Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DIYAM CHAPTER 9

DIYAM CHAPTER 9

- - Post a Comment
DIYAM CHAPTER 9
Na juya ina kallon kofar palon amma na kasa motsa kafata ballantana in tafi, Inna na gami ta budo kofa a zuciye tana kallona "ba kiranki ake yi ba?" Na taho a hankali ko wacce gaba ta jikina tana rawa, ina shiga Inna ta tunkuda keyata na durkusge a tsakiyar palon kaina a kasa. Kawu Isa yace "Diyam, shekaran jiya da na ganki kin fito daga adaidaita sahu daga ina kike?" Ban amsa ba kuma ban dago ba, Alhaji Babba yace "idan anayi miki magana kina yin banza da mutane sai na kakkarya ki anan gurin, ba zaki ansa ba" na fara rera kuka "dan Allah kuyi hakuri kar ku dake ni, dan Allah" Kawu Isa yace "ba zamu dake ki ba indai kika gaya mana gaskiya. Ina kika je ranar nan?" na cigaba da kuka na "wallahi Kawu na daina bazan sake fita ba". Na dago kai muka hada ido da Inna ta rafka tahumi tana kallona, nayi sauri na sunkuyar da kaina, tace "ba zata fadi inda taje ba fa, amma ni nasan inda taje, ba zai wuce gurin wannan bakin mayen ba" ta juya tana kallon Alhaji Babba tace "rannan ba kace in ya sake zuwa gidan nan sai ka kama shi ba? To shine ita ta tafi gurinsa tunda shi an hana shi zuwa. Wato dalilin da yasa kika nace sai na saka ku islamiyya kenan ko?" Na girgiza kaina da sauri "wallahi Inna ba haka bane ba, ranar nan ne kawai naje kuma bazan sake zuwa ba" Kawu Isa yace "to me kika je yi ranar? Me ya kaiki gurinsa?" Ina sheshsheka ina kuma wasa da fingers dina nace "ce masa nayi kar ya kuma zuwa gidan nan" Alhaji yace "au saboda nace zan saka a kama shi shine kika je kika gaya masa ko? To in nayi niyyar rufe sadauki kaf garin nan akwai wanda ya isa ya hana ni ne? Yanzun ma kuma zan tura har gidan da yake takama dasu din insa akama shi a dan lallasa min shi yadda nan gaba ko kince masa zaki je shi da kansa zai hana ki" Kawu Isa yace "tashi ki tafi" nayi sauri na mike nayi hanyar waje sai Alhaji Babba ya ce "kar ki fita daga gidan nan. Kin gama zuwa islamiyya ai. Zo ki wuce ciki" na juya na bi inda yake nuna min, muka hada ido da Hajiya Babba wadda tun da aka fara maganar bata ce komai ba tana dai bina da kallo kawai.+ Kitchen din gidan na shiga, na rakube a jikin kofa na cusa kaina a tsakanin cinyoyi na, me yasa ni bani da sa'a ne? Me yasa duk sanda nayi wani abu sai an kama ni? Karya sam bata karbe ni ba? Sai kuma na kama addu'ar Allah yasa Sadauki ya tafi dan kar Alhaji Babba ya aikata abinda yace.3 A palo bayan na tashi inna tace "na rasa yadda zanyi in raba yarinyar nan da wannan nataccen yaron wallahi. Nayi nayi, Allah ma ta gani nayi iya kokarina amma abin ya faskara, ni farko na dauka soyayyar yarinta suke yi, na dauka in suka fara hankali zasu saki hannun juna amma kamar kara tunzura su ake yi" Alhaji Babba yace "wai soyayya suke yi?. Diyam din yanzu harta isa yin saurayi? Shekarar ta nawa?" Inna tace "sha hudu zata yi nan da wata daya" ya gyada kai yace "ta isa kam. Matanen mu na ruga basu kaita ba ma ake musu aure. Kuma wannan tunda har tasan a raba ta da saurayi ita kuma ta dauki hanya ta bishi to lallai ita ma ta isa auren" inna tayi ƙoƙarin kare ni "ya shanye tane fa, babu maganar wanda Diyam takeji sai tasa" Alhaji Babba yace "anyi daya ai, ba za'a sake biyu ba, mu ba zamu kuma hada jinin mu da mayu ba, yadda bakin cikin Manu ya kashe Inno ba zamu bar bakin cikin Diyam ya kashe Hardo ba dan haka kija mata kunne. Babu ita babu shi, in taki kuma duk abinda ya biyo baya ita ta jawo wa kanta". Shikenan kamar magana ta wuce, zuwa washegari na shiga harkokina sosai kamar babu abinda ya faru amma cikin raina kuma cikin sallolina ina yiwa Sadauki addu'ar samun nasara, sai inke tambayar kaina ko ya samu mahaifin nasa? Ko wacce irin karba a samu daga danginsa? Hankalina rabi yana tare dani rabi kuma yana gurin Sadauki har ya kwana uku da tafiya. A ranar da daddare aka aiko Alhaji Babba yana kiran Inna, ta dauki hijab dinta ta fita shiru shiru har na gaji da jiranta mukayi shirin bacci ni da Asma'u muka kwanta, amma sai na kasa baccin kuma nayi ta juyi ina jin wata irin muguwar faduwar gaba. Na rasa me yake yi min dadi kawai na tashi na zauna na rafka tagumi sannan sai gata ta shigo, sai kawai naga idonta kamar wadda tayi kuka amma sai ta maze tace "ke kuma me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba?" Nace "bana jin dadi ne kawai Inna. Baffa nake tunowa" sai kuma na fara matsar kwalla, ta dauke kai tace in an tuno mamaci addu'a akeyi masa ba kuka ba" sai ta wuce can karshen gado ta zauna ta jingina kanta da jikin gadon, naso in tambayeta in wani abun yana damunta amma nasan ba lallai ta bani amsa ba dan haka sai nayi shiru na koma na kwanta ina kalllon ceiling, mun jima a haka sannan tace min "Diyam Baffanku ya mutu ya huta, mu da muke duniyar mu mune cikin wahalarta" na runtse idona ina tunanin ma'anar maganar ta ta. STORY CONTINUES BELOW