta d'ago aranta tace dear😒? Mikewa tai salman yace umma yau nasanar dake ko? Fulani bakin ciki ne ke neman kasheta amma tad'aure kamar tai kuka ta saki yake tace eh mana, salman ya kalli salma yamata alama dakai muje, salma tafara tafiya jikinta yai sanyi, itakanta tasan bakaken maganganu salman ke fad'a amma ita ta d'auka bakar magana rai abace akeyinta?. 1 Suna Shiga d'aki takalleshi tace dagaske gun Abba zamu😬? Ya hade rai yace saki nai? Tace mene? Yace hakurin da kika bada mana🙄, saki nai? Tace hm ganinai kamar.....yakatseta karki sake banaso, tace amma ai....yace zaki fara ko? Ke ba'a isa ace kaza kice to bako? Salma ta turo baki tace to, salman ya matso yaja leben ta da karfi, ai kuwa ta fara shure_shure, ya saketa tasa kara tace da zafi fa😢tafad'a cikin shagwaba, salman yai dariya yace in ba zafi mezaisa inja? Tace ni wlh ban yarda ba☹ya juya baya yace shikenan in baki yarda ba sai mufasa zuwa gun Abban, dasauri ta dawo gabanshi tace a'a na yarda sosai ma😬 murmushi yai tare dasa hannu ya dungure mata kai yace sai ki fito. Ya juya yai waje, tsayuwa tai a gun tare da daga gun da zuciyarta take, jitai tana harbawa tacw wayyo ni! Yaya ka....dasauri ta toshe bakinta tare da girgiza kai, fuskarta tad'an gyara ta yafa mayafi ta fito. A mota tasami salman tashiga tare da murmushi salman ya hade rai yace da ai nafara tunanin fasa zuwa, dasauri takalleshi tace na'am😱? Yatada mota tare da cewa ina nufin da baki fito ba nan da 5min😏, salma tace ahhh ya fara tafiya, tace hmm yauwa kaga kud'in rannan a jakata sam namanta ban baka ba, tafad'a tana mikowa, hannu yasa ya dunkule hannunta da kud'in yace keep it, salma kam tai sororo jinyanda ya rike hannunta. Shikanshi wani abune ke ratsashi da sauri ya saketa, sai dai salma tana rike da kud'in kuma bata d'auke hannunta ba, akasarima batasan yad'auke hannunsa ba, juyawa yai yakalleta a yanda ya barta, hanni yasa a kafadarta yace menene? Dasauri tai firgigit tadaure tace bakomai tunanin Abba nake. Salman yace karki damu zai warke, kallanshi tai tad'an karkatar dakai aranta tace yaxanyi? In nikad'ai nafara sansa? Tasani sarai ita bata iya so ba. A wani karamin mall ya tsaya ya fita, yana fita salma taji karar waya, wayarta ta duba taga ba ita bace ahankali ta kalli wayar salman, tace oh ankirashi gashi bayannan, tafad'a tare da kallan wayar, number ce, harta kai hannunta zata d'aga tai saurin girgiza kai tace ba ruwana😕. Salman na dawowa tace mai ankiraka yace wa? Tace number, yace ok, yace bazaka kiraba? Ya kalleta yace 4get, ta tabe baki tace nima haka zai dingamin in na kira baya kusa? Batasan afili tafad'a ba jitai yace in kin kira sau d'aya bazan kiraki ba amma in sau uku kika kira bana kusa I promise to call u back. Haushi ya kamata wato sai ma tayi sau uku?tace au in sau d'aya nakira bazaka kira ba? Yace yes saboda inkika kira sau d'aya ai abun ba important bane kenan, salma tadafa kanta aranta tace na shiga uku ni salma🤔. Asibiti suka sauka ahankali suka karasa d'akin Abba, kamal na ganinta yashiga washe baki, sai dai yau salma murmushi kawai tamai tad'auke idanunta, sun gaisa da Abba, nan Abba yasakema salman godiya yace kaganmu ashirye sallama za'a bamu yanzu, salman yace Abba baka gama warkewa ba wacce sallama? Abba yace kayya ai nikam yau gida zani, goggo tace ai fa yadage sai hakuri, salman yace shikenan bari in anso sallamar sai in kaiku gida. Sunzo shiga mota salman ya kalli kamal yace kai sai ka biyomin ko a mashin ne dan gun bazai ishemu ba ko? Kamal ya harareshi yace