GANGAR JIKINSA NA AURA COMPLETE
GANGAR JIKINSA NA
AURA
Chapter 1
Wata kwarababbiyar mota
kirar bus mai karar
fatattakekkiyar salansa ce ta tsaya a bakin get din
makarantar yan mata ta
gwamnatin tarayya dake
garin Kazaure, wato
F.G.G.C. Kazaure. Tana
tsayawa kondastan motar ya ja kofar ya bude
"Barararaa" saboda
kwankwatsewar da kofar
motar ta yi sakamakon cin
ruwa da gafje-gafje da
tsabar tsufa.
Wani dattijo mai kimanin
shekaru saba'in da doriya
ne ya fito, da wata yar
yarinya tana biye dashi
wacce shekarunta ba zasu
wuce shekaru goma sha daya ba, Bayan sun furfito
kondastan motar ya
zagaya baya wato but ya
dauko wata katuwar
akwatin karfe irin ta *yan
makarantar wacce aka dafka sunan mai akwatin
garza-garza da fenti baki wato
HANNE HABU IMAMU. Ya
ajiye gefe ya sake janyo
wata karamar katifa
wacce take daure ya dora akan akwatin, sannan ya
dauko wani bokitin karfe
sabo dal yana sheki shima
an fenteshi da sunan mai
bokitin wato
HANNE HABU IMAMU. Daga karshe ya mayar da kofar but din ya
rufe ya juyo ya kalli
dattijon wato Malam Habu
ya ce "Baba baka fa cika
mana kudin motarmu bafa,
gashi har kun sauka" Malam Habu ya sake
marairaicewa ya ce "Dana
da Allah fa nake hadaka
kuyi hakuri kudin da yayi
saura a aljihuna ko gida
bazai mayar dani ba, sai na nemi ciko kayi hakuri dan
Allah, dan haka nema nace
ta zauna a maleji yanzu
baza ka tausayawa tsoho
ba, karbi arba'in din?"
Kondasta ya sake fusata ya ce "Dalla Baba kana
bata mana lokaci ga
fasinjoji har sun fara tsaki
sun kagu suma a kaisu
inda zasu. Ka zauna kana
mana magiya tun dazu muma fa ba'a bati muke
shan man motar da muke
jigilar nan bafa, da kasan
kudin motar taka bai cika
ba me yasa ka hau? Har
zaka ce wai yarinyar a maleji ta zauna, maleji ba
cikin mota bane? Baka san
har a sittin muke daukar
na maleji ba, daga inda
muka dauko ku zuwa nan
nayi maka ragi nace ka kawo hamsin dinma gashi
kaki biya sai wata arba'in
ka bani, kai wallahi Baba
saika ciko mana gomarmu
kaji ko?
Direban motar dake zaune a wajen tuki wanda yake
jin duk abinda suke yi, sai
yanzu ya waigo inda suke
yayi magana ya ce "K.b
wai yane? K.b ya ce "Har
yanzu wannan tsohon bai daina magiya ba wai shi ayi
masa ragin goma kudin
yarinyar nan data zauna a
maleji, Hansin nace ya
biya, ya wani bani arba'in.
Kuma ma dan rainin hankali harda cewa kudin
aljihunsa bazai mayar
dashi gida ba, wato yana
da kudin, cikawa ne bazai
yi ba. Malam Habu ya danji
dadi ganin direban yayi magana ko zaice a bar
masa amma sai yaji
kalamansa sabanin
tunaninsa gara ma abinda
kondastan ya fada masa,
cewa yayi in har bazai biya ta dadin rai ba to zasu
farka aljihunsa su dauki
gomarsu, Malam Habu ya
rike baki don mamakin irin
wannan rashin mutunci,
can ya nisa ya ce "Allah Ya kyauta, bari na baku
kudinku abin duk bai kai
ga haka ba, yasa hannu a
aljihunsa na dama ya
dauko wata
cukurkudaddiyar naira biyar ya sake saka hannu
a aljihunsa na bangaren
hagu ya dauko gudar
naira ashirin da kwandaloli
guda biyar, ya hada
kwandalolin nan guda biyar da cukurkudaddiyar naira biyar din nan ya mikawa kondosta ya ce
"Gashi dana Allah Ya
kiyaye. Ba kunya ba
tausayin tsohon nan yasa
hannu ya karbe yana
gurnani "Daman kana dashi ka tsaya kana bata mana
lokaci duk fasinjoji sun
kagu, direba ya juyo ya ce
"Yayane K.b ya baka, sun
cika? K.b ya ce "Eh sun cika
jamuje J.J.C. Malam Habu da yarsa Hanne suka bi
motar da kallo har ta hau
titi ta kure sannan
hankalinsu ya dawo kan
kayansu.
Malam Habu ya kalli yarsa Hanne wacce hawaye ya
gauraye idanuwanta da
kumatunta, abin ya bashi
mamaki ganin Hanne na
kuka alhali kuma ita take
son karatu take murna da zasu taho, ya sake juyowa
sosai ya kalleta yaga
hawaye neke zubowa
daga idanuwanta daya
nabin daya, ya ce "Yar
Baba, kukan me kike yi?
Karki cemin yanzu bakya
son makaranta bayan ke
aka kira fadar mai gari aka
tambayeki kika ce kina so.
Ba'a son raina ba nima na
kawo ki makarantar nan ke kika amsa musu. Shine
kuma yanzu kike kuka?
Idan kinsan bakya so to ni
a wajena tafi nono fari sai
mu juya kafin mu shiga
ciki. Kansila da mai gari su suka tilastamin in kawo ki
amma badan haka ba nima
bazan rabu dake ba na
kawo ki nan uwa duniya,
babu wanda kika sani.
Hanne ta girgiza kai cikin shesshekar kuka ta ce
"Baba ba makarantar bace
bana so, rashin kunyar da
masu motar can suke yi
maka shine ya sani kuka.
Malam Habu yaji hawaye ya cika masa ido amma sai
ya jure yayi murmushin
karfin hali ya ce "Allah
Sarki yar Baba, babu
komai duniya ce. Duk
wanda yaga girman tsohon wani, za'a ga
girman nasa. Haka kuma
duk wanda ya raina
tsohon wani sai an raina
nasa, zamani ne ya canja
babu sanin girman Allah, ko an hada mutum da
Allah kamar an hadashi da
sa'ansa, wani cewa zaiyi
daina hadani da Allah
karka cuceni
Wa'iyazubillah. Ya ci gaba da cewa "goge hawayenki
yar Baba kizo in dora
miki akwatin mu shiga ciki
kada dare yayi min kinga
har la'asar tayi. Tasa gefen
gyalen da taci damara dashi ta goge idanuwanta
kana ta matso ya ciccibi
akwatin karfen nan ya
dora mata a kai shi kuma
ya dauki bokiti da katifa a
daya hannun sa'annan suka juya suka doshi cikin
babbar kofar shiga
makarantar, yaci gaba da
yi mata nasihohi masu
ratsa jiki yana nuna mata
wannan abin da aka yi masa a gabanta ya zama
darasi a wajenta duk
lalacewar tsoho koma ba
tsoho bane na gaba da ita
kada tayi masa fitsara. Ta
zamana ko a ina take kuma kome ta zama ta
girmama na gaba da ita. Ta
zama mai taimakawa
mabukata, kasancewar
tasan talauci ta kuma
dandanashi tana kan dandanashi.
Masu gadi uku suka iske a
bakin kofar shiga cikin
makarantar, suna
zazzaune, Malam Habu yayi
musu sallama gami da mimmika musu hannu,
Hanne ma ta duka ta
gaishesu, bayan sun amsa,
Malam Habu ya ce "Yarinya
na kawo makarantar nan,
ta ina zanbi mu shiga ciki? Daya daga cikinsu ya ce
"Mikewa zakuyi sosai zaku
tarar da ofishin Malamai
dana shugaban
makarantar. Malam Habu
yayi godiya suka wuce, har sun danyo nisa suka ji
masu gadin nan sun kwalla
musu kira bayan sun
dawo, sai daya daga
cikinsu ya kallesu sama da
kasa ya ce "Dan Allah Malam muna da tambaya
sai bayan da ku ka wuce
tambayar ta fado mana.
Malam Habu ya gyara
kayan dake hannunsa
gami da yin murmushi ya ce "To Allah Yasa na sani.
Ya ce "Wai shin me kake
tambaya ne? Yar
makaranta ka kawo daliba
ko kuma mai aiki ka kawo
gidan Malamai a nuna maka gidan Malamai
(staff quaters)? Malam Habu ya
ce "A'a daliba na kawo
yar makaranta ce. Su
duka suka kyalkyale da
dariya suna tafawa wani harda buga kafa a kasa.
Abun ya daurewa Hanne
da Mahaifinta kai. Menene
abun dariya? Ko nan ba ita
bace makarantar yan
mata ta gwamnatin tarayya dake Kazauren ba?
Malam Habu ya tambaya
suka ce "Nan ce
makarantar daka ambata
amma watakila kayi batan
kai ko baka ji dai-daiba. Malam Habu ya ce "Batan
kai kamar yaya? Daya ya
ce "Nan makaranta ce ta
*ya*yan masu hannu da
shuni, *yan birni masu
kokari, ba haka kawai dan ance yarka taci
makaranta ba kaje ka
suyo akwati da katifa
kazo ka zabi makarantar
da ranka yake so ka shiga
kace ga dalibaba.
Daya ya ce "Ko dai waccan
makarantar ce ta
gwamnatin jiha suka rasa
suka shigo nan. Koda yake
ko can dinma dakyar su
kwashi wannan. Sannan na karshe ya ce "Ku dai ku
tsaya babu mamaki nan
din taci abun ai na Allah ne,
Malam ina takardar shaidar
taci nan makarantar?
Malam Habu ya ce "Mu babu wata takardar
shaidar cin makaranta a
tare damu, ni dai kansilan
garinmu yazo har gida ya
ce jarabawar da yata tayi
a birni ta fito kuma duk karkararmu ita kadai taci
mai garinmu ma ya turo
inje ya shaida min ya ce
lallai-lallai nan taci in
kawota, ya ce min
makarantun yan mata a Kazaure guda biyu ne data
gwamnatin tarayya data
gwamnatin jiha, ta
gwamnatin tarayya taci in
kawota. Amma ni babu
wanda yayi min zancen takarda. Suka sake
kecewa da dariya. Daya ya
ce "Malam sai kuyi waje
don baza ku shiga ba babu
takardar shaida, ku koma
ku sami kansila ko maigarin naku su baku
takardar shaida sai kuzo
ku nuna sannan mu barku
ku wuce. Yau gashi kusan
kusan wata daya ke nan
da aka riga aka gama kawo yara har sunyi nisa
da fara karatu, kai sai
yanzu kake kawo yarka.
Malam Habu ya ja yarsa a
sanyaye suka yi waje,
zuciyarsu cike da mummunar damuwa.
Hakika Nigeria muna cikin
wani hali. Inji Malam Habu a
lokacin da yake ajiye
kayan dake hannunsa a
waje, ya kamawa yarsa akwatin dake kanta suka
sauke kasa. Suka tsaya
suka yi cirko-cirko suna
kallon masu gadin nan,
wadanda har yanzu basu
daina yabo musu bakaken maganganu ba. Malam
Habu ya nisa ya ce "Allah
Sarki rayuwa, Allah Ka
fimu sanin halin da muke
ciki kai zaka fitar damu,
yar Baba zauna a gefen akwatinki kinji kafin
muga yadda Allah zai yi
damu. Isa kansila da
maigari suka ja mana
wannan wulakancin. Ni
nasan a rina, shi yasa da farko naki fur da akace
za'a kaiki birni daukar
jarabawa, kuma kema da
akayi kiranki me yasa kika
amsa musu? Kika ce kina
son karatun, ga irinta nan ai.
Hanne ta zauna a hankali
jikinta yayi sanyi, wanda
ko yatsanta wuyar
dagawa yake yi mata.
Zuciyarta cike da damuwa, babu abin da take tunawa
illa komawarta gida
haduwarta da iya Abu
kishiyar uwarta da
yaranta....GANGAR JIKINSA NA
AURA
Chapter 2
Irin tsananin azabar da
suke gallaza mata da
bautar da ita din da ake
tamkar baiwa alokacin
cinikin bayi. Ta ce a ranta
"Da ina murna zanzo makaranta nabar gidan da
bana hutawa kuma ban
taba hutawa ba sai yanzu.
Gashi yanzu makarantar
ma sun koro mu dole mu
koma gida. Taci gaba da tuna irin tataburzar da aka
sha da Mahaifinta kafin Iya
Abu tabar su suka fito
daga gida zuwa
makarantar nan. Wai ita
idan Hanne ta tafi babu mai yi mata aikace-aikace su
shara wanke-wanke,
debo ruwa a rafi ko tuka-
tuka. Saboda haka nema
taki fur wai baza a kawo
Hanne makaranta ba. Yaranta kuma garda-
gardane maza da mata suna
zaune ko tsinke basa
daukewa sai Hanne wacce
bata da uwa a gidan. Allah
Sarki hawaye ne ya kecewa Hanne yayi ta
zuba daga idanuwanta.
Maganar da daya daga
cikin masu gadin keyi ita ta
katse ta daga tunanin data
dulmiya tana yi. Taji kamar daga sama yana cewa "Kai
kauyawa ma da rashin
tunani suke dan kawai
ance yarka taci
makaranta sai ka taho ka
zabi makarantar data yi maka kawai ka sako kai,
dubi yarinyar daya kawo
sai kace mai zuwa tallar
kalwa riga a cukurkude,
zanin daga kasa ya nade
kamar an nade tabarma. Takalmin kafarta harda
leda ta daure waye zai ce
daliba ce. Daya ya ce
"Danmarar data ci kai kace
dandali zata, ta daure
kugu tamau. Ina jin ma basu san ana dinka kayan
makaranta ba (Uniform)
balle takalmi kambas da
safa. Hanne tayi ajiyar
zuciya ta hadiye yawun da
ya cika mata bakinta tayi shiru, kanta a sunkuye a
kasa. Tace a ranta "Lallai
ko nafi maye kwakwa
dole na hakura da
makarantar nan harda
kayan makaranta ake dinkawa. Waye zai dinka
min? Ta sake kallon kayan
jikinta tace a ranta "Kayan
sallar tawa shine suke
cewa duk a cukurkude? Ni
ina ganin nayi ado kowa a garinmu da muka zo
wucewa yana cewa Hanne
yau kuma ina zaki kika ci
ado haka? Su anan kazan-
kazan suke ganina ashe,
dole mu koma gida ashe ban rabu da wahalar Iya
Abu ba. Kuka ya sake
kece mata har da
shessheka. Malam Habu ya
kalleta fuskarsa cike da
damuwa ya ce "Yi shiru yar Baba bari zamu san
yadda zamu yi mu koma
gida. Ni yanzu ke nake ji
gashi kudin da ya rage
mun a aljihuna saura Naira
ashirin kacal. Da niyyata innakai ki makarantar in
zan koma gida sai in hau
mota daga nan zuwa
tashar Kazaure daga can
kuma sai in kama hanya da
kafa har Babban-mutum (garinsu) idan dare yayi
mun in sami waje in
kwanta washe gari na
tashi naci gaba. Har dai in
karasa ko kwana nawa
zanyi a hanya. To yanzu ba zai yuwu ba tunda gaki, sai
dai kawai mu shiga mota
muje tashar Kazauren, ko
a bakin tashar sai in siyar
da akwatin nan ko katifar
koma duka mu samu muyi kudin motar komawa
gida. Hanne ta zabura ta ce
"Ka siyar da akwati da
katifa fa kace? Kansila ai
sai yasa a kamaka, cewa
yayi fa gwamnati ce ta siya ta bani. Malam Habu yayi
kasake yana tunani na
wani lokaci mai tsawo can
ya ce "To laifin waye? Shi
kansila da maigari basu
san da kudi za'a zo makarantar ba, babu
wanda ya bamu ko sisinsa,
kansila kullum yana min
alkawarin zai je ya karbo
kudin da za ayi miki
siyayya da kayan makaranta da komai da
komai, har cewa yayi
motar gwamnati ce zata zo
ta kawoki. Daga karshe ya
zo ya fara hanya hanya tun daga
gwangwarmar akwatin nan da katifa da bokiti
babu abunda ya kara
kawowa. Bansan wacce
shawara suka yi da
maigari ba kuma daga
karshe suka ce inzo in kawoki haka za'a aiko
miki kayayyakin daga
baya. To yanzu gashi
takardar makarantar ce
babu aka yi mana korar
kare ina ga idan muka shiga ciki aka ce mu kawo
kudi, muka ce babu ai sai a
rakomu da duka.
Cikin sauri Hanne ta ce
"Lah Baba na tuna jiya
maigari ya aiko da wata takarda da yamma ya ce ta
makaranta tace, baka nan.
Na karba nasa a akwatina
ko itace suke tambaya?
Malam Habu cike da
mamaki da zumudin dauko takardar ya ce "Haba yar
Baba kina yar karamarki
kike mantuwa, tun dazu fa
ake maganar takardar
duk baki tuna ba. Yi maza
ki dauko takardar in nuna musu ko itace takardar.
Hanne ta daga akwatin da
sauri ta bude, babu komai
a ciki sai kayan sawarta
kala biyu a cukurkude
suke kamar anyi sukuwar doki a kansu. Ta binciko
can kasan akwatin ta
dauko wata doguwar
takarda fara ta mikawa
Babanta. Malam Habu ya
karba da sauri ya doshi wajen masu gadin nan
yana cewa "Ga dai wata
takarda a cikin akwatinta
sai yanzu ta tuna ashe mai
gari ya aiko da ita jiya ku
dai ku duba ku gani ko ita ce. A yatsune daya daga
cikinsu ya karba ya duba
yana dubawa kuwa yaga
takardar shaidar an dauki
Hanne Habu Imamu a
F.G.G.C Kazaure ce wato (Admission letter)
Sun sha mamaki kwarai da
ganin nan makarantar
kuwa taci ba batan kai
suka yi ba. Cikin sakin
fuska suka yi musu izinin su kwaso kayansu suzo su
wuce. Cikin murna Hanne
da Mahaifinta suka kwashi
kayansu suka wuce izuwa
cikin makarantan. Basu
tsaya a ko'ina ba sai a bakin wani babban gini
wanda ya kunshi
doguwar baranda da
ofishin Malamai.
Babu kowa a wajen hatta
leburori masu share-share da goge-goge duk basa
nan, wajen tsit kamar
babu bil'adama. Suka sami
gindin wata bishiya suka
sauke kayansu. Hanne ta
hau kan akwatinta ta zauna Malam Habu ya ce
"To fa wannan shine ko in
kula, yanzu kuma ina zamu
dosa ko kuma wa zamu
tambaya? Ni wallahi abun
nan na makarantar bokon nan ya ishe ni daga nan sai
can ana tsattsare ka da
tambaya kamar a lahira
mun gama da masu gadi
yanzu kuma Allah ne kadai
Ya san wa zamu hadu dashi, kai Allah Ya kyauta,
wannan shine ake cewa ba
shiga ba fita wai an bawa
mahaukaci gadin kofa.
Shigowar wata dalleliyar
mota ce Jeep launin koriya (dark green) wacce ta
tunkaro inda suke, ita ta
katsewa Malam Habu
surutun da yake yi. Ta zo
daf da su ta tsaya babu
abinda yake tashi a cikinta sai sautin kida da sanyin
A.C maza ne samari guda
biyu suka fito daga gani
wa ne da kaninsa, kanin
yana sanye da kayan
bautar kasa a jikinsa wato (N.Y.S.C) Yayan kuwa wata
tsadaddiyar shadda ce fara
sol a jikinsa sai kamshin
wani tsadadden turare ne
yake tashi. Abunka da
kauyawa sai kallo suke dukka uba da yar,
kanin ya bude but din baya ya
dauko wata Jakar kaya,
ya mayar ya rufe ya ce da
wansa "Yaya Habib, na
gode sai dai nace maka Allah Ya kiyaye hanya.
Yaya Habib yayi murmushi
ya ce "To madalla. Allah Ya
bada sa'a sai yaushe kuma
zaka zo mana weekend?
Ina fatan dai wannan karan zaka yi kamar wata
baka zo ba ko? Su duka
biyun suka tuntsire da
dariya, kanin ya ce "Ai
Yaya ranar juma'ar nan
zaka ganni a gida ko ba'azo daukana ba ma
zanzo Kano, haba ai sai jini
na ya hau zama a kauye in
ba dole ba wa zai iya?
Yayan yana dariya ya
mikawa kanin hannu suka gaisa ya ce "To Allah Ya
taimaka, ina ganin ranar
juma'ar da zaka zo may be
baza mu hadu ba saboda
da sassafe zan tashi zuwa
america kai kuma nasan sai da yamma zaka taho sai
an tashi yan makaranta
ko? Kanin ya ce "Eh kuwa
ba zamu hadu ba Allah Ya
kiyaye hanya Ya dawo
mana da kai lafiya, Yaya akwatinan auren da nawa
da naka ya zamo iri daya.
Yaya Habib ya ce "Insha
Allahu, Yaya Habib ya
shiga mota har zai ja kofar
motar ya rufe sai ya juyo ya kalli Hanne da Babanta
ya ce "Salamu alaikum"
Malam Habu ya amsa gami
da daga hannu, Yaya Habib
yaja motarsa ya juya ya
nufi kofar fita kanin na tsaye yana daga masa
hannu.
Bayan da motar Yaya
Habib ta kure, idanuwansu
duka na kanta sannan
hankalin kowa ya dawo jikinsa. Tunanin Hanne ya
koma ga kallon
kyakkyawan ginin
makarantar ginin bulo da
bulo, yaune rana ta farko
da take tunanin take sa ran zata kwanta a dakin
ginin bulo ba gidan kasa
ba rufin azara. Ta ce a
ranta "Cafdijan yau kuwa
zan iya bacci? Anya bazan
ringa jin sanyi ba a wannan dogayen
gininnikan. Bata san sanda
tayi murmushi ba har
hakoranta suka fito, sai ta
wayence ta kifa kanta
akan cinyarta kada Babanta ya gane
murmushin dadi take.
Kyakkyawan saurayin
nan ya tunkaro inda suke
yana rataye da jakarsa a
kafadarsa, ya yiwa Malam Habu sallama gami da dan
dukawa kadan, kana ya
wuce su yaje gindin wata
bishiyar dake kusa da tasu
ya daga wani benci ya
zauna ya ajiye jakar kayansa a kusa dashi yaci
gaba da kallon Hanne da
Mahaifinta. Can Malam Habu
yaje ya same shi a inda
yake zaune ya ce "Dan
Allah *yan samari kai maka'aikaci ne anan ko
kaima bako ne? Yayi
murmushi ya ce "Yaya aka
yi Baba? Malam Habu ya ce
"Yarinya na kawo
makaranta tun dazu banga kowa ba balle in
tambayeshi hannun wa ya
kamata in dankata?
Saurayin nan ya gyara
zama gami da cire hular
dake kansa ya ce "Daliba, daliba ce wannan? Malam
Habu ya ce "Eh nan aka ce
na kawota kuma gama
takardar can bari ta miko
Dama korarmu akayi dazu
da babu takardar, ya kwalla kira ya ce "Hanne
kawo takardar nan ta
dazu.
Cikin sauri Hanne tasa
hannu a cikin bokiti dake
gabanta ta dauko takarda tazo ta mikawa Babanta da
hannu biyu ta duka har
kasa. Babu abinda wannan
saurayi yake sai kallon
Hanne sama da kasa kayan
jikinta yake kallo da takalmin dake kafarta
wanda ta daure da leda
saboda ya tsinke kudin
nanin ma aiki ne, tasha wata
uwar danmara kai kace
damben tsiya za'a kwasa, wuyan, hannu da kafa
tsakiyoyi. Saurayin nan ya
kula da lallai Hanne ita
kanta tana jin kunyar
shigar nan tata ganin
kallon da yake yi mata, sai yayi sauri ya fara duba
takardar da Malam Habu
ya mika masa. Ya karance
tsaf, sannan ya dago ya ce
"Hanne Habu Imamu ko?
Tace "Eh, ya ce "To Baba sai kun dan jira don nima
nan Malamin nake jira
gashi takamaimai ma ni
bansani ba ko yana
makarantar ko bayanan
don nima shigowata kenan. Malam Habu yayi
Hamma gami da yin dan
siririn tsaki ya ce "Yaro
yanzu ba yadda za'ayi ka
karbi yarinyar nan, dole
sai waccan din ya zo? Saurayin ya ce "Ni Malami
ne amma kuma ba
permanent teacher ba
bautar kasa (service) nazo
yi, a ka'idar wannan
makarantar kuma senior master ne ya kamata ya
karbeta musamman ma
kasancewarta sabuwar
daliba ce. Gashi yau lahadi,
dama litinin ce ko sauran
ranakun aiki lokacin principal tana nan, da
sauran pamanent teachers
duk sai su karbeta koda
senior master baya nan,
amma yanzu ku jira kadan
idan nan da minti talatin bai dawo ba, zan tashi
nima na shiga staff quaters
din na gani ko yana ma
cikin makarantar dan nima
shi nake so na gani zan
karbi mukullan gidana. Malam Habu ya ce "To Allah
Ya kawoshi lafiya bari nayi
sallar la'asar, nasan biyar
tayi ko sallar la'asar bamu
yi ba. Yaro ina buta? Ya
nuna masa wani fanfo can kusa dashi kuma da
zagayeyyen waje nan ne
Masallaci. Malam Habu ya ce
"To madalla. Ya kalli Hanne
wacce ke tsaye a gefe har
yanzu ya ce "Yar Baba koma kan akwatinki ki
zauna zanje nayi sallah
kinji. Cikin sanyin murya ta
ce "To, ta juya ta doshi
wajen akwatin. Malam
Habu ya bita da kallo zuciyarsa cike da
tausayinta ganin yininsu
guda babu abun da suka ci
tun dan kokon safe da
suka dan kukkurba a
tsattsaye bala'in Iya Abu ya hanasu su zauna su sha
sosai. Malam Habu ya
girgiza kai alamar
tausayawa kansu da
kansu ya ce "Allah Sarki
yar Baba hakuri dai za ki yi, ki kuma ci gaba dayi.
Sannan ya juya ya nufi
wajen fanfo. Kyakkyawan
saurayin nan na zaune
yana kallonsu zuciyarsa
cike da alamomin tambaya da tsananin tausayi. Can ya
nisa yayi ajiyar zuciya ya
zaro gilashin dake
aljihunsa ya saka a idonsa
gami da cusa hular dake
hannunsa a cikin aljihunsa na wando yasa hannunsa
ya dafe habarsa yaci gaba
da kallon Hanne dake
zaune kan akwatinta tayi
lamo tana tunani ba tare
da tasan wani na nan gefenta ta cikin gilas yana
kallonta ba. Ya ce a ransa
"Wadannan daga wanne
kauye suke? Sun kuwa
karanta takardar dake
hannunsu sunsan me ya kamata su tanada suzo
dashi? Kai basu san dokar
da aka rubuta ba a jikin
joining instruction din nan
ba. Lallai kuwa da sun san
me aka rubuta da baza taci uwar danmarar nan ba ta
shigo makarantar nan
haka ba.
Bayan kamar tafiyar
Malam Habu da minti
ashirin sai gashi ya dawo. Ya zo ya wuce ta gaban
saurayin ya ce "Sannun ka
da hutawa, ya katse
tunanin da yake ya ce
"Yauwa Baba. Malam Habu
ya kara da cewa "Har yanzu dai kaga shiru baizo
ba ga rana nan na shirin
faduwa yau kuwa anya
mai karbar yaran nan zai
dawo? Yayi murmushi ya
ce "Ina ganin ka kawo duk abubuwan da aka ce
ta siya da kudin
makaranta zan yi kasada
na karbeta yanzu in yaso
ranar litinin wato gobe
idan mutum yazo ya rubuta risitai yanzu sai
nayi magana da masu
gadin get din Hostel su
kirawo prefect din....
Malam Habu ya matso kusa
dashi ya ce "Yaro fadamin da Hausa sosai na gane me
kake cewa? Har da wani
abu da zan kawo nan
gaba? Ya ce "Eh Baba, ai a
rubuce a jikin takardar
aka rubuta za'a dinka mata kayan makaranta
har kala hudu, wanda zata
sa idan zasu aji da wanda
zata saka a dakunansu,
dana wasanni (sport) duk
an rubuta kuma lallai-lallai sai da kayan makaranta
za'a karbeta ba zata ta
saka kayan gida ba,
sannan daga karshe aka
rubuta zata zo da kudin
makaranta (school fees) shi kuma da yake sabuwar
zuwace sai kun biya sama
da dubu..... Malam Habu ya
katse shi da sauri ya ce
"Tsaya yaro karma ka
kirawomin wadannan dubunnai. Ta faru ta kare
wai anyiwa mai dami daya
sata, yaro na gode
madallah, sai anjima. Malam
Habu ya juya ba tare da ya
jira amsa daga bakin saurayin nan ba ya doshi
inda Hanne ke zaune da
saurinsa kamar zai kifa
cikin gaggawa, ya ce "Yar
Baba tashi maza mu tafi ga
magariba ta kawo kai. Cikin sauri ta mike ya
ciccibi akwati ya dora mata
akai ya sungumi bokiti da
katifa suka kama hanyar
get din fita. Sunyi taku
daya biyu sai sai suka ji magana kamar daga sama
ance "A'a Baba ina zaku
kuma? Su duka suka juya
dan ganin mai maganar sai
suka ga wannan
kyakkyawan saurayin ne ya taso yazo wajensu.
Malam Habu ya ce "To yaro
me zamu yi in ba tafiya ba,
dubunnan kudi fa naji
kana kira, kumama ka tsaya
cak ka kalleni dani da dubu daya a yanzu waye ya
ajiye wani? Daman
kansilan garinmu ne da
maigari suka sani dole na
kawo yar nan
makaranta, suka ce za'a aiko da kudin, na tabbata
har ga Allah basu san
kudin yakai dubunnai ba
da suma basu tanka ba.
Kuma kudin gwamnati
ba'a bashi babu yadda za'ayi nazo na ajiye
yarinya a makaranta babu
kudin makaranta babu
kayan makaranta na ce a
bimu bashi zamu kawo.
"Wannan ba zai yiwuba, inji saurayin. Malam Habu
ya ce "To ka gani cewa
suka yi na zo na kawo ta
za'a aiko da kudin kuma
yadda naji kalamansa shi
kansilan a tunaninsa kudin makarantar bai wuce dari
uku ba, bai san dubunnai
bane kuma koda shine
yazo ya kawota aka kira
dubunnan nan cewa zaiyi
ta fasa karatun. Don ko karamar hukuma baza ta
biya wadannan makudan
kudaden ba.GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 3
Saurayin nan yayi murmushi ya
girgiza kai ya ce
"Amma Baba bai kamata daga
kiran dubunnan
nan ka kwasheta haka da sauri
kace zaku tafi ba.
Malam Habu ya fara jin haushin
saurayin nan, ya
ce a ransa "Wai shin wannan
duk zancen nan da ake bai gane
ba ne? Makaranta sai da kudi
kuma
babu kudin jiran me zanyi, ko
shi bai san babu ba
ne? Saurayin nan yaci gaba da
cewa "Baba kuzo
ku ajiye kayan nan bai kamata
ka juya da yarinyar
nan ba, ai bai kamata ba. Ta ci
makaranta har
kun shigo cikin makarantar
sannan ku kwasa ku tafi
ka
ce ka fasa, babu fa abin da Uba
zai yiwa yarsa a
duniya in ba ya bata ilimi ba,
yarinya kamar
wannan ai kamata yayi tana
makaranta tunda
bata isa aure ba, me zata yi a
gidan? Malam Habu
ya sake jin haushin saurayin nan
kamar ya doke
bakin da yake masa wadannan
kalamai ya ajiye
bokitin dake hannunsa ya ce
"Yaro, wai shin a
harshen Hausa idan akace babu
me ake nufi? Yayi
murmushi ya ce "Baba kenan, na
gane duk dalilan da kake nuna
min yanzu, ni kuma abin da
nake so na rokeka shine ka fasa
tafiya da ita
tunda
ka kawota har cikin makarantar
ka kyaleta tayi
karatu. Abun da ya kamata ka
tambayeni shine
tayaya zata yi karatu tunda babu
kayan makaranta babu kudin
makaranta? Malam Habu
ya ce "To yanzu nasan ka gane
babu, ta yaya
zata
yi karatu babu kudin makaranta
babu kayan
makaranta? Kyakkyawan
saurayin nan ya ce
"Yauwa Baba kayi tambaya mai
kyau, amsar tambayar ita ce in
Allah Yaso Ya yarda Hanne
zata
yi karatu in har ka amince ka
yarda zaka ringa
turo ta makaranta da zarar hutu
ya kare ba sai ta
fara ba kace baza ta dawo ba ka
cire ta. Idan
kayimin alkawarin haka kuzo ku
ajiye kayan nan ka
tafi ka barta. Malam Habu yayi
jigum yana tunani,
a ransa ya ce "Wannan yaron me
yake nufi?
Hanya
zaiyi mana a dauki Hanne babu
kudin makaranta
babu kayan makaranta ko kuma
yaya za'ayi? Bana
tunanin dai shi zai biya mata
kudin makarantar
harda dubunnan da ko karamar
hukumar mu baza
ta iya biya mata ba yadda
zamanin nan ya canja
masu kudi basa taimako, babu
yadda za'ayi yaron
nan ya zare makudan kudi ya
baiwa yarinyar da bai santa ba
bai taba ganin ta ba bazan bar
yar
Baba a makarantar nan ba in
tafi ta wulakanta ba,
wacce bata san hanyar da zata
bi ta koma gida
ba
idan an korota. Yanzu akan
Naira goma masu
mota suke kokarin su danneni
su dauka ina ga dubunnan
kudade ga kayan makaranta har
kala
hudu waye zai dinko mata?
Saurayin nan ya katse Malam
Habu daga tunanin
da yake yi ya ce "Baba tunanin
me kake yi ne?
Karka yi kokonto ba zaka yi
dana sanin barin
Hanne a makarantar nan ba in
Allah Ya yarda babu abin da zai
sami Hanne sai alheri da
kwanciyar hankali ka tsarkake
zuciyarka ka danka
Hanne ga Allah wanda a koda
yaushe Yana kallon
halin da bayinsa suke ciki na
kunci kona farin ciki,
sannan ka danka Hanne amana
ce a wajena. Ni
kuma na maka alkawarin zan
karbi amana na rike.
Cikin
sanyin zuciya da gamsuwa da
kalaman
saurayin nan Malam Habu ya
juya ya kalle shi ya
ce "Allah Sarki duniya wani ya
munana maka wani
kuma ya dadada maka. Yaro
tunda ka ce Allah na
yadda ka kuma ambaci amana,
amana kalmace
mai girma mai wuyar rikewa
kace zaka rike tsakaninka da
Allah, na gode yaro, Allah Yayi
maka
albarka Ya biya maka
bukatunka. Abin da kayi
min
Ubangiji Allah Yayi maka fiye da
haka, yar Baba
muje mu ajiye kayan. Suka juya
harda saurayin wajen bencin da
yake, Malam Habu ya kama
akwatin dake kan Hanne ya
sauke mata ya juyo
ya
kalli saurayin nan dake zaune
akan benci ya ce
"Yaro bazan gaji da yi maka
godiya ba. Madalla
Allah Ya yi maka albarka zan tafi
na barku lafiya, af
kaga ko sunanka ban tambaya
ba. Saurayin nan
yayi murmushi ya ce "Sunana
Haisam, Baba.
Malam Habu ya ce "To madalla.
Ya juya ya kalli
Hanne wacce ke tsaye idonta ya
ciko da kwalla ya
ce "Yar Baba zan tafi na barki
ga Allah na barki ga
wannan bawan Allah. Sai ta
rushe da kuka ta
koma kan akwatinta ta zauna ta
kifa kai a gwiwa
tana kuka. Hawaye ya kecewa
Malam Habu ya ce
"Nima ba'a san raina zan tafi na
barki ba Allah Ya
kaddara saduwarmu. Ya juya ya
kalli Haisam ya ce
"Yaro mai wuyar suna har na
manta sunan na tafi,
sai wata rana. Haisam ya ce "To
Baba Allah Ya
kiyaye. Malam Habu ya juya ya
fara tafiya yana
face majina yana goge hawaye
da gefen babbar
rigarsa, sai yaji muryar Hanne ta
ce "Baba ya juyo ya ce "Yar
Baba. Ta taso da gudu ta karaso
inda
yake ta kama gefen zaninta ta
kwance sai ta
dauko wasu cukurkudaddun
yan Naira ashirin
guda hudu ta ce "Baba karka
tafi da kafa gashi ka
hau mota. Haisam dake zaune
har yanzu akan
benci yana kallonsu sai da yaji
kwalla ta cika masa
ido don tausayin Uba da yarsa.
Malam Habu ya
ce
"Allahu Akbar, yar Baba Allah
Yayi miki albarka.
Allah Ya baki ilimi mai amfani,
kinji? Waye ya baki
har murtala hudu? Hanne ta ce
"Dana shiga makwabta nayi
musu sallama suka babbani
wasu,
sauran kuma kudina ne da nake
tarawa tun na
yawon salla. Malam Habu ya ce
"Kya bani duka
ingo murtala biyu ni na dauki
murtala biyu, kema
ki rika siyan yar gyada kya
zauna haka kina
ganin yara suna siye-siye ke
bakya siyan komai? Hanne
ta ce "A'a Baba murtala biyu
baza ta kai ka gida
ba, bana so ka shiga mota
kudinka bai cika ba,
kana rokon ayi maka ragi irin na
dazu. Malam
Habu ya sake kecewa da kuka ya
ce "To yar
Baba na gode na tafi na barki ga
Allah baki da kowa,
baki da komai, ba ki san kowa
ba, Ya juya ya tafi.
Hanne na tsaye hawaye yana
zuba daga
idanuwanta tana kallon
Mahaifinta yana tafiya
yana waiwayenta. Taji wani
kululun bakin ciki
marar misali a kirjinta da
mummunan tashin hankalin
rabuwa da Mahaifinta, yaune
ranar da ta
taba rabuwa da Mahaifinta
daidai da rana daya
basu taba rabuwa ba. Gashi a
yau ya kawota inda
bata san kowa ba ya juya ya tafi
ya barta.
Hawaye
ne mai radadi yake zubo mata
har sai da ta daina hango
fararen kayansa ya kure, sannan
ta yi
ajiyar
zuciya tasa gefen mayafinta ta
goge idanuwanta
ta juya ta dawo kan akwatinta
ta zauna. Haisam
na zaune akan benci yana
kallonsu zuciyarsa cike
da tsananin tausayi ji yake wani
abu yana yawo a cikin kansa,
saboda wani abu guda daya
daya
bashi mamaki ya bashi al'ajabi,
shine ganin yadda
Hanne take da Mahaifinta suna
cikin tsananin
talauci amma suna da wadatar
zuci. Haisam yaci
gaba da kallon Hanne wacce
take zaune akan
akwati a gabansa ta sunkuyar
da kanta kasa tayi shiru kamar
mai tunani, amma hawaye na
digowa
daga ganinta hankalinta a tashe
yake tana cikin
damuwa. Ya gyara zama gami
da zare farin
gilashin da yake fuskarsa. Ya ce
"Hanne, kukan
mai kike yi ne? Bakya so ki
zauna a makaranta
kiyi karatu kamar sauran yara,ne?
kin fi so ki koma gida
ki
zauna da Baba? Hanne ta girgiza
kai alamar a'a,
ya
ce "To meye kikema kuka? In
kinsan bakya son
makarantar nan yanzu nayi
sauri na tsayar da Babanki kafin
yayi nisa sai ku koma gida.
Hanne
tayi sauri ta ce "A'a bana so na
koma gida, ya ce
"To ai kuka kike meyasa kike
kukan tunda kina
son
makarantar? Bakya son ki koma
gida inda zaki yi
wasa kuyi wake-wake da
kawayenki a dandali? Hanne tayi
dan murmushi ta sunkuyar da
kai.
Haisam ya ci gaba da cewa "Ni
kuwa na dauka
danmarar nan da kika ci ta
zuwa wake dandali ce.
Hanne tayi narai-narai da ido
kamar zata yi kuka
ta
ce "Ni ba'a barina naje dandali
wasa. Kullum aiki nake yi sai dai
inzo in wuce su in zani debo
ruwa.
Haisam ya sake gyara zama ya
ce "Ban gane ba
sai dai ki zo ki wuce su in zaki
debo ruwa? Ke
kullum a debo ruwa kike bakya
zuwa wasa?
Hanne
ta ce "Eh, sai dai su Saude
Yayyena da kanne na ne suke
fita wasa. Haisam ya ce "Ina
Mahaifiyarki
take? Hanne ta sake saka gefen
gyalenta ta share
hawaye ta ce "Tun ina shekara
biyu ta rasu. Yaji
gabansa ya yanke ya fadi ras,
saboda yanzu ya
gane Hanne a gidansu tana cikin
halin wahala
kasancewar Mahaifiyarta ta rasu
da alama kishiyar
Uwa tana wahalar da ita. Allah
Sarki Hanne ya
fada
a ransa yayin daya kura mata
ido. Hanne ta bashi
tausayi da, a yanzu kuma ta sake
kara bashi
tausayi akan tausayi wanda
badan ya daure ba da zai iya
rushewa da kuka. Can bayan
sun dauki
wani lokaci mai dan tsawo babu
wanda ya sake
cewa komai. Dukkaninsu kansu
a sunkuye a kasa
suna tunani, Haisam ya rike kai
da hannuwansa
guda biyu can ya dago ya kalli
Hanne ya ce
"Yanzu dai a gidanku ke kadai
Babarki ta haifa kenan baki da
Yayye ko? Hanne ta ce "Eh. Ya ce
"Shine kuma ake saki debo
ruwa kullum. Hanne ta
ce "Ba debo ruwa kawai ba
kullum ni nake wanke-wanke,
shara, wankinsu, da kai dabbobi
kiwo
daga
can nayo musu ciyawa. Haisam
ya buga kafa a kasa ya ce "Kai
wannan wanne rashin imani ne
haka? To ya akai kike zuwa
makaranta? Hanne ta
ce "Sai wajen sha dayan rana
koma wataran bana
zuwa, tun ana min dukan
makaranta har suka
daina su Malamai. Shine wani
Malami ya je ya
sami mai gari ya ce a yiwa
Babana magana a dinga
turoni makaranta da wuri tunda
ina da kokari,
Haisam ya ce "Sai da maigari ya
kira Babanki ya
fada masa sannan ake turaki
makarantar da wuri?
Hanne ta ce "Cafdijan shima
Baban ya isa? Ya ce
"Kamar yaya bai isa ba. Ta ce
"Shima tsoron Iya Abu yake,
matar tasa zaginsa take,
*ya*yanta
suyi
masa, sai dai in ana dukana ina
kuka shima ya
dinga yi. Hawaye ya sake kece
mata, shima ya ji
kwalla ta cika masa ido, ya
dauko wani hankici
fari kal a aljihunsa ya goge
idanunsa ya mika mata,
yace "Yi shiru Hanne daina kuka
goge hawayenki. Ta
karba ta goge.
Haisam ya ce "Bari na danyi miki
tambayoyi naji
kina kokari? What is your name?
Hanne ta ce "My name is Hanne
Habu. Ya ce "How old are you?
Ta
ce "I'm eleven years old. Wich
school are you? Ta
ce "I'm in Babban-mutum
special primary school.
Haisam yayi dariya ya ce "Hanne
Habu haka kike
da kokari? To ke da bakya zuwa
makarantar sosai
ya aka yi kika koyi duk wannan?
Hanne tayi murmushi ta ce "Ai
daga baya maigari yasa aka
kirawo ita iya Abu da kanta taje
fada ya saka
shaidu ya ce "Duk ranar data
hanani zuwa
makaranta ko na makara sai ya
kaita kara local
goverment. Sannan take barina
na tafi makaranta
da wuri sai dai idan na dawo
tayi ta dukana tana cewa ga
wanke-wankenta nan harya
bushe na
tsaya a hanya ina wasa. Haisam
yayi tsaki ya
girgiza kai alamar tausayawa.
Yayi gyaran murya
ya ce "Hanne ina so kiyi min
alkawarin zaki dage
kiyi karatu duk rintsi duk wuya.
Kar ki zo ki fara
ayi hutu ki koma gida kiga
kawayenki da yayyanki
suna gida basa zuwa makaranta
kema kiki
dawowa. Hanne ta ce
"Kwarankwatsa zan dawo.
Haisam ya kece da dariya ya ce
"Kwarankwatsa
ba
rantsuwa bace wallahi Allah za
ki ce. Hanne tayi dariya ta ce
"Mantawa nayi Malamin
makarantar
Islamiyya ya hana mu cewa
kwarankwatsa.
Haisam ya ce "Kina zuwa
Islamiyya kenan? Ta ce
"Eh, ada makarantar allo muke
zuwa daga baya
aka bude makarantar Islamiyya
da yamma da
kuma dare duka ina zuwa.
Haisam ya ce dakyau Hanne
yanzu idan anyi hutu kin koma
gida sai kici
gaba da zuwa ta Islamiyya karki
fasa zuwafa
kinji?
Hanne ta ce "To. Haisam ya ci
gaba da kallonta
har sai da Hanne ta fara jin
kunyar kallon da yake
mata sannan yayi murmushi ya
ce "Hanne duk wannan kwalliya
ce kika yi a fuskarki, ta zuwa
makaranta ce? Hanne tayi
murmushi ta sunkuyar
da kai kasa tana rurrufe fuska
da hannu ta ce "A'a
ba kwalliya bace. Ya ce "Gashi
nan kin rambada
kwalli kinja wata doguwar
jagira kinyi fashin goshi
da kwalli kinyi digo-digo duk
fuskarki kice ba kwalliya bace.
Ga wannan tsakiyoyi da kika
jifga a wuya da
hannu har kafarki ma kin daura,
Yana dubanta
yana dariya.
Hannan ta ce "Eh sarkar salla
tace Baba ya siya
mun. Ya ce "Kinga nan
makarantar an hana sawa idan
Malamai suka gani zasu kwace
su tsittsinka
miki, ciro su ki bani in ajiye miki
sai anyi hutu in
zaki tafi gida na baki. Cikin sauri
taji zancen
tsittsinkawa ta ciro ta bashi,
yadda take bala'in
kaunar sarkokin nan nata bata
son abun da zaisa
ta rasa su. Haisam ya karba yana
jujjuyasu yaga wasu irin tsohon
wuri ne aka jera su cikin lilo aka
daura ya ce a ransa "Yan kauye
suna gayu. Yayi
murmushi ya jawo jakar
kayansa ya bude wani
karamin zip ya zuba ya mayar ya
rufe. Ya juya ya
kalli Hanne ya ce "Kuma a cikin
akwatin naki bude
in gani ko kinzo da wani
abunda dokar makaranta ta
hana. Hanne ta tashi daga kan
akwatin ta bude
ya karkato ya leka akwatin babu
abunda ya hango
sai tsummokarai, cikin sauri ya
ce "Hanne meye
wancan nake hangowa kamar
miciji a cikin
akwatinki?
Hanne tasa hannu ta zaro wani
dan siririn gyale baki ya
kanannade ya kudindine ta ce
"Gyale ne
ba miciji bane. Haisam ya
kyalkyale da dariya ya
ce "Na dauka kofi kika yimin na
miciji. Hanne ma
tayi dariya ta ce "Gyale na ne
dan bansa ruwa ba
na kadeshi shiyasa ya
cukuykuye, ya sake leka
akwatin sai ya hango wani dan
dogon karfe mai huda huda a
jikinsa, jikinsa kamar farar
azurfa
yana kyalli ya ce "Hanne wannan
fa, karfen
menene? Dauko muga.
Hanne ta yi murmushi ta dauko
karfen ta mika
masa ya karba ya jujjuya bai san
ko meye ba ya
ce "Wannan kuma na maye.
Hanne ta ce "Idan naje
kiwo nake yiwa dabbobi busa
dashi, abun busa
ne.
Haisam ya ce abun busa kuma?
Hanne ta ce "Eh
kawo ka gani. Ta karbi karfen ta
mayar da
akwatin ta rufe ta koma kan
akwatinta ta zauna ta
kaikaice
ta fara busawa Haisam wannan
karfen kai kace
Sarkin busar Sarki ne yake yi,
karin busar mai
dadi
da alama dai waka ce, Haisam ya
buda kunnuwa yana sauraro ya
baza ido yana kallon yadda take
yi.
Can ta kyalkyale da dariya ta ce
"Haka nake yi.
Haisam yayi murmushi ya gyara
zama ya ce "To
ni
abunda ban gane ba, kamar
yaya sai kinje kiwo kike yi?
Daman a wajen kiwo ake yin
busa? Waye
ya koya miki kuma? Nan da nan
Hanne ta canja
daga yanayin farin cikin da
fara'a da sakin jikin da
take jikinta yayi sanyi ranta ya
baci.
Haisam ya ce "Ya kika canja nan
da nan daga
tambayarki? Hanne ta rushe da
kuka ta kifa kai da
gwiwa, Haisam yayi matukar
mamaki da ganin
wannan hali da Hanne ta fada
yanzu-yanzun nan
ya ce "Yaya kina dariya ki koma
kuka, Hanne
dago
kanki. Ta dago ya ce "Goge
hawayenki. Ta goge. Ya ce "Fada
min meye na kukan? Hanne ta
ce
"Wani abu na tuna shine ya sani
kuka. Haisam ya
ce "Meye abun da kika tuna?
Hanne ta sa hannu
ta sake goge hawayen da ke
idonta ta dauko abun
busar dake kan cinyarta ta rike a
hannunta tana jujjuya shi.
GANGAR JIKINSA NA AURA
CHAPTER 4
2pages is gone
ya lullubeta ''
tacehakane malam haisam ni dana
ke cikinsu
yangulma ko sun tambayeni ni nasan
me zan
fadamusu'' haisam yace'' yauwa ku dauki akwati
da bokiti da katifar kamar yadda
nace akai store
aajiye, sai da safe'' suka ce allah ya
kaimu''uwar
biyuta kama akwati ta dora akan hanne ta dauki
bokiti,da katifa a daya hannun suka
doshi store din
kicininda suma suke boye shirginsu .
Malam
haisamkuma ya rataya jakarsa ya nufi gidajen
malamai (staff qurters). Zuciyarsa
cike da
tausayin yaddarayuwar hanne take.
Kuma da burin
canza matanan gaba
* * * *
HAISAM ABDULHAMID
ZAKAR Sunanmahaifinsa ne
abdulhamid zakar.
Mahaifiyarsakuma sunanta NANA
HAUWA'U
Wacce a yanzu akafi saninta da hajiya nana ko
kuma barista nana kasancewarta
kwararriyar lauya
ce. Mahaifinhaisam haifaffun
unguwar kwalli ne a
kano. Kumasun fito daga tushe daya yar kanwace
aka hadasu aure a lokacin alhaji
abdulhamid ya
gama karatumdigiri dinsa a london
yana da
shekaru ashirin dabakwai ita kuma hajiya nana ta
gama karatun sakandire tana da
shekara goma
sha shida.Dukkaninsu iyayensu suna
da matukar
arziki. Don haka an sakar musu kudi yadda ya
kamata antafka musu kerarren gida,
motoci an
kuma bawa alhaji abdulhamid jari
mai tsoka yana
juyawa itakuma hajiya nana ta fara karatunta na
law a jami'a bayero ta kano. Allah
ya albarkacesu
da ya'yahudu, uku maza mace daya
itace autar.
Wacce ahalin yanxu ko yaye ta ba ayi ba karama
ce.Babban shine yaya habib yanzu
yana da
shekaratalatin , mai binsa shine
abdulhamid ake
kiransa da haisam yanzu yana shekararsa ashirin
da shida mai binsa iziddeen
shekarunsa ashirin da
uku. Sai da iziddeen ya gama
sakandire ya shiga
jama'a sannan aka yi masa kanwa mai shekara
daya anakiranta da amratu.Girma
yazowa alhaji
abdulhamid da matarsa amma
kumakarfi ya
tasamma ya'yansa zasu iya kula da dimbin dukiyarsada kamfanoninsa
yaya habib ya
kammala digirinsa a jamia'ar a.b.u ya
karanta
business admin a yanzu yana aiki a
kamfanin babansa shine kuma mai zurga zurga
zuwakasashe daban daban na shige
da fice da
kayan kamfanonin.Haisam wanda a
shekarar nan
ya kammala karatun jami'a yakaranta
geography yanzu yana bautar
kasa a
f.g.g.kazaure da zararya gama
kujerarsa ta aiki
nanan na jiransa a dayadaga cikin kamfanonin
mahaifinsa. Na uku wato
izziddenyana shekara
ta uku (level 3)a jami'ar bayero ta
kano yana
karatun law don yagaji mahaifiyarsa wato barista
nana wacce itace babbar lauyar
kamfanonin . Tana
kuma farin cikin ganin dayadaga
cikin'ya'yanta ya
taso gadan gadan da karatun law wanda a
cikin'yan shekaru kalilan zai gama ya
zama
cikakken lauya ya canjeta alhaji
abdulhamid ya
dankawa yaya habib ragamar aiki ya koma gida ya
zauna yana hutawa sai
dai yajekamfanonin fisha
yaga yadda aiki yake tafiya yakoma
gida.Dan lelen
abba da umma wato haisam shine yafi kowa shagwaba a gidansu ko
kuma nace shi
akafi shagwabawa tunyana kankani.
Amma ai
izidden ne yakamata yayi shagwaba
kasancewarsa ya dade yana auta kafin ayi
masa kanwa ammashi
yana gefe tun suna yara haisam ne a
kancinyar saboda tsananin biyayya,
ladabi , tausayi
da jinkai irin na haisam shine ya kara masa fada a
wajen mahaifansa sunfisha'awarsu
zauna suyi hira
da haisam sau dubu da suyi
Da yayansa habib tun
suna yara saboda haisam yake magana acikin
nutsuwa yake kalamansa masu
muhimmanci
akoda yaushe fuskarsa cike da
annuri(fara'a),wasa
da dariya damanya dayara. Bashi da raini ga
hakuri , baya ga zunzurutunkokari da
Allah ya
bashi a bangaren karatunsa dukka
akur'ani da
bokon yasan alkur'ani kamar me a kansa duk
gidansu babu mai iliminsa. Hatta
mahaifinsa yakan
yi masa tambayoyi akan duk wata
matsalarsu ta
addini ko ta zamani, yana datsananin hakuri sau
tari ana masa abu da yawa yayi
hakuri.Ammakuma duk gidansu babu
mai zuciya
kamarsa idan aka kureshi, idan yayi
fushi abin babu kyau mai hakuri bai iyabacin rai
ba.Da farko a
enugu state aka turashi bautar kasa
(n.y.s.c)kasancewar shakuwa da
sabon da
mahaifansa suka yi dashi basa so yayi musu nisa
don haka alhaji abdulhamid yasa
adawo dashi
kurkusa saboda yasan manya
manyan kasar
nandaga yan boko har rukakkun yan kasuwa.
Ammaduk da haka haisam yana
korafi shifa
kazaure yayi nisa da kano a
dawodashi cikin kano
inda kullum zaina kwana gida, dakyar dai
akablallasheshi yayi hakuri duka duka
bazai yi
shekaradaya ba zai gama ya dawo
gida gaba
daya. Don haka duk juma'a yaketafiya gida wani
lokaci ma a kanon yake yin
sallar juma'a saivlahadi
da yamma ake dawo wa dashi. Gashi
yanzuma
baifi saura wata uku ba ya kare bautar kasa
kwatakwata ma yakoma inda yake
muradi.Bayan
tafiyar hanne gidan uwar biyu da
kwana uku wato
ranar laraba da sassafe sai ga wata mota an kawo
hanne makaranta haisam ya roki wani
abokinsa
safiyanu yaje cangidan uwarbiyu ya
dauko hanne
da kayanta ya kawotamakaranta. Haisam ya gama
mata siyayyarta kakaf ko
yaran attajiran makarantar
baza su fita kaya ba
(provision)kayanmakarantarta
(uniform)suma har kala kala bibiyu yayi
mata takalma kuwa kala kala akwai
kito, sandal ,
kambos fari dabaki tsadaddu, silifas
dan madina
har biyu, ya siyo mata dawasu yan kanti riga da
siket suma kala biyu. Yasuyo
matajakar zuba kaya
mai kyan gaske yar madaidaiciya
wato(travelling
bag)a ciki aka zubawa hanne kayansawarta, nata
nada kuwa yana gidan uwar biyu,
kayan tande
tande damakulashe kuwa abun baya
lissafuwa
kama daga biskit kalakala, alewa (chocolate)indomie, madara,
milo,sugar
,complakes da dai sauransu ko garin kwaki
babu balle
wani kanzo irin na yan makaranta
makilin da brush hadaddu, mayukan shafawa da
sabulansu
masu kamshi gamayukan gashi cike a
akwatin Hanne
sanye take da kayan makaranta
(uniform)kafar ta kumafarin kambos ne da farar safa
an tufke kitson
kantada waniribom mai kyau mai
fulawa, duk
wanda yaga hanne kwanakibiyu da
suka wuce a yau dai bazai gane taba tayifari
kyal kamar yar
larabawa, ashe mai dangwali yaba
nebda
bakin kwalli suka cabe mata fuska
tayi baki kirin. Safiyanu yazobakin offishin malamai
ya tsaya da
motarsa sannanya fitodaga ciki ya
juya ya kalli
hanne wacce ke zaune abaya
tanakokawa da murfin kofa ta kasa budewa abunka
Da
Yar kauye.Wannan ne karo na farko
da hanne ta taba hawa irin wannan motar
don haka bata san ina
zata ja kofa ta bude ba. Safiyanu yazagayo dasauri
ya bude
mata, ta fito yace'' to dauko jakar
litattafan
nakimana'' hanne tasa hannu ta
jawo wata bakar jaka(schoolbag)tsadadda mai kyan
gaske, yar
madaidaiciya daidaibayanta cike
take da kitattafan
rubutu da litattafan karatu
(textbook)duk dai kamar yadda aka zano ajikintakardar
babu wanda haisam
bai siya mata ba ga biruka da
fensir da mathematical set din su ya
siya mata .
Safiyanu ya nunawa hanne yadda zaya rinka
ratayawa a bayanta tarataya
suka nufi cikin ofishin.
Suna shiga suka iske wani
malami bayan safiyanu
ya mika masa hannu sun gaisa sai yayi masa
bayanin abinda ke tafe dasu yace
daliba ya kawo,
sai yanuna masa ofishin vice
principal yace nan
zasu shiga.sukayi sallama suka shiga suka iske
vice principal yanaharhada wasu
takardu a
gabansa, bayan sun gaisa safiyanu
yashaida masa
cewa yarinya ya kawo yar aji daya ce sabuwar
zuwa sai ya nemi daya bashi
takardar shaidar
cewar ita dalibarnan makarantar ce
wato(joining
instruction)daman haisam yabashi ya dauko ya
mika masa ya duba yace''sunanta
hanne habu
imamu daga babban mutum ko ?
Safiyanu yace
''eh,''vice principal din nan ya kurawa hanne ido
yana kallonta zuciyarsa cike da mamaki
ga yarinya
kyakkyawa kamar baturiya gashin
kanta har baya
duk dama antufkemata da ribon amma
kuma sunnan kauyawa gareta gata
kuma daga
kauye. Ya ce a ransa'' wata kila dai
asalin
garinsune babban mutum din amma daga birni
take, can yanisa yace''babu komai,''
ya jawo wani
littafin rasitai ya budeyace
da safiyanu'' sai ku
bibbiya kudaden in baku rasitai dasauri don yanxu
lokacin assembly ne, don taje ta
shiga
cikin dalibai ayida ita. Vice principal
ya lissafawa
safiyanu yawan kudaden dazai kawo safiyanu ya
dauko ya bashi, shi kuma yana
rubuta rasitai har
ya biya kudin komai '' sannan
yafadi
sunan dakin da zata je, sannan zata je j.s.s. 1A
ajin malam haisam sunan ajin, yanzu
ka kaita hall
ayi assembly da ita,kayanta kuma a
barsu a nan
bakin staff room ana tashi tazo zamu samaigadi da
prefect din dakin suje ta bata
gado.Safiyanu ya
ce''to'' yayi godiya suka fito yana
sake yiwa
hanne bayani akan abinda vice principal ya ce,
yana kuma kara lallashinta
ganinyadda nan da nan
ta canja hankalinta yayimummunan
tashidaga
shigar su ofishin vice principal duk kwalla tacika
mata ido saura kiris ta fashe da
kuka. Yace mata''
kar kiyikuka nanmakaranta ce
karatu kawai za.a
koya miki babumai zaginki balle duka kinji. Gashi
ajin malam haisam za,a kai ki don
haka baki da
matsala zai kula dake''suna tsaye a
bakin baranda
yana yi mata nasiha saiga viceprincipal ya fito
daga ofishinsa zai tafi hall
wajen assemble yyace'' ah
har yanzu bata tafi assembly ba ai
gara kuyi
sallama ta tafi,'' safiyanu yace '' aima shikenan
mun gama daman hall din zan
tambaya don bamu
ganshi ba,'' vice principal yayi musu jagora har cikin
hall din yashige
da hanne a lokacin principal tana bayani hall din
yayi tsit kowa yana sauraro. Amma
daga shigowar hanne da
vice principal
sai kowa
hankalinsa yakoma ga kallon hanne.
Hanne ta zama yarinya ''yar dagwas 'yar
karama maikyan
gaske akwai dubbunan dalibai a
makarantar daga
jahohi daban daban amma babu mai
kyawun hanne wato kamar wata tauraruwa ce mai
haske a cikin
taurari. Sai sheki take da farar
fatarta hanci har
baka, ga dan karamin baki,gazar
gazar gashin gira dana ido fatar jikinta luwai luwai
irintayan
hutu amma ita dai daga innallahi ne. Ga
ido dara dara
bata da kibakuma bata cika tsaho
sosai ba gata dirarriya duk dadaikarama ce
masassakin budurci
bai fara sassakataba. Wasukitso ne
yiri yiri aka
yarfa mata kamar bada hannu aka
yisuba. Hanne tayi kyau kwarai da gaske a
cikinkayanmakarantar
nan ga 'yar jakar litattafanta a
baya.Babu
wandazai kalli hanne bai sake
juyowa ya kalli halittar ubangiji ba.Dalibai
manyansu da yaransu
babu wacce bata cedama
nicewannan ba ko kuma
ace 'yata ce a ransu ba.
Hatta haisam wanda ke tsaye a bakin kofa bai gane hanne
bace. Suka zo
sukawuce ta gabansa ya bita da
kallo sai dai a
zuciyarsa yaketambayar kansa da
kansa ina nasan wannan yarinyar?Tabbasa na santa
a wani waje,
sai daga baya zuciyarsa ta bashiamsar
cewa wannan
itace hanne habu kenan.
Yayi matukar mamakin ganin yadda hanne ta koma haka a
kwanabiyu,hanne ta tsorata ta kuma
rikirkice
ganin dubbunnan idanuwa caa a
kanta, ta tsaya
cak, ta kasa tafiya tana shirinfashewa da kuka.Vice
principal yayi kiran wata prefect
dake tsaye agefe
yace tazo ta kaita layin 'yan j,s,s
1A. Tazo ta
kama hannun hanne takaita layin ajinsu ana ci
gaba da assembly kamar yadda
sukasaba. Bayan
principal ta gama jawabinta,
vice principal ma ya
fadi albarkacin bakinsa sai aka nemi sauran malamai sucewani abu akan
dokar
makaranta. Bayan sun gama aka
yi national pledge
kowa ya kama gabansa, ya
nufi ajinsu. Hanne ta tsaya cak a inda take tsaye tana
kallon
dalibai kowa yanatafiya ajinsa ta
rasa ina zata
nufa. Haisam ya matsokusa da ita
yace'' hanne yaya kika tsaya bakya ganin kowa
yanufi ajinsu ke
kika tsaya idan baki sani ba, ba sai
ki tambaya
ba.To nan makaranta ce kowa ta
kansa yake, gara ki rinkatambayar duk abinda baki
sani ba, muje in
nuna miki ajinnaku, hanne tace'' to''
ta bishi suka
doshi bangaren da ajujuwa suke yaci
gaba dayi mata nasihohi akan kada ta sake ta
zama wawuya,
idan bahaka ba sai sauran dalibai su
raina mata
wayo tazama duk abunda bata sani
ba ta tambaya musamman idan malami yana darasi
idan bata
ganeba tayi masa tambaya.Hanne
nasauraro da
alama kuma nasihohin suna
shigarta.Haisam ya kalleta yayi dariya ya ce'' hanne ince
kin
zama cikakkiyar daliba babu wannan
damarar?
Hanne ta kyalkyaleda dariya haisam
yace'' to tunda kin zama yar birni 'yar bokomai aji to
yanzu komai
naki zai koma na aji, kin san
abundanake nufi?
Hanne tace ''a'a'' yace to sunanki zai
tashi daga HANNE HABU IMAMU ZAI
KOMA HANNAH
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 5
Kowa ya tambayeki yaya sunanki sai kice... Kafin ya fada Hanne cikin murna da farin ciki ta ce "Hannah Abubakar Imam.
Haisam ya tuntsire da dariya ya ce "Harma kin rike sunan kenan? Hanne ta ce "Eh, Hannah yafi dadi Allah. A dai-dai wannan lokaci suka hau barandar ajin. Haisam ya wuce gaba ya shiga ajin Hannah na biye dashi a baya. Suka shiga dukkan daliban ajin suka mike tsaye don girmama Malaminsu suka hada baki dukkan su "Good morning Sir" Haisam yayi murmushi ya ce "Morning student, how are you? Suka sake hada baki suka ce "We are fine Sir, ya ce "Thank you sit down. Kowacce ta zauna akan kujerarta. Haisam ya jawo Hannah gaban aji ya ce "Ga wata sabuwar daliba kun samu. Rauda ita ce monita ta mike tsaye ta ce "Lah, what is your name? Hanne ta daga ido tana kallon Haisam, ya harareta ma'ana ta bada amsa, Hanne ta ce "My name is Hanna Abubakar Imam. Kamar yadda Haisam ya ce ta dinga fada. Nusaiba wacce ita ce mataimakiyar monita ta ce "Ehm, nice name your are welcome Hannah. Haisam yayi murmushi ya ce "Kun fara iyayin naku ko? To maza ku saka mata kujerarta a tsakiyar ta ku a gaba kuma kunga ita yar kucilace kamar ku. Cikin sauri Rauda taje bayan aji ta dauko kujera ta kawo ta koma ta dauko tebur tazo ta dasa a tsakiyar su a jere. Dake su duka ukun kansu daya sune yan kananan ajin sunfi kowa kankanta kasancewar akwai dingin-dingin din yan mata a ajin, musamman kabilun nan wata sai ka rantse uwa ce amma yar aji daya ce.
Farin ciki ya lullube Hannah da Haisam musamman ma Haisam yaga Hannah ta samu shiga wajen Nusaiba da Rauda wadanda su suka fi duk yan ajin kokari dan Rauda a America tayi karatun nusery da primary dinta don haka tana da bala'in kokari ga turanci daya kama bakinta. Hausa ma tana kokarin ta subuce mata. Kuma Yayanta Auwal abokin Haisam ne na kut, Babanta Alhaji Shitu abokin Baban Haisam ne, sannan Ramla yayarta ita Haisam zai aura don haka nema aka kawo Rauda makarantar saboda Haisam yana nan tazo akayi mata jarabawa ta ci shikenan aka dauketa, don haka nema take kiransa da Yaya Haisam sabanin Uncle Haisam kamar yadda sauran dalibai suke kiransa.
Nusaiba ma wata tsadaddiyar makaranta ta gama a Abuja. Ita yanzu haka ma Iyayenta suna Abuja karatu ya kawota nan amma haifaffun garin Gombe ne fulani. Rauda da Nusaiba sun zama kawaye tun ranar da suka hadu a ranar da aka kawosu makaranta, ajinsu daya suka kuma ci sa'a dakinsu daya, don haka ga gadon Rauda gana Nusaiba kuma sun hada kayan akwatinsu. Haisam ya ce "Monitor da Mataimakiyarta ku biyoni waje ina da magana daku. Rauda da Nusaiba suka mike suka bi bayan Haisam wajen aji.
Hannah na zaune babu abunda take kallo sai kallon ginin ajin da dalibai daya bayan daya taga kowacce sanye da uniform dinta tsaf-tsaf, fararen takalma kambas da fararen safa kan kowacce kitso ne tar. Hannah ta ce a ranta "Ashe da nasha kunya da ace a ranar da Baba ya kawo ni a haka na shigo ajin nan da na fita daban. Kai wannan Malami ya taimake ni Allah Yayi masa albarka. Ta ci gaba da kallon ginin ajin da irin zane-zane da akayi a takarda duk an lillika a jikin bango ga fankoki a jikin silin sunata fitar da sassanyar iska. Ginin bulo "Hannah ta fada a fili ba tare da tasan a baiyane ta fada ba.
Bayan fitar su Haisam a bayan aji suka tsaya ya kalli Rauda ya juya ya kalli Nusaiba ya ce "Rauda, Nusaiba. Su duka suka amsa ya ci gaba da cewa ga Hannah nan, kamar yadda Rauda kike kawar Nusaiba to Hannah ta zama kawarki itama, sannan kamar yadda ke Nusaiba kike kawar Rauda to ina son Hannah ta zama kawarki. Duk da ku biyu dakin ku daya to Hannah ma yar dakin kuce. Dake Safiyanu ya fada masa sunan dakin Hannah. Ya ce don haka ku uku dakinku daya, ajinku daya.
Kamar yadda a ko ina kuna tare, a hall ne a daki ne to Hannah ma ta zama kuna tare ita ma kanwata ce kunji ko? Su dukka suka amsa. Nusaibah ta ce "Uncle Haisam ko baka ce mu zama kawaye ba daman zamu zama tana burgemu Haisam yayi dariya ya juya ya kalli Rauda ya ce "Kanwata ke baki ce komai ba ke bata burgeki? Rauda ta tabe baki ta ce "Yaya Haisam rannan fa ka ce nice kadai kanwarka a makarantar nan yanzu kuma ka ce ita ce.
Haisam ya kyalkyale da dariya ya dafa kanta ya ce "Rauda kenan, ai har yanzu kina nan a matsayinki na kanwata, itama Hannah yar uwata ce kinga dole kanwata ce, Nusaiba ma kanwata ce don haka karki damu. Gata nan duk abunda bata sani ba akan karatu ku koya mata. Haka kuma magana da turanci ku rika tunasar da ita koda ta manta ta yi Hausa karku rubuta sunanta a masu yin Hausa sai a hankali zata saba itama ta ringa yin turanci sosai. Haka a daki idan bata san yadda zata yi amfani da wani abu ba kamar man gashi in zata shafa a jiki ku nuna mata na gashi ne ba ku ringa yi mata dariya ba kuna gayawa kawayenku kunji? Musamman ke Rauda kinga su Rose suna yawan kawo mun kararki wai kina yi musu tsawa kar in sake ji kina yiwa Hannah kinji ko? Rauda ta ce "Yaya ya za'ayi ta shafa man gashi a jiki sai kace bakauyiya. Haisam ya ce "A'a wai a misali nake nufi, koda a ce zata manta ta dauko man gashin.
Tafiyar wani Malami ce tasa duka hankalinsu ya juya baya don ganin mai tahowa, Haisam ya ce "To shikenan ku koma aji ga Malam Shaiya nan zai koya muku Maths an kada first period. Suka ruga aji a guje, Malam Shaiya ya mikawa Haisam hannu suka gaisa sannan ya nufi S.S.3C yana da period yana koya musu Geography.
Kamar Haisam yayi duba, da ya ce idan ta dauko man gashi zata shafa a jiki haka kuwa aka yi. Hannah babu abunda ta sani a kayan akwatinta, daga ta dauko man wanke gashi (shampoo) ta kwaba a jikinta sai ta dauko man shafawa ta maka akanta, makilin ma wani lokaci a tsagar kitso Rauda tazo ta isketa tana sharbawa. Suyi ta dariya har su godewa Allah daga karshe dai suyi mata bayani dalla-dalla, wannan ne na kaza wannan kuma a waje kaza ake shafawa. Babu laifi a sati biyu Hannah ta waye ta gane da duk kayayyakin amfani na zamani sannan ta koyi cin kayan gwangwani dana kwali, don da farko idan suka dama comflask da madara cokali daya zata yi sai ta fita a guje ta kelaya amai bata sanshi ba. Haka sadin da gesha kifin gwangwani sai taki ci tace tsutsa ce amma daga baya duk ta waye tana ci.
Hannah tana farin ciki matuka da wannan sabuwar rayuwar data tsinci kanta. Abinci lafiyayyu a akwatinta na makaranta, gashi tana cikin yara sa'aninta suyi karatu tare suyi wasa tare musamman Nusaiba tana bala'in kaunar Hannah tafi Rauda kirki don Rauda ta cika nuna isa da nuna tafi kowa kuma duk girmanka sai ta ringa daka maka tsawa. A fannin karatu kuwa ada Hannah dumame kujera take yi kawai saboda tsantsar turanci ake yi a makarantar amma sai Nusaiba ta lura da Hannah bata fahimta don haka a koda yaushe bayan Malami ya gama darasinsa sai ta matso da kujerarta har kusa da ta Hannah tayi mata bayani dalla-dalla. Haka shima Malam Haisam kullum a prep din yamma yana zuwa ya kira Hannah ya koya mata abubuwa da dama. A wata daya Hanna ta fara gane turanci fiye da yadda kuke zato.
Ranar wata asabar da daddare ranar ne ake warewa dalibai su shakata su hole rayuwarsu kamar a saka musu kidan disko su cashe wasu kuma su kada tebur da kansu suna waka wasu rawa. Wasu kuma talabijin ake kunnawa da bidiyo suyi kallon kaset duk dai abunda ransu keso shi zasu yi. Daga *yan J.S.S 1 har zuwa *yan S.S 3 wannan rana ita ake kira da "SOCIAL NIGHT" Uncle Haisam kuma shine social master wato shine Malamin da yake kula da dalibai, yake kula da C.D din da ake kunna disco da bidiyo da talabijin din da ake kunnawa. A wannan dare an yarjewa dalibai su saka kayansu na gida (personal) kowane iri ne kama daga leshi ko shadda riga da siket kai har jeans da tee shirt duk zasu iya tsukewa.
Rauda Sarkin rawa ita har tunanin wannan asabar din wacce irin rawa zanyi don har fili ake bata kowa ya koma gefe yana kallonta rawa salo-salo har wasu suke kiranta Jenet Jacson wai kanwar Micheal Jecson.
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter6
Nusaiba kuwa ita da Hannah babu abinda suka fi so irin kallon bidiyo Hausa fim masu kyau Malam Haisam yake samowa ko Nigeria firms. Social night din wannan asabar din bata yiwa Hanna da Nusaiba dadi ba saboda bidiyo ta lalace babu kallo sai dai C.D aka kunna aka ware kida duk mai bukata yaje ya cashe wasu na rawa wasu kuma na gefe suna kallo.
Amma wasu suna kan barandar wajen Hall din a zazzaune basa sha'awar yin rawa ko kallon masu rawa. Kungiya-kungiya kowanne da group dinsu suna waje suna zazzaune suna hirar duniya. Hanna da Nusaiba suna daya daga cikin wadanda basu shiga cikin Hall din ba wajen kida suna zazzaune a can wata barandar ofishin Malamai suna hirar duniya, hirar ma jifa-jifa suke yi saboda duk rayukansu a bace yake yau babu kallo. Kuma wani hadadden American film mai suna "Mr bones" Uncle Haisam yayi musu alkawarin zai saka musu. Nusaiba tayi ajiyar zuciya ta ce "Anya kuwa yau zan iya bacci saboda bakin ciki na kudiri niyyar ganin film dinnan, wallahi fim din akwai abun dariya muna dashi fa a gidanmu.
Hannah ta ce "Na last week ma yayi kyau ga abin dariya sosai "Osofia in London" Yaya Haisam ya iya zabo mana films masu kyau. Wata murya ce a bayansu tace na kama ku kuna gulmata. Suka juya da sauri sai suka ga Yaya Haisam ne su duka suka tuntsire da dariya ya zagayo suka matsa masa ya shiga tsakiyarsu ya zauna yayi murmushi ya ce "Kuna gulmata ko, dan yau bankunna muku kallo ba ko? Nusaiba cikin shagwaba ta ce "Yaya Haisam har kwalla nayi fa wallahi yau duk ranmu a bace yake. Yayi dariya ya ce "Kai haba harda kwalla? Ke fa Hannah kema kin yi kukan? Tayi murmushi ta ce "A'a banyi ba Uncle Haisam. Ya ci gaba da jansu da hira yana zolayarsu kamar yadda ya saba wasa da dariya da dukkanin daliban makarantar musamman da wadannan ukun. Ya ce da su "Ga Rauda can a Hall tana cashewa kuje ku tayata mana ko kuma kuyi mata liki. Suka yi dariya suka ce "Mu bama rawa, suka ci gaba da jigum. Haisam ya lura yau dai Nusaiba da Hannah babu kanta basa son magana balle doguwar hira ya ce "Nusaiba, Hannah yaya haka kowacce tayi zugum babu nishadi kamar yau ba ranar social night ba. Nusaiba ta ce "Yaya Haisam tsabar bakin cikin rashin kallon nan ne yake damunmu. Ya ce "Shi yasa baku fara'a? To yanzu daya bayan daya sai kun yimin waka da rawa tunda yau social night dole kuyi murna.
Cikin shagwaba Nusaiba ta ce "Yaya ni ban iya waka ba sai dai Hannah ta fara
tunda ita ce karama. Haisam ya kalli Hannah wacce ke murmushi har yanzu ya ce "Kinji wai inji Nusaiba ke za ki fara kece karama. Hannah tayi dariya ta ce "To bari inyi muku wakar Sarkin garinmu, Hanne ta fara tafi ta fara rero waka. Haisam ya ce "To tsaya tafi akeyi muma mu dinga tayaki muna miki amshi? Ta ce "Ai da kwarya ake kidan dan dai babu kwaryar ne.
Yasa hannu a aljihu ya zaro wannan abun busar daya karba a wajenta ya ce zai ajiye mata. Ya ce "Ga abun busarki ma ki busa mana ki kuma rero mana wakar kiwo. Cikin farin ciki Hannah ta karbi abun busarta ta hau jujjuyashi tana cewa "Allah Sarki abun busata na dade ban busa kaba, Nusaiba ta ce "Lah busa muji yadda ake yi. Hannah ta kaikaice ta fara busa abun busarta tana rera waka kamar haka.
Muyi kiwo samari, kuyi kiwo yan mata.
Kiwo baiwa ne, waka baiwa ce, haka busa ma baiwa ce.
Kuyi soyayya samari, kuyi soyayya yan mata.
Ke yar budurwa ina naki gwanin?
Ni nawa gwanin baya nan, yayi tafiya.
Amma koda bana tare da gangar jikinsa, ruhinsa yana tare da ni.
Haisam ya ce "Hanna tsaya meye koda gangar jikinsa bata tare dani ruhinsa yana tare dani? Tayi shiru can ta ce "Oho nima haka ya koya mun wakar, Nusaiba ta ce "Meye ruhi? Hannah ta ce "Nima ban sani ba, ina jin larabci ne.
Haisam yayi dariya ya ce "Yarinta mai dadi.
Kwanci tashi yau kwanan Hannah arba'in a makarantar har an kafe musu time table din jarabawa wato end of 1st term examination kasancewar daman dalibai sai da suka yi kimanin wata guda da dawowa makaranta sannan aka kawo Hanna. Babu abunda Yaya Haisam yake yi sai nasihohin da yakema yan ajinsa wato J.S.S 1A da kowaccensu ta cire wasa tasa littafin karatu a gaba don suci jarabawa. Haka kuma a wasu lokutan kan kira kannansa Rauda, Nusaiba da Hannah yana kara yi musu fada dasu dage sufi kowa cin jarabawa ya sake cewa "Hanna bana jin fargabar su Rauda kamar ke don haka ki dage duk abunda ba ki sani ba ki tambayi Nusaiba ko Rauda idan sun sani su koya miki, idan kuwa basu sani ba to kuzo ku tambayeni.
Haisam yayi musu rantsuwa da Allah a cikin su ukun nan duk wacce ta fadi jarabawarta sai yayi mata bulala kuma daga ranar data fadi jarabawa babu ruwansa da ita ya cireta a cikin kannensa. Gaban Hannah ya fadi ras dajin bayanin Yaya Haisam ta ce a ranta "Idan Yaya Haisam ya ce babu ruwansa dani aina shiga uku tunda babu mai yimin siyayyar makaranta karshenta ma karshen karatunta ya zo. Ta kudiri aniyar daga yau babu ita babu cikakken bacci zata dage da karatu don taci jarabawa, kada Haisam yayi fushi da ita.
A sati daya su Hannah suka gama jarabawarsu, jarabawa bibbiyu suke a rana daya. Don haka babu hutu ba dare ba rana kowacce ta dukufa da karatu, musamman Hannah sallah ce da cin abinci yake tashinta daga kan littafin karatunta, haka kuma ta zana jarabawar cikin sauki ma'ana da an bata question paper sai taga tasan amsoshin gaba daya. Haka take amsa su cikin sauki saboda tsabar ta gama karance Littattafanta. Hannah tasan Yaya Haisam zaiyi murna da sakamakon jarabawarta tunda tayi karatu yadda ya kamata. Hutu kuma sai wata juma'a don haka dukka wadannan ranakun babu abunda suke yi sai wasanni da raye-raye da wasannin kwaikwayo na kungiyoyi (club) din makarantar kamar English club, Hausa club, Jet club, Chemical club, Geography club, Yoroba, Igbo da dai sauransu, kuma kowacce daliba daga yar aji daya zuwa shida tana da damar da zata shiga kowanne club a makarantar. Su kuwa Malamai cikin satin nan suka dukufa da aikin making jarabawar dalibai don ganin kafin ranar hutu sun bawa kowacce daliba sakamakon jarabawarta ta tafi dashi gida Iyayenta su gani.
Ranar alhamis ana gobe hutu Haisam ya tara yan ajinsa a bakin babban dakin taron dake makarantar wato Hall don ya bawa kowacce sakamakon jarabawarta (report card). Yan ajin Malam Haisam suna da dinbun yawa don dalibai saba'in da shida ne a ajin Hausawa da Yarbawa, Igbo Musulmai da kiristoci sama da talatin, wata ko zo bata sani ba da Hausa, tun daga kudu suke babu abunda suka saka a gaba sai karatun littafinsu don shine abunda ya kawo su tun daga can uwa duniya zuwa nan kenan. Don haka babu koma baya a ciki kowacce tayi iya kokarinta matuka a wannan Jarabawa.
Haisam ya kalli fuskokinsu daya bayan daya sannan ya kyalkyale da dariya. Abun mamaki babu wacce ta taya shi dariyar kamar yadda suke wasa da dariya a aji ayau kowacce fargabar jin sakamakon jarabawarta take, musamman ma Hannah.
Tashin hankali ne mara fasaltuwa a zuciyarta tunanin maganar da Yaya Haisam ya fada yayi musu rantsuwa ya ce duk wacce ta fadi jarabawa sai yayi mata bulala kuma babu ruwansa da ita.takeyi Hakika bata fargabar bulalar sosai tafi fargabar babu ruwansa da ita din daya fada, idan Haisam ya cire hannunsa akan Hannah waye kuma zai tsaya mata, a duniya yadda take son makarantar nan aiko hutu bata so ayi wato Hannah na daya daga cikin yan kwaleji tafi gida dadi. Abunda take ci tasha da makwancinta yafi na gidansu, ga uwa uba kwanciyar hankali wasa da dariya da kawayenta, sabanin a gidan su sai bauta, anan makaranta ma akan sasu aiki ko aike amma ba mai wahala ba kasancewarsu kanana yan aji daya dole senior zasu aikesu.
Haisam ya ce "Oh! Yau babu dariya duk kunyi cirko-cirko kuna jiran sakamako to da yawa daga cikinku kun yi kokari amma wasu basu yi kokari ba don haka wadanda basu yi kokari ba sai sun dage idan ba haka ba karshen shekara za'ayi musu repeating kowa ya wuce aji biyu a barku a aji daya ku sake maimaita shekara.
Gaban Hannah ya sake faduwa ras sai addu'a take sannan ta ji dan saukin dukan da zuciyarta take yi mata. Haisam ya ce "Yanzu zan fara kiran sunan wadanda suka yi na daya zuwa na uku sai a tafa musu zan kuma basu kyaututtuka. Sannan na kirawo na hudu zuwa goma suma zasu fito a tafa musu sune suka fi yin kokari, sauran kuma sai ku dage nan gaba. Hadiyar yawu yake ji mukut-mukut dalibai nayi don faduwar gaba dariya ta sake kecewa Malam Haisam ya girgiza kai, sannan ya bude file din dake hannunsa ya ce "Dalibar da tayi matukar kokari ta zo ta daya ita ce Rauda Shitu Muktar. Rauda ta kwalla kara don dadi sauran suka sa tafi suka juyo suna mata kallon sha'awa kowacce a ranta tana dama nice Rauda Shitu a ransu.
Haisam ya ce "Taso, fuskarta cike da fara'a zuciyarta cike da farin ciki ta zo ta tsaya gefen Haisam ya ci gaba da cewa, "Sai kuma wacce ta zo ta biyu ita ce Nusaiba Idris. Farin ciki ya lullube Nusaiba itama ta mike tazo kusa da Raudah Shitu ta tsaya dalibai na yi mata tafi raf-raf, ta uku kuma ita ce Pammella Matin Benin. Pamella ta daka tsalle don murna ana tafa mata ita ma ta fito tazo ta tsaya a kusa da Nusaiba Idris.
Hannah na lungu ta kankame gwiwarta da hannayenta ta zura kanta a matsematsin cinyoyinta yayin da kuka ya kece mata. Taga kawayenta biyu Rauda da Nusaiba wadanda suke karatu tare sun zo sun fita kokari. Ta gama saddakarwa Yaya Haisam ya cire hannunsa daga kanta tunda bata yi kokari ba. Haisam ya rufe file din dake hannunsa ya kalli sauran daliban da suke zazzaune a kasa ya ce "Kunga wadannan ukun sunfi kowa yin kokari a ajina don haka zan basu kyaututtukan da zasu je gida su nunawa Iyayensu suji dadi,
Masu yin comments godia nake Allah yabar zumunci
Marasa yi kuma!!! Kuje kune a qasa
Yanzu fa aka fara muje zuwa
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter7
bawai su daban suke da ku ba a'a kuma kowacce a cikinku ta dage zata iya zuwa na daya, biyu da ta uku. Don haka duk wacce take so itama next term taji sunanta a cikin wadannan ukun to ta dage da karatu, don haka ku sake tafawa Rauda da Nusaiba da kuma Pamella. Tafi raf-raf ya dinga tashi saida Haisam ya ce ya isa tukunna suka daina. Ya dauko wata katuwar anbulam wacce aka like ta da salatif an yi rubutu da maka dara-dara kamar haka:
FIRST POSITION IN J.S.S 1A
RAUDA SHITU MUKTAR.
Ya mikawa Rauda, daliban suka tafa mata raf raf ya ce taje ta zauna. Ya sake dauko wata wacce girmanta bai kai girman na Rauda ba, itama an like jikinta da salatif an rubuta.
SECOND POSITION IN J.S.S 1A
NUSAIBA IDRIS.
Ya mikawa Nusaiba aka tafa mata ta tafi ta zauna itama. Ya dauko ta karshe itama girmanta bai kai ta Nusaiba ba, a jikinta an rubuta.
THIRD POSITION IN J.S.S 1A
PAMELLA MARTINS BENIN
Aka tafa ta karba da murna ta tafi ta zauna, Haisam ya ce "To yanzu zan kira na hudu zuwa na goma suma su fito nan su tsaya a tafa musu don suma sunyi kokari matuka. Fargaba ta sake dira a zuciyar Hannah. Ta ce a ranta "Idan kuma bana cikin mutane goman nan ni kaina nasan banyi kokari ba, shikenan karshen makarantata yazo don nasan tunda Malam Haisam ya rantse nasan da gaske yake sai ya zaneni sannan ya korani gida saboda tsananin da ake mata da azabtarwa. Baya ga bautawa ga horon yunwa, babu wanka ko tayi wankan ma kusan daya ne da bata yi ba don wankan babu sabulu, sai wani lokaci ne idan tayi wanke-wanke idan omo yayi saura take boyewa tayi wankan dashi shima a sati baifi sau daya ba. Anan kuwa sunkinan sabululai Haisam ya siya mata. Ga mayukan shafawa iri-iri masu kamshi, ga man gashi, dake ita daman gashinta ba irin kalar kitso bane ko tayi kitson kwana biyu zai fara zamewa. Amma yanzu da ta sami mayuka masu sa gashi yayi laushi sai take wankewa da man wanke gashi ta mulke shi da man gashi tasa ribon ta daure tamkar na indiya. Baki sidik a kwance fatar jikinta tayi fayau luf-luf sumul-sumul kamar ba ita ba, ita bata ki har shekara shida ba'a yi hutu ba.
Malam Haisam yaci gaba da kiran daliba ta hudu, ya kira ta biyar, ta shida Hannah ba ta ji sunanta ba, ya kira ta bakwai da ta takwas. Sai kukan da take ya kara tsananta har na kusa da ita suka fara jiyo shesshekar kukan da take yi suna juyowa suna kallonta, Haisam ya kira ta tara sannan ta goma ya ce "Hannah Abubakar Imam. Shima sai da yayi ajiyar zuciyar jin dadi. Hannah ta mike ta taho idonta tamkar anyi wasan ruwa kaca-kaca da hawaye. Haisam ya dafa kanta ya ce "Hannah kukan meye haka kike shesshekawa lafiya? Yi shiru goge hawayenki kinzo ta goma kinyi kokari. Dadi da kwanciyar hankali suka lullube Hannah, yasa aka dinga tafawa daliban da zuka zo na hudu zuwa ta goma. Daga karshe ya ce su koma su zauna ya ci gaba da kiran dalibar data zo ta goma sha daya zuwa ta saba'in da shida ta karshe kenan wata gandamemiyar ajin ce tafi kowacce girma a ajin mai suna Eneka Eddiward ita ce ta zo musu ta karshe. Da yawan dalibai suka rushe da kuka jin Malam Haisam ya furta repeating suna tunanin shikenan za'ayi musu repeating, Haisam ya shiga lallashinsu yana cewa kowacce tayi kokari babu wacce za'ayiwa repeating kasancewar da sauran damar da zasu iya dagewa nan gaba ba'ayi second term ba balle third term sannan suka ji dan sanyi a ransu suka fara goge hawayen daya jika musu ido. Hannah ta koma gefe tana kallon jifgin mutanen data kayar yayin da zuciyarta take jinjina mata ai kinyi matukar kokari tunda kin wuce mutane sittin da shida. Farin ciki ya lullube zuciyar Hannah. Ta sake sa ran dawowa makaranta idan hutunsu ya kare. Kasancewar taji Haisam ya yaba da sakamakonta don haka zai sake yi mata siyayyar makaranta da biyan kudin makaranta da aka ce duk term ake biya, kuma dubbunnan nerori.
Bayan kowacce tayi shiru da kukan da dayawa suke yi, sai Haisam ya ce "Duk kunyi kokari kasancewar *yan ajin babu marar kokari ya ce kowacce tazo ta karshe a nan ajin idan a wani ajin ne, B, C ko D ita zata zo musu ta wajen goma sha wani abu, kunga kowacce tayi kokari karku damu.
Ya dauko wata katuwar leda a gefensa ya ce dai-dai da dai-dai su ringa tasowa suna karba. Biscuit ne mai dadi ya rarraba musu kowacce daliba ta samu tun daga kan Rauda har Eneka Eddiward kowacce ta fara fara'a da murna tayi kokari. Da Haisam yaga duk sun ware yana musu wasa suna dariya sai ya ce "Ina so na shaida muku daga yau ko kuma in ce daga gobe ranar da za'ayi hutu idan na tafi hutun nan na tafi kenan. Gaban kowacce ya yanke ya fadi. Bamu gane ka tafi kenan ba Uncle Haisam. Su duka suka tambaya. Haisam yayi murmushi ya ce "Kun san ni copper ne, nazo ne yin bautar kasa wannan makarantar (N.Y.S.C) kuma yanzu lokaci yayi da muka kare don haka idan na tafi hutun nan bazan dawo makarantar nan ba. Ina muku fatan alheri kuma shawara nake baku akan kowacce ta dage tayi karatu banda wasa.
Ko wacce jikinta yayi sanyi fuskarsu alamar basu ji dadin wannan batu na class master dinsu ba. Suna son Haisam saboda kula da soyayya da yake nuna musu wasa da dariya a koda yaushe. Sai wasu da yawa daga cikinsu suka rushe da kuka. Babu kamar Rauda, Nusaiba da Hannah. Ai kuwa gara Rauda da Nusaiba akan Hannah wani sabon tashin hankali ya rufta mata fiye dana dazu. Haisam zai bar makarantar nan ita kuma ina zata dosa?.
Haisam ma wani tsananin bakin ciki ne ya mamaye a zuciyarsa. Yana tsananin son yan ajinsa, baya so ya tafi ya barsu yana tausayinsu kasancewarsu yan yara, babu kuma wani Malami ko manyan daliban da zasu zauna suna basu shawarwari kamar yadda yake yi musu kowanne lokaci. Ga kuma kanwarsa Hannah, wa zai kula da Hannah? A bar zancen kudin makaranta da siyayyar (Provission) ita kanta tana bukatar a kula da ita da kara karfafa mata gwiwa wajen idan ta tafi gida hutu ta dawo makaranta. Koda a gida an ce baza ta dawo ba tasa kuka har sai an dawo da ita. Ga wasu abubuwan da suka yi mata nauyi a aji, ma'ana bata ganewa sai shi Haisam da kansa yake nunnuna mata har sai ta gane.