Washegari bayan na tashi da assuba nayi sallah sai na koma baccin safe, cikin bacci na kawai naji muryar mama a dakin na farka ina mamakin me take yi a gidan da sassafe? Sai naji Inna tana cewa "ni wallahi Hafsa kinfi kowa sani, bana son yaron nan sam zuciya ta bata sonsa ballantana har inyi sha'awar ya zama surukina amma duk da haka saghir fa...." Sai kuma suka ga ina kokarin mikewa sukayi shiru. Na tashi na gaishe da Mama, sai naga fuskar Inna still akwai bacin rai idonta kamar batayi bacci sosai ba, sai kawai naji ina son inji maganar da suke yi. Sai na bude toilet na shiga na rufe na kunna pampo kamar zanyi wani abu amma sai na dawo na sakakunne na a jikin keyhole. Sai naji Mama tana cewa "wannan gajeriyar matar tasa ce zata kissima masa, shi kuma ya hau ya zauna saboda son kansa, amma suma kansu sunsan ai Diyam ba sa'ar auren Saghir ba ce ba, ya ninka ta a shekaru fa, gashi da budadden ido ita kuma fa? Yarinyar da junior waec kawai ta rubuta? Akwai cutuwa sosai a hadin su" Inna tace "babu fa abinda ban gaya masa ba jiyan, sai yaji haushina ma wai ina so in nuna ni na haifi Diyam basu ba, wai ita suke wa gata, wai baza ta taba samun miji irinsa ba, wai gata suke yi mata albarkacin zumunci albarkacin maraicinta" ta danyi tsaki tace "ni da ace Diyam ta fi haka girma ne, da ace misali ta gama makaranta ne wallahi da bani da dumuwa. Ni yanzu abinda nake so kice masa idan kinje shine, ki roke shi a bar yaran su daidaita kafin ta gama makaranta". Na sulale ma zauna a kasa a jikin kofar. Naji dai suna maganar aure, kuma naji sun ambaci sunana sun kuma ambaci sunan Saghir. To tambaya ta anan itace auren wa za'ayi? Aurena za'ayi ko auren saghir za'ayi? Dan kaina ba zai iya daukan aurena da saghir a sentence daya ba ballantana ƙwaƙwalwa ta ta fahimci cewa aure za'a hada ni da saghir. Na wanke fuskata nayi brush na fito ina murmushin yake, suma duk yaken sukayi min har na zauna na fara breakfast sai na lura duk sun zuba min ido suna kallona. Sai na samu kaina da tattauna abincin amma makogwarona yakasa budewa ballantana in iya hadiyewa. Muna nan zaune babu mai magana sai ga aike aba kiran Mama inji Alhaji Babba, ta tashi ta tafi muka cigaba da zama ni da Inna sai ga wani aiken wai inna taje itama, tana tafiya na rufe abincin gabana na tashi na kwanta a kan gado trying hard not to think, trying hard not to let my brain assess maganar da naji su Inna suna yi. Ba zan iya tuna adadin mintina ko awannin da suka wuce ba sai ga yarinya an aiko wai inzo inji ana kira na a palon Alhaji, na tashi na saka hijab dina still trying not yo think na fara tafiya blindly zuwa part din Alhaji Babba. Na murda kofar na shiga da sallama. Duk suka dago kai suna kallona kamar yadda nima nake bin su da kallo. Alhaji Babba, Hajiya Babba, Inna, Kawu Isa da kuma Mama. Na durkusa na gaishe su da muryar da a kunnena naji kamar ba tawa ba. Suka amsa sannan duk suka zuba min ido suna kallona. Alhaji Babba ne yayi magana "Diyam a matsayin mu na iyayenki wadanda baki da wadanda suka fimu kaf duniyar nan mun yanke shawara a kanki. Zamu hada auren zumunci tsakanin ki da yayanki Saghir".1 "Dama an jima da bani shawarar cewa babban abinda zai saka Saghir ya zauna a guri daya ya nutsu shine in na samu kyakykyawar yarinya na aura masa, tun a lokacin Diyam ce ta fado min a raina na kuma kuduri aniyar hada su aure in ta isa auren, to kuma yanzu ganin har ta fara iya bin saurayi zuwa gidansu na fahimci ta isa auren a yanzu, dan haka za'ayi yanzu. Diyam zaki cigaba da karatu kamar yadda mahaifiyar ki ta bukata, amma ba zaki koma makarantar kwana ba, za'a saka ki a day ki karasa secondary, in kin gama in mijinki ya yarda sai ki cigaba in bai yarda ba kuma shikenan. Bamu saka rana ba tukunna, na kira shi Saghir din nace masa lallai ya hawo jirgi yazo ya gobe ina nemansa, in yazo sai muji tsare tsarensa sai mu samu saka lokacin. Shikenan abinda zan ce miki Diyam, tashi ki tafi". Na tashi kamar yadda yace, amma sai kafafuwana suka lankwashe na fadi a gurin, Inna da Mama suka yo kaina a tare amma kafin su karaso na sake mikewa na kama hanyar na fice. Bansan ya akayi nazo ba kawai sai gani na nayi a dakin inna, na durkusa a gaban gado gabaki dayan jikina yana karkarwa kamar ana kada mazari amma idona babu hawaye, lallai wani tashin hankalin yaji gaban kuka. Baffa naji ya fado min arai, na tuna maganar sa sanda yake mana fada ni da sadauki "waye kuke tunanin zaiyi muku aure yanzu? Ba dai ni babanku ba" ashe haka maraici yake? Ashe haka rashin gata yake?1 A gefe na naga handbag din Mama, na dauka da sauri na bincike da dauko wayarta, babu tsoro ko kadan a raina nayi dialing number din da Sadauki ya bani. Ring biyu ya dauka, muryarsa as clear as yana gabana a tsaye wannan yasa na samu relief na san at least lafiyar sa kalau. Yayi sallama amma ni sai na kasa magana saboda karkarwar da baki na yake yi, sai kuma kuka ya kwace min. Na