Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN ADAM CHAPTER 37 KARSHE

DAN ADAM CHAPTER 37 KARSHE

- - Post a Comment
DAN ADAM CHAPTER 37 KARSHE
Kwananta uku gidan Mami har ankon bikin Amina, Mami ce ta bada a dinkamata. Har ta cika kwanakinta babu wata jituwa tsakaninta da Ihsan duk da ita Ummin bata dauki gaba da ita ba don duk wayewar gari sai ta gaisheta matsayin yar uwarta musulma, a dakile Ihsan ke amsawa. Saida Mami ta soma biyawa da ita wajensu Hajja suka gaisa, har Hajja ta matsa akan sai ta kwana, dole ta barta anan ta yi musu kwana daya daman acewar Mamin, ya dace ta kwanarmusu, a wannan kwanan saida Hajja ta kara neman afuwar Ummi don shakka babu ta ji kunya musamman jin cewa Ummin na dauke da juna biyu, tabbas idan Rabo Ya Rantse to duk kiyayyarka da auren sai an yishi. Ummi ta ji dadi ta nunamata babu komai, sun sha hira kwarai har da dariya da su Modibbo wanda ke jikinsa ya matsa mishi a yan kwanakin, washegari ta wuce gidan Hajiya Mama. Nan ma ta ga kulawa da tarba mai kyau daga iyalan Hajiya Mama har ita kanta. Su Maryam kamar su hadiyeta. Amina Amarya ta yi kyau ta gyaru tsaf, anan gidan zaayi yinin biki, kwarai Hajiya Mama ta yi musu kara. Acan gidan Innar Amina, yan uwan babansu ne na Nijar da na Innarsu anan Kano suka cika gidan. Amina ta sha mamaki jin cewa Malam Balarabe da kaninsa Baffa zasu zo daurin aurenta, ta hadata da Dada ta waya inda ta bata hakuri gami da nunamata ta so zuwa saidai bata samu dama ba, Amina ta nuna babu komai. Da dare suna zaune a dakin su Maryam gaba daya suna hira da dariya, wayar Maryam ta yi k'ara, ta mike da sauri ta fita. "Mene na gudun? Ai munsan mai kiran, Adnan ne." Cewar Rukayya cikin daga murya. Amina da Ummi suka dara. Amina ta cafe. "Kai ke kuma ba'a sirri dake." Dariya Rukayya ta yi. "Ai naga sai wani 6oye-6oye sukeyi kamar bamusan komai ba, gwara mu nunamusu mun d'agosu." Ummi da mamaki ta ce. "Wai don Allah soyayya su ke yi?" "Ba ki da labari? Gaskiya Amina kinci amanar kauna da ba ki fesamata ba, ai kullum suna mak'ale da juna ta waya duk da wani 6oye-6oyen da sukeyi munsan komai, daidai da Hajiya Mama ta sani." Ummi fara'arta ta karu. "Kai na ji dadi wallahi, Yaya Adnan ya yi dace kam, Maryam ba ruwanta halayenta na burgeni. Sun dace wallahi." "Karshe ma." Cewar Rukayya daidai lokacin da Maryam ta shigo ta mikawa Ummi wayar. "Ga Yaya Adnan ku gaisa." Ta kar6a tana tsuke baki. Ta yi sallama ya amsa gami da fadin. "Allah Ya kiyayemana ke ranki ya dad'e." Ta hadiye dariyarta. "Ai ni na yi fushi Yaya Adnan, ka daina nemana kuma ko na kira layinka yanzu ba ya shiga." "Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Na ji kunya biyu. Na farko kirana da Yaya Adnan da ki ka yi, na biyun kuma, kiran da ban yi miki da sabon layina ba kasancewar wancan ya fad'i sai na barshi. Ki yi hakuri Ranki ya dade matar bestie." Sukayi dariya a tare, ta girgiza kai. "Har abada, Yayana ne kai wallahi. To na hakura, ya fama da biro da takarda?" "Gashinan sai kuyita tayamu da addua. Kinga surukarki ko? Ta yi ko akwai gyara?" Ta daga idanu ta dubi Maryam da su Rukayya ke tsokana ta yi dariya. "Ta yi 100%." Ya yi dariya cike da mamakin yanda tasan wani 100% domin ko kusa ba shi da labarin ana mata darussa. Saidai kuma bazai iya tambayarta ba. "Yauwa Ranki ya dade, ai da kince akwai matsala tuni zan dakata." "Wace ni da fadin haka?" Suka dara kafin su yi sallama.+ An soma bikin Amina lafiya, ana gobe daurin aure Malam Balarabe suka zo, sun sha hira da diyarsa har ya rasa inda zai sakata don tsabar farinciki. Ita ta yi musu jagora har wajen Inna don yi mata fatan alheri, wani abu ya darsu a zukatan tsoffin sadda suka yi arba da juna. Bayan an daura auren ne Malam Balarabe ya kasa jurewa har saida ya sanarwa Baffa kaninsa don daman ya samun labarin cewa yanzu Inna bata da aure, hakanan yana iya cewa tun bayan Hasiya babu wacce ya kara gani ya ji yana so ya karashe rayuwarsa da ita matsayin mata kamar Inna Bilkisu. Baffa ya ji dadi kwarai kuma zai so hakan. Abinka da batun manya nan suka tuntu6i babban Yayan Bilkisu, Mahmuda, nan ya nunamusu jin dadinsa a fili don kwarai ba ya son zaman kanwartasa haka babu aure duk da cewa ta aurar da yara biyu Fiddausi da Hauwa, sai Amina ta uku, ga kuma autanta Ahmad mai shekaru goma sha daya a yanzu, ya yi musu alk'awarin tuntu6ar Inna Bilkisu. A karshe sukayi musayar lambobin waya sannan a karshe sukayi sallama da kowa suka tafi, Ummi har hawaye ta yi don kewa, shi kuwa babanta dadin yanayin da ya ganta ya ji don ta yi k'iba ta kara kyau. Inna ta ji lamarin banbarakwai duk kuwa da cewa a ganin farko da ta yiwa Malam Balarabe ya kwantamata, ba musu ta amince da hakan. Nan ya kira