Allah Sarki Hannah ya fada a zuciyarsa ji yake kamar ya rushe da kuka dan tsananin bakin cikin rabuwa da dalibansa. Amma ya daure ya dinga lallashinsu, idan wadannan suka yi shiru sai wadansu su rushe da kuka. Haisam dai har ya gaji da lallashinsu ya ce su tashi su tafi dakunansu sai gobe zasu hadu a wajen asembly hutu. Suka nufi dakunansu kowacce na sharbe hawaye. Haisam kuma ya nufi gidansa a nan staff quaters yana mai matukar jin ba dadi a ransa. Kowa yayi shiru ya daina kuka amma banda Hannah. Nusaiba da Rauda suka dinga lallashinta amma ta ki dainawa ta ki cin abinci sai kamar tayi shiru ta daina sai ta tuna karshen makarantarta yazo sai ta sake rushewa da kuka.
Haka ta yini cur tana kuka. Rauda ta ce "Waini Hannah kukan nan da kike yi kinfi kowa son Yaya Haisam ne? Ni fa munfi kusa da shi Babana abokin Babansa ne. Kuma Yayana Auwal abokinsa ne. Haka kuma Yayata Uwa daya uba daya Ramla budurwarsa ce koma na ce matarsa ce don har ansa musu rana. Sanda muke America yan gidansu a gidanmu suke sauka in sunje kuma da muka dawo nan kasar saboda Yaya Haisam ne aka kawoni makarantar nan tunda yana Malami ya ce da Abbana makarantar akwai karatau. To harni na hakura na daina kuka ke ba za ki hakura ba kamar kinfi kowa sonsa. Ya ce dai ke kanwarsa ce kuma ni a sanina yan uwansa duk a Kano suke na sansu kuma amma ni ban sanki ba. Kuma duk a yan uwansa babu masu kama da ke. Ke kamar wata Balarabiya kike ko buzuwa ce ni dai ban sani ba.
Nusaiba ta ce "Haba Rauda meye haka in ita ba yar uwarsa bace zai fada ne? Hannah ta sake rushewa da kuka. Daman abunda Rauda take yi mata ya isheta. Tunda aka kawo ta Malam Haisam ya ce kanwarsa ce taga Rauda tana kishi da ita, wai ya za ayi ace Hannah kanwar Yaya Haisam ce bayan ita kadai ce kanwarsa a makarantar.
Washe gari da sassafe dalibai
suka shirya kayansu
tsaf na tafiya gida suka saka
kayan makarantar
(Uniform) suka dunguma
babban dakin taro (Hall) don yin
assembly hutu. Hannah da
Nusaiba suka
kinkimo jukunkunan kayansu na
sakawa suka kuma rarrataya
jakar littattafansu a baya.
Akwatinansu kuwa da katifu da
bokitai a wani daki
ake lufgawa a rufe. Ba'a tafiya
dasu gida. A bakin
Hall din suka ajiye jakunkunan
sannan suka shiga
cikin Hall din dan yin assembly,
kasancewar Principle, vice
principle da duk Malaman sun
karaso wajen assembly.
Kallo daya Haisam yayi wa
Hannah yasan tasha
kuka kuma tana cikin tashin
hankali. Principal ta
sanarwa dalibai cewa an basu
hutun kwana arba'in
da biyu. Don haka ranar da
kwana araba'in da biyu
ta cika kowacce daliba kada ta
kara ko kwana daya, idan ta
kara to za'a korata gida. Ba za'a
karbeta ba. Sannan tayi musu
nasihohi akan idan
suka je gida su dinga taya
iyayensu aiki banda
yawo a gari, gidan kawaye balle
kuma masu zuwa
gidan samari. Mataimakin
principal ma ya tofa
albarkacin bakinsa. Ya jawa
daliban kunne akan su zama
masu da'a da ladabi da biyayya
a duk inda
suke. Sauran Malamai ma suka yi
musu nasihohi akan suyi amfani
da abinda Principal ta fada
musu
da mataimakinta. Sai kuma daga
karshe Malamai
uku da suka zo bautar kasa
suka yiwa daliban
makaranta sallama akan in sun
tafi sun tafi kenan, ba zasu
dawo ba. Malaman yan bautar
kasar sune
Uncle Haisam, Rose Iliya da
Hassan Bawa. Dalibai
manya da yara sunji ba dadi
saboda sun saba da
Malaman musamman Haisam
saboda kirkinsa da wasa da
dariyarsa yasa kowacce daliba
taji tana sonsa.
Musamman daliban da yake
koyarwa suna matukar bakin
ciki da rabuwa da Malaminsu
wanda
ya kware wajen koyar musu da
Geography. Nanfa
dalibai suka rude da sururtu
wasu na kuka wasu na fadin. "We wll
miss you! We wll miss you so
much!! Uncle Haisam,
Please ,stay don't go
please. A haka dai principal da
sauran Malamai suka fice suka
umarci daliban suma su tafi duk
wacce aka zo dauka.
Hannah da Nusaiba a bakin
barandar Hall din wajen
jakunkunasu suka zauna.
Nusaiba tace
"Allah Yasa Daddy na tun jiya
yazo Kano daga
Abuja. Ya kwana a Kano yau da
safen nan ya kamo hanyar
Kazaure.da ace yau zai taho
daga Abuja
gaskiya inajin ai sai yamma zai karaso,
wallahi murna nake
yi yau kamar za'a sani a
aljannah, dama ace ina rufe
ido na na ganni a gida. Hannah
tayi murmushin
karfin hali don babu walwala a
zuciyarta, dama ace
duk wanda baya son zuwa gida
ya daga hannu sai tafi kowa
daga hannu don ta zauna a
makarantar.
Nusaiba ta kalli Hannah wacce
tun safe bata murna.
Musamman ma yanzu da taji
ance hutun kwana
arba'in da biyu za'ayi sai ranta
ya sake baci. Ga kuma babban
tashin hankali Haisam zai tafi.
Nusaiba ta kula da Hannah ko
irin dokin tafiya gida bata yi. Sai
surutu take ita kadai Hannah
bata
sauraron ta sai wani tunani take
na daban, Nusaiba
ta dan zungureta da gefen
hannu ta ce "Waike Hannah
meke damunki ne ko murna bakya
yi gida fa
zamu. Hannah ta nisa sannan ta
sake yin murmushin karfin hali
ta ce "Me kika gani? Wallahi
nima ina murna dama na bude
ido in ganni a gida yanzu.
Nusaiba taji dadi da wannan
gudunmawar
hira da Hannah ta fara bata. Ta
ce "Ni kuma ina zuwa gida fruit
salad zansa ayi min inci wallahi
shi
nake marmari. Kefa kina zuwa
gida me zaki fara sawa ayi miki?
Hanna ta ce "Wa zansa? Nusaiba
ta ce "A'a masu aikinku man ko
mamarki tunda ana
dokinki ai komai kika ce kina so
za ayi miki. Hannah tayi ajiyar
zuciya, alamar wadanne yan
aiki ko kuma wacce mamar
zansa, Iya Abu? Lallai ashe sai
dai in mutu. Nusaiba ta
zungureta tace "Ke
ma kice a hada miki fruit salad,
fruit salad? Hannah ta tambaya
domin ita bata taba jin sunan ba
ma balle ta sanshi ko yaya yake.
Ta ce "A'a ni makanni
zan suyo inci. Nusaiba ta zabura
ta ce "Meye makani,
kwatantamin yadda yake nima
idan naje
gida ince a soyamin. Hannah ta
ce "Aishi makani
dafa shi ake yi. Ba kisan gwaza
ba? Nusaibah ta ce "Gwaza!
Gwaza!! Menene ma gwaza? Oh
cocoyam
za ki ce min, Kai! Allah ya
sawake inci gwaza sai kace
wata yar kauye? Hannah tayi
shiru don ita
tasan yar kauye ce kuma su
acan gwaza ce abun marmari.
Nusaiba ta ce "A ina kuke samun
gwaza
ni bana ganin ta ma ko a
kasuwar Abuja. Hannah ta ce
"Mu muna samu.
Uncle Haisam ne ya tunkaro
wajen da suke zaune,
su duka suka mimmike tsaye
don girmamawa gami
da cewa "Good morning sir. Ya
ce Morning Hannah,
Good morning Nusaiba. Yau
yan mata sai gida
naga Nusaiba sai murna kike yi
ko? Nusaiba ta ce "Yaya Haisam
murna yau nake yi kamar za'a
sakani
a aljannah. Haisam yayi dariya ya
ce "Hannah ke fa,
kema kina murna kamar za a
saka ki a aljannah?
Hannah tayi murmushin karfin
hali ta ce "Eh ina
murna nima. Shigowar wata
mota kirar end of discussion ce
ta katse hirar da suke tazo ta
tsaya, kafin mutumin da yake
ciki ya fito daga motar Nusaiba
Idris ta daka tsalle ta mike da
gudu ta nufi
wajen motar nan tana cewa
Babana oyoyo. Ya taho
shima da saurinsa ya rungume
ta su duka murma suke yi.
Nusaiba ta ruko hannun
Mahaifinta ta nufo
wajen da Malam Haisam da
Hannah suke a zaune su duka
suka mike don girmamawa.
Nusaiba ta ce "Baba ga class
master din mu da nake baku
labarinsa a wasika nace shi yake
kula damu Uncle Haisam
sunansa. Alh. Idris yayi dariya ya
ce "Oh Uncle Haisam ne duk
wasikun Nusaiba sai ta rubuto
mana labarinka da kai da
kawayenta Hannah da Rauda.
Haisam yayi murmushi ya ce
"Allah Sarki ai ga kawarta
Hannah. Hannah ta duka ta
gaishe
shi ya mikawa Haisam hannu
suka gaisa. Nusaiba ta ce "Baba
daga wannan hutun Uncle
Haisam ba
zai dawo ba. Alhaji Idris ya ce da
Haisam "Ai daman teaching
practice kake yi anan
makarantar ko? Haisam ya ce
"Eh bautar kasa (NYSC) nayi
kuma mun gama. Alhaji Idris ya
ce "Ba dadi yara sun saba
da kai gashi zaka tafi, mun gode
Allah Ya saka da alheri.
Haisam ya ce "Ba komai ai
kannena ne. Nusaiba ta ciro
takarda daga jakarta da biro ta
mikawa Haisam tace ya rubuta
mata lambar wayarsa. Ya karba
ya
rubuta mata, ta karba ta mikawa
Hannah tace "Hannah rubuta
min lambar wayar ki a kasan ta
Uncle Haisam. Hannah tayi turus,
ita bata taba ganin waya a gidansu bama balle ta san yadda
ake amfani da ita har tasan
wata lamba, Haisam yayi sauri ya
ce "A'a ke rubuta mata taki zata
kiraki. Nusaiba ta rubuta
lambar wayarta ta mikawa
Hannah, Hannah ta karba. Daga
karshe Hannah ta kamawa
Nusaiba
jakarta suka nufi wajen mota.
Alhaji Idris ya bude but Haisam
ya kama ya saka. Nusaiba ta
rungume
Hannah su duka suna hawaye.
Nusaiba ta ce "Kina zuwa gida ki
kira ni a waya kuma kullum
zamu
dinga waya muna gaisawa.
Alhaji Idris ya dafa kansu ya ce
"Ku daina kuka hutu za kuje
yana
karewa zaku dawo ai baku rabu
ba gaba daya.
Nusaiba da Mahaifinta suka
shiga mota ya ja suka
tafi Hannah da Haisam suna
daga musu hannu har suka kure
sannan suka koma inda suke
zaune da
suka zauna. Sai ga cincirindon
dalibai suka zo game
da barin makarantar da zaiyi.
Suna bashi lambobin wayar su
shima ya basu tasa, Haisam ya
baiyana
musu cewar in Allah Ya yarda
duk term zai dinga
zuwa yana ganin su. A haka dai
suka dinga wasa da dariya
kamar yadda suka saba.
Rauda ma ta karaso wajen ta
zauna ai hirar da ita
basu lura da sanda motar gidan
su ta shigo ba, sai kawai suka
hango Auwal Yayan Rauda ya
tinkaro
su. Rauda ta mike da gudu taje
ta rungume Yayanta, yana
karasowa ya mikawa Haisam
hannu suka kashe ya ce "Malam,
Dama haka kake sa daliban
naka a gaba kuna rera hira?
Haisam yayi
murmushi ya ce "Bankwana
muke yi kasan daga yau shike
nan bazan dawo ba, Auwal ya ce
"Wai
har kun gama bautar kasar?
Haisam ya ce "Kwarai
kuwa ba fama nake da kai ba
kazo ka dinga yi mana dan
kwana biyu ma kaki to gashi
nima Allah
Yayi min komawa gida gaba
daya mun zama daya.
Ya ce "Lallai shekara kwana ce
kamar yaune muka
kawoka kamar kayi kuka
bakasan kauye. Haisam
ya tuntsire da dariya ya ce
"Gashi kuwa na saba
yanzu har bana jin dadi zamu
rabu da dalibaina. Nan dai
Auwal ya sami yar kujera ya
zauna shima
dake gwanin wasa da dariya ne
da mutane ya dinga hira da
daliban nan yana zolayarsu
dakyar
Haisam ya banbaro shi daga
wajen daliban nan.
Auwal da zolaya ya sami yara
yana ta zolayarsu
musamman Hannah, duk da ma
baisan yadda take da Haisam ba
yana tayi mata wasa wai ita
balarabiya ce ta koya masa
yarensu yana
tambayarta me ake cewa yaro
da larabci? Ta yi
dariya ta ce "Ban sani ba, shi a
tunaninsa taki fada
masa ne kawai, baisan ita ba
balarabiya ba ce.
Auwal ya Mike ya ce da daliban,
"To ragowar kwaki da kanzo na
tafi tunda kun zama yan
kwantai ba'a
zo daukar ku ba. Ya kalli Hannah
ya ce "Ke yar Yemen jirgin
kasarku baizo ba kema mun tafi
mun
barki sai kinfi kowa yin kwantai
saboda ke ba yar kasa ba ce.
Hannah ta kyalkyale da dariya.
Sauran dalibai suka ce "Mu
bama cin kwaki bamu san ma
yadda kanzo yake ba Allah Ya
sawake
kuma muma yanzun nan za'azo
daukar mu. Haka wasa da dariya
aka dinga yi da Auwal da su
Hannah Haisam na gefe yana
kallonsu yana dariya ya ce da
Hannah "Kema dauko jakarki
kizo mu tafi na riga nayi muku
signing ke da Rauda mu tafi
kawai. Auwal ya ce da Hannah
"Ah ke da nace sai
kinfi kowa yin kwantai ashe tare
zamu tafi dake ko a filin jirgi
zamu ajeki ne a Kano? Hannah
tayi dariya
ta ce "Oho, ni dai banyi kwantai
ba. Haisam ya dauki jakar Rauda
Da qar saboda nauyi ba zata iya
dauka ba ya kai ya saka a mota.
Auwal ya ce "Hannah kawo
kema in taya ki tunda baki da
karfi
don nasan a garinku bakwacin
tuwo sai yar gurasa da zuma
ko? Hannah dai murna take
kawai
da ba gida za'a kaita ba Kano
zasu wuce da Yaya Haisam.
Rauda da Hannah suka je suka
shiga mota
a gidan baya suka zauna, Yaya
Haisam da Auwal suma suka
shiga motar, Yaya Haisam ne
yake
tukawa Auwal yana zaune a
gefe, suka nufi get din fita.
Dalibai na daga musu hannu har
suka tafi.
Rabon Rauda da ta yiwa Hannah
magana tun jiya yau ko magana
bata yi mata ba saboda tsabar
tana
kishi da ita wai saboda Yaya
Haisam yana ji da ita, itama ya ce
kanwarsa ce, yanzu kuma taga
yan uwantakar ta tabbata gata
a motarsu Yaya Haisam zai wuce
da ita gidansu ma. Ta kalli
Hannah ta
yamutse fuska ta ce "Kema Kano
zamu da ke kenan, daman a
Kano kike baki taba gaya mana
garinku ba? Hannah tayi shiru ta
rasa amsar da zata bata. Haisam
ya ce "Eh Rauda da ita zamu je
Kano a gidanku ma zata zauna
kinga sai ku dinga karatu a gida
tare ko? Rauda ta ce "Sai ka ce
basu da gida ai a gidansu za'a
nemeta. Cikin rada Hannah ta ce
"Babu wanda zai nemeni, ni
bazani gida ba. Ta mudubi
Haisam yake kallon bakinta yayi
murmushi kawai.
Haisam ya nufi hanyar cikin
Kazaure Auwal ya dubi
Haisam ya ce "A'a Haisam ina
zamuje mu da zamu
kama hanyar Kano. Haisam ya ce
"Cikin gari zani akwai wacce
zamu dauko. Basu tsaya a ko ina
ba
sai a kofar gidan uwar biyu,
daman a shirye take suna aika
yaro yayi sallama ya ce inji
Malam Haisam
sai ta fito da gyalanta daman a
shirye take tsaf ta fito.
Bayan sun gaisa Haisam ya ce da
su Rauda su matsa mata ta
zauna, suka matsa ta shiga ta
zauna
a kujeran baya sannan suka
gaisheta dukkanninsu. Haisam
yaja mota suka tafi bai tsaya a
ko'ina ba sai a babbar tashar
Kazaure ya sami waje a bakin
tasha ya tsaya ya juya ya kalli
uwar biyu da Hannah ya ce "To
anan zaku hau mota ko?
Uwar biyu tace "Eh akwai mota
har Babban -mutum a nan,
Uwar biyu ta yunkura zata fita ta
juya ta kalli Hannah wacce bata
da niyyar fita bata masan da ita
za'a fita ba a tunaninta uwar
biyu ce kawai zata
sauka ita kuma su kara gaba su
tafi Kano. Sai taji uwar biyu ta ce
"To Hannatu fito mu tafi ko?
Cikin
rudani Hannah ta juya ta kalli
Haisam don jin abunda zai ce sai
ya rasa me zai ce mata kwai ya
sunkuyar da kansa kasa ya kasa
magana, ya fito daga motar ya
bude but ya dauko jakar
Hannah.
Nan da nan kwandastocin mota
suka zo suna cewa "Babura
zaku hau ne, ko Daura? Uwar
biyu ta ce
"Motar Babura zamu hau sai mu
sauka a Babban- mutum. Haisam
ya mikawa kondastan da zasu
Babban-mutum jakar Hannah,
uwar biyu ta ce "Af har yanzu
Hannah bata fito daga motar
bane?
Haisam ya leka cikin motar ya
tsaya yana kallon Hannah baice
mata komai ba, ta sunkuyar da
kai
cikin sanyin jiki ta janyo jakar
littattafanta (school bag) ta
rataya ta juya ta kalli Rauda ta
kalli Yaya Auwal ta ce "Na tafi
sai anjimanku.
Rauda tayi murmushi ta ce "Au
har da ke zaku shiga motar haya
kin fasa zuwa Kanon ne?
Hannah
ta kada kai kawai sannan ta
fito. Yaya Auwal yana yi mata
wasa yana cewa "Af ashe ke
yar kauye ce ma, motar Babura
zaku hau ko? Hannah ta fita ba
tare da ta bashi amsa ba.
Haisam da Hannah suma
suka nufi cikin tasha daman
uwar biyu da kwandastan daya
dauki jakar sun shige cikin
tasha. Motar bus ce wacce baifi
mutane hudu ba a ciki bata cika
ba. Uwar biyu ta zauna a kujerar
baya
aka saka jakar kayan Hanna a
but Hannah ma taje kusa da
uwar biyu ta zauna, jikinta sanyi
kalau
kamar marar laka hankalinta a
tashe yake kamar wacce za'a
kaita lahira ba gidansu ba.
Haisam ya zaga ta wundon
uwar biyu dake zaune ya
danko kudi ya mika mata ya ce
"Ga wannan kuyi kudin mota
dan karku matsu ki biya kudin
kujerun bayan a barku ku kadai
sannan ki fito ki shiga Aishalle
super maket kafin mota ta cika
ki suyowa
Hannah sabulun wanka, wanki,
man shafawa dana gashi. Biskit
da alewowi ta yiwa yan
gidansu
tsaraba. Ya sake debo wasu
kudi masu yawa ya ce "Wannan
kuma ki ajiye da zarar hutu ya
kare ya rage kwana biyu kije ki
taho da ita ki kawota gidanki
zanzo in kara yi mata siyayya na
mayar da
ita makaranta. A cikin kudin ki
bawa Mahaifinta dan na
kashewa ki gaya masa lallai-lallai
hutun kwana arba'in da biyu
aka basu da zarar hutu ya kare
za ki zo ki dauke ta inji ni za ki
ce. Ki san dai kalaman da zaki
gaya masa na kwantar da
hankali kada ya
hanata dawowa kinsan tsofaffin
nan namu, kice ke uwar dakinta
ce a wajenki take a makaranta
na
Nina hadaku, ki ce ina gaishe shi da
kyau. Uwar biyu tayi godiya ta
shi albarka kamar ita aka bawa
kudin ko jikarta. Ya dauko wasu
kudin ya mikawa uwar biyu ya
ce "Ki sayawa Hannah sarka da
dankunne na jiyal mai kyau ki
bata. Uwar biyu ta ce "Kai kudin
yayi yawa Malam Haisam duk a
cikin wannan ya isa
nayi mata siyayyar, ya ce "Ba
komai na gode uwar biyu Allah
ya kiyaye hanya ta ce "Amin
Malam
mune da godiya. Ya zagayo jikin
wundon da Hannah ke zaune
tayi tagumi ta langwabar da kai
a
jikin wundon mota hawaye ne
yake sulalowa daga idanuwanta
daya bayan daya.
Nima kawai sai naji hawayen tausayi ya fara biyo kunci na
Mu tara donjin yaddah komar Hannah kauye zai kasance shin zata samu tarbar kirki ko kuwa????
Ina zan Sani mu hade gobe insha Allah
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter8
Haisam ya kalleta yayin da yaji
kamar zuciyarsa zata
fashe don tsananin tausayinta,
yayi karfin hali ya ce "Hannah
kukan meye kike don kawai anyi
hutu
zaki tafi gida? Ai na cewa uwar
biyu zata je ta daukoki kinji ko?
Zan zo inyi miki siyayya na
mayar dake makaranta, yanzu
idan kika je gida kina kuka Baba
zaice wahala kike sha a
makarantar ya ce
baza ki dawo ba. Amma ki
nunawa Baba makarantar da
dadi ga ladabi da biyayyar da
ake koya muku ga karatu da
abinci a wadace shi da
kansa zaice ki dawo, kin ji ko?
Hannah ta gyada kai ta fara
share hawayen idonta. Ya ci
gaba da cewa "Kiyi hakuri da
duk abunda Iya Abu take yi miki
hutu na karewa Uwar biyu zata
zo ta dauke ki ta kawo ki
makaranta. Sannan kullum ki
dinga zuwa makarantar
Islamiyya kina kuma duba
littattafanki na makarantar boko
don karki manta karatu kinji.
Allah Ya kiyaye hanya Hannah. Ya
juya ya tafi, muryarta yaji ta
rushe da kuka, ya juyo ya tsaya
cak
yana kallonta sai ya rasa me ma
zai ce mata sai ya juya ya tafi da
sauri. Yana mai tsananin
damuwa da
takaici, kukan zuci kawai yake.
Ba tare da ya cewa su Auwal
komai ba, ya shiga mota ya fara
tukawa. Can Rauda ta nisa ta ce
"Yaya Haisam daman Hannah
fulanin Daura ne. Ko ba daura
zasu ba?
Haisam yayi dan murmushi
kawai, Auwal ya ce "Haisam ka
cika shige-shige ina ka samu
wannan
yar buzuwar har da kakarta
kuma?
Haisam ya ce "Wai shige-shige
ni da kai za'a san mai shige-
shige naga daga zuwa har
kasan su
Naja'at Sulaiman ko banga
sanda take baka adireshinta bane
balle ni dana yi shekara a
makarantar. Auwal ya ce "To ya
isa ga wannan
zabiyar a baya ta bude kunnuwa
tana daukar rahoto. Haka dai
har suka isa Kano jifa-jifa
Haisam yake magana babu
abunda yake tunawa sai halinda
Hannah zata kasance a gidansu.
Zuciyarsa Cike da tausayin ta,
kulle-kullen yaya zaici gaba da
taimakonta yake gashi kuma ya
bar makarantar.
Har suka isa Kano. A nasarawa
G.R.A Suleman cresent gidan su
Haisam yake suka shiga cikin
katafaren get din gidan. Bayan
Auwal da Rauda
sun shiga sun gaisa da Hajiyar
Haisam sai suka yi
sallama suka nufi suma nasu
gidan da yake Lamido cresent
basu da nisa sosai.
Alh. Shitu Mukhtar sunan
Mahaifin Rauda, Mahaifiyarsu
kuma Haj, jamila sunanta.
Alh. Shitu Mukhtar haifaffen
garin Kano ne, dan unguwar
Kabara ne tare suka yi firamare
da sakandire da
Mahaifin Haisam abokaine tun
suna yara. Haj. Jamila
kuwa Mahaifiyar su Rauda
mutumiyar Chadi ce ya aureta.
Allah Ya albarkace su da ya*ya
uku, Yaya Auwal shine babba
wanda ya kammala karatun
likitansa a America yanzu
cikakken likita ne. Sai Aunty
Ramlah wacce ta gama
sakandire dinta
wannan shekarar tana jiran
sakamakon jarabawarta ta
wuce jami'a bayan an cancara
bikinta da angonta Haisam, sai
ta fara karatu a gidanta. Sai *yar
autarsu Rauda wacce yanzu
take ajin farko a sakandire.
Tsantsar *yan boko ne *ya*ya
uku sun ishesu rayuwar duniya
suna basu
cikakkiyar kulawa da tsananin
so da kauna.
Allah Yayi musu arziki mai yawa
don haka a daula suke
ta ko ina hutu, ba su fi shekara
biyu da dawowa Nigeria ba
kasancewar Alh. Shitu Mukhtar
yana aiki a embassy, shine
jakadan Nigeria a America
(abbasador) don haka duk a can
suka yi karatunsu. Har
Mahaifiyarsu Haj. Jamila a can ta
hada digirinta.
Al'amarin Hannah da uwar biyu
kuwa, bayan
tafiyar Haisam uwar biyu tayi
sauri ta sauka daga motar taje
ta yiwa Hannah siyayya kamar
yadda
Malam Haisam ya umarce ta da
ta yi. Ta dawo cikin mota da
sauri ta iske motar dai bata cika
ba, bayan
mota ta cika suka kama hanyar
tafiya. A hanya uwar biyu ta ci
gaba da lallashin Hannah tana
bata
baki dakyar tayi shiru da kukan
da take yi. Ta dade daman tana
so taji labarin Hannah da
dangantakarta da Malam
Haisam, saboda tsananin
kulawar data ga yana yi mata,
cikin wayo da dubaru irin na
manya uwar biyu ta dinga
bugun
cikin Hannah tana son jin
labarinta. Abunka da yarinya da
kuma neman agaji take yi ta
ko ina Hannah ta fayyacewa
uwar biyu komai daga farko har
karshe. Uwar biyu ta tausayawa
Hannah ta sake jinjinawa Malam
Haisam bisa jahadin da yayi
saboda Allah na taimakon
Hannah.
A garin Babban-mutum suka
sauka aka sauke musu jakarsu.
Tun da sauka Hannah ta fara
faduwar gaba tazo garin da
bawa ya fita jin dadi. Uwar biyu
ta lura da hakan sai tayi ta bata
baki tana
kwantar mata da hankalinta.
Kawayen Hannah maza da mata
*yan garin suka baibayeta suna
kallonta. Wasu kuma suna
shisshige mata har rububin yi
mata magana su ke. Masu
daukar mata jaka suka dauka
suka dunguma zuwa gidansu
Hannah. Samarin garin sai kallon
Hannah suke,
gani suke kamar ba Hannar da
ba ce da suka sani.
Tayi jawur da ita tsaf-tsaf.
Babban mamakin kambas din
data dana a kafarta suke kallo
wasu na
cewa takalmin *yan ball tasa,
wasu na cewa na faretin sojoji
ne. Mamaki ya ishe su yadda aka
yi
Hannah ta zama haka kamar
baturiya a wata guda
nan da nan, kyau na zuba duk
cikar garin da batsewarsa babu
mai kyawun Hanne da
gogewarta. Nanfa samari kowa
ya hau cewa gaskiya tawa ce
wannan, wancan na cewa na
rigaka. Kawayenta da yawa sun
kudiri niyyar suma sai sun
tuburewa Iyayensu an kaisu
makarantar
kwana irin ta Hannah don suma
su goge suyi jawur haka. Kafin
Hanne ta karasa gida labari ya
kai cikin
gidansu ance ga Hanne can
zuwa ta zama fara kal kamar
baturiya ita da wata tsohuwa.
Farin ciki ya cika Mahaifinta yayi
wuf ya fito kofar gida ya tsaya
yana murna yana jiran
karasowar Hanne (yar boko).
Budar bakin Iya Abu kuwa sai
cewa tayi watakila ciki aka yi
mata a makarantar tayi haske
don Hanne ba fara ba ce kal.
Surutai dai na hassada da bakin
ciki barkatai ta dinga yi. Hanne
na doso kofar gida ta hango
Mahaifinta sai su duk murna ta
lullubesu. Hannah ta karasa da
sauri taje ta rungumeshi kamar
yadda taga su Nusaiba suna
yiwa Mahaifansu, sai hawaye
suke ita da Mahaifinta. Iya Abu a
tsakar gida ita da *ya*yanta
babu wanda ya amsawa uwar
biyu sallamar da tayi, sai Mal.
Habu ya ce "Shigo kawai ai baza
su amsa miki ba, ya shiga ya
dauko tabarma
da sauri yazo ya shimfida mata
ta zauna a sanyaye,
cike da mamakin irin wannan
tsana da aka yiwa wannan *yar
karamar yarinya wanda ma yake
sonta an tsaneshi. Hannah taje
gaban Iya Abu ta durkusa ta
gaisheta ko ta amsa taki, ta juya
ta
gaishe da Yayyanta *ya*yan Abu
kenan suma suka mata abun
da Mahaifiyarsu tayi.
Uwar biyu ta rike baki ta ce "Oh
ikon Allah, bayin Allah me yayi
zafi Hannah nawa take? Don
Allah
kuyi mata *yar fara'a mana ko
taji dan sanyi yanzu ko dokinta
ba kwayi kusan wata biyu bata
nan. Ai ko dan
darajar idona bakuwa kwa raga
mata har in tafi.
Suka yo caaa akan Uwar biyu,
uwar nayi *ya*yan nayi, ta mike
tsaye ta juya ta kalli Hannah
wacce ta
kame a jikin katanga tana
makyarkyata hawaye ne
yake zuba daga idanuwanta
tasan yau duka da zagi Allah ne
kadai Yasan iyakarsa da zata
sha.
Hawaye ya kecewa Uwar biyu ta
ce "Hannah yi hakuri wuya bata
kisa ko anki ko anso gidan
Ubanki ne duk inda kika je sai
kinzo gidan dole. Iya Abu ta ce
"Gidan Uban nata kuma
zamansa ya
gagareta idan na so ba. Malam
Habu shima yayi jigum ya kasa
magana tashin hankali ya ishe
shi
saboda yana tausayin Hannah,
yasan wahala zasu
ci gaba da linka mata ganin
Allah ya rufa mata asiri
tayi kyau, Uwar biyu ta fita
Malam Habu ya bita Hannah ma
ta bisu da sauri, Uwar biyu tasa
gefen
gyale ta sharbe hawaye ta ce
"Allah Yana nan, Malam ni *yar
aiki ce Malam Haisam Malamin
daya
karbeta a hannunka din nan.
Malam Habu ya katseta ya ce "Eh
na gane kiyi mana godiya da
kyau da kyau na gode madalla.
Tasa hannu ta dauko kudi mai
dan kauru ta bawa Malam Habu ta
ce
"Malam Haisam ya ce a baja
nasa ne na kashin kansa bana
makarantar Hannah ba ce. Da
zarar
hutu ya kare ita da kanta zata zo
ta dauketa, Malam Habu yayi
shiru yana sauraron uwar biyu
sai
girgiza kai yake kawai yana
mamakin wannan tara
ta arziki da Haisam yake yi musu
yana fadin ashe akwai masu
halin Sahabbai a duniyar nan
masu kyautar da dukiyarsu ga
mabukata irin Haisam.
Malam Habu ya dago ya kalli
uwar biyu ya ce "Kema
daya aikoki kika rike amana
Allah Ya saka miki da gidan
Aljannah dashi da yake mana
hidima Allah Ya
bashi mai yi masa haka,
munji dadi mun gode. Ni ina
nan wata rana na gaza barci ina
tunanin ko yaya *yar Baba, ko
me take ci a makaranta na barta
babu abinci? Ashe tana can ta
fini koshi, kalli
yadda tayi bul-bul ah
Alhamdulillahi.
Mai gari ya
aiko da garin kwaki kwano biyu
da suga rabin kwano sai kudin
motar zuwa Kazaure ya ce in kai
mata makaranta, wallahi matan
nan tawa data ga garin kwakin
nan da kudin mota sai ta sulalo
ina
bacci ta sace kudin motar ta
bula ledar garin ya dinga
tsiyayewa a kasa, da naje na
shaidawa mai
gari ba kiga cin mutunci da suka
yimin ba wai daman talauci ya
ishe ni na sami kayan gwamnati
ina wadaka dashi. Su babu
ruwansu *ya dai *yata ce in
barta yunwar ta kasheta.
Nayi kuka da hawaye nazo na
zauna na hakura sai addu'a na
dinga aika mata daga nan Allah
Ya
hadata da nagari mai bata. Allah
Ya amsa addu'ata, gashi bamu
girbe amfanin gona ba shine
yasa ko
taro nakan tashi babu a
aljihuna. Uwar biyu ta ce "Kaico
haka kake rayuwa Malam?
To ni dai shawarar dazan baka
dan Allah duk rintsi duk wuya ka
toshe
kunnanka kome za'ace game da
karatun Hannah karka cire ta
daga makaranta. Babu sisinka,
ba kai
zaka dauke ta ba, ba kai zaka
mayar da ita ba, nice zan dinga
kawota ina zuwa ina daukarta
kai dai ka bata izini kawai karka
hanata saboda karatu kawai
zai farfado da Hannah ta sami
*yancinta da jin dadin
rayuwarta nan gaba, amma
azabar tayi yawa.
Malam Habu ya ce "Da gudu
kuwa zan barta, aini ba dan
za'ace na siyar da *yata ba, ko
ace na kaita birni tana iskanci
da ko hutu ma sai ince ta dinga
yi a gidanki. Amma yanzu kowa
yaji a redio an yiwa
*yan makaranta hutu ba aga
Hanne ba za'a fara titsiyeni da
tambaya a fada. Uwar biyu ta ce
"Allah Ya kyauta ni zan koma, ga
sabulai can a jakarta da
mayukan shafawa Malam
Haisam ya ce don Allah a dinga
barta tana wanka da wanki da
kitso ba
kamar yadda aka kawota ba,
kazan-kazan ina amfanin
kazanta? Uwar biyu ta fara
tafiya bayan
sunyi sallama da Malam Habu
yana godiya, Hannah ta rushe da
kuka ta bi uwar biyu da gudu ta
rungumeta su duka kuka suke
rusawa Hannah ta ce.
Uwar biyu karki tafi ki barni
wuya nake sha ni zan biki
gidanki in zauna acan. Daya
daga cikin
*ya*yan Iya Abu Musbahu shine
ya fito daga cikin gidan a guje
Uwarsa ta turo shi yazo ya
dauko mata
Hannah da yake suna labe a
zaure suna jin duk maganganun
da suke yi. Ya dauko ta aka ya
mikata
cikin gida ya rufo kofar zaure
sai kukan Hannah ne
yake tashi ya cika unguwar kai
kace rai ake zare mata saboda
irin karar kukan daga ji ba
karamin
bugu ake yi mata ba.
Malam Habu nata kokarin bude
kofar yana bugun kofar kamar
zai balla yana so yaje ya ceci
*yarsa.
Uwar biyu ta juya ta tafi tana
rusa kuka kamar ranta zai fita,
tsananin bakin ciki da tausayin
Hannah ne
ya cika mata zuciya. Tana jin
samarin dake zazzaune akan
benci suna jiyo kukan Hannah
suke
cewa "To baiwar iya Abu tazo
har an fara nada mata duka kai
wannan yarinya Allah dai Ya
rayata
kar itama wuya ta kasheta
kamar yadda ta kashe uwarta
saboda azabtarwar Iya Abu.
Malam Habu Imamu Mahaifin
Hannah haifaffan garin Babban
mutum ne Iyaye da Kakanninsa
su
suka kafa garin. Aurensa na
farko ya auri *yar uwarsa
Salmai. Allah bai basu haihuwa
ba har
tsawon shekara goma sha biyar
suna tare. Salmai da kanta ta
ringa rokar mai gidanta daya
kara aure
ko Allah Zai bashi haihuwa yaki
fur ya ce bazai yi ba, bashi da
sha'awar aure saboda baya son
tashin
hankali kasancewar sa mutum
ne mai hakuri da gudun tashin
hankali ko yaya yake.
Allah Ya bashi dan abun
hannunsa rufin asiri dai, yana
daya daga cikin masu tashen
kudi a wannan
gari nasu a lokacin. Abu wata
yarinya ce da take kawo masa
man gyada daga wani dan
karamin
kauye da yake kusa da garin
duk ranar kasuwa suna siyan
man gyada har gida take kawo
musu.
Cikin siyasa da dubaru Salmai ta
hada auren Malam Habu da Abu
aka sha biki aka kawo amarya,
da
zuciya daya Salmai take zaune
da Abu komai nata gida biyu
take rabawa ta bawa amarya, a
kullum
tunanin yau me zata bawa
amaryarta take yi kawai don
Abu ta saki jiki ta zauna ko Allah
Zai sa rabon haihuwar a jikinta
yake. Ai kuwa kafin shekara ta
zagayo Abu ta sami ciki. Tunda
ta sami ciki ita da *yan uwanta
suka tsani Salmai wai bakin ciki
take yi don Abu zata haihu ita
bata taba haihuwa ba zagi
rashin kunya kala-kala. Ta haihu
da namiji aka saka masa suna
Labaran, kafin ta yayeshi ta sake
samun ciki ta haifi Iliyasu. Nan
dai haihuwa ta bude
ta sake haifar Musbahu sai
kuma Ramatu. Rashin mutunci
yana ci gaba saida ta kai ko
ruwan gidan sai
a boye Salmai take sha kullum
tana daki zaman tsakar gida ya
gagreta. Abu da *ya*yanta su
isheta da rashin kunya. Abun
yazo ya zarce kan Salmai har shi
mai gidan Malam Habu yi masa
suke. Baro-
baro Abu take zaginsa ta cakumi
kwalarsa, tayi masa fata-fata da
dukiyarsa ya tsiyace. Duk da
haka
Salmai ta ci gaba da zaman
hakuri da Malam Habu da
kishiyarya. Amma dole da asirai
Iya Abu tayi waje da Salmai ba
don *yan uwanta sun dage da yi
mata addu'a ba da hauka zata yi
tuburan, don niyyar Abu ta
haukatar da ita, dan dole Malam
Habu ya rabu da ita. Haka Malam
Habu ya kasance abun tausayi
ya zama mijin tace sai yadda tayi
dashi idan taga dama ko abinci
ta dafa baza ta bashi ba, ko zata
bashi sai sun gama dibar yadda
zai ishe su sannan tace yaje
tukunya ya diba ya hada da
kanzo ya ci, bai kai matsayin da
zata zuba ta kai
masa ba. Bayan ta haifi Ramatu
sai ta haifi furera ta haifi *yar
Autarta Mahajana wacce ko
arba'in bata
yi ba da haihuwa a yanzu.
Wata rana Allah Ya kai Malam
Habu kasuwar wani gari mai
suna Dashi a cikin kasar Niger
ya gamu da
Habi *yar buzuwa Mahaifiyar
Hannah. Habi yarinya ce *yar
karama a lokacin shekarunta bai
wuce shekara goma sha uku ba.
kamar wasa soyayya ta
kullu Malam Habu ya aurota ya
kawota gidansu.sai Tururuwar
zuwa kallon Habi akeyi sabida
kyawunta gashinta har gadon
bayanta fara ce kyal mai kyawun
gaske. Nan fa iya Abu ta ce
dawa Allah
Ya hadani in ba da Habi ba, ta
fara azabtar da Habi.
Malam Habu kuma bai isa ba ya
hana. A haka Habi ta sami ciki,
ga ciki tsoho ga debo ruwa,
Yo ciyawa a gona karyo karan
da za'a dafa abinci sussika ita
take yi. A garin kowa tausayin
Habi yake
tayi. Wanke-wanke shara ga
duka da take sha a wajen iya
abu, solobiyun mijin nata bai isa
ya hanata
sai dai ya zauna yana taya ta
kuka abinka da abun asiri ko tak
an hana shi ya ce balle ya
tsawatar ya hana abunda take
yiwa matarsa. Cikin Habi ya isa
haihuwa ta haifi diya mace mai
kyau kamar
uwarta. Aka saka mata suna
Hannatu. Fur Iya abu
ta hana Malam Habu ya kai Habi
garinsu tayi wankan jego ya je
ya sanar musu ma cewar ta
haihu ta hana shi. Haka ta bar
Habi da danyen jego haihuwar
fari bata san yaya ake ba, badan
wata
makwabciyarsu ba data tsaya
sukayi fadi in fada da iya
Abu ba tace dole sai ta dinga kula
da Habi da haka zata barta a
daki ta rufe ita da jaririyar.!! Tun
kafin
tayi arba'ain ta zubar da
wankan, iya Abu ta fara sa Habi
aiki har su debo ruwa a rafi,
haka har Hanne ta isa yaye aka
yayeta, kwanci tashi *yan uwan
Habi dai suka ji shirun yayi yawa
babu Habi babu
labarinta har shekaru uku suka
yo kungiya suka dira a garin
Babban-mutum, tun daga kan
hanya
aka shaida musu cewar Habi ta
haihu har ta yaye *yarta sannan
yanzu a kwance take kusan
wata biyu bata da lafiya saboda
tsananin azabar da take sha a
wajen kishiyarta.
Suna zuwa gidan suka iske Habi
sai kashi a kwance akan katifa
ga *yarta itama a rame kurket a
gabanta, suka sha kuka abun
tausayi babu mai zaman jinya a
wajenta, ko awa nawa Malam
Habu zaiyi baya gida sai sanda
ya dawo zai tasheta ya bata
abinci da ruwa ita da *yar ta
babu mai basu.
Bayan zuwan dangin Habi da
kwana uku ta ce ga garinku nan
Allah Yayi mata rasuwa, sun sha
kuka kamar ransu zai fita, haka
Malam Habu yayi kuka yayi dana
sanin auro *yar mutanen da yayi
ya kawota, matarsa ta zama
sanadiyyar ajalinta. Iya Abu
kuwa da *ya*yanta suna ji a
daki ko su fito ma balle ma suyi
kukan mutuwa, ranar sadakar
uku ita
da *ya*yanta suka ci kwalliya
suna shirin fita biki,
wannan rashin Imani na iya Abu
yayi yawa, *yan uwan Habi duk
suna kallonta, suna nan sai
bayan anyi sadakar bakwai suka
shirya kayansu zasu koma
garinsu suka ce da Malam Habu
zasu tafi da Hannah. Nan da nan
ya amsa musu ya amince don
yasan idan an barta ma wahala
zata sha kamar
yadda Mahaifiyarta tasha, sai
kuwa iya Abu tayi tsallen albarka
ta ce ai babu wanda ya isa ya
tafi da Hanne wato so suke su
tafi da *yar Habu don ya dinga
zuwa garinsu ganin *yarsa daga
nan a lika masa kanwarta ya
aura ko? Dama suna ciki da ita
ai kuwa suka ci damara aka hau
masifa da iya Abu suka kuwa
taru su biyar din suka yi mata
dukan kawo wuka suka farfasa
mata baki har da cire mata
hakorin gaba guda daya, dakyar
da sudin goshi makwabta suka
karbeta. Suka ce sunma fasa
tafiya
da Hannen tama daina tunanin
suna so su sake bawa Malam
Habu *yarsu ko da kuwa
danginsu
kakaf zasu rasa miji baza su
sake bawa Malam Habu *ya ba,
mai gari yana basu hakuri da
sauran *yan gari dakyar dai aka
raba wannan fadan suka bar
Malam Habu rike da Hannah a
hannunsa da *yan
kayanta a leda yana roko su
karbeta suka ki.
Iya Abu kuwa daki *ya*yanta
suka shiga da ita tayi lambar
kwance baki ya hau ya suntuma
tana jinya.
Tun daga wannan lokaci
Hannah yarinya *yar shekara
biyu ta fara gamuwa da wahalar
rayuwa
har rana irin ta yau. Hannah ta
dandana azabar Iya Abu,
kaico!!!!!
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 9
HUTU YA KARE Hutu ya rage
saura kwana biyu ya kare Uwar
biyu
ta shiga mota ta nufi garin su
Hannah. Ta iske Mahaifin
Hannah a shinfidarsa a zaune
yana
karatun Alkur'ani, yayi matukar
farin ciki da ganin Uwar biyu ya
dauko mata kujerar zama irin ta
mata ya kawo mata ta zauna,
bayan sun gaisa. Ta ce "Ina
Hannah take? Nazo daukarta ne
don hutunsu ya kare. Ya ce
"Ikon Allah har hutun ya kare
ashe, to
bari in aika a kirawota tana
dawa ta tafi kiwo ai tun hantsi
take fita da dabbobi kiwo. Uwar
biyu ta ce "Kiwo Malam? Ya ce
kiwo take zuwa kullum sai ta
kora dabbobi yaya zamu yi ai
*yar Baba harta saba.
Ya leka cikin gida ya kwallawa
Mahajana kira ta fito tana
gunaguni. "Baba wai meye bacci
nake ji ni dai "Ya ce "*yar Baba
zaki kirawo mun kice yanzu ta
koro dabbobin tazo gida anzo
daukarta zata koma makaranta.
Mahajana ta ruga cikin daki a
guje.
Uwar biyu ta ce "A'a yaya zata
ruga ciki baza ta je aiken bane?
Malam Habu ya ce "Uwar zata
tseguntawa cewar anzo daukar
Hanne zata koma makaranta,
kinsan cewa tayi inda ranta
Hanne ta daina karatu tunda
wata gulma aka hada na kaita
gidan *yan gayu babu wata
makaranta. Wuf Iya
abu tayi tayo waje daga cikin
daki tazo ta tsaya a dokin kofa
tana girgiza ta kama kugu tana
kallon
uwar biyu a yatsune. Babu
abinda Uwar biyu take sai kallon
wuyan Iya abu galleliyar sarkar
jiyal din
da ta siyawa Hanne ce a
wuyanta. Mahajana *yarta kuwa
riga da siket *yar kanti ta Hanne
ce a jikinta,
saiga Musbahu shima ya zo ya
wuce da jakar Hanne
a rataye a bayansa (School bag)
wai daga kasuwa yake. Iya Abu
ta ce "Bai gaya miki na hana
karatun Hanne bane ko bai fada miki
ba ne? Uwar biyu ta ce "Shine
Mahaifinta shine kuma mai iko
da *yarsa bake ba. Ni kuma
akan kin barin yarinyar nan ta
tafi zan iya cin damarar mu
daku da kowa kuma daga nan
har gaban maigari zamu je dake
idan kika kwatanta yin hakan.
Iya Abu tayi shiru tasan
idan aka kaita kara wajen mai
gari tasan bazai bi bayanta ba
kasancewar sun sha gogawa
akan zata hana Hanne karatu
bata ci nasara ba. Iya Abu ta
nisa ta ce "To kije dawan da
kanki ki kirawo Hannen *yata ba
zata ba. Ta ja hannun Mahajana
suka shige
cikin gida. Malam Habu ya leka
kofar gida ya kira musu dan
makwabtansu ya ce yaje dawa
ya ce da Hanne ta zo yanzun nan
ta koro kiwon su dawo gida.
Uwar biyu ta tabe baki gami da
yin ajiyar
zuciya ta ce "Rabon gado akayi
da kayan Hanne tunda ranta
ba'a jira ta mutu ba? Caraf Iya
Abu ta
fito ashe a labe take ta ce "An
raba kayan Hannen ko Hannen
naga dama zan iya rabata balle
kayanta.
Duk gulmace-gulmacen da
kuke hadawa ya kare a kanku
babu wata makaranta da ake
kai Hanne
yawon bariki kawai ake koyawa
yarinya ta samo abin duniya.
Uwar biyu tayi dariya shekeke ta
ce
"Wannan yawan bariki na Hanne
don ke da *ya*yanki take yi irin
wannan bushasha da kayan
yarinya. Da yake itama Uwar
biyu ba daganan ba wajen iya
masifa da yaba bakar magana
suka yi tayi dakyar Malam Habu
ya hana Uwar biyu magana ya
ce tayi shiru ta kyaleta, Iya abu
tayi ta fada tana
shige da fice bakin ciki ya lullube
mata zuciya kamar ta fashe
ganin anzo za'a dauki Hanne a
tafi
da ita wajen da take hutawa.
Hannah ta shigo a sanyaye tana
fargaba tana tunanin me tayi
kuma aka ce ta koro kiwo ta
dawo
gida yanzu. Tana shigowa sai
taga Uwar biyu da Mahaifinta a
zaure a zaune ta daka tsalle ta
rungume Uwar biyu tana mai
tsananin murna da farin ciki ta
ce "Iya daukata kika zo yi mu
tafi? Uwar biyu ta ce "Yanzu
kuwa shiga ki dauko kayanki
mu tafi. Hannah ta yi kasake a
tsaye murna ta koma ciki tayi
kamar zata fashe da kuka. Uwar
biyu ta kalleta
ta ce "Hannatu lafiya meya faru
kuma kika zama
haka lokaci daya kamar mai
shirin rushewa da kuka? Uban
ya ce "Da kika ce taje ta dauko
kayanta shine jikinta yayi sanyi
ai babu kayan duk sun kwashe.
Harda litattafan makaranta sun
yayyaga sun siyarwa da mai
kosai wasu. Uwar biyu ta kwada
salati ta na cewa "Harda manyan
littattafan
karatu masu tsada suka yayyaga
mata?
Iya Abu tayi wuf ta fito ta ce da
Uwar biyu "Ki kiyayeni don kin
zake da yawa, karfa ki kuskura
ki cika min ciki ba'aja dani. An
yayyaga littafan kiyi abinda zaki
yi kuje ku saya mata wasu ta
kawo na sake
yayyagawa muje duk inda zamu
je aikin banza.aikin banza kawai
Uwar biyu ta mike tsaye ta juya
ta kalli Malam Habu wanda yayi
tsuru abun duniya ya ishe shi ya
kasa magana ta ce "Malam na
tafi da Hanne Allah Yana bayan
mai gaskiya, kuma duk dan
hakin da ka
raina shike tsokane maka ido,
zakaran da Allah Ya nufa da cara
ko ana muzuru ana shaho sai
yayi.
Hanne mu tafi garin da ake
kaunarki. Iya Abu ta rako su har
kofar gida tana zagi tasa hannu
ta fallawa Hanne duka a baya
gami da angazata ta tafi taga-
taga zata fadi uwar biyu ta
riketa taja
hannunta suka tafi. Hanne ta
rushe da kuka Uwar biyu fadi
take "Duk abinda zaki yiwa
Hanne baki isa
ki hanata numfashi a duniya ba
tunda bake kika halicceta ba,
suka kama hanya suka tafi, suna
ji Iya Abu ta koma kan Mahaifin
Hanne tana zazzaga masa
masifa yayi shiru kamar ba
dashi take ba.
A tasha uwar biyu ta siyawa
Hanne sabon silifas domin na
kafarta wari da wari ne, suna
zaune a
mota uwar biyu take ta
tambayar Hanne abubuwan da
ake yi mata. Hannah ta zayyana
mata tsaf ta ce kusan kullum sai
an lakada mata duka an kwace
kayan sawarta da jakunkunanta,
sabulun ma da
mayukan shafawa ko sau daya
ba'a barta tayi wanka da su ba.
Tana dai barinta taje
makarantar Islamiyya kullum
shima saboda tana tsoron
maigari ne. Hanne ta sake
dagulewa kamar ba ita ce tayi
kyau din nan ba das da ita
gwanin sha'awa,
yanzu ta dawo furtunta,
yagulallun kaya. Uwar biyu ta ce
"Yanzu har kayan makarantar
taki (Uniform) duk sakawa
suke? Ta ce "Eh ta rarrabawa
jikokinta
wasu, wasu kuwa ta sayarwa
*yan jagorar makafi. Bani da
sauran kaya sai wannan na
jikina. Uwar biyu ta nisa ta ce
"Allah Ya saka miki, kuma
wannan yaro Haisam shima an
sake ja masa sabon aiki.
Zugum suka yi su duka kowacce
tana tunani har suka isa tashar
Kazaure babu wacce ta sake yin
magana. Suna isa gida Uwar
biyu ta shirgowa Hanne abinci
mai yawa ga mamakinta Hanne
ta tashi da shi ta sha ruwa.
Bayan sun huta Uwar biyu tasa
*yarta Halima ta wanke mata
cukurkudadden
gashinta, Hannah tayi sallah
wanka. Kafin magaruba har an
gama rangadawa Hannah kitso.
Sai suka ji
ana rangada sallama Uwar biyu
ta ce Hannah ta leka zaure taga
waye yake sallama. Tana lekawa
sai taga Safiyanu ne abokin Yaya
Haisam, rike da wata katuwar
Jakar bacco babbar ta karshe a
girma.
Hannah tayi dariya ta ce "Lale
Safiyanu sannu da zuwa, ya ce
"Yauwa Hannah har kin kinzo,
hutu ya kare ko?
Hannah ta ce "Eh ka shigo mana.
Dakyar yake jan buhun a kasa
saboda a shake yake dam da
kaya.
Suka iske uwar biyu a tsakar
gida. "Lale marhaban, uwar biyu
take cewa. Hannah tayi sauri ta
shimfida masa tabarma ya
zauna.
Bayan sun gaisa da Uwar biyu
ya fara zazzage kayan dake cikin
wannan katuwar jaka siyayyar
Hannah ce ta makaranta
(Provission). Kaya ne abun baya
lissafuwa komai akwai kai kace
kanti za'a bude. Uwar biyi ta
rike baki kawai tana kallon ikon
Allah, ta ce "Safiyanu wannan
kaya ai ya yiwa akwatin Hannah
yawa. Safiyanu yayi murmushi
ya
ce ai kudin da Haisam ya bani ne
masu yawa ne ya ce duk ayi
mata siyayya a wadace. Nima da
kaina
naga ya dace na bar sayyayarna
haka ba don kudin sun kare ba.
Uwar biyu ta ce "Ai gara da ka
rago kudin don sai an sake
sayan sabbin uniform da
littattafai. Safiyanu ya ce "Ina
nata na da, ko duk term ake
sake wasu? Uwar biyu ta gyara
zama ta fara bawa Safiyanu
labari duk abunda ya faru da
kayan Hannah tun daga farko
har karshe. Safiyanu ya
tausayawa rayuwar Hannah duk
da yake dama
Haisam ya gaya masa kadan
daga ciki. Ya nisa yace "Abun
babbane, kudin da yawa
musamman na
sayan littattafan karatun (text
book) masu tsada ne gashi
Haisam din bama ya kasar. Uwar
biyu ta ce
"Baya kasar ina yaje? Nifa tun
ranar hutu ban sake sa idona a
kansa ba. Safiyanu ya ce "Ai
kuwa bai dade da tafiya ba shi
da Mahaifiyarsa suka tafi
London kinsan shirye-shiryen
bikinsa ake yi shi da Yayansa
watakila nan da wata uku za'ayi
don haka daman zaiyi wuya
Haisam ya sake dawowa
Kazaure tunda bautar kasa
daman ya zo kuma sun kare.
Nima da yake daman a Kano na
sanshi a can
muke haduwa. Acan kuma ya ce
zai dinga kawo min kudin
siyayyar Hannah. Yanzu dai abun
da za'ayi duk abinda ya tashi na
game da makarantar Hannah a
gaya min zanyi ko nawa ne zan
ranta masa nasan zai biya ni
don haka daga yau zuwa gobe
zanyi kokari na saisayo mata
Uniform din da
takalmi da kuma littattafai. Zuwa
gobe telan daya dinka mata
wadancan zai dinka mata da
wuri, Jibi dai zasu koma
makaranta kafinnan Insha
Allahu komai ya kammala. Uwar
biyu tayi murna dajin bayanan
Safiyanu tayi ta godiya. Amma
Hannah ta
fita yin murna da farin ciki don
ita da a tunaninta za'ace
karshen karatunta yazo tunda
Yaya Haisam
baya Nigeria to sai taji Safiyanu
ya ce zai ranta a dinka mata.
Suka yi sallama da Safiyanu su
duka suna yi masa godiya ya
tafi, akan jibi Hannah ta kwana
da shiri zai kawo mata kayan ya
kuma
mayar da ita makaranta.
Haka kuwa akayi Hannah tana
daya daga cikin wadanda suka
fara dawowa makaranta tun
karfe
sha biyu na rana, kafin yamma
makaranta ta cika makil
kowacce ta dawo tana tsoro
saboda Principal ta ce duk
wacce ta kara kwana daya
baza'a karbeta
ba.
Yaya haisam baya nan kishin da
Rauda take yi da Hannah ya kau
yanzu suna zaune lafiya wasa da
dariya, sai dai su dukkansu basa
jin dadin makarantar sosai
saboda babu Yayansu. Haka duk
*yan ajin Uncle Haisam basa jin
dadin sabon class master dinsu
saboda baya tarairayarsu kamar
Haisam, kowacce bata manta da
nasihohin da Uncle Haisam yayi
musu ba akan suyi karatu suci
jarabawa idan ba haka ba za'ayi
mata repeating . Ko wacce ta
dage da karatu ba dare ba rana
don haka
J.S.S 1A is the best class in F.G.G.C
Kazaure. Yawanci a wajen
asembly Malamai suna fadar
haka Principal
tasa a tafa musu, tana kuma
alfahari da su tana yabawa
tsohon class master dinsu
Haisam saboda
tasan shi ya gyara ajin haka.
Tana kuma nunawa sauran
Malamai da suyi koyi da shi don
ire-iren su
Haisam a makarantar nan ba
karamar nasara ba ce,
Ta ci gaban makaranta. Bayan
dawowar daliban makaranta da
kamar wata guda.
Ranar wata litinin da safe ana
assembly sai kuwa Princpal tayi
musu albishir da cewa
kwararren Malamin nan Uncle
Haisam ya dawo makarantar a
matsayin permanent teacher.
Tasa wani Malami ya leka waje
ya shigo da Haisam saboda a
waje ya
labe kada su ganshi suki
tsayawa ayi assembly suyi ta ife-
ife don haka ya tsaya daga waje.
Malam
Haisam na shigowa dalibai gaba
dayansu yara da manya suka
hau ihu da tafi murna kuwa
ba'a cewa
komai musamman a wajen su
Hannah. Wai! Yau da za'a bude
zuciyar Hannah aga irin farin
cikin da yake zuciyarta da abun
da yawa. Dakyar dai daliban
suka tsagaita da ihu aka karasa
assembly kowacce ta tafi ajinta.
*Yan ajin su Rauda kuwa hada
baki suka yi suka yi kungiya
suka nufi ofishin Principal dauke
da manya-manyan takardu sun
rubuta kamar haka "WE WANT
OUR FORMER CLASS
MASTER UNCLE HAISAM BACK
(munason tsohon malamin
ajinmu uncle Haisam yadawo).
Wai su zanga-zangar lumana
suke yi, principal da sauran
Malamai suka sha dariya sannan
ta basu amsar cewa za'a dawo
musu da Haisam dinsu, su koma
aji sannan suka tafi suna murna.
Haisam ya
dawo yaci gaba da rike ragamar
shugabancin ajinsa J.S.S 1A.
Hutu yana zuwa karshe
jarabawa na karatowa Haisam
na ci gaba da yiwa dalibai
nasiha dasu dage da karatu
musamman ma Hannah yana ci
gaba da nunnuna mata duk
abunda bata gane ba. Ba laifi
Hannah tana sake kokartawa
fiye da wancan term din. Ta fara
gane ayyukan makarantar sosai
tana
kuma gane turanci tana yi kuma.
Wannan term dinma kamar
wancan sunyi jarabawa sun
gama sannan Malamai sun yi
kokarin kammala fitar da
sakamako. Haisam ya tara *yan
ajinsa ana gobe hutu ya bawa
kowacce sakamakon
jarabawarta.
Wannan ma kamar waccan bata
sake zani ba.
Rauda Shitu Muktar itace tazo ta
farko, Nusaiba ta biyu, Pamella
Matin Benin ta uku. Hannah ce
dai ta sami ci gaba maimakon ta
goma data zo wancan karon
yanzu sai tazo ta takwas.
Hannah tayi murna Haisam har
ya fita yin murna ganin ba kudin
banza
yake kashewa ba, da bata
lokacinsa a banza ba.
Kamar wancan hutun, ranar
hutu Principal ta yiwa dalibai
assembly, hutun ne dai bashi da
yawa sosai kwana ashirin da
takwas ne kawai zasu yi a gida.
Amma wannan karon direban
gidan su Rauda da yazo daukar
Raudah, sai Haisam yace ta tafi
shima daga gidansu za'a aiko
da direbansa yazo ya daukeshi.
Bayan tafiyar su Rauda babu
dadewa sai
ga galleliyar motar Haisam kirar
Jeef da Mahaifinsa ya bashi
bayan ya gama bautar kasa.
Muntari sunan
direban Haisam, yazo ya duka ya
gaishe da Haisam, Haisam ya
nuna masa jakar Hannah ya ce
ya dauka
ya saka a but. Bayan ya saka
Hannah ta shiga baya, Haisam
na gaba direba Muntari yana
tukawa suka fita daga
makarantar. Haisam na nunawa
Muntari hanya har gidan uwar
biyu kamar waccan lokacin
suka iske Uwar biyu a shirye
tsaf. Ta fito daga gida bayan sun
gaisa, Haisam ya ce da Uwar
biyu su
dauki jakar kayan su shiga cikin
gida a ajiye, kaya kala biyu
kawai za'a bawa Hannah da
silifas daya
amma duk sauran a ajiye da
littattafanta. Da yake Safiyanu ya
bashi labarin duk yadda Uwar
biyu ta gaya masa abunda ya
faru da kayan Hannah. Muntari
direba ne ya taya su da shigar
da kayan cikin
gida, uwar biyu ta zabawa
Hannah kayan da zata saka ta
cire Uniform da kambas aka
bata silifas da
wani kala a leda wanda zata tafi
dashi. Duk sauran aka ajiye mata
anan gidan. Bayan sun fito daga
gida sai suka shiga mota suka
tafi, basu tsaya a ko'ina ba sai
tasha. Wannan karan ma har
bakin
mota Haisam ya raka su Hannah
ya dauki kudi mai yawa ya bawa
Uwar biyu ya ce suyi kudin mota
na
zuwa can tayi na dawowarta.
Sannan a ciki ta bawa Mahaifin
Hannah na kashewa ta ajiye
wanda zata je ta daukota idan
hutu ya kare. Ya yiwa Hannah
nasihohi ya bata hakuri game
da halin da take ciki a gidansu.
Daga karshe yayi musu fatan
Allah ya sauke su lafiya. Ya juya
ya tafi, Uwar biyu na tayi masa
godiya dashi albarka Hannah na
rusa kuka. L
Haka dai Uwar biyu da Hannah
suka kasance idan hutu ya rage
kwanaki sai Uwar biyu taje ta
dauko Hannah. Haisam kuma
baya gajiya dayi mata siyayya
duk abunda zata bukata na
rayuwar
makaranta.
Ko *ya*yan masu Hannu da
shuni na makarantar baza su
nunawa Hannah gata ba. Idan
aka yi hutu
Haisam yana kaisu tasha ya sasu
a mota Uwar biyu ta kaita gida.
Amma kuma kaya kadan Uwar
biyu
take bawa Hannah ta tafi dashi
garinsu, kadan dinma bata
dawowa dasu, Iya Abu ta kwace
ta
bawa *ya*yanta, ga bakar
wahala da ake bata, wujiga-
wujiga Hannah ke dawowa
daga hutu
kamar ba ita ba, saboda wahalar
da take sha duk sai tayi duhu.
Amma daga baya ta dawo
makaranta kafin suyi hutu ta
sake fes da ita.
Kwanci tashi wannan ne hutun
da su Hannah in sun dawo
makaranta zasu shiga senior
class wato S.S 1. Don haka duk
uniform dinsu sai an sake musu
na seniors daban na junior class
daban. Don
haka tun kafin Uwar biyu taje ta
daukota Haisam ya kawowa
Uwar biyu uniform din Hannah
ta ajiye
harya dinka mata ya canja mata
school bag tsaleliya irin ta
manyan dalibai, akwati mai taya
biyu ya saya mata babba da
karama. Babbar ta zuba
provission
karamar ta kayan sawarta,
kamar yadda yaga *ya*yan
attajirai ana yi musu idan suka
shiga ajin
manya. Ranar da aka dawo
makaranta Safiyanu ya
dawo da Hannah. A duk lokacin
da Safiyanu ya kawota
makaranta takan kirawo
kawayenta su zo su gaisa da
Safiyanu, Yayanta take cewa
kamar yadda taga kowacce tana
kiran kawayenta ta gaisa
da *yan gidansu. Duk *yan
makarantar suna yiwa
Hannah kallon wata *yar gidan
gawurtaccen attajiri ko Nusaiba
da Rauda basu san ba daga
gidansu
ake yi mata wannan siyayyar ba
saboda Haisam yayi mata
gargadi kada ta gayawa kowa
labarinta
ta rike sirrinta. Raudah da
Nusaiba sun dauka Uwar biyu
Kakarta ce kuma Babban-Mutum
din da
suke tafiya duk hutu garin
Kakanninta ne take zuwa. Ko a
hira Hannah bata cika bada
labarin *yan
gidansu ba sai dai tayi ta
sauraron mutane.
Masassakin budurci ya fara
sassaka Hannah. Ma'ana Hannah
ta zama budurwa kyau ya sake
fitowa. A gaskiya Kyan Hannah
bazai iya siffantuwa ba, farinta
ya sake haskakawa, gashin
kanta ya
kara tsawo saboda tayi yawon
gyarashi ga mayukan gashi kala-
kala da Haisam yake siya mata.
Ranar wata social night da
daddare ne Haisam ya hango
Hannah, Nusaiba da Rauda sun
sha wandunan jeans da t.shirt
sun nufi katafaran kantin siyar
da kayayyaki kala-kala dake cikin
makarantar. Suna tsaye suna ta
siyayya, sai dariya suke suna tafi,
cikin sanda ya karasa kantin
don yaga me suke siya haka
suna dariya. Wai ashe rigar
----- (Braa) zasu fara sawa
*yan kanana. To shine ya kawo
su shagon suke jin
kunyar
siya kuma. Hannah ta ce "Ni dai
ba don kunce a suyo bireziyar
nan dani ba da bazan siya ba,
yanzu
fa dole bazan dinga sakewa ba
zan dinga gani kamar ana gani.
Rauda ta ce "Caf aini da gangan
zan dinga sakin hannun rigata
don ta fito. Nusaiba bata ce
komai ba ashe ta hango Uncle
Haisam a bayansu a tsaye tana
kifta musu ido su basu gani ba.
Hannah ta ce "Ko da yake mun
zama seniors har *yan J.S.S 1 ma
naga wasu suna sawa fa,
Nusaiba
zabi. Hannah na daddagawa,
Nusaiba tayi gyaran murya taga
dai basu san Uncle Haisam na
bayansu ba. Sai ta ce "Ba
ruwana ga Yaya Haisam nan
yana jinku, Haisam ya kyalkyale
da dariya. Sai su duka suka juyo
nan fa Hannah ta wurgar data
hannunta ta ruga a guje,
Nusaiba da Rauda kuwa suka
cusa tasu a riga suma suka arce.
Haisam ya zo ya dauki wacce
Hannah ta wurgar shi da mai
kanti suka dinga dariya. Haisam
ya ce "Su Hannah *yan mata.GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 10
Haisam ya dada kyau sosai
hanakalinsa ya kwanta ya zama
mai kudi baya ga albashinsa
account Mahaifinsa ya bude
masa yana zuba masa ribar da
suka ci a kamfaninsu duk wata
yake warewa *ya*yansa, ga
Hannah ba laifi ta girma wahalar
da take sha a gida ta ragu
abubuwa da yawa ta fara
takawa Iya Abu da *ya*yanta
burki, tana kwatar kanta dole
wasu abubuwa suke raga mata.
Don haka kallo daya zaka yiwa
Haisam kasan dan gidan wani
gawurtaccen mai kudi ne
saboda suffarsa ta ya*yan hutu
ce, fari ne sol fatarsa mai haske,
yana da dara-daran ido da
dogon hanci, mai yawan gashin
ido dana gira gazar-gazar. Wani
dan siririn
gemu ne ya zagaye dan
madaidaicin bakinsa (qauter
million) gashi dogo mai *yar
madaidaiciyar kiba. Haisam yana
daya daga cikin irin mazan da
kowacce *ya mace take
mafarkin samun irinsa. Gashi a
makarantar *yan mata masu ji
da kudi da kyau ga gayu. Don
haka kullum Haisam sai ya sami
wasikun *yan mata akan
teburinsa a ofis dinsa sun jefa
masa, wai suna sonsa, soyayya
mai tsanani kuwa sai kawai yayi
dariya ya yaga ya zubar koda
kuma
ya hadu dasu bazai nuna musu
yaga sakonsu ba, *yan aji shida
ne suka fi yi masa wasikun
amma
wasu *yan aji biyar din suna
rubuto masa. Shi gani yake duk
hauka suke zasu gaji su daina,
gasu
kyawawa dasu amma baya
ganin kyawun, *ya*yan attajirai
amma shi bai dame shi ba, shi
kawai ya zo ya cika burin daya
kudira ya tafi ne. Senior Juwairiya
itace shugabar dalibai (Head
girl)
Juwairiya kyakkyawar gaskece
fara sol harma akan ce suna
kama da Hannah, gata
Mahaifinta
wani babban manager ne a
wani banki a Lagos, tana ji da
gata da dukiya ga tsananin
kokari tafi
kowa kokari a shekarar. Amma
sai Allah Ya jarabbeta da
tsananin son Auncle Haisam tun
ba yau ba gashi kuwa da yawa
daga cikin Malaman
sun mutu a sonta, ita bata son
su tafi son Haisam. Ta aika masa
da wasiku sunfi a kirga amma
shiru ko
alama Haisam baya nuna mata
Ma yaga wasikarta.
Data gaji da aika masa wasikun
saita dinga aika kawayenta
baro-baro suke tararsa su gaya
masa,
amsar daya basu cewa yayi duk
yarinyar data sake tararsa da
sakon Juwairiyya sai ya sabar
mata. Don haka Juwairiyya ta
rasa yadda zata yi ta shawo kan
wanda take so. Ranar wata
litinin da daddare an fito
karatun dare (prep). Juwairiyya
ta sami kan wata baranda ta
zauna tana tunani don ita son
Haisam harya fara dasa mata
wani ciwo da yake
damunta a zuciya har take kasa
karatu sosai gashi kuwa tafi
dukkan *yan makarantar kokari,
don haka nema aka nadata
shugabar dalibai.
Zaman da tayi wucewar Haisam
kawai take so ta gani sannan ta
iya bacci. Salaha Nura ita ce
babbar
aminiyar Juwairiyya tazo
giftawa zata tafi ajinsu taga
kawarta a zaune a baranda ita
kadai, taje
wajenta ta dade a tsaye a kanta
Juwairiyya bata sani ba. Ta
dafata sannan tayi firgigit ta
dago,
Salaha Nura ta zauna a kusa da
Juwairiyya ta ce "Juwairiyya
tunanin meye kike, ke kadai
kowa
yana aji? Juwairiyya ta nisa tace
"Allah Salaha ina son uncle sosai kamar zan mutu.
Salaha ta tuntsire da dariya ta ce
"Uncle Haisam wai? Shegu
sunan da kuka saka masa kuma,
to Juwairiyya yaya zamuyi, kin
rubuta a rubuce yaki, kin
aikemu ya zazzagemu idan kikaje da kanki qila ya yarda
Kwarjini yake mun bazan iya
tarar sa ba. Inji Juwairiyya.
Salaha ta ce "To maye abunyi?
Juwairiyya ta zunguri Salaha ta
nuna mata Haisam ne ya
tunkaro inda suke daga staff
quaters ya
karaso inda suke. Suka duka
suka gaisheshi cikin ladabi, ya
ce "Oh shugabar dalibaice da
labour
prepect? Suka ce mune Sir, ya ce
"Wato kun kora yara aji ku
kunzo kun zauna kuna hira ko?
Kamata yayi kufi kowa karatu
yanzu tunda kune masu shirin
yin WAEC da NECO da JAMB ko?
Suka amasa da "Eh ba hira muke
ba wani muke jira, Juwairiyya ta
marairaice murya ta ce "Amma
na ganshi yanzu zamu tafi
daman fatana in ganshi kawai.
Haisam ya
gane abun da take nufi sai
kawai yayi sauri ya katseta ya ce
"Idan zaku tafi gashi kuje S.S 1A
Science class ku bawa Hannah
Abubakar Imam. Ya mika mata
wata leda a daure ya juya ya
nufi ofishinsa ya shiga sannan
ya rufo kofar.
Juwairiyya ta ce da Salaha,
"Kinga abunda nake gudu ko
shariya ce da wannan mutumin
ko fuska
baya bani da zan gaya masa
abunda yake damuna.
Salaha Nura ta ce "To wai ni na
lura meye tsakanin Uncle Haisam
da Hannah Abubakar Imam ne?
Kamar duk makarantar nan yafi
kulata komai Hannah haka zaki
ji yana ambata kamar shi ya
rada mata sunan. Juwairiyya ta
ce "Ance abokin wanta ne wai,
kuma saboda Rauda Shitu
kawar Hannah
ce ita ai kanwarsa ce. Salaha
Nura ta ce "To kanwar abokinsa
ai zai iya sonta. Salaha ta karbe
ledar da ya bawa Juwairiyya ta
kwance sai suka ga magunguna
na ruwa dana kwaya ne, na
zazzabi dana tari ya saya mata.
Salaha ta tabe baki ta ce ''Abbas
"Lallai magunguna ya sayo mata
tafi karfin ma tasha na clinic din
makaranta kenan. Juwairiyya ta
ce "Zo muje nasan abunda zan
hadawa yarinyar nan, Salaha ta
taso suna tafe suna zancen suka
nufi ajin su Hannah. Juwairiyya
ta ce "Ba Uncle Haisam ya ce
kada wata ta kuskura ta kara kai
masa
sakona ba to ni kuma Hannar da
yake ji da ita daga yau ita zan
dinga aike wajensa. Salaha ta ce
"Kwarai kuwa haka za'ayi muga
ko itama zai korota din. Ta
wundo Juwairiyya ta leka ta ce
"Ina Hannah Abubakar? *yan aji
suka ce "Gata can a seat dinta a
kwance bata da lafiya, ta ce "Ko
ciwon ajali take ta taso ta
zagayo tazo ina kiranta. Nusaiba
ce ta
tasheta ta ce "Hannah kije
senior Juwairiyya na kiranki.
Hannah ta daga ido da kyar ta
ce "Bazan iya tashi ba bani da
lafiya, jikinta zafi kau kamar
wuta. Jijiyoyin kanta sunyi rudu-
rudu don ciwon
da yake yi mata. Juwairiyya ta
daka tsawa ta ce Hannah ta taso
Allah Yasa asibiti ne a kanta ba
jinya ba. Nusaiba da Rauda suka
rirrikota suka tasheta tsaye,
Juwairiyya ta daka musu tsawa
ta ce musu munafukai su saketa
ta zo da kanta. Haka Hannah ta
fara tafiya tana rirrike bango ta
fita ta zagaya bayan aji inda
suke. Juwairiyya ta mika mata
ledar
da Haisam ya bayar a bata suka
ce "Gashi in ji saurayinki.
Hannah tayi jigum tana mamaki
can ta
ce "Waye saurayina? Salaha ta ce
"Zaki sanshi munafuka.
Juwairiyya ta mika mata wata
takarda ta ce "Ki kaiwa Uncle
Haisam kice ina jiran amsa
yanzu
kice nace miki karki sake ki
dawo babu amsa.
Hannah ta fara tafiya jiri yana
daukarta ji take kamar zata fadi
saboda yini tayi cur a kwance
babu
ko dan tea a cikinta. Ta isa
ofishinsa ta kwankwasa yayi
mamaki da yaji ana kwankwasa
masa kofa yanzu, ya tashi ya
bude sai yaga Hannah a tsaye.
Mamaki ya kamashi ya ce
"Hannah lafiya? Keda baki da
lafiya kika iya tahowa? Hannah
ta cije baki
gami da rike bango kamar zata
fadi ta ce "Aikoni wajenka aka
yi. Ya ce "Aike kuma, waye ya
aiko ki? Ta mika masa wasika ta
ce "In ji senior Juwairiyya da
senior Salaha sunce dole in taho
musu da amsa
kar in zo babu amsa. Ya bata rai
ya karbi wasikar ya bude ya
karanta. Wasika ce irin ta kullum
daga
Juwairiyya ya ceci rayuwarta
tana sonsa. Haisam ya cikuikuye
ya wurgar ya ce "Sun baki
magungunanki? Ta ce "Ah ina
jin sune anan, ya
karba ya bubbude yana tsiyaya
mata a murfi yana
mika mata sai ta karba tasha. Sai
da ya tabbatar ta sha dukka
sannan ya daure ledar ya mika
mata ya ce ta wuce daki ta
kwanta gobe idan taga baza ta
iya fitowa aji ba tayi
kwanciyarta zai sanarwa da
duty master. Daga karshe ya ce
"Sai da safe Allah Ya
baki lafiya, Hannah ta ce "Amin.
Har ta juya zata tafi sai ta tuna ta
juyo ta ce masa "Me zan cewa
senior Juwairiyya? Ya ce "Ki ce
nace tazo ta karbi amsar da
kanta. Hannah ta amsa da to
sannan ta tafi. Daman su
Juwairiyya na zaune a wata
baranda suna hango su. Hannah
ta zo wucewa suka kirata tace
musu ta kai masa ya ce amsar
taje da kanta ta karba. Salaha ta
ce "Jeki to. Juwairiyya ta nisa ta
ce
"Kinga Haisam ko wallahi
wulakanci yake shirin yimin
tunda ya ce inje da kaina ni
nasan ba wata maganar
amincewa zai yi min ba. Saboda
ai na gani cukuikuye wasikar
tawa yayi ya yar a kasa, ya buge
da bata magani ai dole ma son
Hannah yake.
Salaha ta ce "Amma kuwa sunan
yarinyar nan gawa don sai taci
ubanta a makarantar nan, mu
*yan S.S.3 muce muna sonsa
yaki ya so junior mu ai bazai
yuba. Je ki kiji abunda zai fada
miki don muci uwarta da hujja.
Juwairiyya ta mike ta nufi
ofishin Haisam tana wani
karkade riga tana gyara fuska.
Tayi sallama gami da tura kofar
zata shiga ya dakatar da ita da
hannu ya ce "Tsaya daga nan
baranda kiji abunda zan fada
miki. Don me kike sake yimin
aiken wasika bayan nace kada
wanda ya sake zomin da
wasikarki. Kuma wanne rashin
tausayi ne da zaki taso yarinya
marar lafiya ki aikota, duk
daliban makarantar nan, sai
Hannah?
Me yasa sai ita zaki aiko
Juwairiyya? Juwairiyya ta tsuke
fuska ta ce "Amma Uncle Haisam
duk aiken dana keyi baka taba
kirawoni kace me yasa nake
aiko kawayena ba sai dai
kacewa *yan aiken duk wacce
ta sake zuwa zaka sabar mata.
Me yasa baka
fadawa *yar aike ba a wannan
karon saini ka kira?
Haisam ya fusata ya daka tsawa
ya ce "Ina tambayarki kina
tambayata? To bari kiji yauce
rana
ta karshe da zaki yimin haka. Ki
rike darajarki da mutuncinki a
matsayinki na *ya mace
budurwa.
Idan dole sai kinyi soyayya a
makaranta ba karatu ya kawo ki
ba to ga sauran Malam da suke
rububin sonki amma ni bani da
ra'ayin soyayya, this is the last
warning bana son sake ganin
sako daga wajen ki sai anjima
kije.
Wani jiri-jiri Juwairiyya take ji ta
juya ta tafi tana kwafa. Salaha
tazo ta tare ta a hanya tana
cewa "Meye na hangoki a
baranda,
ofishinsa ma ya hanaki shiga?
Juwairiyya ta ce "Ke dai muje in
baki labarin yadda muka yi.
Daman
lokacin tashi daga prep yayi duk
dalibai sun dungumo daga
ajijuwansu sun doshi
dakunansu. Don haka zUwairiyya
da Salaha Nura sai suka nufi
hostel a hanya ta zaiyana mata
duk yadda suka yi
da Uncle mai kyau wato Haisam.
Washegari talata da sassafe
bakwai da rabi a lokacin dalibai
suke firfitowa daga dakunansu
zuwa ajijuwansu domin daukar
darussa. Uncle Haisam a tsaye
yake kem a bakin get din hostel
yana kallon masu fitowa daga
ciki. Mamaki ya kama dalibai
ganin sabon al'amari meye
Uncle Haisam
yazo ya tsaya anan da sassafe
haka ba shine da duty ba, ba
ranar inspection ba kuma,
kowacce
idan ta ganshi sai ta duka ta
mika gaisuwa ta wuce "Good
morning Sir. Can ya hango
Rauda da Nusaiba da Pamella
suna tahowa daga nesa ya
dauka Hannah ce sai da suka
karaso yaga babu Hannah a
cikinsu. Bayan sun gaisheshi ya
ce "Yau
kuma ina Hannah ko jikin ne?
Rauda ta waiga gaba da baya
taga babu kowa sai ta matso
kusa dashi ta ce "Hannah ba
lafiya tana cilinic a kwance acan
ta kwana, gabansa ya yanke ya
fadi ya ce "Zazzabi ne
ya rufeta? Nusaiba ta ce
"Wannan yafi zazzabi Yaya,
Rauda ta ce "Su senior
Juwairiyya ne suka yi mata
duka da tsakar dare kusan
dukkan S.S 3 sai da kowacce ta
doki Hannah jiya ina ji a sume ta
fadi da kyar Matrons suka zo
suka hana su. Muma bamu san
me tayi musu ba. Kuka mu ma
muka kwana munayi.
Nan da nan Haisam ya canja, ido
ya kada yayi jawur gashin
jikinsa ya mimmike kai kace
muku-mukun
sanyi ake. Amma duk da sanyin
safiya zufa yake yi. Ba tare daya
ce tak ba ya juya ya nufi clinic
inda
Hannah take a kwance ya same
ta rikkicif bata sanma inda
hayyacinta yake ba. Abinka da
farar
fata sai sawun bulalunda suka yi
mata jawur a jiki, har wuyanta
da fuskarta shatin bulala ne
lambar.
Ya dade a tsaye yana kallonta
kawai yasa hannu ya cire mata
wani ganyen Maina daya makale
mata a wuya a sanadiyyar duka
sai yaji jikinta zafi kau kamar
wuta, yaja mayafin dake kan
gadon ya
lullubeta. Babu kowa a clinic din
Nurse din ma bata nan, ya juya
ya fita a fusace ya nufi ofishin
principal. Ya shiga ofishin gami
da yin sallama ya sami waje ya
zauna bayan sun gaisa ta dubi
Haisam ta ce "Haisam lafiya yau
na ganka rai a bace duk
wannan fara'ar taka? Ya ce
"Dole raina ya baci saboda
kusan kashe wata yarinya akayi
a daren jiya a makarantar nan
*yan aji shida ne suka daki wata
*yar aji hudu da tsakar dare
kamar zasu kasheta tana cilinic
a kwance "Principal ta zabura ta
ce
"Subahanallahi,
ta danna
kararrawa masinja ya shigo tace
maza yaje aji shida ya kira mata
Juwairiyya.
Haisam da pricipal na zaune
sunyi jigun kowa yana tunani a
zuciyarsa. Can saiga Juwairiyya
ta karaso ita da wani Malami
mai suna Sahabi tazo ta durkusa
a kasa ta gaishe da principal,
principal ko ansawa bata yi ba
ta rufe Juwairiyya da fada tana
cewa "In har ba zaki iya hana a
aikata laifi ba a makarantar nan
banga amfaninki ba a matsayin
shugabar dalibai. Haisam ya ce
"Madam ai ita ce ta gaiyato
sauran *yan aji shidan suka
hadu suka yi dukan. Principal ta
ce "Oh har da ke head girl ku ka
hadu aka kusa kashe yarinya,
kiyi kneel down yau sai kun
yabawa aya zakinta. Uncle
Sahabi yayi caraf ya ce "Madam
tsaya kiji, Juwairiyya ta fadamun
duk abunda ya faru daman nan
zamu taho wajenki muka hadu
da masinja a hanya, a gaskiya
yarinyar ce bata da kunya wai
cewa tayi zata yi dambe da
Head girl shine Juwairiyya ta
danyi mata bulala uku labour
prefect tayi mata biyu. Ga
yarinyar can ma a
aji tana daukar darasi babu
wani zancen kisa. Haisam ya
fusata yayo kan Sahabi da fada
yana cewa "Karya zanyi musu?
Yarinyar da duk makarantar nan
babu mai shirunta da ladabi
yaushe zata ce zata yi fada da
Head girl? Kawai baza ka tsaya
kayi bincike ba don sun gaya
maka karya da gaskiya shine
zaka yarda, kaje clinic kaga
jikinta a farfashe bata san ma
inda hayyacinta yake ba.
Sahabi ya ce "Madam don Allah
ki raba mana rigima ki aika
clinic a dubo idan akwai wata
marar lafiya.
Babu kowa ta warke ta mike,
ba'a gabanmu Hannah tazo ta
wuce ba dazu ko ba Hannah ba
ce
wacce kake cewa an kusa
kasheta? Kuma kai duk wannan
hakilon da kake akan Hannah
saboda kai
saurayinta ne fa yasa kake
wannan. Sauran da ake duka ka
taba magana? Principal ta lura
maganar nan babba ce sai
manya sai ta ce da Juwairiyya ta
tashi ta tafi aji zata aiko ayi
kiranta. Fusakar Juwairiyya cike
da murmushi ta fice, principal ta
kalli Haisam ta ce "Kwarai tun ba
yau ba ansha fada mun kana
soyayya da Hannah. Dokar
makarantar nan an hana daliba
da Malami yin soyayya. Yanzu
na gane manufarka don an doki
budurwarka shi ne yasa kayi
magana ko? To daga yau zan sa
C.I.D
kada ka kuskura in sake jin ance
kana soyayya. Haisam ya fusata,
ransa ya baci, zuciyarsa ta hau
tafarfasa. Ya dakawa Sahabi
tsawa yaje har gabansa yana
nuna shi da hannu ya ce "Kai
Sahabi karya kake yi ni nafi
karfin ka yi min sharri kai da
Juwairiyya zaku gane kuranku a
makarantar nan.
Ni kake cewa ina son Hannah
ko? Bayan da bakinka kazo ka
sameni kana rokona in hadaka
da kanwata Hannah kana sonta
naki nace kabarta tayi karatu
ashe kana kullace dani kasa aka
yi mata wannan dukan ko? Ke
kuma principal kin goyi da
bayansu sun daki *yar mutane a
banza ko? To ni
sai na daukarwa Hannah fansa
da kaina. Ya kada kai ya fice
Sahabi ya juya ya kalli Principal
ya ce "Kinji kuma ta inda ya
lauya magana ko? Ta ce
"Kyaleshi bayan kai ma Mr. Ojo
ya fada mun cewa son Hannah
yake don haka kaci gaba da kula
da
su. Haisam ya nufi staff quaters
ya shiga gidansa ya
zauna a falon yana huci kamar
ya kashe kansa
yake ji saboda tsananin bakin
ciki yau ko darasi ba
zai je yayi ba. Yini yayi cur a gida
ya kudiri niyyar zai dauki fansa a
kan duk mai hannu a cikin
wannan
al'amarin, wai Sahabi ne zai yi
masa haka Sahabin
da ke zuwa har gida ya ce ya
taimakeshi ya shawo
masa kan Hannah taki kulashi
shine yau ya ce
shine yake son Hannah, wai
Juwairiyya da kanta
take cewa rashin kunya Hannah
tayi mata zata yi danbe da ita
wai shine tayi mata bulala uku,
ita
kuma principal da kanta take
bin bayansu bayan
tasan Hannah tasan halinta
tasha yin kwatance da
ita a assembly akan tafi kowa
da'a da ladabi shine
har ta yarda da kintsin da suka
yi mata ko da kyau,
haka Haisam ya dinga nanatawa
a zuciyarsa. Haisam bai fita daga
gida ba sai da yamma misalin
karfe biyar ya shigo cikin
makaranta a lokacin
dalibai suna prep din yamma ya
wuce kai tsaye
ajinsa don yaga jikin Hannah, a
zaune ya ganta a
kan kujerarta ba laifi jikin,
burdin bulalar ya dan
warware zazzabain ya sauka sai
dai bata iya bude idanuwanta
sosai.
Ya ce da ita. "Hannah ya jikin?
Cikin sanyi murya ta
ce "Da sauki, ya ce kinsha
magungunan naki? Ta ce
"Eh ina sha. Wani masinja ne ya
leko ajin ya ce
Malam Haisam ka zo inji
principal. A fusace Haisam
ya ce "Meye kuma? Dan aiken ya
ce "Waya aka bugo maka zaka
dauka a ofishinta, ya ce "Gani
nan
zuwa Haisam ya juya ya dubi
Rauda da Nusaiba ya
ce "Ku dinga kula da Hanna ku
tabbatar tana cin abinci, kunji
ko? Suka amsa da "To zamu kula
da
ita, sannan ya fita ajin ya nufi
ofishin principal yana
isa ofishin yayi sallama ya shiga
ya gaisheta a murtike. Ta ce
"Yayanka ne Habib yake son yayi
magana da kai nace ya sake kira
nan da minti biyar
za'a kira... Kafin ta rufe bakinta
wayar ta fara kara
Haisam yasa Hannu ya dauka ya
gaishe da Yaya
Habib yaji da kyar Habib yake
amsa wa rai a bace
Yaya Habib ya ce "Kai Haisam mu
fa ba yara bane kanana kana ji
ko? Saboda me zaka dinga
mana
wasa da hankali? Kace shekara
uku zaka yi a
makarantar nan sannan ka bari
yanzu shekara uku
sun cika, last week da ka zo aka
gaya maka cewar
ka bar teachin dinnan ka dawo
gida ga
kamfanonin Baba aiki yayi mana
yawa muna neman ma'aikata,
ka ce da zarar ka koma kafin
karshen watan nan zaka dawo
gida kabar koyarwa gashi munji
ka shiru. Kujerarka na nan na
jiranka ga Ramlah nan na
jiranka itama.
Har anyi bikina da Jidda har ta
haihu *yar mutane na zaman
jiranka kazo ayi bikinku. Wai
shin me ka zamar da mune, har
nawa kake da zaka dinga juya
mu? Don
haka karka sake nazo
makarantar nan da kaina ka
rubuta takardar barin aiki kabar
koyarwan nan ka
dawo gida muna nan muna
jiranka. Kai baka kishin dukiyar
Ubanka sai gwamnati me
gwamnati zata
baka da kake mata wannan
wahala, me kake nema ka samu
wanda a gidanku baza a baka
ba? Haisam ya fusata ya ce "Ka
gama maganarka? To bari in
fada maka gaskiya ba zan bar
koyarwa ba ina nan
bazan dawo gida ba, ya kifar da
kan waya ya fice,
principal ta bishi da kallo har ya
fice.
Cabdijan aradun Allah za'a
kwasheta da zafi,,, kar dai a ce
Haisam son Hannah yake. Hmm
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 11
Wayar ce ta sake yin kara tasa
hannu ta dauka taji
Habib ne. Ya ce "Ina Haisam din?
Ta ce "Ya fice, ya
ce "Ranki ya dade kema har da
laifinki tun rannan
Baba ya kiraki har gida ya ce kiyi
murda-murda
kisa a koreshi daga
makarantarki zai biya ki ko
nawa ne. Kika ce bazai yu ba,
wannan yaron ko
kashe shi za ayi bazai bar
makarantar nan ba.
Wanne irin lallashine ba'ayi
masa a gida ba yaki ya
bar koyarwar, Principal ta nisa
ta ce "Habib tunda
kaji nace bazan iya sawa a kori
Haisam ba to babu
yadda zanyi saboda wannan
makarantar ta gwamnatin
taraiya ce daga can kololuwa
aka dauki
Haisam haka kuma korarsa sai
daga can Abuja.
Dana bincika ma babban
director na federal shine
ya dauke shi aiki Alh. Sabi'u
Auwal abokin
babanku ne ko? To babu kuwa
yadda za ayi na
hada baki dashi a kori Haisam
daga makarantar nan. Habib ya
ce "Zanzo makarantar watakila
nan
da sati biyu, idan na dawo dawo
daga tafiya dole
ne ma ya bar makarantar don
yaga anayi masa
sakwa-sakwa ya dauka tsoronsa
ake yi. Don ni
banga uwar da yake samu ba a
makarantar. A
haka dai suka yi sallama suka
ajiye kan wayoyi.
BAYAN SATI
Ashe ba Sahabi ba kadai akwai
Malamai da yawa da
suke son Hannah, sai yanzu
suka dinga baiyana.
Ranar talata data zagayo Haisam
da sauran Malamai
Uncle Sahabi da Uncle Yusif suna
zaune a gindin
bishiya da prep din yamma sai
Uncle Yusif ya aika wata yarinya
ya ce taje S.S. 1A ta kira masa
Hannah
Abubakar. Haisam na zaune
yana tunanin lafiya
yake kiran Hannah. Hannah ta
karaso tazo ta
durkusa ta gaishe su, Uncle
Yusif bai amsa ba ya ce
"Hannah yau zan nuna miki
karshen taurin kai,
girman kai da ji da kai. Don haka
kije ki karyi bulala katuwa mai
kauri dai-dai tsawanki ki kawo
min.