sai ka fad'a😠nan suka shiga mota sukai gida.1 Tunda suka iso unguwar salman ke kallan unguwar tausayi duk ya kamashi, yanzu anan salma take? Amma ya hanata karatu a skul? Dasuka iso gidan jikinsa duk yai sanyi ya daure ya ajiyesu ya kalli salma yace ana la'asar zanzo tai murmushi tace to zan kula da wayata😊 yanda inka taho sai ka kirani yace to, harta juya ta dawo tace sai na ganka😊 yace hmm sai kin ganni😊 wani murmushi sukama juna yad'ago zaiyi magana aka sake kiranshi, tace bye tare dayin ciki shikuma yabita da kallo tare da d'aga wayar yasa a kunne. Jiyai ance yayana is me? Cikin kid'ima da rudewa yace what? Aka kara cewa haba yayana ai sai in fishi in kace baka ganeni ba, Ur Farha ce, salman yace what? Farha? Tai murmushi tace naji kunya yayana dabaka d'au muryata ba☹anyway gani a airport kainake jira😊 tana gama fad'ar haka ta katse layin. Salman ciki kid'ima yai hanyar airport gudu kawai yakeyi, yana isa ya shiga kiran farha a gigice sai dayai kira 2 ana ukun tad'aga tace yayana har nayi fishi, salman yace farha? Dariya tai tace yayana kana ina? Nan ya mata kwatance. + Sanye take da riga da wando na 'yan kanti, sai dai rigar takai gwiwa, tayane kanta da bakin mayafi karami, jakar dake jikinta irin doguwarnan ce itama black sai takalmi flat akafarta black,tana jan trolley d'Inta. Karasowa tai inda salman yamata kwatance, daga d'an nesa ta hangoshi tasaki murmushi tare da karasowa, sai datazo daf dashi ta ajiye trolley d'in tayi d'age tasa hannu ta rufemai ido, salman yai ajiyar zuciya tare da zare hannun ya juyo a sukwane, tofa kallon juna suka shiga yi, farha ta rufe idanta tace yaya wannan kallon fa? Salman yai gyaran murya yace farha? Kece? Dama zan ganki? Ta turo baki tace ba wani nan bayan kamanta dani?☹ tai maganar cikin shagwaba, salman yace wasa kike kema kinsan I can't, tace nasani yayana kaima kasani ai ko? Tafad'a tana kallansa, yai murmushi yace ina nasani ko mazan paris sun mantar dake ni🤔. Tace su sun isa? Yace waya sani, atare sukai dariya yace muje mota ko? Ta kalli akwatinta sannan ta kalleshi, yace hmm badai ni akeson ind'au jakar ba? Tace yayana nifa mace ce☹kallanta yai ya wucewarsa mota, takalleshi tare da jan jakarta tace har yanzu dai halin nanan. A baya tasa jakar sannan ta bude gaba ta shiga, farha ta kalleshi tace yayana how many years?yace hmm 4 ko? Tace ahh gaskiya mun dade ko? Yai murmushi yace sosai ma, hannu tasa takamo nashi tace yaya kasan meyasa nazo? Ya kalleta yace a'a, tace yaya jinai inban gankaba akwanakin nan kila mutuwa zanyi😪 salman yace haba farha meyasa kike fad'an haka? Tace yaya bakasan yanda nakeji ba, gashi narasa dalili dana ma mum maganar zuwa hanani tai, yace y? Yace cemin tai wai ko kayi aure😄ta d'auka zan yanda in hakura da zuwa, salman ya kalleta yace gaskiya tafad'a farha, cikin tsananin mamaki tace what?me kake nufi da hakan? Bai bata amsa ba yaja motar yace gida ko? Tace eh amma....ganin ya d'auke kai yasa kawai tasa kuka, daurewa kawai yake dan sam bayasan kuka, ganin yanda take shesheka yasa kawai yai parking ya kalleta yace farha?dasauri ta matso ta rungumeshi, janyeta yad'anyi sannan ya miko mata tissue yace bansan kukan nan kinsani sarai, bari in fita inkin gama sai inshigo, yafad'a tare da mikewa zai fita, dasauri tajawo hannunsa tace nadaina, karka fita plz. Yakalleta sannan ya shafa gefen fuskarta yace yauwa farha, kallanta tai tace yaya amma......yace farha please karkibatan rai bayan inajin farincikin ganinki, tace cewa fa zan kasai min icecream😰murmushi