fara rera wa ba kakkautawa nan take ya rikice "Diyam?? Ya Salam Diyam kiyi min magana menene? Me ya faru Diyam? Please talk to me" shima kamar zaiyi kukan, na tsagaita nace "Sadauki ka taimaka min, Sadauki aure za'ayi min wai" yayi shiru kamar baiji ba sannan yace "what?!!!" Nace "yanzu suka kira ni suka gaya min, aure zasu yi min Sadauki, wai hamma Saghir zasu aura min" yace da sauri "su? Su waye su? Diyam kar kiyi min wannan wasan bana so" na lissafa masa duk wadanda suke gurin sanda akayi maganar nace "da gaske suke Sadauki, wallahi da gaske suke, Sadauki mutuwa zanyi ka taimaka min". Yace cikin muryar da ban taba jin yayi magana da irinta ba "Diyam listen to me, zan ajiye duk abinda nake yi zan taho kano gobe and I promise you I will not let anything bad happens to you".1 Kofa ta bude inna da Mama suka shigo fuskarsu babu yabo babu fallasa, sai kuma suka tsaya suna kallona da waya a hannu ina kuka. Na sauke wayar daga kunne na ina ji a raina bana jin wani tsoro kuma, wanne punishment za'a yi min wanda yafi wannan da aka riga akayi min?1 Alherin Allah ya kai gun masoya na a duk inda kuke. Ina gani, ina karantawa kuma ina godiya da duk comments dinku, it kept me going.2 This page is dedicated to duk wadda za'ayiwa ko kuma aka taba yiwa auren dole. This page is dedicated to duk saurayin da aka raba shi da budurwarsa ba tare da wani cikakken dalili ba. This page is dedicated to duk iyayen da suke da ra'ayin yiwa yayansu auren dole. Ina fatan wannan labarin zai saka ku chanza ra'ayin ku. Ku fahimce ni sosai, auren dole nake nufi bawai auren haɗi ba, akwai banbanci tsakanin arranged marriage da kuma forced marriage. Mama ta shigo ta karbi wayar daga hannuna tayi cutting kiran. Bata ce min komai ba ta saka wayar a jakarta ta harhada sauran kayanta ta rataya jakarta. Inna tace "ba dai tafiya zaki yi ba" Mama tace "tafiya zanyi, ni ba zan iya kallon wannan kayan takaicin ba, Allah ya bamu alkhairi". Ta juya da sauri ta bar dakin. Inna tayi ajjiyar zuciya dan ta fahimci Mama fushi tayi akan magana ta, tazo ta zauna a bakin gado daga gefena tace "shi kika kira ko? Diyam taurin kanki ne yake jawo miki koma menene akeyi miki. Ke ba kya jin magana ta, da ace tun farko da na hanaki kulashi kin daina ai da bata kai ga haka ba" tayi shiru tana sauraron kuka na, sannan tayi tsaki tace "nima zuciyata ba son hadin nan naki da saghir tace ba kawai dai dan babu yadda zanyi ne, ba wai saghir din ne bana so ba a'a auren ki ne yanzu bana so, duk da dai kamar yadda Alhaji ya fada ana yiwa wadanda basu kaiki bana aure kuma su zauna amma nasan da babanki yana nan da bazai miki aure yanzu ba. To ni wannan shine damuwata. Amma in kika duba ta wani bangaren fa zaki ga gata akayi miki, Saghir yafi wancan yaron da kike ta naci komai, yafishi kudi ya fishi kyau ya fishi asali ya fishi shekaru ya fishi hankali ya fishi wayewa sannan uwa uba gashi dan uwanki. To me kike nema kuma bayan duk wannan" a hankali cikin dasashshiyar murya nace mata "bana son shi Inna. Bana son Saghir Sadauki nake so, bana son aure yanzu karatu nake so. Inna ki taimaka min kar kuyi min auren dole" sai na dora kaina akan cinyarta na cigaba da rera kuka, ta dora hannunta a kaina tana shafawa, a hankali tace "gata akeyi miki Diyam, yanzu ba zaki gane ba sai nan gaba".7 Kafin azahar zazzaɓi mai zafi ya rufe ni, ko palo ban kuma lekawa ba ina kwance daki a kudundune ina karkarwa. Ina jin yan gidan suna ta zuwa dubani kuma nasan da yawa daga cikinsu tsegumi ne yake kawo su. Ina jin Hajiya Yalwati ta shigo itama suna ta magana da Inna "amma dai Amina in kika yarda da wannan hadin kun zalinci yarinyar nan wallahi. Saghir in ana so ya shiryu ai gagarumar mace wadda taga jiya taga yau za'a samo a hada shi da ita ba yar mitsitsiyar Diyam din nan ba, ya zata yi dashi?" Inna tace "to wai Yalwati ya kuke so inyi ne da raina ne? Nima fa ba son abin nan nake yi ba amma ya zanyi? Yanzu zan iya cewa da Alhaji Babba ba zai aurawa Diyam Saghir ba? Duk duniya tana da wadanda suka fisu ne ko kuma ni duk duniya ina da wadanda suka fisu ne? Hakuri kawai zatayi nima kuma inyi hakurin sai mu hadu muyi tayi musu addu'a. Duk wannan koke koken nata daga anyi auren fa shikenan. Yara nawa ne akayi musu auren irin haka kuma gasu nan har sun hayayyafa sunyi zaman su" Hajiya Yalwati tace "to ba dole suyi zamansu ba tunda sun hayayyafa? Amma kije ki tambayesu kiji idan har yau abin baya musu ciwo a ransu. Kije ki tambayesu kiji irin wahalar da suka sha kafin su hakura din. To wannan fa wai ina yi miki magana ne akan in mace bata son miji aka aura mata shi to ina ga in shi din ma baya sonta? Kar ki manta Saghir fa bashi yace yana son Diyam ba. Kinsan kuwa ciwon auren wanda baya sonka? Kinsan kuwa irin bakin cikin da zai ta kunsa maka?"3 Inna ta dauke kanta gefe tana jin kamar bakar magana ce Hajiya Yalwati take gaya mata. Ita kuwa ita tasan bakin cikin