Haisam na zaune yana kallonsu
Hannah ta tashi
jikinta a sanyaye ta nufi dawa,
can ba da dadewa ta
taho dauke da wata zabgegiyar
bulala. Ta zo ta
durkusa ta mikawa Uncle Yusif
ya ce tayi Kneel
down ta daga hannu ya kuwa
tashi ya fara zabgawa Hannah
wannan reshen. Haisam ya kau
da kai gefe kawai yayi shiru,
Yusif yayi mata bulala
kamar sau takwas sannan ya ce
"Kinsan me kika yi
min? Cikin shesshekar kuka
Hannah ta ce "Ban sani
ba, ya sake daddagewa ya sakar
mata wani dukan,
ya ce "Kin tuna yanzu? Cikin
gigicewa Hannah ta ce "Na tuna,
ya ce "To me kika min? Ta ce
"Jiya daka
aiko kace inzo in sameka a
lambu banzo ba. Ya ce
"Yauwa ashe dai kin gane to yau
sai na lahira ya fiki
jin dadi don kin samu ma ana
sonki, ke din me da
zaki yimin wulakanci? Sahabi ya
tashi ya karbi
reshen nan ya zazzabga mata
sau biyar da karfi kuwa ya ce
"Tashi saura ki ki zuwa nan
gaba idan
muka aika kiranki da prep. Tana
tafe tana rusa
kuka ta tafi ajinsu. Sahabi yana
cewa "Bari muga
zata zo da prep din daren
kuwa? Idan bata zo ba
wallahi double din wannan
zamu yi mata. Haisam
yayi tsaki ya mike ya nufi ajin su
Hannah, zuciyarsa cike da
tsananin bakin ciki da tausayin
Hannah.
Yaje ajin ya tambaya aka ce
Hannah bata shigo ba.
Nan da nan hankalinsa ya sake
tashi yayi waje da
sauri yana dube-duben ko daji
ta tafi ta zauna tana
kuka, yazo wucewa ta ajijuwan
*yan aji shida yaji
nishi kamar wata tana tsallen
kwado ya leka ta wundo da
sauri yaga ashe S.S.3 A sun taru
kusan
dukkanninsu suna azabtar da
Hannah ta jike
sharkab saboda gwale-gwale da
duka. Juwairiyya
ce rike da dorina a hannunta
tana biye da Hannah
tana tsallen kwado tana fyada
mata. A fusace
Haisam ya daka musu tsawa duk
suka waigo wasu suka ruga
ajijuwansu suka zazzauna. Ya
hango
wani masinja ya kirashi ya ce
yaje daji ya karyo
masa manya-manyan reshinan
bishiyar maina ya
kawo masa. Ya zagaya cikin
ajijuwan ya ce
dukkaninsu su firfito waje bai
rage kowa ba duk
S.S3 din. Sun dauka abun da
wasa ne suna tafe suna
rangwada suna tauna cingam,
Juwairiyya
kenan suka firfito waje daga
ajijuwan ya ce su fara
tsallen kwado suma, yaje cikin
ajin ya tarar da
Hannah sharkab tayi gumi ga
sawun bulala nan
duk jikinta lambar. Yasa hannu
ya tasheta tsaye ya
ce ta daure ta tafi daki ta
kwanta. Tana tafe tana layi tana
rike bango ta nufi hostel.
Suna tsallen kwadon a duk
yadda suka ga dama a
zatonsu zai ce su koma aji su
zauna suka hango
masinja dauke da himilin bulali
kai kace jakuna za'a
daka tafka-tafka da su. A fusace
Haisam ya karbi
bulala nan ya fara taf-tafka
musu ita ta ko ina, ji kake
rududu suna tsallen kwado
suna yi yana
binsu duk wcce ta fadi kota
tsaya a baya yana tafka
mata. Wani dogon waje ya nuna
ya ce har can zasu
kai kuma su juyo. Haka suka
dinga yi suje su juyo
har sai da ya tabbatar kowacce
ta jigata hawayen
ma ya kasa fitowa sannan ya ce
su biyo layi kowacce ta zo ta
kwanta flate sannan ya
shassharba mata reshen nan
sau goma sha biyu.
Bayan jikinsu yayi kaca-kaca ya
farfashe, kuka
wiwi dan kwalayensu a hannu
ga kafa ta sage
babu damar tafiya, Juwairiyya
tafi kowa shan wuya
duka yayi mata kamar Allah ne
Ya aiko shi ko kirgawa ma baya
yi da bulalai suka kakkarye yasa
kafa ya dinga ball da ita daman
yana ciki da ita.
Kuka wiwi suke suna bashi
hakuri daga yau baza
su sake ba. Sannan Haisam ya
kyalesu anan a
kwance wasu a durkushe.
Tunda Haisam ya zo
makarantar nan bai taba zagin
wata ba balle duka yau sai ga
Haisam ya canja fuska babu
digon
rahama murtik da ita kamar zai
kashe su haka yayi
susu ligi-ligi dukan da babu
Malamin daya taba
yin irinsa a makarantar ko
displine master baya yin
irin wannan duka. Labari ya kai
gidan principal, a
gigice ta fito ta taho a bakin
ofishinta ta gamu da Haisam. Ta
dube shi sai taga ya canja gaba
daya sai
ta shiga tsoron tayi masa
magana. Can ta ce
"Haisam wanne irin duka
kayiwa S.S3 yau, me suka
yi maka? Ya juyo a fusace ya ce
"Ki tambayi kanki
da kanki daman na fada rannan
tunda baza ki iya
daukar mataki ba akan abun da
su Juwairiyya suka yiwa Hannah ba
to ni na dau fansa, kuma zan iya
yin
haka akan kowa duk wanda
yake marmarin
takurawa Hannah a makarantar
nan.
Principal ta rike baki kawai
tana kallon Haisam, ya wuce ya
barta anan a tsaye ya nufi
gidansa. Yana jiyo
Malaman da suke zazzaune a
wajen suna cewa "Ai kuwa
yarinyar nan sai zaman
makarantar nan ya
gagareta don sai mun zane ta
itama. Nan dai
principal ta hau fadace-fadace
tana cewa "Dole ne
na kira meeting da manyan *yan
federal akan abun
da Haisam yake min a
makaranta.
Magaruba tayi Uncle Yusif da
Uncle Sahabi suka nufi
gidajensu ta jikin gidan Haisam
suka zo wucewa
yana jin abunda suke fada wai
da prep din dare
zasu kira Hannah suyi mata
dukan tsiya. Shima
Haisam din yaji idan da dadi. A
haka suka rabu
kowanne ya nufi gidansa.
Haisam na idar da sallar
magariba yayi shigar wata riga
mai gajeren hannu damammiya
(body hook) ya dora wata suit
aka ya
fita ya nufi gidan sahabi. Ya
kwankwasa kofa,
Sahabi ya zo ya bude fuskar
Haisam ce ya gani a
murtike ta bashi tsoro. Ya ja da
baya da sauri.
Haisam yasa hannu biyu da karfi
ya angaza shi ya
tafi taga-taga ya fada kan
kujerar da ke falon. Haisam ya
shigo cikin falon ya mayar da
kofar ya
datse. Sahabi yayi tsuru-tsuru a
zaune Haisam ya
karaso inda yake zaune yasa
kafarsa daya ya taka
kujerar da Sahabi ke zaune ya
duko dai-dai fuskar
Sahabi suna kallon-kallo. Sahabi
yatsune fuska
ya ce "Meye haka Haisam lafiya
ko ka zama dan ta adda ne kazo
har gidana ka angajeni. Ya
yunkura
zai tashi yaji Haisam ya turashi
karshen kujera,
wannan karon hannu yasa ya
danki wuyan Sahabi.
Sai ido kuru-kuru an shake shi
kai ka ce mujiya ce
ta fada rami. Haisam yasa hannu
a aljihu ya ciro
wata *yar karamar wuka ya
bude ta tana walkiya ya
shinshinawa Sahabi a hancinsa
ya ce "Ka kula da
abun da nake so na fada maka,
idan ka kiyaye ka
kubuta idan kuwa kaki to
kaiconka kaga wannan
wuka zan iya lumata a cikinka
ko na yanka ta a
wuyanka ka fadi ka mutu ko? To
ina da niyyar
aikata haka in har ka kuskura ka
sake takurawa Hannah a
makarantar nan. Zan iya kashe
ko waye
ba kai kadai ba don haka ka
kiyaye. Sannan
Haisam ya sake shi ya mayar da
wukarsa aljihu ya
juya ya bude kofa ya fita yabar
Sahabi nan zaune
yana tunani kamar a mafarki
yau yaji kanshin
mutuwa baro-baro, yana fadin
"Lallai Haisam da gaske yake zai
iya kisa a kan yarinyar nan fa. A
bayyane.
Haisam na fita gidan Uncle Yusif
ya shiga
kasancewar duk yawancin
Malaman samari ne
babu mata a gidan. Daya taba
kofar yaji a bude sai
kawai yasa kai. Kicibus suka yi
Yusif ya fito daga wanka daure
da dan tawul a jikinsa. Yayi
mamaki
daya ga Haisam a tsakiyar
falonsa ko sallama bai ji
ba, murtik Haisam yake babu
walwala, shima sai ji
yayi an tunkudeshi kan kujera
yayi masa gargadi,
kamar yadda ya yiwa Sahabi ya
fito ya barshi nan
zaune yana mamaki. Saboda
tsabagen tsorata su Yusif ko
fitowa basu sake yi ba sai da
safe,
ballantana su je su daki Hannah
da daddare kamar
yadda suka shirya yi. Haisam
tunda ya shiga gida
bai sake fitowa ba sai washe
gari da misalin sha
daya na rana yana da lesson a
S.S 2B zai yi musu
Geography. Yana doso ofishin
principal ya hango motar Yaya
Habib yana cikin ofishin
principal, kuma
yasan yau za'a yi tane kawai
donshi babu mai
rabashi da makarantar nan. Ya
karaso da sauri ya
nufi ofishin principal tun daga
kan baranda yake
jiyo kukan Hannah ya shigo a
fusace gami da yaye
labulan kofar bazar. Ya tarar da
Hannah a durkushe ga jakar
kayanta nan a gabanta, principal
tana
rubuta mata takardar kora
(dismisal letter) takardar
kora daga makaranta kwata-
kwata ga Yaya Habib
a zaune yana cewa "Ai idan yaga
tabar makarantar
zai bari shima dole. A gigice
Haisam ya karaso ya
kalli Yaya Habib ya kalli principal
yaga da gaske suke sunsha
kunu. Hannah na kuka kamar
ranta
zai fita tana magiya don Allah
suyi hakuri. Haisam
ya tabbata muddin principal ta
gama rubuta
dismisal letter nan tasa aka yo
typing dinta ta buga
stamp aikin gama ya gama ko
gaban wa aka je
baza a dawo da Hannah
makaranta ba, kuma duk sharrin
data yi mata a jiki ya zauna babu
gogewa,
sai hankalinsa ya tashi matuka.
Nan da nan ya hau magiya yana
rokar principal
kada ta kori Hannah shi ya yarda
duk abunda suka
ce yayi zai yi zai ma bar
makarantar amma a bar
Hannah tayi karatu. Yaya Habib
ya kalleshi a wulakance ya ce
"Wa zai sake yadda da
alkawarinka? Kai da baka cika
alkawari tun yaushe
kake cewa zaka bar makarantar
nan. Haisam ya
juya ya dubi principal ya ce
"Madam don Allah kada
ki rubuta disimal letter nan ni
zan bar makarantar
ku bar Hannah tayi karatu,
principal ta harareshi ta ce
"Bazai yuwu ba kai da ka kusa
kashe *ya*yan
mutane akan wannan yarinyar
nayi maka magana
ka nuna ko nima zaka iya yimin
haka idan na daki
Hannah kaga gara kai da ita duk
ku tafi kafin
dukan ya dawo kaina. Wasikar
kora ai na riga na
gama rubutawa typing kawai
za'ayi. Ta danna kararrawa
masinja daya ya shigo ta ce
dashi
"Maman Joy tana nan a
ofishinta, a bude yake? Ya
ce "Eh yanzun nan ta shiga. Ta
ce "Ka kai mata
takardar nan ta bugota yanzu ta
baka ka kawo
min. Tana mikawa masinja
Haisam yasa hannu zai
fisge sai Yaya Habib yayi sauri ya
fisge ya ce "Ni kazo ka kwata a
wajena tunda ka zama marar
kunya. Haisam ya fusata ya
dakawa masinja tsawa
ya ce ya fice daga ofishin nan.
Sum-sum ya fita.
Kukan da Hannah take ya sake
tsananta taga an
fara rigima a kanta.
Haisam ya wawuro wata adda a
bayan kyauran ofishin irin ta
yankan ciyawa ya dora a kan
kirjin
Yaya Habib. Wanda mamaki ya
hana Yaya Habib yin
motsi daga kan kujerar da yake
zaune. Haisam ya
ce "Hakika zan iya kashe duk
wanda yake kokarin
jefa Hannah a cikin tashin
hankali da wahala a
rayuwarta. Ban dauka zan
sameka kana daya daga cikin
irin wadannan mutane ba,
amma duk da haka
ba zan karya alkawarina ba. Kai
Yayana ne Uwa
daya Uba daya da irin soyayyar
da Mahaifanmu
suke mana, ka duba kuma irin
soyayyar da muke
yiwa junanmu don haka bana
so na zama ajalinka.
Ba kuma zan bar makarantar
nan ba har sai na cika burina
dana kudira akan Hannah.
Hannun Haisam
rike da adda akan kirjin Yaya
Habib karkarwa yake duk
jikinsa yake hawaye ne yake
shatatowa daga
idanuwan Haisam gaba ki dayan
sai ya canja, Yaya
Habib ya tabbata Haisam yakai
kololuwar bacin rai
don shi yasan yadda bacin ran
Haisam yake abun babu kyau. Da
wuya dai yayi fushi abu da yawa
bai
cika bacin rai ba sai an kai shi
bango idan ya hau to
kowa sai ya tsorata kuma mai
lallashinsa ya sauko
sai an sha wuya kuma idan
ransa ya baci zai iya yin
duk abunda ya ce zaiyi. Hannah
ta kwala kara ta ce
"Yaya Haisam kada ka kashe dan
Uwanka a kaina na yarda ni zan
bar makarantar. Dan Allah Yaya
Haisam, dan Allah kayi hakuri.
Wani zazzafan
hawaye ne ya ci gaba da
zubowa daga idanuwan
Haisam a tsaye yake kawai ya
kurawa Yaya Habib
ido rike da wannan adda a
wuyan yaya Habib.
Principal kuwa tuni ta daka
tsalle tayi lungu tana jiran taga
yadda Haisam zaiyi da Yaya
Habib sannan
ya dawo kanta. A fusace Yaya
Habib ya yunkura zai
tashi Haisam yasa Hannu ya
turashi kan kujerar ya
koma ya zauna. Haisam ya ce
"Bani takardar
hannunka. Yaya Habib ya ce
"Son Hannah kake? Ya
sake fada cikin tsawa ya ce
"Tambayarka nake sonta kake
shi yasa ka kasa barin
makarantar?
Haisam ya ce "Burina inga
Hannah tana cikin farin
ciki a rayuwarta kuma in kwatar
mata *yancinta
kamar kowacce yarinya tunda
ita ba baiwa bace.
Gatan Hannah Allah, sai kuma ni
a duk duniyar nan.
Cikin sanyin jiki Habib ya
mikawa Haisam takardar a
sanyaye sannan Haisam ya
dauke addar daga kan
kirjinsa, ya wurga bayan kyaure
ya dauki jakar
kayan Hannah yaja hannunta
suka fice. Habib da
principal suka bishi da kallo.
Suna fita principal tayi
ajiyar zuciya don da kyar
numfashinta yake fita
saboda tsabar ta tsorata ta
tabbatar yadda Haisam ya
harzuka yau zai iya kashe
Yayansa balle
kuma ita. Bayan wani lokaci mai
tsaho suna zaune shiru
babu wanda ya iya magana
suna tunani kawai.
Yaya Habib ya nisa ya kalli
principal ya ce "Madam
yaron nan da gaske yake don
haka kada a kaishi
bango ya zo ya kashe wani a
dinga kai kawo a kotu, ina
ganin a kyalesu kawai don Allah
a daina
dukan yarinyar balle har ya
harzuka yayi kisa
domin Haisam zai iya aikata
hakan tunda ya furta
yana da zuciya sosai, amma fa
sai an kaishi bango
dan bai taba cewa zai yi kisa ba
sai yau akan
yarinyar nan, zanje in sanarwa
da Mahaifinmu. Ya mike ya fita,
principal kuwa dakyar take iya
magana saboda tsoron Haisam
tana ganin zai iya
binta gida cikin dare ya kashe
ta. Daga karshe ta
yankewa kanta shawara gwara
taje ta sami Haisam
ta bashi hakuri suyi sulhu. Ta
kuma yi masa
alkawari baza ta sake yadda
kowa ya takurawa Hannah ba.
Haka kuwa tayi ta sami Haisam
har gida
cikin lumana suka zauna ta
bashi hakuri suka yi
sulhu. Tana fita Haisam ya
tuntsire da dariya dadi ya
lullubeshi ya ce "Haisam!
Hannah!!.
Kwanci tashi su Hannah sun
shiga aji shida (S.S.3)
sune manya. Cikin ikon Allah da
hukuncin Allah Hannah tazo tafi
kusan duk *yan makarantar
kokari saboda tun tana zuwa ta
takwas ta fara
zuwa ta biyar daga nan ta
kwacewa Pamella Matin
position dinta ya zamana Rauda
ta daya, Nusaiba ta
biyu ita take zuwa ta uku.
Tafia tayi tafiya sai ga Hannah
tazo ta daya a ajinsu wani lokaci
Rauda ta kwace kayanta idan
Nusaiba ma ta hargitso sai ta zo
ta
kwace itama, haka dai ake ta
fafatawa. Amma
yanzu da suka shiga aji shida
har Malamai ma fadi
suke Hannah tafi su Rauda
kokartawa don sau da
yawa ko tambaya aka yi a aji
Hannah ce take
amsawa sau tari. Sannan a class
work da Assignment tafi kowa
ci, an basu mukamai daban-
daban. Hannah Abubakar Imam
itace shugabar dalibai (Head
girl) Nusaiba mataimakiyarta.
Rauda
kuwa dake tayi kaurin suna a
wajen iya rawa da wasanni
(Games) harma ake mata lakabi
da Janet Jacson sai aka bata
social prefect da games prefect
mukamai biyu aka hada mata
kuma tayi murna matuka da
wannan mukamin nata. Duk
ranar social
night har koyawa yara rawar
disco kala-kala take
yi. Hannah ma ta dace da
mukamin saboda ana son
Head girl ta zamana mai kokari,
wacce ta iya turanci
sosai, mai gaskiya, ladabi da
biyayya, mai kamun kanta ba
ballagaza ba, mai aji da tausayi
da adalci.
To duk wadannan Hannah ta
hada su don haka
nema da aka tace aka zabeta.
Domin a yanzu
Hannah ko Hausa bata cika yi ba
turanci ya kama
bakinta sosai Haisam har
mamakinta yake idan yaji
tana zuba turanci. Tana da jan
aji Hannah ba kasafai ta fiye
shiga cikin *yan mate dinsu ba
suna
hayaniya. Gata da tausayi
musamman ga yara *yan
kananan aji, babu ruwanta da
cin zali kuma bata
yarda kawayenta suci zalin yara
a gabantaba, tunda
ita ce shugabar dalibai tana da
ikon ta hana sauran
prefect. Wannan halaye na
Hannah ya sake fito mata da
kyakkyawar surarta. Hannah ta
sake gogewa abun
har baya misaltuwa ta yi kyau
kai kace ba *yar
Africa bace. Yaya Haisam yasan
irin mayukan da
kayan sawar da suka dace da
jikin Hannah.
Tsadaddun riga da wando da
riga da siket kala- kala Yaya
Haisam yake hadawa Hannah sai
dai
kawai idan ta dawo hutu ta
tarar ya aje mata a
gidan Uwar biyu, daman tun ba
yauba baya ga
Mahaifinta babu wani da take
ganin girmansa a
duniya irin Haisam. Amma da
yake Haisam mai
wasa da dariya ne da dalibai
suna wasa da dariyarsu a aji
kamar yadda ya saba yi musu
tun a
aji daya.
A garin su Hannah kuwa
Hannah har gizo take yi
musu, gani suke kawai baturiya
ce ta zo tace ita ce
Hannah, duk ranar da Hannah
zata dawo gida hutu
samari har tsayawa suke a
hanyar da zata wuce suna
kallonta, mata kuma ta katanga
suke lekowa.
Ana cewa Hannah ce fa *yar
Malam Habu a garin turawa take
karatu. Hannah sai tayi
murmushi
kawai ta wuce.
A gidan su kuwa Iya Abu da
*ya*yanta daina
magana suka yiwa Hannah
sunga wannan ci gaba na
Hannah daga Allah yake, babu
irin asirin da
basu yi mata ba akan a korota
daga makarantar ko
kuma ma ta haukace amma
baici ba. Hannah tana
dawowa da duk kayayyakin
amfani wadanda zata
yi amfani dashi har hutu ya kare,
ko ta bawa su Iya
Abu da *ya*yanta sai suce basa
so. Sai tayi hutunta kakaf ta bar
gidan Iya Abu ba ta bata abincin
da
suke dafawa ba. Ita kuwa
Hannah daman tafi son
haka domin ita yanzu ta saba da
cin mai maiko a
makaranta, tuwon dawa miyar
kuka sai su Iya Abu.
Madara da biskit ne abincinta a
lufge a jakarta a
dakinta. Sabulun wanka dana
wanki masu kamshi take amfani
dasu ita da Mahaifinta. Ta bashi
yayi
wanka ta wanke masa kayansa.
Malam Habu yana
jin dadi sosai da wannan abu da
Hannah take yi
masa. Yasan dole idan Hannah
ta zo zata kawo
masa kudi da abun duniya, ga
dinkuna da take
kawo masa tace inji Haisam.
Silifas dan madina dana gayu
yanzu Malam Habu yake sawa,
tsaf-tsaf dashi
na kashewa ya daina gagararsa.
Hmm! ***ajiyar zuciya da
lumshe ido** wannan wasan
yafi karfina,
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 12
Hannah ta zama tamkar wata tauraruwa mai haske cikin taurari a makarantarsu. Akwai kungiyoyi (clubs) a makarantar da yawa, tun Hannah tana aji daya ta shiga kungiyoyi daban-daban. Kuma duk wasannin kwaikwayon da za a yi a kowacce kungiya sai an saka Hannah ko tana so ko bata so saboda kyawunta. Tun ana sata a matsayin yarinya har aka zo ake saka ta a matsayin budurwa. Don haka Hannah ta kware sosai wajen iya wasan kwaikwayo suna fita suje makarantu daban-daban a fadin kasarnan, kamar su F.G.C Azare, F.G.C Bauchi, F.G.C Kano, F.G.G.C Bakori dadai sauransu, saboda kyawun Hannah da iya acting dinta ya jawowa F.G.G.C Kazaure suna da farin jini a wajen daliban sauran makarantu, kowa ya budi baki sai ya ce a F.G.G.C Kazaure da suka zo makarantarmu akwai wata mai kyau Hannah abubakar ta iya wasa. A yau da yamma su Hannah ne suke gwaji (rahazal) din wani wasan kwaikwayo da zasu je Unity Gwaram suyi, sati mai zuwa. Kungiyar *yan Hausa fulani ne suke yi, Malam Haisam shine shugaban *yan Hausa club, shine Malamin kungiyar (club master) don kawai ya farfado da al'adun Hausa a makarantar, ya kuma hada kan Musulmai yara da manya ya zamana sun hadu a waje daya yare daya suyi raye-raye da wake-wake da wasannin kwaikwayo tare.
Hannah Abubakar itace a matsayin yarinyar mai suna Talatu cikin wasan kwakwayo, Maryam Tijjani itace a matsayin saurayin ciki mai suna Abdul. Haisam ne ya rubuta labarin wasan kwaikwayon. A yadda wasan kwaikwayon yake Maryam Tijjani (Abdul) saurayin ciki shine zaiyi tafiya kasar libiya karatu sai yayi shekaru hudu acan sannan zai dawo. Ga budurwarsa Hannah wato Talatu a cikin wasan, sunyi alkawarin zasuyi aure daman sai tafiya tazo masa yazo tafiya ya barta. Daman Haisam ya gutsuro takarda ya rubutawa kowacce abunda zata ca a wajen. Sai ta rike tana karantowa harta rike kafin ranar da zasu yi ba sai da takarda ba. A yau kusan *yan aji shida kakaf suna zaune a hall nan ne wajen da ake yin gwaji (rahazal) din, da wasu da yawa daga cikin *yan aji biyar, hudu da uku *yan kungiyar.
Maryam Tijjani (Abdul) ita ce ta taho da jakar kaya katuwa a rataye a kafadarta tazo wucewa suka hadu da Hannah (Talatu) dauke da kwarya a kanta zata je kogi debo ruwa. Abdul ya sakarwa Talatu wani lallausan murmushi na so da kauna cikin sassanyar murya Hannah (Talatu) ta ce "Abdul ba dai tafiya ba, ya ce "Tafiya zanyi Talatu nazo ne daman inyi miki sallama, sai kwaryar dake kan Talatu ta fado kasa dan gigicewa. Ta rushe da kuka. Abdul a gigice ya ajiye jakar dake hannunsa, Hannah ta fara karanto takardar da Haisam ya rubuta musu ta ce "Abdul kayi min alkawari ba zaka yi aure ba a can har sai ka dawo ka aure ni karka je can ka sami *yar larabawa ka aura ni ka manta dani. Haisam yasa tafi sai duk aka dau tafi a hall din. Haisam ya ce "Kunyi kokari wajen yayi kyau kema Maryam Tijjani ki dage ki bata amsa dan Allah banda dariyar nan da kika saba. Maryam Tijjani ta ce "To bazan yi dariya ba, ta daga ido ta kalli Hannah (Talatu) wani kallon soyayya da Hannah take, tayi wani narai-narai da idanuwanta kai ka ce a gaban saurayinta na gaske take. Sai dariya ta kwacewa Maryam Tijjani sai kowa yasa dariya. Haisam ya ce "Gaskiya kina bata mana lokaci kullum muka zo dariya kawai kike yi saura kwana uku fa mu fita edcusion idan kinsan baza ki iya ba na sa wata. Maryam ta ce "Uncle Allah Hannace take sani dariya baka ga kallon da take yimin bafa kamar ta sami saurayinta da gaske sai kashe ido take. Haisam yayi dariya ya ce "Tsabar ta fiki iya actin kenan, shi daman wasan kwaikwayo ana son duk abunda aka baka kayi kokari ka nuna abun kamar da gaske ne, wajen kuka kayi kuka, wajen murna kayi murna. Kema kiyi mata kallo kamar kece saurayin kin hadu da budurwar da kika fi so a duniya. Wannan yana nunawa kenan Hannah ta iya actin sosai kamar da gaske. Kowa ya hau dariya ana yiwa Maryam tsiya, kema ki yi mata kallon soyayyar mana ko baki iya ba ne?
Haisam ya tashi yaje ya karbi takardar hannun Maryam ya ce "Koma gefe ki dinga kallon yadda zamu yi sosai don ki koya. Ya ce da Hannah "To kara karanto naki, Babu kunya Hannah ta narkar da idanuwanta ta kashe murya lallausa ta dubi Haisam kallo cikin ido ta ce "Abdul kayi min alkawarin ba za kayi aure ba a can har sai ka dawo ka aureni kar ka je can ka sami *yar Larabawa ka aura ni ka manta dani anan. Haisam ma yai marairaice ido ya kurawa Hannah ido kawai wannan kallo da Haisam yake yiwa Hannah ya sosa mata wani waje a zuciyarta ya ce "Talatu ba zan yi aure ba, kuma ba zan manta dake ba, ko a ina nake, ko da GANGAR JIKI NA bata tare dake ruhina yana tare da ke, soyayya baiwa ce, Hannah kina raina a koda yaushe, ina sonki Hannah. Taji gabanta ya fadi don jin yaune rana ta farko da Hannah ta san ma'anar wakar nan da take yi tayi shiru tana tunani tana kallon Yaya Haisam tasan tabbas wannan wajen a cikin wakar nan da take yi masa ya dauko kamar daga sama ta ji Yaya Haisam ya ci gaba da cewa "Ina son ki, ina son ki Hannah! Bazan manta dake ba kina raina har abada. Wannan karan ba karantowa yake a takarda ba kuma ba Talatu ya ce ba, Hannah ya ce. Sai Hannah ta fara ja da baya tana tafiya a hankali tasa hannu ta rufe idanuwanta tana murmushi. Kunya ta kama ta, gaba daya *yan kallon sun zubo mata ido suna kallon saurautar Allah, domin kowa ya san wannan kallon kadai da suke yiwa junan su ya fi karfin gwaji balle kalaman da yake fita daga bakin Haisam, ba a jikin takarda yake ba, sai kunya ta kama Hannah ta fita da gudu daga hall din. Haisam yaja wani dogon numfashi ya juya ya kalli sauran daliba ya ce "Kuje ma karasa gwajin da daddare. Ya fita ya nufi gidansa. Dalibai su ka firfito suna gulmammaki "Wannan anya Hannah da Auncle Haisam ba soyayya suke yi ba, ke kinga kallon da suke yiwa junansu Uncle Haisam kamar ya rungumeta fa. Haka dai suka shiga dakunansu kowacce ta nufi bangarenta.
Rauda ta sami Hannah a kwance kan gadonta ta dora filo a kanta babu abinda take tunanowa sai idanuwan Yaya Haisam sai kuma tsananin mamakin yadda ya rike baitukan wakar nan da take yi masa tun tana aji daya. Ta ce a ranta "Ashe ma'anar wakar nan kenan banda yarinta, nake kaikaicewa nake rera masa ko da gangar jikina bata tare da kai ruhina yana tare da kai. Har Nusaiba take cewa Hannah meye ruhi na ce ina jin larabci ne ashe ban san Hausa ba ce tsaba a lokacin. Ruhina! Ruhina!! Hannah ta fada yayin da ta sake kankame filo a kirjinta. Tsaki taji anayi a kanta ta bude ido sai taga Rauda a murtike. Tayi furgigit ta tashi zaune ta ce "Rauda har kun dawo? Rauda ta katseta ta ce "Haka za ki ce mana har mun dawo da can zamu kwana? Ko muma son wani muke yi da zamu bishi gidansa? Yaya Haisam dai yana da wacce yake so kuma an gama magana gara kowacce ta koma kauyenta ta sami wani bakauyen ta aura amma Haisam sai Ramlah. Hannah ta ce "Rauda me ya faru, wani abun aka yi? Nusaiba ta ce "Ke Rauda meye haka wasan kwaikwayo ne fa kowa yasan gwaji ne ba gaske bane, wai ke Rauda me yasa bakyason a zauna lafiya ne? Rauda tayi tsaki ta fice tana cewa "Duk gulmace-gulmacen da ake ina sane. Dan iskan kauye ya fi na birni iya iskanci da rashin mutunci.
Hannah ta fashe da kuka, tayi ta kuka kamar ranta zai fita. Nusaiba na lallashinta da kyar Hannah tayi shiru suka je suka yi alwalar magaruba. Bayan sunyi sallar isha'i sunci abinci karfe takwas dai-dai sai suka je suka kora dalibai kowacce ta fita ajinsu don yin prep din dare. Uncle Haisam ya fito daga gidansa takwas da rabu yazo ya kirawo *yan Hausa club don suzo su karasa gwajin wasan kwaikwayo da suke yi. Ta bayan wundo ya hango Rauda tsaye akan bencin Hannah tana ta gurza mata rashin mutunci har cewa take da ba'a san asalin balbela ba da sai ta ce Madina ce garinsu. Yaga Hannah a zaune tayi shiru tana hawaye, ran Nusaiba ya baci ta taso ta shigarwa Hannah kamar zasu daku da Rauda. Sai Haisam ya leko ta wundo yayi musu tsawa ya ce su fito waje yana son ganinsu.
Suna zuwa gabansa kallo daya suka yi masa suka san babu wasa yau a murtike yake kasancewar sun san bacin ransa babu kyau sai kowacce ta fara rawar jiki. Ya daka tsawa ya ce kowacce tayi kneel down bayan sun yi ne ya tambayi Nusaiba me ya faru. Nusaiba ta zaiyana masa dukkan abunda ya faru tsakanin Rauda da Hannah tun daga na yamma har na yanzu. Ya juya ya kalli Rauda ya ce "Rauda haka ne? Ta gyada kai gami da tabe baki ta ce "Haka ne kuma gaskiya na fada. Haisam ya fusata ya kaiwa Rauda mari tayi sauri ta kwanta a kasa bai sameta ba. Ta ce "Yaya Haisam yau ni zaka mara akan Hannah? Haisam yayi shiru hannayensa a cikin aljihu kansa a sunkuye a kasa. Can ya dago ya ce da Nusaiba ta tashi ta shiga aji. Ya dubi Rauda wacce ke durkushe akan gwiwarta a gabansa Rauda ta rushe da kuka. Haisam ya ce "Rauda tun ba yau ba, tun kuna aji daya na lura kin kafawa Hannah karan zuka a makarantar nan, yanzu kece kadai kika rage a cikin masu takurawa Hannah zan iya daukar kowanne mataki kuma akanki muddin baki fita harkar Hannah ba ki kiyaye, idan kuma kin ki ni zan fiki farin ciki don zaki ga abunda zan zartar a kanki. Ko Amratu kanwata *yar shekara bakwai zan iya hukunta ta muddin ta nemi takurawa Hannah wannan alkawari nayi wa Allah kuma sai na cika shi don Hannah amana ce a wajena. Kamar a mafarki Rauda take jin kalaman Yaya Haisam, tana fada a ranta "Lallai abun nasa babbane da gaske ya ke. Daga karshe ya ce ta tashi ta shiga tana sharbar kuka ta mike a fusace ta shiga aji. Ya shigo shima ajin ya kalli Hannah wacce ido yayi mata jawur don kuka ya ce Hannah ki kira sauran *yan Hausa club ku taho Hall ku sameni mu karasa Rahazal din. Cikin ladabi Hannah ta amsa masa. Ya fita ya nufi hall. Hannah ta ce "Rauda muje hall Yaya Haisam na kira. Ta dago ta harari Hannah ta ce "Bazan je ba kuma na fita daga club din ko za'a sani dole ne? Hannah zata ce wani abu Nusaiba taja hannunta ta ce "Kyaleta mu tafi mu kira sauran.
Hutu ya kusa karewa har ana shirye-shiryen fara first term exermination. Kowacce karatu take haikan. Sunyi jarabawa an basu sakamako kafin ranar hutu. Hannah ce tazo ta daya a ajinsu wannan karon, Raudah ta biyu, Nusaiba ta uku. Ranar hutu bayan anyi assembly hutu da wur-wuri kafin kowa ya fara tafiya Haisam yazo ya sami Hannah, Rauda, Nusaiba da wasu kawayensa a zazzaune akan barandar hall suna ta hira. Bayan sun gaishe shi sai ya ce "Hannah taso ga Safiyanu yazo daukarki, idan muka sauke ki a gidan uwar biyu zamu wuce dashi Dan Musa can Jahar Katsina acan yake neman aure zamu kai kayan gaisuwar surukai. Su duka suka kyalkyale da dariya. Hannah ta ce "Oh Yaya Safiyanu daman aure zai yi ko ya fada mana sunanta, ranar nida Nusaiba muka ga hotonta a motarsa muka ce budurwarsa ce ya ce wai shi ba budurwarsa bace. Nusaiba ta ce "Haka ne kuwa a bayan hoton an rubuta Dan Musa har nake cewa Dan Musa kuma sunan mace dan Musa ya ce eh haka ne sunanta.
Haisam yayi dariya, sannan ya juya ya kalli Rauda tasha kunu ta kawar da kai gefe daman tunda akayi wannan abun bata cika yiwa Hannah magana ba musamman idan taga Haisam da Hannah. Ga Uwa Uba Hannah ta kwace mata position tazo ta daya, sai take jin haushinta kamar ta kashe Hannah. Haisam ya ce "Rauda ni ba Kano zanje ba sai mun dawo daga Dan Musa don a gida ma nace kada a turomun da Mota. Auwal ne zaizo daukarki ko direba? Tace "Sai dai direba Yaya Auwal yana Maiduguri ya ce "Oh haka ne fa, to ki gaishe dasu Hajiya sai wajen jibi zanzo Kanon. Idan muka tafi yau ba damar muyi tafiyar dare dole mu kwana sannan washegari mu dawo Kazaure, wata kila in kwana a cikin gari jibi muje Kanon da Safiyanu. Rauda ta ce "Zasu ji, Allah Ya kiyaye hanya. Hannah ta kira wasu Juniors suka dauko jakunkunanta suka zuba mata a mota. Tayi wa kawayenta sallama tana zolayar su tana cewa yau itace farkon tafiya duk makarantarnan ta barsu su *yan kwantai ne. Rauda ta tabe baki ta ce "Yanzu watakila har kowa ya isa gida ke baki isa gida ba, saboda hanyar garinmu kwalta ce sambel ba kasa ba.
Hannah da Nusaiba ne kawai suka gane Raudah bakar magana ta fada, wato Hannah Bakauyiya ce kenan take nufi. Sai Hannnah tayi murmushi kawai ta tafi ta shiga mota tana dagawa su Nusaiba hannu har suka fita get.
A gidan Uwar biyu su Haisam suka sauke Hannah, Haisam ya shiga cikin gidan ya bawa Uwar biyu kudaden motarsu da wanda zasu kaiwa Mahaifin Hannah suka yi godiya yayi musu sallama ya juya ya tafi, har yaje kofar fita ya juyo ya ce "Ko yanzu zaku tafi mu aje ku a tasha. Hannah tayi sauri ta ce "Yaya sai da yamma zamu tafi ina so inje gidajen kawayena a nan cikin gari, yayi murmushi ya ce "Wato akuyar daure ta sami sake, su Hannah an iya yawo ko? Su duka suka yi dariya sannan ya fita. Da misalin karfe biyar uwar biyu da Hannah suka isa Babban Mutum, suka je suka iske gida a hargitse anyi tashin hankali. Malam Habu Mahaifin Hannah kuka yake wiwi. Cikin rikici da rudani Hannah ke tambayar meya faru Babanta yake kuka? Iya Abu ta tuntsire da dariya tayi buda da shewa ta ce "Tambayi Ubanki, karshen tukatiki tik, yau Allah Ya nuna mana gaskiya. Hankalin Hannah da Uwar biyu ya sake tashi sosai, suna so suji me Iya Abu take nufi da wannan habaici nata. Malam Habu ya sharbe hawaye da babbar riga ya ce "Muje zaure in fada muku abunda ya faru. Da yake daman a tsakar suka iske su suka je zaure suka zazzauna Malam Habu ya nisa gami da langabar dakai ya ce "Idan ka haifa dole a jawo maka, daman ance dan kuka shi ke jawa Uwarsa zagi. Uwar biyu da Hannah su dai sun kagu suji abunda ke faruwa ya ce "Yanzun nan babu dadewa watakila kun hadu da wata bakar mota katuwa a hanyar shigowa garin nan, wata futsararriyar yarinya ce tazo ta cimin mutunci a kofar gidan nan har ta tara mun mutane. Hannah ta ce "Wace ce Baba? Cikin rudani da fargaba ta tambaya ya ce "Farko da tazo sai ta tsaya ta karemun kallo a wulakance sannan tace naji kunya wallahi. Daman yarinyar ma *yar talakawa ce, yake bata mun lokaci a kanta. To Baba bari in fada maka ka jawa yarka Hannah kunne ta kiyayi mijina idan ba haka ba ni zan zamo ajalinta domin zan iya kashe duk yarinyar da zata rabani da Haisam abun sona. Kuma ka cire *yarka daga makarantar nan domin idan bata bar makarantar ba Haisam ba zai bar makarantar ba ya rabu da ita, muddin Hanna ta sake komawa makarantar to kuwa har makarantar zan bita in zartar da abun da na yi niyya. Ba tana takamar ita kyakkyawa bace to zan kwara mata wani abu a fuska (acid) fuskar ta sale ta kwakkwabe har makarantar zan tarar da ita in yaso sai inga fuskar da zai sota. Don soyayya Hannah take yi da mijina ba karatu ba. Har sakamakon jarabawar kanwata yake dauka ya bata tazo ta daya a ajinsu. To na gaji, wannan shine lokaci na karshe da na bawa Hannah idan taki ji ta koma makarantar to wallahi ta kuka da kanta. Malam Habu ya sharbe hawaye yaci gaba da cewa "Da wata *yar makaranta tana sanye da kayan makaranta irin naki *Yar Baba itama tana taya ta suka yimin tas, Iya Abu na ihu tana dariya tana cewa daman ta sani ba tun yau ba Hanne karuwanci aka kaita tayi ba makaranta ba yanzu gari duk ya dauka maganar ake yi don a gaban mutane aka yi haka. Ta ce Hannah ta ci sa'a da ban sameta ba da sai ta faffalla miki mari sannan suka shiga mota suka tafi. Hannah bata iya cewa komai ba sai ta sunkuyar da kai kasa tana kuka Malam Habu ma kukan yake Uwar biyu ta matse hawaye ta ce "Kuyi shiru, ku daina kuka wannan duk abune na shirme da karya ita wannan yarinyar data zo ina tunanin matar da Malam Haisam zai aura ce take ganin son Hannah yake alhali kowa yasan Haisam a matsayin Yaya koma ince Uba yake a wajen Hannah tun tana karama fa inah, ai zancen so ma bai taso ba. Hannah karatu take a makaranta babu wata soyayya daga wannan hutun ma baza su sake dawowa ba har sai sun gama makarantar ma kwata-kwata, saura wata bakwai su gama.
Malam Habu ya zabura ya ce, "Wacce komawa ai Hanne tazo kenan baza ta koma ba ina wani zancen saura wata bakwai Hanne ta gama, ai ko saura kwana bakwai ne Hanne ta gama karatu bayan a gaban mutane aka ce ba karatu take yi a makarantar ba soyayya take yi sannan in bar *yata ta koma ai sai a dinga cewa tana can tana iskanci har wata bakwai ba ta komo gida hutu ba, ni dai abunda zance muku Uwar biyu ke da wannan yaro Haisam Allah Yayi muku albarka amma Hanne ba zata sake komawa ba karatun ya isa haka duk kawayenta harma kannanta duk sunyi aure gara itama in hadata da wani a dangi tayi aurenta baki alaikum kafin a kone mata fuska. Daman abunda muke ji a redio gaskiya ne ace an fesawa wani ko wata wani ruwa a fuska ta kwakkwabo gaske ne to ba zai faru akan Hanne ba. Karatun da tayi na baya ya isa nagode madalla. Cikin rudewa Uwar biyu ta ce "Haba Malam Habu yaya zaka yi mana haka? Baka kyauta masa ba yarinyar nan duk zance take Haisam ba zai barta taje gurin Hannah ba balle tayi mata wani abu. Bama a barin kowa yaga dalibai in ba ranar visiting ba dokar makaranta ce.
Malam Habu ya mike ya shiga gida yana cewa "Nifa na gama maganata Uwar biyu kiyi hakuri ki bar maganar komawar Hanne makaranta. Ai ko karan hauka ne ya cije ni ba zan bar *yata taje inda za'a hallakata ba ina Hanne ina kishi da wadannan gogaggun *yan birni masu kudi? Tunda tana ganin mijinta son Hanne ya ke ai sai a hakura da taimakon, na baya ma Allah Ya saka. Ya shige ya bar Hannah tana matse hawayen dake idanuwanta da wani farin hankici dake hannunta ta ce da Uwar biyu, "Kyale shi ya tsorata ne kafin hutu ya kare zai yadda idan na wayar masa dakai a hankali na lallabashi sai dai idan hutu ya rage sati guda kizo don muji mai zai ce in yaki yadda sai Yaya Haisam yazo ko kuma ya turo Principal idan kuma yaki yarda na shiga uku karshen karatuna ya zo. Hannah ta rushe da kuka, Uwar biyu tace "Yadda za'ayi shine Haisam zan turo yazo garin nan Mahaifinki ya kalli kwayar idonsa ya ce ya hanaki ki koma makaranta, Haisam zaizo da kansa. A haka Hannan da Uwar biyu suka yi sallama. Hannah tayi-tayi da Uwar biyu ta shigo cikin gida ta huta sannan ta tafi Uwar biyu ta ce ba zata shiga ba, ina zata iya shigowa wajen Iya Abu masifaffiyar matar da zata iya kashe mutum ma don rashin imani. Hannah ta raka ta har tasha ta shiga mota sannan hannah ta dawo gida.GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 13
A zaure Malam Habu ya shinfida tabarmar kaba da wani yagulallen filo da zanin gado irin na da dinnan shekara aru-aru da suka shude. Nan ne shinfidarsa da yake kwana nan ne dakinsa dan duk sanyi da damuna a nan yake saboda Iya Abu ta mamaye dakunan gidan. Dakinsa din ya barwa Hannah data girma ya dawo zaure don da da tana yarinya tare suke kwana a dakin. Ko yaushe Hannah zaka ganta a zaune a gefen Babanta tana lallabashi tana wayar masa da kai game da makarantarsu. Tana nuna masa muhimmanacin karatu da kuma irin bacin ran da Haisam zaiji idan bata koma ba. Ta kwashe labarun abubuwan da suka faru tun tana aji daya har tazo aji shida yadda Haisam yake kula da ita da irin tataburzar da aka sha yi akanta da dalibai da Malamai har ya kwatar mata *yancinta babu mai dukanta ko zaginta yanzu, kuma yayi alkawarin zai iya kashe ko waye yake son ya takura mata. Malam Habu ya gamsu sosai da bayanan Hannah ya kuma san Haisam ba zai yadda a cuce ta ba.
Hutu ya rage sati guda sai ga Uwar biyu ta dira a garin su Hannah ta iske Hannah da Mahaifinta a zaure a zaune zance daya dai suke ta nanatawa kullum shine zancen ya barta ta koma makaranta. Bayan sun gaisa da Uwar biyu ta fadi abunda ke tafe da ita cewar tazo ne ta tafi da Hannah hutu ya kare sai Malam Habu ya kekashe idanuwansa ya ce shifa babu inda Hannah zata je. Hannah tayi mamaki da taji ya fadi haka yanzu bayan ya yarda da tayi masa bayani sai kawai Hannah ta rushe da kuka, magiyar duniyar nan Uwar biyu ta dinga yiwa Malam Habu amma yaki yarda daga karshe Uwar biyu tayi musu sallama ta tafi. Tana isa Kazaure ta wuce gidan su Safiyanu abokin Haisam bata same shi ba ance yana Kano sai ta koma gida ta zuba ido ko Allah zai jeho mata Haisam ko Safiyanu idan zasu kawo sayayyar Hannah ta makaranta tunda sunsan hutu ya kare zasu kawo. Har gobe a koma makaranta Uwar biyu bata ga Safiyanu ba balle Haisam. A can kuwa Hannah hankalinta ya gama tashi taji shiru Yaya Haisam baizo ya taya ta rokar Babanta ba, sai ta dauka shima yayi fushi ne ya ce to abar masa *yarsa kar tayi karatun mana. Da la'asar likis Hannah da Mahaifinta suna zaune akan lintsimemiyar tabarmar kaba a zauren kasa da rufin ciyawa Hannah kuka take yau tun da safe. Malam Habu yayi lallashin duniyar nan tayi shiru ta hakura tama cire ranta a makarantar don shi ya gama magana bazata koma makaranta ba. Ta ki ci ta ki sha sai kuka take rafsawa. Kwatsam suka ji sallama daga idon nan da Hannah ta yi sai tayi ido hudu da Yaya Haisam, Safiyanu da Uwar biyu suka yi sallama suka shigo. Da sauri Hannah ta dauko musu tabarma ta shinfida musu suka zazzauna ta koma ta dauko musu ruwa a randa cikin kwanan sha. Ta kawo ta durkusa kasa ta gaishe su ta koma gefe ta zauna. Murna ce ta rufe Malam Habu yama rasa inda zaisa wadannan manyan baki, *yan gayu, ya lalubo kudi a aljihunsa ya ce Hannah tayi maza taje bakin kasuwa ta suyo musu fura da nono, su Haisam suka ce kai haba ai su a koshe suke ya barshi kawai. Bayan sun gaggaisa Malam Habu ya gama yi musu sannu da zuwa da taki ta kare, sai Safiyanu ya nisa ya ce "Baba munzo ne mu ba da hakuri akan dalilin da yasa ka hana Hannah zuwa makaranta, shine muka zo da kanmu mu roke ka Baba duka-duka saura wata nawa ne yanzu Hannah zata gama karatunta ta dawo gida.
Nan da nan Malam Habu ya canja fuskar fara'ar da yake ta gushe ya ce "Wai me yasa kuke sani ina muku kin kyautawa ne? Bana so ku tambaye ni abinda zan kasa baku na gama magana don Allah don Annabi ku bar zancen karatun *yar Baba, na yanke shawara ba zata koma ba. Haisam kokarin da yake Allah Ya saka maka, hakan ma ya isa ba sai ta kara yin wasu watannin ba. Na ce da Uwar biyu ta yi maka godiya ka cika min alkawarin da ka dauka wallahi ko bata karasa ba ai ka cika alkawari ba laifinka bane. Alkawari da amana ai ba karamin aiki bane cika su, amma cikin yardar Allah ka cika kai dai, Ubangiji Ya saka maka da gidan aljannah. Amma Hannah ba zan bari ta koma ba. Haisam yayi dan murmushi gami da gyaran murya ya ce "Amin Baba, amma idan baka manta ba a ranar dana karbi amanar Hannah nayi alkawarin Hannah zata yi karatu to kai ma a lokacin kayi min alkawari, kaga alkawari girma ne da shi baka cika ba, kayi min alkawari zaka bar Hannah tayi karatu don sai dama nasa kayi alkawari zaka dinga turo Hannah makaranta baza ka hana ta ba wataran sannan nayi maka alkawarina. Malam Habu yayi shiru zuwa dan wani lokaci can ya nisa ya ce "Anyi haka yaro haka akayi nayi maka alkawari to amma ai abinda yarinyar nan ta ce gargadi fa tayi min akan kada in kara tura *yata makarantar nan kaga ai kome tayi mata bata da laifi nine ban ji ba kenan. Haisam ya katseshi ya ce "Kare lafiyar Hannah da duk wani abunda zai cuce ta yana daga cikin manar dana dauka in Allah Ya so babu mai yiwa Hannah wani abu. Ramlah kuwa ta fada ne kawai a cikin bacin rai amma babu abinda zata yiwa Hannah, a ina ma zata ganta balle tayi mata wani abu? Ta dai fadi son ranta donta tsorataka,kawai kaga Baba kuma abinda ta fada ba haka bane Hannah karatu take haikan a makaranta, kanwa ce Hannah a wajena ni ne mai tsawatar mata ma misali da ace tana soyayya da samari a makarantar. Baba mufa canfa akwai doka babu yadda za'ayi wata ta shigo cikin makarantar dauke da wata guba taje ta cuci dalibai don haka Baba ka kwantar da hankalinka ni da kai duk mu cika alkawuran da muka daukarwa Allah. Malam Habu ya ce "To shikenan Allah Ya taya mu cikawa. Hannah dauko kayanki ku tafi Allah Ya kiyaye hanya. Su duka suka ce "Amin, sai murna ta dira a zukatansu. Cikin farin ciki da jin dadi Hannah ta shiga ta fara hado kayanta, Iya Abu tayi caraf ta fito daga bayan kyauren da take labe ta hau Malam Habu da fada "Au yarda kayi da wannan dadin bakin da suka yi maka. Duk wannan gaskiyar data baiyana yarinya iskanci suke a makarantar don yana aiko maka dana goro shine kaki fadar Allah saboda abin duniya? Kallo daya Haisam yayi mata yaga irin wadannan mutanen ne masu abun haushi masu kama da aljanu munana masu bakin hali yaji ya tsani Iya Abu har baya so ya kara kallon fuskar shegiya.
Hannah ta rataya jakarta ta fito ko kallon Iya Abu bata yi ba balle tayi mata sallama. Ta duka ta yiwa Babanta godiya tayi masa sallama ta wuce cikin mota. Haisam ya danko kudi mai yawa ya ajiye a gaban Malam Habu, Safiyanu ma haka ya debo kudi ya ajiye masa suka yi masa sallama dukkaninsu yana godiya suna godiya suka shiga mota suka tafi.
Ba Safiyanu ba har Haisam ya ji ya sake tausayawa rayuwar Hannah saboda ganin yadda gidansu yake. Gidan kasa ne anyi masa katanga da kara rufin azare abin dai abun tausayi talauci ne dai tsagwaronsa. Babu abinda zaka daga a gidan ka sayar dashi dari biyar komai raga-raga. Kaico! Hannah na komawa makaranta tasa littafinta a gaba tahau karatu. Sune yanzu masu shirin zana S.S.C.E don haka babu wasa sai karatu.
Kwance tashi su Hannah sun fara zana jarabawarsu ta karshen (S.S.C.E). Saboda daman tuni sun gama tsarge karatu. Sai suka ga cin tuwo yafi jarabawar wuya sai kawai suka fede ta. Geography course din Malam Haisam ita ce wacce suka yi ta karshe da misalin karfe hudu na yamma suka gama daman jakunkunansu suna bakin hall din da suke jarabawar suna fitowa sai kowacce ta dauki jakarta sai tafiya daman kowacce ta kagu taje gida taga *yan gidansu basu taba irin wannan dadewan a makaranta ba, har watanni bakwai a makaranta. Hatta Hannah da bata so a yi hutu itama yanzu so take taje gida taga Mahaifinta sai mafarkinsa take kullum ta kwanta barci. Hannah da kawayenta sun sha kukan rabuwa musamman ita da Nusaiba sun saba sosai gashi zasu rabu. Gashi kuma babu waya a garinsu Hannah balle su dinga gaisawa a waya. Rauda ma ta rungume Hannah tana kuka taji duk babu dadi yanzu da zasu rabu, kuka wiwi Juniors suke yi na rabuwa da Seniors dinsu zasu tafi su barsu musamman Hannah basu ji dadin rabuwa da ita ba saboda tayi musu mutunci, samun shugabar dalibai irin Hannah sai an bincika. Ta koya musu abubuwa na cikin kungiyoyinsu (club) na makarantar. A haka kowacce ta tafi gida kuka wiwi. Safiyanu ne yazo ya dauki Hannah ya kaita gidan Uwar biyu. Yau Haisam tun kafin su shiga Jarabawa yazo yayi musu sallama ya koma gidansa ya rufe kansa ko wajen da ake bankwana bai zo ba saboda tsananin bakin cikin rabuwa da *yan ajinsa da yake matukar so. Gidan Uwar biyu ma sai washe gari yaje ya samu Hannah acan. Bayan sun gaisa ya ce da Hannah. Yau zaki tafi gida ko sai kin sake hutawa kamar sati daya anan sannan ki tafi? Hannah tayi caraf ta ce "Yaya Haisam yau zan tafi na dade banga Baba ba. Haisam yayi dariya ya ce "Wato ke yanzu kin bar Kazaure kenan zaman Kazaure sai mu? Tayi dariya ta ce "Sai ku ai mu mun daku wannan hutun har na daina sha'awar garin Allah Yaya Haisam. Haisam ya mike ya ce "To ki shirya zanje nan makwabta Safiyanu yana ciki wajen abokansa ana wanke masa motar ana gamawa sai ku fito zan aiko yaro yayi kiranku sai mu kaiku tasha ku tafi. Da har can garin zamu kaiku in yiwa Baba godiya ince masa gaki na dawo masa dake lafiya na cika alkawari shima ya cika, to sai Safiyanu ya ce Kano zai tafi da Kakarsa in anjima. Hannah tayi dariya ta ce "Kai Yaya Haisam ai babu komai yana gani na ma yasan lafiya na dawo lallai kuwa ka cika alkawari. Ya juyo ya kalleta ya ce "Ko? Tayi murmushi ta ce "Eh. Sannan ya fita yana murmushi.
Bayan fitarsa da dadewa sosai yaro ya shigo ya ce "Wai Uwar biyu da Hannah su fito inji su Safiyanu suna kofar gidan Dallatu. Daman a shirye suke tsaf sai Hannah ta fara dorawa yaron jibgegiyar Jakar kayanta. Jakunkunan uku ne. Yakai ya dawo ya dauki biyu sannan yazo ya dauki ta karshe sannan suka fito Uwar biyu ma da buhunta a kanta, suka shiga motar sai tashar Kazaure. Hannah ta hado kayanta kakaf na gidan Uwar biyu, katifa da bokiti kuwa ta ba Uwar biyu kyauta. Kaya masu kyau atamfofi da shaddoji da yawa Hannah ta bawa Uwar biyu kyauta da *yarta Halima. Dake kaya tsadaddu leshina uku, shadda da atamfa bibbiyu Yaya Haisam ya yiwa Hannah na Candy. Bayan takalma da sarka da dan kunne harda ta gwal ya suyo mata. Suna isa tasha a bakin tasha Safiyanu ya tsaya da motar. Ma'aikatan nan *yan Union su biyu suka zo suka tambaye su ina zasu da suka fada sai suka ce babu motar Babban-mutum yanzu amma baza a dade ba zata zo Haisam ya ce su kwashe Jakunkunan su kai cikin tasha. Hannah da Uwar biyu suka shiga cikin tasha. Safiyanu da Haisam suna bakin mota a tsaye a bakin tasha. Can suna tsaye suna hira sai Safiyanu ya kalli agogo ya ce yanzu fa muka yi da Hajja Kakata zan dawo mu tafi Kano tana can tana jira na. Haisam ya ce "Ai ba komai jeka kawai nima idan naga tafiyarsu acaba zan hau in koma cikin makaranta. Suka yi sallama Safiyanu ya shiga mota ya tafi, Haisam kuma ya shiga cikin tasha.
A cikin wata *yar rumfa ya iske Hannaah a zaune akan Jakar kayanta Uwar biyu kuma akan wani benci suna *yar hira suna jiran zuwan mota. Ya karasa cikin *yar rumfar yana tambayarsu. Har yanzu motar bata zo ba ne? Uwar biyu ta ce "Sun dai ce yanzu zata zo munzo da wuri ne wai daman motar bata zuwa da wuri. Ta mike da sauri daga kan bencinta tace da Haisam ya zauna, ya ce "Lah babu komai yi zamanki mana. Uwar biyu ta ce "A'a ka tsaya a tsaye? Ga kawayena acan suna sayar da zogale bari inje wajensu mu gaisa daman dan kar in bar Hannah ita kadai shine yasa banje ba tun dazu. Uwar biyu ta tafi, Haisam ya zauna yana kallon Matafiya da masu mota ana ta hayaniya. Can ya juya ya kalli Hannah wacce ke zaune akan jakarta tayi jigum kamar tunanin wani abu take, ya kura mata ido kawai yana tunani a ransa. Babu abinda ya fara tunawa sai a ranar da aka fara kawo Hannah makaranta ta ci dammara ta hau ta zauna akan akwatinta tayi jigum tayi shiru a lokacin da Babanta ya tafi ya barta. Amma yanzu maimakon dammarar data ci sai tayi shar da wani tsadadden bakin leshi mai duwatsu kala-kala suna sheki a jikinta. Dinki ne filet riga da siket ta yafa dan yalolon gyale ta dana daurin dan kwali yayin da lallausan gashin nan nata mai santsi baki da tsawo ta tufke da bakin ribon a keyarta. Hannah na dago kai sai taga Yaya Haisam kallonta yake kawai a lokaci guda sai kowannensu ya sakarwa dayan murmushi. Abunda itama ta fara tunawa ranar da Babanta ya kawota makaranta ta hau kan akwati ta zauna tayi shiru Yaya Haisam yana zaune akan benci yana kallonta.
Mai tallar biredi ne ya zo ya ishe su da a sayi beridi ga gardi, zaki biredin tsaraba. Haisam ya kalli Hannah ya ce "Baza ki sayi abun tsaraba ba ne ki kaiwa yara? Hannah ta ce "Kyalesu Yaya. Ya ce "Ban gane kyalesu ba, haka zaki yi wata bakwai kije musu hannu Rabbana biscuit ko sweet za ki shiga Aishalle ki saya? Ungo kudin ki aiki wani yaron. Ya ciro kudi a aljihunsa, Hannah tayi dariya ta ce "Su fa sunfi ganewa ayi musu tsarabar biredi. Haisam ya ce "Su sha tea da safe dashi? Hannah ta ce "A'a su ringa gutsira a haka, su duka suka yi dariya. Haisam ya ce da mai biredi ya sauke ya je ya siyo jakar bacco ya dawo. Ba dadewa sai ga mai biredi dauke da jakar bacco. Haisam ya ce ya juye biredin duka a ciki. Hannah ta rike baki ta ce "Yaya Haisam wadannan manya-manyan biredi har wajen guda takwas ai suna da girma sunyi yawa biyu ma sun isa. Haisam ya ce "A'a basuyi yawa ba kowa yazo yayi miki sannu da zuwa sai ki yago masa gayan biredi ki bashi kice ga tsaraba. Su dukkansu suka kyalkyale da dariya harda mai sayar da biredi dadi ya kamashi ana masa ciniki. Mai lemon fata ne ya garzayo da sauri yaga an siye na abokinsa, shima ya bude muryarsa gaba daya yana "A sayi na tsaraba, shima Haisam ya ce ya siyo bacco ya zo ya juye duka farantin, yayi cololo kuwa don cika. Nan da nan ya garzaya da sauri ya siyo bacco yazo ya juye sai kudinsu tumus a hannu. Suka jerawa Hannah bakkuna a gaba suka tafi suna murna. Hannnah ta dago ta kalli Haisam fuskarta cike da murmushi gami da nuna jin dadin kulawar da yake yi mata ta ce "Yaya na gode fa kwarai da gaske Ya ce "Babu komai Hannah. Hannah ta dago ta kalleshi suka hada ido ta ce "Yaya Haisam baka bani abun busa naba da tsakiyoyin da ka ce in baka zaka boyemin kada Malamai su kwace min din nan tun randa aka kawoni aji daya. Haisam ya tuntsire da dariya Hannah ma haka ya ce "Bazan baki ba sai kinyi wannan danmarar da kika yi sannan zan baki sarkokinki. Suka sake tuntsirewa
da dariya ya ce "Busa nake yi da abun busarki fa, kusan kullum da daddare kafin in kwanta zaki yi mamaki idan aka ce yanzu na fiki iya busar da wakar. Nafa rike yadda kuke wakar, da Amratu kanwata zanje in kaiwa a gida ashe baki bani ba, bari inje in dauko miki. Hannah tayi sauri ta ce "Bansan kana so ba na bar maka har tsakiyoyin ma in so kake. Ya ce "Eh suma Amratu zan bawa ta dinga kwalliya dasu. Hannah tayi dariya ta ce "Amratu baza tayi kwalliya dasu ba, ko mu *yan kauye mun daina saka irinsu.
Motar da zata je Babban-mutum ce ta shigo, doguwar bus ce nan da nan Uwar biyu ta taso ta ce dasu, "Hannah ga mota nan tazo daga jakar su zuba a but. Kwandasta ya zo ya debi jakunkunan kayan Hannah da tsarabar ya zuzzuba a but, Hannah da Uwar biyu suka shiga kujerar baya su biyu kacal sauran wajen Haisam ne yake biya daman haka yake musu in dai ya kawo su tasha to mutane hudu basa zama a baya. Hannah da Uwar biyu ne kawai suke zama ya biya kudin kujerun. Matafiya suna shiga mota, Haisam yazo jikin wundon Uwar biyu ya mika mata kudaden motarsu da kuma wanda zata bawa Mahaifin Hannah kamar yadda ya saba aika masa, Uwar biyu tana ta godiya. Haisam ya zaga ta wundon Hannah wacce jikinta yayi sanyi tana daf da fashewa da kuka, ya mika mata wata ambulan fal da kudi, ya fara yi mata nasihohi masu tsuma zuciya kamar yadda ya saba yi mata amma wannan karon nasihohin sunsha bam-bam da na kullum hade da bankwana yake yi ya ce "Hannah Alhamdulillahi Allah Ya kawo mu ranar da kika gama makaranta kin zana jarabawar karshe Allah Ubangiji ya baki sa'a. Hannah ki kula da addininki sosai daman can ke mai addinice nasan da haka amma ki kara. Kada ki damu a duk halin da kika tsinci kanki, na wahala kona jin dadi duk Allah ne ke jaraba bawansa. Duk tsananin da kike ciki Allah Yana sane dake kuma Yana sonki ba wai Ya wareki bane don ya tsaneki yake hadaki da masifu iri-iri da bakin ciki.ba Allah (S.W.A) Yana jaraba bawansa ta duk inda Yaso kiyi kokari kici jarabawar, ki kuma dinga gode masa a duk rintsin da kike ciki. Idan kika gode maSa a duk yanayin da kika godewa Allah to Shi zai canja miki, ina so ki kula cewar babu wani mutum a duniya da zai zama shine gatanki, gatan kowa Allah ki rike wannan Allah Shi Ya halicce ki Shi Yake badawa kuma Shi Yake hanawa, babu me miki wani abu banda Allah, kici gaba dayin tawakkali Allah Yana sane da ke.
Tsananin kukan da Hannah take rusawa shine ya dabar-bartar da Haisam ya rasa abunda zai ce shima ji yayi kwalla ta cika masa ido taf sai kawai ya juya ya tafi ya ce "Allah Ya kiyaye hanya, sai anjima. Wani kululin bakin ciki ne ya zo ya tokarewa dukkansu a wuya tsananin bakin cikin rabuwa da juna. Gagarumin tashin hankali ya mamaye zukatansu kowanne na fidda ran sake ganin dan Uwansa kuma. Ta yaya Hannah zata zo Kano tace tazo ta gaishe da Malaminta bayan Ramlah na nan na nemanta zata hallaka ta idon ta idon ta tace sai taga bayanta. Shi kuma yaya za'ayi Haisam ya je garinsu Hannah bayan duk gari ya dauka sharrin da Ramlah tayi, Iya Abu na yadawa Hannah ba karatu take yi ba soyayya take yi da wani Malaminta.
Hannah tayi zugum a zaune a mota ji take duk duniyar babu dadi. Yanzu zaman din-din-din zata je suyi da Iya Abu tasan ba karamin bakin ciki zata hadu dashi ba a gidan. Ga tsananin bakin cikin rabuwa da Yaya Haisam saboda sun saba sosai don tafi jin bakin cikin rabuwa dashi akan Nusaiba wacce suke kwana tare su tashi, komai tare hatta bacci baya raba su. Uwar biyu ma sai duk jikinta yayi sanyi, shikenan idan ta kai Hannah gida baza ta dawo ta dauketa ba kuma. Suka isa gidan su Hannah, Hannah ta shiga gida da sauri tana murna zata ga Babanta. A shimfidarsa a zaure ta ganshi a kwance sharkab babu lafiya ashe watansa wajen hudu kenan a haka. Ciwo kullum gaba yake sake yi sai an kwantar an tayar.
Tofa Malam Habu?Hmm GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 14
Hannah ta gigice har tana neman rasa hankalinta
yayin
da taga Mahaifinta ya zama kashi kwance kurkut
dashi.
Qaninsa ne Uwa daya Uba daya yazo yana zaman
jinyarsa, dan Iya Abu cewa tayi ya mutu mana tace
ta
gaji da zaman jinya tunda yaki warkewa tayi na
Allah
*yan Uwansa kuma suzo suci gaba da kula dashi
ita ta
huta. Hannah tasa kuka taje ta tsuguna a gabansa
ta
ce
Sannu Baba. Ya ce "Yauwa sannu *yar Baba ashe
da
rabon kizo muyi magana dake ban mutu ba nace
aje a
kirawo min ke a makaranta kizo kiga gawar
Mahaifinki
basu je ba. Cikin shesshekar kuka Hannah ta ce
"Ba zaka mutu ba Baba daina fada ma. Uwar biyu
ma
ta matso kusa dashi ta ce "Sannu Malam Habu ya
jiki?
Ya ce "Jiki dai gashinan Uwar biyu sai dai kuyi min
addu'a idan na mutu, Allah Ya saka miki da alheri
ke da
Haisam da gidan Aljannah abunda kuka yiwa
Hanne na
gode. Uwar biyu ma hawaye take yi. Hannah kuka
kamar ranta zai fita. Anan Uwar biyu ta yini sai da
la'asar tace zata tafi suka yi sallama da Malam
Habu
dake radau yana magana tashi tsaye ne baya iya
yi.
Hannah ta rakata har tasha. A hanya Uwar biyu
take
bawa Hannah shawara ta ce "Tun da ke mai ilimi
ce kiyi
amfani da iliminki, ki kai Mahaifinki asibitin Babura
tunda kudin da Haisam ya bawa Mahaifinki da
wanda
ya baki mai tsokane zai isheku. Da abarshi a gida
ana
masa jike-jike duk wata cuta ake kara masa.
Mutum a
kwance har wata hudu ya kare sai kashi da fata. A
tashar Uwar biyu ta sami mai mota aka yi tsada
zata je
gida a dauko marar lafiya a kaishi asibiti. Hannah
da
Uwar biyu suka shiga mota, dake itama Uwar biyu
daman motar Babura zata shiga daga Babura zata
hau
ta Gumel. Sai kawai su duk su tafi tare. Motar taje
har
kofar gidan, direban da kwandasta da kanin Malam
Habu suka ciccibeshi suka sashi a mota suka
shiga
suma da *yan kayayyakinsu suka nufi asibitin
Babura.
Iya Abu nata yiwa Hannah surutu tana cewa gata
nan
Uwar iya yi wai har tayi kudin din da zata dauki
Mahaifinta ta kai asibiti wai har asibitin Babura ta
zama *yar boko. Sai da Uwar biyu tayi wata guda
cur a
Gumel sannan ta dawo Kazaure tana zuwa tana
niyyar
ta shaidawa Haisam halin da Mahaifin Hannah ke
ciki
sai aka ce mata ai bayan tafiyar su Hannah da sati
biyu
shima ya bar koyarwar ya kwashe kayansa ya
koma
Kano. Ta nemi Safiyanu shima aka ce mata ai shi
tunda
yayi aure a Kaduna ya tare da sabuwar amaryarsa
a
can ya sami aiki, sai Uwar biyu ta hakura da
sanarwa
Haisam don ita bata taba zuwa Kano bama balle
ta tafi
nemansa. Su Hannah kuwa sai da suka shafe wata
guda da kwana shida sannan aka sallamesu daga
asibiti. Kanin Mahaifinta ne a wajensa amma itama
takan je tayi kwana biyu uku acan har dai suka
dawo
gida gaba daya. Jiki da sauki tunda yana zama da
kansa ba sai an tallafo shi ba. Sai dai kudaden
hannun
Hannah sun kare kakaf saboda siyan magungunan
asibiti.
Nan fa balokokon Iya Abu ya tashi akan taga
Hannah
bata da kudin da zata sayi dan biskit da madarar
da
take sha idan tazo hutu da, dole ta ci tuwan gidan.
Hannah ce shara, wanke-wanke da dafa abinci
tuka
tuwan bakar dawa da miyar kuka a murhun kasa.
Kwanci tashi su Hannah sunyi wata biyar da gama
makaranta. Hannah har ta fara zuwa makarantar
bokon
garinsu tana koyarwa. Duk da dai ba'a dauketa a
matsayin Malama ba don Jarabawarta bata fito
ba.
Amma a karshen wata ana bata dan na batarwa.
Ranar
asabar babu makaranta. Da sassafe bayan Hannah
ta
gama wanke-wanke tana kokarin daura tukunyar
tuwon burabuskon gero miyar kuka na rana sai
kawai
Iya Abu tazo ta kashe wutar da ruwan tuwon. Ta
ce ta
canja ra'ayi yau an fasa yin abincin ranar saboda
unguwa zata ita da jikokinta don haka meye
amfanin
tuwon. Ta dauke garin tuwon da kukar kadin tasa
a
daki ta datse ta yafa mayafinta zata fice. Ran
Hannah
ya baci ta ce "To Baba fa, me zai ci shi da bashi
da
lafiya? Yau jikin nasa a rikice yake tunda sassafe
amai
yake. Iya Abu ta ce "Sai yaci hakuri ko ki kwashe
aman
da yayi ki dumama masa. Cikin fushi Hannah ta ce
"Ina
raye a duniya Mahaifina ba zaici amai ba insha
Allah
"Mari tas Iya Abu ta sakar ma Hannah akan
lallausan
kuncin nan nata ta ce "Ke kin isa ina fada kina
fada
lalle wuyanki ya isa yanka. Malam Habu da yake
kwance sai jikinsa ya dau kakkarwa tashin hankali
ya
dira a zuciyarsa yaji marin da aka sakarwa Hanne
sai
ya hau hawaye yana kira "Yar Baba yi hakuri zo
nan
wajena ki zauna. Hannah tana hawaye ta je gefen
shinfidarsa ta zauna Iya Abu tana tsaye akansu
tana ta
balokokonta tayi har ta gaji ta kama hannun
jikokinta
suka fice, da taji ba'a kulata ba. Zuwa can wani
lokaci
mai dan tsawo Hannah da Mahaifinta sunyi zugum
suna tunani sai ta jiyo mai tallar fura da nono ta
zo
tazo wucewa, da sauran *yan canji a jakarta ta
tashi
ta leka ta kirawota, ta dauko kwanon sha ta saya.
Ta
dama ta tashi Mahaifinta zaune ta bashi yasha ya
koshi
sannan ta gyara masa kwanciyar ya kwanta ta
koma
gefensa ta zauna tayi lamo zuciyarta cike da
takaici ga
yunwa tana addabar cikinta. Can Malam Habu ya
ce
"Yar Baba, ta ce "Na'am Baba. Ya ce "Allah Yayi
miki
albarka ya baki miji na gari mai sonki kamar
Haisam,
sai Hannah tayi shiru tana tunani da mamaki ya
akayi
Mahaifinta yake hada mijinta da Haisam.
Malam Habu ya ce "Ya ba ki amsa ba? Ta ce
"Baba
kamar Haisam kuma? Ya ce "Eh kamar yadda yake
kula
dake yake nuna miki kauna. Tayi murmushi ta ce
"Mutunci ne dashi da tausayi amma ba soyayya
bace.
Malam Habu yayi dan tari ya ce "*yar Baba matso
kusa
dani kiji. Hannah ta matso kusa dashi. Ya ce "Yar
Baba
babu mai sonki a duniyar nan kamar Haisam, babu
mai
rikeki tsakani da Allah irin Haisam, babu mai rikeki
amana ko bayan raina wanda ko dar bana yi sai
shi
*yar Baba. Haisam yana matukar sonki. Hannah ta
ce
"Meka gani kake cewa haka? Ba sona yake ba ko
kadan
mutunci ne ai bai taba gaya mun ba. Malam Habu
ya
nisa ya ce "Yanzu tashi kije ki nemi gidansu a
Kano
kice na amince masa ya zo zan bashi ke ya aureki.
Hannah ta zabura ta ce "A'a Baba ya za'ayi inje
kawai
ince masa ka yarda yazo ya aure ni bayan bai ce
zai
aureni ba. Malam Habu ya ce bakya yimun musu,
karki
fara daga yau bazan ce kiyi abunda zaki cutu ba
jeki
kawai ki fada masa. Haisam ne zai rike mun ke
amana
*yar Baba duk duniyar nan shine kadai na yadda
ya
aureki. Jeki ki shiryo ki tafi yi sauri *yar Baba.
Hannah
ta tashi a sanyaye zuciyarta cike da zulumin
wannan
al'amari.
Ta shiga cikin gida ta sake salla wanka ta saka
wani
dandatsetsen sabon leshinta kalar brown ta yafa
gyalenta a kusa da Babanta ta ce "Na shirya zan
tafi,
ya laluba karkashin tabarmarsa ya dauko wasu
kudi ya
bata, ya ce tayi kudin mota. Ta ce ya barshi tana
da
kudin mota, ya ce ta karba shi mai zaiyi da kudin
in
bata karba bama kwashe su za'ayi, kudin da ya
tattarane na *yan dubiya. Har Hannah takai bakin
kofa
zata fita sai ta tuno ai bata san kwatancen gidan
su
Haisam ba gashi bata taba zuwa Kano ba sai can
ta
tuna akwai inda ya rubuta mata kwatancen
gidansu a
jikin littafinta (slum book) da ta bashi ya cike
mata. Ta
koma daki da sauri ta binciko cikin littattafanta ta
dauko sai kawai ta jefa littafin a jaka ta fito.
Malam
Habu na kwance bacci ya fara daukarsa yaji
motsin
mutum sai ya bude ido ya ce "Waye? Hannah ta
ce "Ni
ce Baba, ya ce "Baki tafi ba ne, *yar Baba ko
bakyason
zuwa ne? Ta durkusa a gabansa ta ce "Baba ba
haka
bane mantuwa nayi na dawo amma yanzu zan tafi
zan
bi ta gidan Iya Salma(tsohuwar matarsa ta fari) ko
ita
tazo ta taya ka zama kafin in dawo baza a barka
kai
kadai ba. Malam Habu ya ce "To Allah Yayi miki
albarka. Hannah ta ce "Amin Baba Allah Ya baka
lafiya
ya ce "Amin *yar Baba, kuma ko bayan raina a
daura
aurenki da Haisam ina fatan kema kina sonsa?
Hannah
tayi dariya ta rufe ido, alamar kunya Malam Habu
yayi
dariya shima ya ce "Yar Baba fada min gaskiya
mana.
Ta ce "Baba saboda tsananin kyautatawa da kula
da
yake mun sune suka sa nake ganin girman Yaya
Haisam har naji babu wani mutum da nake so da
tsananin kauna bayan kai Mahaifina sai kuma shi.
Baba
ina son Yaya Haisam sosai har nakan kasa bacci
yanzu
saboda tunaninsa da kewar sa musamman yanzu
da
muka rabu. To amma Baba babu yadda zanyi sai
naga
kamar shi ba haka yake nufi a zuciyarsa ba.
Malam
Habu ya ce "Tashi kije shima yana sonki fiye da
yadda
kike ji. Amma muyi addu'a kafin ki tafi mu karanta
Salati goma ga Annabi (S.A.W). Suka karanta
Malam
Habu ya dinga kwarara addu'oi sannan daga
karshe
suka shafa. Hannah ta sake yi masa sallama ta
fita.
Tana fita gidan Iya Salmai ta nufa ta shaida mata
abunda ke tafe da ita. Nan da nan Iya Salmai ta
zari
gyalenta ta nufi wajen tsohon mijinta dan uwanta
abun
kaunarta wacce dole ce ta raba su don ta kula
dashi
kafin Hannah ta dawo. Hannah na isa tasha ta
tarar da
mota fijo zata je Kano ta cika saura wajen mutum
daya
tayi sauri ta fada sai tafiya.
Babu abinda Hannah take ji a ranta yau sai
tsananin
farin ciki, ji take kamar anyi mata albishir da gidan
aljannah. Tana san Yaya Haisam har a ranta, to
shima
kuma a yadda ta lura yana sonta sosai kuwa
wadannan
dara-daran idanuwan nan nasa ne take hangowa a
zuciyarta idan yana kallonta. Da wasu fararen
hakoransa tas idan yana mata nasiha wai waya
ganni a
Kano yau a kusa da Yayana Haisam kuma wai
yazo
muyi aure an bashi ni. Hannah ke fada a zuciyarta,
dadi
marar misaltuwa ya disu a zuciyarta kowa ya ga
Hannah yasan tana cikin farin ciki a yau. Sun isa
Kano
lafiya a tashar *yan kura aka sassauke su. Hannah
ta
fito daga mota ta kalli gabas da yamma kudu da
arewa,
taga bil'adama ne burjik a gaba da bayanta. Ta ce
a
ranta "Ikon Allah KANO MAI MATA DA MAZA DA
MOTA
DA KUDI DA ILIMI DA WAYEWA, TA DABO TUMBIN
GIWA
KO DAME KAZO AN FIKA, MAI DALA DA GWAURON
DUTSE. Yanzu ina zan fara dosa gabas ko
yamma?
Abum ya bata mamaki ganin yadda ake kallanta
har
wasu mazan waiwayenta suke. Da farko ta dauka
kowa
ya ganta yasan bakauyiya ce bata taba zuwa Kano
ba,
ta fita daban da *yan garin sai da ta ji wasu
samari su
biyu sunzo wucewa sunce mata "Ke kyakkyawa
dan
rufe fuskar nan taki kada kisa wasu mazan suyi
hatsari
a garin kallonki. Sannan ta yarda tsabagen farin da
suka gani da kyakkyawar fuskar da kirarta suke
kallo
sai tayi sauri ta dora gyalenta aka ta rufe fuskarta
idanuwanta kawai ta bude, ta ce a ranta duk
kyawawan
matan garin nan daman har wani kyau na zasu
gani??
Kwalelensu Yaya Haisam ya riga su.
Ta bude jakarta ta dauko littafin da adireshin
gidansu
Haisam ke rubuce ta karanta sunan unguwar
Sulemanu cresent, sai ta sami kwandasta mota. Ta
ce
"Malam don Allah ina motar Sulemanu cresent? Ya
ce
"A'a gaskiya babu takamaimai motar da take zuwa
irin
wadannan manyan unguwanni, amma shawarar da
zan
baki ki sami mai tasi ki dau shata ya kaiki har
kofar
gida. Ga masu tasi nan a tsattsaye babu kowa a
ciki. Ya
nuna mata su, tayi godiya ta karasa wajensu.
Babu
abinda ta fara hangowa sai wajen waya an rubuta
"Make your call here" ta karasa wajen masu wayar
ta
ce "Anan ake yin waya? Mai waya ya ce "Eh nan
ne, ta
dauko littafin nan ta dubo lambar Nusaiba ta mika
masa. Bugu daya wayar ta shiga ta fara ringin,
wata
mata ce ta dauka sannan ya mikawa Hannah kan
wayar Hannah ta karba tana kallon wayar don ita
bata
san yaya zata yi ba. Mai waya ya ce "Kudinki yana
tafiya an dauka fa kisa a kunnenki kiyi magana.
Sannan Hannah ta tuno yadda taga ana yi. Bayan
ta
gaishe da matar sai ta ce "Hannah kawar Nusaiba
ce,
Nusaiba nake nema. Matar tayi dariya ta ce "Oh
Hannah ce? Nice Mami Mahaifiyar Nusaiba, ai
Nusaiba
tana London har ma an samar mata admission
tana
jiran sakamakon jarabawarta ne ta fara
karatu. Hannah tayi bakin cikin rashin samun
Nusaiba
a waya sai suka yi sallama ta mikawa mai waya
kan
wayar, ya duba ya ce "Minti uku kika yi, ta ce
"Nawa
ne? Ya fada ta dauko ta bashi, sannan ta juya ta
tafi.
Murna take kawai a zuciyarta yau gata a Kano
tana
wadaka da komai irin na *yar birni har kan waya
yau
ta rike lallai.
Wani mai tasi Inyamuri baya jin Hausa ta samu sai
suka fara yarawa da turanci. Ta ce Sulaimanu
cresent
zai kaita ya fadi kudi ko ragi bata nema ba ita a
tunaninta komai a birni a ka'ide yake ba'a neman
ragi
kuma ita burinta kawai ya kai ta taga Haisam.
Suna
shiga unguwar sai ta dauko littafinta ta duba
lambar
gidan ta gayawa direban, a shema a kofar gidan
suke
sai ya ce to ai ga gidan ta zaro kudinsa ta bashi
ta fito
daga motar ya ja motarsa ya tafi. Tsantsari, wani
tsalelen gida ne gidan su Haisam yafi duka gidajen
layin tsaruwa Hannah tayi matukar mamakin ganin
gidan su Haisam saboda bata taba zaton Haisam
dan
gidan gawurtaccen mai kudi bane irin wannan.
Wasu
tsala-tsalan motoci ta gani a wajen get din gidan
sun
doshi guda goma. Ta tafi kofar gidan
makwabtansu ta
zauna akan wata kwalbati tana tunanin yadda
za'ayi
yau taga Haisam. Don ita wannan tafkeken get
dogo
baza ma ta iya bude shiba balle ta shiga. Wani
buzu
mai gadi ne ya leko ta jikin get ya hango Hannah
a
kofar gidan da yake gadi sai yayi wuf ya fito ya ce
"Kai
me kana yi anan? Ta ce "Wani nake nema, ya ce
"Waye
wani, ba zaka tambaya ba zaka zo ka zauna
anan?
Hannah ta ce "Haisam na can gidan. Ya ce "Ka ce
na
can gidan me yasa kazo nan ka zauna kuma.
Kaima
bakauye ne ko? Don ka yi kama da *yan garinmu
masu
yalalo-yalalo gashi. Sai duka suka yi dariya shi da
Hannah. Mai gadin ya leka kofar gidan su Haisam
da
yaji hayaniyar mutane. Sai ya ce mata "Yauwa ga
Haisam din can sun fito ita da abokanayenta.
Hannah
ta ce "Dan Allah dan garinmu kirawo min shi akwai
maza bazan iya zuwa ba. Buzu ya karasa wajen
Haisam
ya shaida masa wata na kiransa, Haisam cike da
mamaki ya tunkaro wajen da Hannah ke tsaye sai
tasa
gyale ta rufe fuskarta. Ya karaso inda take a tsaye
yayi
mata sallama ta make murya ta amsa. Ya ce
"Wace ce?
Hannah ta sake make murya ta ce "Bakuwa ce.
Haisam
ya hada girar sama data kasa ya ce "Wai wacece
in ba
zaki fada ba zan koma ina da abunyi. Hannah ta
yaye
mayafin a hankali ta bude fuskarta. Wai, kamar
wani
hasken walkiyane ya haskewa Haisam ido da yaga
fuskar Hannah, cikin fara'a da mamaki Haisam ya
ce
Hannah! Hannah kece!! Tayi lallausan murmushi ta
ce
"Yaya Haisam ni ce, ta duka ta gaishe shi. Taga
Haisam
ya caba ado da wata babbar riga mai aiki a wata
tsadaddiyar shadda fara sol yasa bakin takalmi da
bakar hula yayi matukar kyau. Tayi dariya ta ce
"Yaya
Haisam yau kaine da babbar riga? Har kafi kyau
haka.
Ya ce "Haba? Ta ce "Allah. Ya ce "Yaya su Baba,
da
sauran *yan gidanku? Ta ce sunanan lafiya sunce
na
gaisheku, ya ce "Muna amsawa, to zo ki shiga
cikin
gida ku gaisa da Hajiya. Hannah ta dan yatsune
fuska
ta ce "Kai sai dai watarana ni kunya nake ji kuma
sauri
nake sai dai idan na dawo, ya ce "Au dama ba nan
kika
zo ba ne? Hannah ta ce "Ni kuwa wa gareni a
Kano idan
ba kai ba? Gurinka nazo, Baba ya aikoni. Haisam
ya ce
"To gani fada min aiken. Zumudin yaji abunda aka
aiko
ta ya kama Haisam. Tayi shiru ta hau rufe fuska.
Cikin
zumudi Haisam ya ce "Haba Hannah ki fada mun
mana
kunyar me kike ji ne? Ta ce "Baba ne ya ce inzo in
fada
maka cewar kazo ka nemi aurena ya baka ni. Tun
kafin
ta karasa sai taga Haisam ya fara dariya da alama
farin
ciki ya cika zuciyarsa. Ya kurawa Hannah ido na
wani
dan lokaci ya ce "Shi ne abunda kika kasa fada
daman?
Ya sake yin dariya ya tsaya yana kallan Hannah
wacce
take rufe idanuwanta saboda kunya ga tsananin
farin
ciki.
Ya nisa sannan ya ce "Yanzu Baba da kansa ya ce
ki zo
ki cemin ya bani ke? Hannah ta amsa da "Eh, ya
ce
"Yanzu ya bani ke kacokan a matsayin matata?
Yanzu
Baba ya yarda ki zama uwar *ya*yana mun zama
daya
dangina sun zama danginki, Iyayena sun zama
Iyayenki? Yanzu Baba ya yarda na zama abokin
rayuwarki na dindindin har abada? Yanzu Hannah
kin
amince zaki zama abokiyar zamana har abada?
Hannah
cike da fara'a da murmushi take amsawa Haisam
tambayoyinsa da "Eh' Haisam yayi murmushi ya
sunkuyar da kai na dan wani lokaci can ya dago
ya
kurawa Hannah ido yayin da kowannensu ya
sakarwa
dan uwansa murmushi da wasu masun kauna da
suke
firfitowa daga idanuwan kowannensu, tare da yiwa
junansu wani kallo mai kunshe da so, kauna
muradin
ganin juna. Haisam yayi ajiyar zuciya ya nisa ya
ce
"Alhamdulillahi Hannah na daukarwa Allah alkawari
na
cika, sannan na cika burina dana kudira akanki na
inga
kin kammala karatunki. Kuma yanzu na dawo gida
zan
cika wani tsohon alkawari dana dauka. Nan da nan
Hannah ta kurawa Haisam ido ta daina murmushin
da
take alamar bata gane abunda Haisam yake cewa
ba.
Haisam ya ce "Hannah na gode madalla, ki yi mun
godiya a wajen Mahaifinki. Good bye, Good bye
Hannah. Ya fara ja da baya, yana daga mata
hannu
yana yi mata murmushi. Bakinta ya dau rawa tana
so
tayi magana ta kasa. Gaba daya jikinta ya hau
karkarwa inda jakar dake rataye a kafadarta ta
sulmiyo. Wasu maroka ne suka wayar mata dakai
akan
abunda Haisam yake nufi suna cewa. Ango Haisam
kasha kamshi fari mai farar aniya kaga angon
Ramlah,
*yan boko bayin nasara an daura aure lafiya ankai
maka
amarya gidanta lafiya. Wani abokinsa ne ya taho
da
sauri ya ce da Haisam "Ana tayin waya daga
wajen
daurin aure waje ya cika kai ango kawai ake jira
muje
ka shiga mota mu tafi mana. Haisam da abokansa
suka
shiga tsala-tsalan motocinsu suka zo suka wuce
Hannah anan a tsaye tana karkarwa ido da ido
suke
hadawa da Haisam har suka wuce suka tafi. Ta
juya
tabi motar da kallo har suka hau titi suka kure. Sai
Hannah ta tsuguna a wajen ta rushe da wani
azababban kuka mai radadin fita. Dakyar buzu mai
gadin nan ya dinga bata hakuri ta dauki jakarta
dankwalinta a hannu sai gyalenta ta yafa akai ta
tafi.
Acaba ta hau har tashar *yan kura wannan karon
ma
taci sa'a tana shiga mota ta cika. Kallo daya zaka
yiwa
Hannah kasan hankalinta a tashe yake matuka don
kwandasta sai da yayi magana uku yana cewa ta
bada
kudin motarya bata jiba, hankalinta yana can tana
tunanin daman Haisam ba sonta yake ba, Ramlah
yake
so shine ita da Mahaifinta suke yaudarar kansu.
Yaya
Haisam me yasa kayi min haka me yasa baka
fahimci
son da nake yi maka ba? Ta nisa ta ce "Ko da
yake
bashi da laifi bai yaudare ni ba, ya taimakamin ne
saboda Allah ni na dorawa raina sonsa. Bai san
ina yi
ba kuma, amma na rabu da farin cikin rayuwa na na
rasa
mutum na farko dana taba ji inaso a rayuwata,
gashi
tun bayan gama makarantarmu ko bacci ma
neman
gagarata yake na kwallafa raina da tunaninsa da
tsananin son sa. Sai da wata mata ta kusa da ita
ta
tattabata sannan hannah ta farfado daga tunanin
da
take yi. Kwandasta ya ce "Kudin mota nake
tambayarki
kinyi shiru kina tunani. Sannan Hannah ta zabura
ta
dauko kudin mota ta mika. Mota ta bar cikin Kano
ta
kama hanya sai Babban-mutum.
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 15
Suna isa Babban-mutum, tun
daga tasha Hannah ta dinga jin
faduwar gaba kafarta kamar
baza ta iya
daukar taba dakyar take jefa
kafar burinta kawai ta isa gida
taje ta fada jikin Mahaifinta ta
sharbi
kukanta son ranta tunda yanzu
duk duniya shine kadai ya rage
mata gaba da baya. Kamar
yadda data shiga Kano taga
mutanen garin suna kallonta har
da waiwaye yanzu ma a garinsu
haka ta gani
sai kallonta ake tana tafiya har
da masu nunata kamar basu
santa da ba, Hannah tayi
mamakin irin
wannan kallo da ake yi mata ta
ce a ranta "To ko sun san son
maso wani nake? Wanda nake
so yayi
aurensa da wacce yake so.
Kallon nan dai da ake yi mata ya
daure mata kai. Haka dai
Hannah ta ci gaba da tafiya tana
sauri don ta karasa wajen Mahaifinta
shine kadai mai lallashinta, mai
gaya mata kalaman
da zata ji dan sanyi a ranta. Ta
kusa kofar gidansu, kwatsam
taga wata kungiyar maza dauke
da gawa
sun yi gabas ana Hailala. Taji
gabanta ya fadi ta dubi kofar
gidansu sai taga taron wadansu
mazan da yara a zazzaune ana
jan carbi ta ce a ranta "Ba dai
gawar Babana bace waccan? Sai
ta zubar da takalmanta da
jakarta ta shiga gida da gudu
don ta duba zaure ko shimfidar
Babanta yana nan kuwa.
Tana shiga taga shimfidarsa
wayam baya nan ga silifas dinsa
da butarsa a gefe to ko ban daki ya
zaga. Ga kwanon furarsa a gefe
awurin wacce ta dama masa
yasha ya rage.
Nan da nan taga su Iya Abu dasu
Iya Salmai sun fito daga cikin
gida suna rusa kuka idonsu yayi
jawur suka riketa suna cewa.
Sannu Hannah, wannan ke aka
yiwa mutuwa Allah Ya jikan
Mahaifinki da sunanki a bakinsa
har
ya mutu.
Sai wani jiri ya kwashi Hannah
ta fada kan shimfidarsa ta
rirrike filonsa ta kudindine ta
runtse ido ji take dama kasa ta
bude ta fada itama bakin cikin
rayuwa ya isheta. Ta kwalla ihu
tana kara tana cewa "Inalillahi
wa inna ilaihi raji'un. Allah kana
sane da ni, Allah ka san halin da
nake ciki. Allah
baka tsane ni ba, baka kuma
manta da ni ba. Bani da kowa a
duniya, babu wanda ya ragemin
kuma. Allah kai ne gata na, kai
ka halicceni, ka halicci Mahaifina
kuma ka halicci Haisam, ka
hadani da su
muka saba kuma kai ka raba ni
dasu Allah. Allah kai ne abin
godiya. Allah na gode maka,
Allah kai
ne jagorana, Allah kar ka barni
na dauwama a cikin bakin ciki.