yai yasan waskewa tai amma sai yace bari muje a siya. Haka farha taita sashi yawo daga tace ka za sai tace ka za har suka kai 5 sannan sukai gida. Farha kanwar matar sarkice wato mahaifin salman, lokacin salman na 10yrs Abbansa yakaishi paris gun kanwarsa bayan mahaifiyar salman din ta rasu, anan suka kulla wata muguwar soyayya da shakuwa tsakaninsa da farha, sai dai Abba yabada umarnin gaggawa akan salman ya dawo gida, wannan dalilin yasa salman ya rabu da farha kuma bai karasa karatunshi daya fara acan ba. Salma kam na zaune sai kallan waya take amma sam bataga salman ya kira ba, kamal dake zaune yana mata magana sam batasan me yake cewa ba kawai dai tanacewa eh, ganin hankalinta ba'a kansa yake ba yasa yafit, Abbane ya kwalla mata kira dasauri ta mike ta karasa gunshi. Abba yakalleta yace salma dare yafarayi kinga ankusa kiran magriba, ki kira salman kiji, tace to Abba. D'akinta tashiga tare da kiran wayarsa, sai dai har kira uku tai bai d'aga ba kuma bai kira ba, zama tai taredayin shiru tace ina ya shiga? Salman kam shiya raka farha gun fulani, nan akasa aka gyara mata d'akin dazata zauna, tajashi tace yarakata d'akin nan suka shiga taitamai zance sam yamanta da d'auko salma ga wayarsa na kan madubin farha,a silent take, sarai ta kula da wayar na haske amma ita batasan salman ya tafi, hakan yasa ta juya wayar. Sai da salman ya mike zashi masallacin jin kiran sallar magrib yad'au wayarsa missed call din daya gani na salma ne yasa ya kalli farha yace farha am sry bari inje indawo, takalleshi da shagwaba tace yayana yaushe rabon mu hadu? Ina laifin kai sallah a nan? Ya kalleta kamar baisan metake nufi ba yace zanje mosque daganan zanje wani guri, ta mike tace yaya ina kuma? Nifa yau so nak........ga mamakinta bata karasa maganarta ba taga ya fita. Salman kam yana fita ya kira wayar salma,itakam hartagaji da mitar goggo na tazo ta tafi, ganin kiran salman yasa ta mike da sauri ta d'aga, salman yace kinjini shiru ko? Tace wani abun ne ya tsare ka? Yai murmushi yace ganinan zuwa, kafin tai magana ya katse, ta girgiza kai sannan tai murmushi, goggo tace shi ne? Salma tace eh gashinan, goggo tace ah to gwara dai, dan naga akwai wata yarinya a garinmu daga zuwa ganin gida mijin bai kara komawa ba sai takarda tagani, salma tace shi ai ba haka yake ba😒goggo tace iye? Lalai su bera, salma ta juya zatai d'aki ganin kamal tai a tsaye da alama yaji me suka ce ta, dasauri tai d'aki. Salman ya iso ya kira salma tafito, kamal na kallanta kamar yai kuka sai dai ba yanda zaiyi, salma ta shiga mota ta kalli salman tace irin wannan jirgawa?ya juya yace don't tell me harkin gaji da ganin gidan kinaso ki tafi naki🤔? Dasauri tace bafa haka nake nufi ba nufina ba kira🙄. Wata sansanyar dariya yai yace abinda na dade bangani ba yau nagani shiyasa na sha'afa, duk da gaban salma ya fad'I amma tadaure tace da alama wannan abun nada matsayi, salman yace ehm sosai,yafad'a yana kallanta, ta bata rai tace mutum ne?yace eh, cikin tsoro tace mace?kallanta yai yace lawyer kika koma? Tace bahaka bane yanda kai maganar ne ai☹yace hmm. Atare suka saho, har suka isa part d'insu, sai dai me? Suna shiga falo salma taga wata budurwa zaune tana kallo, mamaki yakamata, budurwar tana ganinsu ta mike da sauri tace yayana......sai dai maganar ta ta tsaya a wuya ganin salma, kallanta ta shiga yi, badai itace matar ba?wannan kyakyawar😳? Salma ma kallanta take, kamar tasan fuskar. + Salman ne ya karasa shigowa tare da cewa yaushe kika zo? Sai alokacin ta d'aure ta