auren wanda baya sonka don har yau tana iya tuno farkon aurenta da Baffa ko kallo bata ishe shi ba, sai gabanta ya fadi data tuno Saghir, idan har Baffa daya tashi ya kuma yi karatu a kauye yayi mata wulakanci saboda baya sonta to ina kuma ga Saghir din da ya gama bude idonsa a kasashen turawa? Da yamma Aunty Fatima autar su Baffa tazo, ita ta tashe ni zaune tana taba jikina tace "Amina anya kuwa wannan yarinyar ba za'a kaita asibiti ba, jikin ta yayi zafi da yawa fa?" Hmmm shine kawai abinda inna tace tana jan charbi, Aunty Fatima ta bani magani na sha na koma na kwanta tana cewa "wallahi baki ji irin dadin da naji ba dazu da Alhaji Babba ya kira ni take gaya min wannan labarin, kai amma Allah ya sanya alkhairi shi kenan munyi abinmu tuwo na maina. Dama tunda Hamma Manu ya rasu yaran nan Diyam da Asma'u suke raina ina ta tunanin su kinga yanzu shikenan, in akayi auren dai ta dauki kanwarta suje can suyi zamansu kema kin huta, duk inda zai tafi yawon nasa ba sai ya saka matarsa a gaba su tafi tare ba? Itama ma a hakan zata waye din ai" a raina nace kaji wata kuma, ita wayewa ce damuwarta. STORY CONTINUES BELOW Washegari da safe jikina ya danyi sauki sai wani matsanancin ciwon kai da nake ji. Inna ta saka na tashi da kyar ina shan kunun gyadar da Hajiya Babba ta aiko min dashi wai taji ance naki cin abinci. Ina cikin sha aka budo kofar dakin kamar za'a balla ta, duk muka tsorata muka daga kai sai idona ya sauka akan Hamma Saghir da yake haki kamar wanda yayi tseren gudu, Inna tana yake tace "a'a Saghir saukar yaushe?" Ya dauke idonshi daga kanta ba tare daya amsa mata ba ya kalle ni cikin ido yace "dan ubanki, tun wuri kije ki gaya musu cewa ba kya sona tun kafin a makala min ke ki zokina nadama" ban dauke idona daga kansa ba har ya juya ya fice ya bar mana kofa a bude, na sauke kaina kasa na ajiye kunun hannuna, ina jin Inna ta tashi da sauri ta fita tana salati. A hankali naji wata irin tsana, tsanar da ban taba tunanin it is possible ba tana shiga zuciyata a game da Saghir, abinda ya fada bashi yafi bata min raiba akan ambaton ubana da yayi.1 Na jawo pillow na kwanta sama sama ina jiyo hayaniya a palo, naji Inna tana tsara musu abinda Saghir yace, muryarta har kakkaryewa takeyi kamar zata yi kuka, sai kuma naji Alhaji Babba yana magana shima amma bana fahimtar me yake cewa sai can naji yace "kai ka haife mu ko mu muka haife ka? To sai an aura maka ita din in yaso in an kaita gidan naka ka kasheta kakawo mana gawarta". Na runtse idona na jawo wani pillown na dora a kaina na toshe kunnuwana. Da yamma Mama ta sake dawowa gidan. Inna ta tsara mata abinda dazu ya faru da Saghir. Mama tace "to dama ni abinda ya kawo ni shine in gaya miki in anjima Sadauki zai zo, ya sake kiran layi na yace min zasu zo shida dan uwan mahaifinsa da kuma Alhaji Bukar na garin nan. Abinda nake so ince miki shine dan Allah idan sunzo kema ki fito ki nuna cewa ba kya son hadin Diyam da Saghir, ki karbi Sadauki sau daya dai a rayuwarki ko dan yarki" Inna ta fara girgiza kai "na gaya miki Hafsa, kin sani kuma bana son yaron nan bana kaunarsa" Mama ta fara daukan zafi "Yanzu kinfi son ki hada Diyam da mutumin daya kalli cikin idonki ya gaya miki baya kaunar yarki akan wanda yake binki kamar zai lashi takalmin ki saboda ki bashi yarki? Wacce irin zuciya ce dake Adda?" Amma inna sai ta cigaba da girgiza kanta kawai.4 Ni kuma jin maganar Mama sai naji hankalina gaba-daya ya koma kan Sadauki. Sadauki zaizo da gaske? Kuma tare da dan uwan babansa? Kenan ya ga babansa da gaske. Amma kuma har zuciya ta ina tsoron yadda zata kasance tsakanin su da Alhaji Babba. Muna nan zaune kuwa sai ga kira a wayar Mama, ta amsa sai ta tashi tana saka hijab dinta tace "sun zo, bara inje" amma inna bata motsa ba, ni dai ina zaune ina jin jira, irin jiran da akuya take yi lokacin da aka kaita mayanka. Har wani daci daci nake ji a bakina.1 Abinda ya faru a waje kuma shine; Mama ce da kanta ta shigo da Sadauki tare da wani mutum da zuka zo tare daga Maiduguri. Babban mutum ne sosai kuma kana ganinsa kaga babarbare harda tsagun su a fuskarsa. Sai kuma Alhaji Bukar wanda shine asalin wanda ya aurar da Zainabu. Suka shigo tayi musu iso har palon Alhaji Babba ba tare dashi Alhaji Babban yasan ko su waye ba ballantana abinda yake tafe dasu. Sai da yaga Sadauki sannan balli ya fara tashi yace a fitar masa dashi daga gidan sa. Mama ta roka dan Allah a tsaya a saurare su tunda dai suka taho kafa da kafa tun daga Maiduguri ai sun chanchanci a saurare su. Mutumin da hausa bata ishe shi sosai ba sai yana hadawa da turanci ya fara bayanin cewa mahaifin Sadauki ne ya turo shi yayi representing dinsa saboda shi baya kusa, gurin nemawa Sadauki auren Diyam kamar yadda shi Sadaukin ya nema. Nan take Alhaji Babba ya basu short ansa da cewa "ba za'a bashi dinba, kuma Diyam mun riga munyi mata miji. Na gama baku amsa ku tashi ku bar min gidana