Allahu akbar, sai kowacce ta
rushe da kuka, hatta Iya Abu
data tsani Hannah yau Hannah
ta bata tausayi matuka. Sai ta
rushe da kuka ta dinga rike
Hannah tana lallashi.
Da kyar matan nan suka iya
banbare Hannah daga kan
shinfidar Mahaifinta suka shiga
da ita cikin gida. Hannah tana
rusa kuka kamar ranta zai fita
amma ta nemi hawaye ta rasa.
Sai tayi shiru ta shiga dakinta ta
kwanta ita da Mahaliccinta ne
kadai sukasan
san me take ji a ranta, wani abu
ne ya tokare mata a
zuciya kamar dutse abun yafi
karfin kuka. Hannah ta kalli
gabas da yamma kudu da arewa
taga babu wani mai fitar da ita
daga tsananin bakin cikin nan
da take ciki sai Allah. Ta tuno
nasihohin da Haisam yayi mata a
ranar karshen da ya raka su
tasha tasa
hannu a jakarta ta lalubo carbi
ta fara ja. Addu'oi iri-iri Hannah
ko magana ta daina yi, *yan
gaisuwa a
jere a jere suna ta shigowa
dakinta suna yi mata gaisuwa
sai dai kawai ta bisu da kallo har
sha'awa take yi idan taga masu
kuka da hawaye. Don ita kukan
ma take nema ido rufe tayi ko
taji dan sanyi
a ranta ta kasa. Sallah ce kawai
ta ke fito da Hannah tsakar gida
sai kuma da asuba take shiga
ban daki
tayi wanka.
Banda wannan babu abinda
Hannah take yi sai lazumi. Babu
ci ba sha sai da akai kwana da
kwanaki Hannah ta ki cin abinci
sannan su Iya Salmai suke dama
dan farau-farau suka tsaya
tsayin daka akanta suka ce sai ta
sha. Kurba kawai take ba don
dadi ba ji take sha kamar madaci
suka
dura mata don rashin jin dadin
bakinta da take ji. Anyi sadakar
bakwai kowa ya watse gida ya
zama daga Hannah sai Iya Abu,
*ya*yanta ma duk sunyi aure
kowacce ta koma gidan mijinta,
sai mutuwa ta sake dawowa
Hannah sabuwal fil sai a yanzu
ne ta fara samun zubar da
hawaye. Kullum Hannah kuka
take rusawa ita kadai a daki babu
mai lallashinta kaico Hannah.
Sati daya sati biyu Iya Abu ta gaji
da ciyar da Hannah, a yau da
sassafe shida da rabi Iya Abu
tazo ta fara bugawa Hannah
kofa kamar zata karya kyauren
Hannah na kishingide akan
abun sallah
tun asuba bayan tayi sallah ta
zauna tana jan carbi gyangyadi
ya dauketa kamar a mafarki take
jin bugun kofar tayi firgigit ta
bude ido taga ba mafarki take yi
ba ta zabura da sauri taje ta
bude
kofar. Iya Abu ta gani a tsaye ta
kama tsantsan tayi kalar rashin
mutunci. Hannah taji gabanta ya
yanke ya fadi tasan rashin
mutunci ya motsa yau kuma sai
yadda Allah Yayi da ita. Ta ce
"Hannah an gama Hada-Hadar
mutuwa nayi
na Allah nayi na Annabi na ciyar
da ke a aljihuna har sati biyu. Ga
goro can na aika an suyomin
zan
dafa in fara zuwa kasuwa ina
siyarwa don nima dan kudin
cefanen hannuna ya kare
Ubanki bakar dawa kadai ya bar
mana a rumbu don haka ke
kinci kashinki sauran ta zama
kashin *ya*yana zan ringa siyar
da goro ina samun na cefane
ina tuka dawata, daga yau ki
fara ciyar da kanki kafin a raba
gado dama sunce sai na fita
daga takaba kar kice daman ban
gaya miki ba dan kar in ajiye
tuwon
dumame kizo ki gutsirar mun
tuwo, in kuwa kika sake kika
gutsirarmin sai na shake ki kin
amayo shi. Hannah ta sunkuyar
da kai kasa hawaye ya zubo
shar ta ce "To, naji "Iya Abu ta
tafi ta barta
anan a tsaye kamar an kafata ta
rasa mafita kuma. Hannah ta
kasance tana kwana da yunwa
sai ruwa da take ta dirka wai ko
Iya Abu taji tausayinta ta dinga
bata dan tuwo amma taga
makatau, sai ta shirya ta nufi
gidan Malam Uba kanin
Mahaifinta ta shaida masa
cewar yanzu bata da abunda
zata ci
ko zai ajiye mata kwano a
gidanasa ta dinga zuwa tana
daukar abinci ko da sau daya ne
a rana. Yana budar bakinsa sai
ya ce mata daman ta girma ta
rika wai ita *yar boko ga irinta
nan abincin da zata ci ya
gagareta shi dai shawara daya
da yaga ta dace
tunda duk samarin garin suna
tsoron zuwa wajenta suce suna
sonta ganin ita *yar boko ce to
ta yarda yayi wa Alhaji Bilya mai
kudin garin nan magana ya zo
ya aureta, zata fi karfin abinci
don har tuwon shinkafa dafawa
akeyi a gidansa da daddare.
Wani daci ya disu a zuciyar
Hannah da taji
bayanin kanin Mahaifinta. Alh
Bilyan da yake magana wani
shirgegen tsohon mutum ne
matan
sa uku *ya*ya kuwa sun doshi
talatin da yawa Iyayensu basa
gidan kuma jikokinsa ma
sa'anninta ne, manomi ne ba
laifi yana samu a dai garin shi
mai
kudi ne amma ai tana zuwa
gidan ada wajen kawayenta
tasan yadda yanayin gidan yake. Wata
katuwar tukunya ake dorawa a
gidan kamar ta *yan makaranta
girki ma kadai ya ishi matan
baya
ga dukan mata da yake yi yana
da ciwon kuturta kuma harma
ta fara fitowa. Hannayensa da
bakinsa
zaka kalla kasan kuturu ne
yatsun ne kawai basu gama
guntulewa ba amma sun fara
Ruwa. Hannah
ta tabbatar lallai Baba Uba ba
sonta yake yi ba tunda zai
hadata da Alh Bilya aure. Tayi
shiru a
durkushe a gaban Malam Uba
tana jin bayanan da yake yi mata
ya ce "Kin amince inje in sanar
masa
ko kuma kina da magana kiyi.
Hannah ta nisa ta sunkuyar da
kai kasa ta ce "Baba ba na ki jin
maganarka bane ko naki yardaba
Alh
Bilya fa kasan halinda yake ciki
yana da lalurar kuturta, Baba
yanzu zaka yarda in aure shi a
haka? Malam Uba ya fusata ya
zaburo Hannah da fada "Ke kinfi
sauran matan zani ne? Asirinsu
a rufe ko goya shi zaki yi kina
yawo dashi? Kuma shi da kansa
ya
same ni ya ce yana son ki zai
aure ki. Nake jira daman a gama
zaman makokin nan in shaida
miki.
Tunda kinki sai ki tafi ki nemo
abinda zaki dinga ci gardiya
dake kinki aure babu mai ciyar
dake, tashi ki tafi bani waje
mutumiyar banza. Hannah ta
tashi sumi-sumi ta fice tana
sharbe hawaye. Tana fita ta nufi
makarantar boko, ta kuwa ci
sa'a ta sami Alhajiji wani
ma'aikacin da yake zuwa daga
local
government ta rubuta takardar
neman aiki (application) tuntuni
zai nemar mata aikin koyarwa
a primaryn garin.
Hannah cike da fara'a da murna
ta zo ta durkusa
har kasa ta gaishe da Alhajiji ya
amsa, tun kafin ta ce masa
komai ya ce "Hannah na kai
takardar
neman aikinki wajen manyana
Alhamdulillahi kansilan garin
nan ya gani ya sa hannu an kai
ofishin secretary. Murna ta rufe
Hannah ya ci gaba da
cewa "To amma abunda
sakatare ya ce shine baza
su iya daukarki aiki ba saboda
akwai wadatattun Malamai a
wannan makarantar akwai
makarantun da aka rurrubuta
za'a kara ma'aikata amma
daman banda garin nan don
haka sai dai kiyi hakuri.
Hannah taji ba dadi hankalinta
Ya tashi ta ce "Yanzu
Malam Alhajiji ko share-share
baza a dauke ni ba ko can local
government din? Ya ce kai
share-share ai kinfi karfin yin
shara Hannah ki je dai kici gaba
da addu'a, na manta ma ban
fada miki ba na tambaya ance
resul dinku na jarabawa (s.s.c.e)
ya
fito amma an rike na F.G.G.C
Kazaure saboda kunyi
matukar ci sosai wai har da
masu nine distinction kinga dole
aki sakin sakamakon sai anyi
kyakkyawan bincike ko an baku
amsa ne. Hannah ta ce "Binciken
zai dade ne? Ya ce "Gaskiya irin
wannan yana daukar kusan
shekara ma ba'a saki ba. Amma
daman da da result dinki a
hannu da tuni na samar miki
aiki ko ba'a nan garin ba.
Hannah ta
dade a tsugune a gaban Alhajiji
tayi shiru ta rasa yadda zata yi,
can ta yunkura zata mike da
kyar
saboda jikinta yayi sanyi sai
Alhajiji ya miko mata *yan kudi
ya ce "Gashi kya dan kashe. Dadi
ya
lullubeta ta sami nacin abinci
don yunwa take ji. Ta yi masa
godiya ta nufi gidan Iya Salmai,
ta isketa a
zaure ta kasa zogale tana zaune
tana jiran masu saya. Hannah
tayi sallama ta shiga, bayan sun
gaisa
Iya Salmai ta ce "Hannah lafiyar
ki kalau kuwa kin birkice gaba
daya kamar ba ke ba? Hannah
tayi
murmushin karfin hali ta ce "Iya
yunwa nake ji ko da sauran
dumame? Ta ce "Wada na
ajiyewa ya tafi kwallo, rabonki
ne zuba ki ci. Da sauri Hannah ta
mike ta nufi kicin don ta zubo
tuwan. Iya Salmai ta bita da kallo
cike da tausayinta. Sharkab tana
kuka Hannah ta fito ta sami Iya
Salmai tana cewa "Allah
Sarki Habu ka mutu kabar
yarinya marainiya a duniya
kaine daman gatanta. Hannah ta
zauna a
sanyaye tana cin tuwon su duka
hawaye suke yi. Iya Salmai na
tausayinta itama Hannah na
tausayin kanta. Bayan ta ci ta
koshi tasha ruwa taje ta ajiye
kwanon a cikin gida ta wanke
hannunta sannan tazo ta zauna
ta shaidawa Iya Salmai halin da
take
ciki ta ce kuma tana neman
alfarmar idan da hali Iya Salmai
ta ajiye mata kwanon tuwo a
gidanta
tana aika mata. Iya Salmai taji
dadi kwarai da Hannah bata yi
kauron baki ba tazo ta sanar
mata da wuri ta ce insha Allah
kome taci da kashin Hannah to
amma itama ba kullum suke
dora tukunya sau uku a rana ba.
Itama ba da ko *ya
gareta ba bishiyoyin zogale ne
burjik a shuke a gidanta. Ta
tsinka ta dafa ta sayar ko azo a
tsinka
danye a biyata. Daga ita sai
Wada wani dan kanwarta data
rasu ta barshi tun ranar da aka
haife
shi ta dauke shi. Shima yana
kokari ya samo kudi,
to da haka suke cin abincin,
ranar da ba'a samu ba
su sayi na siyarwa ko su hakura
idan babu kudin sayan na
sayarwar. Iya Salmai ta ce "Ai
idan naga *ya*yan Habu raina
dadi yake yi, ba don Habu yana
dan Uwana bama, soyayyar da
nake masa ce
Hannah har yau ina jin
dandanonta a raina. Hannah tayi
shiru tana tunani a ranta tana
kuma tausayawa kanta cewar.
In har Iya Salmai bata daina jin
dandanon soyayyar da take
yiwa Mahaifinta ba har yanzu
shekararsu tafi ashirin da biyar
da rabuwa gashi kuma ma har
ya mutu tana zancen sonsa,
ashe har abada Iya Salmai baza
ta daina jin dandanon son nan
ba. To itama tana kyautata zaton
haka zata kasance da son
Haisam tunda
gashi dai yanzu bata ganinsa
yayi aurensa ma amma sai kara
jin kara sonsa take ashe itama a
haka zata dauwama kenan har
karshen rayuwarta.
"Soyayyar gaskiya ce. Hannah ta
fada a baiyane. Iya Salmai ta ce
"Soyayyar gaskiya ce Hanne.
Haka dai suka yini suna hira
Hannah ce ta dafa musu
abincin dare suka ci sannan
suka yi sallama Hannah ta tafi
gida. Sun rabu akan Iya Salmai
zata ringa tura Wada yana kawo
mata abinci duk sanda suka
sami damar dafawa.
Haka Hannah ta kasance duk
sanda Iya Salmai ta
dafa abinci ta aiko mata taci
ranar da itama bata dafa ba
haka Hannah take zama da
yunwa. Ta rame kurkut da ita sai
ido da dogon hanci ta yi duhu
kuma saboda tsabar wahala da
tsananin tunani.
Ranar da Iya Abu ta fita daga
takaba sai mai gari ya hado
Manyan Malaman garin da masu
fada aji na garin da *yan Uwan
Malam Habu don a raba
gadonsa ga Iyalansa.
A zauren gidan aka zazzauna ga
Iya Abu ga *ya*yanta kakaf
mata da maza ga Hannah a gefe,
itama da Iya Salmai. Mai gari ya
ce "A karantawa Mamacin
kulhuwallahu kafa uku-uku, da
Inna a'adaina kalkausar uku-
uku aka shafa Allah Ya kai
kabarinsa. Sai mai gari ya fara
da cewa "Malam Habu ya rasu
yabar mace daya da
*ya*ya takwas. Dukiyarsa kuwa
wannan gidan ne da kuma
katuwar gona, amma tun ranar
daya mutu aka biya masa
basussukan da ake binsa da dan
kudin daya bari. Ga manyan
Malamai nan zasu raba gado. Ga
sunayen *ya*yan nan a wajensu
zasu shiga cikin gidan su
tsattsaga su bawa kowa nasa
bangaren. Iya Abu ta nisa ta ce
"Ina da magana ni dai nice
matarsa Uwar *ya*yansa kuma
bare daya ce Hanne don haka a
tabbata an bata bangarenta
daban kar a saka min ita a cikin
kason *ya*yana azo ana rigima.
Mai gari ya ce "Ai Abu
rabon gado ba'a cewa ga bare
Allah ne Ya raba da kansa don
haka duk yadda ta kama haka
za'ayi. Malamai sun yi iya
kokarinsu sun kacaccala dan
mitsitsin gidan nan da gona.
Allah cikin ikonsa Hannah bata
tashi da komai ba sai runbun
ajiyar abinci wani dan mitsitsine
kasa ce turmus a kasan da
gidan tururuwa sai dan wani
bangare karami a tsakar gida
shine kashin Hannah a gona
kuwa bata ciki. Murna ta lullube
Iya Abu gona da gaba daya
dakunan gidan nata ne da
*ya*yanta sai ta ce
"Wannan rabo yayi dai-dai to
yanzu sai mai gari kasa Hanne ta
hada kayanta ta koma runbunta
ta
tashi daga dakin nan. Mai gari
ya ce "Haba Abu har yanzu
tsangwamar da kike yiwa Hanne
baki bari ba har Mahaifinta ya
mutu ma bakya rangwanta mata
ba. Iya Abu ta ce "A'a babu wani
rangwami *yan haya zansa a
sauran dakunan ina karbar kudi
wannan abu ne fa na gado. Nan
fa duk suka hadu suna ta bawa
Iya Abu Hakuri ta bar Hannah ta
ci
gaba da zama a dakin da take
har Allah Ya yanke mata wannan
zama tunda komai dadewa aure
zata
yi. Iya Abu ta kekashe
idanuwanta ta ce in anga Hannah yau ta sake
kwana a cikin dakin nan
nata to ta bata kudin haya ne a
matsayin tana haya.
A cikin mutanen dake wajen
harda Alh Bilya ya ce to tunda
Abu ta ce haka shi yayi alkawari
zai dinga biyawa Hanne kudin
haya daga yau ya tambayi Abu
ko nawa ne kudin hayar dakin
da Hanne ke
ciki ta kai-kai ce ta zambada
kudi ya zaro ya biya ba tare da
ya nemi ragi ba, ya biya na
shekara ya san
Iya Abu kora da hali take yiwa
Hannah ta zambada kudi dan a
ce yayi tsada a kama mata a
wani gida cikin ikon Allah sai
taga ya biya.
Mai gari da sauran mutanen
dake wajen suka dinga shiwa
Alh. Bilya albarka. Hannah ita da
Baba Uba ne
kadai suka san manufar Alh
Bilya shi a nufinsa auren Hannah
zaiyi shi yasa ya fara yi mata
hidima,
wani gululun bakin ciki ne ya
dira a zuciyar Hannah
musamman da ya biya mata
kudin haya ta san lallai
da gaske yake auren nata yake
so yayi ita ko gara a kasheta da
a daura mata aure da wannan
mutumin kamar ta ce bata son
kudin hayar baza ta zauna a
gidan ba karya ya biya sai tayi
tunani in ba gidan uban nata ba
a ina zata zauna saita hakura
kawai tayi shiru idan ta ce zata
koma gidan Iya
Salmai to ai daki daya ne kacal a
gidan dan karami ita da Wada
suke kwana a dakin, ba zai
yuwu ita ta
hadu da Wada a daki daya ba
saboda yanzu Wada shekararsa
goma sha takwas yama girme ta
da
shekara daya don haka ya
haramta su cusu a daki daya.
Bayan nan babu kuma gidan
wanda zata iya
zuwa ta zauna duk danginta.
Da daddare bayan kowa ya
shiga bacci ya kwanta Hannah
na juyi akan *yar katifarta ta
kasa bacci
tsananin bakin ciki ne ya
dameta a ranta babu abinda
take nanatawa a ranta sai
zancen hayar nan, ita da gidan
Ubanta yau ta zama *yar haya
sai ta rushe da kuka harta gaji.
Ta ce "Allah kana ji,
kuma kana ganina, kana kuma
sane da irin abubuwan bakin
cikin da nake gani tun ranar da
Mahaifiyata ta sako ni a duniya
Allah ka fitar dani,
kai ne gatana Ya Sarkin
Sarakuna. A haka Hannah ta
kasance har shekara guda da
rasuwar Mahaifinta yau ta ci
abinci gobe ta rasa wannan bai
dameta ba
sosai irin zirga-zirgar da Alh
Bilya yake yi a danginta yana
cewa shifa yana so ya aureta.
Dan har yaje ya sanarwa da mai
gari, mai gari yasa aka kira
Hannah fada ya shaida mata
abun da Alh Bilya yake nema a
wajenta shin ta amince zata
aure shi, ta yarda tana so a
daura auren? Hannah ta fito gar
da gar ta fadi gaskiya ta ce
"Ranka ya dade banki jin
shawarar da ka bani ba amma
dan Allah ina so a
barni haka bana so in auri
kowa. Gaba daya aka dau salati
aka fara yiwa Hannah cari "To
ba'a garin nan ba, duk garin
nan wacece ta taba kaiwa
shekara goma sha takwas ba a
yi mata auren fari
ba? Hannah ta ce "Ba zan Iya
auren Alh Bilya ba a matsayinsa
na Mahaifina dan ni tamkar
Mahaifina
yake a wajena. To haka aka yi da
Hannah a fada.
Alh Bilya yaji haushin Hannah
data ki yarda amma yasan
tuggun da zai tafka mata ya
rama.
Bayan anyi haka da Hanna a
fadar mai gari da kwana uku,
Alh Bilya yazo har cikin gidan su
Hannah da rana tsaka. Hannah
na daki a kwance tana jin
yunwa tana jiran a kawo mata
abinci daga
gidan Iya Salmai tana fargabar
ko suma basu yi abinci ba ne sai
ta jiyo muryar Alh Bilya yana
rafsa
sallama Iya Abu ta fito. Bayan
sun gaisa Iya Abu ta ce "Yau
Alhaji da kanka a gidan namu?
Ya ce "Eh
wallahi zauwa nayi mu gaisa inji
ko yaushe kudin hayar dana
biya yake karewa? Iya Abu tayi
dariya
ta sosa kwarkwata a kai ta ce
"Ai saura wata uku ina jin, ya ce
"To ki raba kudin hayar gida
hudu ki
dauki kashi uku naki ki bani
kashi daya na ragowar
watannin uku ki kori Hanne
daga dakin da take haya in bata
biya ki ba babu ruwana.
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter16
Iya Abu ta bata rai ta ce "To ni
yanzu na kashe kudi
yaya kake so nayi a ina zan
samo kudinka da zan dawo
maka dashi? Hanne fakara'u ko
sisi bata dashi ina zata samo
wani kudin haya ta biyani?
Gaskiya Alh Bilya kai ya dace kaci
gaba da biyan kudin haya don
haka kace a gaban maigari, ya
ce "Kash ni baki fahimce ni ba
Abu
ba don in takura miki ba nace ki
bani sauran kudin ki rike sauran
kudin ina nufin a yanzu ki koro
Hanne daga dakin da take haya
donni bada yawu na take zaune
a dakin ba kuma ba'a kudina ba.
Iya Abu tayi dariya ta ce
"Oh na gane wato yanzu dai na
rike ragowar kudin watanni
ukun da suka rage kenan
sannan in koro Hanne waje idan
bata biyani kudin haya ba ko, ko
ba haka kake nufi ba? Alh Bilya
yayi dariya ya ce
"Haka nake nufi mana. Iya Abu
ta ce "An gama ai a gabanka zan
koro shegiyar. Gaban Hannah ya
yanke ya fadi tayi zunbur ta
tashi zaune ta dafe kirji tana ta
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Iya Abu ta wangale labulen
dakin ta shiga ta sami
Hannah a kan katifa a
zaune ta mikawa Hannah hannu
ta ce "Bani kudi, Hannah ta ce
"Bani da kudi. Iya Abu ta
wawuri jakar Hannah zata
wurgar waje Hannah ta rike
tana mata magiya tayi
hakuri dan Allah ta rufa mata
asiri. Amma kamar zuga Iya Abu
take. Hannah ta fito da gudu
daga dakin ta zo ta durkusa a
gaban Alh Bilya tana rokonsa
dan Allah yayi hakuri
ya bar mata kudin hayar wata
uku kafin nan zata san yadda
zata yi ta sake biya. Amma yayi
kunnen uwar shegu da ita yana
cewa "Yauwa Abu ki tattaro
kakaf kayanta ki watso. Ana
cikin wannan hali sai ga
Wada nan dauke da kwanon
abinci ya kawo mata abincin
rana ya sami Hannah kace-kace
tana kuka a durkushe a gaban
Alh. Bilya tana rokonsa Iya Abu
kuwa tana
ta faman watsi da kayanta. Cikin
kuka Hannah ta ce "Wada kaga
halin da nake ciki jeka ka kira
Iya
Salmai tazo ta tayani rokarsu.
Nan da nan Wada ya garzaya
dan ya shaidawa Iya Salmai
halin da yazo ya tarar da
Hannah. Bayan tafiyar Wada ba
dadewa sai ga Iya
Salmai da mai gari da tawagarsa
sun shigo gidan suka iske su
Hannah a cikin wannan hali. Mai
gari ya ce "Subhanallahi Alh Bilya
da girmanka, meye haka?
Alh Bilya ya ce "Ranka ya dade
babu yadda za'ayi taci gaba da
zama a cikin kudina bayan bata
sona shi yasa nazo na ce to in
Abu taga zata bar Hanne taci
gaba da
zama a kyauta to, amma in dai
nine ke biyan kudin nan
dole Hanne ta fita don bazan
barta taci gaba da zama a
kudina ba tunda bata sona. Nan
dai aka hau bama Alh Bilya da
Iya Abu baki ana musu wa'azi
da nasihohi akan rayuwa ce
kuma suma suna da *ya*ya zasu
iya mutuwa su bar *ya*yansu
suma ayi musu haka.
Hannah tasa gefen zaninta ta
goge hawaye ta mike daga
durkusan da take yi ta juya ta
kalli su mai
gari ta ce "Ku kyale su, ni na
hakura da zama a dakin zan
koma rumbun in zauna. Hannah
ta fara dibar
jakunkunan ta tana shigarwa
cikin rumbun nan mai gidan
tururuwa da cinnaku ga
buhunhunan dawa
dana kaikayi. Hannan abun
tausayi Iya Salmai ta ce "Haba sai
kace ba raina ai bazan barki ki
zauna a nan
dakin mai tururuwa ba, ko
Wada ya dinga fitowa yana
kwanciya a waje ni da ke mu
dinga kwana a daki. Hannah
tana hawaye ta ce "Iya Salmai
kyale ni gara in mutu in huta da
irin wannan rayuwar.
Ana cikin wannan badaqalar ne Musa
dan makwabcinsu ya shigo
ya ce "Wasu maza ne guda biyu
gasu nan a waje wasu farare ne
kamar larabawa sunce suna
neman
Hanne *yar gidan Malam Habu.
Mai gari ya ce "Larabawa daga
ina? Musa ya ce "Sun ce wai
daga Niger suke, maigari ya ce
to muma ai tafiya zamu yi mu
tafi kawai. Har Hannah suka yiyo
waje wasu samari farare sol-sol
ne guda biyu a tsaye a kofar
gidan.
Daya daga gani ko tambaya
babu jinin Hannah ne don
kamar su daya kamar an tsaga
kara, mai gari ya
ce "Kune bakin daga Niger?
Suka amsa da "Eh, sannan suka
duka suka gaishe da su maigari.
Hannah ta tsaya a gefe tana
kallon wadannan baki nata, bata
san su ba
amma daya daga cikin samarin
kamar su daya futik daga gani
babu tambaya daga tsatso daya
suka fito. Mai gari ya ce "To ga
Hannen, yaya kamar baku
san juna ba. Mai kama da
Hannah ya ce "Ni sunana Ahmad
wannan abokina ne sunansa
Bello Madu. Ni kanin Mahaifiyar
Hanne ne Uwa daya Uba daya,
Hanne bata taba ganina ba ban
taba ganinta ba shine nazo na
nemota dan muga juna. Hannah
na jin haka sai ta
daka tsalle ta rungume Ahmad
sai ita dashi suka rushe da kuka.
Mai gari da sauran mutane sai
suka hau
girgiza kai suna masu
tausayinsu.
Mai gari ya ce "Alhamdulillahi
gara da Allah Ya kawo ku sai mu
koma daga ciki a tattauna.
Bayan kowa ya sami waje ya
zauna, Hannah ta tashi ta dauki
kwano ta kwalfo musu ruwa a
randa ta kawo musu. Bayan
sunsha mai
gari ya fara bayani ya shaida
musu duk halin da Hannah take
ciki yanzu ma ga jakunkunanta
nan a watse a
waje, dakin da zata zauna ma
yanzu ya zama garari.
Ahmad ya matse hawaye ya ce
"Hakika tuntuni munji halin da
Mahaifiyarki ta shiga har ta rasu
mun san kuma halin
*yarta Hanne zata shiga amma
da yake ni ina yaro bani da ikon
inzo in dauketa shi yasa na
hakura. A
kwanakin nan kuma na dinga
mafarkai iri-iri na *yar uwata
marigayiya Uwar Hanne, kullum
na kwanta bacci sai inga Yayata
Habi tazo tana cewa Ahmad dan
Uwana yanzu ba zaka je ka
nemo *yata ba Hanne kaga
halinda
take ciki a duniya ba, ko daren
jiya ma nayi mafarkinta abu
daya kuma take maimaitawa,
don haka yanzu daman nazo da
niyyar mu tafi da ita ko da
Mahaifinta yana nan zan rokeshi
ya bani ita idan bata yi aure ba
in tafi da ita, balle kuma yanzu
da ya rasu dole in
tafi da ita. Iya Abu ta tabe baki
ta ce "Malam tunda ransa ya
hana akai Hanne wannan garin.
Mai gari da jama'arsa suka yiwa
Iya Abu caa suka rufeta da fada
suna cewa "Ba yanzu kika gama
mata watsi da kaya ba? Bayan
bakar wahalar da take sha tun
tana karama ta zamo tamkar
baiwa a gidan nan.
Ahmad ya ce "Ba saikun bata
bakinku bama wajen
bata amsa mu dai zamu tafi da
ita. Sai yanzu daya mutumin yayi
magana wato Bello Madu, ya ce
"Ai
anan kusa muke a garin Dashi
muke, Dashi da Babban mutum
ai border ce ta raba.
Ni costom ne ina aiki a border
lokaci lokaci zan dinga kawo
muku Hanne kuna gaisawa.
Ahmad ya katse shi ya ce "Bello
Madu duk
zancen ka lallashi matar nan bai
taso ba kaga kankat din garin
wato Maigari da jama'arsa sun
bamu
izinin mu tafi da ita, to ita
wacece kuma da zata ce sai
Hanne ta zauna yunwa ta kashe
ta. Iya Abu taji wani dacin bakin
ciki ya rufeta ganin Hannah ta
sami wajen
da zata je ta huta, ta so ace da ta
yiwa Hannah watsi da
kaya duk garin ta rasa inda zata
zauna. Ahaka dai aka rabu
Ahmad da abokinsa Bello Madu
suka yiwa
mai gari da jama'arsa sallama
suka daukarwa Hannah
Jakunkunanta, Hannah ta yafa
gyalanta ta
rungume Iya Salmai suna kukan
rabuwa Hannah da Kawunnanta
suka tafi.
Sun isa garin Dashi da daddare
gidan Ahmad suka sauka,
Ahmad yana da mata daya da
*ya*ya biyu.
Sunan matarsa Hajir itama irinsu
ce buzuwa. Hajir ta tari Hannah
cikin fara'a da murna ta kaita
daki ta kawo mata ruwa tasha
sannan ta zauna suka gaggaisa
sannan ta je ta shirgowa
Hannah tuwo. Hannah ta ci
tuwon nan kamar tunda Allah Ya
halicceta bata
taba cin tuwo mai dadin haka
ba, saboda tsabar yunwar da
take ji, ta ci tayi nat sannan ta ce
a nuna mata ban daki
zata yi alwalla. Hajir ta nuna
mata. Hannah ta shiga ta dauro
alwalla ta zo ta yi salla tana
idarwa taje ta
watsa ruwa tayi wanka tazo ta
kwanta. Hajir taji tana son
Hannah, tana sonta da kawa
daga gani ma sa'anni ne.
Hajir ta zauna a gefen shimfidar,
Hannah na kwance suna ta hira
kala-kala, Hajir bata bar dakin ba
sai da taga Hannah ta fara bacci
sannan ta hure mata fitila ta
rufo mata kofa ta fita ta nufi
dakin kwanciyarsu.
Da asuba Hannah ta farka taji
ana kiran assalatu ta mike ta
nufi ban daki tayi alwala tazo
tayi sallah ta
zauna tana ta lazumi. Gyangyadi
ne ya dinga daukar Hannah ta
mike ta koma kan katifa ta koma
bacci tayi tayk barci har sha dayan
rana babu wanda ya tashi
Hannah
sai da tayi barcinta ta gaji ta
farka da kanta. Tana tashi tayi
ido hudu da soye-soyen abinci
kala-kala Hajir tazo ta jera mata.
Ba Hajir kawai ba *yan Uwan
Uwar
Hannah da yawa labari ya kai
musu cewar Hannah ta zo don
haka suka aiko mata da abincin
karin kumallo iri-iri sunka ce
kafin suzo su ganta. Hannah ta
fada wanka tayi brush sannan
ta saka kayanta tazo ta zauna a
gaban abincin burjik a jere a
tsakar dakinta duk nata
ne sai taji wani farin ciki ya
lullubeta ba'a sabanba.
Yau Hannah ce da barcin safe ta
farka taga abinci burjiki an
jere mata, haka Allah Ya ke,
duniya juyi-juyi. Tun kafin
Hannah ta gama karin kumallo
taji tsofaffi da
mata suna sallama a tsakar gida,
*yan Uwan Mahaifiyar
Hannah ne suka fara cici rindon
zuwa ganin Hannah. Sai koke
koke daga su har Hannah taga
dangin
Uwarta cunkus amma suka ce
mata wadannan ma kadan
ta gani dan tushen zuriyarsu
abzinawa ne (buzaye) suna
Agadas state. Sai dai wani abu
guda da Hannah ta lura duk
danginta talakawa ne sosai
suna cikin rashi,
wasu nono suke sayarwa a
rugage, wasu kuma manoma
ne. Kawu Ahmad ne kawai dan
boko wayayye mai dan hali akan
sauran koyarwa yake a
makarantar firamaren garin har
ya sami matsayin mataimakin
headmaster.
Shima dai rufin asiri ne kawai
ba wani arziki gare shi ba.
Gidansa ginin kasa ne dakuna
uku ne, bandaki da zana aka
zagaye, kicin kuwa a tsakar gida
aka
dasa murhuna. Haka dai Hannah
taji ta shiga wata sabuwar
rayuwa mai dadi fiye da
rayuwarta ta da a
gidansu.
A koda yaushe tana godewa
Allah da Yayi mata canji daga
ukuba da bakin ciki hantara Ya
kawo ta inda
ake tarairayarta. Hannah da Hajir
sun shaku sosai a koda yaushe
suna tare suna wasa da dariya.
Tun Hannah na boyewa Hajir
wasu abubuwan na dangane da
rayuwarta har ta yaba da
hankalinta ta fara gaya mata
wasu abubuwan da suka faru
da ita ada na dangane da
tsananin son
Haisam da ranar rabuwarsu. Ta
ce har yau kullum da daddare
sai tayi kuka idan taje kwanciya
bacci
saboda tunaninsa. Hajir ta
tausayawa Hannah sosai har
hawaye tayi mata, daga karshe
tayiwa Hannah nasihohi akan
tayi hakuri kaddara ce daga
Allah
haka Allah Ya rubuto musu.
Bayan zuwan Hannah da kamar
wata guda Kawu Ahmad da
sauran manyan danginsu suka
kira
Hannah babban zauren dake
gidan. Bayan ta gaishe da
kowannensu ta koma gefe ta
takure. Baba Sha'aibu ya ce
"Hannah kinsan dalilin da yasa
muka kiraki nan?
Hannah cikin ladabi ta amsa
musu da "A'a, ya ce
"To a matsayinmu na Iyayenki
da Kakkaninki munyi nazari mun
kuma tsayar da shawara, abinda
da nake nufi da munyi nazari
shine bai kamata ba mu zuba
miki
idanu haka nan babu aure ba. Don
haka ya kamata kiyi aure a
watannan. Gabanta ya
yanke ya fadi ras dajin kalmar
aure cikin rudani ta ce .......
"Wa zan aura ai ni bani da kowa
a garinmu anan garin ma babu
wanda ya ce yana sona. Su duka
suka kyalkyale da dariya.
Ahmad ya ce "Hannah kwantar
da hankalinki dole mu aurar
dake ga mai sonki kece dai baki
sani ba
amma zuwanki garin nan maza
sun doshi goma suka sameni
suka ce suna sonki. Shawarar da
muka yanke ita ce muduba a
cikin su waye yafi hankali,
addini, sana'a, asali wanda zai
rikeki tsakani da Allah mu aura
miki shi tunda ke bakuwa ce ba
sanin halayensu kika yi ba babu
kuma ishasshen lokaci da za'a
barki kina soyayya
dasu har ki zabi miji mu baza
mu zaba miki wanda zai cuceki
ba. Hawaye ne ya fara zubowa
shar daga idanuwan Hannah
babu wanda ya fado mata a rai
sai Haisam, soyayyar da take
yiwa Haisam sai kara yabanya
take a cikin ranta, Hannah ta cire
sha'awar
auren wani a rayuwarta tunda
ta rasa Haisam shine ma hawaye
yake zuba daga idanuwanta
don tasan ta rasa wanda take so
duk duniyar nan ta rasa farin
ciki kuma.
Wannan hawaye na Hannah da
yake zubowa daga idanuwanta
yasa jikin su Ahmed yayi sanyi
kuma mamaki ya rufe su yaya
za'ayi Hannah ta fara
kuka tun kafin taji waye aka
zabar mata ta aura. Ko akwai
wanda
ta kudira zata aura ne basu sani
ba? Inna Rabi ce ta ce "Hannah
kukan me kike bafa cewa muka
yi dole sai kin auri wannan
wanda muka zabar miki ba idan
kina da
wanda kike so fadi mu aura
miki. Daman ganin babu kowa
ne shi yasa muke tunanin
hadaki da wani.
Hannah ta share hawaye ta
girgiza kai ta ce "Babu wanda
nake so zan aura duk wanda
kuka zabar min
zanyi biyayya in aure shi ko
waye, kuma nasan baza ku
zabar min wanda zai cutar da ni
ba. Gaba daya
suka fara shiwa
Hannah Albarka suna jinjina
mata bisa tsananin biyayya da
take yi musu, Allah Ya yi mata
albarka. Kawu Ahmad yayi
gyaran murya ya gyara zama ya
ce "Hannah tun farkon zuwanki
abokina
koma in ce ya zama dan uwana
saboda tun muna yara muke
tare nasan halinshi ciki da bai
fiye da Uwar da ta haifeshi bata
sanshi ba fiye da yadda nasan
yadda yake, yana da mutunci da
sanin ya kamata ya ce yana
sonki tsakani da Allah zai aureki
wannan aboki
nawa shine Bello Madu abokina
din nan da muka je Nigeria
garinku dashi muka dauko ki,
yana da sana'arsa kuma yana da
ilimi gaba daya boko da arabiya
yanzu ma babba ne ba laifi a
aikinsa aikin custom yake sune
suke tsaye a bodar Nigeria zuwa
niger. Ni dai a ganina Bello
Madu ne kawai ya cancanci ya
aure ki ko ya kika
gani?
Iya Ma'ida ta ce "Wanne irin yaya
ta gani bayan ta gama magana
ta ce ko waye muka zabar mata
tana so. Cancanta ma ai ba sai
an fada ba sun dace ai.
Hannah ta sunkuyar da kai sai
hawaye shar ya sake keto mata.
Bello Madu kam ya cancanci a
soshi bashi da makusa kyau
kuwa kamar shi yayi kansa dan
buzayen
asali kamar balarabe, hankali da
tausayi kuwa ba'a magana don
da yaji labarin Hannah hawaye
ya dinga yi don tausayinta bashi
da makusa ko kadan amma ita
abun da ya kara sata kuka shine
tana matukar ganin mutuncinsa
don haka bata so aka ce shine
zai aure ta ba don duk wanda
ya aureta sai yayi hakuri
saboda bazai sami soyayyarta
ba GANGAR JIKINTA zai aura
zuciyarta na wajen Haisam har
abada. Hankalin Hannah ya sake
tashi sosai da taji sunan wanda
zata aura. Kawu Ahmad ya ce "Ni
wannan kukan naki ne yake
tsoratani Hannah kiyi magana
idan akwai wani abun da yake
damunki. Hannah ta yi dan
murmushi ta
girgiza kai ta ce "Babu komai
zabin da kuka yi min yayi.
Inna Goshi ta dau buda kowa ya
hau cewa "Allah Ya sanya alheri
ya baku zaman lafiya. Hannah ta
mike
ta shiga cikin gida bata tsaya a
ko'ina ba sai cikin dakinta ta
rufe kofa ta fada kan katifa sai
ta bude
shafin kuka mai tsanani taji a
ranta kamar wata sabuwar
soyayyar Haisam aka kara zuba
mata taji
sonsa ya sake sarketa kamar
zata yi hauka. Bayan anyi haka
da kwana uku Hannah na zaune
tsakar gida tana tankaden gari
da yamma tana taya Hajir aiki,
Hajir kuma na wajen murhu
tana kada
miyar kuka, suna taba hira. Hajir
ta ce "Hannah ina ganin kinfi
sauran mata yin sa'ar samun
kintsattsan miji a duk *yan
matan garin nan saboda duk
yawanci
*yan matan garin babu wacce
bata kaiwa Bello Madu hari ba
farin jini gareshi sosai.
Kyawunsa ne, ko kuwa iliminsa,
ko kuma jan ajinsa ne yake
rudarsu oho? Amma ke
gashi kwatsam ya damu da
sanki kinsan tun ba yauba
Kawunki Ahmad ya fadamin
cewar Bello Madu yana sonki
amma ya gargadeni da nayi
shiru kai in
sanar miki har sai ya sanarwa
da magabatansa shima.
Hannah ta cije tayi dan
murmushi ta ce "Hajir kenan
wato nayi sa'a sosai ashe dana
sami Bello ta sama, ba tare da
nasha wahala ba? Amma ni a
wajena sai dai ma
ince shine yayi sa'a sosai ma
kuwa. Alhamdulillahi amma
akwai matsala tabbas.
Hajir ta juyo gaba dayanta tana
kallon Hannah can ta ce "Ban
gane akwai matsala ba, wacce
irin matsala kuma Hannah? Ko
bakya sonsa ne? Hannah ta
girgiza kai ta ce "A'a naki shi
bayan shine zabin Iyayena ina
sonsa mana. Muryar Bello Madu
ce ta ce
"Assalamu Alaikum. Kai tsaye ya
shigo cikin gidan kamar yadda
ya saba shigowa daman. Kai
tsaye wajen Hannah ya dosa,
Hajir ta amsa masa sallamarsa
gami da yi masa tsiya
ta ce "Oh dan halak kaki ambato
yanzu zancenka fa muke yi ango
kasha kamshi daga zuwanka ka
doshi wajen Hannah, da idan
kazo wajen wa kake dosa?
Bello Madu ya kyalkyale da
dariya ya ce "Kai Hajir kin fiye
tsokana kinsan da sai inyi sati
biyu a boda ban damu da zuwa
garin nan in kwana ba amma
yanzu
kusan kullum sai nazo garin nan
ko banzo gidan nan ba ina jin
dadin garin saboda matar da
nake so tana cikin garin. To
yanzu an bani izini inzo wajenta
kina nufin sai
in doshi wajenki duhu, bayan
daga shigowata hasken fuskar
Hannah ne ya bugi idanuwana.
Kinsan ko a kabari haske ake
nema ana neman tsari da duhu.
Hajir ta rike baki ta ce "Ah Bello
Madu daina hadani da duhun
kabari Allah Ya baka hakuri.
Wannan hira tasu ta bawa
Hannah dariya bata san sanda ta
tuntsire da dariya ba duk da
wani kululun bakin cikin daya
dira
a ranta yanzun nan da Bello ya
shigo. Haisam kawai zuciyarta
take haska mata, inama- inama
ace da Haisam za'ayi musu
auren nan wata guda ya rage
ayi bikinta. Bello Madu ya ce
"Hajir yi hakuri
bada duhun kabari nake hadaki
ba ni na isa? Ai nasan kokarin
da kike min wajen turani fadar
zuciyar
Hannah tun dazu ina zaure a
tsaye ina jin hirar da kuke yi,
kuyi hakuri ba labe nake yi
muku ba ina doso kaina Bello
Madu naji ana ambato shiyasa
na dakata sai da na gama jin
komai.
Hajir ta yi dariya ta ce "A'a Baba
Bello ka fara labe a gidan
mutane dai kawai zaka ce min.
Ya karasa wajen Hannah ya
jawo wata kujera a gefenta ya
zauna a hankali yayin daya
kafawa Hannah ido yana
kallonta, ji yake tamkar ya
hadiyeta saboda son da yake yi
mata, fargabarsa daya yana
tsoron kada Hannah taki
amincewa da soyayyar da yake
yi mata haka nan
ko bayan abokinsa Ahmad ya
shaida masa an bashi Hannah
yayi farin ciki amma farin cikin
ragagge ne yana gudun kada a
takurawa Hannah ta aure shi
yazo ya rasa soyayyarta amma
yau sai gashi da kunnensa yaji
Hannah ta ce "Ni na kishi bayan
shine zabin Iyayena ina son sa.
Don haka yau yafi kowa farin
ciki. Hannah ta dago a kunyace
ta gaishe shi ya amsa cike da
fara'a ya mika hannu ya karbi
rariyar dake hannunta ya fara
tankade Hannah na zuba masa
gari yana tankadewa. Hajir
kuma tana yi masa tsiya tana
cewa "Wai
Bello wannan bamu san wanne
irin abu za'ayiwa Hannah ba
bayan anyi auren, tuwan ma nasan kai
zaka dinga tuka mata
Hmm wai ya abin yake ne!!?
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 17
Bello ya ce "Ke kin fadi kadan
tauna abincin ne kawai bazan
yiwa Hannah ba saboda bazai
yuwu in
tauna mata ba amma a baki zan
dinga bata bayan na dafa mata
domin Hannah tafi sarauniyar
da take mulkin duniyar nan idan
ma akwai yadda nake jinta a
raina.
Ga mamakinsu sai suka ga
hawaye shar ya tsiyayo daga
idanuwan Hannah, babu abinda
ya sata kuka sai tausayin kanta
dana Bello Madu domin
kowannensu
son maso wani yake yi, inama
Haisam ne yake jinta a ransa
haka kamar yadda Bello Madu
yake jinta a ransa.
Shima inama ma yadda yake
sonta shima tana sonsa haka.
Allah Sarki Bello ka makara.
Hannah ta fada a ranta. Sai Bello
ya kurawa Hannah ido kawai
yana kallo sai ya juya ya kalli
Hajir wacce
itama tayi kasake a tsaye tana
kallonsu. Ya mike tsaye
ya kade garin da yake hannunsa
ya ce da Hannah ta taso suje
zaure yana son ganinta yana da
magana da ita.
Hannah ta mike ta dauko ruwa
ta wanke hannayenta ta
yafa gyalenta tana biye dashi
suka fita zaure.
Tambayoyin da Bello madu ya
jerawa Hannah sun doshi goma
don son yaji meye ya sata kuka
ko
aurensa ne bata so amma dukka
da a'a Hannah take amsa
masa. Domin idan ta kuskura ta
baiyana abunda yake
ranta ta sake shiga uku tasan
Bello ba zai takura ya ce zai
aureta ba hakura zai yi idan ya
fasa aurenta wa zata aura kuma
tunda bata da maganin ciwon
da
yake damunta. Na san na rasa
Haisam, na rasa shi kuma har
abada na rasa soyayyarsa na
rasa farin cikin rayuwata,
meye ya rage mun a duniya
kuma? Banda jiran mutuwata.
Bello ya katsewa Hannah tunani
ya ce "To tunda na tambayeki
kince babu komai akwai
magana
guda da nake son muyi dake,
Hannah dan Allah kiyi hakuri ki
sake hakuri da duk yanda kika
tsinci
rayuwarki, abin da nake nufi shi
ne, watakila Hajir ta fada miki
ina da gida nawa na kaina,
yanzu ma a
ciki nake zaune nan za'a kaiki
bayan anyi bikinmu, to
kinsan halin Iyaye musamman
ma mata.
Mahaifiyata ta kekashe kasa tace
lallai-sai dai a kaiki cikin
gidanmu ma'ana gidan da take
zaune da kishiyarta wanda ba
karamar takura bace, daki ne
kwaya daya jal ga nata ga
wanda za'a kaiki. Kiyi hakuri ko
bayan
bikin zanci gaba da bata hakuri
akan ta yarda in mai da
ke gidana. Hannah ta sunkuyar
dakai kasa ta ce "Kawu
wannan ba wani abu bane da
zaka damu kankaba ka bi maganar
Mahaifiyarka domin abunda
babba ya hango yaro ko ya hau
bishiyar rimi bazai hango ba, ita
ta
haifeka ta fika sanin dalilin da
yasa ta ce ka zauna da matarka
a kusa da ita, Allah Ya bamu
zaman lafiya gaba dayanmu ni
da ita, ni da kai kuma na gode.
Wannan kalaman na Hannah ya
kwantarwa da Bello Madu
hankali don bai taba zaton
Hannah ba zata
damu ba idan taji tare da
surukai zata zauna amma sai
yaji ita take kokarin yi masa
nasiha, akan ya kwantar da
hankalinsa ya bi maganar
Mahaifiyarsa. Kuma
Hannah ita ce take yi masa
godiya. Daga karshe ya yiwa
Hannah sallama ya ce zai koma
wajen aiki sai nan da kwana
hudu zai dawo an turashi boda
dake
tsakanin Maigatari da Niger da
zarar ya dawo za'a kawo
lefe insha Allah. Hannah tayi
masa fatan dawowa lafiya
ya tafi ita kuma ta shiga gida. Ta
iske Hajir tana kwasar
tuwo, ta je kusa da ita ta jawo
kujera ta zauna. Hajir ta kalleta
ta ce "Amarya a gidan custom
Bello Madu kinsha kamshi,
amaryar nan da wata guda, wai
naga duk jikinki yayi sanyi ne
har koke-koke kike
yi?
Koda yake muma fa duk munyi
wannan don gabannin bikina
kurket na rame sai kuka ina
zaton auren wani tashin hankali
ne ashe babu abin da ya kaishi
kwanciyar hankali, ke kuwa
daga ke sai masoyinki ku biyu a
gida ku rakashe kowa kokarin
ya farantawa dan uwansa yake
yi. Ke gidanki na siminti ne
kewayayye ai
Bello Madu ya zuba sumunti a
gidansa tal a lailaye da simunti
kamar a birni. Mu da muke
gidan kasa ma muke jin dadin
rayuwarmu balle ke. Hannah ta
ce
"Kai Hajir ai da gidan sumunti
dana kasa duk daya ne yanzu
yake cemun Mahaifiyarsa ta
tubure lallai-lallai bata yarda ya
kaini gidansa ba sai dai in zauna
a gidansu.
Hajir ta zabura ta wurgar da
marar da take kwasar tuwo ta
mike tsaye ta rike haba da
hannu ta ce
"Hannah me kika ce kina nufin
yanzu cikin gidan su Bello za'a
kaiki? Lallai mun shiga uku mu
masu kai amarya ma balle ke da
za ki zauna da ita. Hannah ta
jawo hannun Hajir ta zaunar da
ita ta ce "Hajir zauna mana muyi
maganar daga zaune me yasa
kika ce mun shiga uku wani abu
ne? Hajir tayi ajiyar zuciya ta
koma ta zauna ta ce "Hannah
bazan boye miki ba a gaskiya
Innar Bello bata da hali saboda
duk garin nan babu wanda bai
san bala'in Inna Haule ba har
tafi Iya Abu matar Babanki da
kike bani labarinta don tun
maigidanta yana nan bai rasu
ba take azabtar da
kishiyarta Indo, wahalar duniyar
nan yau idan kika
je gidan Indo da *ya*yanta
tamkar bayi ne a gidan. Debo
ruwa a rafi ma ya ishe ki bayan
zuwa gona da
sassake, amma shi Bello me yasa
zai yi mana haka bayan
yasan halin Mahaifiyarsa ko da
yake ba laifinsa ba ne, don
idan ta saka musu kara basu isa
su tsallake ba musamman Bello
yana yi mata ladabi sosai fiye da
sauran kannensa, shi ne babba
a gidan. Ina jin bata so yayi nisa
da itane, gani take komai ya samu
yanzu ke zai dinga kaiwa,
kinsan ko albashinsa aka ce
kusan ita
yake dankawa gaba daya. Kafin
Hannah ta ce wani
abu Ahmad ne ya yi sallama ya
shigo suka amsa masa
gami da yi masa sannu da zuwa.
A murtike ya amsa sannan ya
juya ya kalli Hajir ya daka mata
tsawa ya ce "Ke Hajir ki iya bakin
ki
don me kike kokarin rikita
Hannah game da aurenta da
Bello Madu akanta aka fara zama
da surukai. Ya juya ya kalli
Hannah ya ce "To sai kin toshe
kunnuwanki shi aure dan
hakuri ne ki ji, kiki ji, ki gani kiki
gani, ladabi
da biyayya shine zai rabaki da
masifa da takurawar surukarki.
Kada ki yarda da *yan zuga
masu nuna miki kin hadu da
masifaffiyar suruka mutum ko
shaidan
ne yasan mai kyautata masa don
haka idan kika bi Inna Haule sau
da sau dole ta daga kafa. Bawai
na ce
Hajir tayi karya ba haka halaiyar
Inna Haule take amma
sai kinyi hakuri kin daure kin
mata biyayya zaki ga ashe duk
abunda ake fada miki ba haka
take bama.
Hannah ta sunkuyar da kai kasa
ta ce "To Kawu naji abunda ka
fadamin zanyi amfani dashi na
gode madallah. Ta mike ta shiga
daki Ahmad ya juya ya kalli Hajir
wacce ta cika tayi fushi taf
kamar zata fashe. Ya shafa
kumatunta ya ce "Ke kuma daga
magana maye abun yin fushin,
Hajir ta ce "Haba Ahmad me
kake nufi da ka ce kada Hannah
ta saurari *yan zuga, kana nufin
ni ce *yar zugar kenan zan
hanata yin aure ko? Ya ce "A'a
abunda naga
laifinki shine muddin kika sanar
mata da halin Innar Bello
Madu ai zata tsorata kuma zata
ji ta tsani auren ta tsani
surukarta daga nan zaman lafiya
babu kuma
ni Bello ne yafi bani tausayi har
cewa ya yi ko zai fasa auren
Hannah ne saboda yasan tabbas
zata hadu da halin Mahaifiyarsa
shi kuma a duniya babu abinda
yaki jini irin batawa Hannah don
yana sonta kamar yadda
yake son rayuwarsa. Mun kada
mun raya da Inna Haule ta
hakura ta bar Bello ya tare da
amaryarsa a
gidansa taki fur don wani uban
ashar ta soka min ashe
haushina take ji wai na dauki
*yata na bashi, ashe tana so ta
hada shi da wata shi ne yaki.
Sum-sum nayi
na fice daga gidan. Kuma wani
abun bakin cikin shi ne Bello
yayi-yayi ta yadda ya rushe
bangarensa yayi na siminti ya
zagaye da katanga ta ce bai isa
ba ana
kasar zai saka amaryar tasa. Sai
zana ya suyo yadan
zagaye dakin su kwaya daya jal.
Kuma abincinsu a hade
dana *yan gidan zasu dinga yi
Allah dai Ya kyauta muna
nan mun dukufa da addu'a Allah
Ya dora shi akanta ta hakura ta
barshi ya zauna a gidansa.
Hajir ta ce "Amin nima zan taya
Hannah da addu'a, amma caf
wannan suruka ta Hannah, ai ko
gidan bazan taba takawa
ba da sunan ziyara ni tun ina
yarinya daman tsoranta nake
ko gidan bana shiga Allah Ya
sani banasan masifa. Duk hirar
nan da suke yi kakaf a kunnen
Hannah wacce ke daki a zaune
tana jiyo su. Tayi ajiyar zuciya ta
girgiza
kai don tausayin kanta da kanta
ta ce a ranta "Haka
Allah Ya so yi dani haka zan kare
a kunci, wahala da bakin ciki na
rabu da wahalar Iya Abu na fada
wahalar
Inna Haule, Allah Kana sane da
ni, Kasan halin da nake ciki Kai
ne majibancin lamarina
La'ilaha'illa'a
nta subhanaka
inni kuntun minal zalimin.
Babana yayi
gaskiya da ya ce yasan babu
mijin da zan aura da zai rikeni
amana in ba Haisam ba. Baba
baka san
yadda muka yi da Haisam ba ka
mutu ka barni akan inje
in cewa Haisam ya zo ya aureni
ka bashi ni, Yaya Haisam ya auri
wacce yake so ya barni. Baba ka
barni a duniya baka san na rabu
da Haisam din bama. Ta rushe
da kuka mai tsanani. Ta koma ta
kwanta a tsakar dakin tana
tunanin rayuwar da suka yi da
Haisam shine farin cikinta a
makaranta baya so ko kuda ya
cijeta yana tattalinta wasa da
dariya kullum har ya zuwa ranar
rabuwarsu. Hannah tayi kuka
har ta gaji sannan ta mike don
zuwa ban daki tayi alwalar
magariba,
ashe ta dade dayi bata sani ba.
Kamar yadda Bello Madu ya ce
za'a kawo lefe da sauran
kudade na al'ada an kawowa
Hannah lefe
akwati uku kowacce a cike
danma Inna Haule duk ta
rarrage kayan amma duk da
haka masha Allah an
zuba mata kaya. Anan kauyen
sai zancen yawan kayan ake
yi, *yan uwan Hannah sai murna
ake amma banda Ahamad
domin ya tsorata da ganin
yawan lefen
nan yasan dole za'a zuba ido
aga me kuma za'a kai dakin
Hannah. A matsayinsa na dan
karamin Malamin makarantar
firamare mai daukar dan
karamin
albashi shi zai yiwa Hannah
gado, gara da kuma abincin
*yan biki gashi kuma a kurarren
lokaci aka saka ranar bikin.
Gashi duk danginsu shine wai
mai dama-dama duk a jikinsa
dangi suke nema. Yasan ko za'a
taimaka
masa da gudunmawa bai wuce
ayi masa fantekar alkaki da
nakiya ba sai *yan kwanukan
cin abinci wadanda suka
daddage ne zasu bashi setin
samira. Da cin bashi da komai
Ahmad ya hada kudin gado
lamba one da mudubinsa. Dan
kudin da Hajir take tarawa na
dinkin hular da take, ta bashi ya
hada da sauran *yan
gudunmawar da ya samu ya
sayi ledar daki da labule
shi kenan sai kwanukan rabon
abinci da samira seti hudu aka
hada aka jerawa Hannah a daki.
Bayan ansha biki an kai amarya
dakinta tsaf-tsaf daidai karfinsu
sai dai wani babban tashin
hankali Ahmad ya buga sama da
kasa ya rasa kudin siyawa
Hannah gara. Don haka ya ce
Hajir da wasu matan suje su
bawa Inna
Haule hakuri insha Allahu kafin
ta haihu za'a kawo mata gara
donhar ta fara habaici an kawo
amarya babu gara.
Kwanan Hannah uku cur tana
rusar kuka bayan an kaita gidan
miji. A ran na hudun ne Bello
Madu ya
shigo dakinta da jakar kayansa
shi ma ya kauro gidan daga can
gidansa. Da misalin karfe goma
na dare gari yayi shiru kowa
yayi bacci abinka da rayuwar
kauye amma a zaune a gefen
gado ya tarar da Hannah tayi
tagumi tana tunani ido yayi
mata jawur a kumbure, yayi
mata sallama ya shigo. Ta daga
kai da sauri ta dube shi sannan
ta amsa masa sallamar da yayi
mata. Ya shigo ya ajiye jakarsa a
gefen akwatinta yazo
kusa da ita ya zauna yana yi
mata murmushi da nuna
farin cikinsa a fili, ya dubi
kwayar idanuwanta yaga jawur
don tsananin kukan da tasha yi
ya ce "Hannah kukan
ne har ya zamar miki da
idanuwanki haka? Don
Allah ki daina kuka, Hannah ni
mai kaunarki ne bazan
cutar da ke ba, ta sake rushewa
da kuka yasa Hannu ya
jawota a jikinsa sai yaga tayi
sauri ta zabura ta mike tsaye.
Wannan zabura ta Hannah ta
bawa Bello mamaki kamar
wanda ya jona mata wuta, ya
mike yasa hannu zai rukota,
Hannah tayi sauri taja da baya
tana kokarin ta fice waje. Bello
ya ce "Ah har waje zaki fice to
na kyaleki zo ki zauna bazan
sake taba ki ba. Sannan Hannah
ta dawo tazo ta zauna a kasa
kan ledar dake shimfide a tsakar
dakin ta hada kai da gwiwa
tana
kuka tamkar ranta zai fita.
Wannan kuka na Hannah yana
tayarwa da Bello hankali ji yake
kamar tana soka masa wuka a
zuciyarsa idan Hannah tana
zubar da hawayen
nan. Ya nisa sannan ya ce.
Hannah kiyi hakuri dan Allah ki
daina kuka meke damun ki ne?
Nifa yanzu mijinki ne ki daina
guduna kuma kina kuka kina
tayarmin da hankali. Na ce kiyi
shiru kinki ki daina,
ko kina so inyi fushi dake Allah
Yayi fushi dake Mala'ikun
Allah su dinga la'antarki har sai
gari ya waye ne? Hannah
ta dago da sauri ta kalleshi ya ce
"Yaya kike kallona?
Gaskiya nake fada miki ai duk
macen da take gudun
mijinta Allah da Mala'ikunsa zasu
dinga la'antarta har sai gari ya
waye ko kin yadda ki halaka?
Hannah ta girgiza kai ta ce
"Bana so na halaka, ya ce "To in
bakyaso ki hallaka zo nan kusa
dani ki zauna muyi hira.
Hmm su bello madu sarkin wayo
To gafa Hannah a gidan Iya haule me zai faru!! Ku biyoni GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter18
Cikin shesshekar kuka Hannah ta ce "Kawu na
zalunci
kaina, na kuma zalunceka da ban fada maka
gaskiyar
abunda yake damuna ba. Kawu na kasance ina
cikin
wani hali na tsananin damuwa wanda har nake
tunanin
bazan iya auren kowa ba. To amma dole nasan
za'ayi
min aure shi yasa na hakura na amince na aureka
a
tunanina zan iya daurewa in zauna amma yanzu
bayan
da akayi auren ciwon da yake damuna ya dawo
min
danye bana jin zan iya zaman aure har in samu
aljarnar da kowacce mace take nema a karkashin
tafin
kafar mijinta ta hanyar biyayyar aure. Kawu kayi
hakuri
ka yafe ni dan Allah ka rufamin asiri. Ka
sauwakemin
mu zauna a haka ba tare da kowa ya sani ba,
saboda
sai in halaka idan muka zauna a haka da igiyar
aurenka. Bello ya bude baki yana kallon Hannah
can ya
taso yazo gabanta ya durkusa ya rike hannunta
cikin
siririyar murya mai dauke da tsananin dimaucewa
ya
ce "Hannah, fadamin ni Kawunki ne mai shirin
taimakonki ta kowacce hanya kada kiji tsoron
fadamin
ko mene ne. Ta janye hannunta a hankali ta
share
hawayenta ta ce "Idan baka manta ba a labarin
dana
baku a garinmu nace nayi makarantar sakandire
da
taimakon Allah da taimakon Yaya Haisam, son
Yaya
Haisam ne ya zame mun dafi a zuciyata wanda
dafin
nan zai iya zamar min ajalina. Kawu Bello ina son
Haisam harni kaina ina mamakin yadda akayi
zauciyata ta kamu da sonsa haka nayi addu'ar
don
Allah Ya goge mun, nayi azumin nayi kukan
kullum
akan Allah Ya yayemun amma kamar karamin
ake.
Daga karshe sai nake addu'ar Allah Ya dauki
raina da in
dauwama a haka amma ka ganni har yanzu a
haka na
rasa yadda zanyi. Ta rushe da kuka. Bello yayi
shiru
yana kallonta can ya nisa ya ce "Hannah me
yasa baza
kiyi addu'ar Allah Ya hadaki da Haisam ba kuyi
aure
kike addu'ar Allah Ya yaye miki sonsa ko kuma
Allah Ya
dauki ranki? Hannah ta goge hawaye ta ce
"Haisam
yayi aure a ranar da Mahaifina ya rasu "Bello ya
gyara
ya zauna a gaban Hannah ya lankwashe kafa don
jin
labarin wannan rikirkitaccen ala'amari na
Hannah.
Hannah bata boye masa ba ta bashi labarinta da
Haisam tun daga ranar da Babanta ya kaita
makaranta
har ranar da taje gidansu ta iske shi zai tafi
daurin
aurensa, daga karshe ta ce "Ashe Yaya Haisam
ba sona
yake ba taimako kawai yayi min ni kuma zuciyata
ta
kamu da tsantsar kaunarsa. Don haka ne a koda
yaushe nake addu'ar Allah Ya yayemun sonsa
bana
addu'ar Haisam yazo ya aureni. Bello Madu yayi
murmushin karfin hali ya ce "Haisam yana sonki
yana
kaunarki sosai fiye dani kaina da duk wani mai
sonki a
duniya. Akwai wata matsalar da tasa bai aureki
ba
Hannah.
Hannah cike da mamaki ta kurawa Bello ido ta ce
"Me
yasa kace haka, me ka gani da ka fadi haka?
Bello ya ce
"Saboda ke yarinya ce shi yasa baza ki fahimci
hakan
ba, kuma nasan irin yadda kike ji Hannah bawai
haka
ta taba faruwa akai na ba a'a ina kwatanto nima
rayuwata zata iya shiga irin wannan halin da kika
shiga
idan na rasa kine, saboda kece wacce na taba ji ina
so a
duniya. Ni na yadda na amince zan ci gaba da
zama
dake a haka a matsayinki na matata amma babu
zancen saki a tsakanina dake in Allah Ya yarda
sai dai
mutuwa ta raba mu saboda son da nake miki,
Hannah
da ace Haisam nacan yana jiranki baiyi aure ba
da zan
daukeki in kaiki wajensa in aura miki shi don kiyi
rayuwa cikin fari ciki, ni in dawo gida in zauna
ciwon
son da nake yi miki ya kashe ni na yadda in dai
na ceto
rayuwarki. Amma yanzu da yake Haisam yayi
aure kiyi
hakuri, a cikin kashi dari bisa dari na soyayyar da
kike
yiwa Haisam, ki daure ki bani kashi daya a cikin
dari
har karshen rayuwarmu ta aure na gode. Hannah
ki
daure ki ci gaba da zama dani a haka kada ki
barni ni
dake muyi biyu babu, kin rasa Haisam ni kuma in
rasa
ki. Yasa hannu ya jawota jikinsa zai rungumeta
tayi
sauri ta mike ta juya masa baya. Ya tashi a
sanyaye
yaje ya rufe kofa ya datse da mukulli. Yayin da
Hannah
taji wannan rana tamkar ranar da Mahaifinta ya
rasu ta
kuma rasa Haisam yau gata a daki daya zata
kwanta
gado daya da wani a matsayin mijinta ba Haisam
ba.
Hawaye yaci gaba da tsiyayo mata daga
idanuwanta.
Bello yazo ya rungumeta ta bayanta yana mai
sunbatar
kunnuwanta da gefen kumatunta cikin
sanyayyiyar
murya Hannah ta ce "A matsayinka na mijina
akan
babu yadda zanyi ka sami GANGAR JIKINA amma
ruhi,
zuciyata tana wajen Haisam. Bai iya bata wannan
amsar ba cik ya dauketa ya dorata a tsakiyar
gado.
Hannah ta shide tama fita haiyacinta saboda
tsananin
bakin ciki yau ga wani daban zai fara saninta *ya
mace
kafin Haisam, wannan bakin cikin ne yayi mata
yawa
yasa ta fita hayyacinta tama iya cewa suma tayi
amma
gogan naka baima lura ba ji yake yau tamkar an
masa
albishir da gidan aljannah gashi ya auri Hannah
harma
ta mallaka masa GANGAR JIKINTA.
A ranar da Hannah ta cika sati guda ta fara sanin
halin
Uwar mijinta ashe da kara take yi mata. Da
sassafe ko
tashi daga bacci basu yi ba Inna Haule tayi dirar
mikiya
a bakin kofar dakinsu tana bugun kofar da karfi
tana
fadin a tashi haka baccin ya isa duk inda sati
guda yayi
angama cin amarci bakunta ta kare kin zama
*yar gida
fito ki dora dumame. Indo zata je rafi debo ruwa.
Furgirgit Hannah ta mike ta diro daga kan gado,
ta bude
kofa ta fito. Ta durkusa har kasa ta gaishe da
Inna
Haule. A yatsune ta amsa ta ce "To a tafi wajen
murhu
a dora dumame ga dawa da gero can idan kuka
karya
kumallo ke da Indo ku surfa. Bello wanda yaji
tamkar
yayi ihu saboda takaici yasan Hannah kuma ta
shiga
uku ta lalace kamar yadda amaryar Babansa Indo
take
dandana wahala kullum kamar baiwa. Ya tashi
zaune
ya rike kai tausayin Hannah yana ratsa zuciyarsa
da
tunano ina zai samo mata mafita kafin ta zama
baiwa.
To amma babu wata mafita tunda har yau har
wayewar
gobe Inna Haule ta ki amince masa ya koma
gidansa
shi da matarsa. Da ya isheta ma da maganar sai
ta ce
duk ranar daya sake rokonta wannan bukata tasa
Allah
Ya isa kuma zata tsine masa, don haka Bello yaja
bakinsa yayi gum.
Haka Hannah ta kasance tana yin iya kokarinta
na
ganin ta farantawa Uwar mijinta tana binta sau
da kafa
kafin ta saka ta aiki tuni ma tayi mata, amma a
banza
Inna Haule bata gani. A ko da yaushe zagin
Hannah
take tana cewa auren da ba gara ma ai bai cika
aure
ba. Wai Hannah ta mallake mata da don da sai
yayi sati
biyu, uku bai zo garin ba daga wajen aikinsa
amma
yanzu baya sati guda. Zantuttuka barkatai
marasa
ma'ana dai na nuna tsana tsagwaronta. To
wannan
al'amari yasa Hannah ta sake fitar da rai daga
samun
zaman lafiya a rayuwarta. Inna Haule halinta
daya da
Iya Abu koma tafi Iya Abu, ko Uwarka ka yanka
musu
ka dafa ka basu baza su gode maka ba. Sai dai
kawai
idan abun ya isheta ta shiga daki tayi kuka ta
gaji. Idan
Bello Madu ya dawo ya ganta a wannan hali sai
ya
shiga lallashinta yana bata hakurin nan nasa,
babu
abinda yake karawa Hannah banda takaici. Abu
daya
ya gano logarta in har yana so tayi dariya a duk
Bakin
bacin ran da take, shine ya ce mata Haisam.
Haka yake
sakata a gaba ya tilasta mata ya ce dole sai ta
bashi
labarin Haisam tun tana jin kunya da nauyinsa
har ta
saki jiki tayi ta bashi labarin Haisam na dariya
suyi
dariya na tausayi ya tausaya mata, na tambaya
ya
tambayeta. Da haka Bello ya fara samun shiga a
wajen
Hannah. A koda yaushe Hannah na kirga
kwanakin
yaushe Bello zai dawo daga wajen aiki saboda
dashi ne
kawai take hira mai dadi har tayi dariya hirar ita
ce
hirar Haisam.
Hannah da Indo ne suke surfe a yau, Inna Haule
ta fita
unguwa shine ma suka samu suna *yar hira. Duk
da
Indo ta girmewa Hannah amma duk da haka bata
fi
shekara ashirin da shida ba a matsayin suruka
take a
wajen Hannah tunda matar Baban mijinta ce.
Amma
dole tasa suka zama kawaye. Hannah na bakace
dusar.
Indo tana tikar dawa a turmi, Indo ta tsagaita da
dakan
ta ce "Hannah sai dai hakuri ni harna saba da
wannan
bauta haka Allah Ya rubuto mana rayuwarmu.
Hannah
tayi ajiyar zuciya ta ce "Allah Yana barin
bawansa a
halinda Ya so Ya ganshi. Amma duk abubuwan
da Inna
ke yi mun baya damuna irin duk abunda muke yi
mata
batagani, dubi fa irin aikin da muke yi kamar
zamu
mutu yanzu idan tazo cewa zata yi munyi ha'inci
bata
surfu ba. Ga zagin da take yimin akan gara ni na
rasa
yadda zanyi da rayuwata wallahi. Indo ta ajiye
tabarya
ta ce "Ai wai ke kina nufin duk abinda ake baki
sani ba
a gidan nan yau? Hannah ta ajiye faifan dake
hannunta
ta tattara hankalinta gaba daya a wajen Indo
tana jiran
taji me yake faruwa. Indo ta ce "Ko da yake kin
tafi
debo ruwa dazu da sassafe Inna Haule tasa na
shiga
dakinki na miko mata akwatinan aurenki guda
biyu
wadanda baki dinka kayan ciki ba tasa almajiri ya
daukar mata wai zata kai wani gida ajiya tunda
ba'ayi
miki gara ba suma baza ki daura lefansu ba.
Daman wata uku ta daukar miki a kawo gara
gashi
yanzu kin shiga wata na hudu da aure. Don haka
da
zarar Bello ya dawo zata sa ya sake ki, lefan
kuma ta
kaiwa wata yarinyar a daura masa aure da wacce
zata
kawo mata gara. Kuma kinsan Bello babu yadda
zaiyi
idan tasa shi a gaba ta ce ya sake ki. Hawaye ne
sharrr
yake zuba daga idanuwan Hannah ta mike da
gudu ta
shiga daki ta tarar wayam an kwashe akwatina
sai
kwaya daya *yar karamar kaya kala uku ne ta
dunka a
lefen, su suka rage sai sauran tsofaffin kayanta
nada
ga sunan a zube a kasa an watsar mata. Sai ta
kwanta
a kan gado ta fara rusar kuka, Hannah ta kware
wajen
iya kuka dan ko gasar masu iya kuka aka je ta
duniya
ina ganin ita zata zo ta daya. Can ba dadewa
Inna
Haule ta dawo ta tarar da Indo ce kadai take
aikin
abincin rana ta ce "Ina Hannah? Indo ta ce
"Ciwon ciki
take tana daki. Ta leka ta tarar da Hannah
sharkaf cikin
kuka sai ta ce "Babu wani ciwan ciki ba ciwan
ciki ba ko
ciwan nakuda kike sai kin bar gidan nan bazan
iya ba
harkar talauci anyi biki ko gara babu lefen dana
dauke
ne shine yasaki bakin ciki ya kwantar dake. Haka
Hannah
ta yini shiru a kwance babu ci babu sha sai kuka,
Allah
cikin ikonsa sai ya jeho mata Bello da yamma
kwanakinsa biyu jal da tafiya ba zato ba
tsammani
Hannah taji sallamarsa ya shigo, furgigit tayi ta
tashi
zaune kallo daya yayi mata yasan akwai abunda
aka yi
mata har ta sha kuka. Yaje da sauri ya zauna a
kusa da
ita ya jawota jikinsa ya tambayeta meke damunta
take
kuka. Ta amsa masa da ba komai, ya ce yasan
dole da
wani abu karta boye masa ta fada masa gaskiya.
Sai ta
ce cikinta ne yake ciwo, yayi shiru shi dai ya jita
ne
kawai amma bai gamsu ba. Sai can da aka jima
hankalinsa yakai wajen akwatina yaga basa nan
ya ce
"Hannah ina akwatinanki suke? Tayi shiru can ta
ce
"Inna ta kwashe ta kai ajiya wai tunda ba'ayimin
gara
ba wata zata kaiwa ta aura maka ita, ni ka sake
ni. Sai
ta rushe da kuka. Bello ya cije baki don tsananin
bakin
ciki yayi shiru ya kasa magana sai yasa hannu
yana
goge mata hawaye ya nisa ya ce "Daina kuka
kece baki
sani ba na bawa Ahmad kudin da zai saya miki
gara
kakaf, yanzu ma cikon kudin da zai karasa
sayayyar na
kawo masa. Daman zan koma wajen aiki tunda
ina da
aikin dare. Daman Inna bata ganni ba ance tana
makwabta bari inyi sauri in tafi baza ta san nazo
garin
bama balle tayi min maganar sai in cewa Ahmed
suyi
kokari su kawo garar gobe kinga an kashe
bakinta kafin
in dawo. Ya rungume Hannah ya sumbaci
kumatunta
ya ce "Bazan sake ki ba Hannah ina sonki da yawa ki
kwantar da hankalinki kinji ko? Sannan ya fice
yana
sauri ya tafi. Hannah ta bishi da kallo yayin da
zuciyarta ke ce mata "Ba Haisam kadai ba Bello
Madu
ma mai sonki ne Hannah ki kaunace shi.
Haka kuwa akayi washe gari da misalin karfe uku
na
yamma sai Hannah taji buda an doso cikin gidan
kamar a mafarki taga kartan maza suna ta ajiye
buhunhuna a kofar dakin Innah Haule. Mata suna
ta
shigowa da fantekun alkaki, nakiya dibulan da dai
sauransu. Wannan al'amari ya bawa Inna Haule
mamaki, nauyi da kunya saboda sunyi mata bazata
duk tabi gari tana fadin ba'ayiwa Hannah gara ba
kuma
ba zasu iya yi ba kwatsam sai taga gara wacce
ko
*ya*yan attajiran garin ba'a taba yi musu gara
mai
yawan buhunhuna haka ba.
Hmm bello madu dai ya bude wuta wato shida hanne mutu ka raba me zai faru? Ku biyoni!!!!!GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter19
Nan dai Inna Haule ta hau borin kunya tana cewa "Ashe kuna tafe ku ka ki sanar min nima in gayyato *yan uwana suzo su tayani karbar irin wannan abun alhairi sannunku da zuwa ku shigo daki mana ya zaku zauna a waje. Hannah debo tabarmarki dana Indo a shimfidawa baki. Ai da kun sanarmin zaku zo da nasa anyi muku girke-girke da soye-soye irin wannan abun arziki haka. *Yan uwan Hannah suka ce "Babu komai ai ba zama muka zo yi ba mun kawo gara gata nan, zamu koma don *yar mu ta sami salama a zamanta na aure da mijinta. Suka yaba mata ba dadi.
Washe gari da sassafe Inna Haule taje ta debowa Hannah akwatinanta ta kawo mata amma an kwashee wasu kayan da yawa babu. Ta kuma gargadi Hannah kada ta sake ta fadawa danginta ko mijinta tayi shiru da bakinta. Da Bello Madu ya dawo faran-faran Inna Haule ta kira shi ta nuna masa gara har tana cewa "Allah Sarki ashe ba karamin shiri suke yi ba shi yasa basu kawo da wuri ba irin wannan yawan gara sai ka ce *yar Sarkin noma ka auro. Bello yayi dariya ya ce "Allah Ya sanya alheri ya bamu zaman lafiya. Ya nufi dakin Hannah, bayan tayi masa sannu da zuwa ta kawo masa abinci da ruwa ya sha, sai ya janyo akwatinan ya bude kamar yadda ya zarga tabbas Mahaifiyarsa zata kwashe wasu kayan, haka kuwa ya gani ta kwashe kaya da yawa. Ya waiga ya Kalli Hannah sai ta sunkuyar da kanta kasa bata ce masa komai ba. Ya ce Hannah an kwashe miki lefenki ko? Kiyi hakuri zan suyo miki wasu insha Allah idan muka yi albashi wani watan. Hannah ta dago cikin ladabi da tattausar murya ta ce "Ni na yafe duniya da lahira ba sai ka biyani ba, wahalar zata yi maka yawa. Kawu Bello babu abinda zance maka sai godiya da wannan garar da ka yimin Allah Ya saka da alheri domin ka kwatar min *yanci na tun daga ranar da aka kawo Inna bata sake yimin gori ba. Yanzu zanyi zaman farin ciki a gidan aurena. Yayi murmushi ya ce "Farin cikinki shi ne nawa Hannah, Allah Ya kara sanya ki a farin ciki fiye dana yanzu. Ta ce "Amin na gode.
Karshen wata nayi Bello ya dau albashi sai da ya sissiyawa Hannah kayayyakinta da Mahaifiyarsa ta kwashe, cikin dare ya kawowa Hannah a boye ya ce ai hakkinta ne dole ya biya ta. Hannah tayi godiya ta karba. Haka Hannah da Bello suka kasance yana kyautata mata a boye komai ya gani na sakawa kona marmari sai ya suyo mata da daddare ya shigo mata da shi ya bata a boye ba tare da ya bari Mahaifiyarsa ta gani ba. Bello yana kara son Hannah saboda ladabinta hankali da nutsuwa da Uwa Uba tsananin hakurinta da tawakkali. Ita kuwa Hannah har yau har wayewar gobe ta kasa masanya gurbin Haisam ta mayar da Bello amma mafarkin Haisam take, idan tunani take Haisam kawai take hangowa a zuciyarta. Tana kokarin mayar da soyayyar da take yiwa Haisam kan Bello saboda ita ma ta saka masa soyayyar, saboda irin kyautata mata da yake amma abu ya faskara haka dai take dagewa tana nunawa Bello tana sonsa wanda a zuciyarta ba haka ba ne. Wasu lokuta da yawa idan suka tashi da safe, Bello yakan ce mata yaya Haisam? Don naji jiya kina kiransa a mafarki. Hakika Hannah duk sanda ta kwanta mafarkin Haisam take yi ashe har ambatonsa take a fili. Saboda tsananin son da Bello yake yi mata ya yarda ya amince kuma zai zauna da ita a haka. Bai taba nuna mata bacin ransa ba, ita kuwa Hannah sai taji tausayinsa ya kamata nauyi da kunyarsa ta lullubeta. Amma yaya zata yi tunda
GANGAR JIKINTA YA AURA zuciyarta na wajen Haisam.
Matsalar gara ta wuce tsakaninta da surukarta sai kuma matsalar da Inna Haule ta dauko ta dorawa Hannah ita ce har yanzu Hannah ko batan wata bata yi ba balle ta samu ciki. Fada da gori a wajen Inna Haule babu dare babu rana. Bello yayi kokarin ya wayar mata da kai akan cewa ba laifin Hannah bane ciki Allah ne ke badawa amma abu ya ci tura Inna Haule taki saurarawa Hannah cewa take ga sa'annin aurenta nan dukka ciki garesu wata bakwai-bakwai tunda yanzu watan Hannah bakwai da aure.
Yau Hannah tun karfe biyun dare take kai kawo a tsakar gida bacci ya gagari idanuwanta. Duk bude idon da Bello zaiyi sai yaga Hannah tana fita ko tana shigowa cikin dakin kamar a mafarki yake ganinta. Can yaji ana kiraye-kirayen sallar asuba tayi. Yasa hannu ya laluba gefensa yaji Hannah bata nan. Yayi firgigit ya tashi ya fito tsakar gida ya hango Hannah a gaban murhu tana hura wuta. Ya karasa inda take ya ce "Hannah yau lafiyarki kalau kuwa tun dare kike shige da fice kinki ki kwanta, yanzu da asubar nan wutar me kike hurawa? Hannah ta danyi murmushi ta ce "Kawu ka manta yau da duku-duku oganka ya ce zai aiko da mota za kuje Agadas shine nake dora maka ruwan wanka naji yau garin da sanyi-sanyi. Yayi murmushi ya ce "Ai jinsa nayi kawai, meye abun turo mota da duku-duku sai ka ce zamu bar kasar, Hannah ta ce "Agadas ai da nisa shi yasa, kuma watakila ba kwana za kuyi ba ko? Ya ce "Gaskiya Agadas da nisa ba kuma cikin garin zamu shiga ba Local Government din Agadas din zamu Aderbisanat local government zamu je ina ganin wajen 540km ne kuma bana jin zamu kwana ziyarar aiki zai kai can mu kuma yan rakiya ne. Hannah ta ce "Allah Ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya. Ina jin kiran sallah assalatu kafin ruwan yayi zafi ga buta ka fara yin sallah. Ta mika masa buta ta durkusa har kasa, Bello ya tsaya yana kallonta kawai saboda wata tsantsar soyayyarta ce take kara sarke masa zuciya. Musamman wannan kulawa da ladabi da Hannah take yi masa, ya karbi butar ya shiga ban daki, kafin ya idar da sallar Hannah ta hada masa ruwan wanka takai masa ban daki ta zo ta durkusa a gabansa har sai da ya idar ta ce masa ta kai masa ruwan wanka. Ya tashi ya shiga wanka, kafin ya fito ta debo masa wankakkun kayansa data wanke ta goge masa ta dora a kan gado ta goge masa takalmin da zaisa kamar yadda ta saba yi masa kullum.
Bayan ya kammala yana goge-gogensa da *yan shafe-shafe sai ya dauko kayan da Hannah ta fitar masa ya saka. Ta zo tana balle masa maballin wuyan rigarsa, yayi murmushi ya ce "Hannah na gode da irin wannan hidima da kulawa da kike nunamin wannan yasa nake kara sonki dari bisa dari, idan akwai soyayyar da tafi dari bisa dari ina miki Hannah sai dai anya kuwa na sami kwaya dayan nan kacal da nake so a sammin a cikin darin da ake yiwa Haisam? Cikin kunya Hannah ta ce "Haba daya kacal ai kafi guda daya. Ya ce "A'a Hannah zancen gaskiya muke, nawa aka karamin? Tayi dariya ta ce "Kawu ka wuce goma ma zaka kai sha biyar. Su duka suka tuntsire da dariya. Ya ce "To tunda a wata bakwai na sami goma sha biyar nan da shekara bakwai zan iya tadda Haisam. Suka sake tuntsirewa da dariya. Muryar Innah Haule ce ta katse musu dariyar da suke yi tana bakin kofar dakinsu tana cewa "Tun dazu magana nake muku baku jini ba kun shige daki kuna tuntsira dariya da duku-dukun safiyar nan to motar ofishinku ce ta zo suna ta kwankwasa gida. Daman Hannah abunda kika sani kenan ki shiga daki da miji kina dariya aikin kenan ciki fal kashi, babu gurbin kwanciyar da sai gurbin tarin kashi. Hannah tayi kasake jikinta yayi sanyi fara'ar da take ta koma ciki ranta ya baci domin da ana siyar da ciki da ta suyo, haka kuma da a wani waje ake nemoshi da taje ta nemo duk wahala koda kuwa zata mutu ne. Ko ta huta da wannan zagi da gorin da ake yi mata. Bello yayi ajiyar zuciya ya ce "Inna gani nan zuwa shiryawa nake. Ta wuce ta tafi tana tsaki tana cewa "Kaje ka dawo dai daga tafiyar kazo mu zauna muyi maganar
saboda bazai yu ba, in zuba muku ido haka kawai aure yau wata bakwai kenan babu ciki ba alamarsa kaina da kafata turawa yarinya abinci nake sai dai ta ci tayi kashi kawai. Ai ba dan tazo ta cika mana shadda muka aurota ba muma muna so muga dan jariri a gidanmu. Tunda ta shanye ka ta asurce ka baka ganin laifinta to ni bata asurce ni ba dole ma ka sake ta ka auro mai haihuwa don daki daya garemu a gidan nan. Har Inna Haule tayi nisa ta juyo ta dawo ta tsaya a kofar dakin su Hannah ta ce "Hannah kiyi ki fito daga dakin nan yau duk ke zaki yi aikin gidan nan shara wanke-wanke surfe da girki ki fara debo ruwa tukunna idan kin cika randunan gidan nan kakaf sai ki fara aikin gida da yamma kuma kije gona ki tsinko wake da gyada dan sun nuna. Yau wacce kuke aikin tare Indo aikenta zanyi garin magarya wajen kawata. Tunda ba ciki gareki ba ba goyo ba ai wannan aikin bazai gagareki ba, sai dai idan kinji kashi kiyi a gonar, tunda cikinki sai kashi babu haihuwa, kinga kuwa kashin naki ya zamar mana taki a gonar kinga kin taimaka kema. Bello Madu ya fusata baisan sanda ya ce "Haba Inna ki daina yiwa Hannah gorin haihuwa ba laifinta ba ne, rashin haihuwa Allah ne Yake bayarwa. Innah har yanzu daman Hannah ce take dauko ruwa a rafi ina almajiran dana dauko aiki nace zan dinga biyansu. Ita taji da aikin gidan su kuma almajiran suje gonar. Hannah tasa hannu ta toshe masa baki ta ce "Yi shiru karka sa taji haushina, Mahaifiyarka ce babu komai duk zanyi aikin.
Inna Haule ta rike baki ta ce "Inye dannan ka fara fada in fada dani akan matarka lallai abun babba ne, jeka ka dawo ka sameni don wallahi ina ganin zamanka ya kare da wannan yarinyar mai kama da tumatur ina ganin rabaka take so tayi da kowa a duniya har dani dana haifeka. Ba'a haiyacinka kake ba na sani bayinka bane. Ta tafi tana surutanta dai barkatai. Hawaye yana zuba shar daga idon Hannah, Bello yasa hannu ya goge mata zuciyarsa cike da tsananin tausayinta amma yafi jin tausayi kansa da kansa, saboda zaifi Hannah shiga wani hali idan Mahaifiyarsa tasa ya saketa don shine yafi sonta fiye da yadda take sonsa idan ya rabu da Hannah ya rabu da farin cikin rayuwarsa.
Kalma daya ce yasan idan ya fadawa Hannah duk irin bacin ran da take zata yi dariya idan ya ambaci sunan Haisam, yayi dan murmushi ya kalleta ya ce "Hannah dama a ce a yanzu haka kina da ciki ki haifamun da namiji in saka masa suna Haisam. Hannah ta dago ta dubeshi idanuwanta a cike suke da hawaye sunyi jawur don kuka amma saida murmushi ya subuce mata a take taji zuciyarta ta fara dan hucewa daga tsananin tafasar da take yi saboda kunar maganganun da Inna Haule ta fada mata. Hannah ta ji wani dan sanyi a ranta wani abu ya dazu a zuciyarta da Bello ya ce dama a ce tana da ciki ta haifi da namiji ya saka masa suna Haisam taji dama ace hakan ta faru . Amma data tuna yanzu ma haka al'ada take don haka zancen ciki ma babu shi, sai ta sake rushewa da kuka. Bello ya jawota ya rungumeta a kirjinsa yana shafa lallausan gashinta ya ce "Hannan lallai yau ranki ya baci sosai har in kira miki Haisam amma kici gaba da kuka kiyi hakuri ki yafewa Innata muci gaba da yi mata addu'a Allah Yasa ta gane gaskiya Allah Ya cusa mata soyayyarki a ranta. Hannah tayi ajiyar zuciya ta ce "Amin, amma ka tayani addu'a Allah Ya bani ciki kafin karshen watan nan ina ganin haka shi zai saka soyayyata a zuciyar Inna. Bello ya ce "Amin ya Allah, zan dukufa da addu'a kema kiyi Allah Ya amsa mana. Ya goge mata hawayen idanuwanta ya sumbaci kumatunta ya ce "Haisam sunan danmu fa. Hannah ta kyalkyale da dariya ta rufe ido sai taji wani farin ciki ya lullubeta. Ta tsuguna ta jawo takalminsa ta fara saka masa a kafa tana sake goge masa da tsumma. Ta feshe masa jikinsa da turare ta ce "Kawu Allah Ya kiyaye hanya ku je lafiya ku dawo lafiya. Ya ce "Amin Hannah Allah Yasa na zo na sameki lafiya cikin farin ciki. Yana tafiya yana waiwayan Hannah, itama ta fito har bakin kofar dakin ta tsaya tana daga masa hannu har ya shiga dakin Mahaifiyarsa sannan Hannah ta koma daki.
A zaune a kofar gado Bello ya iske Mahaifiyarsa tana tunani tana gyada kai ya durkusa ya gaisheta ta amsa a fusace ta fara masa fada ta ce "To dan nan abunda nake so da kai shine kada ka sake ka yimin musu akan duk hukuncin da na yanke akanka ina nemar maka aure a gidan dagacin garin nan *yar Sarauta ka dace ka aura tunda ka makalewa Hannah baza ka iya sakinta ba to ta zauna anan gidan tare dani ita kuwa waccan idan anyi auren sai a kaita gidan ka. Bello ya daga kai ya kalleta zauciyarsa cike da bakin ciki. Gidan da yasha magiya ta yarda akai Hannah taki yau gata da bakinta tana cewa yayi aure ya kai matarsa can amma bada Hannah ba. To ashe Hannah din ta tsana kawai. Ya nisa ya ce "Inna me zai hana mu tare mu duka da amaryar da Hannah duk in hadasu acan din. Ta girgiza kai ta ce "Na ce maka karka yimin musu ko? Haka naga dama, tashi kaje ka dawo din mu karasa maganar amma idan ka matsa akan sai ka mayar da Hannah gidanka zaka sa ince sai ka sake ta don wallah Hannah baza ta tare a wancan gidan ba sai dai idan bani na haifeka ba. Ko bayan raina ka kaita can Allah Ya isa. Bello ya rike kai don takaici can ya ce "Naji Inna na gode, dan Allah ki yafe min duk abin da nayi miki, idan na bata miki rai a rayuwata gaba daya. Ta yi dariya ta ce "Babu abinda ka taba yimin wallahi ko musun ma daka tarka kake mun bayin kanka bane ta shanye ka ne, na yafe maka Allah Yayi maka albarka. Bello ya mike ya fita hawaye ne shar yake fita daga idanuwansa. Yana fitowa yaga Hannah tana jika gero. Tayi sharkaf da hawaye daga gani ta gama jin duk maganganun da suke yi. Kallo daya yayi mata yaji hawaye ya sake kece masa. Ya zo ya wuce ta gabanta ya ce "Hannah kiyi hakuri, ki sake yin hakuri, Allah Yana tare da mai hakuri. Ta bishi da kallo tana hawaye yana waiwayenta yana hawaye har ya fice. Tayi shiru tana sauraren karar tafiyar motarsu har suka yi nisa ta daina jin karar motar. Ta rushe da kuka tana cewa a ranta. A bakin ciki ashe zan dauwama? Yanzu aure Inna zata sa Kawu Bello zaiyo ya tare da amaryarsa a gidansa ni abarni anan, me yasa Inna ta tsaneni? Me nayi mata ta tsane ni? Me yasa kowa ya tsane ni a duniyar nan? Ubangijina yana sane dani, Allah Ka san halin da nake ciki, Allah Ka fitar dani, Allah Kai ne abin godiya.
Bayan fitar Bello Madu da kamar awa guda. A lokacin Hannah tana surfa gero, Inna Haule tana tsakar gida tana cin dumamen tuwo, Indo kuwa daga wanka ta fito zata shirya ta tafi Magarya inda Inna Haule zata aiketa. Suka ji mota turus ta tsaya a kofar gidansu. Wani ma'aikaci ne mai sanye da kayan *yan sanda yayi sallama ya shigo ba tare da ya gaishe da su ba. Ya ce "Nan ne gidan su custom Bello Madu ko? Inna Haule ta tsaya da cin tuwonta ta ce "Nan ne amma baya nan waye yake nemansa? Ya ce "Ina zuwa. Ya fice, gaban Hannah ya dau faduwa daf-daf daman tun daren jiya ta kasa bacci sai faduwar gaba take. Ta jingine tabaryar da take surfe ta tsaya. Kawai ji suka yi ana cewa "Ku kama da karfi wajen kafadar zaku rike. Inna Haule ta zabura ta mike da gudu ta leko, Hannah ma ta biyota da sauri idanuwansu suka gane musu wannan gagarumin tashin hankali. Gawar Bello Madu ce ake shigowa da ita. Allah Yayi masa rasuwa a sanadiyyar hatsarin motar daya ritsa da su yanzu-yanzun nan suna hawa hanyarsu ta tafiya Agadas wata babbar mota ce ta gwara musu suka kutsa ta tsakiyar motar cikin ikon Allah Bello ne kawai ya rasu, sauran sun sami munanan raunika suna asibiti. Take Hannah ta fadi ta suma, yayin da Inna Haule take neman tube kayan jikinta don gigicewa, sai da aka rirriketa. Kafin ka ce kwabo gidan ya cika yayi makil da *yan Uwa da makwabta maza da mata.