ya shaidamusu, basu yi wata wata ba suka sanarwa iyayensu, Malam ya ji dadi haka ma Dada wacce ke tausayawa dan nata. Aka tsaida magana nan da sati biyu za'a je a daura aure. Su Anti Hauwa sun ji abin banbarakwai, wai Innarsu aure. Tun basu ji ko waye mijin ba suka nuna rashin goyon bayansu, acewarsu da shekarunta na arba'in da takwas me ya ragemata banda ibada? A bakin matar Kawunnasu suka ji waye manemin auren, hankalinsu ya kwanta suka ji dadi, kusan Amina ta fisu jin dadin lamarin don a take ta bugawa Ummi wacce ke shirin komawa Abuja. "Albishirinki." Ummi ta ware ido. "Goro fari k'al Antina." "Inna zata zama matar Babanmu." Cikin rashin fahimta ta ce. "Anti inace kin cemin Baba ya rasu." Ta ja tsaki. "Dallah can, babanmu fa na Gombe." Daskarewa ta yi a tsaye ta bar ninke kayan. Ita abin kamar mafarki haka ta jishi. "Ke ya ki ka yi shiru, wallahi dagaske ne." Tiryan-tiryan ta labartamata abinda ta ji. Hawaye kawai Ummi ta shiga fitarwa tana kara jin kaunar Amina da yan uwanta. Banda hamdala babu abinda ta dunga nanatawa a fili. Bayan komawarta Abuja ta sanarwa Faruk wanda shima ya ji dadi ainun, ya sanyawa lamarin albarka. Kowa ya ji sai ya sanya albarka ciki. Koda ta kira mahaifinta, dariya kawai ya yi ya ce. "Lamarin Allah kenan Hasiya, a tayamu addua." Farinciki fal cikin ranta haka suka sha hira suka yi sallama. *** *** *** BAYAN WATANNI BIYAR Ayau ake bikin yaye su Ikram daga sakandire, acan Kano ma su Ihsan na nasu shagalin don lokaci guda aka yi bikin yayesu. Duk yayyun Ikram sun je mata banda Baraka dake wankan jego ta haifi danta namiji wanda ya ci sunan mahaifin Mijinta suke kiransa da Abulkhair. Ummi ma da cikinta dan wata bakwai katon gaske haka ta zo. Fuskarta duk ta chanja, tana sanye da wata tsadaddiyar abaya Faruk na rike da hannunta. Ikram duk bata tare da walwala sai lek'e-lek'en wuya ta ke faman yi. "Wai me ki ke nema haka?" Cewar Fadila wacce ta kasa shiru. Ikram ta dubeta, kafin ta yi magana suka ji sallama a gefensu duk suka waiga, mamaki karara ya bayyana a fuskokinsu. Yana sanye da doguwar riga da wando na shadda dark green wacce ta sha aiki, ya dora hula mai fari da koren din sak'a, ya yi kyau kuma ta haskakashi ainun. Sai murmushi ya ke faman dokawa. "Yaya Gidado?" Ummi ta furta da tsantsar mamaki kafin kuma ta saki fara'a sosai. Ya bita da murmushi kafin ya karasa ya soma mikawa Mazajen Hajiya Babba hannu suna gaisawa. Suma sun saki fuskokinsu, Fadila da Jidda suka yi turus suna kallon ikon Allah, sun kuwa gane waye shi amman idan ka ganshi saika rantse ba daga kauyen Jar Kwami ya fito ba tsabar iya daukar wanka. Ikram ta kasa rufe baki, zuciyarta na kara nutsawa cikin kogin so da kaunarsa, babban abinda yasa ta ke kwadayi da mafarkin zuwan wannan ranar kenan don kuwa ya bata tabbacin zai zo mata da kyakkyawan albishir duk ranar da ta yi Candy. Toh yau ga ranar ta zo. "Ashe kana tafe ba ka sanarmana ba mu yi maka kyakkawan tarba?" Cewar Faruk cikin sakin fuska. Gidado ya danyi dariya. "A yi hakuri surukina, ai gani yanzu ma bata 6aci ba." "Lallai kam, saidai kamar zuwan ba namu bane na kanwarmu ne ko?." Cewar Haidar wanda ya riga yasan dawan garin daga Intisar., ya fada yana duban Ikram. Suka yi dariya, kunya ta kama Ikram. "Eh to, kusan hakan." Cewar Gidado, shi kuwa babban Yaya da Ridwan mamaki sukayi don basu zata ba , hakanan Faruk shi kansa bai ji daga matarsa ba. Ya dan matse hannunta ta yi karamin kara. "Shine ko ki gayamin?" Ta waro ido. "Babu wani abu fa tsakaninsu." Murmushi kawai ya yi. Har aka tashi taron Gidado bai samu ke6ewa da Ikram ba sai bayan sun koma gida, bayan ya gaisa da su Hajiya suka ke6e da ita a dakin bak'i. Ya fiddo wani akwati daga aljihunsa ya mik'amata. "Ga kyautar da na zo miki da ita, ki yi hakuri babu yawa.". Ta kar6a tana washe baki. "A wajenka ne babu yawa." Sukayi dariya. "Ba za ki bini bashin zance ba Ikram, yau zan sanarmiki abinda ban ta6a sanarmiki ba. Haka kuma zan cika alkawarin da na daukar miki." Ta lumshe idanu ta budesu. "Ina jinka Yayana." Shiru ya dan biyo baya kafin ya cigaba da magana. "Karambanin so ke neman kaini inda aka fi karfina, duk iya kokarin da na yi na dannewa da kaucewa faruwar hakan, saidai ya gagara, bazan iya hana Allah zartar da hukuncinSa, ban isa ba ban kuma kai ba. Wallahi na kamu da sonki Ikram, so na gaskiya, a rayuwa ban ta6a zaton zan kara son wata diya nace ba bayan Hafsa, amma cikin ikon Allah da sannu-sannu kyawawan d'abi'unki da kuma hakurinki suka rinjayi zuciyata na afka cikin kogin son wacce ta fi karfin dan kauyen Jar Kwami." Ta kasa motsi, ta kasa gaskatawa, ta kuma kasa tantance hakikanin yanayin da zuciyarta ta fada. Kallonsa kawai ta ke tamkar wata