kalleshi, cikin sanyin jiki tace d'azu, ganinai baka dawo ba😕. Salma ta kalleta sannan ta kalli salman tamai alama dakai wace? Murmushi yai sannan yamatsa gun farha yace kefa dadina dake kenan farha, ba hakuri. Gaban salma ne yafad'I farha? Farha? Farha? Abinda zucuyarta keta maimaitawa kenan, da sauri tai hanyar d'aki, farha ta kalleta tace in_law ku nake jira muyi dinner fa? Salma ta kalleta sannan ta d'auke kai riga da wando ne a jikinta 'yan kanti sai d'ankwalli data d'aura, salma bata amsa mata ba takara yin hanyar d'aki, salman yace magana take miki fa? Salma ta juyo kamar tai kuka tace ina zuwa, yace alright. Salma nashiga d'aki ta zauna a gado dabass...ta rike kanta tace nashiga uku, meke faruwa? Can wata zuciyar tace kika sani ko kanwarsa ce uwa_daya uba_daya? Sai a lokacin tai _Hamdala_ sannan ta d'an mari fuskarta kad'an da hannu biyu tace hakane, salma kidaina tunanin komai.1 Toilet ta shiga sannan ta fito, suna zaune a dinning farha na kusa da salman, ahankali salma ta karasa tazauna, farha kam ta tsorata dakyan salma sai dai bataso agane. Har salma takaraso ta zauna idan farha na kanta, daga d'an nesa dasu kad'an taxauna, farha tace in_law kin fito? Salma ta kakaro murmushi tace yp, salman ya kalleta sannan ya d'auke kai, farha ta fara jawo kwanuka tafara zubama salman abinci, salma naxaune na kallam ikon Allah, bayan farha ta gama sai ta bud'e kwanon karashe,tace kai kamar da tafarnuwa, tafad'a tare da d'an d'anawa, dasauri tasha ruwa ta kalli bayin dake gefe tace ke meyasa kuke sawa abincinsa tafarnuwa?salma tace bangane ba? Meye da ita? Bayan magani ce? Farha tace haba in_law yayana fa is allergy to tafarnuwa, jikin salma yai sanyi takalli salman sai dai takasa cewa komai. Salman ya kalli farha yasaki murmushi yace ya isa, basu sani bane, farha tace nidai akula kar a jama wani abun, in rasa ya zan, salma dake kallan salman tuni ta maida idanta kan farha, cikin tsananin mamaki tace me kika ce? Farha tace bakomai, salman ya kalli salma yace kici abinci, salma dakyar ta zuba sai dai ko loma d'aya takasa ci, farha ta kalli salman tace yayana kasan nima nadainacin tafarnuwa? Yace why? Tace yaxa'ayi inci abinda baka ci☹? Salma kam ranta yagama b'aci da karfi ta ajiye cukalin dake hannunta, dukansu suka juyo tamike tare da kallansu ko magana bata musu ba tanemi wucewa, tazo saitin salman, yasa hannu ya riko ta, ta tsaya cak,batare da ta juyo ba,idanunta taf kwalla, salman yace kI koma kici abinci,salma ta had'iyi wani abu, ta runtse ido tace na koshi banajin yunwa, salman zai magana farha da kishi ya zo mata wuya tai sarin tasowa ta raba hannunsu ta rike salma tace in_law kici abinci plz? Salma ta fizge hannunta tace nace miki na koshi, ko bakya fahimtar yaren? Tana kainan tai d'aki, farha ta kalli salman tace yayana matarka ta iya fad'a, sannan kamar kuka zatai, an ma.........kafin ta karasa taga salman ya mike, d'akin ya shige ya barta anan. Salman na shiga ya salma azaune tana kuka, ya kalleta yace ke kuma fa? Dasauri tafara goge hawayenta ta mike zatai toilet da sauri ya jawota jikinsa ya rungume yace menene? Baki da lafiya? Bakin ciki ya kamata wato baimasan meke damunta ba? Salma ta kwace jikinta tace kaina ke ciwo, yace eyya akwai magani a drawer inkin fito kisha, yafad'a tare da juyawa, salma tace ina zaka? Yace gun farha,jitai kamar tasa ihu, tad'aure tace nikam farha ya kuke? Yace oh banfa fad'a miki bako? Cousin d'ina ce,'yar kanwar Abba ce. STORY CONTINUES BELOW Salma jitai kamar ta mutu sai dai gani tai