tun kafin in kira muku yan sanda" Alhaji Bukar yace "shikenan dai? Shikenan maganar 'yan sanda dai?" Alhaji Babba yace "ai gida na kuka shigo, dan haka duk abinda nace kunyi min ya zauna kenan" Alhaji Bukar yace "ai kai abinda baka sani ba shine, in kai baka rufe mu ba mu sai mu tufe ka kuma muga wanda zai tsaya maka ya fito da kai" Alhaji Babba yace "anji din, aure dai ba za'a bayar ba in kaji haushi kamar yadda kayiwa zainabu aure dan munki yarda Manu ya aureta to shima Sadauki ka daura masa aure gobe mu gani" Alhaji Bukar yace "tabbas nayi wa zainabu aure, aure kuma wanda manu baiyi irinsa ba, amma kuma da amincewar ta ba wai tilasta mata nayi ba kamar yadda kake da niyyar tilastawa marainiyar Allah ta auri lalataccen danka. Wallahi indai kayi mata wannan auren sai Allah ya kamaka da hakkinta tun a duniya ba sai kunje lahira ba". Ya mike tare da dayan mutumin daya ke ta mamaki yana tambayarsa dama haka mutanen suke? Anan kuma Aliyu ya girma? Amma Sadauki sai yaki tashi daga inda yake a durkushe. Sai ya rarrafa gaban Alhaji Babba yace "Alhaji dan Allah, nasan nine ba kwaso na yarda kuma ba zaku aura min Diyam ba amma dan Allah, dan Allah Alhaji kar kuyi mata aure, in dai saboda nine to na hakura na janye neman aurenta please ku barta tayi karatunta, ku barta ta girma ta zabi wani da kanta" Alhaji Babba ya dauke kansa, Sadauki ya sake cewa "in kuma lallai sai kunyi mata aure please not Saghir, ga Mukhtar nan" ya fada yana nuna Mama, "ku aura mata Mukhtar indai har sai kunyi mata auren yanzu but please banda Saghir".4 Alhaji Babba ya mike "kai a matsayin ka na waye zaka gaya mana wanda zamu aura mata da wanda ba zamu aura mata ba? To albishirin ka, Saghir din zamu aura mata kuma rana ita yau za'a daura auren idan kaji haushi kaje ka fada rijiya ka mutu".1 Ina daki a kwance, na bude idona a hankali ina kallon dakin na lura Inna bata nan. Sai na tashi zaune haka kawai naji ina son in fita waje. Na fito palo sai naga Inna da amaryar Alhaji Babba a can gefe suna magana kasa kasa amma basu ganni ba, sai na wuce su na bude kofar palon na fita waje ina karewa compound din kallo, haka kawai naji zuciyata tana gaya min in tsaya anan wajen. Ban jima ba kuwa sai na hango su sun fito daga part din Alhaji Babba su hudu, manyan maza guda biyu da Mama sai kuma mutumin da ko cikin duhu na hango shi zan gane shi. Sadauki. Su biyun sauri suke yi shi kuma a hankali yake tafiya yana ta waige waige, sai kawai na sati handle din kofar na fita da gudu na tafi inda yake, tun daga nesa ya hango ni sai ya juyo ya bude min hannayensa ni kuma na wuce direct zuwa kirjinsa ya mayar da hannayen ya rufe. Na fashe da kuka ina kankame shi.5 A hankali yace "shshshsh, ya isa haka kukan, stop crying please. Wai litre hawaye nawa zaki zubar ne a cikin wata daya?" Sama sama naki hayaniya a compound din amma sai nake ji kamar wani background noice ne akan maganar da Sadauki yake gaya min. "Be strong Diyam, you are stronger than this. Ki zama jaruma ki bude hannayenki ki karbi duk wata kaddara da Allah zai dora miki ki dauke ta a matsayin jarabawa, ki dauka cewa Allah yana jaraba ki ne dan yaga how strong are you for the blessings He plans a head for you. Ki sani cewa Allah yana tare dake a ko da yaushe, kuma ki saka a ranki cewa ni Sadauki zan kasance tare da ke a koda yaushe, this is my promise to you, I will be with you forever and ever, I will love you forever and ever. Always ki saka a ranki cewa an angle is watching over you. Always. No matter what happens and no matter how long"1 Hayaniya ake yi sosai yayinda ni kuma nayi luf a kirjinsa ina jin kamar anan aka halicceni, ina jin muryar Inna "ba zaka shika ta ba? Maye" Alhaji Babba "kuyi ta dukansa har sai ya sakar mana 'yarmu" dan uwan baban Sadauki "kar wanda ya taba shi, wallahi duk wanda ya taba shi sai yayi nadama". Lokaci daya kuma sai Sadauki ya sake ni, ya rike fuskata yana kallona idonsa cike da wani yanayin da ban taba gani ba and then without another word ya kama hanyar waje da sauri, ina jin Alhaji Babba yana bawa yaran gidan umarnin su dake shi amma sai naga kawai kaucewa suke suna bashi guri har ya fita. Ni nasan a wannan yanayin da yake ciki da wani ya taba shi da tabbas in bai kaishi lahira ba to kuwa zai kaishi asibiti.3 Yana fita daga gidan naji wani nauyi a zuciyata, wani duhu ya mamaye idanuwana, sai kuma kafafuwana suka lankwashe na zube a gurin unconscious.3 Na bude idona a hankali ina kallon ceiling kamar mai son fahimtar yadda aka tsara shi. Kaina yayi min nauyi haka kirjina. Sheshshekar kukan da naji a kusa dani ce ta sakani waigawa ina kallon mai kukan, Asma'u, tayi sharkaf da hawaye da majina da gumi sai kukanta take yi bil hakki. Na tashi hannuna dafe da kaina nace "Asma'u?" Sai ta juyo da sauri ta rungume ni "Adda dan Allah kema karki mutu ki barni" na rungume ta ina dan jijjiga ta nace "bazan mutu ba kinji, ina nan tare