doluwa. Ya kai yatsa kamar zai tsone idonnata ta yi saurin lumshewa, sai kuma ta yi kasa da kai tana murmushi. "Wannan kallon fa ya tsoratani, ko ba'a sona?" Ya fada don jin ta bakinta kawai bawai don baisan cewar tana sonsa ba. "Bance ba, saidai na yi mamaki ne kawai ace kamar ka kana sona?" "Kina neman ki ce kinfi karfina ko?" Ya fada a raunane. Ta yi saurin girgiza kai kamar mai shirin kuka ta ce. "Wallahi aa, ni don Allah ka daina bambanta kanka da ni, kaima cikakken DAN ADAM ne mai daraja, ina girmamaka hakanan ina sonka tsakani da Allah." Ya murmusa gami da sunkuyowa saitin fuskarta cikin muryar rada. "Za ki iya zaman aure da ni a Jar Kwami?" Ta lumshe idanu gabanta na bugu da sauri-sauri. "Yayana ba Jar Kwami ba, koda cikin daji ka ke rayuwa wallahi zan iya binka muyi zaman aure, ina sonka fa." Ta karashe kamar za ta yi kuka, ai kuwa hawayen da ta ke makalewa suka kwaranyo. "Komai na Allah ne." Ta tuna furucin Ummi gareta a watarana da ta je gidanta da korafin yanda ta ke kara jin son Gidado a ranta kamar ta mutu. "Idan Allah Ya kaddaro mijinki ne, za ku yi aure." Fadin Intisar a watarana suna hira ta ke kokawa bisa yanda Gidado kan share kwanaki ba ya nemanta koda ta waya sai idan ta nemeshi. "Na gaji da jin maganar Gidadon nan, don Allah ki hakura ki fiddashi cikin ranki, idan mijinki ne fa sai kunyi aurennan ko ba ya so." Cewar Hajiya a wataran da ta risketa tana kukan yanda ya ke yawan yi mata hirar matarsa wanda batasani ba wani zubin da gayya ya ke yi don kawai ya gwada ko tana kishinsa. Ta share hawayenta. Gidado zaune ya cigaba da fayyacemata irin son da ya ke mata ya kuma tabbatarmata ba da wasa ya zo ba, sonta ya ke yi tsakaninsa da Allah. Koda ta yi mishi batun Hafsa, ya nunamata wannan ba matsala bace, matarsa nada saukin kai tana son abinda ya ke so. Ranar saida ta yi nafilfilu don nuna godiyarta ga Ubangiji. Daidai da Hajiya ta taya diyarta murna hakanan duk wani masoyinta da yasan tana son Gidado, ko Ihsan ma ta dan ji sanyi ganewar ba yar uwarta kadai ke wahala ba, ashe shima yana so. "Allah Ya ba ki sa'a." Shine kawai abinda Jidda ta fadi. Ita kuwa bata biyemusu ba don ta gane yan adawa ne. Kamar wasa, aka tsayar da maganar auren Ikram da Gidado wanda takanas iyayensa suka zo Abuja nema mishi bayan an samu an shawo kan Hafsa dakyar wacce ta dage akan saita bar gidan Gidado ta ya ya zai hadata kishi da wayayyiya kamar Ikram? Acewarta wannan cutarwa ce, da dai ya auri Ikram gwara ya auromata yar kauyen Jar Kwami irinta sun zauna. Wasu cikin yan uwa suka goyi bayanta wasu kuwa ba su goya ba, hakanan a cikin dangin Gen. Ahmad Danzaki, wasu da yawa basu amince ba, acewarsu Ikram ba zata iya rayuwa a kauye ba da kuma dan kauye, ita kuwa ta dage lallai sai Gidado, to Daddy shima ya goyamaya baya ko babu komai autarsa ce yana ji da ita. Haka aka tsaida auren Ikram da Gidado wata uku ba da son ran wasu ba. Aka shiga shirye-shiryen bikin Abubakar da Ihsan, sai Iklima da Musaddik, mijin da Abba ya za6ar mata akayi sa'a sun hada kansu, da kuma kanwarsu Hassana da Abdullatif. Biki ya yi biki, dukkan yan uwa sun iso Kano, ciki harda KB wanda ya zo hutu daga Ghana, gaba daya ya chanja ya zamo na kirki kamar ba shi ba. Ummi ce ta samu dakyar Faruk ya amince da zuwanta, acewarsa cikinta ya tsufa babu yawo....! Ansha shagalin biki su Abida da sauran yan uwan Gombe na Jar Kwami duk sun hallara. Sai nan nan Hajiya Salma ke yi da Ummi, hakanan duk motsi da zata yi sai an tambayi ko akwai wata matsala. Tana zaune ta sanya kayan ankon Party a gaba tana kumbure-kumburen fuska, Ikram ta dubeta. "Allah Sarki Antina, yanzu shikenan ba za ki je ba?" Dariya su ka sanya gaba daya wanda ya kara k'ular da ita. "Tana gani zamu wuce amma ba inda za ta je tunda Oga ya hana." Cewar Baraka kenan. "Ke banda abinki, kina fama da wannan katon ciki haihuwar yau ko gobe ina ke ina wani dinner party?" Ta yi narai-narai da fuska. "Nasan da wanda zan hadashi ai, bari na kira Yayana." Sukayi dariya, ta kira Abubakar. "Innota ya akayi na ji muryarki na rawa?" Daman kiris ta ke jira kawai ta soma kuka. "Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun, me akayi? Kinga kina ina yanzu?" "Dakin Ihsan." "Ok ina zuwa." Ya katse kiran Faruk dake zaune gefensa a benci ya dubeshi. "Me ya samu Innontaka?" "Bari na je na gani." Ya bi bayansa da kallo kafin ya ta6e baki don yasan zancen bai wuce na party ba. Suna daga dakin suka ji falon ya dauka ga Ango ga Ango, da mamaki Baraka ta ce. "Eh lallai yar gatan yayanta, kiga har ya shigo." Ihsan wacce bata jima da shigowa dakin ba batasan me akeyi ba, sai ganin Abubakar ta yi ya shigo. Tana zaune saidai ban ma lura da ita ba ya yi wajen kanwarsa. Itama