salman ya bude kofa ya fita, komawa tai tazauna akasa, hutunansu ta tuno, tace shikenan nikam😰. Salman na fita yaga baiga farha ba,dakinta ya wuce, tana kwance tana kuka, girgiza kai yai tare da karasawa, ya d'au tissue yazauna kusa da ita, yace ga tissue, zan fita inkin gama kukan nadawo, yafad'a tare dayin kamar zai mike, dasauri ta rungumoshi ta baya tace karka fita plz yaya, yace to meyasa ki kuka? Tace kawai gani nai kamar now I am useless in ur lyf, salman yace ya zaki fad'I haka bayan kinsan matsayinki? Yafad'a yana zare hannunta, kara kankameshi tai tace yaya naga fa yanda ka mike dazu, yace naji to sakeni sai muyi magana ko? Tace uhm uhm nidai a haka, nafijin dadi☹ tafad'a cikin shagwaba, murmushi yai yace badai haka kike taba mazan paris bako? Dasauri tasakeshi tace haba yaya😕nifa ban taba rike hannun wani ba bayan kai, ya kalleta yace anya kuwa? Tace 'yar iska kamaidani? Yace haka kalmar take nufi? Farha tace ohh yaya bakar magana fa kake fad'amin☹ yai murmushi yace kedai kin fassara kawai. Ta sauko tazo gabansa ta tsugunna tace yaya plz karka yada ni, yace yaza'ayi in ya da 'yar uwata🤔?tace bafa irin wannan ba, nasani sarai kai bakasan auren ko mace biyu shiyasa nake farin ciki,bazakamin kishiya ba to yanzu gashi kayi aure yazamuyi?salman ya kalleta tare da mikewa yace umarni kike nema ki bani ko me? Tace ba haka bane yaya, amma ai kaga ni kakeso, sai ka rabu da waccen ka aureni ko? Salman yakalleta yace farha kanki d'aya kuwa? Itama ta mike tace menai kuma? Yace bakisan niba kenan indai kinsan banasan kara aure ba, ban kuma fi tsanar saki ba😏 . Yana kainan yai hanyar kofa binshi tai da sauri tasha gabanshi ta tare kofa da hannunta, yace me kike?tace to ya kake so inyi yaya? Yace bani gu farha akwai abinda zan? Hawaye ya zubo mata tace zakagun matarka?yace oh god farha meke damunki? Tace kishi tafada tare da tsugunnawa agun tasa kuka mai tsuma zuciya, tugunawa yai ya jawota jikinsa yana shafa bayanta, sai dai baice komai ba, farha kam kuka kawai takeyi. Salma bayan tayi sallar isha'I tai shirin bacci, sai dai har lokacin salman bai dawoba, ahankali ta bude kofar falon, ga mamakinta ba kowa a falon, gabanta ya fad'I badai suna tare ba? Nikam na shiga ukuna🙆🏻 kanta taji ya shiha sarawa ta kalli maganin kawai taga bazata ma iya sha ba, ta rufe drawer tare da mikewa da kyar tai shimfid'a, ta zauna tana jiran salman saI dai har 1q ba labarinsa, har bacci yafara d'aukanta. Salman kam nacan dakyar farha tai shiru nan tacemai ya tsaya ta nunamai wani abu, nantashiga kunnamai videos dinta a paris tana yawon inda suka saba zuwa da salman,dariya kawai suke sam abin yad'aukemai hankali. Bai ankaraba sai ganin 12:30 yai yace farha dare yayi so sai😳sarai tasan time, amma sai tace inalilahi yaya yazamuyi?gashi 12 ake kulle ko ina ko? Salma yace eh, yanzu yazanyi? Tace yaya in akaga ka fito daga nan sai anyi gulmar abun, kawai kabari da safe tunda fulani ba fitowa takeba, in an sauko sai ka fita kamar irin daga gunta kake d'in nan, salman yai shiru, yace a'a idan na kira salma nace tazo mu tafi tare ba wanda zai zargi komai, yafad'a tare da laliban wayarsa, haushi yakama farha. Sai dai me? Wayarsa nakan dinning🤔yakalli farha yace nabar wayar a gida, dadi yakamata tace yaya ka kwana anan kawai, yace me zaisa inkwana anan?tace yay.....ya katseta there must be another way bayan wannan🤔. Nikam haushi duk ya ishen na d'auko sanda nace aikuwa ka kwana anan salman rad'a ma sandarnan zan😣😏.

Post a Comment for "NI DA PRINCE CHAPTER 10"