An yi masa wanka, an suturtashi an kaishi an binne kamar yadda Shari'ar Musulunci ta tanada. Bello ya tafi ya bar rikicin gidansa kuma shi tasa ta kare a duniya, domin rikicin duniya da mai rai ake yi duk wani rai sai ya dandana mutuwa, Allah Ya sa mu cika da imani. Hannah ta yiwa Bello addu'a har yawun bakinta ya kame idan ta gaji da addu'a ta rushe da kuka tayi ta huta haka dai har akayi sadakar bakwai *yan zaman makoki suka watse aka bar *yan gida. Yayin da barci yake gagarar idanuwansu, kamar yadda Inna Haule take kuka cikin dare haka Hannah ma sai ta laluba kusa da ita taji ita kadai babu Bello sai ta tashi tayi ta kuka har ta godewa Allah. Kaico Hannah ta rasa kowa a duniya.
Hannah bata shiga wata matsala ba ta bangaren ci ko sha ko aikin gida ba har ta fita daga takabarta. Sai bayan ta fita daga takaba an fara zancen rabon gado sannan Inna Haule ta daka tsalle ta dire ta ce babu abunda za'a bawa Hannah na gadon danta tunda Hannah ba haihuwa tayi ba da Bello sai dai ta hada *yan komatsanta ta bar musu gida. Kawu Ahmad yaji haushi sosai ya kuma lashi takobin ko sama da kasa zata hade sai ya kwatarwa *yarsa Hannah hakkinta na tumulin takaba shari'a shi da Inna Haule har kotin koli idan bata bari an raba gadon nan da Hannah ba. Ya ce kuma babu inda Hannah zata je gidan zata zauna saboda Bello yana da gado a gidan Ubansa. Inna Haule kuma ta ce ita kuwa baza ta bayar da dukiyar Bello ba sai dai su zuba.
Makudan kudi kuwa aka kawo daga wajen aikin su Bello, gashi da filaye da wannan tafkeken gidan nan daya sha sumunti da bulo. Inna Haule kuwa ta ce duk nata ne banda Hannah ko sisi baza ta bata ba tunda ko kwai bata saka a gidan ba. Tashin hankali ya tabbata a zuciyar Hannah ta rasa yadda zata yi da rayuwarta da Kawunta zai hakura ya bar Inna Haule ta rike dukiyar Bello dukka ba sai an raba da ita ba. Saboda duniyar nawa take wanda ya tara ma ya tafi ya barta kowa ma mutuwa zai yi. Duk wani hango jin dadin rayuwar duniya ya goge a zuciyar Hannah babu abunda take bege sai mutuwa tazo ta dauketa ta tafi ta huta itama. Daga gidan Kawu Ahamad ake aiko mata da abincin dare da rana. Tafi tafiya suma wata rana basa aiko mata don yau da gobe sai Allah. Hannah ta fara fitar da zannuwan daurawarta da kwanukanta tana siyarwa sannan ta ci abinci.
Hmm hanne na ganin jarabawa
Mai zai faru!!!? Ku biyoni GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 20
Wata rana da yamma Hannah da
Indo sun je rafi
sun
debo ruwa suna tafe suna hira
sai suka ji Hassan
me
yekuwa yana sanarwa yana
cewa "Yekuwa jama'a ga
wata sanarwa, mai girma
dagacin garin nan ya ce
a sanar muku, mata wadanda
mazansu suka rasu
suka barsu da suzo fadarsa yanzun
nan. Ma'aikata daga
Nigeria sunzo musu da tallafin
taimako. Gwamnatin
jihar Kano a Nigeria ta aiko da
taimakon kudi za a
raba musu jari domin su rike
kansu da marayun *ya*yansu.
Amma kada wata ta kuskura
taje idan ba mijinta
bane ya mutu, sai wacce mijinta
ya mutu. Indo ta
zunguri Hannah ta ce "Hannah
muje wajen taron nan ko Allah
zai sa mu dace. Hannah ta rike
baki ta ce "Babu ruwanmu
yanzu idan muka je ai mun
shiga uku a
wajen Inna cewa zata yi munje
mun tona musu asiri ci
muka rasa ko sha. Indo ta ce "To
shike nan amma idan
muka je mu tambaye ta ko zata
yadda. A hanya suka
dinga haduwa da mata
wadanda mazansu suka rasu
suna ta tafiya gidan dagaci don
karbar wannan tallafi
mai tsoka. Kowacce taga su
Hannah sai ta ce "Au,
baza ku taho fada ku karbi
wannan tallafi ba daga Nigeria
fa baki suka zo. Indo ta ce
"Gaskiya Hannah in baza ki ba ni
zanje saboda idan muka
kuskura muka je gida
Inna Haule baza ta barmu ba,
amma idan mun riga
munje mun karbo babu
yadda zata yi damu fada ne dai
da zagi ya zama jiki. Hannah ta
ce "To mu shiga
gidan Adama mu ajiye ruwan
muje din daman gudun
fadan Inna nake, to ko babu
abunda muka yi ma kulllum
zagin mu take muje kawai. Suka
shiga gidan Adama suka ajiye
ruwan da ya ke kansu suka nufi
fada
wajen taron. Mata ne makil akan
layi suma su Hannah
suka je karshen suka tsaya.
Wata kyakkyawar mata ce a
zaune a kan kujera da
tebur a gabanta an dora wasu
files a kan teburin.
Kallo daya zaka yiwa matar
kasan tana cikin daula fatar
jikinta mulmul-sumul. Duk da
matar ba fara bace amma ba
baka bace kalarta mai kyau ne
kayan jikinta
kuwa ko ba'a fada maka ba
leshin zai doshi dubu hamsin
sarkar gwal da dan kunnenta da
zubbunan
gwal reras a hannunta wasu
manyan warwarayen
gwal ne a hannunta guda hudu
sai sheki suke yi. Matar mai
fara'a gata bata kyamar
talakawa sai gaggaisawa
dasu take suna yin hannu. Ta ce
kowacce tazo gabanta
ta rubuta sunanta don asan
yawansu kuma nawa ya
cancanta a basu. Kowacce tahau
zare ido saboda basu iya rubutu
ba cikar wajen da batsewarsa
aka rasa
wacce ta iya rubuta sunanta.
Matar ta ce "Yanzu duk
cikinku babu wacce ta iya
rubutu ta zo ta taimaka min
mu rubuta sunayenku? Hannah
tayi shiru kamar ta ce ta iya
amma gudun surutun *yan gari
nan kar a ce ta cika nuna iyawa
sai tayi shiru. Indo ta zungureta
ta ce
"Hannah bakin iya rubutu ba ki
rubuta mana.
Hannah ta ce "A'a Indo babu
ruwana a samu wani yazo
yayi dan kar ace nazo garinku
na zake. Matar ta sake cewa "To
tunda babu wacce ta iya rubutu
ina ganin ba zaiyu mu aiwatar
da aikin da zamu aiwatar ba a
yau sai
mun nemo wacce ta iya rubutu
sannan saboda da mata zalla
muke so mu kafa kungiyar, dole
mace ce zata zo
ta rubuta mana sunayen. Indo
da taga kiri-kiri zasu rasa kyautar
bata san sanda ta ce "A'a ranki
ya dade ga Hannah ta iya rubutu
Saura suka hau cewa
"Hannah
taimaka mana ke kuwa ashe
daman kin iya rubutu, rubuta
mana kar mu rasa. Matar ta ce
"Wace ce Hannah?
Ta fito tazo nan. Hannah taje
gaban teburin matar ta
tsaya ta ce "Gani ranki ya dade.
Matar ta kalli Hannah
sama da kasa wata burgujejiyar
doguwar rigace wacce
aka dinkata da wani wagambari
mai kauri irin na da dinnan
itama kanwar kakarta ce ta bata,
gashinta a tufke a tsakiyar kai
tayi gammo dashi da zasu
debo ruwa, sai wani yalallen
gyale baki ta yana a kanta da
takalminta dan madina a
kafarta. Matar tayi murmushi
ta ce "Yaya sunanki? Hannah ta
ce "Suna na Hannah Abubakar
Imam. Matar ta ce "Hannah
Abubakar kin iya rubutu?
Hannah ta ce "Na iya ranki ya
dade.
Matar ta ce "Ko da yake ku anan
Franch kuke yi ba turanci
ba ko irin na *yan Nigeria?
Hannah ta ce "Ni nafi iya
turancin
Nigeria, french din kadan-kadan
na iya mijina yana koya min.
Matar ta ce "To jawo kujera kizo
nan
kusa dani ki dinga rubuta
sunayensu, ki fara rubuta
sunan ki sannan ki rubuta
sunayen sauran. Hannah ta
zauna tana rubuta sunayen
matan nan daya bayan daya
suna tahowa a layi. Ta gama
rubuta sunayen sai
magaruba tayi sai aka tsayar da
shawarar sai gobe da safe
karfe tara na safe su kara
taruwa anan don a raba musu
tallafin suka nufi gidajensu.
Matar kuma gidan dagaci
aka kaita a can zata kwana, na
mijin kuma da suka zo
shima aka kaishi wani gida aka
sauke shi tunda dare yayi dole
su kwana. Kowacce ta tafi gida
tana
murna tana dokin gobe tayi su
koma fada. Hannah da Indo
kuwa sai suka hau faduwar
gaba suna shirya kalmar da
zasu furta wajen kare kansu
daga fadan Inna Haule. Ai kuwa
daga shigarsu gida ta fara yi
musu fada don labari ya kai
mata cewar anga su Hannah a
fada sunje karbar jari. Tana
cewa "Dole Hannah ki barmin
gidana saboda so kike ki
koyawa Indo qinji da fitina
wanda da bata iya ba, ki tafi can
gidan ku acan ake yunwa
ake neman jari mu nan Allah Ya
rufa mana asiri. Kema
Indo tunda wanda ya dau
nauyinki ke da *ya*yanki ya
rasu Bello ne daman ya ce shi
zai dinga ciyar da ku gashi ya
mutu dole kema asan yadda
za'ayi idan bangaren
gadonku zaku siyarmin to, idan
ma wani zaku siyarwa dai duk
daya ki karbi kudinki keda
*ya*yanki ku koma can Tawa
local Government garinku. Ba
zaku zo
ban haifeku ba ku samun
hawan jini tunda kun hallaka
mazan naku ni dai ku kyale ni.
Washe gari da sassafe su
Hannah suka tashi suka hau
ayyukan gidan, bayan sun gama
suka leka ko ina
basu ga Inna Haule ba ta shiga
makwabta sai suka debi
bokitansu suka cewa Masa'ud
dan gidan Indo in Inna tazo ya
ce mata sun tafi rafi debo ruwa.
Atamfa
mai kyau Hannah ta daura basu
tsaya a ko ina ba sai
a fada wajen taro, sunma dan
makara don yanzu tara da
rabi tayi suka ajiye bokitansu a
lungu suka je taron.
Matar ta kalli Hannah tayi
murmushi ta ce "Hannah ke
muke jira ki fara kiran sunaye in
rarraba muku kudin.
Hannah ta gaisheta faram-faram
da fara'a sannan ta karbi
takardar ta fara kiran sunanta ce
"Hannah Abukar Imam
ce ta farko, matar ta ce "To ki
kira sunayen daya bayan
daya suzo su bi layi sai kawai in
dinga mimmika musu
kudin a layi Hannah ta fara kiran
sunayen, kowacce
tana zuwa tana shiga layi kamar
yadda sunayen
suke a jikin takardar. Bayan
Hannah ta kammala kiran
sunayen sai matar ta mike ta ce
"To madallah Assalamu Alaikum
jama'a. Su duka suka ce
Wa'alaikumussal am. Ta ce
"Ni sunana Haj. Hindatu Umar
daga Kano state Nigeria.
Nazo nan garin mai suna Dashi
karkashin karamar hukumar
Magarya a Janhuriyar Niger ne don
in kawo wa *yan uwana mata
tallafi da taimako yadda matan
da suke da maza su ke samun
taimako daga wajen
mazajensu to ku da baku da
maza sai ku samu sana'ar da
zaku taimakawa kanku da
marayun *ya*yanku.
Suka sa tafi raf-raf suna cewa
"Allah Ya saka da alheri
mun gode Hajiya Hindatu. Ta ci
gaba da cewa "Daga gwamnatin
Jihar Kano, matar maigirma
gwamnan jihar
Kano ta bude wata kungiya
wacce za'a dinga taimakawa
mata da mazansu suka rasu
suka
barsu, shine taga ya dace mu
shigo makwabciyar kasarmu
Niger suma mu hada kai da
gwiwa mu taimaka musu
saboda abunda yayi Nigeria shi
yayi Niger duk Uwa daya Uba
daya muke. Tafi suka hau yi
suna murna suna cewa "Allah Ya
kiyaye Nigera da gwamnatin
Jihar
Kano. Hajiya Hindatu Umar ta ci
gaba da cewa "Yanzu
anan garin zamu kirkiro wani
suna mu saka wa wannan
kungiya tamu don muci gaba da
turo muku da
tallafi ta ko ina daga kasarmu.
Bani zan bawa kungiyar
suna ba ku da kanku ya kamata
ku saka mata suna. Nan
dai wannan ta ce a sa mata kaza
waccan ta ce asa
mata kaza, daga karshe sai dai
aka tsayar da shawara
akan a sawa kungiyar suna
Hindatu Umar. Tayi dariya ta
ce "A'a ba suna na za'a sa ba
saboda watakila ba
zaku sake gani na ba sai dai
kuga an turo muku wata
saboda muma can *yan
kungiyar muna da yawa. Idan
aka
turo ni yau gobe wata za'a turo
muku. Amma yanzu
tunda ga wacce ta iya rubutu da
karatu Hannah ita zata
dinga wakiltarku idan ta kama
ma har can Nigeria zata
dinga zuwa tana karbo muku
tallafi ina ganin idan kun amince
asawa kungiyar sunan Hannah.
Gaba daya
suka hau cewa mun amince asa
sunan Hannah.
Daga karshe matar ta jawo wata
jaka ta fara mika musu damin
kudi kowacce kudin data samu
idan
aka kiyasta da kudin Nigeria zai
kai kimanin dubu sha biyar-
biyar. Bayan kowacce ta karba
ta ce ba'a
kare ba.
Akwai atamfofi da wasu kudade
da za'a sake basu shima daga
gwamnatin Nigeria sai dai basu
zo da kudin yanzu ba amma
idan zaiyu su nada wata daga
cikinsu da zata je ta wakilce su
don taga waje taci gaba
da zuwa tana karbar musu
lokaci-lokaci. Murna ta kama su
sai suka hada baki suna cewa
"Mun
wakilta Hannah a matsayin
wakiliyarmu. Hajiya Hindatu ta
juya ta kalli Hannah ta ce "Kin
amince Hannah za ki bini
Nigeria ki dinga karbo musu
taimako? Hannah
tayi murmushi ta ce "Hajiya me
zai hana sai in biki din, akan
haka suka yi sallama cewar
Hannah zata bi
Hajiya Hindatu Kano don karbo
musu wasu tallafi masu
yawa,
kafin Hannah tabi matar sai da
taje da sauri gidan Kawu Ahmad
ta shaida masa duk shawarar da
suka
yanke akanta ya amince ya
kuma yi mata fatan Allah Yasa su
dauketa aiki acan tayi ya ce, idan
da
sarari taje makarantarsu ta
karbo sakamakon jarabawarta
ta nemi aiki ko Allah Yasa ta
dace. Ta raba kudinta gida biyu
ta bashi rabi. Ta sake raba nata
gida biyu ta
bawa matarsa Hajir, ko gidan
Inna Haule bata je
dauko kayanta ba, kawai ta fada
motar su Hajiya Hindatu
Umar sai tafiya daman Hajiya
Hindatu tayi sallama da
dagaci da sauran hakiman garin
ta basu kaudi masu yawa
suma ta sanar musu zata tafi da
Hannah donta sake
karbo musu wasu kudaden
taimako. Sunyi murna
sosai sun shi albarka sunyi
musu fatan Allah Ya kiyaye
hanya. Mutumin da suka zo
dashi mai suna Shehu shine
yake tuka motar. Hajiya Hindatu
a baya ta zauna Hannah ce ta
zauna a gidan gaba, motar kirar
Hummer Jeef dindimemiya mota
mai dauke da rundimemiyar
rikoder an saka sauti mai tashi a
hankali sai sanyayyiyar na'aurar
sanyi ce ke dukan jikin Hannah.
Cikin motar ma abun kallo ne
lausasan kujerun
motar su suka sa Hannah ta
nutsu ko magana bata
iyayi. Ta ce a ranta "Allah Ya
baku duniya wannan mota ce
kawai ba gida ba. Allah mai
azurta wanda Ya so. Sun hau titi
dodar suna zuba gudu a titi sai
hanya.
kafin karfe uku ma a cikin garin
Kano tayi musu tafiya
suke kamar bayi suke yi ba
saboda babu wata kura ko
gajiya irin ta matafiya a tare da
su. Hannah sai kallon
Kano takeyi galala komai yaci
gaba ba kamar lokacin
data zo ba. Babu abunda ya
fado mata a rai sai ranar
da ta zo wajen Haisam zuwanta
Kano na farko kenan
kuma bata taba saka ran sake
dawowa ba ashe zata
dawo yanzu Allah Ya kawo dalili.
Ta dinga kallon hanyoyi ko
zata gane gidan su Haisam
amma ina ba tama gane
Hanyar ba balle ta gane gidan.
Haisam, Haisam take ta kira a
zuciyarta yayin da kwalla ta cika
mata idanuwanta Ta mudubi
Hajiya Hindatu take
kallonta ta ce "Hannah yaya dai
naga kamar kwalla ta cika
miki ido ko iskar A.C ce tayi miki
yawa a ido a rage? Hannah
ta ce "A'a babu komai suka ci
gaba da tafiya can Hajiya
Hindatu ta ce "Hannah ga
garinmu fa, Kano kenan TA
DABO TUNBIN GIWA kin taba
zuwa Kano ne tunda naga
kamar a Nigeria kika yi karatu?
Hannah ta ce "Nan F.G.G.C Kazaure nayi na taba
zuwa Kano amma
sau daya shekaru biyu da suka
wuce amma bazan iya tuna
ina ne unguwar dana zo ba,
Sulemanu cresent
sunan unguwar. Hajiya Hindatu
ta ce "Oh Sulaiman cresent
sunan unguwar ai bamu da nisa
sosai yanzu muna Ahamadu
Bello way zamu bi ta wajejen
dai, ni a
Sokoto road farm center nake
zan nuna miki kwanar.
Hannah ta ce "To suka ci gaba
da tafiya.
Dai dai get din wani
tsantsareren katafaren gida
motar su Hannah ta tsaya yayin
da mai gadin ya taso da
sauri ya bude musu. Hajiya
Hindatu ta kalli Hannah ta
ce "Hannah nan gidana ne ina
so muyi sallah muci abinci
mu huta wajen gobe sai in kaiki
wajen kungiyar su baki tallafi a
kaiki can garin naku ko?
Hannah ta ce "Babu komai na
gode. Hannah taga duniya
wannan gida shine
ake kira aljannar duniya saboda
kana shiga farfajiyar
gidan wasu fulawoyi ne an
zagaye wani dan tudu yana
bul bulo da ruwa sanyi garai. Ga
lilo irin na hutawar nan da ake
saka shi a gidan attajiran gaske.
Wasu
Dawisu ne da talo-talo da
tsuntsaye masu kyawu
aka watsa a farfajiyar gidan
suna ta yawo can gefe kuma
wajen wanka ne (Swimming
pool) an kewaye da wasu
kujerun hutawa can gefe kuma
wajen wasannin
yara ne na motsa jiki (games)
wajen basket ball, table tennis,
foot ball da dai sauransu. Sai
kuma ga wata tafkekiyar kofa
wacce zaya kaika cikin gidan.
Daga
can baya kuma boy's quater ce
itama kamar wani katafaren
gida. Arziki ma anan ai ba'a
magana kai kace a turai kake ba
a Nigeria ba. Hajiya Hindatu
ta yunkura zata fita daga cikin
mota ta juya ta kalli
Hannah wacce ke zaune tayi
turus ta ce "Hannah fito
mana. Hannah taja kofar zata
bude ta kasa sai da Hajiya
Hindatu ta fito daga kujerar
baya ta bude
mata ta waje, sannan Hannah ta
fito. Gidan ya bawa Hannah
sha'awa kwarai da gaske. Ta ce
"Hajiya gidanki yayi min kyau
wallahi. Ta kalli Hannah tayi
murmushi ta ce "Na gode
Hannah.
Wani dogon saurayi ne
kyakkyawa a gefe a zaune akan
wata kujerar roba yayi tagumi
ya rike kai. Hajiya Hindatu taje ta
same shi tana zolayarsa ta ce
"Mijin me akayi maka yau? Kana
gani na ko ka dago kayimin
magana ko budurwarce ta bata
maka rai? Daga nan Hannah ta
tantance kanin mijinta ne wasan
kanin miji take yi masa. Ya dago
a sanyaye ba fara'a dakyar
ya kalleta ya ce "Auntyna muje
daga ciki muyi magana.
Hajiya Hindatu ta kyalkyale da
dariya ta ce "Kai dalla
rago nasan fada kuka yi kai da
Ummi duk yadda aka yi.
Ya ce "Wannan mai sauki ne
muje ciki dai. Ya juya ya kalli
Hannah ya ce "Aunty wace ce
wannan? Ta ce "*yar Niger ce,
ya ce "Niger? Daman Niger kika
je yau
kwana bakwai bakya nan? Ta ce
"Eh muje ciki dai,
Hannah zo mu shigo ciki. Suka
isa wani tafkeken falo wanda
zan
iya kiransa da aljannar Duniya,
nan Hajiya Hindatu ta ajiye
jakarta akan kujera ta
kishingida don gajiya. Ta ce
Hannah zo ki zauna bakuwa
kema kin gaji. Hannah
tayi murmushi dukka sassan
jikinta ya dau sanyin na'ura, a
fakaice kallon alatun da suke
jifge a falon
take, tana tambayar zuciyarta
abin da bata sani ba bata taba
gani ba. Saurayin yaje wajen
wata
telephone da take sakale a jikin
bango ya dauka yana latsa
wasu lambobi can da aka jima
ya ce "Hello Hajiya ga
Aunty ta dawo ashe wai Niger
taje. Hajiya Hindatu ta tashi
zaune ta ce "Lah Hajiya kake
gayawa ashe Niger naje,
daman haka kake kai in angaya
maka magana sai ka fada? Ya zo
a sanyaye ya zauna akan kujera
ya ce
"Aunty dole fa Hajiya tasan kin
dawo kuma ina kika je tunda
neman ki ake yi tuntuni. Hajiya
Hindatu ta ce "Hajiyar a asibiti
take ko kuma a ofis? Yaya mai
jikin ina ta tambayarka baka
bani amsa ba? Ya ce "Yana can
yaji sauqi. Ta ce bari inje inyi
Sallah in je in duboshi,
har yanzu basu sallame shi ba?
Yana premier hospital
ko Aminu Kano aka mayar
dashi? Ya ce "Yana can dai.
Ta ce "Wai meke damunka ne
duk da kyar kake magana na
lura? Hannah ta ce "Wani ne
bashi da
lafiya? Allah Ya sawake. Hajiya
Hindatu ta ce "Wallahi
mai gidana ne bashi da lafiya
yana asibiti. Hannah ta girgiza
kai ta ce "Kai kai Allah Ya sawake
masa,
ciwon ya tsananta ne haka har
da kwanciya a asibiti me
ya same shi? Ta ce "Ciwon
zuciya yake ta fama dashi wallah
Hannah. Hannah ta ce "Zuciya? Allah Ya bashi lafiya.
Hajiya Hindatu ta ce "Amin,
shigo ga
bandaki muyi sallah ko azahar
bamu yi ba gashi uku da
rabi yanzu la'asar ta kusa.
Hannah na biye da ita har wani
katafaren daki mai dauke da
wani kayataccen
gado a ciki dakin, kuma da wani
kayataccen bandaki.
Hajiya Hindatu ta ce Hannah ta
shiga bandaki tayi alwala idan ta
fito sai ta shiga. Hannah ta shiga
bandaki sai da tasha kallo ta gaji
sannan tayi alwala ta
fito. Hajiya Hindatu ma ta shiga
ta dauro alwala. Suna idar da
sallar azahar sai kawai suka yi
la'asar don lokaci yayi. Hannah
na tahiyar karshe Hajiya Hindatu
ta
idar tana jan carbi suka juyo ana
rafsa kuka kamar na mutuwa a
babban falo a guje Hajiya
Hindatu ta tafi
Hannah kuma ta hau sauri tana
so ta idar taje itama taga meke
faruwa Hannah taji ihun ya kara
karuwa da Hajiya Hindatu ta fita
kuka wiwi suke yi. Hannah
ta fita da sauri ta iske mata
makil a falo ana ta kuka.
Hannah tayi kasake tana
kallonsu bata san me ya faru ba
balle tasan me zata ce musu.
Hajiya Hindatu ce ta taso
tazo ta kama hannun Hannah ta
kawo tsakiyar matan
nan wadanda suka doshi su
ashirin. Hannah ta durkusa
akan kafet ta gaishe su wata
kamilalliyar Dattijuwa
mai kyau ta dago luhu-luhun
idanuwanta ta dubi
Hannah ta juya ta kalli Hajiya
Hindatu ta ce "Ramlah wacece
wannan? Ta ce "Wannan ita ce
Hannar Haisam. Su duka suka
bude baki suka ce "Hannah,
Hannah ce
wannan ina kika nemota? Ta
rushe da kuka ta ce "Har Niger
naje na nemota. Sai gaba daya
aka rushe da kuka. Hannah ta
kasa gane abunda ake nufi,
kanta ya daure abun ya bata
mamaki. Ta ce "Meke faruwa, a
ina nake anan? Haj. Hindatu ta
goge hawaye ta ce
"Hannah nan Kano ne, ta nuna
wannan dattijuwar matar ta ce
"Wannan ita ce Mahaifiyar
Haisam. Hannah cikin mamaki ta
ce "Mahaifiyar Haisam! Haisam!!
Haisam!!! Hajiya Hindatu ta ce
"Haisam, ta nuna wannan
saurayin ta ce "Wannan shine Izzuddin
kanin Haisam ne, ni kuma ba
sunana Haj. Hindatu ba, sunana
Ramlah ni ce matar Haisam.
Hannah ta zabura ta
mike tsaye ta ce "Ramlah, meke
faruwa, me nayi miki?
Ramlah ta jawo hannun Hannah
ta zaunar da ita ta ce "Zauna
Hannah zan baki labarin Haisam
yanzun
nan.
Hannah ta koma ta zauna a
sanyaye ta tattara hankalinta
baki daya tana sauraron Ramlah.
.
Kukan da nake yasa nakasa
karisawa sai kuma Gobe in Allah
ya kai mu..........GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 21
Ramlah ta sharbe hawayen da suka cika mata ido
ta ce "Hannah, Haisam yana sonki, Haisam ne mai
sonki, babu wani mai sonki a duniya irin Haisam.
Haisam ya fi kowa kaunarki a cikin duk masu sonki
a duniya. Hannah ta ce "Ramlah me yasa kika ce
haka? Ramlah ta ce "Abun da yasa nace haka
shine Haisam bai taba yin soyayya ba sai a kanki,
bai taba ganin wata *ya mace ba a duniya da yaji
yana sonta kamarki Hannah. Hannah ta dago ta
kalli Ramlah ta ce "Amma Haisam ke ya fara so
kafin ma mu hadu dashi har yayi miki alkawarin
zai aureki. Ramlah ta girgiza kai ta ce Haisam ya
sanni tuntuni amma ba sona yake ba. Allah Ya
jarabeni da tsananin son Haisam tun muna
America idan sunje hutu gidanmu. Nasha sanarwa
Mahaifiyata sai ta ce kada ma in fara bazai yiwu
ba, saboda Mahaifiyar Haisam Kawarta ce tasha
gaya mata cewa Haisam bashi da ra'ayin soyayya
ya ce shi bai taba jin yana son wata ba kuma yana
ganin bazai taba ji ba. Har muka dawo kasar nan.
Amma naki hakura naci gaba da cusa soyayyar
Haisam a zuciyata, na dinga kokarin nunawa
Haisam irin soyayyar da nake yi masa amma sai
yake nuna min baisan abunda nake nufi ba. Da
naga haka sai na dinga bin ta hanyar Iyayenmu
don na sami Haisam. Da farko Mahaifina na samu
nasa masa kuka cewar in ba'a bani Haisam ba zan
kashe kaina. Mahaifina ya lallashe ni ya ce "Duk
mai sauki ne zai sami Mahaifin Haisam. Haka
kuwa akayi Mahaifina yaje ya sami abokinsa
Mahaifin Haisam ya shaida masa bukatata.
Saboda sanin ra'ayin Haisam akan soyayya bai
amsa masa kai tsaye ba sai dai ya ce zai tuntubi
Haisam zai kuma yi shawara da Mahaifiyar
Haisam. Kusan shekara guda bamu ji wata
cikakkiyar amsa ba daga gidansu Haisam, to sai
nasan Haisam yaki amincewa ne yasa babu wata
cikakkiyar amsa da naji game da bukatata akan
nifa har yanzu ina son Haisam. Babu irin kalmar
da Mahaifina bai furta min ba wajen wayar min da
kai akan na cire son Haisam, in so masu sona ga
sunan barkatai suna zuwa, naki na ce Lallai-lallai
sai Haisam.
Nazo nayi yajin cin abinci naki ci naki sha na
kaura daki sai kuka. Iyayena suna ta lallashina
naki canja ra'ayina. Shi kuwa Haisam bai san ma
abunda nake yi ba, yana can Jami'a yana
karatunsa. Kawarki Rauda Kanwata nake aike da
wasika in shaidawa Haisam halin da nake ciki
amma bai taba bani amsar wasikata ba. Ko da
naje gidansu baya cemin komai koda zamu yini
tare ko uffan bazai ce min ba. Haka idan yazo
gidanmu wajen Auwal Yayana abokinsa idan muka
gaisa babu abunda zai sake cemin ko hira nake
musu bai cika sa baki ba. Da Mahaifina yaga na
damu sosai da son Haisam shi ne ya sake samun
Mahaifin Haisam suka zauna suka yi magana
sosai Mahaifina ya nuna bacin ransa ya ce ba
yadda za'ayi suce Haisam yaki amincewa tunda
bashi ya haifesu ba, su suka haifeshi in har suna
so zasu san yadda zasu sashi ya amince dole.
Gudun kada abokantakarsu ta baci Mahaifin
Haisam ya kira Haisam ya ce "Ko yaki ko yaso sai
ya aureni. Da farko Mahaifiyarsa taki ta ce baya
yiwuwa a yiwa namiji auren dole a barshi tunda ya
ce bashi da ra'ayin soyayya gashi yanzu karatu
yake a lokacin yana shekara ta karshe a jami'a.
Mahaifiyar Haisam taga dai abun zai koma tashin
hankali tsakaninta da Mahaifana da kuma mijinta
sai ta amince ta ce ayi auren, ta ci gaba da lallaba
Haisam akan ya yarda ayi bikin. Da aka zo sa
ranar auren Yaya Habib sai aka hada damu. Aka
saka ranar auren mu shekara daya dai-dai lokacin
da Haisam zai gama bautar kasa ni kuma na
gama sakandire sai ayi bikin. Har lokacin da aka
saka rana Haisam bai taba zuwa gidanmu ba da
sunan yazo zance. Ni ce kullum nake yi masa
waya musamman da tsakar dare. Yana amsa mun
wayar amma wani lokaci sai yayi barcinsa abinsa
ma ya barni a layin wayar ina ta magama ni kadai.
Haka a cikin hirarrakin da muke akwai wasu
tambayiyi da nake yi masa bai taba amsa mun ba
sai dai yayi shiru. Tambayoyin kuwa sune Haisam
yanzu kuwa kana jin sona a zuciyarka? Me yasa
baka zuwa gidanmu zance? Idan ban ganka ba ko
naji muryarka bana iya barci kaifa? Baya amsamun
duk wata tambaya da ta jibanci soyayya. Na sani
kuma na gane Haisam ba sona yake ba kiri-kiri
amma idona ya rufe tunda ni ina sonsa zan iya
zama dashi a haka.
Haisam yana bautar kasa a F.G.G.C Kazaure ina
gida ina jiransa ya gama sai ranar daurin aure a
bada da sadaki in zama matarsa kawai ya tage.
Kwatsam da Haisam ya kammala bautar kasa sai
ya ce shifa ba yanzu za'ayi bikin ba a yi na Yaya
Habib tunda shine babba ayi namu daga baya. Aka
yarda da bukatar Haisam tunda lallabashi ake yi
akayi bikin Yaya Habib. Sai kawai muka ji Haisam
ya koma F.G.G.C Kazaure a matsayin cikakken
Malami wai shi koyarwa yake so yayi shi yasa ya
nemo aikin acan. Na ce na yarda ayi bikin zan iya
binsa Kazaure mu zauna. Haka dai Haisam yayi ta
yi mana hanya-hanya yaki yarda ayi bikin. Da
yaga an takura masa ance ya baro Kazaure ya
dawo Kano ga kamfanin Babansa anan zaiyi aiki
ayi bikinmu kuma sai ya ce shi ya amince idan na
sami wani in aura don shi kuma sai nan da
shekara biyar. Na ce na yarda zan jira shi in shiga
Jami'a kafin nan nima na kare sai muyi auren
kawai. Ran Mahaifina ya baci Mahaifiyata ta
zazzageni ta ce bazan jira shi ba sai kace bani da
zuciya wanne irin so ne wannan. A lokacin akwai
wani saurayina mai suna Dalhatu dan jarida ne
yana sona sosai, yana so ya aureni nace bana
sonsa bazan aureshi ba dai-dai lokacin nan an
tura shi B.B.C London ya ce idan anyi bikinmu sai
ya tafi dani can London nayi karatun jami'ata, naki
fur. Babu irin nasihar da Iyayena basu yimin ba da
lallashi naki ji nifa idan ba Haisam ba sai dai in
fasa aure. Iyayen Haisam ma sun yi iya kokarinsu
wajen tilastawa Haisam ya dawo yazo ayi bikin
nan namu sai ya daina zuwa week end dinma da
yake zuwa kwata-kwata. To kowa ya rasa yadda
zaiyi da mu suka zuba mana ido sai addu'a.
Na shiga Jami'a a nan Kano B.U.K ina karantar
bangaren labaran *yan Jarida (mass
communication). Ina karatuna ina jirar Haisam na
sami samari kala-kala akwai kyawawan da suka fi
Haisam kyau nesa ba kusa ba akwai masu arzikin
da suka fi Haisam, masu sona fiye da Haisam
amma naki su ni sai Haisam don bazan manta ba
har Mahaifiyata take cemun zaki auri Haisam in an
takura masa amma ba zaki sami soyayyar da kike
nema ba. Na ce idan anyi auren zai so ni ai. Nasa
Kanwata Rauda ta binciko mun wanne irin buri ne
Haisam ya kudira a F.G.G.C Kazaure yake so ya
cika kamar yadda kullum yake cewa, Rauda ta ce
ai wata yarinya ce *yar ajinsu mai suna Hannah ya
ce kanwarsa ce tana jin saboda ita ya ki barin
makarantar. Na sa Rauda ta ci gaba da lura da
abinda yake gudana tsakanin Haisam da Hannah.
Kuna aji hudu (S.S 1) Rauda ta zo min da
cikakken bayani game da binciken da nasa tayi
mun. Ta ce abu ya tabbata Haisam son Hannah
yake yi, duk makarantar an sani zance ya fito fili.
Ta bani labarin irin gwagwarmayar da aka yi
tsakanin Haisam da Malamai masu takurawa
Hannah da Dalibai masu takura miki, Yaya Habib
ma ya fada mana yadda suka yi da Haisam har
Haisam ya wawuri adda kamar zai daba masa,
Yaya Habib ya ce Haisam sai addu'a saboda
kamar ya zautu a son wata yarinya don haka nema
yaki dawowa gida.
Raina ya baci sosai da naji ance Haisam yana son
wata, na lashi takobin ko wacece wannan Hannah
sai naga karshenta ko ani ko a ita, shine nabi
direban mu da zai dauko Rauda ranar hutu don in
ga wacece wannan Hannah? Kuma *yar waye?
Dame ta fini da Haisam yafi sonta da ni? In kuma
ja mata kunne akan ta rabu da mijina, don a
lokacin yadda nake ji zan iya hallaka duk wanda
yake kokarin ya rabani da Haisam. Na je
makarantar na tarar bakya nan ance su Haisam
sun tafi dake sai muka biki garin ku muka tarar
bakya nan, sai Mahaifinki. Na fadi maganganu iri-
iri a cikin bacin rai saboda Mahaifinki ya rabaki da
makarantar don ki rabu da Haisam. Haisam bai
bar Kazaure ba sai da kika gama makaranta da
sati biyu sannan ya dawo gida da kayansa.
Mahaifinsa na ganinsa cewa yayi Haisam har ka
cika burin daka kudira ka dawo? Haisam yayi
murmushi ya ce "Eh Baba, Mahaifiyarsa ta ce idan
baka gama cikawa ba ka koma ka gama ka dawo
Ramlah na jiranka ayi bikin ku. Haisam ya ce ya
gama sai dai kuma ya zo wajensu neman alfarma
guda daya don Allah su taimaka masa, suka
bukaci Haisam ya fadi abunda yake so ya fada
insha Allahu idan bata fi karfinsu ba zasu yi masa
sai ya zauna ya basu labarinki tas tun daga ranar
da aka kawo ki makaranta har halinda kike ciki a
gidanku, ya kuma bayyana musu tsananin son da
yake miki ya ce su taimakeshi su bashi izini ya
hadamu mu biyu ya aura saboda kece rayuwarsa
zai iya shiga wani hali idan suka ki amince masa.
Bai rufe bakinsa ba Mahaifinsa ya daka masa
tsawa ya ce bazai yuba karma ya sake yi musu
wata magiya. Mahaifiyarsa ma ta ce in har ita ta
dauki cikinsa wata tara ta haifeshi yasha nononta
har ya girma to bata amince masa ya auri Hannah
ba.
Kwana biyu Haisam ya fara ramewa kullum ka
ganshi yana tunani, kallo daya zaka yi masa kasan
yana cikin wani hali na tsananin damuwa, ya daina
ci ya daina sha balle yayi hira da mutane
Mahaifinsa da yaga haka sai ya kira shi ya ce yaje
ya same ni yayi mun bayani akan ko zan yadda ya
auremu mu biyu, idan na amince to zaije ya sami
matarsa Mahaifiyar Haisam ya lallasheta ta yarje
masa. Haisam ya sameni a lambun gidanmu da
yamma yake cewa in taimakeshi in ceto rayuwarsa
ya auremu mu biyu ni da ke. Na kekashe kasa
nace ban yarda ba, Haisam ya durkusa
gwiwowinsa biyu a kasa yana rokona in duba
girman Allah da tsananin son da nake yi masa da
zumuncin da yake tsakanin Iyayensa da Iyayena
tun suna yara in barshi ya aureki yayi min alkawari
zaiyi adalci a tsakaninmu kawai don ya ciro
Hannah daga cikin wahala ta dawo wajensa ba
don yafi sonta ba a kaina. Mahaifansa sunce in har
na amince suma sun yarda ya aure mu mu biyu.
Na ce har abada bazan taba amincewa ba.
Hawaye ne yake zubowa daga idanuwan Haisam
yana rokona amma naki fur.
Ramlah ta sharbe hawaye taci gaba da cewa.
Bayan anyi haka Haisam ya hakura akayi bikinmu
ranar daurin aure ma Haisam kuka yake ko a
bidiyo kaset an nuna babu abinda zaka gani a
idanuwan Haisam sai hawaye. Anyi biki an kaini
gidana kowa ya watse aka barni da Haisam. Babu
abinda Haisam yake sai dai ya zauna a falo yayi
shiru yana tunani sai inyi magana sau goma
Haisam baya sanin abinda nake cewa yana tunani.
Hira wannan ba mayi da Haisam balle zancen
wata soyayya, ina alkunya ina sharewa a matsayin
na sabuwar amarya bai kamata in dinga binsa shi
namiji bai bini ba. To in har zanyi sati ban shiga
bangarensa ba ba zaizo inda nake ba, gaisuwa ce
kawai take hada ni da Haisam. Bayan mun gaisa
sai kallo da ido kawai ko abinci na kai masa baya
ci sai da ruwan shayi kawai yake sha. Tun yana
lekawa ofis wajen aikinsa kamfanin Babansa anan
yake aiki harma ya daina zuwa kwata-kwata.
Yayansa Habib yayi fadan har ya gaji ya kyale shi,
abokansa gaba daya magana suke meke damun
Haisam ya canja gaba daya baya zuwa wajensa
babu walwala baya son yin magana ko sunje
wajensa. Nima har wannan abu na Haisam ya fara
damuna. Inyi wanka in caba ado amma Haisam bai
san ina yi ba. Sai mu yini a zaune Haisam bai
dago kai ya kalli fuskata ba balle yaga jan baki da
hodar dana shafa balle yaga fari da idon da nake
yi masa da kallon soyayyar da nake yi masa. In
takaice miki munyi wata hudu cur da Haisam a
haka ko hannu na bai taba rikewa ba balle ya
shiga dakina. Sai da abun ya isheni nayi yaji na
tafi gidansu naje na sami Mahaifiyarsa na shaida
mata halin da muke ciki da Haisam, ina kuka
kamar zan mutu. Ta lallasheni ta ce in daina kuka
muka tafi gidan ni da ita muka sami Haisam a
zaune a falonsa akan kujerar da ya saba zama
yayi tagumi yana tunani kamar yadda ya saba.
Hajiyarsa tayi masa fada sosai ta shaida masa
gara ya saki jikinsa ya dawo da walwalarsa
zamansa da ni daram kuma har abada baza ta
yarje masa yaje ya auro wata Hannah ba. Bayan
nan ne Haisam ya yarda ya shiga daki na da
daddare wani babban takaici ma muna kwance
yana kirana da sunan Hannah. Nayi fadan nayi
fushin sai dai ya bani hakuri ya ce mantawa yayi
gobe ma haka jikina ya fara sanyi na fara sarewa
na fara fitar da rai akan samun soyayyar Haisam,
yayi nisa sosai a fagen son Hannah.
Kullum sai sake dulmiya yake a tunanin Hannah,
baya cin abincin kirki ba a hira dashi shi dai gashi
nan ne kawai yana Kano amma zuciyarsa tana
Babban-mutum garinku. Wasu lokutan da yamma
yakan shiga lambu yana busa wani dan karfe dogo
kamar na azurfa da nayi bincike aka ce mun abun
busarki ne akwai wasu tsakiyoyi a akwatinsa suma
wasu lokutan yana dauko su ya baza a gado da
wani hoto tun kuna J.S.S one ke da Rauda
kanwata da Nusaiba Haisam a tsakiyarku shima ya
kura ido yana kallo in takaice miki soyayya ta fara
zautar da Haisam ni kuma ina gefe ina son maso
wani, ni da dutse duk daya nake a cikin gidan. A
haka muka shekara da Haisam sai muyi wata uku
sannan nake samu ya shiga dakina, to koda ya
shigo ma ba faranta min zaiyi ba daga karshe
sunan Hannah zai dinga kirana da shi. Nayi fada,
nayi yaji har na gaji Haisam baya tankamin balle
ya bini biko idan nayi yaji. Da kaina nake zuwa in
dawo. Ban sami kulawar Haisam ba, babu
soyayyarsa. Akwai abinci, ga kudi, galla-gallan
motoci duk wacce nake so ita zan shiga.
Mahaifiyar Haisam ce take yimin sutura, ba'a yin
wata guda sai ta aiko min da dinkuna haka
Mahaifinsa ya budemin account a banki yana
turomin da kudi. Yaya Habib duk wata yake
siyomin kayan abinci komai da komai. Mahaifana
kansu da kafarsu kudi suke bani suka kara rokona
inci gaba da hakurin zama da mijina tunda ni nace
naji na gani ina sonsa haka. Amma kuma dukka
gatan da surukaina suke yimin da Iyayena duk na
banza ne ba dadin rayuwata nake ji ba tunda na
rasa soyayyar mijina. Kowa ya rasa kan Haisam an
rasa yadda za'a kamo bakin zaren bare a warware
mana matsalarmu. Wani lokaci Mahaifiyata ta
kirani take shawarta ta ko zan hakura da wannan
aure in zo in auri mai sona shima yaje ya auro
wacce yake so nace ai ni ko da zan mutu gara naci
gaba da zama da Haisam a haka saboda tsananin
son da nake yi masa.
Haka naci gaba da zama da Haisam, kullum a cikin
tunani yake har zuciyarsa ta samu matsala ya
kwanta ciwo likitoci suka ce lallai-lallai Haisam
Ba,anan ya qareba
Shiga cikin wannan website din domin qarisa karanta chapter 21
Www.littafanhausane.com.ng
yana cikin matsananciyar damuwa da tunani da
kunci dole ne a dinga kwantar masa da hankali
don har zuciyarsa ta ta kamu da ciwo saboda
damuwa. Bamu da maganin wannan matsalar ta
Haisam saboda kece maganin, tsananin sonki shi
yake damunsa. Don haka ciwon Haisam ya ci gaba
da yaduwa kusan kullum a asibiti Haisam yake
daga ya dawo gida sai ciwo ya tashi a mayar
dashi asibiti Haisam ya rame yayi duhu abin
tausayi. Wani abin mamaki a karkashin filonsa na
asibiti abun busarki ne da tsakiyoyinki yake yawo
dasu. Likitoci sunyi-sunyi da Haisam ya rage
damuwa saboda samun lafiyar zuciyarsa abu ya
faskara. Akwai lokacin da Haisam yayi wata biyu a
kwance a premier clinic jikin babu sauki saida aka
mayar dashi Aminu Kano Teachin hospital amma in
yanzu kaga Haisam zaka dauka kafin ka fita bakin
kofar dakin zai mutu saboda tsananin jin jiki da
yake. Numfashinsa sama-sama dakyar abun
tausayi.
Hannah ta rushe da kuka gaba daya wajen sai aka
fara hawaye. Ramlah ma hawayen da take ya kara
karuwa. Ta ci gaba da cewa "Nafi kowa sanin
takamaimai meye ke damun Haisam ina ta zargin
kaina nice silar wannan ciwon na Haisam tunda
nice na raba shi da abar kaunarsa. Da naga haka
sai na yankewa kaina shawarar kawai in shiga gari
duk inda Hannah take inje in nemo wa Haisam
saboda ita ce kadai soyayyar da zan nunawa
Haisam a matsayina na mai tsananin sonsa bana
son in rasa shi gaba daya, gara na nemo masa
maganin wannan ciwo da yaki warkewa fiye da
shekara guda yana fama. Ban bari kowa ya sani
ba, ban shawarci kowa ba na shirya tsaf da kayana
da guzirina da direba na na shirya fita neman
Hannah. Na yiwa surukaina da Iyayena sallama
akan zanje Kaduna gidan wata kawata da mijinta
ya rasu inyi mata ta'aziyya kwana biyu kawai
zanyi. Mahaifiyata ta nemi ta hana ni tafiya
saboda ga jikin Haisam yayi tsanani yana kwance
a asibiti yaya za'ayi ince zanyi balaguro duk da
ma dai bani bace nake zaman jinyarsa kaninsa ne
Izziddin da Mahaifiyarsa ai sai suga ban damu
dashi ba harkata ma na tafi. Nasan hakan da ta
fada gaskiya ne bai kamata in tafin ba amma na ce
ni dai zanje ba dadewa zanyi ba. Tayi min fatan
Allah Ya kiyaye hanya sai na dawo, na tafi.
Hmm soyayyah!!!!!!!GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter22
Karku manta daga yau duk post din da zamuyi bazamu Kawo complete chapter dinba don samun complete sai a shiga cikin wannan website din www.littafanhausane.com.ng
Kowa ya gyara zama dan yaji labari
cike da mamaki da tausayin Ramlah
kowa ya zubo mata ido yana kallo
musamman Hananah. A zuciyarta
cewa take wai shin ko mafarki nake ne ba gaske bane ni Ramlah ta
nemowa Haisam. Yau zanga Haisam
kenan? Ikon Allah, Allah Mai Girma,
Allah na gode maKa, ko bazan auri
Haisam ba in ganshi ma na gode wa
Allah. Ramlah ta ci gaba da cewa "Babban-mutum garinku na nufa na
rasa gidan naku ma sai da muka yi
tambaya don ban manta sunan
Mahaifinki ba Malam Habu. Na ce yana
da *ya Hannah wata fara. Da afarko
basu gane ki ba da Hanne suka fi saninki ashe ko *yar Baba na ce kece
sannan aka kaimu gidan naku. Ashe
Mahaifinki ma ya rasu? Hannah ta
gyada kai ta ce "Yafi shekara biyu ma
da rasuwa. Ramlah ta ce Allah Ya
jikansa. Mahaifiyar Haisam babu abinda take
iya cewa sai kuka kawai take yi kamar
ranta zai fita, Mahaifiyar Ramlah ce
take rike da ita tana lallashi itama
kukan take. Ramlah ta ce "Sai matar
Babanki muka iske take cemun suma basu san inda kike ba, kanin
Mahaifiyarki ya zo ya dauke ki tun
bayan rasuwar Mahaifinki kun tafi
kasarsu Niger. Na tambaya wanne gari
a Niger ta ce Dashi. Na dan sha wuya
kafin na gano inda kike. Munyi kwana biyu a gidan wani bawan Allah a garin
muna yiwa matansa kwatance sai can
daya daga cikin matan ta ce Hannah
matar marigayi Bello Madu custom. Na
ce mijinta ya rasu ne? Suka ce ya rasu
harta fita takaba, naji dadi da suka ce a yanzu baki da miji don zan iya tahowa
da ke. To amma yaya zanyi gashi baki
sanni ba, *yan Uwanki da *yan uwan
mijinki ba zasu bari in taho da ke ba.
Na tambaye su *ya*yanki nawa yanzu
suka ce baki taba haihuwa ba watanki bakwai da aure mijinki ya rasu ya
barki. Sai kawai na tuno wata dabara
na ce to tunda mijinki ya rasu bari ince
daga gwamnatin jihar Kano matar
gwamna ta aikoni don in kafa wata
kungiya da za'a tallafawa matan da mazajensu suka rasu suka barsu da
marayun *ya*ya. Haka kuwa akayi
nasa aka rakani fadar mai gari ni da
direbana muka hada baki muka ce
tare aka turomu. Dajin haka mai gari
da jama'ar gari suka yi farin ciki da wannan ziyara tamu. Washe gari yasa
akayi shela aka tara mana matan da
mazansu suka rasu suka barsu. Kallo
daya nayi miki na gane ki, saboda na
sanki a hotuna a wajen Raudah
kanwata tun kuna aji daya har aji shida. Tunda nasan kin iya rubutu
sauran basu iya ba sai na ce kowacce
tazo ta rubuta sunanta. Basu iya ba, na
ce to wacce ta iya tazo ta dinga
rubutawa suka nuna ki kika zo kika
rubuta. Na babbaku taimakon da zan baku sannan na ce tunda kin iya
rubutu to ke zaki dinga wakiltarsu
kina karbo musu taimako daga Kano
na nemi da ki biyoni Kano. Na ci sa'a
kuwa *yan uwanki suka amince kika
biyoni. Don kawai in kawo ki wajen Haisam.
Wannan karon Hannah murmushi ne
ya kece mata saboda tsananin farin
ciki. Ta sake tattara hankalinta wajen
Ramlah tana sauraronta. Ramlah ta ci
gaba da hawaye ta ce "Hannah gaki a tsakiyar falon gidan Haisam don kece
kadai maganin da zaisa Haisam ya
warke daga wannan matsanancin
ciwon zuciyar da yake fama dashi. Ta
sharbe hawaye ta ci gaba da cewa.
Haisam ya sha wuya Hannah a sanadiyyar tsananin sonki, Haisam ya
rasa walwala a rayuwarsa a
sanadiyyar tsananin sonki. Haisam mai
kaunarki ne fiye da duk wani mai
sonki a duniya. Sai yau Hannah ta ji
amsar wannan kalmomi da ta dade tana nema dalilin da ake cewa Haisam
yafi kowa sonta a duniya. Mahaifinta
ne ya fara fada mata, Bello Madu ya
fada mata haka, sannan Ramlah ta
fada mata. "Lallai na yarda Haisam yafi
kowa sona, Hannah take fada a zucitarta. Ramlah ta sake rushewa da
kuka mai tsanani ta ce "Ban sami
soyayyar Haisam ba ban barshi kuma
ya auri wacce yake so ba. Hannah ta
matso ta rungume Ramlah tana
lallashinta tana bata hakuri itama kukan take yi. Ramlah ta ce "Hannah
dole nayi kuka dole na dauwama cikin
bakin cikin dana jefa Haisam na
cuceshi na cuci kaina. Hannah ta ce
"Aunty Ramlah daina cewa haka Allah
Ya rubuto sai anyi haka amma bake kika sa haka ta faru ba, Ramlah ta
dago ta kalli Hannah ta ce "Haisam
yasha wuya, kullum yana tunani
kamar ya zautu don wani lokaci sai
kaga yayi murmushi ya ce Hannah
kenan saboda tsananin tunaninki da yake. Ni dai kawai ina tare da GANGAR
JIKIN Haisam ne amma zuciyarsa na
wajenki. Ramlah ta sake rushewa da
kuka ta ce "GANGAR JIKINSA NA
AURA!!! Zuciyarsa na wajenki Hannah.
Ke kadai ce maganin ciwon nan na Haisam Hannah kece kadai zai gani ya
warke.
Hannah tasa hannu tana gogewa
Ramlah hawaye can cikin zuciyarta
kuma cike take da farin cikin da ta
dade bata ji irinsa ba cikin sanyin murya ta ce "Yanzu ina Yaya Haisam
din yake, ku kaini in ga jikin nasa..
Gaba daya falon suka dauki kuka mai
tsumama zuciya Hannah cike da
mamakin me yasa suka sake rushewa
da kuka kuma. Hannah ta dubi Ramlah ta ce "Lafiya kuka sake
rushewa da kuka? Ramlah ta dafa
kafadar Hannah ta ce "Hannah sai dai
kiyi hakuri Allah Ya yiwa Haisam
rasuwa jiya Yaya Habib yayo waya.
Zasu taho da gawar a yau da daddare zasu iso.
Hannah ta zabura ta mike tsaye yayin
da zuciyarta ta fara dukan uku-uku
kanta ya fara sarawa kamar zai fashe
ta dora hannu aka yayin da jiri ya
dauke ta ta koma ta zauna, Ramlah ta riketa. Izzidin kanin Haisam ne ya
katse Hannah daga tunanin da take
ciki yazo gabanta ya durkusa yana
mai tsananin kuka da hawaye ya ce
"Ni nake zaman jinyarsa ya ce min duk
ranar dana ganki na baki wannan. Ya mikowa Hannah tsakiyoyinta da abun
busarta. Cikin sanyin jiki tasa hannhu
ta karba tana jujjuyawa ta gansu gar
da su kamar yau ya karba daga
wajenta. Sai ta tuno ranar da aka kai ta
makaranta tana zaune akan akwati, Haisam na kan benci yana mata
tambayoyi har ya karbi wadannan
tsakiyoyin. Sai hawaye ya dinga
digowa daga idanuwanta. Izziddin ya
ce "Bayan tafiyar Ramlah jikin Yaya
Haisam ya rikice sosai har aman jini yake yi. Ashe Yaya Habib yana ta
cuku-cukun zai fita dashi turai. Bayan
tafiyar Ramlah da kwana biyu Yaya
Habib ya tafi dashi London. Ranar da
suka isa da dadddare Allah Yayi
ikonsa Yaya Haisam ya rasu. Gingirin Hannah ta tsaya tana kallon Izziddin
tamkar wata gunki. Izziddin ya ci gaba
da cewa "Yaya Habib yana kuka yayi
waya ya ce yau da daddare gashi nan
zai juyo da gawar Haisam shine
wannan taron da kika gani anan jiran isowarsu muke. Kiyi hakuri Hannah
haka Allah Ya rubuto miki. Haisam
yasha wuya a sanadiyyar son ki. Kowa
yayi shiru babu abinda kake ji a falon
sai sautin shesshekar kuka kowa nayi.
Can Hannah ta rushe da kuka tana cewa "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un
haka Allah Ya rubuta min Allah haka
Yake so ya ganni na godewa Allah.
Yanzu babu Babana, babu mijina Bello
Madu haka babu Haisam din da a
kullum nake saka ran zan ganshi duk daren dadewa. Hannah tana rusa
kuka tana basu labarin rayuwarta tun
ranar da Mahaifinta ya kaita
makaranta suka gamu da Haisam har
izuwa aurenta da Bello Madu har zuwa
rana irin ta yau da aka bata labarin mutuwar Haisam. Ta ce ta dauka ita
kadai take haukarta Haisam yana can
da matarsa ya manta da ita tunda ya ce
min ya cika burin daya kudira a kaina,
na inyi karatu ya dawo gida yanzu zai
cika alkawarin da ya dauka. Sai na dauka Haisam ya manta da wata
Hannah ashe ina like a ransa. Hannah
kuka wiwi Jama'ar dake a falon
Iyayensa da Iyayen Ramlah daginsa
da dangin Ramlah da makwabta duk
suka ji tausayin Hannah fiye da kansu. Hannah ke akayiwa mutuwa. Inji
Mahaifiyar tace Haisam ya ce min Hajiya ku
barni in auri Hannah, Hajiya Hannah ce
rayuwata amma naki fur ashe kuwa
da gaske yake yi gashi yanzu babu
shi. Inama Haisam na da rai yazo ya ga Hannah. Sai duk falon aka dauki kuka
gaba daya.
Hannah ta kankame tsakiyoyinta da
abun busarta a cikin gyalenta ta mike
dakyar tana hada hanya tana tafiya
dakyar ta nufi cikin wani daki ashe dakin Haisam ne, can lungun
gado ta shige ta zauna yayin da
idanuwanta suka fada wani katon
hoton Haisam dake like a jikin bangon
dakin yayi kyau sosai yana dariya a
hoton. Taji gabanta ya yanke ya fadi ta kurawa hoton ido kem yayin da taji
wani ruwa daga hancinta yana zurara
ta cikin kanta numfashinta yana
kokarin dauke mata abunda zata iya
tunawa kenan, ashe suma tayi.
Amratu kanwar Haisam aka turo tazo dakin taga wanne hali take ciki karta
nemi ta halaka kanta, sai kuwa tazo ta
ganta a jingine a lungun gado a zaune
ido babu baki sai fari ta kafe. Amratu
ta kwalla ihu sai duk suka shigo aka
tarar da Hannah cikin wannan hali, ba ayi wata-wata ba aka daukota ana
salati aka yayyafa mata ruwa ta
farfado.
Tana bude ido taga dandazon jama'a
har sunfi na dazu mata da maza an
idar da sallar magariba an sake taruwa ana jiran isowar gawar Haisam. Kofar
gida cike taf da maza. Hannah tayi
salati ta shiga ta zauna tana tunanin a
ina take ko dai mafarki takeyi dazu
ance mata Haisam ya mutu. Allah Yasa
mafarki ne, amma ta mutsike idon ta goge ruwan dake fuskarta taga zahiri
ne ba mafarki bane Haisam ya rasu, ya
rasu da gaske ne. Hannnah taji sai
sannu ake yi mata yayin da taji wasu
na tambaya ita ce Hannah? Wannan ce
Hannar? Wadanda suka zo yanzu kenan. Hannah ta ce a zuciyarta wato
kowa ma ya sanni kenan kamar
yadda nima acan duk wanda ya sanni
sai yasan Haisam. Hannah ta matsa
kusa da Mahaifiyar Haisam ta zauna sai
ta ji Mahaifiyar Haisam tasa hannu ta goge mata hawaye, ta ce mata
"Hannah kiyi hakuri Allah Ya kaddara,
haka fatana ki dinga yiwa Haisam
addu'a kinji ko? Allah Ya jikansa ya
gafarta masa. Allah Ya hadaki da mai
sonki fiye da yadda Haisam yake sonki. Hannah ta girgiza kai ta ce "Har
abada ba'ayi ba, baza ayi ba kuma
Hajiya, na rasa mai sona, nima na rasa
wanda nake so. Sai su dukka suka
rushe da kuka. Kan Hannah akan
cinyar Mahaifiyar Haisam tana kuka kamar ta shiga cikinta don tsananin
son da taji tana yi mata tamkar Haisam
tunda ita ta haifi haisam. Itama
Mahaifiyar Haisam ta dafa kanta jin
Hannah take kamar Haisam ita tunda
Haisam na son Hannah itama har ga Allah taji Hannah ta shiga ranta. Amma
aikin gama ya gama Haisam din daya
hada ya tafi ya barsu.
Can Hannah ta dago ta ce "Zanje inyi
sallar magariba. Hajiyar Haisam ta ce
"Eh jeki kiyi. Hannah ta mike dakyar ga tsananin faduwar gaba da ciwon
kai, ita kanta baza ta iya misalta yadda
take ji a wannan rana ba. Ta shiga
dakin ta kalli wajen da hoton Haisam
yake manne taga an cire shi sai ta
wuce ta shiga bandaki ta dauro alwala tazo ta fara sallah. Bayan ta idar da
sallar magariba ta tashi ta fara jero
nafiloli sai taji gaba daya an dau salati
tun daga *yan kofar gida har matan
dake falo sai taji ana cewa sun iso, an
iso da gawar. Tana tsaye tana sallah sai taji ta sulmiye ta zauna kafarta ta
kasa daukarta gabanta ya yanke ya
fadi. Ta ji duk tsikar jikinta tana tashi.
Kukan da yaki zuwa dazu ya kece
mata tamkar ranta zai fita. Can taji
salatin da ake ya lafa sai ta rike bango ta tashi tsaye da kyar don ta fita falon
taje taga gawar abun kaunarta don
idan taga fuskarsa yanzu ita ce kadai
zata dinga tunawa har karshen
rayuwarta.
Duk dama taji a jikinta
itama ba dadewa zata yi ba a duniya zata bi Haisam dinta. Tunda damuwa
da tunani ne ya kashe Haisam a
shekara biyu ita yanzu yadda take ji ya
linka yadda Haisam yake ji don haka
zuciyarta zata iya fashewa a wata uku
ta mutu ta huta. Tana tafiya a hankali dan karta fadi
har ta fita daga dakin, tana fitowa taga
gaba daya daruruwan mutanen da
suke zazzaune a falon sun juyo suna
kallonta gaba dayansu. Idonta ya dira
akan wata fuska wacce take tunanin ba gaskiya take gani ba gizo ne.
Ku shiga cikin nan domin karanta qarishen chapter 22 www.littafanhausane.com.ng
Haisam ta gani zaune akan doguwar
kujerar da ke falon, Yaya Habib a kusa
dashi. Ta sake zare ido tana kallon
Haisam taga dai shi din ne haka taga shima yana murtsike ido yana kallonta
yayin daya jawo hannun Mahaifiyarsa
ya ce "Hajiya ga Hannah can a mafarki
ina ganinta. Mahaifiyarsa ta rushe da
kuka ta ce "Haisam ba mafarki kake yi
ba Hannah ce. Ya zabura zai mike da sauri Yaya Habib ya rike shi don baya
iya tashi tsaye, ya mayar da shi ya
zaunar. Ramlah ce taje wajen Hannah
ta riko hannunta ta nufo da ita wajen
Haisam ta ce "Haisam ga Hannah,
Hannah ga Haisam da gaske ne ba mafarki ku keyi ba. Hannah ta rushe
da kuka ta rungume Ramlah tana
cewa "Ramlah daman ba da gaske
kuke yi ba da kuka ce Haisam ya
mutu. Ashe zan sake ganin Haisam da
idona? Hawaye ne yake zubowa daga idanuwan Hannah da Haisam. Yaya
Habib ya nisa ya ce "Ikon Allah
Hannah yi hakuri daina kukan yanzu
duk jama'ar nan sauraro suke suji
yaya akayi aka ce musu Haisam ya
mutu kuma gashi yazo da ransa. Sami waje ku zauna. Hannah da Ramlah
suka sami waje suka zauna babu abin
da Haisam yake sai kallon Hannah ko
kiftawa baya yi itama kuma ta manta
da a gaban jama'a take duk idonsu
kuma a kansu itama wani irin kallo take yi masa mai dauke da tsantsar so
da kauna, Mahaifin Haisam da sauran
jama'ar duk suma sun shigo.
Yaya Habib ya ce "Kamar yadda kowa
ya sani Haisam na cikin tsananin ciwo
muka bar kasar nan ranga-ranga muka tafi London. To muna isa can
nayiwa asibitin da zamu kwanta waya
suka aiko da motar asibiti aka
daukemu muka tafi. Likitoci na ganin
yadda jikin yake baki da hanci jini sai
suka ce zasu wuce dashi tiyata. Na sa hannu akan na amince ayi masa. Ina
bugo waya ina sanarwa da Baba duk
halin da ake ciki. Bayan sun gama
masa tiyatar ne suka yi suka yi ya
farfado yaki farfadowa suka sa masa
iskar kara numfashi (oxygen) don a jawo lumfashin amma abu ya faskara
sunyi iya kokarinsu na su nemo
lumfashin sun kasa. To ni kuma da
naga haka sai na rikice na bugowa
Baba waya ina kuka nace Haisam ya
rasu. Wani likita yayi-yayi kada in bugo waya har sai anyi wasu awanni
a gani ko zai dawo saboda akwai
alamar bai mutu ba, na ce ina ai babu
sauran wata rayuwa a jikin Haisam. A
take Baba ya yiwa abokansa dake
London waya akan suzo su sameni a asibiti suyi kokari a bamu gawar a
gobe mu juyo gida Nigeria ba sai an yi
ta dogon bincike ba har kwana da
kwanaki. Tunda ya rasu azo gida ayi
masa sutura a binne. Abokan Baba
suka zo aka hau dogon turanci likitoci suka ce sai an basu awa goma sha
biyu suga ko zai farafado dansu basu
yarda ya mutu ba doguwar suma ce in
har bayan awa goma sha biyu bai
farfado ba to saisu bamu gawar. Mun
dauka duk haukarsu ce ta nasara mutuwa ai daya ce kuma kallo daya
zaka yiwa Haisam kasan ya mutu,
ganin babu inda yake numfasawa a
jikinsa. Su ashe sunga akwai wata
jijiya a hannunsa da suka ji tana dan
harbawa shine suke sa ran zai dawo ya rayu.
Muna kirgawa awannin da suka dibar
mana sun cika su bamu gawar mu
taho shine nayi waya nace gabannin
magariba zuwa isha'i zamu iso azo a
taremu. Da rana karfe uku jirgi zai tashi daga London zuwa Nigeria haka
kuma da karfe biyu awannin goma
sha biyu zasu cika da suka dibar mana
sai mu taho. Muka sayi akwatin saka
gawa, na cike form din zan tafi da
gawa. Karfe biyu na cika cikin ikon Allah akaga numfashinsa ya fara
dawowa. Likitoci sukayi-sukayi mu
barshi suci gaba da ceto rayuwarsa
naga gara kawai mu taho tunda dai
sunyi masa abunda zasu yi masa
shikenan sauran sai a barwa Allah ikonSa. Tunda acan gida nace ya mutu
gara dai mu taho din idan ya rayu
Alhamdulillahi idan kuwa ya mutu
dama nace musu ya mutu shikenan.
Muka taho a haka sunan dai yana da
rai wasu daga jijiyoyinsa suna harbawa amma ko motsi bayayi. Naga
gara nayi shiru kada ince bai mutu ba
kafin mu karaso ya mutu gara ace
kafin mu karasa ya farfado. Kuma
cikin jirgin ma akwai likitocin da suka
yi ta taimaka masa wajen jawo numfashi. Cikin ikon Allah muna dira a
garin Kano ya fara numfasawa sosai.
Mun sashi a cikin mota zuwa nan
gidan ya bude ido yayi salati. Shine
yanzu da yaga wannan taron jama'a
yake tambaya me ake yi, aka ce ai an dauka ka rasu shine *yan jana'iza
suka taru, shine yayi karfin halin ya
tashi zaune ya jingina.
Farin ciki a zuciyar jama'a abun ba zai
misaltu ba musamman Mahaifan
Haisam da Ramlah da Hannah. Tamkar anyi musu albishir da gidan Aljannah
Alhamdulillah jama'a ke cewa. Don da
aka ga Haisam an dauko shi da idonsa
kiri-kiri yana kallon mutane wasu da
yawa har sun fara rugawa a zatonsu
sunga fatalwa. Wani abin kunya ma ba mata kawai ba har wasu mazan a
kofar gida sun fara rugawa. Nan fa
kaji falo ya hargitse da Kabbara da
Hamdala. Ana ta taya Mahaifin Haisam
da Mahaifiyarsa murna da fatan Allah
Ya bashi lafiya da tsawan kwana mai amfani. Murmushi kawai Haisam keyi
murna ce ta cika masa zuciya haka
kawai ya tsinci kansa yana mai
tsananin farin ciki badan rashin karfin
jiki ba da tsalle zaiyi ya taka rawa don
murna. Murnar kuma ita ce ga Hannah yau a gabansa, kusa dashi tana
kallonsa tana masa murmushi.
Hmmm GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 23
Zuciyar Hannah kuwa tunda uwarta ta haifeta bata
taba jin farin ciki irin na yau ba taji duk ta manta
kunci da bakin cikin da ta shisshiga ada. Tamkar
ba'a taba bata mata rai ba a duniya balle tayi
kuka. Haisam ne yanzu wannan a gabanta bai
mutu ba ashe? Kai Allah Shine abin bautawa da
gaskiya mai rayawa mai kashewa mai yin duk
yadda yaso da bawansa. Hannah take jinjinawa a
ranta. Ramlah kamar tafi kowa farin ciki a ranta
kasancewar Haisam bai mutu ba ta sanadiyyar jefa
shi cikin kunci da tayi ta hana shi ya auri wacce
yake matukar so, bayan haka babu wani da namiji
da take so fiye da dashi a duniya har yau. Ramlah
na son Haisam fiye da tunanin duk wanda yasan
soyayya. Wani babban Malami ne ya rufe taro da
addu'a akan Allah Ya kara bawa Haisam lafiya.
Bayan an shafa ne Ramlah ta mike ta ce tana da
magana aka bata izinin yin maganarta. Bayan ta
nemi gafarar Haisam da Iyayen Haisam da Hannah
da duk wasu *yan uwansa da suka fada halin
tashin hankali a sanadiyyar wannan ciwo na
Haisam, sai ta zo gaban Haisam ta durkusa ta
dube shi tayi murmushi ta ce "Haisam ina neman
wata alfarma a gareka idan Allah (S.W.A) Ya baka
lafiya ina so ka auri Hannah saboda a yanzu
Hannah bata da miji ni zan biya sadaki, lefe, kayan
dakin amarya da duk hidimar da za'ayi a bikinku,
nayi kuskure ada dana hana ka auri Hannah yanzu
na gane kuskurena. Haisam yayi wani lallausan
murmushi ya gyada kai don bashi da karfin yin
magana. Sai gaba daya aka dauki kabbara duk
wajen, sai kowa ya fara shiwa Ramlah albarka
musamman Mahaifan Haisam. Hannah ta ji wani
sanyi kamar kankara a ranta abun mamaki Ramlah
ta amince ta aura mata Haisam da kanta babu
abinda take yi a ranta sai godiya ga Allah wani
sabon Imani ya kutso a ranta ta sake gasgatawa
kowa yayi tawakkali ga Allah, Allah Zai saka masa
ta wata hanyar da bai taba zato ba.
Allah Shine
mai iko Shine yake bayarwa a duk sanda Yaso.
Mai hakuri baya tabewa a sannu zaiga biyan
bukata. Duk tsanani kada ka manta da Ubangijinka
yana sane da kai idan ka shiga kunci sai ya
kaddara maka jarabawa ce don ya gwada imaninka
Allahu Akbar.
Mahaifin Ramlah ne ya sake rufe taro da addu'a
ya dinga shiwa Ramlah albarka da fatan alheri a
rayuwarta da sabuwar abokiyar zamanta Hannah.
Jama'a na amsawa da amin daga karshe aka
shafa jama'a suka fara watsewa. Ramlah ta duka
gaban Mahaifiyar Haisam ta ce "Hajiya abar min
Haisam anan gidan ni da Hannah zamu ci gaba da
kula dashi. Ko tantama Mahaifiyar Haisam ma
bata yi ba ta amsa da "To shikenan. Don tasan
barin Haisam a kusa da Hannah babban maganin
wannan ciwon nasa ne. Kowa ya tashi ya nufi
wajen motarsa don tafiya gida, babu kowa a falon
daga Haisam sai Ramlah a kusa dashi da Hannah
da Amratu kanwarsa *yar kimanin shekaru goma a
kusa da Hannah suna zaune a gefe. Ramlah ta
fuskanci Haisam ya gaji da zaman alamar yana so
ya kwanta sai ta ce "Bari in dauko maka filo a daki
ka dan kwanta kafin in hada maka dan shayi
kasha, kasha magani sannan in kai ka daki ka
kwanta. Ta mike ta nufi daki. Hannah ta dago
zata kalli Haisam taga babu abinda Haisam yake
yi sai kallonta tamkar ya sami talabijin a gabansa
ko kiftawa baya yi. Tayi murmushi ta ce "Yaya
Haisam sannu. Ya dan lumshe ido ya gyada kai.
Ramlah ce dauke da filo ta iso wajen da suke gami
da yin sallama. Hannah ta amsa. Ramlah ta ajiye
filon akan doguwar kujerar da Haisam ke
kishingide ta kama shi ta gyara masa kwanciya ya
kwanta sosai. Hannah ta yunkura ta tashi tana
rike da hannun Amratu ta ce "Aunty Ramlah zamu
shiga daki mu kwanta, wanne dakin ne? Ramlah
tayi murmushi ta ce "Haba Hannah aike ba
bakuwa ba ce yanzu, duk dakin da ya yi miki shiga
ki kwanta ai gidanki ne. Amratu tayi caraf ta ce
"Aunty Hannah zo muje dakina mu kwanta zaki ga
*yar tsanata da Aunty Ramlah ta siyomin. Taja
hannun Hannah suka tafi har sun juya Hannah ta
juyo da kyakkyawar fuskarta ta kalli Ramlah da
Haisam tayi murmushi ta ce "Sai da safen ku.
Sannan ta juya suka tafi. Haisam har dan daga kai
yake don leken Hannah ganinta yayi tayi kyawun
da duk a cikin kabilu, kama daga bakar fata har
farar farar fata turawa da Indiyawa bai taba ganin
wacce tayi masa kyau kamar Hannah ba
musamman a yau. Ramlah ta tsaya kawai tana
kallon Haisam taga kamar zaije ya jawo Hannah
ya rungumeta koma ya hadiyeta yadda yake binta
da kallo, sai tayi murmushi ta dan taba hannunsa
ya juyo ya kalleta tayi fari da ido ta kanne ido
daya ta ce "Haisam ya akayi ne ko Hannah ta
dawo muyi hira ne? Sai yayi murmushi ya koma ya
kwanta. Ramlah ta wuce kicin don hado masa dan
abu mai ruwa-ruwa da zai sha.
Bayan Hannah da Amratu sun shiga daki, Amratu
tayi ta nunawa Hannah kayan wasanta da
kasissina cartoons dinta da litattafan makaranta.
Hannah tayi ta taya ta suna wasa da *yar
tsanoninta har tsawon awa guda bayan shigarsu
sannan Hannah ta ce "To Amratu ya isa haka jeki
kiyi wanka ki dauro alwalar sallar isha'i ki fito
nima zanyi wankan da alwalar. Da ke akwai
bandaki a cikin dakin. Amaratu ta fada ban daki
bayan ta fitone Hannah ta shiga. Tana wanka
Ramlah ta shigo dauke da sabuwar doguwar riga
mai rubi biyu ta barci mai tsananin laushi da
santsi ta kawo wa Hannah sai ta bawa Amratu ta
ajiye mata kafin ta fito, Ramlah ta fito ta jawo
musu kofa ta rufe. Hannah na fitowa Amratu ta
mika mata sabuwar rigar bacci dal a leda ta ce inji
Auty Ramalah. Cike da fara'a Hannah ta karbi rigar
baccin ta saka sannan ta tayar da kabbarar sallar
isha'i. Har Amratu ta gaji da jiran Hannah ta idar
suyi kallon kaset din catoon taga Sallar take ta
jerowa har bacci ya dauketa Hannah bata idar ba.
Sai ukun dare sannan Hannah ta idar da nafiloli da
addu'oin da take na goduya ga Allah (S.W.A) da
Ya nuna mata wannan rana da fatan Ubangiji Allah
Ya tabbatar da abinda Ramlah take shirin hadawa
da fatan Allah Ya bawa Haisam lafiya. Sai kuka ya
kece mata don farin ciki. Ta hau gado kusa da
Amratu tasa hannu ta kashe fitila sannan ta
kwanta. Wani laushi ne ya nutsu a cikin tsokokin
jikinta don bata taba kwanciya a irin wanan katifar
ba tunda take. Sanyin na'urar sanyaya daki ne
(split A.C) yake ratsa hudojin jikinta ta lumshe ido
sai ta hango fuskar Haisam dauke da gwarza-
gwarzan idanuwansa yana kallonta. Bata dade ba
bacci mai dadi ya sureta. Alarm din agogo ne ya
tasheta karfe biyar dai-dai asuba tayi, tayi firgigit
ta bude ido taga fitila a kunne Amratu harta shiga
ban daki tana alwala. Hannah tayi murmushi ta ce
a ranta "Birni sai dan birni ga kudi ga ilimi, yarinya
karama tasan ta saita agogo ta farka da asuba
tayi sallah.
Bayan Hannah da Amratu sun idar da sallah. Sai
suka koma gado suka kwanta wani daddadan barci
ya sake sure su. Goma dai-dai Hannah ta bude ido
sai taga gari yayi tangararai. Tayi firgigit ta tashi
zaune taga rana harta ralle gari. Ta fada bandaki
dan yin wanka ta dauki brush dinta a cikin jakarta
daman ta taho dashi. Ban dakin ma abin kallo ne a
wajen Hannah taga komai na tangaran ne ga
madubai a kewaye da bandakin. Ruwan sanyi da
na zafi a shaya da fanfuna abun gwanin ban
sha'awa. Abubuwa da yawa sai dai Hannah ta
taba ta barshi saboda bata san amfaninsa ba bata
taba gani ba. Aljannar duniya kenan gidan Haisam
kamar a turai. Duk inda ka zagaya falo ne iri-iri
wajen cin abinci dakuna masu gadaje na alfarma
abin baya misaltuwa.
Ramlah tayi matukar mamakin Haisam dubi yadda
yake tsananin jin jiki amma sai ta ganshi daram
kamar ya warke sai dai rashin karfin jiki. Babban
abin da yafi bata al'ajabi shine tunda take da
Haisam bai taba tsayawa yana kallon fuskarta
yana yi mata murmushi ba sai a yanzu data kawo
masa Hannah har ma ta ce zata aura masa ita.
Wannan abunda Ramlah tayi wa Haiam yaji
tsantsar tsanar da yake yiwa Ramlah ta fara
komawa soyayya kawai don ta fara son Hannah.
Haisam ya ji duk duniyar nan babu wanda ya taba
masa kyauta mai girma kamar Ramlah yaga babu
abinda ya kamata ya saka mata itama sai ya karbi
soyayyar da take yi masa shekara da shekaru.
Tunda ta hada shi da wacce yake azabar so. Duk
sanda zai kalli fuskar Ramlah sai yaji sanyi yanzu
maimakon haushinta da yake ji ada. Ramlah ta
fuskanci hakan duk inda tayi Haisam na binta da
kallo yana murmushi Haisam yaji dadin wannan
al'amari amma Ramlah tafi jin dadi kamar a
mafarki take ganin wadannan al'amari har Haisam
ne yake daga ido ya kalli fuskarta har yayi mata
murmushi. Turkashi !!!
Kwanci tashi yau kwanan Hannah shida a gidan
Haisam da Ramlah. A kullum da safe Hannah da
Amratu suna fitowa daga dakinsu su iske Haisam
da Ramlah a falo ko wani lokaci ma a daki suke
samun su, su shiga su gaishe su suyi masa ya jiki
su koma dakinsu. Duk lokacin cin abinci Ramlah
tana lekowa ta kirasu, su fito suci abinci a dinning
table, kuku biyu ne suke dafa abinci a gidan, masu
share-share da goge daban. Dan haka babu aikin
da Ramlah take yi a gidan balle Hannah ta tayata.
Sai dai suyi wanka su zauna suna kallon satelite
da kaset. Dinkuna masu kyau da tsada Ramlah
tasa aka dinkawa Hannah. Dan kunne da sarka da
zobe na gwal Ramlah ta bawa Hannah. A kwana
shidan nan ita kanta Hannah tasan ta canja ta
zama *yar birni. Turarruka kala-kala Ramlah ta
sissiyo ta bata. Haisam kuwa jiki Alhamdulillahi
sauki yana samuwa yana tashi tsaye yana dan
takawa daga daki zuwa falo, in ya gaji ya zauna a
kan kujera a falo. Ranar da Hannah ta cika sati
guda da sassafe ta tashi ta fara harhada kayanta
a jaka na tafiya. Dan taga ya kamata ta tafi gida
kuma tun ana marmarinta kuma jikin Haisam yayi
sauki gara ta tafi duk da ba hakan take so ba.
Bayan sun gama cin abincin safe ita da Ramlah,
yau Amratu ta tafi makaranta tun bakwai da rabi
na safe. Haisam daman ba abinci yake ci ba yana
kallonsa yana kurbar shayi. Hannah ta dubi
Ramlah tayi murmushi ta dan sosa kai cikin ladabi
da alamar jin kunya ta ce "Aunty Ramlah babu
abinda zance miki sai godiya Allah Ya saka da
alheri kuma Allah Ya kara bawa Yaya Haisam
lafiya. Tunda naga jikin nasa yayi sauki inaso zan
koma gida yau kar suji shiru su fara tunanin ko ba
lafiya ba. Ramlah tayi murmushi ta ce "Har za ki
tafi ki barmu, bako zai yi halinsa kenan, ai ba laifi
kinyi kokari tunda kinyi mana sati guda mun gode.
Akwai wasu atamfofi nasa an siyomin gasu can a
jaka na kuma zuzzuba kudi a ambulan dubu
goma-goma kowacce na rubuta sunanta a bayan
ambulan din daman ina da jerin sunayenku saiki
rarrabawa *yan kungiyata in kinje. Hannah ta duka
tayi godiya. Ramlah ta tashi ta shiga falon Haisam
ta iske shi a zaune kan doguwar kujera ya mike
kafafuwansa akan centre table taje ta zauna akusa
dashi tana yi masa murmushi ya dago ya dubeta
ya ce "Uwar gida yaya akayi ne? Tayi fari da
idonta ta ce "Ranka ya dade bakuwarmu ce take
so yau ta koma gida ta ce kar hankalinsu ya tashi
in sunji shirun yayi yawa. Haisam yaji wani dum a
ransa ba haka yaso ba yaso Hannah ta dade yana
ganinta yana jin dadi. Can ya nisa ya ce "Har zata
gudu ta barmu baza ta sake kwana biyu ba?
Ramlah ta ce "A'a gani nake gara taje in yaso ta
dawo daga baya kaga ni na daukota daga garinsu
karsu dauka guduwa nayi da ita. Haisam yayi
murmushi ya ce "To shikenan Allah Ya kaita gida
lafiya. Ramlah ta ce "Amin bari in kirata ta shigo
tayi maka sallama. Ramlah ta tashi ta fito falo ta
duba wajen cin abinci taga Hannah bata nan sai ta
nufi dakin Amratu inda suke kwana. A bakin kofa
suka gamu Hannah ta ratayo jakarta zata fito.
Ramlah ta ce "Oh, Hannah har kin fito lallai Kano
ta ishe ki muna sonki ne ke kuma kina gudun mu.
Hannah tayi dariya ta sunkuyar da kai kasa ta ce
"Aunty Ramlah ba haka bane garin namu ne da
nisa shiyasa na fito da wuri don in isa da wuri.
Ramlah ta ce "Haka ne sai kizo ki yiwa Haisam
sallama yana nan a falonsa. Hannah ta ce "To, sai
ta ajiye jakar ta tana biye da Ramlah har zuwa
falon Haisam sai Ramlah ta fito ta barsu. Ta fito
ta nufi dakinta yayin da zuciyarta ta hau dukan
uku-uku tana fargaba game da yadda taga kyau
irin na Hannah musamman yau da tayi ado da
wata tsaleliyar shadda data dinka mata
combination ja da baki ga wannan lallausan gashin
nan nata a tufke a bayanta. Zuciyar Ramlah na
nuna mata Hannah fa tayi miki fintinkau a fagen
kyau idan baki yi da gaske ba duk wannan iya
kwalliyar taki da har mutane suke yaba miki
Hannah zata zo ta fiki iyawa. Kalli yadda tayi wani
kyau tamkar *yar tsanar roba. Sai wata zuciyar ta
ce Ramlah rufawa kanki asiri ki kwantar da
hankalinki karki sa wannan tunanin a zuciyarki har
wani tashin hankali ya biyo baya yadda Haisam ya
kwallafa ransa da son Hannah kema kika kwallafa
sonsa a ranki to in kina so ki zauna kalau ki sami
soyayyarsa to kiso Hannah tunda gashi kin fara
gane kansa yana nuna miki soyayya.
Hannah ta durkusa a gabansa ta ce "Yaya ina
kwana, yaya jikinka? Yayi narai-narai da ido ya ce
"Hannah da sauki. Tashi daga nan kizo nan kan
kujera ki zauna. Hannah ta tashi ta zauna a wata
kujera a gefensa kowannensu zuciyarsa cike da
tsananin farin ciki sai suka ji dama kar su rabu su
zauna din-din-din suna ganin junansu. Kallon-kallo
suke yiwa junansu na tsananin kaunar juna. Yayi
murmushi ya ce "Hannah zaki tafi ki barni ne,
bayan ina ganinki ina jin dadi ko bakyaso inji sauki
da wuri ne!!
kece fa kwayar magananin da take kwantar
min da ciwon. Hannah ta sunkuyar da kai tana jin
kunyar bada wannan amsar. Ya ce "Yaya naji kinyi
shiru ne? Hannah ta ce "Yaya dole ce tasa ba a
son raina nima zan tafi in barka ba. Amma nayi
Qarishen chapter 23
Na cikin wannan website din
Www.littafanhausane.com.ng
maka alkawari kullum nayi Sallah zanyi maka
addu'a Allah Ya sauwake maka. Haisam ya gyada
kai ya ce "Nagode amma ina so ki min alkawari a
rana zaki dinga tuna ni har sau biyar, duk lokacin
da kika zo yin Sallah zaki tunani kiyi min addu'a?
Hannah tayi dariya ta ce "Ina tuna ka fiye da sau
hamsin a rana ba biyar bama ko ina ganin ka, ko
bana ganinka. Haisam ya gayara zama ya juyo
yana kallon Hannah sai tasa gyalenta ta rufe ido
alamar jin kunya. Haisam yayi ajiyar zuciya ya ce
"Naji dadin duniya da za ki dinga tuna ni sau
Hamsin a rana.. Yanzu ki fada min kalma daya da
zan dinga tunawa a raina a duk lokacin da
tunaninki yayi min yawa sai ta kwantar min da
hankali. Hannah tayi shiru can ta dago tana
murmushi ta kalli Haisam suka hada ido taga ya
kura mata ido kawai yana kallonta. Sai ta sake jin
kunyarsa ta lullube fuskarta ta sake jawo gyalenta
ta rufe ido ta mike tsaye a hankali ta nufi kofar fita
tana tafiya a hankali. Haisam ya ce "A'a tafiya za
ki yi ko sallama babu, kuma ai baki bani amsar
abinda na roka a wajenki ba. Hannah ta juyo a
hankali ta kalle shi kallo irin wanda yake jinsa har
tsakar kansa ta ce "Abinda nake so kasa a ranka
shine ko da GANGAR JIKINA bata tare da kai
zuciyata tana wajenka. Haisam ya sake dagowa ya
dubi Hannah sai yaga ta daga masa gira tayi fari
da ido ta ce "Kada ka manta soyayya gaskiya ce.
Na tafi na barka lafiya ina kuma yi maka fatan
kara samun lafiya. Haisam ya kasa magana sai
kawai ya bita da kallo harta daga labulan kofar ta
fice. Ya rike baki yayi shiru jinsa yake kamar ba'a
duniya yake ba, kamar a aljanna aka jefashi yau
gashi ga Hannah a matsayin masoya masu shirin
yin aure harma wadannan dadadan kalamai suna
fitowa daga bakinta izuwa kunnuwansa. "I can't
believe this, Hannah! Hannah ce kuwa. Haisam
yake fada a baiyane. Ramlah ce ta shigo falon ya
dago ya kalleta fuskarsa cike da fara'a farin ciki taf
a zuciyarsa a yau. Ta ce "Yallabai kun gama
sallama da Hannahr ko? Ga Shehu direba ya fito da
mota zai kaita. Haisam ya ce "Munyi sallama da
Hannah Ramlah sai dai ki bata kudin da zai isheta
tayi hidindimunta Aunty Ramlah. Ta dan harareshi,
su duka suka sa dariya ta ce "Kaima Aunty zaka
ce min? Ai na bata kudi ranka ya dade duk abinda
ya kamata in bata na bata, kada ka manta in so
yayi so ra'ayi yana zuwa daya. Haisam ya ce "kika
ce me? Tayi murmushi ta ce "I feel what you feel
saboda ina sonka. Haisam yayi murmushi ya ce
"Ramlah! Ramlah!! Ramlah tayi dariya sannan ta
fita. Ta raka Hannah har bakin mota sai da suka
fita daga get sannan ta daina daga musu Hannu.
Haisam ne ta wundon dakinsa yake kallon Hannah
har suka tafi, yayin da ya ji wani kululun bakin ciki
na rabuwa da ita.
Bayan tafiyar Hannah da kimanin wata taji shiru
babu Ramlah ba Haisam. Gashi babu waya a
garinsu balle ta buga musu taji lafiyar su. Tun
tana boye damuwarta akan haka har Hajir matar
Kawunta ta fara fuskantar halin da take ciki. Ayau
da yamma bayan Hannah ta idar da sallar la'asar
sai ta shiga ta sallo wanka tazo ta hade da wani
sabon dinkinta na material din da ake yayi.
Material din baki ne anyi masa kwalliya da jar
fulawa. Matsatsan dinki ne akayi, a rigar zanin ma
anyi masa kwalliyar iri daya da yankar rigar.
Hannah ta tufke gashinta da jan madauri (ribon)
ta dana daurin dankwali mai kyau. Tasha hoda a
fuskarta da jagira sannan ta sako sarka da dan
kunnenta da zobe na gwal da Ramlah ta bata.
Haka kawai yau da yamman nan taji tunanin
Haisam yayi mata yawa shine take rayawa a ranta
shine tayiwa wannan kwalliya. Ta tsaya a gaban
mudubi ta kalli kanta ta juya gefe ta sake juyawa
baya taga lallai tayi kyau sosai kamar ba ita ba.
Dama Yaya Haisam na kusa mana yaga wannan
kwalliya da tayi.
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter24
Karku manta shiga www.littafanhausane.com.ng
Don karanta complete chapter din
Ta fito tsakar gida wajen girki ta taya Hajir aikin abincin dare don taga hayaki na tashi tasan an
hura wutar itacen abincin dare. Tana fitowa Hajir ta zabura ta mike tana cewa "La! La!! La!!! Hannah me zan gani wacce irin kwalliya kika caba yau kamar mai shirin barin kasar? Kai amma gaskiya wannan atamfa mai kyau ce ni ban taba ganin irinta ba. Tasa hannu tana
taba kayan jikin Hannah. Ta ce "Kai ai laushi garesu wannan ba atamfa ba ce. Hannah tayi dariya ta ce
"Ba atamfa bace material sunansa kinsan a wajen *yan birni kaga abubuwa iri-iri a gunsu. Hajir ta ce
"Lallai kuwa wannan matar ta caba ki da kayan alatu iri-iri.
Hannah ta nufi wajen garin tuwo ta dauki rariya zata yi tankade Hajir ta rike rariyar ta ce "Hannah ba za ki bata jikinki da gari ba ga kayanki bakake barni kawai in
karasa tuwona tunda har na gama miya na dora ruwan tuwo talge kawai zanyi in tuka na gama. Ga kujera can a gefe jeki ki zauna ni ina zaune ai yanzu sai ki huta ni
inyi. Hannah ta ce "Ni ai zaman haka kawai bana so saboda tun ina *yar karama na saba da aiki barni
kawai ba komai inyi miki tankaden. Hajir ta ki fur suna ta jayayya daga karshe Hannah ta hakura ta koma
gefe ta zauna tana kallon Hajir tana aiki. Hajir ta dago ta kalli Hannah ta ce "Kwanan nan sai
inga kamar kina yawan damuwa da tunanai ko dai wani abu yana damunkine Hannah? Hannah tayi murmushi ta ce "Babu abin da yake damuna. Hajir ta ce "A'a Hannah
fadi gaskiya ko sai na miki baro-baro ne? Ai dole kiyi tunanin Haisam musamman kin baro shi bashi da lafiya. Su duka suka kyalkyale da dariya. Hannah ta ce
"Don Allah ya akayi kika gane ni? Da gaske abun ya fara damuna ni dai fatana ace lafiyar sa kalau ba jikin bane ya dawo. Hajir ta ce "Insha Allahu lafiyarsa kalau
ita lafiya ita ke buya. Amma lalle Haisam ya samu shiga fiye da kowa har yafi marigayi samun waje.