tana ganinsa ta kara turo baki tana murmurza idanuwa. "Ya Salam, meyafaru ne wai kanwata? Hankalina ya tashi wallahi." Ganin yanda duk ya rude yasa ta dan sassauta fuskarta, fuska ba walwala ta ce. "Ba shine ya ce wai bazan je dinner party ba." Ya dan runtse ido gami da numfasawa, hankalinsa ya dan kwanta. "Inji wa? Ai ya zama dole ku je don kafarki kafata. Barni da shi, kedai ki tabbatar kin shirya kinji ko?" "Yanzu bayanta za ka goya? Da wannan tulelan cikin ina ita ina wata dinner?" Cewar Rahila yayar Ihsan. Ya dan harareta don sun saba wasa da dariya. "Ina ruwanki to? Zuwa kuma ai ta yishi ta gama, atoh." Dariya sukayi banda Ihsan da ta k'ulu ganin kamar baisan da ita wajen ba. "Idan kaine mijinta ma ji ma gani." Ta kara fadi cikin dariya. "Shima a tafin hannuna ya ke, surukai muke." Daga haka ya fice suna mishi tsiya. Ihsan jikinta ya yi sanyi, wane irin Ango ne mai fifita wata akan matarsa? Haushi ya cika zuciyarta saidai dole ta danne ta mike bisa umarnin Aisha wacce ta shigo kiranta zuwa kwalliya don Magriba ta gabato kuma ana sallar Isha zaa wuce. Ya murza karan hancinsa gami da dora kafa daya kan daya kamar wani basarake yana dubansa. "Ka ce me?" Abubakar ya harareshi. "Na ce idan Inno ba zata je ba to fa nima babu inda zanje, kafarta k'afata." Wani murmushi mai burgewa Faruk ya yi kafin ya dubeshi. "Shikenan, ai ba kai kadai ne Angon ba, sai muje mu sha shagalinmu." Dariya su Haidar da Kb su ka yi don duk gaba daya suna zaune a babban falon na bak'i. Abubakar cikin dariyar ya amsa. "Kafata kafarta fa Malam, ai ba yawo za ta yi ba, wuri daya zata zauna." Baki Faruk ya ta6e baice uffan ba, yana ji Abubakar ya dauki waya ya kira Ummi gami da kara jaddadamata cewa ta shirya zuwa babu fashi don ya amince. Ya kalleshi kawai ya kauda kai kawai. Haka har aka tashi tafiya, idan kaga Amarennan saika k'ara kallonsu tsabar haduwar da sukayi domin kuwa wani arnen leshi suka sanya fari da silver ya zauna das a jikinsu., su kuwa Angwayen farin shadda k'al mai surfani ruwan toka suka sanya. Saura kuwa suka yi ankon bulun french lace mai ratsin ruwan toka sai silver head, yayinda tawagar samarin suka hade cikin (Sky blue)shadda, sunyi kyau har sun gaji da haduwa. Kowa ya shirya tsaf harda Ummi, ita buba ta yi na zani sannan ta dora mayafi ruwan toka-toka, ta yi kyau duk da cewa ta ajiye kumatu ga chanjin fuska da jiki sakamakon ciki. Aka soma fita itama ta fito, Mami ta kama ha6a. "Harda ke Ummi?" Hakan yasa sauran iyayen suka dubeta. Ta yi murmushi. "Eh Mami." "To ki bi a hankali banda tsalle-tsalle don Allah ki zauna wuri daya." Fadin Hajiya Mama kenan don wannan karon banda manyan iyaye a zuwa. Da haka Ummi ta fita ta na cigaba da gwada kiran Faruk wanda ya kashe wayoyinsa kaf. Takaici ya isheta, a waje ta tsaya tana waige-waige, motoci masu tsada sun cika farfajiyar gidan wasu kuwa da basu samu shigowa ba suna daga waje, to biki ne bana mutum daya ba, Hajiya Lubna itama yan uwanta na Maiduguri sunzo da yawa don bata ta6a aurar da diya ba, hakanan Hajiya Binta wacce rabin yan uwanta a Kano suke, su dinma duk hallara. Tana nan tsaye anata tafiya ta hango Gidado na kokarin shiga mota da sauri ta karasa gareshi. "Yaya Gidado." Ya waigi, yana ganinta ya karaso ya cimmata ganin yanda ta ke tafiya da sauri. "Yi a hankali mana Ummi, za ki je dinne?" Ta gyada kai gami da yin narai-narai da fuska. "Eh, ina Yaya Faruk?" Ya yi murmushi. "Yana kofar gida amma nasan yanzu sun wuce, taho mu tafi kawai." Ba musu ta bi bayansa, kafin ta kai ga shiga wayarta ta dauki k'ara, Abubakar ne. Ya tambayeta ko tana ina, ta sanarmishi gatanan za ta bi Gidado, ya ce ta jira tare zasu wuce. Ta amsa da toh gabanta na faduwa, kada fa ya zamana Faruk bai yi na'am da zuwannata bane, to amman ai Abubakar bazai mata karya ba tunda ya ce ya amince ta je. Aikuwa motar Ango da Amarya ta hau, gidan gaba ta zauna, Kb ne matuk'in Abubakar da Ihsan. Ihsan ta ci magani ganin Ummi k'ame a gaban mota, har akaje ba ta ce uffan ba sai kuwa Abubakar da Kb ke kwasar hirarsu, jefi-jefi sukan sanyo Ummi da Ihsan, motocin Amare a jere haja suka isa. Gaban Ummi ya fadi ganin Faruk zaune saman mota a farfajiyar wajen tare da Jafar abokin aikinsa suna hira. Ya yi kyau har ya gaji da haduwa. Tun shigowar motocin idanunsa suka hangomishi matarsa a gefen mutumin da har gobe bai mance abinda ya so aikatawa ga iyalinsa ba, wato Kb. Wani abu ya soki kirjinsa, kishi mai tsanani ya turnuk'eshi x ya dauke kai fuskarsa kamar an aikomishi sak'on mutuwa, wannan ba karamin firgita yan hanjin cikin Ummi ya yi ba, ta hau karanto adduo'i cikin ranta har motar ta daidaita fakin, har Amarya da Ango saida suka rigata fita, sannan a karshe