dake" sai ta daho kai tana kallona tace "Adda wai Sadauki ya tafi da gaske? Inna tace wai ya tafi kuma ba zai kuma dawowa ba" naji gaba-daya abinda ya faru yana dawomin kaina kamar film, wani kuka ya taho min amma sai na rike shi a nace mata "zai dawo kinji Yar Asama (sunan da yake tsokanar ta dashi) zai dawo wata rana". Na gyara mata kwanciyar ta a jikina naja bargo na lullube mu tare, sai kuma na fara bitar abubuwan da suka wakana, na hango fuskar Sadauki a idona da irin bacin ran dana gani a idonsa, na tuno kalaman daya gayamin a kunnena. "Be strong" he said, but how can I be strong without him bayan shi din shine strength dina? Yace in bude hannayena in karbi duk wani abin da ya tunkaro ni but how can I do that bayan ya sabar min da kasance wa shield dina? Shi yake tsayawa a gabana ya kare ni daga duk wanda yayi niyyar zalintata, shi ya shagwaba ni inyi duk abinda nake so saboda ina takama ina da Sadauki. Yanzu banj da Sadauki kuma. I felt so exposed. So alone. So scared. Ji naui kamar duk mutanen duniya ne suka hada kansu suke nema su zalince ni. Suddenly sai naji duk duniyar ta ishe ni, to menene amfanin zama a cikinta? Me zan tsinta a cikin rayuwar indai har aka aura min wanda bana so aka ce in cigaba da zama dashi har karshen rayuwata? Sai naji feeling irin feeling din da yammatan da suke kashe kansu saboda auren dole suka ji kafin su kashe kan nasu. Sai naji feeling irin feeling din da yammatan da suke guduwa daga gaban iyayensu suke shiga duniya suke ji kafin su gudu din, ashe dai laifin su kadan ne, ashe dai tura su akayi zuwa limit din da shaidan ya kada musu gansar sa su kuma suka bishi. Sai dare sannan na tashi na hada sallar magrib da isha saboda wani irin zazzaɓi da ciwon kai da nake yi. Ƙwaƙwalwa ta ta zama blank kamar babu komai a cikinta saboda na rasa wanne tunanin zanyi. Ni dai bana so in shiga duniya saboda I might end up never seeing Sadauki again tunda bansan inda zan same shi ba. Ba kuma naso in kashe kaina saboda nasan wuta zan tafi. Bani kuma da wanda zan kai kara gurinsa saboda su masu shirin yi min auren nan su ne dangin uwata kuma sune dangin ubana, dan Alhaji Babba a lokacin zan iya cewa shi yake juya kowa a family, saboda shi yake da naira. Sai na dora goshina a kasa na fara gayawa Allah, ina rokon sa ya sakamin ga duk wanda ya zalince ni, ina rokonsa kuma ya bani karfi da juriyar daukan duk wata kaddara daya rubuta min. A kan sallayar na kwanta na lulluba da hijab dina, ina jin Inna ta shigo ta taba wuya na sai kuma ta fita, sai gasu sun dawo da Hajiya Yalwati da Murja, ina jin su suka kamani suka saka ni a mota sannan naji muna tafiya, na dago kai na kalli Hajiya yalwati data rungume ni a cinyar ta nace "Hajiya, dan Allah bana son auren hamma Saghir". A asibitin muna zuwa suka bamu gado, sunce temperature ta tayi sama da yawa dan haka sai na kwana a gurinsu for monitoring, suka yi min allurai ciki har dana bacci dan haka na samu nayi bacci amma cike da mafarkai. Cikin mafarkan da nayi harda wanda na ganni na soka wa hamma Saghir wuka a ciki.1 Washegari aka sallamo ni tare da warning cewa jini na yana neman hawa, as young as I was. Muna dawowa gida Hajiya Yalwati ta zauna tana jera wa Inna bayanin likita Inna ta fara sharar hawaye tana cewa "ni in kuna wannan maganar sai inga kamar kuna dora min laifi ne, ni ya kuke so inyi ne wai? Ta yaya kuke tunanin zan je gurin Alhaji Babba in ce masa ba zai aurawa Saghir Diyam ba? Ta yaya? Ga Hafsa ma tayi fushi dani tunda ta tafi jiya har yau taki daukan wayata" Hajiya Yalwati tace "kamar yadda shi da matarsa suka so kansu suke neman hada Diyam da tantirin dansu kema haka zaki so taki yar kice ba za'ayi ba" Inna tace "yanzu zumunci har ya kai haka lalacewa? To ku ku gaya masa mana? Ku gaya masa Diyam tace bata so gashi har tana neman salwanta saboda haka" Hajiya Yalwati ta rike baki tace "ni asu wa? Ina magana cewa za'ayi kishi nake da bakin ciki".1 STORY CONTINUES BELOW Da rana sai ga abinci kala kala wai inji Hajiya Babba, ko kallon inda suke banyi ba. Ana jimawa sai gata tazo, tunda muka zo gidan ban taba ganinta a dakin ba sai yau. Ta zauna a bakin gado suna gaisawa da Inna sannan ta data jikina tace min "sannu Diyam" kai kawai na gyada mata, tace da Inna "ba zai wuce malaria ba fa, ita ake ta fama yanzu" Inna ta kauda kai tace "likita yace jininta ne yake neman hawa, hawan jini ne yake kokarin kamata" Hajiya Babba ta bude baki tace "hawan jini kuma? Wa likitan ya gayawa?" Inna ta ce "Hajiya Yalwati, ita ta kaita asibitin ai" Hajiya Babba tayi murmushi tace "hmmm, neman magana ne kawai irin na Hajiya Yalwati. Babu wani hawan jini ni na sani" sai kuma ta kauda maganar "kinga fita ma zanyi nace bara inzo in duba ta. Kinsan dazu da safe Alhaji ya siyasa Saghir gidan da zasu zauna, shine yanzu zanje in ga gidan sannan inyi lissafin duk kayayyakin da za'a siya. Wannan abu ai tuwona mai na ne. Kar kiji