Hannah tayi dariya ta ce "Ni dai baza ki ji a bakina ba.
Hajir ta ce "Jiya kuwa Ahmad yake ce min a kalla masu sonki a garin nan sun doshi mutane biyar da suka
same shi suka yi masa zancen don Allah ya basu izini su zo su nemi aurenki wai in sun zo wajenki bakya fitowa. Hannah ta bude baki don mamaki ta ce "Don Allah da gaske kike yi? Hajir ta ce "Wallah da
gaske nake. Hannah ta gyara zama, ta dafe kirjinta ta ce "Me Kawun ya ce musu? Hajir ta ce "Cewa yayi har a dangi an fara damunsa ya kamata kiyi aure ga masu sonki ki
zabi daya ya ce min shi gaskiya baya so ki sake aure a kauyen nan yafi son ki auri Haisam, to amma gashi yau kusan wata biyu bai zo ba bai aiko ba. In har ya bashi wasu lokuta bai aiko ba zai shawarce ki, ki zabi wani tunda har akwai samarin da basu taba aure ba a wadanda suka same shi da zancen suna sonki.
Hannah tayi ajiyar zuciya tayi shiru ta rasa ta cewa sai tsananin bugun da zuciyarta take yi. Ta ce a ranta "In har Haisam ya kara wata bai zo ba to nasan akwai matsala.
Ko ya hakura da sona ne?
Kai Haisam ba zai hakura da
sona ba. Yaya zanyi yanzu in har Kawu ya zo ya sani a gaba ya ce in fitar da wani in aura? Sallamar Kawu Ahmad ce ta katsewa Hannah
tunanin da take yi. Ya shigo da saurinsa ya suri tabarma sannan ya juyo ya kalli Hannah ya ce "Ki dauko gyalenki ki kawowa baki ruwa a sabon kwanon sha da
kofina masu kyau.
Hannah ta amsa da "To Kawu. Ta juya suka hada ido da Hajir. Hajir ta ce "To ko Haisam ne dan halak yaki
ambato ya iso garin gabannin magariban nan? Hannah ta ce "Banji a jiki na ba, Haisam ba zai zo yanzu ba. Ni har gabana ya na faduwa Allah Yasa dai ba masu
neman auren nawa bane aka sami wani dan...... ya canjawa kawu ra'ayi. Hajir ta ce "Kai haba dai tashi ki kai ruwan kiga ko waye. Dakyar Hannah ta mikewa saboda sanyin da jikinta yayi ta shiga daki ta yafo dan yalolon gyalenta ja ta dauko kwanon sha da kofuna biyu ta zo ta wanke su tas ta cika da ruwan randa mai sanyi ta nufi zaure. Kanta a sunkuye a kasa tayi
sallama ta ajiye kwanon sha a gaban bakin sannan ta gaishe su ba tare da ta dago kai ta dubi fuskokinsu ba.
Wata murya ce ta amsa mata gaisuwar kamar a mafarki muryar da take muradinta. Ta dago kai da
sauri ta dubi mutumin sai taga Haisam dinta ne a gefensa Kawu Ahmad. Sai tayi murmushi ta sunkuyar da kai ta ce "Sannu da zuwa Yaya.
Ta yunkura zata tashi ta shiga cikin gida sai Kawu Ahmad ya ce "Hannah ki kawo ruwa a butoci guda biyu don magariba ta kusa yi. Hannah ta amsa da "To Kawu. Ta shiga gida. Ai kuwa da murna ta karasa wajen Hajir.
Hajir na ganin yadda Hannah ke murna sai ta ce "Hannah ko dai addu'ar tawa ce ta ci, Haisam ne ya zo?
Hannah taje ta rike mata hannu ta ce "Hajir wallahi shi dinne kuwa, ko mafarki nake yi ne? Hajir ta ce
"Gaske ne Hannah Allah Sarki ya cika alkawari ya zo, daman Kawun ki yafi sonki dashi. Daman ina jin jikin ne ya hanashi zuwa Hannah ta ce "Kai gaskiya babu alamar jinya a tare dashi yayi fari ya murmure daga ramar da yayi, kinga kibar da yayi kuwa? Ba za ki ce ya taba yin
wani ciwo har an fasa masa kukan mutuwa ba.
Hajir ta ce "Don Allah? Hannah ta ce "Ai yau duk kunyarki saikin leka kin gaisa da mijina. Su duka suka tuntsire da dariya. Hajir ta ce "Hannah ko *yar kunyar nan
babu wannan karan lallai anayi da Haisam, ai kuwa zanzo mu gaisa. Hannah ta wuce ta debo butoci ta wanke su tas ta ciko su da ruwa ta nufo zauren da suke zaune.
Daf da ta shiga zauren taji Haisam na cewa "Zan yi tafiya zan dauki kimanin watanni biyu a turai amma
ina neman izini zan turo magabatana su zo neman auren Hannah. Ina fatan dai Hannah ta gabatar dani a wajenku daman ko? Kawu Ahmad ya gyada kai ya ce "Kwarai kuwa tun sanda naje Nigeria zan daukota tun daga can ta fara bani labarinka. Kai ka dauki dawainiyar karatunta harta gama sakandire.
Sannan data dawo daga Kano tafiyar nan ta kwanan nan ta fadamin kakaf yadda akayi. Allah Ya saka da alheri.
Haka Allah Ya kaddaro muku Shine Yake yin yadda Yaso da bawanSa. Babu komai ka aiko magabatabka ai ba sai anyi wani dogon bincike ba ai kunsan juna tuntuni. Hannah tayi sallama ta shigo zaure ta ajiye butocin a gefe kanta a sunkuye a kasa ta koma cikin gida. Bayan sunyi alwala, Masallacin dake kofar gidan suka shiga suka yi Sallah tare da jama'a. Hannah ma anan cikin gida tayi Sallah bayan ta idar ta sake rangada kwalliya a fuskarta ta gyara daurin dankwali, ta sami waje ta zauna tana jira akirata taje ta gana da abin kaunarta. Amma abu daya ya tsaya mata a rai
take ta nanantawa da Haisam ya ce zai tafi turai sai bayan wata biyu zai dawo. Ita kuwa anya zata iya daurewa har sai ta sake yin wata biyu kafin ta sake ganinsa?
Son Haisam ya sake yaduwa a zuciyarta fiye dana da a kullum yana like a zuciyarta ko sakon daya bata iya yi ba tare da tayi tunaninsa ba. Kawu Ahmad ne ya shigo ya ce "Hannah za ki iya zuwa ku gaisa shi kadai ne a zaure ki kunna fitilar kawai don zauren da duhu.
Ya ce a yau zasu koma Kano ba zai kwanan ba ni kuma zanje wajen Baba Shu'aibu in fara sanar masa da zancen aurenku. Hannah ta amsa da "To Kawu.
Kawu Ahmed ya fita. Ta mike ta shiga daki ta dauko fitila ta nufi zaure tana takawa dai-dai tana rangwada. Tayi sallama ta ajiye fitila a gefe.
Haisam ya dago kai da sauri yana kallonta harta shige lungu can gefe ta takure ta tsuguna sannan cikin
ladabi ta gaishe shi. Yayi murmushi ya amsa mata. Ya ce "Hannah kamar zan gudu da ke kika tafi can
nesa kika takure, ga nan gefen tabarma kusa dani ki zo ki zauna mana. Koda yake Hannah kin manta da Uncle Haisam tun wata shekara ko. Hannah tayi dariya
ta kubce mata, Haisam ma yayi dariya. Hannah ta taso tazo gefensa ta zauna. Ta daga ta dube shi suka hada ido yayin da wata kibiyar so ta caccaku a zuciyoyinsu, Hannah ta lankwashe murya ta ce "Yaya jikinka?
Ya kura mata ido can ya ce "Ai tun ranar da na hada ido dake na nemi ciwon narasa, kuma tun ranar da
nace miki good bye na tafi na fara ciwo. Hannah tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa ta ce "Ina fatan har abada zan dauwama a wannan matsayin daka bani.
Mamaki ya kama Haisam ya ce a ransa "Hannah ce take fada min haka ko mafarki nake, a zato na sai
nasha bakar wuya da Hannah kafin ta fara sona sai kuma nayi da gaske kafin ta waye da irin wannan
soyayyar ta *yan birni. Ashe ni Hannah a waye take harta wuce tunanina. Ga iya kwalliya cas kamar
*yar birni, ga wani kallo da take yimin ko wata *yar birni me digiri bata iya ba. Hannah ta katse masa tunaninsa ta ce "Naga an doshi wata biyu ban ganka ba sai na shiga fargabar kode ciwon ne ya dawo maka. Haisam ya ce "Ciwo ya tafi kenan Insha Allahu tunda Allah Ya kawo min maganinsa. Hajiya ce dai ta hanani zuwa wai a rame nake tafi so in zo miki da kibata. Zaki fi murnar ganina wai. Hannah tayi dariya. Haka suka shafe fiye
da awa guda suna hirar so da kauna kowa na fadar kalmar da zata dadawa dan Uwansa. Yau jinsu suke kamar a aljannah suke dan zamannan da suka yi.
Daga karshe Haisam ya shaida mata cewar zasu tafi New York jibi shi da Ramlah zasu hado kayan lefenta kuma Ramlah ta ce ace mata itama Honey moon dinta ne wannan fitar don tunda suka yi aure ko Abuja basu taba zuwa tare ba kafin amarya ta zo itama taje
nata.
Shiga www.littafanhausane.com.ng domin karanta complete chapter 24
Hannah ta yi murmushi ta ce "To Allah Ya kiyaye hanya Ya dawo da ku lafiya. Haisam ya ce "Abunda za ki ce kenan? Hannah ta ce "Me zance wanda yafi wannan? Haisam ya ce "Kice asha hony moon a hado min lefe mai kyau. Kuma in cewa Ramlah in Allah Ya yarda kema za ki zo ki fita da angonki Hony moon lafiya.
Hannah tayi dariya ta rufe ido ta ce "A'a Yaya Haisam ka rufamin asiri karka fada mata haka ni na isa in fadawa Auntyna haka? Haisam ya ce "To meye Ramlah kanwa da kawa ta dauke ki, bata da wata hira da ta wuce tayi min hirarki shi yasa nake jin dadin hira da ita yanzu. Hannah tayi shiru tana tuno yadda Bello Madu yake yi mata. Hakika Ramlah tayi dabara a sannu zata samu soyayya a wajen mijinta kamar yadda Bello Madu ya fara samun shiga a wajena saboda kawai yana yi min hirar Haisam.
Haisam ya miko mata wata katuwar ambulan tasa
hannu biyu ta karba ya ce "Inji Ramlah ki rabawa *yan kungiyarku tunda kece shugabar kungiyar ashe.
Hannah tayi dariya ta ce "Ashe ka sani wa ya gaya maka? Ya ce "Ramlah ta bani labarin yadda kuka yi kakaf. Ya miko mata wata katuwar leda ya ce wannan nakine inji Ramlah. Ya miko mata wata kwalin waya mai tsada ya ce "Wannan wayar tafi da gidan kace zaki ga direction dinta a jiki da cherger in an kawo wuta ki dinga sawa a caji. Hannah tayi kasake tana kallonsa tana tunanin ya za'ayi ya bata waya a kauyen nan bayan babu service a garin. Haisam ya gane abun ya daurewa Hannah kai sai ya ce "Wannan wayar THURAYA ce tana yi a wajen da babu service dan haka duk sanda na bugo miki in dai da caji kuma a kunne take zan sameki ina fatan duk kinsan yadda za ki yi.
Hannah ta ce "Na sani Yaya, ai satin da nayi a Kano Amratu ta nunnunamin a tata. Kudi ne a shake a wata *yar jaka ya mika mata ya ce "Dallar America ce wannan saboda ban da kudin Niger amma Dalla za'a iya canjata a ko ina, ki dinga kashewa. Ki bawa Kawunki duk yadda kika ga dama a cikin kudin.
Kada ku sake ku sayi ko cokalin cin abinci na aure. Sabon gida nake gina muku mai bangare biyu naki dana Ramlah yadda kowa da bangarensa a sati ma wani ba zaiga wani ba. Idan kuwa kika bari suka suyo miki wani abu asararsa za'ayi. Turawa ne suke gina gidan, haka su zasu zuba kayan ciki irin kalar data dace. Bana son abinda za'ayi asararsa kinji.
Farin ciki mai hade da mamaki ya rufe zuciyar Hannah ta tsaya kawai tana kallon Haisam. Can tayi ajiyar zuciya ta ce "Yaya naga gidan naku ma mai tsananin kyau ne kuma sabo gashi da girma me yasa zaka sake gina wani? Yayi murmushi ya ce "Haka Ramlah ta ce ita ma in hada ku kada in warewa kowacce bangarenta ni dai a tsarina da ra'ayina naga gara in bawa kowacce bangarenta. Kuma
kinsan ko harshe da hakori ma ana sabawa ni kuma gani bani da hakuri idan naga za'a taba min *yar
kanwata Hannah, ina tsoratarwa da cewa zan iya kashe duk mai shirin jefata a cikin tashin hankali a rayuwarta.
Suka kyalkyale da dariya gaba dayansu.
Haisam ya mike tsaye yana shirin tafiya, Hannah ta durkusa gwiwowinta a kasa ta ce "Yaya na gode madallah Allah Ya saka da alheri. Sai ta fara hawaye shar daga idanuwanta ya ce "A'a Hannah kukan me kike yi ne? Kada fa in kasa tafiya in naga kina
kuka.Ya sa hannu a aljihu ya ciro wani farin hankici ya mika mata ya ce ta goge fuskarta kuma baya son ganin hawaye a fuskarta. Ta taso tana rakashi yana mata hira
mai dadi akan ta kwantar da hankalinta ba zai iya kaiwa wata biyun bama zata ganshi ya dawo.
Kuma ko da basa tare zuciyarsa na gareta. Direban da ya kawo Ramlah shine ashe ya kawo Haisam. Hannah ta ce "A'a ashe tare kuke kaki shigowa kasha ko ruwa ma?
Shehu ya ce "Ba komai suna da ruwa a mota. Ya durkusa har kasa ya gaishe da Hannah. Taga abincin
gwangwani iri- iri da lemon gwangwanaye ga robobin ruwan
swan nan a cikin motar sai taja bakinta tayi shiru. Don da har zata ce sai sun tsaya sunci tuwo. Taga masu cin irin wannan daula ya za'ayi su iya cin tuwon su miyar
kuka lami sai wake aka watsa a ciki. Haisam ya ce da direba ya bude but ya shigar da kwalayen da suke but din cikin zaure. Kwalayene manya-manya guda uku, makil suke da kaya. Daya na ruwan swan ne, daya na lemo iri-iri ne da kifin gwangwanaye da biskit da alawoyi karamin cikinsu kuma cike yake da kayan shafe- shafe na kwalliyar *yan mata, hoda, jan baki, mayukan shafawa a jiki dana gashi dana hannu. Daman Haisam mai son irin wadanan abubuwanne shi yasa ya siya mata mayukan gyara ta sake yin fes. Ga turarurruka designers abun baya misaltuwa tsadaddu.
Hannah ta langwabar da kai, ta rike murfin motar Haisam kuma na zaune a cikin motar gidan gaba. Yayin da Shehu direba ya tsaya can kofar gida yana jira su kare sallamar. Ta yiwa Haisam wani luguiguitaccen kallo cikin murya sanyayyiya ta ce "Yaya Haisam na gode. Ban san wacce kalma zanyi amfani da ita wajen nuna maka godiyata ba, tun ina karama kake fama dani har yau ba ka daina ba Ubangiji Allah Ya saka maka da alherin Sa. Ya ce "Kina bata bakinki wajen gode min, balle harki dinga tunanin kalmar da zaki yi amfani wajen nuna min godiyarki. Ni a tunanina duk abinda nayi miki dole ne a wajena ba sai kin gode
mun ba ki dauka aikina ne ai dole inyi miki. Hannah tayi dariya ta ce "Haba Yayana ni na fara saka haka a zuciya? na gode dai zance. Daga karshe suka yi sallama akan zai bugo mata waya. Yana tsokanarta wai yaga duk ta rame ko bata son aurensa ne, za'ayi
mata auren dole. Hannah ta kasa bashi amsar wannan tambayar ta bishi da kallo direba yaja motar suka tafi.
Yana dago mata hannu itama tana daga masa. Bata shiga gida ba sai da ta daina hango fitilar motarsu.
Kawu Ahmad da matarsa har sunfi Hannah mamaki da tsananin farin cikin wannan kyaututtukan na Haisam da matarsa. Raba dare suka yi kawai suna kallon dukiya suna sumbatu. Hannah kuma ta shaida musu cewar ya ce bai yadda a siya mata ko da cokali ba na kayan daki shi zaiyi komai. Nan Kawu Ahmad ya sake jin wani sabon farin ciki ya lullubeshi. Sai wajen sha biyun dare sannan Hannah da Kawunta da matarsa
suka shiga dakunansu don su kwanta. Hannah na shiga nata dakin ta jawo kofa ta bame sai kuwa ta dauko kwalin wayarta ta fara karanta yadda ake amfani da ita. Abun ka da Nasara ya rubuta
dalla- dalla yadda ake amfani da ita in har ka iya karanta turanci zaka fahimta nan take karfe daya dai-dai
aka kawo wutar lantarki. Hannah ta mike daga kan katifarta taje ta jona caja a soket ta jona wayar sai nan da nan taga ta fara caji. Murna ta rufeta ta koma ta kwanta. Taji bacci yaki zuwa sai tsananin tunanin Haisam. Ta ga da wannan kwanciyar da take tana ta tunani gara ta tashi tayi *yan nafilfili ta godewa Allah da Ya bata abin da ta dade tana nema.
Bayan tafiyar Haisam da kwana hudu. Hannah na kwance a dakinta misalin karfe goma sha daya na
dare taji wayarta ta hau kara ta zabura ta tashi zaune ta jawo wayar tana kallo taji bata daina karar ba. Sai ta ce a ranta ko Haisam ne yake kira. Ta jawo kwalin wayar da sauri ta sake karanta direction din taga inda ya kamata ta danna idan ankirata. Wayar dai ringin take ana sake radialling. Hannah ta dannan wajen da ya kamata ta dannan don amsawa.
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 25
Www.littafanhausane.com.ng
Murya ta ji ana cewa Hello Hannah, Hannah, ko
ba Hannah ba ce? Haisam ne. Hannah kiyi
magana mana ko bakya ji ne? Hannah ta
kyalkyale da dariya ta ce "Yaya Haisam kaine?
Haisam yayi dariya ya ce "Bakauyiya ashe kina
jina kina tsoron kiyi magana. Hannah ta gaishe
shi ta ce "Kwana biyu shiru banji kayi waya ba
kullum da ita nake kwana a kusa da ni wai ko
zaka kira cikin dare. Haisam ya ce "Oh I'am very
sorry tun shekaran jiya ban zauna ba ina zurga-
zurga a airport jiya kuma a jirgi muka kwana.
Hannah ta ce "Har kunyi tafiyar. Ya ce "Yanzu ma
muna London ni da Ramlah. Hannah ta ce "Lah
Yaya ina Aunty Ramlah take mu gaisa. Haisam ya
ce "Ramlah ta fita kasuwa kinsan da daddare aka
fi yin hidindimu a turai da kasashen larabawa.
Hannah lefen mu fa Ramlah ta tafi suyowa lefen
auran Haisam da Hannah fa. Hannah tayi dariya
ta rungume filo. Haisam ya kashe murya ya ce
"Banji kince komai ba Hannah ko daman auren
dole za'ayi miki bakya sona? Tayi fari ta yamutse
fuska ta ce "Cewa zaka yi ko na daina sonka ne
bawai ko bana sonka ba, tunda kasan ina... Sai
tayi shiru. Ya ce "Yaya kika yi shiru, da kina me?
Hannah ta ce "To ai shikenan a bar maganar.
Haisam ya ce "Ai sai kin karasa, so nake daman ki
fadi wannan kalmar shi ya sa na tsokano zancen
kina me? Hannah ta ce "To yanzu dai so kake inyi
rashin kunya Yaya da kunya ince ina... Ta sake
yin shiru bata karasa ba. Haisam yayi murmushi
ya ce "Hannah kenan aure fa zamu yi yaya za'ayi
aure da kunya ai da kin dan fara rarrageta kafin
in fizgeta gaba daya in yasar. To ni bari in fada
miki abin da nake so ki fadamin kika kasa.
Hannah ina sonki. Taji wani abu ya disa a ranta,
dadi ya lullubeta tayi ruf da ciki akan katifarta ta
dora kanta akan filo tana sauraron daddadar
muryarsa. Tayi shiru bata amsa ba ya ce
"Hannah, ko bakya jina? Cikin shagwaba da kashe
murya ta ce "Yaya ina jinka shirun da nayi wani
abune ya disu a zuciyata yake zagayawa ta
kwakwalwata nake kokarin warware abun da yake
kokarin ya cushe min. Ya lumshe ido ya ce
"Kamar yaya fa? Ta nisa ta ce "Ina cikin wata
matsananciyar soyayya wacce ta zame min ciwo a
raina na fara zama mutum mutumi, gangar jikina
na wani wajen zuciyata kuma tana wani waje. A
kullum kuma a koda yaushe ina sake-saken
wasikar jaki idan ina ido biyu, a bacci kuma ina
mafarkan da nake daukarsu tamkar tatsuniya. Sai
gashi a yau tatsuniyata ta fara zama gaskiya.
Shine nake tunanin shin a mafarki nake jinka ko
kuma a ido biyu? Haisam yayi murmushi ya
ringisa akan kujerar shakatawa da yake a bakin
swimming pool din wani katafaren Hotel da suka
sauka a london yake. Ya ce "Hannah this is real,
not a dream so our dream come true. I love you,
of cours I do. You mean much to me Hannah. I
missed you so much. Kafin Haisam ya rufe
bakinsa sai yaji muryar Hannah kamar daga sama
cikin sanyayyiyar murya ta ce "Yaya Haisam na
soka, ina sonka fiye da tunaninka fiye da duk
wani mutum a duniya. I love you so much. Ya
gyara zama ya ce "Hannah har fiye da tsohon
mijinki daya rasu, haba Hannah ko dai don kinga
ya rasu ne? Su duka suka kyalkyale da dariya
Hannah tama rasa irin amsar da zata bashi. Haka
Hannah da Haisam suka kasance suna hira mai
dadi har karfe biyun dare sannan suka yi sallama
suka ajiye waya. Kowannensu juyi kawai yake yi a
kwance don murna bata barsu sun iya yin bacci
ba. Kullum haka Haisam yake sai ya tabbatar
Hannah ita kadaice shima shi kadai sai ya buga
mata waya su kashewa junansu zuciya.
Bayan tafiyar Haisam da sati uku *yan uwan
Haisam maza suka zo neman auren Hannah suka
bada kudin komai da komai sadaki ne da lefe
kawai suka rage ba'a bayar ba. Murna wajen
Hannah da Haisam abin baya misaltuwa. Watan
su Haisam daya da sati biyu da tafiyarsu sannan
suka dawo. Cikin ikon Allah sai ga Ramlah tayo
tsarabar ciki, kowa murna yake musamman
Iyayen Haisam suna jin dadin yadda rayuwar
Haisam ta fara gudana kamar ta kowa. Duk inda
ka ganshi fara'a yake wasa da dariya da mutane
kamar yadda yake a da. Ga wata uwar kiba da
yake yi da fari baza kace wannan kashi da ran
bane. Ramlah ma kamar tafi Haisam samun canji
a rayuwrta saboda itama mafarkinta ya zama
gaskiya. Tana samun kulawar Haisam suna zama
suyin hira, suci abinci tare su kwanta gado daya, in
tayi kwalliya ya daga ido ya kalleta ya ce tayi
kyau. Wannan ba karamin canji Ramlah ta samu
ba. Mai hakuri yakan dafa dutse yasha romonsa
inji Bahaushe.
Bayan su Haisam sun dawo da kwana uku dangin
Haisam mata suka cika hadaddun motocinsu na
alfarma suka nufi Dashi garin su Hannah da lefe
da sadaki. Daman Hannah ta sanarwa da Kawunta
ranar da zasu zo dan haka suma suka kuke
suka harhada suka sissiyo kayan dadi suka
hadawa baki abinci da abin sha irin nasu na *yan
hutu. Harda Mahaifiyar Ramlah akazo danginta
wasu kawai dan suga Hannah suka zo. Cikin
rashin sa'a basu sami ganin Hannah ba don tun
bakwai na safe Hannah ta gudu ta tafi can garin
Magarya gidan wata tsohuwar Kakarta ta buya
don kunyar surukan take ji.
Dangin Hannah sai suka zama baki bude son
tsananin mamaki ganin yawan lefen Hannah
tunda suke basu taba ganin irin akwatinan nan ba
balle kayan dake ciki. Wasu runduma-runduman
akwatina ne masu santsi har guda shida bi da bi
ta karshensu *yar kit ce a dankare take da gwala-
gwalai da fassion mai tsada irin na turawa.
Leshina da shaddoji da kayan tsukewa abun
bazai misaltu ba takalma da jakunkuna hadaddu
mayuka kuwa da turarruka ba sai na zaiyana ba
daman can ya siyo mata balle yanzu, akwatinsu
suma daban. Iya Haule surukarta na wajen
karben lefen Hannah sai ta zama abun kallo wasu
kuma ta zamar musu abun dariya gaba daya saita
rikice ta hau surutai. Ita abun ya zamar mata
kamar wani rufa ido yanzu duk wannan kayan na
Hannah ne, yanzu Hannah ta dage ta tafi ta barta
tayi kudi kenan baza ta iya ganinta ba balle ta
sata aiki. Allah kenan haka Yake ikonSa. Ansa
ranar daurin aure sati biyu kacal suka ce kuma a
ranar suke so a zo a tafi da amarya ba sai an bata
lokaci ba. Daman sun taho da kudin sadakinsu da
kudin dinki duk suka bayar, makudan kudi suka
jifgewa dangin Hannah a gabansu. Wasu suka dau
kukan murna wasu suka rafsa buda suna kirari.
Dangin Haisam sunji dadin yadda aka tarbe su a
garin su Hannah. Kamar za'a hadiyesu anata yi
musu marhaban da wasa da dariya suka rabu
akan nan da sati biyu zasu dawo su tafi da
amaryarsu.
RANAR DAURIN AURE.
Ranar Juma'a ne ranar daurin auren Haisam da
Hannah da misalin karfe ukun ranar za'a daura
auren bayan sallar juma'a. Garin Dashi ya cika
makil da jama'a, taron da ba'a taba yin irinsa ba
a garin. Manya-manyan masu kudin Kano sun
halarci daurin auren Haisam, abokan Babansa da
*yan Uwansu abun sai wanda ya gani harda
gwamnan Kano na wannan lokacin ya halarci
wannan daurin auren. Dangin Hannah na nesa
dana kusa sun hallara, *yan garin kuwa da
wadanda aka gaiyata da *yan gaiyar sodi duk
sunzo su ganewa idanuwansu kar suji ana fada su
basu gani ba. Babu abinda zaka dinga hangowa a
garin sai wasu jifga-jifgan motoci bakake masu
bakin gilashi sai kuma fararen shaddoji da
tsadaddun yadika a jikin manyan masu kudin da
suka halarci daurin auren. Kamshin turare har
cikin gidajen *yan garin *yan jaridu tududu na
nan Nigeria dana Niger suna ta dauka a hoto da
bidiyo kaset. Ga Mahaifin Haisam dana Ramlah a
kewaye da jama'a. Haisam kuwa ko hangoshi ma
baza ka iya yiba saboda jama'a kowa so yake ya
gaisa dashi kowa yana so Haisam ya ganshi yasan
yazo don duk dangartakarka da Haisam ya ce
zaku bata in har baka zo masa wannan daurin
aure ba. Kafin karfe hudu har an shafa fatiha an
daura auren Haisam ya zama mijin Hannah.
Allah Ya bada zaman lafiya, *yan daurin aure
maza sun fara shiga motocinsu masu babura da
kekuna suma sun fara hawa suna kama gabansu,
anci, ansha lemunan gwangwani da ruwan kwalba
kudi aka dinga rabawa a wajen daurin auren.
Haka ango ya dinga danko kudi yana rabawa
mutane don murnar da yake ciki a ranar saida
Babansa ya ce ya isa haka sannan ya daina.
Maroka duk sun cika aljihunsu da kudi da goro da
alewa ga ruwan sanyi sun jika makoshinsu. Kowa
yana sanya albarka da fatan zaman lafiya ango da
amarya.
Bayan maza sun watse motocin da zasu dauki
marya da kawayenta da *yan uwanta don rakata
gidan mijinta suka karaso kofar gidansu Hannah
cikin gidan makil yake da mata ko Hannah baka
hangowa mai bidiyo kaset dakyar ya nemo
amarya ya haskata. Hannah ta caba ado da wani
rantsattsen leshi baki mai adon rawayar fulawa
tasa goggoro rawaya takalmi da jakarta baki.
Fararen hannayenta da kafafuwanta sunsha
fulawar lalle. Kirjinta da kunnuwanta da
hannayenta dambara-dambaran gwalagwalaine.
Babu abin da zaka ji idan ka matso Hannah sai
kamshin turaren wuta (Dukan) don tsuma da tun
ana saura wata guda auren, Kakarta ta dinga
tsumata ciki da waje abunka da Azbinawa sunsan
sirrin shirya amarya tayi tsaf ciki da bai. An dilke
fatar Hannah an gurjeta da kayan gayaran jiki
tayi sumul-sumul ta kara jawur. Abunka da
farare jawur jawur zaka dinga hangowa a cikin
gidan, gashi yalo-yalo har baya dangin Hannah
dai-daine bakake duk jajaye ne.
Motar da za'a dauki amarya tafi kowacce girma
da kyau. Hannah ta shiga ita da Hajir matar
Kawunta da sauran sa'anninta *yan Uwanta dan
ita bata da kawaye *yan Uwanta ne kawayenta.
Tsofaffi suka dinga duruwa sauran motocin kana
shiga sai kaji wani sanyi ya daki hancinka. A.C ce
ta gauraye motocin. Hatta manya-manyan bus
din da aka turo masu A.C ne da labulaye a
wundunan. Duk yawan motocin da Haisam ya
turo sai da wasu suka rasa saboda yawan jama'ar
Da suke so suje Kano suga gidan Amarya. Motoci
suka fara tafiya sai Hannah ta kece da kuka tana
dagowa mutane maza da mata hannu. Har aka
iso Kano Hannah kuka take su Hajir suna
lallashinta tayi shiru. Can ta tuna da Mahaifinta
dama ace yana nan da rai mana wannan daula da
tazo mata data taimaka masa, haka yayi
rayuwarsa har ya mutu a cikin talauci sai kuka ya
kece mata. Sai da magariba suka isa gidan
Amarya a wata Unguwar jigajigan masu kudin
Kano gidan Hannah yake mai suna Nassarawa
G.R.A Rigiji gafji Haisam ya tantsama gida duk
layin babu mai girman na Haisam da kyau. Aka
wangame jifgegen get din gidan motocin duk
suka shigo farfajiyar gidan, amma duk da haka ga
fili nan fetal wasu motocin ma fiye da biyar zasu
iya shigowa ciki saboda filin farfajiyar gidan
babba ne. Fulawoyi ne a shuke a jikin katangar
gidan ga tsuntsaye nan da dawisu da talo-talo a
zube a farfajiyar gidan suna ta shawagi. Sanyi
kalau ciki saboda wasu zagayayyun duwatsu aka
gina masu bulbulo da ruwa yana tashi sama.
Kasan da ake takawa abun a kalla ne balle cikin
gidan. Gidan bangare biyu ne iri daya ga wani
dankareren gida a tsakiyarsu. Sai aka nuna musu
gidan Hannah na gefen dama suka duru a ciki
wai! Wai!! Wai!!! Ai suna shiga ciki suka ga ashe
basu ga komai a waje ba. Sanyi da kamshi ne zai
fara dukan fuskarka sai walkiyar tiles da fitulu su
fara walle maka ido sannan ka fara cin karo da
kayatattun kujeru a wani katafaren falo ga wajen
cin abinci mai dauke da kujeru da tebur a
tsakiyarsu, gefe guda kuma wani falo zaka taka
wata matattakala tayi kasa shima a gefe. Ga
makeken kicin nan mai dauke da manya-manyan
furij da furiza ga cooker gas da kayan kicin gaba
daya koren launi ne aka hada. Hatta cokulan dake
kicin din koraye ne har lokokin kicin din.
Dakuna uku ne a gidan daya a kasa kowanne da
bandakinsa a ciki da gada dan kamfani da mudubi
da waduruf. Biyu kuma a sama makada-makadan
hadaddun gidaje ne yafi na kasa, suma da
bandakunansu a ciki da wani katafaren falo a
saman. Duk kusurwar gidan an ajijiye fulawoyi
irin na robar nan masu kama dana gaske. Ga
kayan kallo da na jin kida a faluka, kowanne daki
kuma akwai talabijin ana hada ta da tauraron dan
Adam (settelite). Tunda Hannah ta shiga gidan
kukan dadi take a zuciyarta kuma tana hamdala
tana yiwa Allah kirari tana gode maSa. Allah
Akbar. Karfe takwas dai-dai bayan duk sunyi
salloli sai Haisam yayiwa Hannah waya ya ce ta
shirya ita da kawayenta kawai banda tsofaffi da
yara zai turo motoci azo a dauke su matar
gwamna ta shirya musu liyafa a Tahir quest palace
har mutane sun fara zuwa tayi sauri. Hannah ta
shaidawa kawayenta nan fa duk suka fara shiri,
ita kuwa ta fada wanka ta fito ta tarar Haisam ya
aiko mota da wasu kaya da takalmi da jakarsu da
ribon duk kalarsu daya ya ce inji matar gwamna
ta ce ta saka. Kayan kansu abin kallo ne wata
shadda-shadda, leshi-leshi mai surfani riga da
zani anyiwa zanin kwalliya dankwalin kayan kuma
an nadoshi kamar goggoro irin kayan nan ne da
ake dinkowa daga Senegal to wannan na
musamman ne sai irin matan gwamnonin ne
suke siyansu. Hannah ta saka kayan nan ta tufke
gashinta da ribon kalar kayan ta dora goggoron
kayan bayan hoda da jagira da janbaki da tasha
tazo ta saka tsadaddun sarka da dankunne irin
kalar kayan, ga takalmi da jaka ta dana. Sai kowa
ya bude baki yana kallon kyawu daga Allah.
Hannah ta zama kamar wata tauraruwa mai
haske a cikin taurarin masu disasshe haske. Sai
walkiya take, Hajir ta fesheta da turarurruka
designer sai kawayenta suka take mata baya suka
fito suka shiga motocin suka nufi Tahir quest
palace dake Lamido cresent.
A bakin get din hotel suka iske Haisam da tulin
abokansa suna zazzaune akan motocinsu suna
jiran isowar su Hannah. Hannah na isowa suka
bude baki suna kallon ikon Allah. Ko a mafarki
basu dauka zasu ga amaryar Haisam kyakkyawa
kamar balarabiya ba. Musamman da suka je
daurin auren suka ga wannan kauyen sai duk
suka raina bikin suke cewa banda soyayya ma me
Haisam zaiyi da matan kauyen nan, a bayan
idonsa amma fa. Ashe wannan *yar kauyen ta
ninka matansu na birni haduwa. Suna ganin
Hannah kamar idan akayi mata Hausa baza ta iya
mayarwa ba tsabar babu wata surarta guda daya
data yi kama da Bahaushiya. Ta karaso ita da
kawayenta wajen da suke, tayi *yar
siririyar dariya ta duka kadan ta gaishe su duk
suka amsa. Haisam kam ko amsawama ya kasa yi
sai murmushi yake ya kura mata ido. Ya mika
mata hannu wai su gaisa sai Hannah tasa hannu
ta rufe ido. Abokansa suka hau cewa ai yanzu
Hannah amarya komai yazo karshe babu kunya
Haisam ya zama mijinki. Haisam ya diro daga
kan mota ya rike hannun Hannah abokansa da
kawayenta suka take musu baya suka dunguma
zuwa wani katafaren dakin taro (conference hall)
inda ake gudanar da liyafar, ashe jama'a jingim
sun taru isowar ango da amarya kawai ake jira.
Hall din haske ne tar kamar safiya ga wani sanyin
na'urar sanyaya daki wasu dogayen tebura ne
tafka-tafka a jejjere a cikin dakin taron jama'a
maza da mata a zazzaune. Kwalayen lemune da
kofunan tangaran da robar ruwa a gabansu, gefe
guda kuma masu kida ne da gangunansu a gefe
*yan police band suna dan kadawa a hankali kafin
a fara gudanar da biki. Hannah na shiga taga
idanuwa cununu akanta gaba daya an tsaya ana
kallonsu. Tebur guda Ramlah ce da kawayenta
hadaddun *yan boko duk sun zubo mata ido.
Hannah ta dago ta kalli Ramlah sai taga Ramlah
tayi mata murmushi itama ta mayar mata. Koda
kuwa ta hada ido da sauran kawayen Ramlah sai
taga harararta suke da kallon banza. Hannah ta
sunkuyar da kai kasa suka wuce hannunta gam a
hannun Haisam suka nufi kan wani kayataccen
dogon teburi akan wata matattakala (high table)
da kayatattun kujeru guda biyu irin na ango da
amarya. Anan suka zauna sannan kowa ya dau
tafi. Abokan ango da kawayen amarya suma suka
sami kujera suka zazzauna. Babban abokin
Haisam wani mai surutu mai suna Jibril (jibson)
shine yake jawabi a lasfika. Bayan ya bude taro
da addu'a ya ce ga matar mai girma gwamna nan
da tawagarta suna shigowa wacce ta hada wannan
taron itama tazo taya ango da amarya murna
kowa ya zauna yayi tsit ana kallon kofar shigowa
wadanda basu taba ganinta a fili ba suna so suga
yaya take a fili wadanda daman sun taba ganinta
suna so suga wanne irin kayane a jikinta
musamman mata masu tsegumi irinsuuuuu ana jira aga
wanne irin leshi yau zata saka, wacce irin jaka
kuma zata rike. Dan daman an san Uwargidan
mai girma gwamna akwai iya tsala kwalliya kuma
irin ta hadaddun *yan boko, ga gayu da kyau.
Hmmm GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter26
Mai girma Uwar gidan gwamna ce ta sako kafarta cikin katafaren dakin taron gefenta matar mataimakin gwamna ce daya gefen ta kuma wasu daga cikin matan kwamishinonin gwamna suma sun doshi goma bayansu kuma wasu mata ne guda biyu inyamurai suna tsaye da riga da suit da dan gajeren siket iyakar gwiwowinsu sune body guards dinta (S.S.). Dogon tebur guda aka ware mata da tawagarta. Suka zazzauna ita ce a tsakiya.
Kayan jikinta irin na Hannah sai kalarce ta ban-banta, na Hannah green ne na matar gwamna kuma komai nata pink ne. Hannah ta kalli matar mai girma gwamna ta sake kallonta sosai itama matar gwamna ta juyo ta kalli Hannah suka hada ido tayi mata murmushi. Hannah ta juya ta kalli Haisam taga shima kallonta yake sai tayi murmushi ta ce "Yaya amma matar gwamna nan tayi kama da wata kawata. Haisam ya ce "Kawarki Nusaiba ko? Ta ce "Ashe kaima ka gani wallahi sak Nusaiba Idris. Yayi murmushi ya ce "Ai ba kama bace Nusaiba ce cewa tayi kar in gaya miki sai dai kawai ki ganta. Hannah ta dafe kirji don mamaki tana cewa "Wayyo Allah yanzu wannan Nusaiba Idris ce ashe zan sake ganin Nusaiba a rayuwata?
Hall ya cika ya tumbatsa da hamshakan matan masu kudi a hankali Hannah ta dinga hango wasu daga cikin kawayensu *yan makarantarsu ta hango Rauda ma a zaune a gefen Nusaiba. Ta ce ashe Rauda zata girma tayi tsawo da kiba? Mai waqane yake cashewa, kannen Ramlah da Haisam suna cashewa su Amratu. Sai Jibril mai jawabi a lasafika ya ce a bawa amarya da ango fili su fito su cashe. Kowacce ta koma ta zauna. Hannah ta kalli Haisam shima yana kallonta taji wani nauyi yaya za'ayi ta fito tayi rawa ita da Yaya Haisam a matsayinsa na Malaminta wanda take matukar jin kunyar. Sai taji ya kamo hannunta suka mike gaba daya suka fara saukowa daga kan stage. Ramlah ta aika wani kaninta wajen masu kida ta ce police band ne zasu kadawa ango da amarya wakar sarmadan kauna in tayi dadewa mutuwa ce ke rabawa. Haka kuwa akayi police band suka saki kida da waka. Ango da amarya ne kadai a tsakiyar fili. Ango ya tsaya cak yana kallon Amarya, itama amarya a tsaye take ta daga kai tana kallon Haisam. Sai hawaye yake zubowa daga idanuwanta, yasa hannu yana goge mata. Sai shima hawaye ya fara diso masa. Sai Ramlah ta taso tazo tana zuba musu kudi abunka da mata sarakan bidi'a nan fa kowacce tana ji da kudi ta bude bakin jaka ta nufo fili don ta yiwa ango da amarya liki. Jiddah (Hidaya) aka fi kiranta dashi matar Yaya Habib ta fara tasowa filin ta dinga yiwa Ramlah liki da *yan dubu dai-dai dake aminiyar Ramlah ce sosai. Sai sauran kawayensu suka shigo fili suna likawa Ramlah kudi daga *yan dari biyar-biyar sai *yan dubu-dubu ita kuma Ramlah tana likawa mijinta da amaryarsa kudi. Matar gwamna Haj. Nusaiba ta dinga liki ai kuwa police band da suka ga ruwan kudi sai suka saka himma suna sake dukan ganga. Lallai biki yayi biki Hannah ta rungume Nusaiba da Raudah sai hawayen farin ciki suke yi. Ba'a tashi daga taro ba sai karfe daya da rabi na dare. Bayan anci ansha an cashe.
Kwanan dangin Hannah biyu a gidan amarya kawai suna shakwatawa sai da Kawu Ahmed ya aiko ya ce maza-maza su hado su dawo su dukkansu kar a rage kowa sannan suka tarkato suka tafi ba'a son ran su ba. Hannah kuka suma kuka suka shiga motoci suka tafi. A hanya ne dangin Hannah suke yiwa Iya Haule habaici ganin duk jikinta yayi sanyi ganin Allah Ya sakawa Hannah da gidan tangaran ma bana suminti ba. Wata Kakar Hannah ce ta fara cewa "Allah Ya bawa Hannah gida, gida kamar ba'a duniya ba. Wata ta sake cewa "Oh harda ake tada jijiyar wuya wai baza akai Hannah gidan sumunti ba ashe gidan tangaran ma Allah zai bata. Sauran suka tsoma baki suna yabawa Inna Haule magana. Innah Haule tayi tsuru-tsuru a zaune a mota tasan da ita ake tasan tayi kuma ba sharri akayi mata ba.
Suna tafiya masu aiki mata suka shigo bangaren Hannah suka hau kalkalewa suka wanke ban dakuna suka shisshinfida sababbin zannuwan gado suka feshe gidan da turarurrukan kamshi. Wani kuku ne a kicin yana ta shirya mata abinci kala-kala. Hannah tayi kuri a zaune a katafaren dakinta dake sama ita kadai sai talabijin ta rasa meke damunta murna take ko bakin ciki. Taji ana kiran sallar magariba sai ta tashi ta shiga ban daki ta dauro alwala tazo ta shimfida abin sallah tayi sallar magariba da nafilfilin data saba. Ta zauna tana lazumi har sai da taji ana kiran sallar isha'i sannan ta tashi ta kawo sallar isha'i. Ta idar tana linke abin sallar ne taji wayar dake ajiye a gefen gadonta tana kara ta dauka a hankali gami da cewa Hello, sai taji muryar wani bagware ne turanci yake yi ya ce, "Madam nine kukunki daga kicin nake yi miki waya na gama abinci na jere miki a kan darning table zan iya tafiya babu wani abu da za'a dafa miki? Hannah taji wani abu banbarakwai wai namiji da suna Zainabu. Abu na farko daya bata mamaki wai yau ita ce Madam ake shaida mata an gama abinci tazo ta ci kawai in harma akwai wani abunda take so a dafa mata ta fada. Mamaki na biyu kuma shine yaya za'ayi a bar garjejen Namiji bama Bahaushe bane ya shiga gidan matar aure yana dafa mata abinci daga ita sai shi wannan ba tsarin Musulunci bane. Hannah ta ce zai iya tafiya babu wani abu da zaiyi mata. Taji motsin bude kofarsa ya fita. Ta zauna a gefen gado tayi shiru tana tunani. Can ta tuna ashefa yanzu ita amarya ce, kuma tunda babu kowa watakila Haisam ya shigo bari taje tayi wanka ta sake tsala kwalliya irin ta matan da suka san darajar mazansu. Tayi sauri ta fada ban daki ta dinga salla wanka ga sabulai nan kala-kala har dana ruwa. Tana fitowa ta zauna akan mudubin dake shake da kayan shafe-shafe ta fara rangada kwalliya da fesa turarurruka duk jikinta. Tasha hoda da jan baki da gazal ta zubo gashin kanta har baya bata tufke ba ta barshi bazar. Ta saka wani dogon siket na jeans da wata *yar yaloluwar riga bulawus mai dogon hannu da dan budadden kirji. Tasa wani takalmi marar nauyi mai kama da sosan katifa ta fara saukowa daga kan benen.
Tana isowa babban falon da ke kasa sai taji wayar da ke ajiye a falon tana kara. Hannan ta karasa kan teburin da wayar take a ajiye tasa hannu ta dauka sai taji muryar Ramlah ce take fara'a ta ce "Hello amarya yaya kadaici ke kadai yau kowa ya watse an barki ko? Aiya don't worry haka rayuwar aure take sai a hankali zaki saba. Amma yau bazan barki ki kwana ke kadai ba zan kawo miki mai taya ki kwana gamu nan zuwa. Hannah tayi murmushi ta ce "Aunty Ramlah ina yini. Ramalah ta ce "Lafiya kalau kanwata gamu nan ma zuwa sai mu gaisa sosai. Suka ajiye kan waya. Hannah tayi jigum a tsaye tana mamakin yadda Ramlah take fara'a da nuna mata so da kauna ta ce a ranta "Allah kenan, ya hadani da duk abinda zanji sanyi a rayuwata. To wa Aunty Ramlah zata kawo mun ta taya ni kwana ina jin Amratu ce kai ko dai Haimsa ne? Hannah ta dubi matsattsun kayan dake jikinta taga gaskiya baza ta iya sakewa ba a gaban Haisam. Sai ta koma sama ta dora doguwar riga baka mai dan kwala kafin ta sauka sai taji muryar Ramlah tana sallama a falon kasa. Hannah ta sauka tana rangwada ta karaso wajen da Ramlah da Haisam suke tsaye tayi dariya ta ce "Sannunku da zuwa kuzo ku zauna. Suka zazzauna dukkan su fuskarsu cike da fara'a. Hannah ma ta zauna a kunyace ta gaishe suka amsa. Ramlah ta ce "Munzo muci abincin don yau anan zamu ci abinci in tayaku hira in tafi in barku, ko baki yi abincin damu bane? Sai a lokacin Hannah ta dubi dinning table taga katan teburi cike yake da manyan food flask din abinci tayi murmushi ta ce "Aunty na isa in ki yin abinci daku, da ku aka yi. Suka mimmike suka nufi dinnin area. Haisam ne a tsakiya Ramlah a gefensa na hagu, Hannah na daya gefen, suka fara zuzzubawa a filet suna ci suna hira. Ba sosai Hannah da Haisam suka cika magana ba, Ramlah ce take ta zuba surutu suna jinta suna satar kallon junansu. Bayan sun kammala suka dawo kan kujerun falo suka zazzauna suna kallon wani fim da ake yi a sonny. Haisam ne a tsakiyar kan doguwar kujera Hannah na gefensa Ramlah na daya gefen nasa duk a doguwar kujerar suke.
Haisam ya nisa yayi gayaran murya ya ce "Uwar gida Ramlah tare da amarya Hannah babu abinda zance daku sai godiya. Ina fatan alheri a rayuwarmu gaba daya ina fatan Allah Ubangiji Ya bamu zaman lafiya. Ramlah ke ce babba kuma alhamdulillahi kin nuna halin manya kinyi mana halacci babu abunda zance miki sai Allah Ya saka miki da alheri da gidan Aljannah. Ramlah kin kasance mai tsananin hankali da tunani dan haka don Allah ina rokarki da kici gaba da yadda kika fara kici gaba da nunawa kanwarki kuma abokiyar zamanki Hannah kaunar da kike nuna mata kada ki saurari mazuga masu zuwa suyi zuga don su hargitsa ma'aurata. Ramlah tayi murmushi ta ce "Haba Haisam ya kamata ka fahimceni idan nasa raina nace zanyi abu gaskiya babu mai zugani in fasa. Ina sonka da yawa naga ya dace in so duk abunda kake so don haka naji har raina ina son Hannah musamman na lura Hannah nada ladabi da son zaman lafiya, insha Allahu zamu zauna lafiya. Haisam ya juya ya kalli Hannah wacce kanta yake a sunkuye a kasa tana wasa da dan yatsanta yayi murmushi ya ce "Amarya ke baki ce komai ba. Hannah ta dago kai tayi murmushi ta ce "Insha Allahu zamu zauna lafiya zan zama mai yin biyayya a gareku kuma ni tsakanina daku sai godiya Allah Ya saka da alheri. Ramlah da Haisam suka amsa da "Amin. Ramlah ta yunkura ta mike tsaye fuskarta cike da fara'a ta kalli Haisam ta juya ta kalli Hannah ta ce "To amarya da ango zan tafi in barku sai da safe. Haisam ya ce "Uwar gida tafiya zaki yi bari mu raka ki har gidanki ko? Hannah ta mike suka dunguma suka fita suka nufi bangaren Ramlah. Haisam na tsakiya suna tafe suna hira har kofar shiga bangarenta suka raka Ramlah, Ramlah tayi murmushi ta ce "Rakiyar ta isa haka ku koma ni dai gudunmawata da zan baku anan ita ce na bawa kanwata kwana goma da angonta ku huta sosai. Hannah tayi murmushi ta sunkuyar da kai ta ce "A'a Aunty Ramlah kwana biyu ya isa. Haisam ya harari Hannah ya ce "Maimakon ki yi godiya shine kike ki har guduna kike? Su duka suka tuntsire da dariya. Ramlah ta juya ta shiga gida ta ce "Ni dai na barku lafiya sai da safenku. Tana shiga ta turo ta rufe tasa mukulli ta bame sai ta sulale ta zube a kasa yayin da wani zazzafan hawaye ya dinga zubo mata tsananin kishi ya kamata saboda tana son Haisam matukar so babu yadda ta iya dole taso abunda yake so. Hmmmm Kishi kumallon Mata, uhm.
Haisam da Hannah suka juya suka nufi bangaren Hannah, suna tafiya a hankali suna hira. Haisam ya kai hannu zai rike mata hannu sai yaga ta goce tayi gefe. Haisam yayi murmushi ya ce "Allah Ya baki hakuri Hannata na fasa rike miki hannu tunda rowa kike min. Suka shigo cikin gida Haisam ya jawo kofar falon ya datse. Haisam ya ce da Hannah "Zo muje sama muyi sallah. Hannah ta langwabar da kai cikin siririyar murya ta ce "Yaya nayi sallar isha'i tun dazu. Haisam yayi murmushi ya ce "Ai nafila zamu yi. Ta mike kanta a sunkuye a kasa ta wuce gaba Haisam na biye da ita suka hau sama. Daki Hannah ta wuce kai tsaye ta shiga ban daki. Haisam kuma sai ya shiga daya dakin yana shiga sai ya cire kayansa ya daura tawul ya shiga ban daki don ya sake watsa ruwa a jikinsa bayan yayi wankan ne ya dauro alwala yana fitowa ya wuce wajen katuwar waduruf din dake dakin ya bude wani bangare kayan sawarsa ne da kayan bacci. Ya zabi wasu kayan bacci masu kyau da laushi tubus auduga ne zalla riga ce gajeriya iya cinya mai dogon hannu da dogon wando farare ne sol anyi musu fulawa da kalar shudi sababbine gar a ledarsu ya ciro ya saka a jikinsa ya juya ya nufi wajen mudubi wanda aka dankareshi da mayukan shafawa da mayukan nan masu kamshi kana ya feshe duk ilahirin jikinsa da tufafinsa da tsadaddun turarurruka masu masifar kamshi wannan na cewa wane wannan suka hadu suka bada wani daddadan kamshi. Haisam ya dauko comp ya taje gashinsa ya mulke da man gashi sai kamshi, hakika ko shi da kansa yasan yayi kyau a daren nan balle wacce yayi dominta. Ya fito ya nufi dakin da Hannah take zaune gefen gado ya ganta tayi shiru tana jiransa. Yayi sallama ya shigo ta dago ta dube shi suka sakarwa juna murmushi ta amsa masa cikin sanyayyiyar murya. Ya ce "Oh sorry my love na barki kina jirana ko? Tayi murmushi ta ce ba komai ai baka dadeba. Ya bude wadruf ya dauko wata katuwar sallaya ya shimfida ya juya ya kalli Hannah to Bismillah zo bayana ki tsaya zamu yi sallah raka'a biyu ta godiya ga Allah da Ya nuna mana wannan ranar da muka zama miji da mata da kuma yin addu'ar Allah Ya kade mana duk wata fitina Ya bamu zaman lafiya da zuri'a ta gari ko ba haka bane? Hannah tasa hannu ta rufe ido saboda murna da farin cikin daya rufeta da kunya ta ce "Haka ne Yaya.
Bayan sun idar Haisam ya daga hannu sama yana kwararo addu'oi Hannah na amsa masa da amin daga karshe suka shafa. Haisam ya juyo yana kallon Hannah kallo mai kunshe da tsananin soyayya da sha'awa ji yake tamkar ya hadiyeta a daren yau. Ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi mai hade da kunya. Ya nisa ya ce "Zo nan kusa dani Hannah. Ta matso kusa dashi ta zauna, ya ce "Nan kusa dani zaki matso sosai. Ta sake matsowa daf dashi ta zauna yasa hannu ya shafa gefen fuskarta a hankali har zuwa gefen wuyanta yayin da dankwalinta ya sulale zai
Shigo cikin www.littafanhausane.com.ng domin qarisa karanta chapter26
fadi kasa tayi sauri taja dankwalin ta daura ta dan ja da baya. Yayi murmushi ya ce "Ja da baya ma kike? Naga dole ki cire wannan bakar doguwar rigar da dankwalin ki saka rigar barci ko dasu zaki kwana? Hannah ta gyada kai ta ce "Da su zan kwana. Haisam yayi dariya ya mike yaje ya bude wadruf ya zabowa Hannah wata tsaleliyar rigar bacci. Rigar *yar karama ce iya gwiwa yaloluwa marar nauyi mai shara-shara, kalar pink ce anyi mata kwalliya da wani gashi mai laushi a kasan rigar da wuya, hannun rigar dan siriri ne wanda za'a iya daureshi ko a kwance. Ya ciro ta daga leda ya mikawa Hannah ya ce "Ina ganin gara kisa wannan zaki fi jin dadin bacci tunda bata da nauyi. Hannah ta karba ta daga rigar don taga yaya girman rigar take, sai taji gabanta ya yanke ya fadi saboda ita a gaskiya tana jin nauyi da kunyar Yaya Haisam yaya za'ayi ta iya sa wannan *yar riga a gabansa. Tana son Haisam matuka amma bata jin zata iya kwana a gado daya dashi zuciyarta ta tuno mata yadda Haisam yake da girma da kima a idanuwanta tamkar wani Kawunta take ganinsa saboda dawainiyar da yasha da ita tun tana yarinya. Haisam ya ce "Tashi ki saka ko inzo in taya ki balle maballin. Hannah ta ce "A'a, ta tashi ta mike ta tafi can lungun gado ta cire dankwalin rigar ta cire doguwar rigar sai matsattsen siket da rigar da suke jikinta (boody hook). Haisam ya koma kan kujerar da take gaban madubi ya zauna yayin da idanuwansa suke tsaye cak a kan Hannah, ta juyo ta dube shi taga ita yake kallo sai ta dauki rigar baccin ta nufi bandaki. Haisam ya ce "Ina za ki kuma? Cikin kunya kanta a sunkuye a kasa ta ce "Ban daki zanje in canja. Haisam ya bude baki zaiyi magana sai wayarsa ta fara kara. Hannah ta fada bandaki ta rufe kofa tasa makulli ta bame. Ya duba yaga mai yi masa waya sai yaga Safiyanu ne abokinsa daga Kaduna. Ya danna ya ce "Safiyanu yaya kake? Safiyanu ya kyalkyale da dariya ya ce "Daman na bugo ne don inyi tsokana in dami ango da amarya. Haisam yayi dariya ya ce "Babu kyau fa zaka dauki alhaki. Safiyanu ya ce "Tunda baka yi barci ba yanzu taimaka ka dubo min lambar Shafi'u na Dubai da kace saika zauna, yi hakuri ka bani yanzu saboda gobe fa zan tafi Dubai ina so in neme shi idan naje can. Haisam yayi ajiyar zuciya ya ce "Safiyanu ban da kaine wallahi da bazan fita ba a yanzu sai na je mota fa sannan zan dubo maka a diaryna. Safiyanu ya ce "Na sani abokina taimaka min nasan abun is not easy ango danye sharab kamar ka, ka fita kabar amarya at this late hours sorry dan Allah, ka mika min gaisuwata zuwa ga kanwata Hannah. Suna hira a waya Haisam ya bude kofar dakin ya fita ya sauko kasa ya bude kofa ya nufi wajen da motoci suke.
Bayan Hannah ta shiga ban daki sai ta fada wanka ta fito, ta saka rigar ta dubi kanta a madubi ta ganta tamkar wata baturiya rigar tayi matukar yi mata kyau har da wani ribon na daure gashi a sakale a jikin rigar. Hannah ta daure gashinta dashi. Ta sake kallon kanta a jikin mudubi sai taga duk ilahirin jikinta tana gani a cikin rigar sai ta girgiza kai ta ce a ranta gaskiya bazan yarda Yaya Haisam ya ganni a haka ba. Ta tsaya tayi shiru a bandaki tana tunanin yadda za'ayi ta fito a haka. Ta bude wata lokar gilas dake makale a jikin bangon ban dakin sai taga abubuwa ne kala-kala na gyaran baki, masu sa baki yayi kamshi, huci yayi wasai. Ta fara karanta jikinsu daya bayan daya don ta sanin amfaninsu da yadda za'ayi amfani dasu. Bayan tayi brush sai ta shiga daukar kowannesu tana amfani dashi. Na kuskure baki ta kurba ta kuskure na fesawa ta fesa. Sai da ta dauki tsawon minti goma sha biyar tana abu daya. Da ta gama sai tazo ta bude kofar a hankali ta leko sai taga Haisam baya nan, ta fito daga ban dakin ta sake duba ko ina Haisam baya nan taji dan sanyi a ranta don da fargaba da kunya sun isheta. Ta nufi gaban madubi, nan fa ta zauna tana rangwada kwalliya shafe-shafe da feshe-feshen turare. Hannah ta kalli kanta da kanta tasan dole ne ma yau Haisam ya rikice saboda tayi kyau sosai.
Hmm su Hanna sarakan iyayi GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter27
Bayan ta gama kwalliyar ne ta tashi daga gaban mudubin, ta tsaya cak a tsakiyar dakin tana shawarar yadda zata yi. Shin ta hau gado ta lulluba ne? Ko ta datse kofa da mukulli tayi kwanciyarta
ne, ko kuma ta koma ban daki ta rufe kanta ne? A gaskiya Yaya Haisam ba zaiji dadi ba, ita kuwa bata son ta bata masa rai ko kadan a rayuwarta saboda Haisam bai taba bari wani ya bata mata rai ba balle shi da kansa burinsa kullum ya faranta mata ya ganta cikin farin ciki. Ji tayi burum ya bude kofa ya shigo, ta tsorata taja da baya. Haisam ya kura mata ido yana yi mata murmushi ya tura kofar dakin ya rufe da mukulli ya nufo inda Hannah ke tsaye a hankali. Yasa hannhu biyu ya jawota kan kirjinsa ya rungumeta tsam yayin da dukkansu zuciyoyinsu suka hau bugawa a lokaci guda kowannensu yana
jin yadda ta danuwansa ke bugawa don tsananin farin cikin da suka tsinci kansu a wannan lokaci.
Kowannensu kwakwalwarsa na kokarin ta tantance masa shin da gaske ne ko kuwa mafarki suke yi. Hannah ta dago da kanta a hankali ta kalli Haisam don ta tabbatar shi din ne kuwa, dai-dai lokacin shima ya dago yana kallonta don shima ya tantance tunanin da yake irin na Hannah ne. Cikin sanyayyar murya Haisam ya ce "Hannah kece kuwa
ko mafarkinki nake yi kamar yadda na saba yi kullum? Da kyar ta iya magana ta gyada kai ta kashe ido ta ce "Abun da nake so in tabbatar kenan don nima ina kokonto a zuciyata. Kafin ta rufe bakinta sai taji bakinsa cikin bakinta. Nan da
nan ta sulale ta tsuguna a kasa tasa hannu ta rufe fuskar ta. Haisam ya tsuguna a gabanta yasa hannu ya dago da fuskarta yayi mata kallon ido cikin ido ya ce "Kada ki manta ada GANGAR JIKINKI bata tare da ni RUHINKI ne yake tare da ni, amma a yanzu GANGAR JIKINKI DA RUHINKI suna tare dani don haka karki ji nauyina ni mijinki ne. Ya mike tsaye ya jawo hannunta ya tasheta tsaye suka zubawa juna ido. Ta kashe ido cikin zazzakar murya ta ce "Kaine farin cikina, abun yardata, abun
alfaharina abun da nafi so a rayuwata na mallaka maka zuciyata tuntuni a yanzu kuma na mallaka maka GANGAR JIKINAAAA. Ta dora kanta akan kirjinsa ta lumshe ido yayin da shi kuma yasa hannunsa daya ya rungumeta yasa daya hannun yana shafar lallausan gashin kanta. Hakika ma'auratan nan yau sun fi kowa farin ciki a rayuwarsu jinsu suke tamkar ba'a cikin duniya suke ba domin a wannan duniyar tamu akwai bacin rai su kuwa basa ji, ana ciwo su kuwa sumul suke ji sai tsantsar farinciki da yake nukurkusarsu. A tsakiyar gado Hannah ta jita yayin da Haisam ya shiga sumbatarta, yana sinsinar kamshin da takeyi, yana lasar duk ilahirin sassan jikinta. Sai a yau Hannah tasan tayi aure kuma ta sami tsantsar soyayyah har dama yadda ake yinta, ashe Bello Madu shafar mai yake yi mata bai san yaya ake yin soyayya ba. Kuma shima Haisam sai yau yasan yayi aure don da zuciyarsa a dagule take hankalinsa a tashe yake idan yana tare da Ramlah!!!
shi kansa bai san sanda yake yiwa Hannah wasu abubuwan ba sun raya daren yau sunna.
Yau ango da amaryarsa idanuwansu basu ga barci ba. A kunnensu aka kira assalatu. Dakyar da sudin goshi Hannah ta samu ta zare jikinta daga jikin Haisam don ya cukukuiyeta ya rungume ta kam kamar zai fasa kirjinsa ya zurata a ciki. Hannah ta mike da kyar saboda duk gabobinta sun jigata, ta
shiga ban daki tana shiga ta sakarwa kanta shayar ruwan zafi ta dai-daita ta surka da ruwan sanyi daidai wanka. Bayan ta gama wanka sai ta daura alwala ta fito sai Haisam ma ya shiga. Bayan ya fito ne sai ya saka wata doguwar riga Hannah kuma ta saka bakar doguwar riga mai dan kwali suka yi
jam'i suka yi salla. Ba su bar kan sallaya ba sai da gari yayi haske kamar karfe bakwai na safe suna lazimi da hailala da hamdala ga Ubangijinsu Sarkin Sarakuna daYa basu dama da ikon yin aure. Saboda suna tsananin kaunar junansu. Hannah ta mike tabar Haisam a zaune yana jan carbi ta fita ta sauka kasa ta shiga kicin. Butar ruwan zafi ta jona ta cika flask saita fasa kwai da yawa ta soya waina masu kaurin gaske ta zuba a faranti ta debo ta hau sama..
A kwance akan gado taga Haisam har ya fara dan bacci, bude kofar da tayi ne ta tashe shi. Ya daga ido ya dubeta sai yayi murmushi ya ce
"Daman kicin kika shiga da sassafen nan. Hannah tayi dariya tazo ta ajiye katan faranti me dauke da plate din wainar kwai da flask din ruwan zafi. Ta sake fita ta dauko wani faranti mai dauke da kofuna biyu da cokula kanana da madara, suga da millo ta zo ta ajiye a kusa da farantin farko, ta karaso wajen gado inda Haisam yake kwance ta durkusa har kasa cikin sassanyar murya ta gaishe shi, ya makale murya yana kwaikwayon maganarta ya amsa. Su duka suka tuntsire da dariya. Haisam ya tashi zaune ya zuro kafafuwansa kasa daga kan gado ya jawo Hannah a jikinsa ya ce "Hannah ai yanzu nafi karfin gaisuwar ina kwana Yaya a wajenki. Kinsan irin gaisuwar da zaki dinga yimin?
Hannah ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba. Ya ce "Duk sanda zaki gaishe ni idan ni dakene sai kizo ki tsotsi bakina ki rada mun a kunne gaisuwar, idan kuma da mutane a wajen sai ki mika min hannu mu gaisa.
Irin wannan gaisuwar zaki dinga yiwa Yayarki Ramlah ki mika mata hannu kuyi musabaha sannan ku gaisa. Hannah ta ce "Zanyi yadda ka ce insha Allah. Yayi murmushi ya ce "Na gode my love, af na manta ban tambaye ki ba yaya jiya? Hannah ta rufe fuska da tafikan hannunta ta ce "Shi yasa naga ya dace kasha ruwan tea da sassafen nan saboda na ga ka gaji. Haisam ya harareta ya ce "Au nine ma na gaji banda ke? To gobe ko ruwan tea din ma baza ki iya tashi ki dora ba ni da ke zanga wanda zai iya motsi da safe, ai tausayinki naji yau. Hannah tayi dariya ta ce "Yi hakuri dan Allah ni ba haka nake nufi ba.
Bayan sun gama karin kumallo ne suka koma kan gado suka kwanta. Hannah na kwance akan kirjin Haisam tana shafawa a hankali yayin da shi kuma yake shafar gashinta da gefen fuskarta ya zuwa
wuyanta suna hira mai dadi har barci mai dadi ya sure su, kowannensu ya dora da mafarkin dan uwansa. Basu tashi farkawa ba sai karfe biyu saura kwata ana sallar Azahar. Bayan sunyi wanka sun caba ado sunyi sallah sai Haisam ya kama hannun amaryarsa suka nufi bangaren Ramlah wacce tuntuni tasa an shirya musu abinci kala-kala da yake tasan anan zasu dinga cin abincin rana dana dare saboda Haisam ya dakatar da Kukun Hannah sai nan da sati biyu sannan zasu zo suci gaba da yin abinci kada suzo su dame su, su rage musu wani bangare najin dadi.
Ramlah na ganinsu ta taso da fara'a da murna ta rungume Hannah sannan ta rungume Haisam ta sumbaci kumatunsa ta ce "Kun tashi lafiya? Suka amsa mata da "Lafiya kalau. Ta kaisu wajen katafaren teburin cin abinci mai dauke da nau'ikan girke-girke kala-kala. Suna cin abinci suna hira suna tuntsira dariya kai kace gidan biki ne. Haisam ya iya surutu da hira haka Ramlah ma tana da magana Hannah ce dai sai tayi da gaske tunda ita ba gwanar surutu bace. Tana jinsu suna ta surutu sai dai tayi dariya idan na dariyane idan kuma Haisam yayi mata tsiya Ramlah ta shigar mata tana tare mata don ita bata iya surutu ba sosai kuma ko ba haka ba tana ganin Haisam da Ramlah da wata kima da girma a wajenta don haka take jin nauyin tayi ta shiga hirarsu da zolaye-zolayen da suke yi,
da suka gama cin abincin sai suka koma kan kujerun falo suna kallo. Haisam da Ramlah akan doguwar kujera suke a zaune, Hannah kuma na wata kujera a gefensu. Suna kallon kaset din bikin Hannah da Haisam na shagalin da aka yi a Tahir Guest wanda dan asharalle, boda da police band suka cashe. Ango da amarya aka dallaro a tsakiyar fili yayin da suka kurawa junansu ido Hannah na hawaye a kaset din. Ramlah tayi ajiyar zuciya ta ce "Soyayya. Haisam ya dan harareta ya ce "Meye wani soyyaya. Ramlah ta tuntsire da dariya ta ce "Meye to abin hararar don nace soyayya? Kawai cewa nayi soyayya masoya na gani. Haisam yayi murmushi ya ce "Nasan da magana a bakinki haba Ramlah kece fa, nasan halinki sarai. Tayi dariya ta ce "Da dai zance wani abu amma na fasa tunda har kasa a ranka zance wani abu. Haisam ya jawo hannunta
ya murde ya ce
Shiga nan www.littafanhausane.com.ng domin karanta complete chapter 27
"Saikin fada zan sake ki. Hannah tayi murmushi ta ce "Yaya Haisam karka karya mun Aunty na fa. Ramlah tayi dan kara ta ce "Yallabai yi hakuri sake ni zan fada maka. Haisam ya sakar mata hannu ya ce "To fadi ina saurarenki. Ramlah ta gyara zama ta dube shi tayi murmushi ta ce "Kafin in fadi abinda zan fada don Allah zanyi muku *yan tambayoyi zaku amsa mun? Haisam ya ce "Zamu amsa miki yaya zamu yi tunda Allah Ya hadamu da *yar jarida. Ta juya ta kalli Hannah ta ce "Kefa kanwata idan na tambayeki zaki bani amsa tsakani da Allah, akwai abunda
nake so inji ne sai in hada in fadi abun da yake raina. Hannah tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa ta ce "Mai zai hana in baki amsa Auntyna zan amsa duk abinda na sani, insha Allah. Ramlah ta jawo lokar jikin centre table ta dauko wani dan littafi da biro ta ce "Yallabai ta kanka zan fara tambayoyin. Ya gyara zama ya ce "Ina jinki, sharadi daya idan kika yi min karkatacciyar tambaya saina kara murde miki hannu. Ramlah tayi dariya ta ce "Na yarda, tambaya ta farko ita ce zaka iya gaya mun yaushe ka fara son Hannah a zuciyarka.
Hannah ta juyo ta kurawa Haisam ido tana son taji amsar da zai bata
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter28
Haisam yayi shiru can yayi murmushi ya dago ya kalli Hannah ya juya ya kalli Ramlah ya ce "Tun ranar dana fara ganin Hannah naji ta kwanta mun a raina a matsayin *yar yarinyar daya kamata in taimakawa a hankali kuma sai naga tana da hali nagari kamar ladabi da biyayya, kunya, tawakkali, hakuri sanin ya kamata, tsafta, tausayi da dai sauransu sai naji tana sake shiga raina amma bazan ce a lokacin soyayya nake yi mata ba saboda yarinya ce.
A hankali kuma naji Hannah ta hau wani matsayi a zuciyata wanda ya wuce sabo ya zama idan tunani nake tunaninta zanyi haka kuma idan ina hangoni da matata ta aure sai in hango Hannah,
daga nan kwakwalwata ta tantance mun son Hannah nake saina danne shi a zuciyata na kasa
furtawa, saboda wasu dalilai nawa masu karfi.
Haisam da Hannah suka hada ido suka yiwa juna murmushi. Ramlah tayi ajiyar zuciya ta ce "Na gode
sai tambayata ta biyu. Kana tuna Hannah a zuciyarka kamar sau nawa a rana?
Haisam ya ce"Ko ina ganin Hannah ko bana tare da ita koda yaushe ina tunaninta. Ramlah ta ce "Ita tsohuwar abokiyar zamanka meye matsayinta a zuciyarka tsakaninka da Allah. Su duka ukun suka tuntsire da dariya. Haisam ya ce "Ita Aunty Ramlah da farko
bana ra'ayin soyayya don ni har kunya nake ji idan aka ce ina da budurwa daga baya naga lallai-lallai
Aunty Ramlah na sona da gaske sai naga ya kamata in aureta. To akasin da aka samu har ta bani haushi shine da naje na durkusa har kasa ina rokarta tayi min izini in auri Hannah taki. To shine nima na toshe mata hanyar walwala kamar yadda ta hanani nima. Su duka suka tuntsire da dariya.
Ramlah ta ce "Da fatan yanzu an bude mata hanyar walwala tunda ta bude maka ita ma. Yayi dariya ya ce "Ai tuntuni ma zancen da ake yi yanzu babu matsala ina sonta sosai. Ramlah tayi ajiyar zuciya ta
ce "Allah Yasa haka ne amin. Ta fara rubuce-rubuce a jikin takardar dake hannunta. Can ta dago ta dubi
Hannah ta ce "Kanwata gare ki na dawo, shin yaushe kika fara jin son mijinki Haisam? Haisam ya zura mata ido kem yana kallonta. Hannah ta gyara zama tayi murmushi ta ce "Yaya Haisam dai wani muhimmin mutum ne a rayuwata. Tamkar dan jariri ne wanda ya budi ido daman wacce ya kamata ya fara sani a duniya ita ce Mahaifiyarsa. To haka ya kasance ina bude idona sanda na fara sanin meye rayuwa Yaya Haisam na fara sani don haka shine
wanda na saba dashi, dana fara sanin meye so sai tsuntsun son ya fada kansa, na kasance koda
yaushe shine a raina. Murmushi kawai Haisam yake yi Ramlah ta ce "Haka ne na gode kanwata. Ta sake yin rubuce-rubuce, daga karshe ta rufe littafin ta ajiye a gefe ta dago ta dube su ta ce "Abin da yasa nayi wannan tambayoyi shine akwai wani shiri da nake yi a zuciyata in har mijina ya bani izini ina so in fadakar da matasa samari da *yan mata game da soyayya saboda na koyi darussa da dama akan wannan lamari naku. Haisam ya ce "Ki fadakar a ina? Ramlah ta nisa ta ce "A matsayina na wacce ta karanci harkar yada labari ko ince *yar jarida a gidan radio mana. Haisam ya girgiza kai ya ce
"Bazan yarda wani kato ya dinga jiye min wannan zazzakar muryar taki ba. Hannah ta ce "Ai bashi da
aibu don mace tayi aiki a gidan radio. Ramlah ta ce "Yauwa kanwata fada masa, ni bama aiki nace zanyi ba kawai a sati sau daya zanyi shirin kuma ni zan dauki nauyin shirin. Haisam ya ce "Meye shirin?
Sai cewa kike shiri, fadamin me zaki ce acan kuma yaya sunan shirin? Ramlah tayi dariya ta ce "Ni dai zan fadakar akan soyayya mecece soyayya kuma yaya ake yinta, kuma dawa ya kamata ayi? Haisam ya ce "Haka sunan shirin kenan dawa ya kamata ayi soyayya? Ramlah ta ce "Sai nayi tunani dai in san sunan shirin da zansa. Kanwata ko zaki zabar
min sunan daya dace in sawa shirin. Ta tambayi Hannah. Hannah tayi dariya ta ce "Aunty kisawa shirin suna SOYAYYA GASKIYA CE. Haisam da Ramlah suka hada baki suka ce "Soyayya gaskiya ce. Ramlah ta ce "Gaskiya sunan yayi, haka zansa masa kanwata kince wani abu kema ina fatan zaki
tallafamin shirin yayi farin jin wajen bugomin waya da bada shawarwari a FREEDOM Radio zanyi shirin insha Allah in yallabai ya barni. Kaga itama kanwata Hannah sai ta rubuta Jamb wannan shekarar ta karbo result dinta tazo ta shiga B.U.K ni kuma ina *yan shirye-shirye na a gidan radio ni ina bala'in sha'awar yin aiki a gidan Radio ko telebijin tun ina
yarinya don haka nema na karanci Mass Communication. Kefa Hannah me kike sha'awar karanta. Hannah tayi murmushi ta ce "Ni da yake science's nayi a secondry ina sha'awar in karanci medicine ko Biochemistry. Haisam ya dube su su
dukkansu ya tura hula keya ya ce "Ku gama shawarar ku ina jinku ba saina barku ba.
Ramlah ta ce "Haba yallabai ya zaka yi mana haka sai ka ce wani mutumin can kauye, kamar wani tsoho kake kokarin hana matanka karatu da aikin da zai anfani jama'a. Kaga yanzu kamata
yayi karshen watannan kai da amaryarka ku fita honey moon zuwa kasashe kuyi kamar wata guda a can. Ni kuma kafin ku dawo na fara shirina a FREEDOM. Haisam ya ce "To Uwar tsari tsara mana tafiyar wacce kasa zamu je. Ramlah ta ce "Kaga da farko ku fara zuwa Dubai daga can sai London ku huta sosai, ku wuce America da Germany daga can sai ku wuce saudia kuyi aikin Hajji tunda lokacin aikin Hajjin ya kusa ina ganin dai a wata biyu zaku je ku zagayo ku dawo.
Haisam ya dubi Hannah ya ce "Hannah haka yayi miki. Hannah tayi murmushi ta ce "Yayi mun tunda haka yayiwa Auntyna ai bani da zabi. Ramlah ta ce "Haka za'ayi yallabai ni kuma sai ka barni in fara
shirina a gidan radio duk sati. Haisam yayi dariya ya ce "Naga kin damu da wannan shirin naki to na
barki kije kiyi Allah Ya taimaka miki. Idan kinji an fara saida form din Jamb sai ki sayawa Hannah
idan a lokacin bama nan. Kafin mu tafi zan je Kazaure in karbo mata sakamakon jarabawarta, sai
ki cike mata form din tazo ta zana jarabawarta sai ta shiga B.U.K. Shikenan ku sakar mun marata in huta zance ya wuce ko? Suka hada baki dukkansu suka ce "Mun gode.
Murna ce ta lullubesu dukkan su musamman Hannah sai take ta nanata sunayen kasashen nan a
zuciyarta. Dubai, London, America da Makka. Lallai waya ga Hannah a turai, har aikin Hajji zan yi. Yadda
Hannah ta ke so taje Makka sai gashi ko sati bata yi ba a gidan miji an biya mata Makka. Sai Hamdala
take yiwa Allah a zuciyarta. La'asar tayi sai dukkaninsu suka tashi suka yi alwala suka yi jam'i suka yi sallar la'asar suka ci gaba da hirar da kallon talabijin sallah ce kawai take tashin su. Bayan sunyi sallar isha'i ne suka wuce teburin cin abinci suka ci abincin dare Ramlah ta raka su har bangaren Hannah tayi musu sai da safe ta dawo nata bangaren. Hannah tana mamakin irin wannan kirki irin na kishiyarta Ramlah ashe yanzu akwai kishiyoyi irin Ramlah da zuciyarta daya abinta wasa da dariya. "Hakika nayi dace da miji da kishiya ta gari. Hannah ta fada a zuciyarta. Babu bacin rai a zuciyar Hannah a yanzu sai farin ciki ko ina ta waiga. Haka Allah Yake ikonSa, Allah Mai Girma.
Kwanan Haisam goma a dakin Hannah kamar yadda Ramlah ta amince masa yayi. Haisam da
amaryarsa Hannah sun cancare da amarci a cikin kwana gomar nan. Sun farantawa juna an aiya ce
irin son da suke yiwa juna.
Bayan sun idar da sallar isha'i suka wuce kan teburin cin abinci suka ci suka koshi kamar yadda
suke yi kullum a bangaren Ramlah. Sai Haisam ya ce su taso suje
gidansu su gaishe da Hajiyarsa. Haisam ne yake tukawa Ramlah ce ta zauna a gidan gaba tunda ita ce zata karbi kwanan a daren yau.
Hannah ta zauna a kujerar baya. Suna ta hira wasa da dariya a hanya har suka isa Sulaimanu Cresent gidansu Haisam. Hajiyar Haisam tayi matukar yin farin ciki da taga danta da matansa suna zaune lafiya cikin farin ciki. Hankalin Haisam a kwance ita ma sai farin ciki ya kamata. Hannah da Ramlah suka durkusa gaba dayansu a gaban surukarsu suka gaisheta cikin ladabi da biyayya. Ta amsa musu cikin fara' gami da yi musu nasihohi akan suci gaba
da zaman lafiya kamar yadda suka fara kada su saurari *yan zuga. Su toshe kunnuwansu saboda wasu mutane suna da bakin ciki basa so suga ana zaman lafiya. Ta ci gaba da cewa zaman lafiyarsu shine farin cikin danta Haisam, farin cikin Haisam kuma shine kwanciyar hankalinta daga karshe tayi musu godiya da fatan alheri.
Lemuna da snacks kala-kala tasa masu aiki suka kawo musu. Bayan sun sha hira sai Haisam ya ce su taso su tafi. Har bakin kofa Hajiyar Haisam ta rako su tayi musu sai da safe sannan ta koma gida suka shiga mota suka tafi. Gidan Yaya Habib suka nufa da yake Hotoro G.R.A suka daki gurbi don Yaya Habib baya gida amma matarsa Hidaya tana nan. Ta tare su da fara'a ta rungume aminiyarta Ramlah suka shiga cikin daki. Hannah da Haisam suka zauna a falo suna kallo talabijin din dake kunne. *ya*yan Yaya Habib guda biyu Zakar da Nana suka zo wajen Hannah da Haisam suna taya su hira. Ramlah da Hidaya suna cikin daki a zazzaune a gefen gado. Hidaya ta ce "Kinsan me yasa na jawo ki daki muka kebe? To ba wani abu bane illa ince ni da su Aisha Sule da Hauwa Muhammad muka ga mun dace muyi miki nasiha, wallahi Ramlah kin bamu mamaki duk wannan zafin naki ashe na banza ne iya bakin naki na masifa har kika yarda kika zama baiwa *yar kallo saboda wata yarinya *yar kauye. Gata zata kwace miki miji.
Ramlaha tayi ajiyar zuciya ta ce "Au har meeting ku ka shiga a akaina ke dasu Hauwa Muhammad?
Hidaya ta ce "Eh mana daman jibi muka yi zamu hadu a gidansu Aisha sule muje gidanki dan dole mu fada miki gaskiya akan abunda zai cuce ki meye kawancen idan bamu gaya miki ba wa zai fada miki. Wallahi wannan *yar buzuwar da kike gani kina wani kara wayar mata da kai sai ta waye ta ci ta koshi sai ta mamaye gidan ki zama *yar kallo. Ramlah ta ce "Haba Hidaya yanzu ke da kanki kike cemin haka? Bayan kinga duk tashin hankalin
da Haisam ya shiga da Iyayensa da danginsa gaba daya a sanadiyyar rabashi da Hannah. A gaban idona da bayan idona babu surutun da ba'ayi ba na ana cewa Haisam na hana shi ya auri wacce yake so gashi nan nima ban sami soyayyarsa ba.
Yanzu Allah Ya amsa addu'ata ya kuma yaye mun tsananin kishi ya cusa mun kaunar Hannah muna
zaune kalau da mijina kamar kowacce mace yanzu Hidaya ba sai ku tayani da addu'a ba da fatan alheri Allah Ya kara mun juriya da ci gaba da samun zaman lafiya ni da abokan zamana ba. Ramlah na rufe bakinta sai suka ji muryar Haisam ya leko yana cewa "To kus-kus din ya isa haka ku fito falo a hadu ayi hira har Hannah. Hidaya haka ake karbar baki? Hannah ce bakuwa sai kija *yar gida daki ki bar bakuwa a waje bayan kawo ta nayi itama ta saba da dangi. Hidaya da Ramlah suka yo waje Ramlah tayi dariya ta ce "Kuyi hakuri ina kallon kayan jariran data suyo su ne kasan ta kusa haihuwa. Hidaya ta tabe baki ta ce "Wa yaga bakuwa ai ni nan daka ganni bana marhaban da zuwan amarya ko ba tawa bace balle abunda yayi Ramlah shi yayi ni. Haisam ya dan harareta ya ce
"Ban gane ba? Hidaya ta ce "Haka zaka ce mana wannan bakuwar da kake cewa nayi nace bana marhaban da zuwan ta saboda ni Allah bai samin son amare ba me za'ayi da su, su shiga gida su tarar
da mace da *ya*yanta suyi kane-kane su kwace mata miji idan ba'ayi sa'a bama sai sun fitar da ita. Ni Ramlah na sani sai kai duk wata bakuwa ban santaba. Ramlah taji wani yarr jikinta nauyi da kunya suka rufeta tayi sauri ta katse Hidaya ta ce "Hannah ai kawarmu ce, bari in dauko mata lemo ma a kicin. Ta yunkura zata tashi Haisam yasa hannu ya dakatar da Ramlah ya ce "Ramlah barshi ba komai, ba sai kin dauko mata lemo ba tunda matar gidan bata dauko mata ba kema baza ki dauko ba, tunda ma ta ce Hannah ba bakuwarta bace sai mu tashi mu tafi inda ake nemanta ake sonta. Hannah ta sunkuyar da kai kasa jikinta yayi sanyi kalau. Hidaya ta sake yatsine fuska ta ce "Lallai Ramlah sannu da kokari irin wannan rawar kan mijinki yake yi akan amaryarsa *yar gwal ce kenan ba'a tabata. Hannah ta mike tayi wuf ta fice da sauri ta nufi wajen mota ta tsaya yayin da gabanta ya hau faduwa tana fargabar kada fa Hidaya ta zuga Ramlah ta canja musu yananyin zamansu in har Ramlah ta canja hali lallai Hannah zata shiga halin kunci muddin suka shiga yin tsiya- tsiya da Ramlah. Hawaye ya zubo sharr daga idanuwan Hannah ta jingina kanta a jikin mota tana hawaye. Haisam ya tsaya kawai yana kallon Hidaya haushinta ya hanashi tunano kalmar da zai fada mata ya girgiza kai ya juya ya dubi Ramlah wacce itama tayi tagumi a zaune ranta ya gama baci saboda abunda kawarta ta yiwa kishiyarta. Yayi
ajiyar zuciya ya ce "Ramlah ai kinji abunda Hajiyata ta fada muku dazu ko don haka ki kula, ki kiyaye sai kin toshe kunnuwanki saboda *yan zuga, *yan neman kar a zauna lafiya kiyi amfani da hankali da
tunani sai kinyi yaki da zuciyarki kinyi watsi da wasuwasun da ake cusawa a zuciyarki na munanan shawarwarin da ake baki.
Gaskiya Hidaya ba Hannah kika wulakanta ba ni kika wulakanta don Hannah bata san hanyar gidanki ba ni na kawota kuma Hannah bata auro kanta ba sai da na aurota na zo na hada ta da Ramlah, banji dadin abunda kika yimin ba Hidaya ko Yayana Habib ne yayi wa Hannah haka irin wannan wulakancin zan fada masa gaskiya kuma bazan sake takowa gidansa ba har abada balle Hannah
tazo.
Shigo cikin www.littafanhausane.com.ng domin karanta complete chapter 28
To amma yanzu tunda ba shi bane yayi mun haka ba!! Ba zance na daina zuwa gidan ba kwata-kwata tunda donshi nake zuwa, na gode sai anjima. Ya mike ya fita a fusace. Ramlah ta da karfi cikin fushi ta ce "Hidaya ya zaki mun haka, me yasa kika mun haka Hidaya? Ya kike so nayi da rayuwata? Hidaya ta tabe baki ta ce "Dalla banza kema bacin rai kike don nayiwa kishiyarki wulakanci, ni Ramlah kina bani mamaki wallahi duk yadda akayi wannan amaryar taki ta shanyeki.
Tasa hannu zata riko Ramlah don taga Ramlah tayi matukar damuwa Ramlah ta kauce ta ce "Banji dadi ba gaskiya yau kin bata mun rai. Ramlah ta mike ta
fita. Hidaya ta bita da kallo har ta fice. Tayi murmushi ta rike baki ta ce "Banza wai fushi take akan na batawa kishiyarta, ki mutu mana ai har gida sai munzo mun yiwa Hannah tas sai dai a tsiremu.
Yarinyar data rikita miki miji har ya kusa mutuwa sabida ita kiri-kiri kina ganinta a cikin gidanki kin kasa yi mata komai, kema sai ta halaka ki tukunna.
Da Haisam ya fita ya nufi inda Hannah take a jingine a jikin mota tana kuka, yasa hannu ya dafa bayanta ta juyo da sauri sai taga Haisam tayi murmushi tasa hannu zata goge hawayen idonta da sauri don kar yaga kuka take sai Haisam ya rike hannun ya ce "Kuka kike yi? Ta sake zubo da hawaye sharr ya ce "Hannah daina kuka kinji kiyi hakuri, meye na kukan kuma me Hidaya ta isa ta sa ko kuma me zata hana karki damu mutane daban-daban masu halaye daban-daban dole daman a sami *yan zuga marasa son suga ana zaman lafiya. Ya rungumeta yana goge mata hawaye. Sallamar Ramlah ce tasa su duka suka dago. Ramlah tayi ajiyar zuciya ta ce
"Kuka take yi? Haisam ya ce "Lallashinta nake yi don bata ji dadin abunda Hidaya tayi mata ba.
Ramlah ta matso ta dafata ta ce "Hannah yi shiru daina kuka kada ki damu kinji ko, ina da hankali
kuma nasan duk mai hankali mai kaunata bazai bani shawarar kar in zauna da kishiyata lafiya ba.
Kamar yadda Hajiya ta fada mana dazu sai na toshe kunne na kema haka zaki sami kawaye ko *yan
uwanki masu zuga akan zamana dake sai mun toshe kunnuwanmu mu duka. Hidaya kuma bata fahimci wacece kishiya ba kuma meye kishi bane amma insha Allahu komai zai dai-daita tsakaninki da ita.
Hannah ta gyada kai tasa hannu ta goge idonta ta ce "Naji Aunty Ramlah na gode. Haisam ya ce "To yi murmushi sai mu san kin huce. Sai su duka ukun suka tuntsire da dariya Hannah ya budewa Ramlah
kofar mota, ta shiga ta zauna sannan ta rufe itama ya bude kofar baya ta shiga ta zauna. Haisam ya
shiga ya kunna ya ja suka tafi. Basu tsaya a ko ina ba sai a kofar gidansu mai gadi ne ya taso a guje ya bude musu get. Ya duka har kasa ya mika gaisuwa.
Haisam ya wuce kai tsaye cikin gidan yaje ya tsaya a wajen da ake ajiye motoci su duka suka bude kofofin motar suka firfito. Haisam ya ce "To sai muje mu raka Hannah bangarenta. Suka dunguma suka nufi bangaren Hannah suna tafe suna hira har suka shiga. A babban falo suka zauna, Hannah ta shiga
kicin ta dauko lemon gwangwani guda uku wanda aka yishi da kwakwa ta dora akan dan faranti ta zo ta dora akan centre tebur ta dauki daya ta bude ta durkusa har kasa ta mikawa Haisam ta dauko wani ta bude ta durkusa ta mikawa Ramlah sannan ta
dauko na karshen ta bude ta koma kan doguwar kujera (three seater) kusa da Haisam ta zauna.
Ramlah ma na daya gefen na sa. Suna shan lemo suna kallon settlite tashar African magic wani Nigera film suke mai suna THE LAST UPPER fim din yayi musu kyau matuka saboda tsantsar soyayya ce ake yi a ciki. Basu iya tashi daga kallon nan ba sai da fim din ya kare, karfe daya da rabi na dare.
Haisam ya dubi agogo sai yayi sauri ya mike ya dubi Ramlah ya ce "Aunty ya kamata mu tafi haka
kada mu takurawa Hannah ko tana so taje ta kwanta tayi bacci nasan yau da bana nan sai tafi sakewa tayi ta juyi ita kadai a gado. Hannah ta kalleshi sai tayi murmushi ta sunkuyar da kai.
Ramlah ta tuntsire da dariya ta ce "Kai Yallabai ka cika tsokana kana so dai ka cewa kanwata yau ta zama gauruwa da kyar in zata iya bacci. Hannah ba ta ce musu komai ba murmushi kawai take yi, ta mike ta je ta kashe talabijin ta kwashe gwangwanayen lemon da suka sha ta kai kicin.
Ta fito ta iske Haisam a tsaye a tsakiyar falon Ramlah na zaune har yanzu. Hannah ta ce "Muje to in raka ku. Ramlah ta ce "Ai ke muka rako ko za'ayi rakiyar kara ne? Barshi kanwata mu biyu ne fa.
Haisam yayi murmushi cikin tsokana ya ce "Nasan tsoro kike ji muje in rakaki sama ki kwanta. Hannah ta dan harareshi ta ce "Tsoron me?, ni ba tsoro nake ji ba, ni yanzu ma kallo zanyi gaba daya.
Haisam ya ce "Ai sama ma da kallo muje sama sai kiyi kallon. Ya juya ya kalli Ramlah ya ce "Ki jira ni
dan Allah minti biyu zan raka wannan gwauruwar. Ramlah tayi dariya ta ce "Ka cika tsokana, waccce irin gwauruwa bayan gata da miji a kusa da ita. In kuma kana ganin ba zata iya kwanciya ita kadai ba tazo muje mu kwana a bangarena. Haisam ya ce "Hannah kinji in baza ki iya kwana ba zo muje mu baki daki daya ki kwana. Hannah tayi dariya ta ce "Aunty Ramlah sai da safe babu komai zan iya kwana, ba tsoro nake ji ba. Ta wuce ta fara hawa sama Haisam na biye da ita suna shiga daki Haisam ya jawota ya rungume ta ya kalleta ya ce "Fada min gaskiya yau zaki iya barci da bana nan ko baza ki iya ba? Hannah ta sulale daga jikinsa ta nufi kofar bandaki ta juyo tayi masa fari da ido ta ce "Me yasa ka damu da sanin halin da zan shiga kai dai ba kana tare da Uwargidanka ba. Haisam ya rike baki ya ce "Ah tambayata kike me yasa na damu da halinda zaki shiga, Hannah kin manta Haisam da
Hannah? Hannah tayi murmushi ta ce "To yi hakuri tunda tambaya ka yi zan fada maka. Ta murda kofar bandaki ta shiga ta juyo ta dubi Haisam ta kashe ido ta ce "Daren yau zai zame min marayan dare kwana dayan da baka nan zai zame min tamkar shekara guda zan kagu gari ya waye wani daren yayi domin ka kusanto gareni. Guzurin da zan baka shine zuciyata tana gareka, amma kai ba zan so ka barmin zuciyarka gaba daya ba sai dai ka dan gutsuro min rabi, saboda idan ka bani gaba daya zan shiga hakkin abokiyar zamana, tunda yanzu Yaya Haisam bana Hanna bane ita kadai.