ta daure ta bude mota ta fito, nan masu hoto suka yi musu ca, da sauri ta samu ta bar wajen ta nufi wajen mijinta, saidai babu shi babu dalilinsa, can ta hangeshi wajen Angwaye suna gaisawa da Abokai, jiki a sanyaye ta koma ta shiga ciki, saidai me? Zaman namiji da mace ne, ga mai aure da matarsa, marar aure kuwa budurwarsa. Intisar ana k'ame gefen Haidar, hakanan su Jidda, ta yi shiru ta kasa karasawa ciki dole ta juya da zummar fita saidai ta ji an riko hannunta. Da sauri ta dago kanta, Faruk ne saidai fuskarnan tasa babu digon walwala ya ja hannunta zuwa ciki, ta kasa cewa uffan ga uban tsoro da ya cikata kamar ta saki fitsari a wando, ya dan saki fuska gudun kada a dagosu, itama ganin haka ta saki nata. Haka suka karasa mazauninsu kusa da su Ridwan. "Madam daga nan sai Asibiti ko?" Cewar Ridwan cikin zolaya. Murmushi kawai ta yi. "Kema dai Ummi, ai da kin hakura kin zauna gida." Fadila wacce ta sauko yanzu ta fada da murmushi saman fuskarta. "Ina zata zauna wata ta yi mata kwace? Da gaskiyarta ai." Haidar ya fada yana yar dariya, hakan yasa Ummi fadada fara'arta wanda duk yak'e ne ganin gogannata bai wani sakarmata ba, sai murmushi da ya ke wanda ya zamto yak'e. "Au Madam ashe kinga ogannaki ina can ina nemanki naga kamar ba ki shigo ba." Suka tsinci muryar Kb daga gefe, ta yi yar dariyar yak'e tana fargabar abinda zai biyo bayan amsawarta. "Um, na shigo yanzu." "Yauwa." Daga haka ya maida akalar hirar da Haidar dake tambayarsa ko da wa zai zauna. Ya nunamishi wata cikin kawayen Ihsan wacce a ganin farko ta kwantamishi. Can kuwa Gidado na tare da Ikram kamar su hadiye juna don so. Party ne na yan boko, komai bisa tsari aka yishi, ba'ayi wani raye-raye sosai ba, sai ko (step-dance) da dangin Ango Abdullatif suka shirya suka yi wanda ya k'ayatar sosai. Anci an sha, an kuma yiwa Angwaye da Amare lik'i kwarai. Kafin akai ga tashi ta soma buga uban hamma don ta gaji ga bacci dake cinta, ta dubi Faruk da hankali kwance ya ke kur6ar lemu abinsa, lokacin su kadai ne saman tebur su Babban Yaya da sauransu an tafi daukar hoto. "FAR HAS na gaji wallahi bacci nake ji." Ko kallo bata isheshi ba, kamar ba da shi ta ke magana ba haka ya nuna. Jikinta ya kara sanyi, ta lalubo hannunsa na dama ta matse cikin nata. "Don Allah ka yi hakuri na yi maka lai..." Kallon da ya watsamata ne yasa ta hadiye maganarta babu shiri, har lokacin hangota ya ke zaune kusa da Kb a mota. Ya zare hannunsa cikin nata. "Ai ba ni na kawoki ba, ki nemi wanda ya yi miki iznin zuwa da wanda ya kwasoki a motarsa har ku ke hira da dariya su yafi dacewa ki je su maidaki." Hawayen da ta ke rikewa suka zubo. "Amma Yaya Abubakar cemin ya yi ka amince." "Tunda shi ki ke aure ai ya miki izni kin zo, shikenan kuma, komawa kuma ni ba yanzu zan tafi ba sai na gama abinda ya kawoni." Daga haka ya mike ya soma tafiya a kasaitance, tafiya mai cike da aji, babu budurwa da bata kyasa ba, ya wuce gurin Angwaye, yana zuwa ya fiddo rafar yan dubu-dubu ya hau lik'i. Nan wuri ya chanja, kida ya chanja, Mai wak'a ya tambayi sunansa aka sanarmishi habawa tuni ya hau wak'eshi yana mishi kirari da yayan Amare kuma Abokin Angwaye. Ummi hawaye ta ke na bakinciki da tsananin kishin yanda yan mata ke faman zubamishi lik'i shima, ji ta ke kamar ta dora hannu akai ta kwara ihu, ga bakincikin fushin da ya ke da ita, ga kuma na kishin mijinta. Mamaki ta ke na yanda yau bai damu da zubar hawayenta ba. Mikewa ta yi jiki a sanyaye, ji ta yi fatin ya fice a ranta, ita kuwa ko tasi ne zata hau ya maidata gida da dai ta zauna ta shak'i wannan kayan takaici. Tana jinta wani iri, Faruk bai kamata ace ta bak'anta mishi rai haka ba, idan da alk'awari sam Faruk bai kyautu ta musgunawa zuciyarsa ba, ya cancanci komai daga gareta. Haka ta ke faman tunani har ta fito farfajiyar dakin taron. Nan kuma ta shiga rarraba idanu, to ina zata nufa? Waya ta ciro da zummar kiran Abubakar sai ta tuna abinda Faruk ya ce kawai ta fasa, ta maida wayar jaka ta soma tafiya tana fatan ganin direban gidan su Mami ko Hajiya Mama don ya maidata gida, saidai akwai mutane da motoci sosai babu damar gane hakan. Takalmin yana da tudu, ya isheta, hakan yasa ta zuwa daidai motar Haidar ta tsaya gamicireshi sannan ta soma kokarin dauka, saidai durkuso ya yi wuya agareta, ta kara kokarin durkusawa ta ji an rike kafadarta, a razane ta dubeshi, Faruk ne, ya durkusa ya dauki takalmin ya rike mata, kai tsaye ya wuce ya bude motarsa ya tayar, ya yo ribas ya saita kafin ya budemata gidan gaba. Sauke gilashin motar ya yi yana dubanta batare da ya ce uffan ba. Hawayenta suka zubo ta soma tafiya, ya kuramata idanu cike da tausayi, tabbas ya kula a gajiye ta ke, abinda ya gujemata kenan