komai duk abinda ake yiwa yarinya na gata to za'a yiwa Diyam a dakinta. Ni da kaina zan siyo komai tun daga kayan daki har kitchen".1 Tana fita Inna ta bita da harara tana magana kasa kasa. Sai kuma ta dauki waya ta kira zuwa can aka dauka ta fara magana "haba Hafsa, wai dame kike so inji ne, da mutuwar mijina ko da auren dolen da za'ayiwa Diyam ko kuma da fushin da kike yi dani? Yanzu Hajiya Babba take gaya min wai an bata kudi zata siyo wa Diyam kayan daki, saboda Allah bake da Fatima ya kamata kuyi wa Diyam siyayya ba? Wannan ai ba hurumin ta bane ba. Gaskiya kizo kije gurin Alhaji sai ki nuna masa kamar baki san maganar ba ki tambayeshi ya bayar da kudin kayan dakin Diyam zaki je ki siyo mata" sun jima suna ta mayar da magana sannan suka yi sallama. Mama bata zo gidan ba sai washegari, shima tana zuwa tace "ni fa ba wannan maganar ce ta kawo ni ba, zuwa nayi in duba jikin Diyam. Su je suyi ta siya mata koma menene ba damuwa ta bace wannan. Ni damuwa ta shine in dauko yaron nan kafa da kafa in kawo shi har gidan nan amma a wulakanta su har dake a ciki, ni da ban shi nake yi ba dan Diyam nake yi. Kuma wallahi yadda naji takaicin abinda kukayi wa yaron nan ko wallahi da niyya nayi in bashi auren Rumaisa, dan dai kawai yace min a'a ne wallahi da sai dai kawai ki gansu tare da Rumaisa sai kuma inga yadda zaki yi da shi. Suma kuma yan uwansa suka ce a'a ba yanzu zasuyi masa aure ba wannan ma dan rana daya ya tayar da hankalinsa suma kuma ya tayar musu shi yasa suka taho nema masa". Haka ta gama fadanta ta tafi babu wanda ta gaisar a gidan. Washegari na dan samu sauki babu laifi. Amma zuciyata babu sauki a tare da ita sai ma kara zafi da takeyi kamar ana hura min wuta a cikinta. Inna ta matsamin dole nayi wanka wanda rabona dashi tun ranar da Sadauki yazo gidan. Na fito daga toilet na tsaya a gaban mudubi ina kallon kaina. I can't believe how many things ne sukayi changing a rayuwata in just few weeks? Har yanzu fa ba'ayi arba'in din baffa da Ummah ba amma wai har mutane sun manta dasu, har an shafe babinsu an bude sabon babi na yiwa yarsa aure a shekara goma sha huɗu. Nayi wa yarsa auren da aka san inda ace yana da rai babu wanda ya isa ya ko tunkare shi da maganar danshi ba damuwa yayi da kudin mutum ba ballantana mutum yace ya daina bashi. Ina cikin saka kaya ne naji hayaniya a palo har da guɗa, sai kuma gasu Murja nan sun shigo inda nake suna ta murna da dariya. "Amaryar Hamma" Salma autar Hajiya Babba wadda ba'a jima da bikinta ba ta fada. Sai kuma suka kwashe da dariya. Kusan duk yayan Alhaji Babba wadanda suke aure dama yammata da suke gidan duk suna nan. Na dauke kaina ba tare dana kula su ba na zauna ina daura dankwali na, "munga kaya masha Allah, kaya sunyi kyau, ko dan gidan gwamna ne iya kacin kayan lefen da za'a kawo kenan" naji wani suka a kirjina "lefe? Nawa?" Sai na kwanta a kan gado na rufe idona. Ina jin murja tace "ku bata so fa, kar ku saka ta kuka" Suwaiba tace "bata son wa? Hamman? Anya kuwa akwai macen da zata ce bata son hamma komai kyanta? Kunya ce dai kawai take ji amma babu ma zancen wai bata sonsa" Aysha tace "ni kam zan so inga yayanku, wow, Diyam kyau hamma kyau, in ina da ciki zanke zuwa gidan ku dan in haifi yaya kyawawa nima" na juya baya na jawo hijab dina na rufe fuskata a raina ina cewa 'ya'ya kuma? Ni da Saghir? Tabbas nasan me akeyi ake samun yayan but I will die first kafin in barshi ya taba ni. For I thought I belong to one, and one alone. Sadauki. Sai kawai tunanin matan da suke kashe mazajensu cikin dare yazo min and it didn't look so bad.2 STORY CONTINUES BELOW Adda Zubaida ce ta shigo ta kore su gaba-daya. "Manya manya daku kunzo kun saka yar karamar yarinya a gaba kuna tsokanar ta" Salma tace "yar karama ce amma ta kusa shiga layin manya" suka fice suna dariya. Adda Zubaida ta zauna a kusa dani ta dafa ni taji ina sheshshekar kuka tace "kiyi hakuri Diyam kinji? Kiyi fatan wannan hadin ya zamo miki alkhairi. Duk sanda kike bukatar wani abu ko wata shawara ki neme ni kinji? Karki dauka cewa ni yayar Saghir ce ki dauka cewa ni yayarki ce kinji" na gyada mata kai. Ina nan kwance aka yi ta shigowa da akwatinan ana jere wa a gefe, ina jin daya daga cikin yan aikin gidan da suke shigowa da kayan tace da dayar "ai ga amaryar nan a kwance" sai kuwa suka hada baki suka rangada min wata uwar guda a kaina wadda naji kamar zata tsaga min kan. Sai bayan da kowa ya watse sannan Inna ta shigo ita da Asma'u. Ta tashe ni zaune tana murmushi "tashi Diyam, tashi kiga kayan lefen ki" ta fara bubbudewa, "kinga wadannan sarkokin? Wannan zata yi miki kyau. Kinga pearls din da kike ta nacin in siya miki. Kinga wani lace? Dankari! Wannan ai na zuwa gidan biki ne. Ga takalmin can mai tsini irin wanda kike so" ni dai kallon ta kawai nake yi ko kadan banji zuciyata tayi sha'awar wani abu a cikin kayan ba, na kalli Asma'u data baje a gefe tana ta zaben