Haisam yayi murmsuhi ya gyada kai ya ce "Nagode Hannah kinyi gaskiya kuma nayi farin ciki da kike
sakani a hanyar adalci a tsakaninku. Kin iya magana kin iya tsara zance mai dadi kanwata zan
tafi da zuciyarki gaba daya amma gaskiya nima sai nayi da gaske zan iya bar miki rabin zuciyata saboda gaba dayanta tana gareki. Yana nufo inda Hannah take a hankali ya karaso bakin kofar inda take tsaye suka zubawa juna ido me cike da soyayya tamkar kada su rabu da juna suke ji, can Haisam ya nisa ya ce "Allah Ya jarabbeni da wani ciwo mai tsanani, wanda na rasa maganinsa, sai daga baya Allah Ya saukar min da maganin ciwon saboda daman kowacce cuta sai da aka saukar da maganinta kafin a saukar da ita. Hannah ta kalle shi cikin mamaki ta ce "Cuta! Wacce irin cuta Yayana?
Yayi murmushi ya juya yana tafiya a hankali ya nufi kofar fita. Hannah ta fito daga ban daki ta tsaya tana kallonsa zuciyarta cike da zulumin kada ya tafi bai faiya ce mata abunda yake nufi da wannan kalamai nasa ba. Yasa hannu ya bude kofar dakin sannan ya juyo ya dubeta yayi murmushi ya ce "Cutar ita ce tsananin sonki, maganin kuma dana sami wacce nake so Hannah na soki, ina sonki kuma, bazan daina sonki ba har abada, sai da safe kiyi bacci lafiya. Ya fita ya jawo mata kofa ya rufe.
Da bandaki zata shiga tayi wanka ta tsinci kanta ta nufi kan gado ta jawo filo ta kifa kanta tayi ruf da
ciki tana murmushi zuciyarta cike da farin ciki da shaukin so. Ta sami soyayyar wanda take tsananin so. Wata dankararriyar soyayyar da take yiwa Haisam ta dinga narkewa tana sake hawa kanta. Ta
lumshe ido sai ta hango kyakkyawar fuskarsa sai taji kamar muryarsa na yi mata rada a kunnuwanta.
Hmm kaiiiii ana zuba soyayyah anan GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 29
Www.littafanhausane.com.ng
Haisam na saukowa ya nufo inda Ramlah take zaune yasa hannu ya tasheta tsaye ya ce "Uwar gidana yi hakuri kinsan bakuwa kwanan sabon waje dole in dan tattausheta in bata hakuri. Ramlah taji wani haushi ya tokare mata wuya ta dubeshi sai taga gaba daya kalar idanuwansa sun canja muryarsa ma ta canja ta tabbatar a cikin shaukin so yake. Lallai Hannah ta caccako dankararriyar soyayyar dake zuciyarsa. Ta fusge jikinta daga hannunsa ta juya masa baya cikin fushi ta ce "Haka zaka ce mana in yi hakuri kana can kuna kashewa juna zuciya gashi nan idonka duk ya narke kana wani kashe murya to in har kwana goman dana baka bai yi maka ba ka koma sama ni inyi tafiyata. Kafin ta rufe bakinta Haisam ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam a kirjinsa yana cewa "Haba Aunty Ramlah ya ina yabanki sallah zaki kasa alwala karfa ki bata rawarki da tsalle mana, babu wani kashewa juna zuciya da muka yi cewa nayi ta tottofa addu'a a kowacce kusurwar daki shikenan fa abin da nace mata, wannan idon nawa kuwa da kika ga ya zama haka barci ne muryata kuwa mura nake. Ta harareshi ta ce "Naga alama mura ce ta kama ka amma a yanzu daka hau sama ko? Haisam ya kyakyale da dariya ya ce "Naga alama yau Ramlah so kike ki rikice mun, yau rigima kike ji zo in goyaki mu tafi. Bata yi niyyar yin dariya ba dariya ta subuce mata ta kyalkyale da dariya ta ce "Kyaleni ni ba wani goyo. Haisam ya jawota da karfi ya ce wai dole sai ya goyata. Ramlah ta ce "To tsuguna in hau da kaina. Haisam ya tsuguna, Ramlah ta haye bayansa sannan ya fito ya lalubo mukulli a aljihunsa ya kulle ta baya. Ramlah ta ce "Ah ya zaka kulleta a ciki. Haisam ya ce "Da mukullinta ai a wajenta in zata bude saita bude ta ciki. Ya fara tafiya ya nufi bangaren Ramlah can ya tsaya cak a tsakiyar hanya ya ce "Wai wai nauyi sauko haka goyon ya isa ki karasa da kafarki. Kinsan fa ba ke kadai bace. Ramlah ta harari keyarsa ta ce "In bani kadai ba ce ni dawa nake? Yayi dariya ya ce "Ke da dan ciki mana. Ta dan ja kunnensa ta ce "Daga fada maka magana harka fara yayatu akai to saura ka dinga fada har kowa yasan ina da ciki. Kuma bazan sauka ba sai ka kaini har cikin gida kan gado furnishment ne, daman ku maza idan kuka yi sabuwar amamrya sai dai Uwar gida ta toshe kunnuwanta ta rufe idanuwanta ta daina kallonku saboda wannan zumudin sai kunyi shi. Yarinya ta ce ba tsoro take ji ba wai kai dole sai ka rakata tsoro take ji ko waya saka oho. Ramlah na baya tana yiwa Haisam tsiya shi kuma yana ta tafiya yana dariya a ciki. Har kan gado ya kai Ramlah sannan ta sauko ta shiga bandaki Haisam kuma ya mike akan gado yana nishi wai qashin bayansa ya kusa karyewa saboda nauyin Ramlah da dan cikinta, Ramlah na jiyo shi tana wanka tana dariya tana cewa ka santa. Bayan Ramlah ta fitowa sai Haisam ya tashi ya shiga shima yayi wanka ya fito daure da tawul a jikinsa ko kayansa baisa ba Ramlah ta kara danewa bayansa ta ce ya kaita kicin zata dauko ruwan sha, nan dai suka hau kokawa Haisam ya ce bazai goyata ba itama daman tsokanar sa take ba kishirwa take ji ba suka rumtuma kan luntsumeman gadon dake malale a tsakiyar dakin suka cakuda suka yamutse junansu yayin da kokawa ta koma sumbatar juna, da shafa juna da rungume juna. Haisam da Ramlah sun farantawa junansu matuka a cikin daren yau.
Kamar yadda Hannah da Haisam suke kaiwa Ramlah ziyara bayan sunyi sallar azahar yau Ramlah da Haisam sun dungumo bangaren Hannah don suci abincin rana dana dare a wajenta daman sunyi mata waya sun sanar mata, da kukunta yazo tana biye dashi tana koyon duk yadda yake yin abinci irin na *yan gayu na zamani don ta koya ta iya, ta hutar da masu aiki ta dinga yi da kanta. Haka Hannah da Ramlah da mijinsu suka kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali, zaman lafiya da kaunar juna.
Kwanci tashi Hannah tayi wata guda da rabi a gidan mijinta. Misalin karfe biyar na yamma Haisam da matansa suna zaune a falon Ramlah suna hira wasa da dariya. Haisam ya ce gaskiya na gaji da bin dakunanku duk mai girki tazo ta same ni a bangarena kullum ni kenan cikin rarraba kayana sai ina bangaren Ramlah na tashi zan dauko agogona sai in tuna yana bangaren Hannah idan na tashi zan dauko gilas dina sai tuna na barshi a dakin Ramlah, shekaran jiya ma sai rigar Hannah na saka ta barci saboda ashe mai wanki da guga ya wanke ya fitarmin da kayan barcin gaba daya ya hada a kayana ya kai bangarena. To na gaji kowacce ta hado min kayayyakina na bangarenta ta kawo mun nawa bangaren. Abinci ma duk mai girki tasa a dafo a zo a ajiye akan teburin cin abincina sannan kowacce tazo mu hadu muci. Ramlah da Hannah suka kece da dariya suna cewa "Kai din dai ka dinga zuwa tunda haka ka fara yi. Haisam na cewa "Naki wayon ai yanzu na fara gane wayo kuke min. Hayaniya da dariyar da suke yi ita ta hana suji ana dannan kararrawa ana ta kwankwasa kofa. Can Hannah taji ta ce "Ana danna kararrawa fa. Ta mike da sauri ta zo ta bude. Wasu mata ne guda uku hadaddu *yan gayu masu ji da kudi kallo daya zaka yiwa dukkanninsu ka gane *yan hutu ne, suna da kyau kuma dukkanninsu. Mace daya a cikinsu tana da tsohon ciki ko yau ko gobe. Hannah tayi musu murmushi gami dayi musu sannu da zuwa. Bata ishesu kallo ba balle su amsa mata kai tsaye suka wuto cikin gidan. Ta bisu da kallo zuciyarta cike da mamakin meye haka kuma lafiya daga zuwansu su hau bata rai da harare-harare. Ta sake kallon me cikin don tana yi mata kallon sani, sai can ta tuno ashe Hidaya ce matar Yaya Habib "No wonder" Hannah ta fada a ranta. Ta tura kofa ta rufe ta nufo inda suke zazzaune a sanyaye cike da fargaba tasan ko ta gaishesu baza su amsa ba. Ta bari suka gama gaisawa da Haisam sannan ta gaishe su. Kokonto ya zama gaskiya ai basu amsa mata ba sai ma wata harara da suka sakar mata dukkanninsu. Nanfa aka hau kallon-kallo tsakanin Haisam da Ramlah da Hannah da kuma wadannan baki. Hidaya ta yamutse fuska ta ce "Aisha Sulaiman, Hauwa Mamman kuzo mu koma wancan falon mu zauna mun isa muzo mu zauna tsakiyar amarya da ango. Aisha ta ce "Da kuma Uwargidansu Ramlah kin manta baki fada ba. Hauwa Mamman ta ce "Oh haka ne fa baku gani ba, amarya sai hararar mu take lallai zuwa gidanki Ramlah nan gaba sai mun shirya, to bangarenki ma *yan Uwanki da kawayenki basu isa suzo ba ashe to ta biyoki ta biyo mijinta. Suka mike suka nufi daya falon.
Ramlah ta rasa ta cewa ta bisu da kallo kawai can ta nisa ta juyo ta dubi Haisam wanda yayi shiru yana kallon talabijin amma kallo daya zaka yiwa fuskarsa kasan cikin bacin rai yake. Hannah kuwa ta sunkuyar da kai kasa hakika nan da wasu *yan dakikai zata fara zubar da hawaye.
Ramlah ta ce "Yallabai wai me su Hidaya suke nema ne dani, yaya suke so nayi. Yasa hannu ya dakatar da Ramlah ya ce "Yi shiru karma ki bata bakinki barni dasu jeki gurinsu bakinki ne. Can Ramlah ta yunkura ta mike ta nufi kicin ta shaidawa kuku da sauran masu hidimmarta su hado juices da snacks su kawowa bakinta, tazo falon da kawayenta suke suka fara cafcafkewa suna hira. Haisam ya kurawa Hannah ido yana kallonta can ta dago ta dube shi saita daure da kyar ta kirkiro wani dan busasshen murmushi. Ya ce "Yauwa ko kefa, meye abun damuwar? Ki daina damun kanki akan irin wadannan *yan matsaloli kinsan dai ba za'a sake tataburzar da akayi a Kazaure ba ko? Ba za'ayi irin yadda kikayi da su Juwairiyya ba, Sahabi, Principal, Yaya Habib da Rauda ba ko? To duk wadancan basu zamar mun matsala ba wajen wargazasu balle su Hidaya, zanyi maganinsu Insha Allah kallonsu nake yi tukunna wata rana ko kudi aka basu akace suzo gidan nan su yadar miki da magana baza suyi ba. Hannah ta nisa ta girgiza kai ta ce "Yaya da zaka ji shawarata ka taimakeni ka kyalesu dan Allah ko me zasu yimin kuma kome zasu ce kabar su ni na saba da duk irin wadannan tsangwamar tuntuni a rayuwata. Tsorona daya kada yau da da gobe suna zuga Aunty Ramlah tun bata dauka har tazo ta fara dauka zamanmu yazo yaki dadi. Haisam ya girgiza kai ya ce "Haba Hannah ai tun daga ranar da muka sake haduwa ranar da aka ce miki na rasu kika fito daga daki kika ganni na ganki kikayi murmushi hakika nasan farin cikin da kika ji a ranar bazai misaltu ba da kika ganni a raye ban mutu ba, to da yardar Allah tun daga ranar har karshen rayuwarki kin dinga farin ciki kenan, kin rabu da damuwa da tsangwama insha Allahu. Hannah tayi murmushi ta ce "Na gode maigidana, to amma ina gudun zuciyar ka da zafin fushinka irin na Kazaure. Haisam yayi dariya ya ce "Tunda na same ki yanzu komai ma a sauki zan dinga daukarsa na daina fushi da yawa my love. Suka sakarwa juna murmushi. Ya ce bude dirowar can ki mikomin Jarida zan karanta, ta mike a nutse ta dauko masa tazo ta durkusa ta mika masa tazo kusa dashi ta zauna, yana karatu ita kuma tana kallon talabijin.
Wayar dake dore akan tebur tayi ruri (land line). Ramlah tasa hannu ta dauka muryar kawarta taji Mrs. Blessing ma'aikaciyar filin jirgi a Abuja bayan sun gaisa sai ta sanar mata da cewa bizar Hannah da Haisam ta fito don haka su zama cikin shiri nan da kwana biyu jirgi zai tashi zuwa London daga Abuja. Ramalah tayi mata godiya suka yi sallama ta ajiye wayar, ta ce da kawayenta tana zuwa. Ta mike ta nufi falon da Haisam suke zaune ta fusge jaridar da take hannunsa yana karantawa tayi dariya ta ce, "Albishir nazo zanyi muku bizar ku ta tafiya kasashe ta fito nan da kwana biyu zaku tashi zuwa London daga Abuja. Haisam yayi dariya ya ce "To madallah Ramlahta ai shi yasa bana fargaba da sha'aninki yanzu ko sati biyu baki yi ba da zuwa Abuja neman mana biza har an samu. Ramlah tayi murmushi ta ce "Haba don neman biza, ai ko tashar jirgi kake nema a kwana daya zansa a nemo maka saboda kawayena wajen su uku ne acan ko banje ba in nayi musu waya zasu yimin duk abinda nake bukata, balle in tashi inje Abujar da kaina kasan dole ne ma su zage dantse su nemo min bizar da awuri sun san ba karamin sauri nake yi ba. Hannah dai sai murmushi take yi, ta ce "Auntyna godiya muke yi fa sannu da kokari. Ramlah ta kalleta tayi dariya ta ce "In banyi muku ba, wa zanyi mawa babu komai fatan alheri nake muku kuje lafiya ku dawo lafiya ku same mu lafiya. Hannah da Haisam suka hada baki suka ce "Amin. Ramlah ta juya ta nufi wajen kawayenta wadanda suka kasa kunne suna sauraren abinda suke fada. Sai suka sake jin haushin Ramlah kowacce ta rike baki don mamaki wata na salati wata na tsaki. Ramlah ta karaso da murmushinta ta zauna. Ta daga ido ta kalle su sai taga gaba dayansu harararta suke yi. Tayi mamaki matuka kafin ta ce wani abu sai taji an turo kofa an shigo gami dayin sallama, mai gadinsu ne ya zo ya durkusa a gaban Ramlah ya gaisheta ya ce "Daga gidan gwamnati aka turo wasu mata guda biyu wajen Hajiya Hannah na nuna musu bangarenta sunje sun ce a kulle yake, shine na ce bari in duba musu nan dan dai banga fitarta ba ko tana nan? Ramlah ta ce "Tana nan kace musu tana zuwa. Ya mike yana godiya ya fita. Ramlah ta kwallawa Hannah kira. Cikin ladabi Hannah ta amsa ta taso tazo wajen Ramlah. Ramlah ta ce "Baki kika yi may be Nusaiba ce ta aiko su suna waje inji mai gadi. Hannah tayi murmushi ta ce "To bari in je na gode. Ta wuce ta nufi kofar fita su duka suka bita da kallo. Wata dandatsetsiyar shadda ce a jikinta pink colour anyi mata surfani da design me kyau a zani da rigar da dankwali wato (ready made). Hannah tayi kyau matuka. Lallausan gashinta ne har tsakiyar bayanta ta sake shi bayan ta daure da pink din ribbon.
Aisha Sulaiman ta ce "Turkashi. Hauwa Mamman ta ce "Rigijigafji inji masu iya magana. Hidaya ta ce "Wani kayan sai Amale. Ramlah ta dubesu dukkansu ta ce "Ah wanne yare kuke yi ne bana jinku? Hidaya ta ce "Yaran Hausa muke yi mana. Ramlah ta ce "Ban fahimce ku ba. Aisha Sulaiman ta ce "Turkashi na ce, Hauwa ta ce rigijigafji, Hidaya kuma ta ce wani kaya sai Amale gaba daya abu daya muke nufi gaba daya muna magana ne akan babban aiki. Ramlah cikin mamaki ta ce "Wanne irin aiki kuma? Aisha Sulaiman ta ce "Hidaya ku fada mata danni idan na cika yawan magana sai jinina ya hau saboda takaici. Hidaya ta nisa ta ce "Ramlah, Ramlah sau nawa na kira kunnanki? Kin bani kunya, kina bani mamaki wai shin meke damunki ne? Ramlah me yasa kika zama makauniya alhalin kina gani da idanuwanki guda biyu, kin zama wawuya alhalin kina da wayo. Kin zama kamar baki san abunda kike yi ba alhalin kina sane. Ina miki fargabar ranar da zaki zo kina dana sani, kina zubar da hawaye da idanuwanki. Ramlah taji gabanta ya fadi ta fada cikin rudani "Wai meke faruwa ne? Me kuke nufi? Dan Allah ku fada mun abunda nayi yadda zan gane na kasa fahimtar ku.
Hauwa Mamman ta ce "Abunda muke nufi shine kinyi kuskure, kinyi sake, kin dau abin da sauki alhali ba mai sauki bane. Ramlah yanzu kece kika samarwa mijinki bizar da zai fita da amaryarsa suje su shakata a kasashen waje ke kina gida a zaune. Wai shin ke me kika dauki kishiya ne?
Karfa ki dauki Hannah karamar yarinya ce wacce bata waye ba, ki dauka baza ta bude idonta ba tayi miki rashin mutunci a gidan nan ba dubi yadda Hannah ta zama a cikin wata biyu ta goge tayi kyau tamkar wata baturiya kina zaune. Na daya tana da kyau harta fiki, na biyu ta iya kissa da kisisina da iya magana da ladabin munafurci. Da sannu zata tafi da zuciyar mijinta da Iyayensa da duk danginsa kina zaune bude da baki. Aisha ta ce "Ah to. Mudai mun zo ne mu fada miki gaskiya kin sakarwa kishiyarki da yawa duba kiga falonki shekara biyu kuna tare da Haisam baku dauki hoto ba ku biyu kin lika a falonki sai zuwan Hannah kuka hadu ku uku kuka dauki hoto kalli hoton ko kishi ba kyaji kika lika hoton kishiya a falonki. Gaba daya kin canja Ramlah kamar ba keba. Ki tsare girmanki ko ganinki tayi sai gabanta ya fadi karyarta nan gaba ta ce zata waye ta ce zata takaki. Shima dole yaji shakkar ba zai sake da ita ba. Haka rannan naji ance har gidanku kika dauketa kika kaita kuka yini, lallai kishiya ta zama kawa. "Hauwa Mamman ta ce , "Wallahi ni duk ranar da Ibrahim mijina ya tarki aure daga shi har amaryar saina babbakesu aina fada masa. Bai isa ba shi da kansa yanzu yake cemun ko bashi mace aka yi ba zai karba ba, to kin gani namiji zuma ne sai an babbaka masa wuta. Hidaya ta yamutse fuska ta ce "Ke kin fadawa mijinki ma irin hukuncin da zaki dauka idan ya qaro auren, to ni ban fada masa bama matakin da zan dauka, amma shi da kansa ya sanni ko a hanya muna tare bai isa ya daga ido ya kalli mace ba balle yayi min zancen aure a wasa ranar sai dai ya kwana a bakin get dan kulle kofata nake yi in kyaleshi, balle yayi dare. Aisha Sulaiman ta ce "Muktar mijina ai ya taba tarkar aure Ramlah kin manta da irin tashin hankalin da mu kayi ba shiri ya fasa to haka akeyi muddin kika yi sakwa-sakwa za'ayi babu ke. Tunda ta riga ta shigo yanzu ke abunda ya kamace ki Ramlah ki iya takunki, kishiya ba abar yarda bace kada ki barta ta sake ta baje ta baza kayanta tayi kane-kane ta mallake miki miji ta mallake ki. Hidaya ta ce "Wai kishiyar ma data sake mai da ita wayayyiya,
kyakkyawa irin Hannah, ai irinsu Hannah bai kamata ki sake ba saboda duk wani da namiji burinsa ya sami mace kamar Hannah balle wanda ya aureta dole ya rikice ya mace mata ke kuma kina zaune a gefe. Kiyi dai tunani Ramlah akan nasihar da muka yi miki don gaskiya mu mun hango miki abunda ke baki hango ba.
Cab Mata?? Uhm bari dai nai shiru,,,,,
Www.littafanhausane.com.ng GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter30
Ramlah tayi shiru kanta a sunkuye a kasa jikinta yayi sanyi sai yanzu ta dago ta dubesu tayi ajiyar zuciya ta ce "Naji abinda kuka fadamin nagode. Ta kirkiro wani laujajjan murmushi dakyar ta ce "Hidaya, Aisha da Hauwa kawayena kenan. In tambayeku mana shin Nana Aisha (R.T) matar Manzon Allah (S.A.W) kishiyoyinta nawa ne? Matan Annabi tara ya aura suka zauna tare. Kun manta inda Allah (S.W.A) Ya umarci maza da su auri mataye bibbiyu ko uku-uku ko hurhudu idan sunga baza suyi adalci ba su auri daya. To ashe ba Haisam bane ya kirkiro auren mata biyu don ya cusguna min ko ya bata mun rai shi da amaryarsaba. Hakika na riki wannan hadisin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya ke cewa "Imanin dayanku bazai cika ba har sai ya sowa dan uwansa abun da ya sowa kansa.
Su duka sukace "Allahu Akbar !. Yayin da dukkaninsu suka sake tattaro da hankalinsu ga sauraren Ramlah. Ta ci gaba da cewa "Kuma rai yana son mai kyautata masa. Hannah tana kyautata mun, Hannah tana girmamani haka Haisam yana faranta mun. Kullum addu'a nake Allah Ya zaba mana abunda yafi alheri tsakanina da Haisam. Alherin da Allah Ya zabar mana shine ya kawo Hannah, tsananin kishin da nake dashi da kin Hannah da nake yi da sai Allah Ya yaye min a raina naji ina son zama da ita musamman dana yaba da hankalinta. Ni a yanzu da kuka ganni bani da wani buri a duniyar sai inyi biyayya ga mijina in shiga Aljannah kuma in kiyaye kada in cuci abokiyar zamata mu gama lafiya saboda duniyar nawa take yanzu kana nan an jima babu kai ka mutu ka kuma tafi har abada. Daman yanzu a wannan zamanin da muke duk wani mai hakuri shine abun zagi an dauke shi wawa marar hankali kamar yadda a yanzu kuke daukata to gaskiya ba haka bane nasan abun da nake yi. Ina kuma jin dadin rayuwar aure na a yanzu fiye da rayuwar aurena ada. Kuna murna kuna jin dadi a zuciyoyinku harma kuna furtawa da bakinku kuna tinkaho da takama kun hana mazajenku aure kuma sun hanu saboda suna tsoronku kuma kun isa, nice marar wayo dana bar mijina ya kara aure har muke zaune lafiya to alhamdulillahi naji dadi. Ku yi hakuri bawai na gwaleku bane, kuma bawai ban gode muku bane naji dadi da kuka hango abunda zai cuceni kuka sanar dani. Sai dai ina ganin baku fahimci wacece kishiya ba da zaman tare. Sai muke kallon-kallo ni daku, ma'ana kuna mun kallon inama inji abunda kuke cemun, ni kuma ina hango muku wata babbar illa akan mazanku har nake cewa inama zaku yarjewa mazajenku suyi aure kamar yadda Haisam ya kara aure ku zauna lafiya yafi kwanciyar hankali.
Hidaya tasa hannnu ta dakatar da Ramlah ta ce "Karma ki fara hango mana inama mazajen mu su kara aure mu zauna lafiya wanne irin zaman lafiya anyi mana kishiya ai lokacin ma zama zai hargitse. Aisha ta ce "Ke dai Ramlah da Allah Yayi miki zuciya irin ta matan sahabbai kinji dadi kina son kishiyarki amma mu babu sauki idan akayi mana kishiya. Su duka suka kyakyace da dariya suna tafawa. Hauwa ta ce "Kishiya, kishiya Ramlah kinji yadda nake ji kuwa idan naga anyi kishiya a makwabtanmu ma balle a cikin gidana ai har abada bazan yadda da kishiya abokiyar zama ba ce idan kuwa ya kuskura yayi min karshen zamana ya zo a gidan kuma suma sun rasa kwanciyar hankali a zamansu, lallai Ramlah baki san kishi ba. Ramlah tayi murmushi ta gyada kai ta ce "Hauwa kin tabo wani kyakkyawan misali da nake so in baku kince daga ranar da mijinki yayi aure kin bar gidansa, a matsayinki na *yar shekara ashirin da biyar kina nufin idan kika rabu da mijinki kin rabu da yin aure kenan a rayuwar ki har abada? Hauwa Mamman tayi shiru can ta ce "Sai in sami wani in aura. Ramlah ta ce "Saurayi ko bazawari? Tunda ke bazawara ce kinga saurayi ba zai zo neman aurenki ba sai dai wani ikon Allah. Masu mata ne zasu dinga zuwa neman auren ki to su matan da zaki auri mazansu su ba mutane bane da zasu kyale mijinsu ya aureki? Kingafa ko yanzu kin bar sunna don baki sowa dan Uwanki abunda kika sowa kanki ba kin auri mijin wata. To ai haka ne abunda nake nufi da inama zaku yarjewa mazanku su kara aure yafi kwanciyar hankali shine na dade ina son in fada muku abunda yake raina na rasa ta ina zan fara fada muku ku fahimta amma yanzu zan fada muku tunda yanzu mun shiga babban dakin bawa junanmu shawarwari Allah Yasa ku fahimceni kamar yadda na fahimce ku. Hidaya tayi dariya ta ce "Ai yanzu ra'ayoyin mu ya banbanta aminiyata kin baude daga cikinmu kinbi wata baudaddiyar hanya ta gushewar ganewa mun kasa gane kanki. Yaya gashi kiri-kiri ana cutarki kowa yana gani kince ba cuta bace, mufa muna nan akan bakanmu kuma kullum zamuci gaba da fada miki har sai kin gane.
Ramlah tayi dan murmushi ta mike tsaye taje ta rage muryar talabijin din dake kunne ta dawo ta zauna ta dubi fuskokinsu dukkansu sai fara'a suke alamarma dariya take basu, sai itama suka bata dariya ta kyalkyale da dariya suma sai suka yi dariya. Hidaya ta ce "Ai babu abinda zaki gaya mana Ramlah kema kyayi dariya saboda ba'a haiyacinki kike ba tuntuni na fada miki wannan kishiyar taki ta gama dake. Ramlah ta nisa ta ce "Ina da abun cewa ne yasa ma har nake dariya. Ku gafarce ni Hauwa Mamman bari kiji abunda baki sani ba game da mijinki amma ina so ki nutsu kafin ki yanke hukunci dole tasa zan fada miki yanzu ma don kawai ki yarda da bayanin da nake so in wayar muku dakai akai ku ka kasa ganewa, kinsan Amira Nasir? Hauwa Mamman ta zabura ta rike kirji ta ce "Ramlah ina kika san Amira Nasir? Ai ita ce tacacciyar *yar iskar yarinyar dana fada miki *yar Minna ce take yiwa mijina waya tana sonsa amma ban fada miki sunanta ba, nima sai daga baya na binciko sunanta amma ai yanzu ta rabu dashi ko hanyar da yabi ma ta daina bi. Ramlah tayi murmushi ta ce "Haka ya fada miki to ga irinta nan abunda nake fada muku kun kasa ganewa. Da mace tasa mijinta a wani hali na bin matan banza gara ma ka barshi yayi auren. Hauwa Mamman ta gyara zama ta narairaice ta ce "Ramlah meke faruwa ne gabana faduwa yake fadamun gaskiya. Ramlah ta nisa ta ce "Gaskiya basu rabu ba kuma sau biyu muna haduwa dasu a London ni da Haisam duk fitar da yake yi da ita yake fita ina amfanin haka bayan Uwar dukiyar da yake tura mata. Ai ba a London kadai ba jama'a da yawa sun sani kece baki sani ba ana tayi miki kallon wawiya. Kinga da irin wannan harkar gara ma ace ya auro miki ita cikin gida kun zauna tare kamar ni da Hannah dai. Hauwa Mamman ta dora hannu aka ta tsala kuka, Aisha Sulaiman na rirriketa kuka take tana cewa "Wallahi Ramlah gara ke daya auro miki Hannah ashe, yanzu haka Ibrahim zaiyi mun na shiga uku yanzu Ramlah yaya zanyi? Ashe kowa ya sani baku fada min ba? Ramlah ta juya ta kalli Aisha Sulaiman taa ce "Ke kuma da kike ganin kin hana Mukhtar aure ya hanu to kece baki sani ba yana nan tare da yarinyar kuma yakai kudin auren a boye, yana gina mata gida a Abuja can zai kaita inda yake aiki ayi auren karki sani. Hidaya ko ba kawar yarinyar bace take fada mana tare dake ba? To ashe ni da Haisam ya sanar dani ga wacce yake so ya aura sai in masa butulci ince ba zamu zauna lafiya ba. Aisha Sulaiman tahau cire mayafi tana fisge dankwali ta ce "Ramlah da gaske kike ko da wasa na shiga uku na lalace. Ramlah ta ce "Baki lalace ba Aisha darasi ne a kanku domin kunsan kara aure fadar Allah ce babu wacce ta isa ta soke ta ce ba za'ayi ba. Hidaya ta rike baki ta ce "Kai duniya abin tsoro Ramlah na fara tsorata da al'amuran maza yanzu. Ni kuma me Habib yake ban sani ba? Ramlah tayi murmushi ta ce "Ciki gareki Hidaya bai kamata a fada miki maganar da zata tayar miki da hankali ba. Hidaya ta zabura ta ce in akwai ni fadamun Ramlah karki ci amanata babu wani abunda zai sameni don ina da ciki fadamin gaskiya. Tana rufe bakinta sai taga Haisam a kanta ya miko mata wani kati. Ramlah tayi sauri tasa hannu zata fusge sai Hidaya tayi sauri ta fusge tana karantawa taji kamar an daba mata wuka a kirjinta. Katin daurin auren Habib mijinta da za'ayi nan da sati gudane. Ko da wasa Habib bai taba fada mata ba saboda yasan tsananin kishinta shi kuma so yake ya kara aure don haka ya kwabi duk wanda yasan zaiyi aure da kada ya fadawa Hidaya cewa zaiyi aure.
Hidaya ta rike hannun Haisam gam ta rushe da kuka tana cewa "Wallahi saika karbo min takardata a wajen Yayanka na fasa auren. Haisam ya hau dariya yana cewa ni asuwa ke da kika isa da mijinki jeki ki same shi, kiyi hakuri kawai ki zauna ga tsohon ciki ga *ya*ya ina zaki kaisu Hidaya zama da kishiya ya sameki sai hakuri daina ma kuka. Ya juya ya dubi Hauwa da Aisha kowacce tamkar zararriya abunda ya dameta a ranta ya dameta. Babu sallama kowacce taja gyalenta ta nufi hanyar fita. Ramlah na cewa ku dawo ku bari a gama abinci kuci mana, inahh, babu wacce ta kalleta balle susan me take cewa. Direban Hidaya ne ya kawo su, mota kawai suka fada. Ramlah ta bisu tana rokarsu don Allah su kwantar da hankalinsu su bari zuciyarsu ta huce kafin su yanke hukunci karsu yanke hukunci cikin fushi subi komai a hankali. Basu iya ko magana ba saboda makakin bakin ciki kowacce sauri take burinta ta ganta a gida tayi arba da munafikin mujinta maci amana, suka ja mota suka tafi.
Haisam ya jawo hannunta suka shige gida su duka dariya ce ta hana su yin magana. Sunyi minti goma sha biyar suna dariya suyi su huta su sake tunowa su kwashe da dariya haka dai suka yi tayi. Haisam ya ce "Ai duk hirar da kuke ina jinku nayi shiru ban tanka musu ba saboda naji kina basu amsar da ta dace. Hakika Ramlah kin burgeni kin cika mai hankali da tunani da kaifin basira. Kin burgeni da yawa da baki dauki shawarrar su ba amsoshin da kika basu yayi daidai da tambayarsu. Nasan Yaya Habib zaiyi fada don me na fadawa Hidaya to ko me zaiyi yayi ni dai na riga na gama fada saboda ta cika min ciki tun rannan nake ciki da ita. Wai shin ina ruwansu da gidan wata? Banda gulma irin ta mata ina ke ina matsalar wani gida ita wacce aka yiwa kishiyar ta ce babu komai ku kun dage kunce akwai komai, suna bani mamaki wallahi. Ya jawo Ramlah ya rungumeta ya ce "Yanzu haka wani sonki ne na daban ya kara lullubeni. Ramlah ta lumshe ido ta ce "Na gode da yawa. Tana rufe bakinta Hannah ce ta turo kofa ta shigo gami da yin sallama tayi turus ta tsaya cak don ba zata iya karaso inda suke tsaye a rungume da juna ba. Tayi kamar ta bude kofa ta fita sai dai ta daure ta hadiye makakin kishin daya taso mata, nauyi da kunyarsu ta kamata. Haisam ya saki Ramlah daga rungumewar da yayi mata, ya dubi Hannah wacce kanta ke sunkuye a kasa ya ce "Meye kika tsaya acan ki karaso mana. Tayi murmushi kawai ta nufo inda suke ta dubi agogon dake daure a hannunta ta ce "Zanje inyi alwala magaruba tayi. Sai su duka suka nufi ban daki don yin alwala. Bayan sunyi jam'i sun idar sai suka zazzauna akan abin sallarsu kowacce ta bude Alkur'ani tana karantaawa. Har lokacin sallar isha'i. Bayan sun idar suka yi addu'oin su suka shafa. Kafin su idar masu aiki sun gama jera musu abinci kala-kaala akan teburin cin abinci.
Kai tsaye suka nufi dinning table, Ramlah ta fara zuzzubawa a kowanne plate. Ta zuzzuba lemo (juice) a kowanne kofi ta koma ta zauna kowa ya fara cin nasa. Suka dauki lokaci mai tsawo babu wanda yayi magana. Haisam ya dubi Ramlah ya juya ya dubi Hannah ya ce "Yau abincin yayi dadi sosai ko magana kun kasa yi. Su duka suka yi dariya. Hannah tayi masa wani lallausan kallo ta ce "Ka cika neman magana kaine fa kace mudaina magana idan muna cin abinci yanzu kuma ka ce mun kasa magana. Ramlah ta ce "Ai dokar da yasa shi tafi effection saboda yallabai baka iya zaman minti goma baka yi tsokana ba. Haisam ya ce "Kullum dai bakinku daya ne abunda Yaya ta ce haka kanwa take cewa haka abunda kanwar ta ce Yaya sai ta ce haka ne, kanwata babu mai bin bayana a cikinku ko? To shikenan tunda hademun kai kuke nima zan samo me shigarmun inyi kanwa. Hannah ta harari Haisam ta ce "Wacce irin kanwa kuma? Haisam ya ce "Kishiya mana kunga sai ayi bibbiyu kenan ku biyu nima ni da ita sai ta shigar mun, "Ramlah ta tuntsire da dariya ta ce "Kanwata ke yake tsokana ai na gaya miki shi dai yayi tsokana yaji dadi. Haisam yasa hannu yana shafar kumatun Hannah ya ce "Ke da wasa nake miki, ai na gama aure a rayuwata Insha Allah. Kuma ina jin dadin wannan hadin kan da kuke mun. Tsokana nake yi ina ni ina wani kara aure har a lahira na gama karin aure. Ramlah Uwar gidana Hannah amaryata har abada. Su duka suka yi dariya ya ce "Allah da gaske nake, ko kunga nayi muku kama da wanda zai kara aure ku kalleni tsaf a nutse ku kare mun kallo. Suka tuntsire da dariya dukkaninsu har Haisam din. "Hannah dai dariya kawai take yi bata ce komai ba kai kayi kidanka kayi rawarka. Haisam ya ce "Ni yanzu abin da yake gabana shine inga dukkanninku na baku jari kowacce ta kama sana'a ta kanta, Ramlah yanzu misali idan aka baki jari me kike da sha'awar budewa. Ramlah ta ajiye kofin dake hannunta tayi fari da ido ta ce "Ni a gaskiya ina da burin bude kantin sayar da kayan Senegal na mata da maza sannan inyi wani kanti wanda zan dinga sayar da takalma na kasar waje tsadaddu na mata da maza da yara. Haisam ya ce "To ya isa haka Aunty Ramlah so kike ki bude kantina daban-daban. Idan na kyaleki saiki kirgo min guda goma biyu ma sun isa. Kefa amarya ta? Hannah ta narairaice ido ta ce "Ni burina da ace ina da kudi makarantar Islamiyya zan bude da masallaci da rijiyoyi da bishiyoyi zan shuka ince Allah Ya kai ladan Kabarin Iyayena da suka rigami gidan gaskiya. Haisam ya ce "Allah Sarki shike nan? Hannah ta zubo da hawayen daya cika mata ido ta ce "Shikenan burina. Haisam yasa hannu ya share mata hawaye ya ce "Kar kiyi kuka ajiye wannaan a gefe za'ayi insha Allah a sana'a me kike da burin yi? Hannah ta danyi murmushi ta ce "Ina so in bude katon kanti (Super market) a kusa da nan kuma in bude wani dan ofis na taimakawa marayun yara. Haisam ya ce "Duk kun zabi sana'oi masu kyau, nima bari in fada muku tawa sana'ar a Abuja na gina wani katafaren waje kerarre, kayatacce mai kyawun gaske nan da wata biyu za'a kawo min motoci daga Germany zan fara sayarwa idan mun dawo daga tafiya in Allah Ya kaimu zan kaiku ku gano wajen. Hannah da Ramlah suka yi murmushi dukkansu suka kuma tayashi murna da fatan alheri.
Haisam ya ce "Na gode sai dai kuma na kasa tuno sunan da zan sakawa wajen misali Hannah da zaki bude Supermarket wanne suna kike so kisawa wajen? Kema Ramlah yaya sunan boutik dinki da zaki bude ku dan bani satar amsa sai insan wanne suna zan sawa wajen sayar da motocina. Ramlah tayi dariya ta ce "Aini sunanka zansawa wajena. Haisam senegalise boutique, Haisam ya girgiza kai ya ce "Baiyiba, kefa? Hannah tayi dan murmushi ta ce "Sunanka dana Auntyna Ramlah zansa HaiRam Supermarket. Haisam ya ce "Hairam? Ke kuma laifin me kikayi da kika cire sunanki kara Hannah akan Hairam din sai yafi dadi. Hannah tayi dariya ta ce "HAIRAMHANAH Supermarket. Haisam da Ramlah suka hada baki suka maimaita HAIRAMHANAH sunan yayi dadi gaskiya. Haisam ya ce "To da nawa dana Aunty Ramlah dana Amaryata Hannah dukka sunan daya ne, kunga Hairamhannah super market, Hairamhannah senegalise boutique, Hairamhannah motors da dai sauransu. Yanzu kowaccenku zan bude mata account zan zuba muku miliyan hamsin-hamsin ku fara jarin dashi kafin nan gaba in kakkara muku, nima ina cikin zamana Babanmu ya kira mu ya ce tunda munyi hankali kowannen mu ga takardun hannayen jarin da ya dinga zuba mana tun muna yara a bankunan kasashe daban-daban da bankunan nan kasa Nigeria, kudade masu yawa sun taru shekaru da yawa bamu taba karba ba ya ce muje mu kula da kanmu da Iyalinmu. Sannan an biyani kudin kwangilar da nayi ta miliyan dari biyu sai naga ya dace nima inzo in bawa kowacce jari ta juya da kanta don tayi hidimomin gabanta ba sai kun jirani ba kullum ina dan sammuku na dan kashewa ba. Ramlah ta rike baki ta ce "Yallabai miliyan hamsin-hamsin fa kace? Hannah ta ce "Fifty millions? Haisam ya ce "Miliyan hamsin kowaccenku. Hannah da Ramlah suka zo suka durkusa a gabansa suka yi ta godiya. Yasa hannu ya tashe su tsaye ya ce babu komai shi ba sai sun gode masa ba. Hannah ta nufi kofar fita ba tare data yiwa kowa sallama ba a tunaninsu kicin zata shiga sai suka ga ta bude kofar fita ta fice da alama kuma kuka take yi.
Comment da yawa yana kara mana karfin gwiwan muku posting fa.
Amma sai ku dinga comment kamar bakwason labarin.
Ko so kike muci gaba da rabi anan rabi a can!!?
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 31
Haisam da Ramlah suka hau kallon-kallo, Haisam ya ce "Ina kuma wannan zata je babu sallama. Ramlah ta ce "Ka bita ka gani, ina jin gidanta ta tafi da alamar kuka take yi. Haisam ya ce "Ai kukan ma ta tafi zata yi ya isheta domin gwanar kuka ce na tabbata ta tuna maraicinta ne zata ga kudin bashi da amfani a wajenta saboda sunzo lokacin da babu Mahaifanta. Ramlah ta girgiza kai ta ce "Allah Sarki jeka ka bata hakuri kada ta damu haka Allah Ya rubuto mata yaya zata yi duk mai rai mamacine kowa jiranta yake banda abun Hannah bai kamata ta dinga damuwa ba tunda Allah Ya bata miji tamkar Uwarta da Ubanta. Haisam ya ce "Iyaye daban ne da miji Ramlah karma ki hada. Ramlah tayi dariya ta ce "Miji dai irin na Hannah zan iya cewa daya ne da Iyayenta tunda tun tana karama yake rainonta baya so ko kuda ya tabata zai iya hallaka duk wanda ya nemi ya takura mata saboda tsananin so da kulawa da yake mata. Haisam ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune yana dariya ya ce "Raudah ta cika gulma haka ta fada miki? Suka sake tuntsirewa da dariya dukkanninsu. Ramlah ta kara da cewa "Baka ji masu iya magana na cewa fini da gidan Uba in fiki da gidan miji ba? Ai duk masu gata a wajen Iyayen nan borori ne a gidan mazajensu. Irin su Hannah marayu su kuma su caba da miji mai tsananin son su. Haisam ya juya ya fara tafiya ya nufi kofar fita. Ramlah na biye da shi a baya. Ta ce "Kayi shiru sai murmushi kake baka ce komai ba. Haisam ya ce "Aunty Ramlah kin cika son magana me kike so ince miki? Ta ce wai dana ga hira muke sai ka dan tayani hirar kayi min musu kace Rauda karya take ba'ayi haka a Kazaure ba. Haisam ya ce "Kishi! Kishi!! Ya motsa kumallon mata ai gara ki amayoshi, yanzu fa nake yabonki kin nunawa su Hidaya baki da kishi ni kuma kinzo kina son tutsiyeni. Ramlah ta ce "A'a ba haka bane ni dai nasan kana son Hannah da yawa fiye da... Yasa hannu ya toshe bakinta ya ce "Kema ina sonki kima daina tunanin wani abu kinji ko. Suka tuntsire da dariya Ramlah ta daga gira ta ce "Naji dadin amsarka na gode tunda na fita daga sahun masu son maso wani. Haisam yayi dariya ya fice, Ramlah ta rufo kofar ta shiga cikin gida. Haisam na fitowa ya nufi bangaran Hannah ya taba kofar yaji a datse yasa hannu a aljihunsa ya dauko mukulli ya bude ya shiga ya tarar babu kowa a falon sai ya nufi sama kan bene. Ya tura kofar dakin ya shiga a can karshen gado ya hango Hannah a kwance ta takure tana rusar kuka yayi sallama ya shigo ta dago da sauri suka hada ido Haisam sai ya girgiza kai ta sake kifa kai yayin da kuka mai tsanani ya rufo mata. Ya karasa gareta ya rada mata a kunne cikin sanyayyar murya ya ce "Goge hawayenki, bana so in sake ganin hawaye a idanuwanki zamu yi wata magana. Bayan kamar minti uku kukan da Hannah take yi ya tsaya. Can Haisam ya dago kanta suka hada ido sai ta sake kwantar da kanta a kirjinsa yana shafar lallausan gashinta ya ce "Hannah meye yasa ki kuka? Karki boyemin ki fadamin gaskiya kuma bana so ki sake rushemun da kuka. Tayi dan murmushi cikin sanyayyiyar murya ta ce "Nayi kuka ne saboda farin cikin da yayi mun yawa da wadannan kudi masu dunbin yawa daka bamu ni da Yayata. Haisam ya ce "Dalilin kukan ki na biyu kenan baki fadamin na farko ba, ina ganin babban dalilin da yasa ki kuka shine Allah Ya kawo miki kudi mai dunbin yawa a lokacin da babu Mahaifanki wadanda za ki bawa suma suci gajiyar arzikin da Allah Yayi miki. Haka ne ko ba haka bane? Hannah ta gyada kai ta ce "Hakane. Haisam ya ce "Yauwa na gode baki boye mun ba, Hannah kina da ilimi, kina da tunani da hankali matuka bai kamata ki dinga damuwa akan kaddara da jarrabawar da Ubangiji Allah Ya rubuto miki ba. Hakuri da tawakkali da kika yi a baya shi zaki ci gaba duk lokacin da irin wannan tunani ya fado miki a rai kiyi sauri ki kawar ki sawa ranki Allah Ya dauke ran Mahaifanki Ya mayar dake marainiya gaba da baya akan haka Yaso Ya ganki, amma sai yayi miki canji da wani mutum a matsayin mijinki kuma mai kaunar yaga farin cikin ki tamkar Iyayenki. Hannah ina ganin ko *ya*yan cikina bazan jisu a raina ba kamar yadda nake kwana in yini dake kullum a zuciyata ina ta sake-saken yadda zan faranta miki, daidai da sakon daya bana so ki shiga matsala. Bacin ranki ko kukanki tamkar dalmar wuta ake soka mun a zuciyata ki taimakeni Hannah ki daina saka kanki cikin damuwa domin damuwarki tana jawo mun mummunar damuwa. Tsakaninki da Mahaifanki sai addu'a nima kuma nayi miki alkawarin zan dinga taya ki da yi musu addu'a har karshen rayuwata. Ta dago ta dubeshi kallo mai kunshe da tsananin so da kauna tasa bakinta a gefen kumatunsa, ta sumbace shi ta rungume shi.
Ranar da Hannah da Haisam zasu tafi da misalin karfe goma na safe Ramlah da kanta take tuka motar ta kaisu filin jirgi tana daga musu hannu har suka hau jirgi suka tafi Abuja. Ita kuma ta dawo gida, haka ta kasance gidan shiru babu dadi sai ita kadai. Washe gari taje gidan su Haisam ta roki Hajiyarsa ta bata Amratu tazo ta tayata zama suka taho tare. Babu abinda Ramlah tasa a gaba yanzu sai shirye-shiryen yadda za'ayi ta fara gudanar da shirinta a gidan rediyo wato shirin nan nata mai taken SOYAYYA GASKIYA CE. Tana ta sintiri gidan rediyon nan mai farin jini wato FREEDOM RADIO domin bincike tasan yadda za'a sayar mata da filin da zata dinga gudanar da shirye-shiryen duk sati. Sun karbeta da farin ciki sun kuma zabar mata lokacin da suka ga ya dace ta dinga gudanar da shirin sannan sunyi mata alkawarin zasu fara yi mata tallar shirin kafin ranar da zata fara gudanar da shirin. Ramlah bata damu da dunbin kudin da zata dinga kashewa ba duk sati na sayen filin da zatayi shirin burinta shirin ya samu karbuwa a wajen jama'a sakon da take so ta isar ga al'umma ya isa gare su.
Duk ranar lahadi misalin karfe tara zuwa goma da rabi Ramlah zata dinga gudanar da shirin, sannan kuma duk ranar laraba da daddare a maimaita shirin. Wannan ne sati na farko da Ramlah zata fara gudanar da shirinta, jama'a da dama sun matso da akwatinan rediyonsu kusa da su don jin wannan sabon shirin da ake ta tallarsa kullum wannan gidan rediyo. Ga hirar kamar haka.
FREEDOM RADIO: Assalamu alaikum Jama'a ni Hajiya Hassana Hassan Safiyanu Gumel zan gabatar da wannan sabon shirin tare da Malama Ramlah Haisam Shitu. Malama Ramlah Haisam sannu da zuwa.
Ramlah: "Salamu alaikum.
Haj Hassana: Malama Ramlah jama'a da dama sun kagu suji wannan shirin saboda suna jin tallar shirin mai taken SOYAYYA GASKIYA CE. Zamu so mu fara dajin takaitaccen tarihinki, da kuma dalilinki na kirkiro wannan shirin, da ma'anar kalmar SOYAYYA GASKIYA CE.
Ramlah: murmushi, "asSalamu alaikum jama'a ni sunana Ramlah Shitu, shekaruna Ashirin da shida nayi makarantar nursery da primary wato secondry a kasar America bayan mun dawo nan kasa Nigeria na shiga jami'ar Bayero (B.U.K) na yi digiri akan harkar yada labarai (Mass communication).
Haj Hassana, dariya: "Ashe ma kema ta gidan ce *yar jarida.
Ramlah, dariya: "Kwarai kuwa nima *yar Uwar kuce *yar jarida. Don haka nema naga ya dace nima in bada tawa gudun mawar duk da ni ba ma'aikaciyar gidan redio bace ko talabijin naga ya kamata inyi amfani da karatuna inzo in bada tawa gudunmawar ga al'umma. Kamar yadda kika tambayeni meye ma'anar SOYAYYA GASKIYA CE, kuma meye dalilina na kirkiro wannan shirin? Dalilina na kirkiro wannan shiri shine, sai don kawai naga *yan Uwana Musulmai, Hauswa samari da *yan mata yara da manya muna da matsala wacce muke nema a wayar mana da kai akanta. Matsalar kuma ita ce ta mace-macen aure da rashin samun zaman lafiya a cikin zaman aure, zaki ga ko an zauna ba'a rabu ba to zaman ma babu dadi kaga miji da matarsa kamar ba suna son juna suka yi aure ba sun zama abokan gaba kowa na kokarin ya cusgunawa dan Uwansa shima ya rama laifin da dayan yayi masa, babu fahimtar juna. A gaskiya Hausawa basu yadda soyayya gaskiya ba ce. Zaki ga da zarar anyi aure shikenan soyayya ta kare sai zaman hakuri ko zaman *ya*ya to gaskiya ba haka bane. Yaune ranar farko da muka fara gudanar da shirin bazai yiwu in faiya ce muku komai ba a yanzu sai a hankali zanyi muku bayanai dalla-dalla. A yau dai abunda zan fara yin bayani akai shine, Mecece soyayya? Dawa ya kamata kayi soyayya? Kuma yaya za'ayi soyayya ta dauwama har abada?
Soyayya ita ce kaga mutum mace ko namiji kaji kana son ta ko son sa saboda Allah, ka zauna dashi saboda Allah, kana kula da halayensa abunda yayi mai kyau ka kara karfafa masa gwiwa ya ci gaba. Idan yayi abu marar kyau ka hana shi cikin nasiha da dabaru. Kana sonsa a lokacin da bashi da shi. Kana tunani a kullum yaya zaki faranta masa rai ku taimaki juna a lokacin da dayanku yake tsananin neman taimako. Mutum ba'a gama masa halitta har sai ranar daya mutu don haka kada ka guji dan Uwanka don wani tsautsayi ya same shi halittar ta canja. Ma'ana akwai hatsari na mota akwai wuta duk mutum zai iya nakasa idan soyayyar gaskiya ce baza ka tsaneshi ba, wannan ita ce ma'anar soyayya.
Haj Hassana: Malama Ramlah munji ma'anar soyayya, sai ki gaya mana dawa ya kamata kayi soyayya?
Ramlah, murmushi. Ko mace ko namiji ya kamata kasan dawa ya kamata kayi soyayya ma'ana kaso mai sonka. Soyayya takan fada kan mutumin ko mutumiyar da ita kuma bata da ra'ayinka kunga akwai matsala kenan.
Haj. Hassana. Wato kina nufin kenan kar a yi son maso wani?
Ramlah. "Yauwa zaki ga wani lokaci mace tana son namiji shi kuma baya ra'ayinta duk da dai ba'a cika samu ba, an fi samun namiji nason mace amma ita bata sonsa. Shi kuma zaka ga Allah Ya jarrabeshi da tsantsar sonta ita kuma bata sonsa, duk wata hanya da zai bi yaga ya mallaketa zai yi ta bi, ya yi ta shisshige mata yana mata kyaututtuka amma ita baya burgeta saima tsana da haushinsa yake sake lullubeta kuma har abada bazai burgeta ba saboda bata sonsa a zuciyarsa. To abu na farko daya kamata shine ya kyaleta yaje ya nemi mai sonsa itama ta auri wanda take so kada ya damu karya kullaceta bayin kanta bane domin soyayya abace wacce Allah Yake sakawa a zuciyar bayinSa. Hakika bana karfafawa jama'a gwiwa akan su nacewa wanda baya son su ina ganin hakuri shine babban magani, kaje ka auri mai sonka. Amma muddin aka takura akayi mata dole ko akayi masa dole, in namiji ne baya so, to lallai za'a samu mummunar matsala bayan auran. Saboda aure yafi yin karko in namijin da macen suna son junansu. Daga karshe zanyi magana akan yaya za'ayi soyayya da dauwamammiya har abada?
Soyayya zata iya dauwama har karshen zaman miji da matarsa har tsufa bata gushewa , shine da farko akwai kyautatawa. Namiji da mace kowanne yana neman kyautatawar dan Uwansa. Na biyu kulawa, mace ta kula da mijinta ta kowanne bangare, misali dafa abincin da zai ci tsafta ce ruwan shan sa, makwancinsa, ban dakinsa, tufafinsa, kulada dukkan yanayinsa na farin ciki ko na bakin ciki, ki kwantar masa da hankali ki lallashe shi har yaji wasai. Haka ma namiji ya kamata ya kula da matarsa gwargwadon karfinsa. Cinta, shanta, mahallin da zata zauna, lafiyarta ya kaita asibiti in bata da lafiya ita da yaranta. Kalamai masu dadi, wasa da dariya, tufafin da zata sa na fita kunya dai-dai karfinsa da magana mai dadi ba kullum zai fita ba da fada. To in har duk wadannan abubuwan suka samu tsakanin miji da matarsa zasu dauwama cikin farin ciki da son juna kullum.
Haj Hassana. "Gaskiya Malama Ramlah kin faiya ce mana manyan matsalolin da suke addabarmu a wannan al'umma tamu. Yanzu kuma zamu bude layin wayoyinmu don jin ra'ayin masu sauraron mu. Masu tambaya ko karin bayani. Sai dai don Allah jama'a ayi tambaya akan abunda muke tattaunawa yanzu, a cikin shirinmu na SOYAYYA GASKIYA CE.
Ramlah tayi mamakin ganin yadda ake ta bugo waya anata yabawa da shi mata albarka, wasu kuma suna tambaya akan matsalolinsu da suka dade suna nukurkusarsu sai yanzu Allah Ya kawo musu mafita. Ramlah tayi amfani da iliminta da tunaninta ta basu shawarwari har sai da suka gamsu. Daga karshe suka yiwa masu sauraro sallama akan sai sun hadu a wani sabon shirin wani satin. Ramlah ta fito farfajiyar gidan rediyon inda ta ajiye motarta kafin ta bude motar ta shiga, sai wayar hannunta ta hau ruri tana dubawa sai taga Hidaya ce take yi mata waya. Ta matsa gami da yin sallama cikin shesshekar kuka Hidaya take magana ta ce "Ramlah zo gidana kiga halinda nake ciki. Cikin rikicewa Ramlah take tambaya "Lafiya, me ya faru?
Hidaya ta ce "Ga danyen jego ina yi ko arba'in banyi ba ga tashin hankalin kishiya, shine Hajiyar su Habib tazo tayi min tas a gidan nan wai ita bazata yadda a kara zamar da danta zararre ba kamar yadda aka zamar da Haisam wai in har nasan bazan zauna lafiya da amaryata ba lalle ba dole in bar gidan, ga Habib nan hankalinsa a tashe a kullum. Ramlah ta hau lallashin Hidaya ta ce gata nan ma zata so gidan yanzu.
Daga Freedom radio sai gidan Hidaya Ramlah ta garzaya ta shafe awa uku tana lallashin Hidaya ta bata shawarwarin yadda zata zauna da kishiyarta lafiya.
Bayan tafiyar su Hannah da wata guda, Ramlah taji labarin an fara sayar da form din Jamb. Don haka ta garzaya Banki ta suyowa Hannah, ta cike mata domin Hannah ta sanar da ita irin cours din da take so first choice ta ce Medicine, second choice Biochemistry.
Hannah da Haisam kullum suna yiwa Ramlah waya da daddare suyi ta hira suce suna missing dinta sosai. Sun shaida mata sunje Dubai da London yanzu kuma suna America. Ramlah tayi musu fatan alheri da fatan su dawo gida lafiya. Daga America sai suka wuce Saudia don yin aikin Hajji. A lokacin saura sati biyu ayi arfa. Kasancewar Ambassadon Nigeria dake Saudiya abokin Baban Haisam ne don haka waya kawai Haisam yayi masa cewar gasu nan zuwa. Don haka kafin jirginsu ya sauka a filin jirgin Jiddah an turo motar da zata dauke su. An basu masauki a Jiddah Haisam ya ce ai Madina zasu wuce kai tsaye baza su zauna ba. Mota da direba aka basu suka tafi Madina Hannah tayi matukar farin ciki da ta ganta a cikin wannan gari mai albarka fiye da duk kasashen da suka zazzaga. Kamar a mafarki ta ganta a shabbaki harma gata ga Kabarin Annabi Muhammad (S.A.W) ta rike katangar kabarin ta rungume tayi kuka ta yiwa Allah godiya. Sannan tayiwa Mahaifanta addu'oin nema musu gafara da rahama a wajen Mahaliccinsu. Hannah tayi mamaki matuka ganin yadda Haisam yake mata ko Sarauniya sai haka.
An yiwa mazan Larabawa shaida wajen kulawa da matansu, sune masu rike musu takalma su rike musu yara da duk wasu kaya ita dai macen balarabe tafiya take sunke a cikin bakar abaya ta rufe dukkan jikinta har fuskarta, yana biye da ita yana kakkareta kada wani ya tabata, duk da wannan kulawa da ake yi musu sai suka ga ba komai bace akan yadda suka ga Haisam na yiwa Hannah. Haisam na rike da hannun Hannah gam duk inda zasu je ko tsinke baya barinta ta rike shi da direba ne masu rike kaya idan yaga kamar mutane suna tahowa ta daya bangaren sai kaga yayi sauri ya dawo gefen, a jima ya dawo bayanta yana kareta ya dawo gabanta ya komo daya bangaren nata yana kareta wai shi a dole kada wani ya tabata ko kar a tureta ta wahala. Haka suka sami kwana takwas a Madina duk sun kai ziyara zuwa wuraren da ake zuwa kamar Bakiyya, Masallacin Kuba da Dutsen Uhudu inda Kabarin su Sayyadina Hamza (A.S) yake. Haka duk kantin da suka shiga Haisam yayi ta jidowa Hannah kaya har hana shi take yi, ya ce shi dai sun yi masa kyau sai ya siya mata idan akwai guda biyu iri daya sai ya saya musu su biyu da Ramlah. Haka kantin gwal yayi ta saya mata har diamond ita da Ramlah da Mamarsa da kanwarsa Amratu. Kafin su bar Madina sai da suka yi dilar kaya katuwa aka daure musu akasa a mota suka nufi birnin Makka. Daga shigarsu Makka kai tsaye suka wuce kayataccen hotel din nan na masu hannu da shuni wato Intercontinental Hotel wanda ko a Larabawa ma sai wane da wane ne suke iya kama wannan hotel saboda tsadarsa, gashi gaf da Harami yake. Bangare guda Haisam ya kama a Hotel din ma'ana ga falo, dakuna biyu kowanne da toilet a ciki ga kicin da kayataccen darning area. Lallai duk wanda ya budi ido ya ganshi cikin hotel dinnan zaiyi tunanin ba'a cikin wannan duniyar yake ba sai dai ya kwatanta da Aljannah. Kayansu kawai suka sauke sai suka nufi Harami daman sun riga sunyi wanka sunyi niyya tun daga can Mikati tsakanin Madina zuwa Makka sun saka haraminsu. Suna shiga Harami sai suka yi Umara. Suka gama aikin Umara lokacin Sallar azahar ce sai suka bi Limamin Masallacin Sallah, wato Sudes.
Bayan an idar sai suka dawo hotel dinsu suka sa aka yo musu odar abinci kala-kala har da direban suka hadu suka ci, bayan sun gama sai Haisam ya dauko kudi mai yawa ya bawa direban ya ce ya koma Jiddah sai ranar da za'a fita Minnah ya zo ya daukesu da sassafe. Tunda ga su ga Harami ga kantina akusa babu inda zasu je da mota. Direba yayi ta godiya saboda yaji dadi sosai a wajen Haisam kayan da Haisam ya dinga saya masa a Madina shima sai da yayi akwati guda tasa. Suka yi sallama ya tafi. Haisam da Hannah sun kasance suna ta hutawarsu cikin wannan katafaren hotel sai lokacin Sallar la'asar suke fitowa su sami Sallar Jam'i sai suyi ta dawafi har magariba, bayan Sallar magariba sai su jira lokacin Sallar isha'i. Bayan an idar da Sallar isha'i sai su fito suyi ta shiga kantina suna siyayya. Nanma haka kayan da Haisam ya dinga sayawa Hannah abun baya lissafuwa. Haka Hannah duk danginta kowa da sunansa ta sisiya musu tsaraba komai dozin suka dinga siya. Bayan dilar da suka yo a Dubai da London da America da Madina duk sun aunasu Nigeria ta awan Kago wato Jirgin kaya.
HmmmmmmGANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter32
Ranar da za'a tafi aikin Hajji tun da asuba Mahajjata suka tashi suka yi wankan niyyar Hajji suka sa haraminsu da sassafe suka fara shiga motocinsu suna tafiya Minna. Direban su Haisam ya baiyana tunda sassafe don haka Hannah da Haisam suka fito sanye da haraminsu sai wata karamar jaka dauke da *yan kayayyakinsu kadan suka shiga suka tafi. Yadda ake fadar wahalar aikin Hajji Hannah bata ga wuyar ba saboda komai na su daban ne da sauran Mahajjata, domin suna tare da Ambassadon Nigeria da Iyalansa a Minnah, shemarsu ba a wajen da ta *yan Nigeria suke ba suna can gaba kusa da wajen jifan shaidan taku daya biyu zasu yi suje wajen jifan shaidan sabanin ta sauran Alhazai wadanda sai sunyi tafiyar miles da yawa kafin su isa wajen. Ga Haisam na rike da ita babu wanda yake murkusheta ko taka ta. Sunyi aikin Hajjinsu a nutse cikin sauki, sannan kowa ya fara neman hanyar garinsu.
Haisam da Hannah sun dawo Makka inda suka karayin kwana biyu a hotel dinsu daga karshe suka je suka yi dawafin bankwana suka zuba dilar kayan a mota suka nufi Jiddah. A gidan Ambassador suka sauka nan ma suka yi kwana biyu sun shisshiga kasuwannin Jiddah kamar su Baba Sharif da sauran kasuwanni da ke Jiddah. Ana gobe zasu tafi suka je tekun da ke nan Jiddah (beach) nan fa iska mai sanyi take kadawa ga larabawa nan da matansu da *ya*yansu suma suna zazzaune suna ciye-ciye da shaye-shaye lemuna da gahawa da dabino. Haisam da Hannah da *ya*yan Ambassador su biyu kanana Husain da Hussaina suma suka shimfida katuwar darduma suka baje kayan marmari dana kwalaye iri-iri suna ci suna hira. Husain da Husaina kanana ne *yan kimanin shekara shida, Husain ya jingina a jikin Hannah ya ce "Aunty Hannah bama so ku tafi dama kuyi ta zama anan tare da mu. Hannah tayi dariya ta shafa kansa ta ce "Husain ayi haka kuwa, muyi ta zama a gidanku mu ma fa *yan gidanmu suna can suna jiranmu mu dawo. Sai dai idan ka yarda in tafi dakai. Husain ya ce "Eh na yarda zan biku. Su duka suka tuntsire da dariya, Haisam ya ce "Kin samu da lallai a fadawa Mamarka ka hado kayanka. Hussaina ce ta tabe baki alamar zata fashe da kuka wai taji ance za'a tafi da dan Uwanta Husain. Haisam ya ce "Lah Hussaina kuka zaki yi don ance za'a tafi da dan Uwanki to share hawayenki ki daina kuka baza mu tafi dashi ba. Hussaina ta goge hawayenta tana dariya sai ta ce da Haisam "Uncle zaka bar mana Aunty Hannah anan? Bama so ta tafi. Haisam da Hannah suka tuntsire da dariya. Haisam ya ce "Lallai ma yarinyar nan kin fiye wayo na dauka yanzu kike kuka karmu tafi da dan Uwanki wato sai dai in bar muku tawa *yar Uwar ko? To naki, in bar Hannah anan in tafi Nigeria inje inyi me? Ai gara ace an kwashe mutanen Nigeria Kakaf an kawosu Saudia ni kuma a barni da Hannah a Nigeria mu biyu muna shawagi a kasar. Hussaina sake shawara ko kuma ki sake neman wata alfarmar ta wani bangaren banda wannan. Hannah tayi tsai tana kallon Haisam kallon da yake kashe masa dukkan sassan jikinsa wanda har cikin zuciyarsa yake
jinsa. Tayi dan murmushi ta sunkuyar da kai kasa ta ce "Tuntuni wannan bayanin naka ya wuce fahimtar Hussaina bata ma san me kake ce mata ba sai dai wacce ake yi dominta ita take gane abunda kake nufi. Haisam ya mayar mata da irin kallon da tayi masa ya lumshe ido ya ce "Alhamdulillah tunda wacce nayi dominta tasan abunda nake nufi. Hannah ta mike taja hannun Haisam suka fara tafiya a cikin yashi lubus yayin da ruwan teku yake yin kukan kura feshin ruwan yana feso musu. Tafiya suke a hankali suna hira Hannah ta kashe murya ta ce "Nawan, na dade ina mamaki amma ba'a mamaki da ikon Allah saboda ikon Allah ya wuce haka. Kiftawar ido da budewa yayi yawa a wajen Ubangiji Ya zamar da mai kudi talaka, Ya zamar da talaka mai arziki, Ya zamar da bawa Sarki Ya maishe da mai lafiya marar lafiya Ya canja kunci izuwa farin ciki. Haisam ya ce "Haka ne gaskiya ne. Hannah ta nisa ta ce "Akwai lokacin dana zamana a cikin kunci da tashin hankali, gabas da yamma kudu da arewa, sama da kasa duk inda na waiga sai bakin ciki da tashin hankali babu wanda zan gani naji dadi a rayuwata, babu mai lallashina, babu mai kwantar min da hankali. Na cire rai da kara samun walwala a rayuwata, nayi sallama da farin ciki nayi ban kwana da soyayya tunda wanda nake so ya ce min good bye ya tafi ya barni. Abu daya na rike shine Allah Yana tare dani kuma ko bai yimin sakayya a duniya ba nasan zai bani a lahira musamman ranar da nazo gidanka maimakon in ganka sai aka ce mun ka rasu hakika a ranar na sake tabbatarwa nayi bankwana da farin cikin duniya, ko me na zama nan gaba ko dawa Allah Ya hadani bana jin zan sake son kowa a duniya. Ba zato ba tsammani gaba daya Allah Ya juya mun rayuwata daga tsantsar bakin ciki izuwa tsananin farin ciki, na godewa Allah ina sake yiwa Allah godiya fatan Allah Ya hadamu a Aljannah ni da kai da Aunty Ramlah da Mahaifana masu sona da Iyayanka. Ta zubo da hawaye sharr daga idanuwanta. Haisam ya jawota suka zauna yasa hannu yana goge mata hawaye ya ce "Hannah kenan gaki yarinya mai hankalin manya. Addu'a bata faduwa kasa sai dai jinkiri. Ina addu'a Allah Ya hadani dake kullum dare da rana wani lokaci har in nemi yawun bakina in rasa, makogwarona ya bushe hawaye ya kafe amma shuru Allah bai hadamu ba sai bayan da duk muka fitar da rai, muka cire rai akan farin cikin rayuwa sannan Allah Ya hadamu, hakika Allah Yana ikonSa Yana kuma yin yadda Yaso a lokacin da Yaga dama, Allah Shine abin godiya mu gode maSa. Bayan sun gama zagayen su, su ka dawo wurin Husain da Hussaina su ka zauna suka ci gaba da ciye-ciyensu suna hira har karfe goma da rabi na dare sannan suka nufi wajan da direba yake suka shiga suka tafi. Bayan shigar su dakin da aka sauke su, suka yi wanka suka kwanta. Hannah ta jawo wayar dake dakin (land line) ta bugawa Ramlah sukai ta hira har Haisam yayi barci ya barta suna waya suna ta kyalkyala dariya yana mamakin me suke cewa a hirar. Hannah ta nunawa Ramlah tana farin ciki da zasu dawo gida su ganta. Har karfe biyun dare suna hira sannan suka yi sallama.
Washegari da misalin karfe goma sha biyu na rana jirgin su Hannah ya taso daga Jiddah zuwa Kano sun ci sa'a kuwa suna isa suka iso da dilolin kayansu da suka auno. Shehu direban su ne da Amratu, Karimat amaryar Yaya Habib da Yaya Habib su ka zo taryar su da motoci biyu su ka zo, aka shirma kayan a daya suka shiga daya suka tafi. Tun daga get suka fara ganin an lillika wani abu mai kyalkyali suna shiga farfajiyar gidan suka ga an kewaye ginin gidan da kyalkeli an rubuta WELL COME BACK HAISAM & HANNAH. Gefe guda kuma balo ce aka huhhura da yawa akayi runfa da ita a tsakiya an ajije wani tebur dauke da wani katon kek an rubuta a jikinsa WELL COME BACK HAISAM & HANNAH. Sunyi mamaki matukar mamaki ganin yadda jama'a suka taru, ashe liyafa Ramlah ta hada saboda murnar dawowarsu. Kujeru aka zuzzuba a farfajiyar gidan, can gefe Mahaifiyar Haisam ce da Mahaifiyar Ramlah da sauran tawagarsu a zazzaune. Gefe guda kuma matar mai girma gwamna ce Haj. Nusaiba Idris da babbar kwarta Rauda Shitu da sauran kawayensu. Gefe kuma Ramlah ce da manyan kawayenta Hidaya, Aysha Sulaiman, Hauwa Mamman da wasu da yawa daga cikin kawayensu. Mamaki marar misaltuwa zaka iya gani a fuskokin Haisam da Hannah.
Suna fitowa daga mota Ramlah ta taso da sauri tazo ta rungume Haisam, ta rungume Hannah ta kama hannayensu zuwa cikin gida bangarenta yayin da *yan waje suka dau tafi raf-raf-raf. Daga shigar su wata kayatacciyar shadda irin ta jikinta ta dauko musu dan su saka suyi anko su uku. Cikin sauri suka fada ban daki da suke dakunan suka yi wanka su ka dauro alwala, bayan sun idar da salla su ka cankama ado da wannan kayatacciyar shaddar wadda ta sha surfani da danyen zare. Kalar shaddar ruwan zuma ce ta yiwa Ramlah da Hannah matukar kyau. Haisam ma abun sai wanda ya gani musamman ma da ya dora hula kalar shaddar. Ramlah ta fito da su zuwa farfajiyar gidan inda jama'a suke, hakika wanna ma'aurata sun burge jama'a, jikin *yan gulma yayi sanyi, masu tsananin kishi sun fara yayyafawa zuciyarsu ruwan sanyin cewar kishiya ashe abokiyar zama ce. Bangaren Mahaifiyar Haisam su ka nufa su duka suka durkusa a gabanta su ka gaisheta da kawayenta, suna amsawa cikin fara'a da farin ciki suka yi musu sannu da zuwa bayan nan sai su ka dinga zagayawa wajan jama'a suna gaigaisawa. Hannah da Nusaiba suka rungume juna, lallai Nusaiba ta kasance tana tsananin kaunar Hanna tun suna yara. Raudah tayi nadama sosai akan abunda ta yiwa Hannah ada, har yanzu ta kan kasa sukuni sosai duk sanda suka hadu da Hannah. Hannah nata kokarin janta a jiki dan ta saki jiki da ita kamar yadda suke da Nusaiba. Daga nan suka nufi bangaren kawayen Ramlah wato su Hidaya, Hannah tayi mamakin yadda taga sun mika mata hannu sun gaisa faram-faram, suka yi musu sannu da zuwa, Ramlah ta jasu zuwa wajen kek dan su yanka. Bayan an kirga daga daya zuwa uku Hannah da Haisam suna rike da wuka su ka luma a cikin Kek su ka yanka aka tafa musu cikin farin ciki masu hoto da bidiyo suna ta dauka, *yan hidimar gidan ne suke fitowa da lemo kala-kala suna ajiyewa baki a kan teburan da ke gaban su wasu kuma na ajiye abinci da snacks kala-kala. Bayan anci ansha sai shahararren makadin da aka dauko ya fara buga kayan kidansa wato Shaba dan Kwalisa ya ware murya ya fara rero wakar "Uwar gida ran gida Haisam yana miki rawa. An yi rawa an cashe Haisam ya likawa Ramlah da Hannah kudi lokacin da suke tsakiyar fili har magariba ana cashewa sannan kowacce ta fara hada kayanta don kama hanyar gidanta.
Bayan dawowarsu Hannah da kwana uku sun gama baccin gajiya sun huta sosai sannan suka fara ware kayan tsaraba kowacce dila aka bude, sannan Hannah ta fara warware kowa tasa kasancewar Hannah tasan tsarabar da suka suyowa kowa. Akwati guda aka cikawa Ramlah da tsaraba, tayi mamakin wannan tsaraba wanda ko ita taje abunda zata suyowa kanta kenan. Abunda ya kara bata al'ajabi wata akwati daban Hannah ta ciko da kayan jarirai (Uni set) masu matukar kyau ta bawa Ramlah ta ce na Baby ne idan ta haihu. Ramlah tayi matukar godiya da nuna farin cikinta a fili. Wata katuwar akwati aka kai gidansu Haisam tsarabar Hajiyar Haisam da Babansu da Amratu da Izziddin, suma sunyi godiya kwarai. Ta tura direba ya kai wa Yaya Habib da matansa da yaransa gaba daya kowa da tasa, suma sun gode. Ba tare da Ramlah ta sani ba Hannah ta aikawa Mahaifan Ramlah turarruka (designers) da kannan Ramlah kowa da abin da ya dace da shi. Sai kuma tsarabar kawayenta Nusaiba da Rauda suma da *ya*yansu kakaf sai da ta bawa kowa tasa. Kama daga masu gadi zuwa masu share-share, da goge-goge, masu bawa fulawa ruwa da masu kwasar sharar gidan babu wanda Hannah ba ta bawa tsaraba ba suma suna murna suna godiya. Himilin kaya Hannah ta lufga cikin wasu tuma-tuman akwatina guda uku wannan tsarabar *yan Uwanta na Niger ne. Tana so taje tun kafin suyi tafiya tayi musu sallama Haisam ya ce sai sun dawo daga tafiya, yanzu gashi sun dawo taga yana mata kame-kame wai ba yanzu ba ta bari sai ta gama jarabawar Jamb tunda lokaci ya kusa ta zauna tayi karatu. Ramlah na taya shi bata hakuri akan ta bari bayan sai ta gama jarabawa sai ta tafi a nutse. Wasu litattafan karatu Ramlah ta suyowa Hannah na karatun Jamb din da zata yi, subjects hudu zata yi akwai English, Physics, Biology da Chemistry kuma Ramlah tayi mata Register a wata makaranta da ake bayar da horo na musamman (lesson) akan Jamb. Don haka Hannah ta hakura da tafiyar har sai bayan ta zana jarabawar. Kullum karfe hudu zuwa shida Haisam da kansa yake kai Hannah makarantar da take lesson ya jirata ta gama ya dawo da ita.
Hannah ta kasance tana karatu haikan domin har ta fara manta karatun da suka yi a sakandire amma yanzu karatun da take yi shi yake tuno mata da karatunta na baya. Lokacin da za ta zana jarabawa ya rage kwana uku Haisam yaje Jamb ofis ya karbo mata center ta. A management za tayi dan haka ranar litinin da sassafe bakwai na safe acan tayi mata. Haisam ya kawo ta kafin ta fito daga motar ya sumbaci kumatunta yayi mata fatan alheri Allah Ya bada sa'ar jarabawa daga karshe ya ce mata da zarar ta gama ta kirashi a waya ya zo ya dauketa Hannah ta shiga dakin jarabawa aka miko mata question paper da answer sheet sai kawai tayi murmushi da ta karanta tambayoyin kamar cin tuwo yafi su wahala a gurinta. Nan da nan Hannah ta ciccike ta gama, ta zauna kamar minti talatin bayan ta gama tana zaune kawai tana kallon masu hada zufa da cizon biro da kallon sillin taji tausayinsu wasu dan babu yadda za tayi ta taimake su ta basu amsa. Ta so ace wani ya rigata mikawa amma har ta gaji da zama babu wanda ya gama har yanzu, sai ta mike taje ta kaiwa masu tsaransu sunyi mamaki da su ka ga har ta gama daya daga cikin Malaman ya ce ta sake zama dai ta duba ko tayi mantuwa. Hannah ta ce babu komai ta gama. Tana fitowa daga dakin jarabawar sai ta nufi hanyar get din fita dai-dai kantin wata bayerabia taga benci, bayan ta gaishe da matar cikin fara'a ta roketa zata
zauna ta jira maigidanta zaizo ya dauketa. Bayan ta zauna ta bude jakarta ta zaro wayarta, bugu daya taji Haisam ya dauka shima yayi mamaki da yaji ta ce ya zo ya dauketa ta gama. Ya ce gashinan zuwa yanzu-yanzu.
Daya daga cikin Mamalam da suke tsaransu a dakin jarabawa ta hango ya nufo inda take, yana karasowa yayi musu sallama suka amsa sai ya yiwa Hannah lallausan murmushi ya ce "Minti biyu dan Allah *yan mata za muyi magana. Cikin mamaki Hannah ta tambaya ta ce "Ni? Ya gyada kai ya ce "Eh ke, dan ke na fito. Hannah ta harareshi ta ce "Malam yi hakuri ba zan iya zuwa ba sabo da kana magana ne da matar aure yanzu ma haka ina jiran mijinane zaizo ya dauke ni. Kamar
ta dabawa mutumin wuka a kirji, haka ya zabura ya rike kirji yana fadin "Subhanallahi yanzu ke matar aure ce, yanzu kina nufin kina da aure? Karki boye min fada min gaskiya. Hannah ta sake gyara mayafinta ta ce babu zancen wasa tsakanina da kai Malam ban sanka ba, ba ka sanni ba, yaya za'ayi in yi maka wasa? Ya rike baki yana sosa keya da daya hannun fadi ya ke "Subhanallahi yanzu ke matar aure ce, yaya za'ayi kenan? Ni gaskiya na gani kuma ina so zan iya fadawa cikin wani hali dan wallahi a rayuwata ban taba ganin yarinyar da na kamu da santa ba a *yan mintina. Cikin fushi Hannah ta mike ta kalli matar nan mai kanti ta ce "Madam sai anjima zan bar wajan nan. Matar na cewa "Ah ba yanzu kika yiwa maigidanki waya ba ya zo ya dauke ki, ya za'ayi ki tafi? Hannah bata iya juyowa ta bata amsa ba saboda kallon da mutumin ya ke yi mata yayi yawa, ta kada kai ta nufi get din fita ba tare da ta san inda zata ba. Tana fitowa ta tsaya cak ta kalli gabas da yamma sai ta hango wata *yar yarinya wacce shekarunta basu wuce goma ba tana tsugune a jikin katanga ga faranti da kwanika akai da alama dai mai tallar abinci ce. Yarinyar kuka take haikan cikin sauri Hannah ta nufi inda yarinyar take tana karasawa wajen yarinyar babu abinda ta fara gani a jikin yarinyar sai shatin bulala har wani wajen zaka iya hango jan jikin fatarta ta fashe.
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter33
Hannah ta gigice ta tsugunna a gaban yarinyar kafin ta tambayeta me ya same ta ta fara zubar da hawaye. Ta sa hannu a jakarta ta zaro wani hankici fari kal mai kamshi ta mikawa yarinyar ta ce "Goge hawayenki. Yarinyar ta karba tana gogewa kafin ta goge hawayen da ya zubo wani ya sake tsiyayowa. Hannah ta goge nata hawayen ta ce da yarinyar "Yaya sunan ki? Cikin shasshekar kuka yarinyar ta ce sunana Abida. Abida daina kuka goge hawayenki ki fada min dalla-dalla abin da yasa kike kuka zan taimake ki in Allah Ya yarda. Hannah ta tambayi Abida. Abida ta ce "Tallar wake da shinkafa nake yi, sai wani mutum ya kirani shagonsa ya ce in kawo masa zai siya na ajiye farantin abincin a kofar shagonsa sai ya ce in shigo ciki nace ai kofar karama ce farantin bazai iya wucewa ba sai ya ce to in dauko masa kwano daya in kawo masa. Na dauko kwanon abincin na shiga shagon sai ya ce mun zai saye abincin duka zai biya ni harma ya kara min kudin fiye da kudin abincina amma sai na yadda ya kwanta dani, na ce na ki ni ba *yar iska bace sai kawai ya rufe kofar ya kama ni da karfi na kwalla ihu da karfi shine ya doke min bakina har ya fashe ya bude
mun kofa yasa kafa ya maujeni na fado waje kan farantin abincin ya zube shine naje gida na fadawa Babarmu shine ta zane ni da bulala ta koroni ta ce duk inda zan nemo mata kudin abincinta inje in nemo. Yanzu bansan yadda zanyi ba. Abida ta rushe da kuka mai tsanani. Hawaye fal a idon Hannah tayi shiru can ta ce "Abida Babarki ita ta haifeki ko kuma kishiyar Babarki ce? Abida ta ce "Uwata ta mutu Ubana ya mutu wannan Yayar Mahaifiyata ce take rike ni. Hannah ta ce "Bata da *ya*aya sai ke kadai? Abida ta ce "Basa zuwa suna gida kullum wata rana kuma su tafi makaranta. Hannah ta ce "Kefa bakya makarantar? Ta ce "An cire ni da dai ina zuwa ajina ma iku yanzu na daina zuwa.
Hannah ta jawo Abida jikinta ta rungumeta ta fashe da kuka mai tsanani, tausayinta ya kamata ta tuno rayuwarta irin ta Abida ada maraici bashi da dadi. Can ta dago da kan Abida ta goge mata hawayen fuskarta ta ce "Abida dauko farantin ki zo muje kan tudun can mu zauna. Hannah na gaba Abida dauke da farantin abinci tana biye da ita. Ihun da Abida ta tsala ta kifar da farantin dake kanta shine ya razana Hannah taji gabanta ya yanke ya fadi ta juyo da sauri sai taga wata mata dauke da bulala da cakume rigar Abida ta baya tana kokarin taftafka mata murtikekiyar bulalar dake hannunta. Hannah ta taho da dauri ta fisge Abida daga hannun matar. Yayin da Abida ta taho a guje bayan Hannah ta labe fadi take "Hajiya ki taimake ni karki bari ta dake ni. Matar fada take harda kumfar baki danna ashar take tana cewa "Kyaleni da tsinanniyar yarinyar nan yau saina kusa kasheta idan ma ban kasheta ba, ta sani a Uku abincin naira na dukan naira har dari hudu da hamsin ta zubar min. Hannah hakuri take bawa matar kamar zata durkusa mata amma matar nan fadi take yau ta shiga uku asara ta sameta sai ta daki kudinta. Sai da taga magiyar da Hannah take yi tayi yawa har hawaye ne yake fitowa daga idanuwanta sannan matar ta tsagaita ta fara sauraron abinda Hannah ke cewa. Hannah ta goge hawayen fuskarta ta ce da matar "Kina Musulma Bahaushiya *yar Uwata ina rokarki ina hadaki da Ubangijinki ya baza ki saurareni ba? Haba Baiwar Allah wacce hasara ce ta sameki haka har zaki manta da Ubangijinki? Musulmin kwarai baya mantawa da Kalu innalillahi wa inna ilaihi raji'un, duk sanda masifa ta same shi. Kina ta dankara ashar kina fadin kin shiga uku kin lalace saboda Allah Ya dora miki asara ke kuwa baiwar Allah baza ki tattara al'amuranki gaba daya ba ki mika wajen Mahaliccinki mai bayarwa mai hanawa ba? Matar ta tsuke fuska yayin da haushin Hannah ya rufeta ta ce "Malama wa'azi kike mun ko kuma jaje kike mun? Don na kasa gane abin da kike nufi. Kin hanani in daki *yata kuma kina tutsuyeni akan nayi masifa dame zanji da asarar da nayo ko kuma da fadan da kike min? Hannah ta nisa ta ce "Yi hakuri ba fada nake yi miki ba shawara nake baki a matsayinki na *yar Uwata Musulma ki rike kalmar Kalu inna lillahi wa inna ilaihi raji'un a lokacin da masifa ta afka miki zaki ga yadda Allah Zai saka miki da alherinSa. Matar ta ce "Wannan kuma tasha nawa nake fada, yaya zanyi tunda Allah Ya hadani da shegiyar diya. Hannah ta ce "Karki ki shawarata nasan kina cikin bacin rai da damuwa amma ki ce Kalu inna lillahi wa inna ilaihi raji'un zaki ji sanyi a ranki. Matar ta ce "Bazan ki taki ba yarinya Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Hannah tayi murmushi ta ce "Yauwa sai ki jira kiga sakayyar da zaiyi miki. Ta ce da Abida ta tsince kwanikan da suka watse a kasa suzo su karasa kan wani dan dakalin siminti suka zauna. Abida kuma ta tsuguna a kasa cike da fargaba.
Hannah tasa hannu cikin jakarta ta zaro kudi naira dubu dubu guda goma ta mikawa matar, matar ta bude baki tana jujjuya kudin. Hannah ta ce "Naki ne wannan ki kara jari, amman dan Allah ki canja sana'a ki daina dorawa Abida talla kibar Abida ta koma makaranta tayi karatu ta daina talla. Ta zaro wata dubu goma ta mikawa matar ta ce "Wannan na Abida ne ki saya mata Uniform da takalmin makaranta da litattafai da jaka ta koma makaranta. Sai matar ta rushe da kuka ta durkusa a gaban Hannah tana godiya. Hannah ta kama hannun matar ta zaunar da ita ta ce "Babu komai Abida kanwata ce daga yau zan dinga taimakon ku insha Allah. Hannah tasa matar tayi mata kwatancen gidansu sannan Hannah ta rubuta lambar wayarta a wata *yar takarda ta mikawa matar ta ce idan suna da wata matsala ta buga mata waya ko nawa ne zata taimaka musu ita dai fatanta a daina dorawa Abida talla a daina tsangwamarta don Allah. Hannah ta dora da bawa matar labarinta tana nuna mata tasan irin halin da Abida take ciki kuma gallazawa maraya haramun ne. Matar tayi nadama tayi dana sani taji kunyar Hannah sosai. Kuka take kawai tana neman gafara wajen Abida ta yafe mata.
Haisam ne ya karkato da motarsa zai shiga get din makarantar ga mamakinsa sai ya hango Hannah zaune a gefe ita da wasu. Ya karkata motar ya nufi inda suke cikin rikicewa ya fito daga motar ya nufi inda suke saboda ya hango su suna magana suna koke-koke. Ba tare da sun ga zuwansa ba sai suka ga mutum a kansu ya tsaya kawai yana kallonsu cike da mamaki. Hannah tayi sauri ta goge hawayen dake idonta tayi murmushin dole ta ce "Yaya yaushe ka zo, Yaya ya akayi kasan ina nan? Ya ce "Zan shiga ciki na hango ku anan. Lafiya, wadannan fa, kukan me kuke yi? Matar ta rushe da kuka tana cewa tsakanina da ku sai godiya Allah Ya saka da alheri. Hawaye ne yake zubowa daga idon Hannah. Haisam ya zaro hankici a aljihunsa yana goge mata yaja hannunta suka shiga mota Abida da Babarta suna ta dagawa Hannah hannu suma suna ta kuka, Haisam ya ja mota suka tafi. Yayi shiru baice komai ba can ya nisa ya ce "Wannan yarinyar marainiya ce ko? Hannah ta kalleshi cikin mamaki ta ce "Yaya akayi ka sani. Haisam yayi murmushi ya ce "Haba *yar Baba nasan ki nasan halinki fiye da kowa ina ganin babbar matsalarki yanzu a rayuwarki bata wuce maraici ba, duk sanda naga kinyi kuka nasan kin tuna Mahaifanki wanda koda yaushe ina miki nasiha kiyi hakuri ki cirewa ranki tunanin mamaci duk wanda ya mutu ya mutu kenan bazai dawo ba har abada, naga yanzu kukan naki ya wuce maraicin da kike ciki ya koma kan duk marayun duniya kuka kike musu, kamar ma zuga ki nake nace bana son inga kina kuka hankalina yana bala'in tashi kinki ji. Hannah ta marairaice ido yayin da taci gaba da zubo da hawaye Haisam yasa hannu daya ya jawota jikinsa yana tuki da dayan ya ce "Yi hakuri to fada min yadda kika hadu da wadancan mutanen. Hannah ta gyara zama ta goge hawayen idonta ta fara bawa Haisam labarin abin da ya faru. Dai dai lokacin sun iso Tarauni ya karkata ya shiga wajen da ake sayar da kayan ciye-ciyen makulashe wato Oasis. Hannah ta ce "Zaka ci kek ne? Da ka bari naje gida sai inyi maka. Haisam ya ce "Haba ai sai wahalar tayi miki yawa tun shekaran jiya rabon da kiyi barcin kirki musamman jiya kusan a zaune kika kwana kina karatu. Tea din ma dana hada miki da safe ko kurba daya ba ki ba kika tafi kika barshi kuma yanzu na tabbata baki ci komai ba, naga duk kinyi wuri-wuri shine nake so in saya miki wani abu anan. Ya tsaya a bakin wajen ya ce da ita su shiga ciki, suka fito suka shiga. Hannah ta zazzabi abinda take so kamar meat pie da kek da shawarma sai juices na gwangwani da yogot. Bayan Haisam ya biya kudin suka zuzzuba musu a leda.
Suna fitowa bakin wajen Haisam ya kira almajiran da su ke bara a wajen ya mika musu ledojin duka ya ce su je su rarraba su ci. Hannah tayi kasake tana kallon ikon Allah, Haisam ya kalleta yayi murmushi ya ce "Kina mamaki ne? Yanzu na canja shawara baza ki ci kayan zakin nan ba gara mu wuce Tahir Guest Place ki huta sai da yamma ko ma da daddare mu koma gida. Hannah ta ce "Amma ai ya kamata mu koma gida Aunty Ramlah ta ganni tasan na dawo. Haisam ya ce "Zo mu tafi ke dai kin fi jin tausayin Aunty Ramlah a kaina komai ki ce Aunty Ramlah zanje in gani. Sun isa kayataccen katafaren Hotel din Tahir Guest Place dake unguwar Lamido Creasent. Kayataccen daki suka kama mai dauke da falo, darning area, ga daki mai dauke da katafaren gado da ban daki a ciki.
Abinci kala-kala ma'aikata suke shigo musu da shi suna jerawa akan darnin table. Hannah da Angonta sun ci sun sha sun gyatse har sun rage. Haisam ya ruko hannunta suka nufi cikin daki kai tsaye bandaki suka shiga dan su watsa ruwa su ji sanyi a jikinsu duk da ga sanyin split AC daya gauraye dakin daga can suka dauro alwala suka zo suka yi sallar azahar. Bayan sun idar ne suka kwanta akan katafaren gadon nan, yayin da Hannah taji gaba daya kashin bayanta ya hau qara saboda gajiyar da tayi saboda tsabar zama ga barci a idonta. Haisam yana mata tausa har barci mai dadi ya fara surarta. Kamar a mafarki taji Haisam na cewa "Gaskiya Nusaiba kawarki na sanki yanzun nan daga ofis din mai girma gwamna nake, na karbo miki takardun kwangila Nusaiba tasa a baki ta miliyan ashirin da biyar, bai fi ki kashe miliyan goma ba wajen gyaran jiki zaki gina mata da saloon da wajen kunshi. Rauda ma ta miliyan ashirin da biyar aka bata zata zuba kaya a sabon gidan da ta ginawa wan Babanta (interrior decoration). Bayan kwangilar titi da suka bani kwanakin baya ta miliyan dari biyu, yanzu ma sun sake bani kwangilar gina wani titin shima wasu miliyoyin ne gashi su biya akan lokaci ina gamawa. Hannah tayi zunbur ta tashi zaune tana sauraronsa. Yaci gaba da cewa "Na saya miki wannan katon filin na jikin katangar gidana anan za'a gina miki Masallaci da makarantar Islamiyya da ki kace kina son a gina miki. Hannah ta ce ina so a gina gidaje guda biyu a gefe don ina so in dauko Iya Salma da Uwar biyu su zauna a daya, Wada kuma ya zauna a daya yana kula da Super Market. Haisam ya ce "Filin babbane ai zai isa. Hannah ta rungume Haisam dan murna ta sumbaci bakinsa ta ce "Thank you my Dear, shima ya rungumeta daga nan suka shiga farantawa juna.