shine babban dalilinsa na dagewa kan ba zata zo ganin anyi kamu anyi yini duk tana faman zirga-zirga. Ta shigo ta zauna ta rufe kofar, ya soma ja a sannu-sannu har suka fita, saida ya hau titi kafin ya dan k'ara gudu. Ta dubeshi saidai ta kasa magana, a hankali ta soma kuka sosai harda sheshsheka, duk yanda yaso ya basar, ya kasa, dole ya sauka daga saman titi ya yi fakin a gefe. Dubanta ya yi na yan mintoci kafin ya soma magana cikin sanyin murya. "Meyafaru kuma?" Ta dan matso kadan ta dora kanta saman kafadarsa gami da rungume hannun gam. "Don Allah FAR HAS ka yafemin, na fito bada izninka ba kuma na yi abinda kishinka ya motsa, don Allah ka yi hakuri." Wani so da tsantsar tausayinta ya cikashi, shima yana cikin dakin taron ya dawo daga lik'i ya ga batanan hakan yasa shi fitowa a rude, karshe ya hangeta jikin mota. Ta ya ya zai iya fushi mai tsawo da Umminsa? Ya sanya hannunsa na hagu ya dafa kanta. "Kinmin laifi Ummina, saidai duk iyakar laifin da za kimin bazan iya rabuwa da ke ba saidai wata kaddarar da bana fatan ta rabamu idan har ba mutuwa dayanmu ya yi ba, ina kishinki Ummi musamman da Kb wanda ya kusan cin rabona." Ta dago kanta cikin marairaicewa ta ce. "To ka yi hakuri bazan k'ara ba." Murmushi ya yi ya ka karan hancinta. "Haka ake bada hakuri?" Ta yi murmushi. "A hanya muke fa." Ya share mata fuskar. "Muje ki huta, daman nasan bebina bazai jure wannan Dinner ba shiyasa na hana ki zo amman Abubakar ya nunamin ke yar uwarsa ce." Ya karashe da dariya, ta tayashi kawai. Haka ya cigaba da tafiya, ta koma kujerarta ya kwantar mata da kujerar kadan ta yi filo da hannunta tana dubansa yana tuk'i, a haka bacci ya yi awon gaba da ita don sosai ta ke jinsa. A waya Faruk ya sanarwa Abubakar sun taho Ummi ta gaji don ba wanda ya sani. Koda ya yi fakin, saida ya karemata kallo don ba don baccin ta ke ji ba da bai ci ace ta yi ba don tafiyar ba wata tafiya ce sosai ba. Ya shafi gefen fuskarta, hakan ya sanyata bude idanunta. Kyakkyawan murmushi ya jefeta da shi. "Mun iso." Ta mike, ya zagayo ya budemata, da taimakonsa ta zura takalmi ya rike fos dinta suka shiga ciki. A falon Mami duk an ragu babu kowa, wasu sun yi bacci, har daki ya kaita, nan ma yaran su Jidda ne duk sun yi bacci, ya dubeta. "Ko za ki dakin Fahad? Kinga nan ma a cike." Ta dubeshi ta girgiza kai. "Aa zan kwanta gefensu karka damu." Bai bar dakin ba saida ya tabbatar ta rage kayan jikinta ta chanja zuwa na bacci ta kwanta, ya sumbaci goshinta. "Goodnight." Ta lumshe idanu tana murmushi. "Kaima ka kwanta fa." "Aa, zan koma wajen budurwata." Ya fada a wasance, ta kai mishi bugu a kirji sukayi dariya. "Bakasan na ji haushin yanmatan nan masu yi maka lik'i ba ko?" Ya ja karan hancinta. "Na fiki kishi Madam, karki damu ke kadai zuciyata ke so da kauna. Oya kwanta." Ta muskutawa ya rufeta, sannan ya kashe musu fitila ya fice, Allah Ya taimakeshi babu wanda ya ganshi balle tsoffin su ce ya yi rashin ta ido....! Washegari da safe ya koma bakin aikinsa Abuja, a ranar aka kai Amaren biyu, Iklima da Hassana, ita kuwa Ihsan Adamawa zasu wuce washegari. Bayan Magriba Mami ta yi kiran Ihsan da Ummi zuwa sashen Abba ta rufe don samun damar yin maganar da ta ke so....! Kowaccensu ta yi shiru tana mamakin wannan kiran, Ummi zata zauna k'asa Mami ta nunamata kujera. "Zauna nan Ummi kada ki takura." Ba musu ta zauna kujerar da ke fuskantar Mamin hakanab Ihsan ta zauna gefenta saidai nesa da ita. Tsaf Mami na lura da yanda Ihsan ke faman cin magani, ta numfasa ranta babu dadi kafin ta soma magana. "Abinda yasa na nemi da na ganku bai wuce fahimtar irin rashin jituwar da ke tsakaninku ba har zuwa wannan lokacin da ya ci ace komai da ku ka sanyawa zuciyoyinku ya kau. Matsalar ba daga Ummu ta ke ba sai daga ke." Ta nuna Ihsan wacce ta kara tamke fuska. "Na lura kin sanyawa ranki kiyayya, muguwar kiyayya ta Ummi alhalin banga wani mugun abu da ta ta6a yi miki ba har ta cancanci hakan. Ihsan kina wasa da addininki, wannan ba d'abi'ar musulmin kwarai bane, ina mamakinki, ba ki da rik'o akan kowa sai akan Ummi, yarinyar da gatanan zan shaidi cewa takan yi kokari matuk'a wajen kulaki saidai ba za ki amsamata ba, ko sau daya ban ta6a ganin kin bita da kallon arziki ba. Anya kina son gamawa da duniya lafiya?" A razane Ihsan ta dubi mahaifiyarta har idanunta sun ciko da ruwan hawaye saidai ta kasa cewa uffan. Mami ta jinjina kai cikin tabbatarwa. "Hakika wannan hali ba inda zai kai ki a rayuwa, ke duk abinda ya faru bai zame miki ishara ba? Ni na haifeki, ni nasan halinki saidai ban ta6a saninki da nunawa mutum kiyayya ba sai akan Ummi." "Ni Mami me ta yimin da zan k'i ta?" Ta fada cikin rawar murya idanunta cike da ruwan hawaye. A