kayan kwalliya wai duk tana so in bata. Sai kuma ina ta tashi ta fita ta bani guri. Na kalli kayan, akwatuna ne set hudu, pink, purple, peach da blue kowanne kuma da kyar ake rufe shi saboda kaya. Na mika hannu na na dauki wata bra ina kalla a raina nace "ko me suke tunanin zan saka a cikin wannan brazier? Na mayar da ita na ajiye na koma na kwanta na juya wa kayan baya.4 Kwana biyu bayan nan ina zaune ina cin abincin da yanzu kullum sai Hajiya Babba ta girka ta aiko min dashi Inna kuma sai ta matsa min naci, sai ga Murja nan ta shigo "Diyam Alhaji yace ki shirya zamu fita yanzu gaba daya" ban kalle taba nace "babu inda zanje" ta daga hannu tace "ni dai yar aike ce". Sai kuma ga Hajiya Babba nan tazo da kanta, taci kwalliya kamar mai shirin zuwa gidan biki tace "innar Asma'u Alhaji yace Diyam tazo muje ganin gida da ita, in yaso in da akwai wani abin da take so sai ta fada a siya" tana fita Inna tace "ki tashi maza ki shirya ku tafi" na bata rai "Inna ni babu abinda nake so, in na gani ma babu abinda zan ce su kara" ta watsa min harara dole na tashi na shiga toilet na wanke fuskata na fito na saka hijab tace "kuma ko dan mai ba zaki shafa ba?" Na dawo na lakuci mai na shafa na juya tace "au dan nace mai shine kika shafa man shi kadai?" Nayi kamar zanyi kuka tace jeki. Ina fita na tarar da yayan gidan suna ta shiga mota, matan gidan kuma suna gefe a tsaye suna hira. Na tsaya daga gefe ina kallon compound din, na kalli dai dai inda muka tsaya da Sadauki rannan sai naji ina ma dai ranar zata dawo in sake ganin sa at least koda sau daya ne. Na kalli gurin motoci sai idona ya sauka a kansa, cikin normal shigarshi ta dogayen kaya yayi kyau sai kyalli yake yi amma fuskar nan babu annuri ko digo a cikinta. Kallo daya nayi masa naji kamar duniyar ce take kara kuntatamin dan haka na juya na bar gurin na tafi inda yara suke shiga mota sai kuma naji kira da muryar Hajiya Babba "Diyam, ki dawo nan tare zamu tafi dake" na juya kamar zanyi kuka na koma, sai naga sun doshi motar da yake tsaye a kusa da ita, anti amarya tace "Diyam shiga gaba mu sai mu zauna a baya" na tsaya kawai ina kallon su kamar in rufe su da duka har suka gama shiga, shima ya shiga seat din driver ya zauna ya tayar da motar, sai da suka sake yi min magana sannan na kama handle din kofar jishi a rufe ni kuwa na koma da baya na nade hannu na a kirji. Hajiya Yalwati ta leko. "Ki shigo mana Diyam, ke fa muke jira" nace "kofar a rufe take Hajiya" ina jin Hajiya Babba tana yi masa magana, ya dauke kai kamar bai jita ba sannan kuma bayan wajan minti daya sai ya bude lock din. Na bude na zauna a makale a bakin kofa ba tare dana ko kalli side din da yake ba. A hanya naji Hajiya Babba tana yiwa kishiyoyinta bayani "kunsan halin Saghir da rashin son hayaniya, wai shi ba zai zauna a cikin gari ba saboda kar mutane su dame shi, nace to kai me kanne da yawa? Namiji tilo a cikin mata? Ai dole ko gari ka bari sai kannenka sunje gidan ka, shine Alhaji ya biye masa aka siya masa gidan a can wajen gari, unguwar tokarawa acan zasu zauna" a raina nace 'wato yadda zai samu damar kasheni hankali kwance' ni a lokacin ban ma san unguwar ba sai dai naga mun dau hanyar barin gari, sai da muka wuce 'yan kaba sannan muka sauka daga titi muka shiga unguwar dana lura kamar sabuwar unguwa ce. Tun daga nesa na gane gidan. A house fit for the only son of Alhaji Babba amma ko kadan banji kyan gidan ya burge ni ba. Mukayi packing kusan a tare dasu Murja, na fita na tafi gurin su muka shiga tare amma sai na zame na zagaya bayan gidan nayi zamana akan veranda r backdoor din gidan. Ina jiyo su suna ta hayaniya da iface ifacen su alamar suna cikin nishadi amma ko sha'awar inje inga gidan banyi ba, addu'a nake a raina kar Allah yasa ina da rabon ganin cikin gidan nan in dai a matsayin matar Saghir ce. Naji wata irin kewar Sadauki ta taso min, sau dubu gwara ace in zauna da Sadauki a gidan kasa me yoyo akan in zauna da Saghir a wannan gidan.1 Kamshin turare naji, na daga kai sai na ganshi a tsaye yana kallon gefe da alama bai san ma ina gurin ba. Fuskar nan kamar an aiko masa da mutuwa. Nayi saurin share hawayen fuskata saboda bana son ko kadan yaga weakness dina ballantana ya kara rainani. Motsin da nayi ne yasa ya juyo ya kalli inda nake, sai kuma naga ya tako cikin gadara yazo gabana ya tsaye ya kara tamke fuska yace "ke! Me na gaya miki rannan? Ba zaki je ki gaya musu ba sai kin je kin daukowa kanki abinda ba zaki iya ba ko?" Na mike tsaye na karkade hijab dina na juya zan bar masa gurin, ya damko hijab dina ya juyo dani yace cikin barazana "ba dake nake magana ba?" Na zabga masa hararar da nasan ba'a taba yi masa irinta ba nace "su wadanda kake magana a kansu ai sunfi kowa sanin cewa bana sonka, sunfi kowa sanin ina da wanda nake so wanda kuma yake sona, asalima dan su raba ni dashi ne suke neman makalamin kai"

Post a Comment for "DIYAM CHAPTER 9"