Bayan kwana biyu da sassafe Hannah ta tashi tafa shirya kayan tafiya a akwati guda kayanta dana Haisam sai akwatinan tsaraba da zata kai musu guda uku. Ta leko ta wundo ta kira shehu direba ya lufga a cikin but din motar da zasu tafi da ita mai kirar CRB. Wayar Hannah ce ta tashi Ramlah da Haisam daga barci Ramlah ta lalubi wayar ta dauka Hannah ta ce "Yayata yi hakuri naji muryarki kamar kina barci na tasheki gashi ba a son tashin mai ciki daga barci wallahi banji dadi ba yi hakuri, Ramlah tayi murmushi ta ce "Lah Kanwata babu komai wallahi. Kin tashi lafiya? Hannah ta ce "Lafiya kalau daman sallama zanyi miki saboda kar inzo in buga miki kofa da sassafe, sai dai ince sai Allah Ya dawo da mu. Ramlah ta ce "Haka tsai-tsaye sauri kike har ba za ki bari a gama break fast ba ku ci. Yallabai ne ya azazzale ki ya ce ki shirya da sassafe za ku fita ko? To ai kuwa ga shinan yana ta shirgar barcinsa ke ya hanaki kiyi barcinki. Haisam yayi zunbur ya mike ya fada ban daki da sauri. Ramlah tayi dariya ta ce "Yanzun nan kin ganshi muna magana ya mike ya fada wanka. Hannah tayi dariya ta ce "Cemin yayi in tashi da asuba in shirya tafiyar sassafe zamuyi, dan da asubama ya dinga waya na dauka ma ya shirya, to shikenan bari na jira shi. Ramlah ta ce "Ki fito kizo bangarensa ki same mu muci abinci, bari in yiwa su Zuwaira waya a bangarena ina ga sun gama abinci su shigo mana da shi. Hannah ta ce "To gani nan zuwa. Suka ajiye waya.
Suna cin abinci suna hira Hannah ta dubi Ramlah tayi murmushi ta ce
Shiga www.Littafanhausane.com.ng
Domin karanta complete chapter din
BARKA DA SALLAH ALLAH YA MAIMAITA MANA YASA MUGA NA BADIN BADADA LFY DAGA
DAGA:the founder of littafan Hausa zallah
.. "Auntyna badan ina ganin kin kusa haihuwa ba da sai nayi wata guda a can amma yanzu sati daya zanyi kawai. Haisam ya harari Hannah ya ce "Wai ke me wayo kina so dai kice min komin abuna duk da rakiyar da zanyi dan karki dade kina so kice min sai kinyi sati acan, kin san dai bazan iya mikewa a garin surukai in ta kwana har sati daya ba. Hannah ta narairaice ido ta ce "Na dauka saukeni zaku yi ku juyo idan na gama kwanakin ku dauko ni. Haisam ya ce "In kin dauka ma to ki sauke ai kafarki kafata kwana daya jal za muyi. Ramlah ta ce "A'a bai kamata ba ai dole tayi dan kwanaki Yallabai. Haisam ya lura da Hannah ta kule tana daf da ta fashe da kuka sai ya hau lallashinta yana cewa "To shikenan ai amarya bata laifi za muyi shawara a hanya dai. Ramlah ta ce da Hannah "Ga atamfofi can a jaka nasa Shehu ya dauka ya saka a mota da kudi a ambulan ki rabawa *yan kungiyata. Hannah ta ce "Kai Aunty har yanzu dai wahala baza ta kare ba? Ramlah ta ce "Babu komai Hannah yiwa wani yiwa kai, Allah ne fa Ya bani ikon tashi daga nan na je Niger na bude kungiya Allah Shine Ya ke bani abunda nake taimakonsu, Hannah tayi godiya daga karshe suka dunguma wajen mota, Haisam na cewa Ramlah lallai-lallai ta dinga kwana da wata a daki ta daina kwanciya ita kadai ko nakuda kan iya tashi cikin dare, ya shaida mata GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter34
A gidan baya Haisam da Hannah
suka kame Direba na jansu suka
tafi. Sun kama hanyar garin
dashi
cikin Janhuriyar Niger, tafiya
suke kamar ba'a mota suke ba
sanyin A.C na tashi yayin da
sautin kida ke
tashi a hankali. Hannah ta
kwanto akan cinyar Haisam
cikin shagwaba ta ce "Yaya nifa
so nake inyi sati guda a Dashi
sai mu wuce Babban-Mutum
inga Iya Salmai daga can sai mu
shiga Kazaure wajen Uwar Biyu
duk muga lafiyarsu. Haisam ya
ce "Amma sati daya yayi yawa
kiyi kwana hudu dai ni zan
wuce Maradi gurin abokina in
kin gama kwanakin sai muzo
mu dauke ki mu tafi Babban
Mutum da Kazaure a raar sai mu
wuce Abuja zanje inga yadda
suke sayar mun da motoci
sannan sai
mu huta a Nicon da Sharaton,
bayan kwana hudu sai mu koma
Kano. Yayi miki ko baiyi miki ba?
Ta ce "Yayi min tunda yayi maka
Nawan. Sun isa garin Dashi
yayin da mamaki da farin ciki ya
lullube
dangin Hannah. Hannah da Hajir
suka rungume juna suna murna,
Kawu Ahmad kuwa yasa aka
shimfidawa su Haisam tabarma
a zaure suka zazzauna dangi na
ta shigowa suna yi musu sannu
da zuwa. Nanfa aka garzaya
kasuwa dan siyo kayan abinci
iri-iri wanda za'a dafawa
wadannan
hadaddun *yan gayun baki. Fura
mai dadi da kindirmon nono
mai kyau aka kawo musu kafin
a
gama dafa musu abinci. Haisam
ya sha fura da nonon sosai
kasancewar yana son fura da
nono.
Bayan sunyi sallar azahar dai-dai
lokacin abinci ya nuna sai aka
fara zuwawa ana jerewa Haisam
nasa,
direba ma aka kai masa nasa a
kofar gida inda aka yi masa
shimfida. Hannah na cikin gida
tana cin nata kawaye da dangi
duk sun zagayeta kai ka ce biki
akeyi a gidan. Haisam da Kawu
Ahmad suna cin abinci suna hira
sai godiya Kawu Ahmad yake
yiwa Haisam.
Bayan sun gama ci la'asar tayi
suka yi Sallah sai Haisam ya
shaidawa Kawu Ahmad cewar
zai wuce
Maradi sai nan da kwana hudu
zai dawo ya dauki Hannah.
Kawu Ahmad ya roki Haisam ya
kwana
mana kafin ya tafi, Haisam ya ce
ba komai ai dare baiyi ba zasu
wuce kawai. Yasa yara suka
dinga
jido akwatina suna shigarwa
cikin gidan, ya ce kuma su cewa
Hannah ta fito suyi sallama zai
tafi.
Hannah ta bude akwatin
kayansu ta cire nata, ta bar
masa nasa a cikin akwatin tasa
aka kai masa
mota. Tasa Hijab ta fito ta iske
Haisam a zaune a zaune shi
kadai, ta durkusa ta gaishe shi
ya amsa
cikin fara'a ya ce "Kinga abinda
nake gudu ya faru dani. Hannah
ta ce "Yaya, meye ya faru da kai?
Ya
ce "Daidai da rana daya bana
son in rabu da ke amma gashi
kin jawo min sai nayi kwana
hudu zan
ganki. Hannah ta marairaice ta
ce "Allah Sarki kar ka damu
GANGAR JIKINA ce kawai bata
tare da kai
RUHINA yana tare da kai sai, su
duka suka yi dariya.
Haisam ya ce "Ai ni yanzu daga
GANGAR JIKIN har RUHIN so
nake su zamana tare dani, koda
yake
babu komai tunda mu duka
muna kasar Niger din tururin
numfashinki zai dinga buso ni.
Hannah tayi dariya ta ce "Nima
zanyi missing dinka. Haisam ya
mike tsaye ya ce "Babu wani,
dadin baki ne kin sami Hajir
kuna hira yaushe za ki tuna
wani Haisam.
Hannah ta ce "Ai kuwa da kasan
irin hirar da muke da Hajir da
kace mu shekara muna hira,
domin
asalin shakuwata da Hajir
hirarka kawai take taya ni.
Haisam yayi murmushi yayi mike
ya ce "Harna
fara jin kasala zan tafi ni kadai
in bar abinda nafi so a
rayuwata. Yanzu dai abinda
nake so dake shine ki sami biro
da takarda ki rubuta duk
wadanda ki ke so a dangi a
taimakawa da jari ko kuma
wata bukatarsu da suke neman
taimako kiyi min total zan canjo
kudin Niger acan, idan na zo sai
na baki ki rarraba musu. Hannah
ta amsa masa da to gami dayin
godiya da nuna farin cikinta a
fili. Ta ce "Kuma inaso in ginawa
*yan kungiyar Aunty Ramlah ofis
wanda zai zama anan za'a dinga
yin
taro kuma duk wani mai
sha'awar taimakonsu zai iya
kaiwa can. Haisam ya ce "This is
A very good idea, sai kicewa Kawu Ahmad ya
nemo fili ya kiyasta nawa za'a
kashe wajen ginin sai a bar
masa
ya gina. Hannah ta raka shi har
cikin mota suka dinga hira har
kamar bazai tafi ba, shi dai sake
nanatawa yake bai ji dadi ba
zaiyi kwana hudu bai ganta ba,
ita kuma hakuri take bashi har
dai ta
lallabashi ya tafi sannan ta shigo
cikin gida.
A kwanaki hudun da Hannah
tayi ta ziyarci *yan Uwa da
abokan arziki da yawa na cikin
garin dana
wajen garin kowacce tana kawo
kukanta wasu talauci ya ishesu
sun rasa yadda zasu yi, wasu
kuma auren *ya*yansu ya tashi
basu da kudin siyan kayan daki.
Hannah ta kaiwa *yan
kungiyarta ziyara bayan shela da
akayi aka tara su
a inda suka saba taruwa. Sunyi
murna da wadannan atamfofi
da kudadan da Hannah ta raba
musu ta ce inji Ramlah ta ce a
basu, ta shaida musu wannan
kadan ne kafin ta tafi zata sake
tara su ta
raba musu kudi fiye da
wadannan daga karshe tayi
musu albishir da cewa za'a gina
musu ofis da
katafaren dakin taro wato hall
za a zuba kujeru a ciki wajen da
za a dinga yin meeting. Ta kara
da
cewa da yardar Allah kungiyar
zata bunkasa zata dinga taron
tallafi ko da yaushe. Murna
wacce ba
zata misaltu ba a wajen *yan
kungiyar sai godiya da shi
albarka suke yiwa Hannah da
addu'ar fatan
alheri. Ranar da Hannah ta cika
kwana hudu tasan daga inda
gari ya waye Haisam zai dira a
garin
gashi bata gama ziyarar *yan
Uwa ba, don haka karfe bakwai
a gidan su Inna Haule tayi mata.
Tana
shiga tayi sallama ta iske Inna
Haule da Indo suna sana'ar da
suka saba, Inna Haule tasa Indo
a gaba
tana mata fada Indo kuma tana
tikar aiki. Inna Haule ta daga kai
ta dubi mai sallama sai taga
Hannah sai ta durkar da kanta
kasa ta kasa hada ido da ita ta
mike sumsum ta shige dakinta.
Indo ta
taho da sauri ta rungume
Hannah sai ta rushe da kuka.
Hannah ta zubo da hawayen
idonta ta ce
"Indo wajenki nazo na dauka
zan ganki a wajen taro ban
ganki ba na tambaya aka ce kina
gida
baki zo ba amma na bayar da
kashinki an kuwa baki? Indo ta
ce "An bani kinsan bani da halin
fita
inje wajen taro saboda aiki.
Hannah ta ce "Bari in shiga in
gaishe da Inna in zo mu shiga
daki muyi magana.
Hannah tayi sallama a dakin
Inna Haule sannan ta shiga ta
durkusa ta gaishe da ita ga
mamakinta sai taga hawaye fal a
idon Inna Haule ta zauna ta ce
"Inna lafiya kike kuka? Haule ta
sake rushewa da
kuka tana cewa "Ina ganin ki sai
Bello ya fado min a rai, tsananin
bakin ciki da takurawar dana
haddasa masa a sanadiyyar
gallaza miki dana yi.
Bello yayi min biyayya, ranar da
zai rasu mun rabu dashi yana
kuka yana rokona in sassauta
miki
Allahu Akbar sai gawarsa aka
kawo min ya mutu da bakin
cikina a ransa, duk da ni Uwarsa
ce mai zan
cewa Allah amma Bello mai
biyayya ne nasan zai yafe min.
Hannah ki yafe min a madadin
Bello da ke kanki abinda nayi
miki. Allah kenan Ya canja miki
rayuwarki kin min fintinkau,
yanzu kira Kawunki ki zo a
araba gadon Bello a baki naki.
Hannah ta zubo
da hawayen idonta ta ce "Inna
na yafe miki daman ba Bello kika
yiwa ba ni kika yiwa shi dai
yana damuwa a ransa duk
sanda zaiga kin gallaza min.
Sannan zancen a raba gado,
Inna rike duka na yafe miki ina
ganin yanzu gadon babu abinda
zai yi min,
ma'ana baki bani kaso na ba a
lokacin da nake bukatarsa. A
yanzu haka idan na karba sai
dai na
bayar saboda babu abinda na
nema na rasa kinga da in karba
in rabaki da shi in bawa wani
gara ki
rike duka tunda ga tsufa ya karu
karfi ya kare. Mai taimakon ki ya
rasu, ni ya kamata na baki ba na
karbi naki ba. Ni a ganina da kin
koma sabon gidan can na
siminti ki bar na kasar nan Inna
ki huta
saboda kar gidan ya zama asara
shi bai zauna ba ke baki zauna
ba, Allah Ya jikan Bello. Inna
Haule ta
ce "Amin na gode. Can zuwa
wani dan lokaci babu wanda
yayi
magana sai Hannah ta nisa ta ce
"Inna shawara daya zan baki,
mai zai hana ki bar Indo ta huta
da
wannan aiki da zagi da take sha
shekara da shekaru, Inna duba
kiga yadda Indo take tamkar
baiwa ita da *ya*yanta ita ce
gona, ita ce surfe da nika. Inna
Indo bazata iya tafiya ta barki
ba, ina zata kai *ya*yan nan? A
nan dai a jikinki take
samun dan abun da zata ci da
*ya*yanta ku zauna lafiya mana
amma aikin yayi yawa. Inna
Haule ta
nisa ta ce "Hannah naji abinda
kika cemun ni yanzu jikina yayi
sanyi in Allah Ya yarda zamu
koma sabon gidan Bello mu
zauna harda Indo da
*ya*yanta ko ni kaina nasan
bani da wata *yar Uwa mai
taimakona me min hidimomi
kamar Indo,
yanzu kwanaki amai da gudawa
nayi cikin dare Indo ce a kaina
har gari ya waye ita ta wanke
kayan kashin da amai. Gaskiya
kike fada mun kirawo Indo
itama in nemi gafarar ta. Inna
Haule ta
rushe da kuka. Hannah ta
kwallawa Indo kira ta taho da
sauri tazo ta durkusa ta ce "Ga
ni. Hannah
ta gyara zama ta yiwa Indo
bayani Inna ta saduda tasan
bata kyautawa don haka ta
daina takura mata. Amma sai bayanin Hannah
ya bambanta da tunanin Inna
Haule Hannah ta ce "Indo na
taho
miki da kudi ishasshe Kawuna
zai tsaya miki a rushe
bangaranki a gina miki na
siminti kema ki
zauna da *ya*yanki za'a fasa
miki kofar shigarku daban. Zan
baki jari mai yawa zan baki ki
dinga
sana'a kina cin abinci da
*ya*yanki, na dauki nauyin
karatunsu su koma makaranta,
kema ki huta da wahala a
rayuwarki. Indo ta rushe da
kuka tana godiya, Inna Haule na
kuka itama tana neman
gafararsu tana cewa
Shiga www.Littafanhausane.com.ng domin karanta complete chapter din
"Ai baza ayi
haka ba idan Indo ta barni
dawa zan zauna ya dinga
taimakona, ga tsufa bana iya yin
komai da kaina tunda ba gani
nake sosai ba. *Yan*yan Indo
sune aikin gonata sune suke
mun talla jikokina na cikina ko
aikensu
nayi basa zuwa. Hannah idan
kika yi haka kin raba zumunci.
Mu dai kaura can gidan siminti
da Indon
mu zauna. Hannah ta ce "A'a
Inna ai ba'a sabo da wuya,
*ya*yan Indo karatu zasu yi ba
talla ba. Indo ta ce "A dangi zaki
nemi wata ku zauna ni kam ai
nayi gaba shekara nawa ana
azabtar dani da *ya*yana an
hutar dani sai inki, ba dai ni ba
nemo wata. Hannah ta ce "Indo
ma *yar aiki zan daukar
mata ita ta kwanta ta huta. Inna
Haule ta rike baki tana
maimaitawa *yar aiki? Indo da
*yar aiki. Yaro ne ya shigo ya ce
"Wai Hannah tazo anzo daukarta
inji wani mutum a cikin mota.
Hannah ta ce musu tana zuwa ta
fito sai taga Haisam ne ta
karasa cikin motar bayan ta
gaishe shi ta shaida masa cewar
gidan su Bello Madu tazo zata
gaishe
da Mahaifiyarsa. Haisam ya
harareta ya ce "Gidan tsohon
mijinki ki ka zo ga alamar kuka
nan kinyi wato kun tuna baya.
Hannah ta tuntsire da dariya ta
ce "Kai Yaya wanda ya mutu ma
kishi kake da shi? Ba wani tuna
baya da akayi ta ganni dai tahau
kuka. Hannah ta tambayeshi
kudi tana so ta raba
musu. Wata *yar akwati ya nuna
mata a kujerun baya tana
budewa sai taga kudi himili
guda ya ce ta
dibi yadda zai isheta. Ta dibi
kamar dubu dari da hamsin
idan aka canja da kudin Nigeria,
ta ce yazo
ya shiga ya gaishe su. Bayan sun
shiga Haisam ya zauna kan wata
tabarma a dakin Inna Haule
suka
gaisa sai Hannah ta ajiyewa
Inna Haule dubu Hamsin ta ce
gashi ta sayi goro. Ta wuce
dakin Indo
ta sami Indo nata rusar kuka, ta
zauna tana lallashinta ta mika
mata dubu dari ta ce ta fara yin
jari sannan ta tabbata *ya*yanta
sun ci gaba da makaranta. Ta
kuma ce mata duk sanda take
da
matsala taje ta fadawa Hajir ko
Kawunta Ahmad zasu fada mata
a waya zata aiko mata ko nawa
ne,
kuma karshen watan nan zata
turowa Kawunta kudi a fara yi
mata ginin. Indo tayi farin ciki
tayi
murna kwarai. Ta shaidawa
Hannah cewar yau jinta take
kamar a aljannah saboda lokaci
guda an *yanta ta ta fita daga
sahun bayi. Suka dunguma suka
fito har Inna Haule suka rako
su har bakin mota suna koke-
koke suna godiya,
Haisam yaja suka yi gaba. A
zauren Kawu Ahmad aka
zazzage akwatin kudi ana hasafi
ga sunan
kowa a jikin takardar da yawan
tallafin da za'a bashi. *yan mata
goma sha biyu Hannah ta yiwa
kayan daki wasu jari ta basu,
duk an mikawa Kawu Ahmad ya
raba musu. Kudin Nigeria Miliyan
biyu
Hannah ta bawa Kawunta check,
matarsa dubu dari biyu da
Hamsin suyi jari su gina sabon
gida na
suminti, Kawu Ahmad yaji kamar
a mafarki yayin da kuka ya
barke masa yayi godiya sosai.
Haka Hajir ma tasha godiya da
kukan farin ciki. Haka dai
Hannah ta zuba kayanta a mota
suka shiga direba
Shehu shima ya shiga ya tashi
mota *yan Uwa cunkus a bakin
motar ana daga musu hannu
suka
tafi. Farin ciki fal a zuciyar
Hannah harma kamar tafi su
farin ciki saboda taimakawa
danginta data yi sun fita daga
tsantsar fatara da rashin da
suke ciki.
Sun nufi hanyar Babban-mutum
a Janhuriyyar Nigeria.
Karfe uku dai-dai a kofar gidan
Iya Salmai tayi musu.
Hannah ta shiga gidan da sauri
yayin da take kwada sallama
waige-waige take taga ta ina Iya
Salmai zata fito tayi tsalle ta
rungumeta. Wada ta gani a
bakin kofar dakin a tsaye yana
cike da
damuwa. Hannah ta karasa
gareshi cikin sanyin jiki da
dimuwa ta ce "Wada lafiya, ina
Iya Salman take?
Wada karka cemun Iyata ta rasu
. Yayin da ta fara hawaye. Wada
ya ce "Bata rasu ba gata nan a
zaune a daki tana kuka tun jiya
da yamma taki ci taki sha.
Hannah ta fada cikin dakin da
sauri ta iske
Iya Salmai tayi tagumi tana kuka
tana ganin Hannah sai ta sake
tsala kuka. Hannah ta ce "Iya
lafiya me ya faru? Wada ya shigo
ya zauna ya ce "Bansan taka
maimai meke damunta ba jiya
da rana ita da wani mutum suka
je wani gari ni dai bata fadamun
sunan garin da suka je ba sai na
ganta ta dawo da yamma tana
kuka ta ce mun wai
yau ido da ido taga Malam Habu
Mahaifinki har sunyi magana da
shi. Hannah ta zabura ta daka
tsalle ta dafa kirji ta fara ja da
baya ta fita daga dakin taje
tsakar gida ta zauna yayin da jiri
yake
daukarta bata gani sosai,
gabanta ya hau faduwa ta
tabbata lallai ciwon so ya zautar
da Iya Salmai har Malam Habu ya
fara yi mata gizau.
Uhm zasu dadeba zasu dawo..
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 35
Haisam ne ya shigo ya tarar da
Hannah a tsugune yaje ya tabata
yaga taki dagowa yasa hannu ya
tasheta tsaye yaga kuka take yi,
jikinta gaba daya karkarwa yake
idonta ya ki budewa gaba daya.
Ya
girgizata yana kiran sunanta ta
rushe da kuka ta rungume shi ta
ce "Yaya daman ana mutuwa a
dawo? Ya ce "Ban gane ba? Ta
ce "Iya Salmai na kuka a daki
wai jiya taga Babana har sunyi
magana da shi. Haisam yaja
hannunta zuwa cikin dakin
wajen Iya Salmai. Haisam yasha
wuya kafin ya lallashi Iya Salmai
ta daina kuka ta fara amsa
tambayoyinsa. Iya Salmai ta
bude baki ta fara
basu labari tiryan-tiryan. Ta ce
"Duk ranar kasuwa ina kai tallar
zogale ina zama tare da fulani
masu sayar da nono. Muna
labari dasu har suke bani
labarin wani bawan Allah
wanda yanzu ya zama
Malaminsu shi yake koya musu
karatun Sallah da basu iya ba sai
zuwansa garinsu. Suke cemin
mutumin basu san taka maimai
ko dan asalin wanne gari bane
don yaki ya fada. Yayi doguwar
suma har an binne shi masu
binne shi na juyawa sai su kuma
fulanin rigarsu suka kawo gawa
kusa
da wannan kabari sai suka ga
kabarin yana motsi, sai aka ce a
tona aga ko meye saboda daga
dukkan alamu yanzu aka rufe
kabarin watakila bai mutu ba
doguwar suma yayi yanzu ya
farka. Suna tonowa saiga
mutum mai rai bai rasu ba yana
salati, aka garzaya dashi asibitin
Babura wajen watansa guda
baya magana Malam Sule har
saniyarsa ya sayar yana sayawa
mutumin magani.
Bayan an sallamesu daga asibiti
ya warke ragas ya ce sunansa
Malam Garba amma bazai koma
garinsu ba saboda yasan an
gama zaman makokinsa ansan
ya mutu zasu tsorata suce yayi
fatalwa. Iya salmai ta sharbe
hawaye ta ce "Da raina na kawo
ko Malam Habu ne sai na ji ance
Malam Garba sunansa. Na
tambayesu ina ne garin su
mutumin sai suka ce bai fadi shi
ko dan wanne gari bane yaki
fada sai ya ce yana rokarsu dasu
rikeshi su taimake shi shi kuma
zai dinga taya su da kiwo zai
dinga koya musu karatu. Aka
gina masa bukkarsa a bayan
gidan Malam Sule. Malam sule ya
rike Malam Garba tamkar dan
Uwansa suje kiwo tare suci
abinci tare ya koya mana karatu
da daddare bayan kowa ya
dawo daga kasuwa
mutumin yana da kirki. Cikin
zumudi Hannah ta ce "Da ganan
sai akayi yaya? Iya Salmai ta ce
"Sai nabar maganar anan na
manta da ita saboda zaiyi wuya
ace Malam Habu ne kuma bance
su suffantamin yadda mutumin
yake ba na dai tambayesu yana
zuwa kasuwa wataran su
nunamun shi, suka ce baya
zuwa ko ina kullum
yana cikin riga. Wataran wani
mijin kawata ya zo ya same ni ya
ce yau yaje wata riga wajen
kanwarsa da take aure a rigar
yaga wani mutum kamar an
tsaga kara kamarsa daya da
Malam
Habu, har na tambaye shi yana
da wa ko kani a Babban-mutum
ya ce min bashi da kowa. Sau
uku
mijin kawar tawa idan yaje rigar
yake zuwa yake fadamun irin
kamar mutumin da yake gani da
Malam Habu harta baci,
tafiyarsu, maganar komai iri
daya da Malam Habu. Sai jiya na
ce muje rigar
nan inga mutumin nan. Wallahi
ina zuwa saiga Malam Habu, na
yanke jiki na fadi sai yazo ya
tasheni ya ce "Salmai lafiya? Na
sake tabbatarwa shine sai ya ce
"Ina yar Baba? Hannah ta rirrike
Iya Salmai tana kuka tana cewa
tashi ki kaini gurin Babana in
ganshi. Haisam ya rike baki
kawai yana
kallon ikon Allah sai Kabbara
yake yana cewa "Allahu Akbar.
Ya jawo Hannah jikinsa yana
lallashi ta kwantar da hankalinta
yau komai dare zasu je su
ganshi insha Allah. Wada ya ce
"Iya da kin lallabashi ya dawo
garin nan kun taho tare. Iya
Salmai ta ce "Nayi-nayi yazo mu
tafi yaki ya ce kuma kada in
fadawa kowa na ganshi yace
baya
son ya sake irin rayuwar da yayi
a baya tare da Iya Abu da
*ya*yanta shi zamansa a
rigarma yafi masa alheri da
kwanciyar hankali, daman
Hanne yake ji ya aiko a duba
halin da take ciki ance *yan
Uwanta sun tafi da ita Niger.
Shikenan hankalinsa a kwance
sai dai wani lokaci idan ya
tunata zaiyi
kuka harya godewa Allah.
Hannah ta girgiza kai ta ce
"Babana kuwa ki ka gani Iya
Salmai? Kai bashi bane Babana
ya mutu, mutuwa daya ce Yaya
Haisam ka tuna kaifa kace min
ba'a mutuwa a tashi. Haisam ya
ce "Hannah kar kiyi mamaki ikon
Allah ya wuce haka. Ana samun
irin haka mutum yayi doguwar
suma a binneshi ashe bai mutu
ba, aga kabarin yana motsi a
tono kuma mutum ya tashi ya ci
gaba da rayuwa sai dai wasu
sukan rasa ido ko kansu ya
karkace
ko bakinsu ya juye. Yana faruwa
amma a mutane goma baifi a
sami irin haka sau daya ba,
zamu je
mu gani Allah Yasa shine
Hannah ki huta da koke-koken
nan da kullum ki keyi na rashin
Mahaifanki. Iya Salmai ta ce
"Shine mana na ganshi har
munyi magana da shi, Malam
Habu ras yake babu inda
ya lahanta a jikinsa. Haisam ya
ce "Ikon Allah ne, ba tare dake
muka ji shirin INDA RANKA ba na
FREEDOM RADIO akwai mutumin
da aka binne shi sau uku ana
tonoshi ashe bai mutu ba suka
yi hira da shi shima ras yake ba
inda ya nakasa.
Hannah ta mike da sauri tana
cewa "Ku taso muje. Jikinta
rawa yake kamar ta zama
tsuntsuwa ta
dira a gaban Mahaifinta. Haisam
ya cewa Shehu direba ya zauna
shi da Wada zasu je su dawo.
Haisam na tukawa Hannah a
gefensa Iya Salmai a baya tana
nuna hanya suna tafiya. Sun isa
rigar suka iske bukkarsa babu
kowa wani bafillatani
yana biye da shanunsa suka
tambayeshi ko ina Malam Garba
yake sun leka bukkarsa baya
nan sai ya ce "Yanzun nan ya
rabu da su shi da Malam Sule
suna can kogi shanunsu suna
shan ruwa. Ya kwatanta musu
inda kogin yake suka nufa. Har
suka isa surkukin da mota ba
zata iya wucewa ba
suka ajiye motar suka fara
dabawa da kafa tun daga nesa
suka hango shanu suna shan
ruwa da
wasu mutane guda biyu suna
zazzaune. Suna karasawa
mutanan na juyowa sai ga
fuskar Malam Habu tar muraran,
ya gigice ya zabura ya mike
tsaye Hannah sai ta kwalla kara
ta rike kai ta
sulale ta fadi a sume Haisam ya
riketa dan razana.
Suka taru akan Hannah ana
zuba mata ruwa sai ta farfado,
fuskar Mahaifinta ta sake gani,
ta fada a
tsorace "Baba kai ne kuwa? Ya
matsa hawaye ya ce "*yar Baba
nine, suka rike juna sai kuka
suke
tamkar ransu zai fita yayin da
farin ciki tamkar ya hallakasu.
Wohoho hasko min zukatan
wadannan bayin Allah Uba da
*yarsa masu tsantsar son juna
da shakuwa.
Hannah ta ce "Baba kai ne
Uwata kai ne Ubana, kana raye a
duniyar nan baka mutu ba kaki
ka nemeni ai sai kazo in ganka
kayi min bayani in yaso sai kace
kar in fadawa kowa.
Malam Habu ya ce "Yi hakuri
*yar Baba da ace haka kawai
nazo miki tsorata zakiyi, ko
kuma ma
ki rasa hankalinki ban san ta ina
zan baiyana kaina gare ku ba,
da dai aka ce min kin bar
hannun Abu hakika na san kin
fita daga kangi. Suka karasa
cikin bukkarsa inda suka
zazzauna har Malam Sule.
Malam Habu ya zaiyane musu
labari kamar dai yadda fulanin
nan suka gayawa Iya Salmai.
Hannah ta bawa Babanta labarin
rayuwar ta har zuwa rana ta irin
ta yau ya dinga hawaye daga
karshe yayi hamdala ya mikawa
Haisam hannu suka gaisa yana
ta shi masa albarka. Daga karshe
Hannah da Haisam sunyi-sunyi,
juyin duniyar nan akan yazo su
tafi da shi Kano yaki.
Kasancewar Hannah tasan yana
matukar son yaje kasa mai
tsarki wato Makka sai ta ce
"Baba Makka fa zamu wuce da
kai. Tana ambaton Makka sai ya
ce "Indai Makka ce zanje kunga
sai inyi zamana acan in dinga
ibada har Allah Ya dauki raina,
kuje ku
gama shirye-shiryen ku kuzo ku
dauke ni ku kaini,
Allah Ya shi muku albarka.
Hannah ta nunawa Haisam ya
tafi kawai ya barta ita zata
zauna anan da Babanta tunda
bazai yarda ya bisu su tafi dashi
ba. Dakyar Haisam, Malam Habu,
Malam Sule da
Iya Salmai suka lallasheta ta
tashi suka tafi tana rusa kuka ita
a wajen Babanta zata zauna. Ta
bisu
bisa sharadin za suje Babban-
Mutum su kwana washegari in
zasu tafi su sake biyowa ta
ganshi sannan su wuce Kazaure
sai su wuce Kano kuma duk
bayan sati zata dinga zuwa tana
ganin
Mahaifinta.
Suna tahowa a mota Hannah ta
ware take ta murna kamar zata
zuba ruwa a kasa tasha. Ta ji
zuciyarta wasai tamkar bata
taba jin bacin rai a rayuwarta
ba, Haisam yaji wani sabon farin
ciki
saboda Hannarsa no more cry
(babu yawan kuka). Suna shiga
Babban-mutum suka bullo ta
kofar gidan Iya Abu har sun
wuce Hannah ta cewa Haisam ya
dawo
baya zata shiga ta gaishe da su
Iya Abu. Da farko Haisam yaki sai
da Iya Salmai ta sa baki sannan
ya bar Hannah, ta ce ya taho su
shiga tare suka dunguma su
duka da Iya Salmai cikin gidan.
Suna shiga tsakar gidan suka ji
yiiim a fuskarsu an watso masu
tsommokarai. Wasu mata ne
guda
biyu sun damko wata tsohuwa
zasu yi waje da ita.
Hannah ta jawo tsohuwar daga
hannun matan ta ce "Ku lafiya
ina zaku kai ta, me tayi muku?
Haisam ya tashi tsohuwar zaune
ya ce "Iya mai ya faru, ta ce "Ku
taimakeni bayin Allah wadannan
mugayen matan zasu kashe ni
wuya su ke bani.
Hannah ta matso kusa ta ce "Ke
wacece, kuma meye hadinki da
su? Tsohuwar ta ce "Sunana
Abuwa da gidana ne muka
sayar yanzu kuma haya nake a
ciki ban biya kudin haya ba
shine za su
kore ni. Sai Hannah ta ce "Iya
Abu kece? Ta ce "Ni ce, wace ce
nake gani kamar Hanne?
Hannah ta ce
"Ni ce, ikon Allah Iya Abu kece
kika zama haka, meya same ki a
ido daya ya tsiyaye? Ga kafarki
daya ma ta kumbura kamar
jarka ciwon kafa kike yi? Iya Abu
ta rushe da kuka, Haisam yayi
murmushi ya ce "Wai yanzu
Abun ce ta zama
haka? Iya Salmai ta ce "Abu ai
tayi kyan gani tun wata sadaka
mai tsoka da wani mai kudi ya
basu
dubu uku-uku ita da abokin
bararta Alh. Bilya, kunsan
kuturtar tasa ta baiyana, matan
da *ya*yan
duk sun watse kudi babu. Itama
Abu duk *ya*yan nata sun zama
*yan iska matan da mazan, sun
sayar da gidan Uban yanzu haka
haya take dan ba su da gidan
zama.
Matan gidan suka ce "Sun sayar
mana da gidan muka ji
tausayinta muka sakata a daki
daya haya
gashi yau wata biyu bata biya
mu ba *ya*yan nata *yan daba
basu je sunyo dabar ba sun biya
mata.ba
Wallahi yau bazata kwana a
dakin nan ba sai dai in ta shiga
cikin rumbun nan mai gidan
tururuwa.
Hannah ta bude baki zata roki
matan Iya Salmai ta katse ta ta
ce "*yar Baba barta ta kwana a
runbun tururuwar ko kwana
daya ne taji idan da dadi, kin
manta ranar da ita da abokin
bararta Alh.
Bilya suka yi watsi da kayanki
suka ce ki koma runbu. Haisam
ya ce "Haka akayi, ai kin bani
labarin yadda kuka yi, ta kwana
ko sau daya ne ta ji "Iya Abu ta
rushe da kuka tana cewa "Yanzu
yaya za'ayi mutum dan Adam
ace ya shiga wannan runbun
mai tururuwa ya kwana.
Shaga www.littafanhausane.com.ng domin karanta complete chapter din karku bari a Baku labari
Iya
Salmai na kwasar kayan Iya Abu
tana watsawa cikin runbun tana
cewa. "Kwana daya kawai zaki yi
kafin Hanne tayi tunanin inda
zata samar miki ki dinga kwana.
Hannah taji wani hawayen
tausayi
ya zubo mata ta fita kofar gida
tana hawaye.
Haisam da Iya Salmai kuma suna
can suna lallashin Iya Abu tayi
hakuri ta kwana a gidan
tururuwar zuwa gobe, Iya Abu
ta rarrafa ta shiga rumbun tana
rusar kuka tana cewa "Duniya ta
juya min baya yau na shiga uku
na lalace. Haisam da
Iya Abu suka fito kofar gida
suka sami Hannah da Musbah
dan gidan Iya Abu, kaca-kaca da
shi kamar mahaukaci talauci
tsantsa. Hannah ta girgiza kai ta
ce "Musbah ya haka? Ya fashe
da kuka ya fara zaiyanawa
Hannah irin halin da suke ciki na
talauci da bala'in da yake ta
bibiyarsu ya bata labarin cewar
sunyi aure sun kai matansu
gidan suna zaune da Iya Abu.
Iya Abu ta fara yi musu masifa
tana so ta gallaza musu su kuwa
suka bijire mata, har wata rana
suka rufe gidan babu kowa
suka yi mata duka har sai da
suka tsiyayar mata da ido daya
daga karshe ma suka fice suka
fasa auran. Mu kuma a
tsakaninmu muka dinga fada
akan gidan, matan su Mahajana
sun
zama karuwai suma suka ce nan
gidan zasu dinga kawo maza
mu kuma muka ki yadda a kayi
ta
rigima daga karshe gidan aka
sayar muka raba kudin ba tare
da Iya Abu ta sani ba duk muka
watse, yanzu sai tayi bara
sannan ta biya kudin haya. Ga
wani ciwan kafa, kafarta ta
kunbura
kamar bokiti komai ya cakude
mana. Hannah ta share hawaye
ta ce "A gidan Iya Salmai zan
kwana
gobe da safe ka tattaro min
kanku kuzo ku same ni kafin na
tafi. Ya rakasu har mota yana
soshe-soshe ya ce "To Hanne
bani na kashewa da daddare
mana, Iya Salmai ta ce "Zai sha
wiwin dare kenan. Hannah ta
ciro dubu biyu ta bashi ta
ce "Musbah kar kasha wani
abun maye kaci abinci ka
sayawa Mahaifiyarka abinci ka
kaimata. Ya dinga godiya da
farin ciki. Har zasu shiga mota
saiga Alh. Bilya ya taho ta ce da
su Haisam "Ga Alh. Bilya bari na
bashi sadaka ta karasa wajensa
ta zuba masa dubu biyar a
kwanan bararsa ta ce "Alhaji ga
sadaka. Ya ce "Na gode Allah Ya
karba.
Iya Salmai ta matso kusa dashi
ta ce "Bilya ka gane ta kuwa? Ya
ce "Baturiya ce ne? Kai kamar
balarabiya, daga Makka take ne?
Iya Salmai ta ce "Hanne ce *yar
gidan Malam Habu, budurwarka
ta
da mai dakin haya. Ya sunkuyar
da kai kasa dan kunya. Iya
Salmai ta sake cewa "Ina zaka
jene? Ya
ce "Abu na biyowa muje bara
ance za'a bada sadakar abinci a
kofar gidan mai gari, Iya Salmai
ta ce "Abu tana ciki kayi sallama
a runbun nan mai tururuwa
zaka ji ta amsa. Hannah ta shiga
mota
cike da tausayinsa, Iya Salmai
ma tazo ta shiga, daman Haisam
yana ciki yana kallan su ya
girgiza kai yaja motar suka tafi.
A hanya Hannah take cewa
"Yanzu tun a duniya Allah Yake
sakayya ba sai an mutu ba ko?
Haisam ya ce "Kwarai kuwa
shiyasa a ke son mutum ya
dinga shirya alheri a rayuwarsa.
Hannah ta ce "Allah Sarki yanzu
dubi kudi irin na Alh. Bilya babu
kamarsa a garin nan, dubi isa da
mulki da rashin mutunci irin na
Iya Abu yanzu sun zama a bamu
dan dago-dago. Iya Salmai ta ci
gaba da basu irin bala'in da Iya
Abu da *ya*yanta suke ciki.
Hmmmm su Iya Abu anga rayuwa GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 36
www.littafanhausane.com.ng
Da sassafe sai ga Iya Abu da *ya*yanta sun dira a gidan Iya Salma. Sun iske Hannah da Iya Salma
suna shan koko da kosai bayan sun gaisa sai Hannah ta bi kowannen su da kallo daya bayan daya, yamutsi sunan wani kaya. Duk sunyi kaca- kaca dasu kayan jikinsu dukkansu matan da mazan, nan fa aka hau koke-koke. Kallon Hannah
suke tamkar sun sami hoto saboda kyawun da tayi kamar gwal. Sai Hannah ta shiga yi musu nasihohi
tana basu shawarwari akan masu karuwanci, sace- sace da shaye-shaye su daina abu ne marar kyau. Ta kara da cewa harda rashin ilimi yake damunku babu arabi babu boko. Don haka su shiga makaranta su koyi karatun alkur'ani su yaki jahilci.
Daga karshe ta shaida musu zata bar musu kudi a wajen Iya Salma a hankali a samu gida mai dakuna
da yawa a saya musu su koma su zauna su rungumi Uwarsu sannan suyi aure, ta ce zata basu kudi akai Iya Abu asibitin kashi na Kano ayi mata maganin ciwon kafa sannan dukkan su zata ba su jari kowa ya samu sana'ar yi, kada su kara barin
Iya Abu tayi bara. Sai suka fashe da kuka dukkansu suna godiya. Iya Abu na kuka tana cewa "Na shuka tsiya na girbi tsiya, na cuci kaina
da *ya*yana na hana su karatu yau gashi sun tashi atutar babu. Hannah ki yafe min abun da nayi miki na yiwa Mahaifinki Allah Ya jikan Habi da Habu. Iya Salma ta ce "Allahu Akbar, albarkacin Hanne yau Malam Habu ya samu addu'a da dai ba'a taba yi masa ba.
Haisam ne ya shigo ya same su suna magana, Iya Abu na kwakwazon kuka tana nadama. Ya ce "Abu yi hakuri haka duniya ta gada ka so naka duniya ta kishi, sharri da jafa'i babu wanda baki dora akan Hannah ba, saboda tana
zuwa makaranta kin bi duk gari kina fadin iskanci take zuwa ba karatu ba a karshe kalmar iskanci sai ta dira akan *ya*yanki mata suna aure ma suka kaso auran suka zama karuwai, Allah Ya kiyaye
gaba. Iya Abu ta ce "Tone-tone ma ai a barshi Uncle Haisam kuyi hakuri dai Allah Ya baku ku bamu
amma bala'in duniya wanne ban gani ba, sakayya babu wacce Allah bai nunamin ba ni da *ya*yana
tun bayan tafiyar Hanne ban huta ba, zuciyata bata huta ba, sai bakin ciki kala-kala. Daga karshe Iya
Abu da *ya*yanta suka tafi da kudin da Hannah ta raba musu suna ta godiya. Hannah da Iya Salma da Wada suka zauna suna lissafi, Hannah ta bayar da kudin gidan da za'a kaiwa mai gari a sayawa su Iya Abu. Sannan ta dauko kudi mai yawa ta bawa Iya
Salma ta ce nata ne ta zauna a gida ta dinga cin Kaza da abinci mai dadi ta daina zuwa kasuwa talla,
sati na sama za'ayi bikin Wada ta bada kudin komai wanda za'a bukata na hidimar bikin. Ta shaidawa Iya Salma cewar nan da *yan watanni za'a gama
gina gidaje zata zo ta dauketa ita da Wada da matarsa su kaura Kano, katafariyar Super Market
zata bude shine take son Wada ya zauna mata a kantin yana kula da wajen. Murna tasa Iya Salma
kuka sai juya makudan kudin da Hannah ta basu take yi tana godiya.
Haisam da Hannah da direbansu sun fito daga Babban-mutum sai suka nufi Rigar da Malam Habu
yake, sun iske shi bai fita kiwo ba yana jiran isowarsu. Bayan sun gaisa Haisam yayi masa
bayani nan da sati uku za'a gama biza za suzo su dauke shi su tafi Makka. Sai farin ciki ya rufe Malam
Habu kudi mai yawa suka jifge masa, Hannah sai zarowa take tana tulewa a gabansa shi kuma
hanata yake yana cewa "*yar Baba kudin ya isa haka mai zan saya a Rigar nan da wadannan
makudan kudi. Shima Malam Sule sun shiga har gidansa sun raba musu kudi shi da matansa sai
godiya suke suna murna. Aka hadu a gidan aka yi ta hira har hira tayi hira Hannah ta gane ashe Malam
Sule kanin Malam Sale ne tsohon da ya bata abin busa a wajen kiwo tun tana yarinya. Aka rakata
gidan marigayi Malam Sale ta yiwa Iyalansa alheri mai yawa. Dakyar Haisam ya banbaro Hannah daga
rigar nan, bada son ranta ba ta baro mahaifinta.
*yan rigar suka fito kusan gaba dayansu wajen motar su Hannah suna daga musu hannu. Shehu
yaja motar suka tafi. Hannah zata fara hawaye saboda zata tafi ta bar Mahaifinta sai taga Haisam yana harararta, ya tsareta da ido baya ko kiftawa sai ta wayance ta fasa yin kukan ta hau yi masa
hira. Haisam yayi murmushi ya ce "Hannah kuka sunanki daga yau. Hannah ta kwanto a jikinsa ta
kashe murya ta ce "Kukan farin ciki zanyi Yaya, daka barni na yi, kadan fa zanyi hawaye daya biyu shikenan sai inyi shiru, suka kyalkyale da dariya dukkansu. Haisam ya ce "Kinyi digiri a kuka har kaiyadewa kike yi kenan.
Ba su tsaya a ko'ina ba sai a garin Kazaure kofar gidan Uwar biyu. Suka iske ta a tsakar gida tana
sakin danwaken siyarwa. Ciwon kafa ya hanata aiki a makaranta sai a gida take siyar da abinci
kala-kala na safe daban na rana daban na dare daban. Uwar biyu ta bude baki tana mamakin
ganin Haisam da Hannah. Haisam yayi dariya ya ce "Uwar biyu Hannah matata ce, munzo gaisheki ne.
Ta yi hawaye ta ce "Har Babban mutum naje neman Hannah da naji ance Mahaifinki ya rasu inyi miki
ta'aziyya, inga yaya zamanki yake da Iya Abu inda hali in dauko ki kizo mu zauna tare, sai aka cemin
kin koma Niger. Hannah ta ce "Allah Sarki Uwata ta kaina nima ina tunaninki kullum. Ta shimfida musu tabarma a gindin wata bishiya mai iska a tsakar gidanta, ta zubo musu ruwa da danwaken ta kawo musu sannan tazo ta zauna suka gaisa. Bayan sun
gaisa sai Hannah ta kwashe labarin Mahaifinta ta fadawa Uwar biyu cewar bai rasu ba yana nan da
ransa. Uwar biyu tayi murna ta taya Hannah murna matuka. Haisam ya dubi agogon dake daure a hannunsa ya ce "Yanzu sha biyu da rabi a Kano nake so muyi Sallar azahar muci abinci a gurguje
muka zo mu gaishe ki, sannan idan ba zaki damu ba Hannah tana so tazo ta dauke ki ki koma Kano
da zama tare da ita kibar wahalhalunnan. Yanzu haka tasa a gina muku gida a kusa da nata ki koma ke da Iya Salma. Uwar biyu ta fashe da kukan murna, kudi dumus taga Hannah ta debo daga
jakarta ta ajiye mata a gaba tayi godiya ta rako su har wajen mota suka shiga suka tafi.
Suna isa Kano basu tsaya a ko ina ba sai a filin jirgin sama Haisam ya cewa Shehu direba ya tafi gida da motar ya shaidawa Ramlah sun wuce Abuja nan da kwana hudu zasu dawo. Bayan sun sayi tikiti suka yi Sallah suka ci abinci a filin jirgin. Sun isa Abuja da yamma, direban ofis din Haisam yazo ya daukesu wato wajen sayar da motocinsa. Kai tsaye ya wuce
da su katafaren Hotel din nan wato Sheraton Hotel. Hakika hutu ya yiwa masoyan nan biyu dadi fiye da
na kasashen wajen da suka je. Saboda hankalin Hannah a kwance yake, sai farin ciki ya rufeta idan
ta tuna Maihaifinta na nan a raye bai mutu ba har tsalle take akan gado ta diro kasa ta fada kan
Haisam tana murna. Haisam sai ya zauna yana kallonta kawai yana murmushi domin farin cikinta
shine farin cikinsa.
Da yamma suna saukowa wajen swimming pool suyi ta wanka da safe kuma sai direban ofishin
Haisam yazo ya dauke su suyi ta yawo a cikin gari waje-waje na hutawa da wajen ciye-ciyen makulashe. Gidajen *yan Uwansa da abokan arziki duk sun zazzaga haka ake ta bawa Hannah
kyaututtuka. Sunje wajen sayar da motocin Haisam wajen ya kawata ga motoci galla-galla. Kamar da
wasa Hannah ta zabarwa Mahaifinta wata galleliyar mota ta ce idan ya dawo daga Saudia zata bashi, maimakon tayi godiya Haisam ne yake mata godiya saboda yaji dadi sosai yau Hannah ta tambayeshi abinsa. Kwanansu takwas a Abuja sannan suka
hau jirgi suka dawo Kano. A daren da suka dawo Ramlah zata haihu. Haisam da Hannah suka rakata
asibiti, ta haifo zukekiyar *yarta mai kama da Ubanta sak. Bayan kwana biyu Haisam ya tambayi
Ramlah wane suna za'a sawa *yar, abin mamaki sai ta ce asa mata sunan Hannah. Hannah tayi farin ciki matuka gata jininta ya hadu da *yar, bacci ne kawai yake rabo Hannah daga dakin Ramlah wajen *yar jaririyar. Ranar suna anyi bidiri Naira ta sha kashi an kashe Naira, an lika Naira. Taron mata kuwa harda wadanda ba'a gaiyace su ba, kasancewar Ramlah yanzu ta zama mai jama'a ana ta sanarwa a radiyo sai jama'a masu sauraron shirinta suke nemo inda take suna zuwa tayata murna.
Saboda hidimomin suna Hannah da Haisam basu samu dama sunje sunga Malam Habu a cikin satin
nan ba, sai sati na sama Haisam ya fara cuku-cukun neman bizar tafiya Makkah. Ya ba Hannah hakuri ta
bari in an samu bizar tafiya sai suje su dauko shi su wuce. Suna cin abinci suna hira suka sanarwa da
Ramlah halin da ake ciki cewar Mahaifin Hannah bai rasu ba, tayi mamaki kwarai ta taya Hannah murna sosai, sun shaida mata nan da sati mai zuwa zasu je
su dauko shi su kai shi Saudia. Haisam da Hannah sunje gidansu Haisam sun shaidawa Alhaji da
Hajiyar Haisam labarin Mahaifin Hannah, da farko Mahaifin Haisam da dariya ya tuntsire saboda labarin yayi masa kama da tatsuniya,, Mahaifiyar Haisam cemusu tayi yaushe muka zama Kakannin ku kuke mana wasan haka? Sai da suka ga da gaske suke har rantsuwa Haisam yake ya shaida musu zasu je su dauko shi sati mai zuwa su raka shi Saudia don ya ce ba zai biyo su ya zauna anan ba. Sunsha mamaki sun taya Hannah murna kwarai da gaske.
Bayan komai da komai na tafiya ya kammala Haisam da Hannah suka shirya suka nufi rigar da Malam Habu yake suna isa babu bata lokaci mai yawa suka dauko shi suka taho da shi Kano. Malam Habu yasha mamaki da ganin gidan Hannah ya bude baki kawai yana kallon kayan alatu, a bangaren Hannah aka sauke shi a dakin kasa.
Ramlah tazo ta gaishe shi sai da fuskarta ta fado masa a rai, ya hangota lokacin da tazo ta ci masa
mutunci akan Hannah ta rabu da Haisam, ya jinjina a ransa ya ce rayuwa kenan yau gata a durkushe a gabansa tana gaishe ni cikin girmamawa. Ya karbi *yarta yayi mata addu'a daga karshe ya nuna farin cikinsa da aka sa ma yar sunan Hanna.
Shiga www.littafanhausane.com.ng
Domin karanta complete chapter din
Da daddare Mahaifan Haisam suka zo suka gaishe shi suka kawo masa farfesun dakwalan kaji da juice kala- kala. Bayan zuwansa da kwana uku suka nufi kasa mai tsarki. Kwanan su Hannah goma a Makka.
Bayan sun tabbata sun samarwa Malam Habu gidan zama wadatacce kudi mai dinbin yawa wanda zai ishe shi ci da sha da sutura sun daukar masa ma'aikaci daya da zai dinga kula dashi, wankin kayansa da kuma rakashi duk inda zaije kamar Madina ko Jeddah duk dai inda yake so ya je.
Mallam Habu yayi matukar jin dadi da ya bude ido ya ganshi cikin wannan kasa mai tsarki ga shi ga
Ka'aba, zai je duk inda yake so a cikin kasar Makka babu mai kamashi saboda sun yi masa igama ma'ana takardar izinin zama a kasar har lokacin aikin Hajji.
Bayan su Hannah sun dawo Nigeria ba dadewa jarabawar Jamb dinsu ta fito kai tsaye suka bata
Medicine saboda points dinta ta cancanci idan course din da yafi Medicine ne a bata, murna a wajen Haisam abin baya musaltuwa har ya fi Hannah murna. Haisam ya taya ta yin registration,
bayan registration ba dadewa suka fara lectures. Karatu tukuru ta sa a gaba musamman ma idan ta
tuna irin yadda karatun Medicine yake da muhimmanci a wajen taimakon al'umma. Tana da burin ta ga tana taimakon talakawa a rayuwarta.
Ginin da ake yiwa Hannah yayi nisa, duk da ba'a kare ginin ba amma zaka san katafaren gini ne mai
kyan gaske. Shinfideden masallaci, daya bangaren makarantar Islamiyya ta matan aure da yara ga
bandaki nan a gefe. Can baya kuma wata kofa ce inka shiga zaka tarar da gidaje iri daya guda biyu,
masu dauke da katafaren falo da dakunan barci uku-uku kowannensu da bandakinsa a ciki da kicin. Haisam ya sayawa Hannah da Ramlah wani katon fili a Ahmadu Bello way inda kowacce a cikin kudinta ya ke gina mata katafaren kanti kamar yadda Hannah ta ce tana son super market a kusa da nan ake gina mata wani ofis na tallafawa
marayun yara. A kusa da shi katafaren kantina biyu ne na Ramlah, daya na sayar da kayan Senegal dinkakku (ready made) daya kuma na sayar da takalma da jakunkuna *yan waje.HaiRamHannah! HaiRamHannah!! Bayan an gama ginin an kawata
shi da fitilu da tiles sai akayo odar kaya wasu daga kasar waje wasu daga kamfanonin nan kasar. Dai-
dai lokacin an gama ginin Masallaci. Islamiyya da gidajen Hannah sai aka zuzzuba kayan da suka
dace a cikinsu. Hannah da direba suka nufi Babban-mutum don dauko Iya Salma da Wada da matarsa, *yan kayayyakinsu na sawa kawai suka tsinto sababbi suka shigo mota suka biyo Hannah,
suka bi ta Kazaure dan dauko Uwar biyu. Daman ta gama sanarwa danginta zata koma Kano Haisam da Hannah sun yi alkawarin zasu dau nauyinta gaba daya har bayan ranta. Suna zuwa awa biyu tayi yawa Uwar biyu ta dauko dan buhun kayanta ta yiwa Makwabta sallama daman babu wanda ta
ajiye banda *yarta Halima kuma tayi wani sabon Auren a Daura, ta shigo mota suka tafi. Sun sha
mamaki suna ta kallon katafaren gidajen da akace nasu ne komai da komai akwai a gidan. Kowanne
daki an shimfida kafet da makeken gadaje da mudubai da waduruf din jikin bango. Haka falo ansa kujeru da kayan kallo. Kicin ma da cooker
gas, fridge da duk abubuwan amfani, komai sabo fil a ledarsa. Hatta kayan sawarsu Hannah tasa an dinko musu atamfofi an zuba a cikin waduruf. Sanyin A.C ko ina ya gauraye gidan, masu aiki biyu
aka ajiye a gidajen daya mai girki daya mai shara da wanke-wanke da wankin bandaki. Ga mai
wanki da guga nan duk sati zaizo ya dinga dauka yana wankowa. Wada ya gigice a lokacin da Hannah da Haisam suka kaishi katafariyar super market din, anan
akace ya dinga kula da ma'aikatan wajen yana sa ido akan yadda ake gudanar da cinikin.
Kasancewar yayi makarantar sakandire ya iya karatu da rubutu. Hannah ta kara masa da cewa "Yanzu baka san gari ba kuma baka iya mota ba za'a dinga kaika ana dauko ka da motar kantin,
nan gaba zan saya maka taka ta kanka. Wada yana ta murna yana godiya haka Iya Salma da Uwar
biyu sun sha koke-koke don murna suna ta godiya. Wada da matarsa Jidda a gida daya, Iya Salmai da Uwar biyu a gida daya kowacce a daki daya, daki daya ne babu kowa aka kulleshi. Su ci, su sha suyi wanka a kunna musu kallo shikenan
aikinsu suyi ta hira. Wani lokaci Iya Salma ta ce azo a danno mata lamabar Malam Habu a Makka su
gaisa. An huda kofa wacce zata kaika gidansu Hannah, kullum Hannah sai ta shigo gidan tsofaffin
nan ta tayasu hira bayan ta taso daga makaranta,
gaba dayansu suna cikin tsananin farin ciki da nishadi ko ba'a gaya maka ba idan ka kalle su.GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter37
Hannah taji dadi ta gama jarabawa a lokacin da ake tafiya aikin Hajji don haka ta shaidawa Haisam tana so taje Makka ita da Uwar biyu da Iya Salmai suje su hadu da Mahaifinta suyi Hajji gaba daya don ta taimaka masa kada yasha wuya. Haisam ya amsa mata da cewa babu komai zaiyi kokari yasa a nemo musu biza su dukka gidan ma sai su tafi, har shi da Ramlah da *yarta Hannah, da Wada da matarsa da gaba daya *yan aikin gidan mata da maza. Haka kuwa akayi, suka dunguma suka dira a kasa mai tsarki kwatsam Malam Habu ya gansu nanfa murna ta hargitse. Kamar yadda su Hannah suka yi aikin Hajji a waccan shekarar cikin sauki haka wannan shekarar ma, mota katuwa da direba aka aikowa Haisam daga gidan ambassador. Bayan an sauko daga arfa lafiya, sai suka dinga shiga kasuwanni ana ta siyayyar tsaraba. Makudan kudin da Haisam ya rarrabawa dukkanninsu kowa ya yiwa *yan Uwansa tsaraba. Kowa yaji dadin tafiyar nan sosai da sosai. Haisam da Hannah da Ramlah ne suka shigo bangaren Malam Habu dan su gaishe shi da sassafe. Suna zaune suna *yar hira saiga Uwar biyu da Iya Salmai suma daga dakinsu sun shigo don su gaishe da Alhaji Habu aka hadu ana ta hira wasa da dariya.
Hannah ta ce "Baba da kai zamu tafi fa tunda yanzu kayi umara sau da yawa ka yi aikin Hajji sai mu koma gida. Alh. Habu ya girgiza kai ya ce "*yar Baba ki barni kawai inyi zamana daman ku kadai nake da su a Nigeria kuma gaku nan akai-aikai kuna zuwa gara inyi zamana inci gaba da ibadata har lokacin mutuwa in mutu anan. Hannah ta ce "Haba Baba kaso ka mutu babu aure bayan ga masoyiyarka tana nan tana jiranka ka dawo ka aureta. Alh Habu ya ce da Hannah "Ke *yar Baba bana son shakiyanci wacce irin masoyiyata, wacece masoyiyata kuma? Gaba daya aka sa dariya. Hannah ta ce "Baba har zaka manta tsohuwar matarka *yar Uwarka, jininka Iya Salma a tuna baya mana Baba a koma ayi aure. Haisam ya ce "Baba Hannah dai nason ayi tuwona mai na ga Uwa ga Uba, Baba a duba wannan al'amarin. Malam Habu yayi murmushi ya ce "Kaima tayata kake? Kyale *yar Baba tsokanarmu take yi Salma dince ta ce mata tana so tayi aure? Iya Salma sai yanzu tasa baki da murmushi kawai take yi ta ce "Da dai na gama aure tin daga kanka amma yanzu da yake kaine ai bana ce a'a ba. Soyayya ai bata tsufa. Hannah ta rangada buda ta ce "Ai an gama daurin aure sadaki kawai zan dauko in biya, da Riyad ma zan biya kudin Makka, Uwar Biyu tayi dariya ta ce "Lallai wannan aure naku Alhazawa ne don a Makka aka kullo shi, Allah Ya sanya alheri Ya ba da zaman lafiya. Hannah ta ce "Iya Uwar biyu ko kema in tuno miki baya ne? Ta ce "Ban gane ba? Hannah ta ce "Ko kema zaki zama amaryar Iyata Salma ne ku zama ku biyu a daura dukka rana daya tunda gidanku daya tuwona maina kenan. Gaba daya aka kece da dariya. Haisam ya ce "Lallai har kin yiwa Iya Salma kishiya tun kafin ta tare. Hannah ta ce "Ai itama tsohuwar soyayya ce tun a lokacin da take kaini gida daga makaranta ta fadamun, ai shima Baban ya sani, sun so su daidaita ya ce mata masifar Iya Abu ce kawai zata hana ya aureta. Iya Salma tayi caraf ta ce "Ni da za'ayi haka ma da nayi murna saboda ni a rayuwata ina son kishiya, bana kyamar kishiya ko Abu aini nasa dole ya aurota. Hannah ta dauko turare tana ta fesa musu su dukka ukun wai amare da angonsu. Wannan abu ya yiwa kowa dadi ba kamar Hannah. Ramalah da Haisam sunsha dariya har sun godewa Allah. Yanzu Malam Habu ya yarda zai biyo su su dawo Nigeria. Haisam ya shaida masa an nadashi a matsayin Limamin Masallacin da Hannah ta gina daman sunansa aka sawa Islamiyyar ABUBAKAR IMAM ISLAMIYYA.
Su dungumo gaba daya sun dawo Nigeria su na dawowa da sati biyu bayan Uwar biyu ta je Kazaure ta shaidawa *yan Uwanta ta dawo daga Makka ta raba musu tsaraba saita shaida musu wannan abun mamaki abun murna cewar zata auri Malam Habu Baban Hanna. Don haka ranar juma'a *yan Uwan Uwar biyu waliyanta suka zo aka hadu da Haisam da *yan aikin gidan suka taru aka daura auren Iya Salma da Malam Habu bayan an shafa aka daura na Uwar biyu da Malam Habu. Wannan abu yayi kyau aka raba goro da alewa aka watse. Daya dakin na kulle aka budewa ango Habu ya shiga ga na amarensa a gefe. Ko kofar gida Malam Habu bai cika fita ba, yana gida yana shan A.C yaci kaji yasha juice da abinci kala-kala. Idan lokacin Sallah yayi yayi taku kadan zuwa Masallaci ya shiga yaja jama'a Sallah da daddare kuma ya koyawa maza magidanta karatun alkur'ani mai girma Malam Habu yayi shar da shi ya girgije duk tsufan ya ragu daman ashe wahala tafi tsufan yawa. Haka Uwar biyu da Iya Salmai sunyi shar kamar ba sune wadannan tsofaffin ba, kayansu kullum iri daya Hannah take dinko musu.
Makarantar Islamiyya a hankali a hankali ta cika makil da dalibai yara da manya. Kullum da yamma yara ne suke zuwa, a ranar asabar da lahadi kuwa manyan matan aure suke zuwa da safe goma zuwa sha biyu. Manyan Malamai masana Alkur'ani da Hadisai, kawa'idi, fikhu da dai sauransu daban-daban su suke koyarwa a makarantar. Ramlah da Hannah suma sun shiga makarantar. Iya Salmai da Uwar Biyu ma ba'a barsu a baya ba sun tashi haikan neman ilimi dan da basu iya komai ba yanzu kuwa gashi komai dalla-dalla suna koya. Matasan *yan mata ne suke ta tururuwar zuwa wajen Ramlah akan matsalolin da suka dame su akan soyayya. Ramlah na kokarin warware musu ta hanyar basu shawara, wata tambayar idan suka yi mata sai ta hada su da Hannah tana ganin Hannah zata fita sanin amsar saboda ta taba crossing irin wannan rayuwar so zata fita sanin amsar. Wani lokaci har Haisam yakan taimakawa Ramlah wajen amsa wasu tambayoyin. Aji na musamman Ramlah da Hannah suka ware a makarantar Islamiyya lokacin da babu Makaranta suna zama da matasa suna wayar musu da kai akan mecece soyayya. Duk sanda Ramlah take gudanar da shirinta Hannah ce ta farko da take fara bugo waya ta bada tata gudunmawar, Ramlah tana jin dadin haka, ita kuma alkawarine kullum a gidan radio kafin ta fara gudanar da shirinta sai ta ce fatan alheri ga Haisam da Hannah.
Wata rana Hannah ta sako kai zuwa cikin gidan Iyayenta ta iske Wada yana yiwa tsofaffi nan tsiya yana cewa "Wai ku yanzu bakwa iya cin abinci sai kuna korawa da juice, katan daya baya yi muku sati guda, ba'afi kwana biyar ba na kawo muku wancan kwalin har ya kare, musamman Iya Salma ana dauke wuta kafin a tashi inji sai kaji tana Subhanallahi bana son duhu wallahi a rayuwata, ko da a Babban-mutum ya kike yi ke da ko wuta baki ja a gidanki ba. Iya Uwar biyu kuwa ita dai a kunna mata sattilite tana kallo tana tsalle akan kujera tana dariya, su Baba Habu kuwa shi dai asha A.C a figi naman kaza.
Hannah ta talli keyar Wada, ya zabura ya juya da sauri. Sai yaga Hannah. Iya Salmai ta ce "Gara da Allah Ya kawo ki gashi nan ya zamar damu kamar kakkanninsa wai tsiya yake yi mana. Hannah ta ce "Wada bana son irin haka meye don sun shanye katan din juice a sati, daga yau katan goma zaka dinga dauko musu daga kanti yana karewa ka dauko musu katan gomar. Kake yi musu tsiya ina kai nan matarka ta ce ka kunna mata A.C har riga ka cire ka jawo kujera ka hau ka ballo murfin A.C zaka girgideta Allah Ya kawo ni gidan na nuna maka inda zaka matsa remote ka kunna. Wai kai a dole ka nunawa amaryarka kai dan birni ne zaka burgeta. To gaskiya karka kara yiwa Iyayena haka wallahi ko kayan kantin dukka suke so zansa a kwaso musu don wa nake sana'ar? Dadi ya kashe tsofaffin nan suka hau shiwa Hannah Albarka.
Allah Ya albarkaci sana'ar Hannah a shekara ta sake bude wata Super market din a Zoo road komai Hannah ta sawa hannu na kasuwanci sai kaga kamar farashi yana ta hauhawa riba tsibubu Allah Ya dubi zuciyar Hannah Yana ta buda mata ita kuwa bata gajiya da bayarwa ga Iyayenta da *yan Uwanta talakawa na Niger dana Babban-mutum da duk al'Ummar Annabi da suke neman taimako.
Shiga www.littafanhausane.com.ng
Domin karanta complete chapter din
Yara da dama Hannah ta dauki nauyin karatun su, da yawa ta dau nauyin yi musu aure da yawa ta biya musu Makka. Wata rana Haisam ya dawo daga wajen hidimominsa da yamma kai tsaye bangarensa ya nufa don ya watsa ruwa yaji sanyi a jikinsa kafin ya fito lambun da yake zama yayi hira da matansa kullum da yamma. Abun mamaki sai yake jiyo ana yin busa mai dadin gaske wacce ta yi masa kama da wata busa da yake matukar so a rayuwarsa. Yayi sauri ya bude labulan windon dakin sa ya leka sashan da busar ke tashi, sai ya hango Hannah zaune cikin lambun tana busa abin busarta. Cikin sauri ya fada ban daki ya watsa ruwa bayan ya shirya ya fito ya nufi cikin lambun inda Hannah take. Ya lallabo ta bayanta ba tare da ta sani ba, ya tsaya cak kusan minti goma yana sauraranta, ya kare mata kallo tsaf ya ga tayi dammara da mayafinta ya kalli kunnanta da wuyanta ya ga sanye da tsakiyoyin nan na ta. Ya zagayo ya durkusa a gabanta yana kallon dige-digen da tayi da kwallli a fuskarta, ta dube shi tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa. Haisam ya ce "Lallai yau kin tuna baya kuma kin soso min wani abu mai muhimmanci da yake cikin kundin tarihin rayuwata. Su duka suka yi dariya. Haisam ya mike tsaye ya jawo wata kujera ya zauna ya ce "Ci gaba da busarki kuma kiyi min wakar ina sauraranki. Hannah ta mike tsaye ta kara tsuke danmararta ta kugu sannan ta koma ta zauna, su duka suka kwashe da dariya. Ta kaikaice ta fara busa tana rero wakar kiwo kamar yadda take yi masa da. Haisam yayi shiru yana kallonta yayin da zuciyarsa ta harba can ta tuno masa baya wato ranar da aka fara kawo Hannah makaranta, da bayan rabuwarsu da ita, da halin da ya shiga bayan rabuwarsu da irin busar da yake yi idan tunaninta yayi masa yawa. Bai ankara ba sai ya ga Hannah tana hawaye itama babu abin da take tunawa sai lokacin da Malam Sule ya bata wannan abun busar da kuma lokacin da Haisam yake sa ta tayi masa busa. Hannah ta kifa kai akan cinyarsa ta saka kuka, ya mike tsaye ya jawota jikinsa ya rungumeta sai shima kwalla ta fara zubowa daga idanuwansa. Ya laluba damarar da tayi a kugunta ya ce "Hannah meye wannan nake ji a kugunki kamar miciji? Ta ce "Ba miciji bane mayafina ne. Suka kwashe da dariya, Haisam ya sa hannu a aljihunsa ya ciro wani abu a daure a bakar leda ya mikawa Hannah, ta karba cikin sauri ta kwance ta duba, sai taga wata *yar karamar rigar nono mai kyau. Ta dubi Haisam alamar bata gane ba. Ta ce "Wannan fa? Ya ce "Kara kallonta dai sosai ki tuna baya. Hannah tayi shiru tana tunani, sai Haisam ya ce "Tuno ke da Nusaiba da Rauda a wajan mai kanti a makaranta? Ta ce "Laa shine ka ke ajiye da ita har yanzu. Haisam ya ce "Ai duk wani abu da ya shafeki Hannah bana mantawa dashi saboda muhimmancinki a rayuwata. Sai ta rungume shi suka koma suka zauna, suka ci gaba da busa abin busar tare.
Kwanci tashi Hannah tayi nisa a karatun likita "Medicin" sun gama shekaru uku a BUK an turasu teachin hospital na Aminu Kano don yin cilinicals. Sai yanzu Hannah ta sami ciki, wai zo kuga tarairaya da murna wajen Baba Haisam. Duk mutuncin Nusaiba da yake gani fur ya hana Hannah taje ta raka ta hada-hadar kanfen din zabe, suna so su zarce takarar gwamnan. Ya ce shi dai sai inda karfinsa ya kare amma Hannah ba zai barta ba saboda dan cikin zai wahala da ita kanta. Zabe ya doso Haisam yayi kokarinsa wajen taya mai girma gwamna yakin neman zabe. Kasancewar Haisam shine Kano, yasan *yan Kano, yana son Kanawa, Kanawa suna sonsa shi da Hannah da Ramlah saboda rin gudunmawar da suke bawa Kanawa, Kanawa sun amsa kiran Haisam sun sake zabar mijin Nusaiba a matsayin gwamnan Kano karo na biyu. Mai girma gwamnan da kansa ya jinjinawa Haisam ya kuma kuduri niyyar sai ya linkawa Haisam tara ta arziki, fiye da yadda Haiam yayi masa. Haka kuwa akayi sai dai kwangila mai tsoka bata taso ba amma Haisam yake bawa ta daruruwan miliyoyi kuma a biyashi da zarar ya gama. Haisam Kano kenan, arziki ya dada bunkasa yanzu Haisam yaso ya fi Mahaifinsa kudi dan yafi Yayansa Habib kudi shine ma yake basu kudi.
Hannah ta haifi santalelen danta kyakkyawa mai kama da Babansa amma ya dauko farar fatar Uwarsa, Hanna ta ce a sa masa sunan Babanta Abubakar ana kiransa da Walid. Bayan haihuwar Walid da wata uku Ramlah ta haifi da namiji shima mai kama da Babansa aka saka masa sunan Mahaifinta Shitu ake kiransa Khalil.
Hannah ta tashi tukuru tana ta karatu bata da matsala wajen rainon Walid tunda ga Iya Salma nan da Iya Uwar biyu suna rike mata shi, nono ne kawai take zagayowa ta bashi ta koma karatu har ya isa yaye ta yaye shi.
Tafi tafiya Hannah ta gama karatun likita da bautar kasa. Ta sake haifar *yan biyu mace da namiji masu kama da Hannah sak, Hannah ta roki Haisam da asa musu sunan Haisam da Ramlah da gudu ya amincewa bukatarta. Hai Ram Hannah kenan. Tubar kallah alhamdulillahi. Iyali sun hadu gida yayi albarka *yan dugul dugul yara zaka iske a farfajiyar gidan suna ta guje-gujensu Haisam na tsakiyarsu yana tayasu ball. Dr. Hannah Haisam Abubakar ta cika burinta ta zama cikakkiyar likita ta sami damar ta taimakawa al'umma ta fara aiki a Aminu Kano sai taga gara ta koma karatu ta karanto bangaren mata wato (gaenea)A.B.U Zaria tayi karatun shekara hudu a inda ta zama consultant gyanea doctor. Abunda Haisam ya fara yi shine ya bude mata asibiti nasu na kansu. Dr. Hannah da wasu likitocin su suke kula da marasa lafiya a asibitin.
Hmmmm GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 38
Mai girma Nusaiba matar governor suna nan
suna ta siyasa, tafi tafiya takarar
shugaban kasa mai gidanta ya
tsaya.
Haisam dai na nan na taya su
yakin neman zabe. Allah cikin
ikonSa ya lashe zaben
shugabancin kasar Nigeria,
Nusaiba a matsayin first Lady.
Mukami mai tsoka ta zabarwa
kawarta Hannah, quest what?
Ministar lafiya tasa mai gidanta
ya nada Dr. Hannah Haisam
Abubakar Imam (*yar Baba) an
duba cancanta Hannah ta
cancanci a bata. Haisam kuma
aka bashi jakadan Nigeria dake
kasar
America (ambassador of U,S.A).
Hannah baza ta iya kaura
America gaba daya ba saboda
aikinta, haka
Ramlah ma bata so ta tafi tabar
aikinta na gidan Radion data ke
yi. Gashi har Haisam da Hannah
da
Ita da Ramlah suna kokarin
bude gidan Radio station. Ka-ka-
ka-ka to yanzu yaya za'ayi
wannan zaman kenan Haisam
na America, Hannah tana Abuja
a katafaren gidan gwamnatin
da aka bata a unguwar
Ministoci. Ga Ramlah a Kano tana
bude gidan Radion kanta don
watsa shirye-shiryent a.
Daga karshe shawarar da aka
shirya ita ce Haisam da Ramlah
da Yaransu duka biyar din wato
Hannah, Walid, Khalil, Haisam da
Ramlah dukka zasu koma
America da karatun yaran gaba
daya.
Sannan za'a bude gidan Radio a
zuba kwararrun ma'aikata suci
gaba da fadakar da al'aumma
sannan duk sati kamar yadda
Ramlah ta saba gudanar da
shirinta zata ci gaba da
gudanarwa
amma ta hanyar wayar
tangarahu za'a dinga jonata da
gidan Radion amma fa wannan
wayar tangarahun tar ake jin
muryar, haka kuma take jin
tambayoyin da ake yi mata take
amsawa. Wani
lokacin kuma ana jinta a Radio
muryar America, idan taje
London kuma ana hira da Ita a
BBC
London. Ita dai burinta ta
fadakar da mata akan soyayya
da zamantakewar aure duk
mahakurci
yana tare da samu. Itama ta
shiga makaranta a America tana
yin masters akan Mass com.
Ci gaba wai bera akan cinyar
mage yana kallon talabijin da
remote a hannunsa yana
matsawa inji
wata mai iya magana. Gaba daya
gidan Haisam kacokan an
mallakawa Malam Habu kyauta
shi da matansa. Iya Salma a
bangaren Hannah Iya Uwar biyu
a bangaren Ramlah Malam Habu
shine mai
gida a bangaren Uncle Haisam.
Masu gadi da masu bawa
fulawa ruwa da masu dafa
abinci da direba
duk sunci gaba da aiki a
karkashin Malam Habu yana
biyansu da dinbin kudin da *yar
Baba take
jubgo masa. Hakika Malam Habu
ko da a lahira ya samu haka lallai
ya samu rahama, irin wannan
daula abin sai wanda ya gani sai
ma kun hango shi a jifgegiyar
mota mai A.c ana tukashi ya
kame a
owners yasha jifga-jifgan kaya
na alfarma, wayyo ba a fidda rai
da rahamar Ubangiji rabon
mutum
gudu yake ya zo ya same shi fiye
da yadda mutun yake nemansa.
Allah Kayi mana arziki ta hanyar
halak Amin.
Ku hasko min Iya Abu an guntile
mata kafa daya a asibiti da
sanda biyu take dogarawa. A
yau da yamma ita da *ya*yanta
duka suka dira a kofar gidan
Hannah da kwatance da
tambaya suka gano
gidan, da kyar masu gadi suka
barsu suka shiga ciki suna
shigowa suka iske Malam Habu
da matansa biyu a zaune akan
katuwar darduma suna shan
kayan marmari iri-iri. Nan fa
kaga gigicewa da razana a
wajan Iya Abu da *ya*yanta a
guje suka
ruga ba tare da sun san kofar
fita ba. Sandunan Iya Abu suka
zube kasa gashi idon daya ne
take dan
kyallarawa. Ta fadi fuk a kasa
tana ihu tana kuruwa wai yau
gata a lahira a gidan matattu ga
Malam
Habu ga Uwar biyu ga Iya Salma
ashe dama su Salma duk sun
mutu, yau gata a gidansu na
lahira
a zo a fita da ita daga kiyama.
Kuzo kuga dariya har da faduwa
a wajan Malam Habu da matan
sa, bayan
dariyar da taci karfinsu ta lafa
Malam Habu ya kwallawa mai
gadi kira ya ce ya shiga cikin
lungunan gidan ya harhado kan
mutanan nan da suka ruga ace
su zo ba fatalwa suka gani ba
mutane ne. Iya Salma ce ta taso
tazo wajen da Iya Abu take
durkushe tana kururuwa ta fara
yi mata bayani akan ta kwantar
da hankalinta a duniya take
cikin mutane *yan Uwanta ba
matattuba.
Bayan duk an hado kansu sun
zo sun zauna a gaban Malam
Habu gaba dayansu a firgice
suke kamar kace kule suce cas,
sai makerketa suke musamman
ma matan sun fi tsorata.
Malam Habu yayi gyaran murya,
yayi bismilla, yayi hamdala
sannan ya dora musu da bayani
ya basu labari kakaf abinda ya
faru da shi tun daga ranar da
aka kai shi kabari har rana irin
ta yau, ya shaida musu ya auri
Salma da Uwar biyu. Sai duk
suka dau kuka
suna bayyana rashin jin dadinsu
akan abinda yayi musu na
rashin damuwa dasu koda wasa
Hannah
bata taba fada musu ba kuma
tana zuwa garin, sai dai suji a
gari ana fadin wai-wai Malam
Habu bai rasu ba ana ganinsa a
gidan Hanne amma su basu
yadda ba sun dauka zancen
*yan gari ne dan ba a
mutuwa a dawo ashe da gaske
ne. Malam Habu yayi murmushi
ya ce "Kuyi hakuri nina gargadi
Hanne karta fada muku, amma
kada kuga laifina saboda a
cikinku babu wanda na tafi na
bari yana karami dukkanku na
ciyar daku, na shayar da ku, na
tufatar da ku, na saka ku a
makaranta kuka ki
yi, na yi muku aure musamman
matan dukkanku kuna gidan
mazajenku sanda na barku dan
haka nasan bani da nauyin
kowa a kaina.
Abu kuwa tuni kin yar da ni,
bola ma ta fini daraja, kin gaji
dani kin fi son in mutu ki huta
da wahala dani nima har nazo
nafi son haka. *ya*yanki gaba
daya sun raina ni kamar ba nine
na haifesu ba ban isa in saku ba,
ban isa in hana ku ba saboda
Uwarku ta nuna muku bani da
amfani. Bakin cikin rayuwa da
wulakanci babu wanda ban
gani ba ni da marainiyar *yata
*yar Baba. Na samu labarin irin
rashin mutuncin da ku ka dinga
yiwa *yar Baba tun daga wajan
rabon gado sai dai ta fita daga
dakinta
ta koma runbu sai da aka biya
mata kudin haya, ta zo ta rasa
mai bata abinci duk garin sai
Salma itama da take ci dakyar.
Abu yanzu wa duniya ta waya?
Duk abinda kika shuka shi kike
girba. Na sha wuya ainun a
zamana daku na ga bakin ciki
naga rashin mutunci kala-kala,
haka Mahaifiyar Hanne Habi har
ta koma ga Mahaliccinta tana
shan azabarki Abu har Hanne
babu wuyar da bata sha ba dan
dai
wuya bata kisa da tuni ta mutu.
Ba gori ba, yanzu gidan da kuke
zaune wacece ta siya muku?
Kafarki
da ta fara rubewa waye ya biya
miki kudin asibiti aka cire? Bara
da kikeyi waye ya hana ki bara
ya
baki jari ke da *ya*yanki? Amsar
ita ce *yar Baba ita ta muku duk
wannan. Allah Ya yiwa *yar Baba
Albarka akwaita da tausayi ta
danne duk abin da ku ka yi mata
ta saka muku da alheri. Yanzu
katafaren asibiti tasa ana ginawa
a agarin Babban-mutum wa
gareta a garin yanzu in baku
ba? Ta ce
min Baba nasa a gina Masallaci
da makarantar Islamiyya a
Babban-mutum za'a gina ajin
yara,
*yan mata matasa da tsofaffi
mata da maza saboda tsofaffi
irin su Iya Abu su samu su koyi
karatun
Sallah. Asibiti kuma da angama
ginin zata zuba magunguna da
gadajen kwanciya kyauta
saboda
talakawa. Hanne tasa shugaban
kasa yasa a gina muku titina ga
ruwan fanfo da wutar lantarki
duk
an baku a dalilinta, badan ita ba
wa zai tuna da wani kauye
waishi Babban-mutum.
Sha www.littafanhausane.com.ng domin karanta complete chapter din
Yanzu ta
taimakeku a lokacin da kuke
neman taimako ba kamar yadda
dukkannin *yan garin kuka
wulakanta ta kuka ki taimakontaba.
Abu ga amfanin boko fa, bokon
da kike yadawa a gari, kina
shela
kina cewa yawan iskanci nake
kai ta ba makaranta ba, da na
biye miki da tuni na cireta a
bokon ta
zauna a gida ta zama kamar
*ya*yanki da suka ki makaranta
gasu nan ba arabi ba boko.
Yanzu idan
kika kunna talabijin a kasar
nan babu wacce aka fi nunawa
daga shugaban kasa sai
ministan lafiya
Hannah, kullum gata ga
shugaban kasa ga matarsa.
Wani lokacin har Nusaiba
kawarta ta ce mata Hannah wai
ke ba zaki huta ba? Kullum kina
kauyuka kina jigilar magini da
kayan asibiti. Hanne
ta ce mata hutu bai kamaa ce ni
ba Nusaiba ta yaya zan huta
bayan talakawa na kauyuka
suna shan
wahala suna neman taimako.
Zuciyata, jinin jikina da kuma
dukiyata zanyi jihadi saboda
Allah iyakar kokarina in
taimakawa talakawa domin
babu ciwon da yafi ciwon
talauci wahala.
Allahu Akbar, ina alfahari da
Hannah a matsayin *yata,
al'ummar Musulmai suna
alfahari da Hannah a matsayinta
na *yar Uwarsu Musulma, *yan
Nigeria suna alfahari da Hannah
a matsayinta na *yar Kasarsu,
Gwamnatin Nigeria tana alfahari
da Hannah a matsayinta na
ministan lafiya, *yan Niger suna
alfahari da Hannah a matsayinta
na *yar Uwarsu,
jininsu saboda ta gina asibiti a
garin Dashi komai kyauta, ta
gina Masallaci da makarantar
Islamiyya sunana nema sunan
makarantar ABUBAKAR IMAM
ISLAMIYYA.
Yanzu a garin Dashi mace bata
fargaba idan mijin ta ya rasu ya
barta da marayu tasan ko
tantama babu Hannah ta
tanadar mata tallafi mai tsoka.
Babu abinda Iya Abu da
*ya*yanta suke iya cewa sai rike
baki da girgiza kai suna jinjina
wannan
daukaka ta Hannah da
Mahaifinta. Iya Abu ta
langwabar da kai ta sharbe
hawaye ta ce "Nayi
kuskure ainun, gara da Allah
Yasa baka mutu ba da ka mutu
ina zan shiga da wannan tulin
alhakin
naka dana dauka, ku yafe mun.
Ta fashe da kuka taci gaba da
cewa "Yanzu sai ka daure ka
mayar da ni dakina ni da
*ya*yanka ka rungume mu mu
zauna lafiya da kishiyoyina
Salma. Ki
taimakeni kisa baki Malam ya
mayar dani nasan ki da tausayi
kinga daman ke kika hada
aurena da Malam Habu tun farko
duk abinda nayi miki a baya
kuskure ne yanzu zamu zauna
lafiya. Iya Salma ta zabura ta ce
"Wacce ni? Ai Abu kinfi karfina
da dai
Da bansan halinki ba na jawoki
jikina kika cuceni har hauka kika
samun dole kika rabani da
mijina
abin kaunata, shekara arba,in
bama tare ina tajin kaunarsa
nayi sallama da aure sai yanzu
Allah Ya sake hadamu muka yi
aure. Yanzu kina nufin in dauko
shinkafar bera in zubawa
kaina a abinci
inci in mutu. Iya Abu ta sharbe
hawaye ta ce "Yanzu Salma nice
shinkafar berar? Malam Habu
yayi
murmushi ya ce "Abu ai kinfi
shinkafar bera tsiya sai dai a
kiraki da Bomb mai wargaza
gari guda, to aini babu yadda za
ayi in sake kara zama da ke.
Rabona da samun kwanciyar
hankali tun ranar da Salma ta sa
na auro ki haka ban huta ba sai
ranar da aka dauke ni daga
gidanki zuwa kabarina, tun
daga ranar na ke hutawa a
rayuwata har rana irin
ta yau, kuma ina saka ran har
karshen rayuwata zanci gaba da
hutawa. Ina zan sake jajuboki
da
*ya*yanki in jajubawa kaina
tashin hankali.
Abu ta fashe da kuka, *ya*yanta
ma kuka kuke suna cewa "Baba
yanzu gudunmu kake, ya ce "Har
yanzu ku *ya*yana ne kuma ba
zan so ku tozarta ba ni ina
suturce nayi alkawari zan dinga
aiko direbana duk karshen wata
yana kai muku kudi da kayan
abinci amma karku fiye zirga-
zirga zuwa Kano har wani
ya bata a hanya ku bari zan
dinga yo muku aike.
Iya Abu ta sake kallon katafaren
gidan nan ta ce "Babu inda
zanje Malam saboda akwai
igiyar
aurena a kanka tunda baka
mutu ba. Malam Habu ya ce "To
tunda kina kokonto to bari na
tsinka
igiyar kije na sawake miki
saboda bazan sake zama da ke
ba har abada. Uwar biyu ta nisa
ta ce "Ikon Allah yau naga naci
wai ba Malam Habun da kika
raina bane? Ki ke zagi ta
Uwa ta Uba yana kuka da
idanuwansa mai yasa yanzu
kike sonsa? Mu fa ba zamu
zauna da ke ba Abu, ya ce ku
tashi ku tafi zai dinga yi muku
aike. Suna zaune suna ta koke-
koke yaran suna fadin Iya Abu
ke kika jawo mana ga rashin
ilimi ga
rashin tarbiyya duk baki bamu
ba. Malam Habu ya shiga gida ya
dauko musu kudi mai yawa ya
rarrabawa kowannensu yasa
ma'aikata suka
dauko buhunan abinci daga
store suka zuba a wata
doguwar mota kirar bus ya ce
da direban ya
kai su Babban-mutum suka
shiga suka tafi. Babu abinda
suke sai kallon Malam Habu ya
zama wani
danye sharaf da shi sai kace ba
wannan yagulallan tsohon nan
bane, furfura gemun nan buzu-
buzu, duk babu an aske yasha
farin danyen boyel a jikinsa ga
wani farin gilashi a fuskarsa
tsadadde
Hannah ce tasa aka yankar masa
a America da ta kaishi Medical
check up wanda zai kara masa
gani
tar. Babu wani ciwo da yake
damunsa sai dai magungunan
kara lafiya da Hannah take
jubgo
musu ta ce suyi ta sha kamar
bitamin A da bitamin E nasa
kwarin ido, karfin kashi da hana
zubewar
hakora. Lallai tsofaffin nan shar
da su tubarkalla.
Insha Allah GANGAR JIKINSA NA AURA
THEND
QARSHE
Chapter39
Kusan kowacce weekend a America Hannah keyi wajen
mijinta, duk satin da aiki yayi mata yawa ba za ta samu
damar zuwa ba, Haisam da yaran duka sai suzo suyi
mata weekend dan basu da matsalar jirgi ko babu
fasinja zai dauki Hannah ya kaita America. Kudi masu
gidan rana suna aiki, lallai nan gaba zasu sayi jirgin
HAIRAMHANNAH saboda zirga-zirga daga Nigeria zuwa
America. Wannan satin kayatacciyar liyafa Ambassado
Haisam ya hada a Amrica ta Anniversary auransu da
Minister of health Dr. Hannah Haisam Abubakar da
Uwar gidansa Haj. Ramlah Haisam Shitu. Mai girma
shugaban kasar Nigeria da Uwar gidansa da da yawa
daga kusoshin gwamnati, Mahaifan Hannah, Mahaifan
Haisam, Mahaifan Ramlah, Iyalan gidan Yaya Habib,
Amratu da Izziddin, Kawu Ahmad da matarsa Hajir,
Rauda da mijinta da hadaddun *yan Uwa da abokan
arziki duk an gayyacesu su halacci wannan kayatacciyar
liyafa da za'ayi a birnin U.S. Jirgi kawai zasu taka su
haye kyauta ba tare da neman wata biza ba ko tikitin
Jirgi an riga an wankesu saboda mai girma shugaban
kasa, haka shugaban kasar America yasan da
zuwansu.
----- Haisam da Hannah sun sami arzikin duniya fiye da
tunanin mutum, duk da bayarwa suke amma ta ko ina
samu suke. Sun mallaki gida a America, Saudia, London
balle kuma anan gida Nigeria akwai wasu a Abuja,
Lagos, na Kano ma ba zasu kirgu ba, Babban-mutum da
wani a Dashi inda take sauka idan taje. Duk wannan
daula da Hannah take ciki bata wulakanta talakawa taci
abinci tare dasu tayi wasa da dariya dasu ta dauko
abun duniya kuma ta basu. Hannah ta kara kyau data
sami jin dadi kamar a hango jinin jikinta don farar
fatarta, gata bata tsufa duk wanda yasanta shekaru
goma a baya idan ya ganta yanzu haka zai ganta bata
canja ba, sai kyau data kara. Babu wanda zaiga
*ya*yanta ya ce ita ta haifesu saboda *yar karama da
ita kamar yarinya. Talakawan Nigeria sun fara yiwa
kansu sha'awar Haisam ya tsaya takarar shugabancin
kasarsu su zabe shi sun san zai yi musu aiki. Ba
talakawa kadai ba shi kansa mai girma shugaban kasar
yana cewa Haisam ya shirya da zarar ya sauka shi zai
gaje shi, haka manyan *yan siyasar Nigeria sun yarda
da wannan batu na mai girma shugaban kasa. Kowacce
safiyar duniya nan Haisam ji yake yana kara son
Hannah a ransa, itama kuma haka. Haisam, Ramlah,
Hannah da *ya*yansu biyar suna zaune cikin jin dadi
da kwanciyar hankali da kaunar juna. Arzikinsu yana ta
bunkasa, basu ba ma duk wanda ya rabesu ma yayi
bankwana da talauci balle *yan Uwansu na jini balle
Uwa Uba Mahaifansu. Malam Habu yayi bankwana da
talauci, Uwar biyu yanzu ta azurta *yan Uwanta da
dama balle *yar ta ta cikinta. Gidansu ya zama gidan da
kowa yake kawo kukansa ake share masa. Malam Habu
ya kan je Babban-mutum amma wannan karon
girmama shi kowa yake yi, gaisuwa har kasa ake
zubewa ana yi masa. Iya Abu ta dauwama cikin nadama
duk sanda taga Malam Habu sai ta hau kuka tana
rokarsa ya aureta babu wanda take tsananin so sai shi,
yakan bata amsa da cewa akai kasuwa.
Hannah sai da ta sayi jirgi mai daukar mutane dubu
dari biyar musamman domin Members na wannan
page, yanzu haka tikiti na hannu na, masu son zuwa
liyafar Ambassador Haisam a Amrica sai suyi magana
in basu. Lolz bari naga masu son zuwa America. Hmmm
Karshe
Sai ku jira sabon littafi mai zuwa nan gaba,
Karku manta kullum Ku kasance da www.bankinhausanovels.com.ng
Domin akwai Littafai da dama dake can wadanda bamu Kawo anan ba
Naku ne (A'I'S)
0 Comments