fusace Mami ta ke dubanta, Ummi ta dubi Ihsan kadan saidai ba ta ce uffan ba ta maida kanta k'asa. "Shi nakeson a yau ki bude zuciyarki ki sanarmin, me Ummi ta yi miki ki ke k'in sakin jiki da ita kamar yanda sauran yan uwanki ke yi? Ko kinsan cewa nasha kamaki kin harararta? Fuskarki na nuni da tsantsar kiyayya gareta koyaushe. Annabinmu s.a.w ya hanemu da zurfafa kiyayya ga dan uwa musulmi. Abu hurayrah ya ruwaito Annabi SAW ya ce "Na rantse da wanda raina ke hannunsa mutum ba zai shiga aljanna ba har sai ya mika wuya, sannan ba zaka mika wuya ba har sai kunso junanku. Ku yaɗa alkhairi zaku so junanku. Sannan ku guji kiyayya don kaifi gare ta, bance yana aske gashi ba amma yana aske addini." Wannan kadai bai isheki hujjar da za ki yi watsi da makamanki ki rik'i Ummi yar uwa ba? Mami ta cigaba da magana, ta inda ta shiga ba tanan ta ke fita ba har yanda ta fusata ya tayarwa Ihsan da Ummi hankali, musamman ma Ihsan wacce ke son mahaifiyarta ta sosai, kokadan batason abinda zai 6ata ranta, kuka sosai ta ke yi, ta mike ta nufi wajenta ta durkusa gami da riko hannunta. "Ki gafartamin Mami, wallahi na daina, zan riki Ummi duk yanda ki ke so, Ummi don Allah ki yafemin abubuwan da na aikata gareki, bazan k'ara ba in sha Allah." Ummi ta share hawayenta tana murmushi a hankali ta mike ta tako har wajen da suke, zama ta yi gami da riko hannayen Ihsan. "Ban ta6a rikeki a raina ba daidai da rana daya, na yafemiki tun kafin ki rok'a, karki damu, nima ki gafartamin idan akwai abinda na yi miki da bansani ba." Kunya ta rufe Ihsan, ta sauke kanta jiki a sanyaye. "Ba abinda kikamin, idan ma kin yi to na yafemiki duniya da lahira." Mami murmushi kawai ta ke yi, ko babu komai tana alfahari da Ihsan a fagen jin maganarta, da wuya ta sa6a umarninta. Ta riko hannuwansu ta sanya cikin na juna. "Allah Ya muku albarka, Ya kara hada kanku." Ummi da Ihsan suka dubi juna suka yi murmushi alokacin da suka amsa da amin. Tun daga wannan lokacin, suka dinke, idan ana zaune ana hira, Ihsan ta daina barin wajen idan ta ga Ummi, har takan tsokani Ummi cewa ita fa yayarta ce yanzu. Ummi dariya ta yi saboda rashin sabo da hakan daga gareta. Su Intisar gaba daya sunyi mamaki. "Ko kefa." Cewar Aisha yayar Ihsan a saitin kunnenta, ta dubeta kawai suka yi murmushi. Hatta Amina, saida Ummi ta kira a wayar ta sanarmata batun shirinsu don ranar yini kawai ta zo wanda shima Bellon dakyar ya amince don acewarsa bai isa ace ta soma fita ba. Babu wanda bai yi murna da shirin Ihsan da Ummi ba. "Wallahi kinsan me Ikram? Yanzu jin zuciyata nake wasai babu ko digon damuwa, ashe kiyayya babu dadi? Ni sai yanzu ma na ke kara fahimtar Ummi mutum ce, halayenta abin so da sha'awa." Abinda Ihsan ta fadawa Ikram kenan sadda suka shigo falon Mami bayan ta raka Ihsan din wajen mijinta da ya bukaci ganinta. Ikram murmushi ta yi. "Kwata-kwata gaba bata yi ba ai, Allah Ya k'ara nisantamu daga shaidan." "Amin." Washegari aka yi shirin tafiya Adamawa tun karfe takwas na safiya, Ihsan nan ta shiga kuka sosai dakyar aka 6an6areta daga jikin Maminta, nan kuma ta kama hannun Fahad gam ta rike, shi kansa kuka ya ke kasancewar sun shaku da ita. "Ya kamata ki samarwa Fahad k'ani." Mami ta tuno furucin Mijinta a daren jiya, kwarai da zata kara haihuwa tasan ba karamin dadi zaiji ba, saidai kuma likita ya tabbatar mata cewa tsarin iyali na shan magunguna da ta yi ya janyomata matsala a mahaifa, abu ne mai wuya ta kara haihuwa sai ikon Allah, ya yi mata wannan bayanin ne sadda ta ga 6atan watanta kwanakin baya da har Hajiya Mama ta shawarceta da zuwa ganin likita ko ciki ne da ita. Kwarai ta yi da na sanin yin tsarin iyali musamman ma da ya kasance ba da iznin mijinta ba. Haka kukanta ya kasance biyu, da jimamin rabuwa da diyarta wacce kusan tafi kaunarta duk a yarannata idan an cire Adnan wanda Abban ke so sosai, sun shaku da ita yau ga aure ya raba. Aka wuce gaba daya har su Hajiya Babba, Ummi kuwa a ranar suka wuce da su Jidda zuwa Abuja. *** *** *** A farkon zamantakewar Ihsan da Badiyya, sun sami matsala na kishi, saidai da ikon Allah komai ya zo ya wuce suke zamansu lafiya, ga Abubakar ya na takatsantsan sosai don ya rage kula yanmata musamman da ya ke 6arje Angoncinsa, hakanan ya rage hira a waya a gaban matansa gudun 6atawa wata cikinsu, yanmatan ma duk sai ya ke ji suna ba shi haushi, watan Ihsan biyu a gidan, ta samu ciki, murna wajen iyayen Abubakar ba a magana, shi kansa har kuka ya yi don tsananin farinciki. Ya zamana hankalinsa kacokam ya koma ga kula da Ihsan, Badiyya ta shiga tashin hankali matuka saidai ta yi jarumtar 6oyewa bata nuna ba. Da ita aka hadu aka yi ta kula da Ihsan. Ummi cikinta ya shiga tara cif, a wannan lokacin sosai an soma shirye-shiryen bikin Ikram da Gidado, bata fita ko'ina banda asibiti, wataran kuwa ya kwasheta ya kaita gidan Hajiya ta wuni, komai ba bukatar mace da danta na haihuwa Faruk ya siya ya ajiye, haka itama kamar yanda aka Jidda ta yi mata bayani, ta sanya dukkan abin bukata na ranar farko ga macen da ta haihu cikin karamin akwati. Bata da aiki sai adduoi, da kallon kayan bebi, yau ma tana zaune saman gado ta bararraje tana kallon kayan jariran da Faruk ya siyo duk kuwa da cewar dauriya ce ta ke yi sakamakon mararta dake dan murdawa, Batula na aikin jera wasu cikin 'yar kwaba na saka kayan yara da Faruk ya siyo. Ta juyo gami da sakin murmushi "Kai Anti, kullum idan Yaya ya siyo kaya sai kinyi zaman kallonsu." Ummi ta numfasa tana dariya. "Bari kawai Batula, wallahi idan ina kallon kayan sai na ji son bebi na k'ara shiga raina ne, yanzun ma ba ki ji yanda na ke ji ba, Allah dai Ya rabamu lafiya." "Amin Anti." Fadin Batula cikin dariya. Suka kammala hada komai suka maida duk Batula ce karfin aikin, ta mike saman gadon. "Bari na kwanta ko ciwon marar nan zai yi sauki, inajinsa kadan-kadan." STORY CONTINUES BELOW "Sannu Anti, ko za ki sanarwa Yaya?" Ummi ta girgiza kai tana dan yamutse fuska. "Kayya, barshi, nasan yanzu yana tare da su Hajiya, in sha Allah idan na samu na dan runtsa zai bari." Ta gyada kai. "Allah Ya baki lafiya." Ta lumshe idanu tana mai amsawa, bayan fitar Batula daga bacci ya dan fisgeta sai ciwo ya motsa ta farka, lokacin karfe biyar na yamma, can dai ta ji ciwo ya motsa babu kakkautawa, firgigit ta mike zaune tana ambaton sunan Allah gami da rike cikin. Ta kasa jurewa ta sauko kasa bayan ta dafe gadon da hannunta na dama. "Wayyo Allah." Ya yi daidai da shigowar kiran Faruk wanda ta sanyawa sauti na daban, ta daure ta kai hannu saman dirowarta ta dauka gami da sanyawa a kunnenta. "Ummina kina lafiya?" "FAR HAS zan mutu..." Ta fada cikin rawar murya wacce ke nuni da jigata. "What?! Nakudar ce?!!!" Ina! Tuni ta ajiye wayar sakamakon murdawar da cikinta ya k'ara yi. A wannan yanayin Batula ta iso domin ta lek'ata ko ta samu baccin, gaba daya ta diririce ta hau salati, ganin yanda Ummin ta ke ba'a hayyaci ba kawai sai ta soma kuka don ta rasa taimakon da zata bata. Dabarar kiran direba ne ya fadomata, a guje ta fita tana kiransa. "Malam Musa! Malam Musa!!" Da sauri suka shigo gidan har maigadi kasancewar suna waje saman benci suna hira. "Lafiya?" Suka fada har suna rige-rige. Ta nuna hanyar gidan dakyar ta iya magana. "Anti..Anti zata mutu." Ai da gudu suka nufi ciki, saidai kafin su karasa ciki suka ji ana doka mahaukacin hon, da gudu kuma suka fito, har suka ci karo da Faruk wanda ya bar motar waje ya shigo Hajiya Babba da Dakta na mara mishi baya. Suna shiga suka tarar tana ta fama, da sauri ya riketa. "Sannu Ummina." Ya dauketa cak ya nufi waje, lokacin har maigadi ya bude kofar. Suka sanyata a mota sai asibiti. Shima Haidar wanda isowarsa kenan tare da Intisar suma har da su a gidan sadda Ummi suka yi waya da Faruk, suka bi bayansu zuwa asibitin. Dakta Ridwan wanda tun a mota ya yi kiran wayar abokiyar aikinsa Dakta Farha, ita ta kar6i Ummi suka shiga dakin haihuwa. Suna nan tsaye suna faman adduoi, Faruk ya kasa mance furucinta na ambaton mutuwa da ta yi gareshi, ya runtse idanu ya budesu, tuni suka kada zuwa ja. Hajiya ta umarci Intisar da ta koma ta dauko akwatin Ummi na kayan haihuwa, Haidar ne ya jata suka koma. Mintuna talatin da shigar da Ummi, lokacin an soma kiraye-kirayen sallar Magriba har Intisar sun dawo, kukan jariri ya cika kunnuwansu, suna cikin wannan farin cikin, suka kara jin wani kukan. Fitowar Dakta Farha ne yasa su maida hankali gareta. "Alhamdulillah, ta sauka lafiya ta haifi...." Sai kuma ta sanya dariya lokacin da ta kar6i akwatin kaya tana mai mikawa nos din gefenta dake dariya, nos din ta yi ciki. Su kuwa duk sun k'agu da son jin abinda zai fito bakinta. "Me ta haifa?" Cewar Haidar. Dakta Ridwan wanda ya riga yasan manufarta ya sanya hannu cikin aljihu ya fiddo dari biyar ya mik'amata yana dariya. "Ga abinda ki ke jira." Ta kar6a suka yi dariya, Faruk ji ya ke kamar ya tura kansa dakin. "Na kar6a amman ya yi kadan kaima ka sani, ta samu twins mace da namiji." Ai Haidar da Faruk tuni suka rungume juna suna dariya, Hajiya murmushi kawai ta ke yi tsabar farinciki ta rasa inda zata saka ranta, wai Sadaukinta ne da d'a, har biyu ma, kyautar Allah. Hawayen farinciki ya tahomata ta yi saurin daukewa da hannu. "Dakta jikin Ummi fa?" Cewar Faruk. "Alhamdulillah, babu wata matsala." Ta koma ciki, nan fa suka shiga kiran abokan arziki suna sanarmusu. Ihsan saida ta ji kamar ta budi ido ta ganta a Abuja tsabar murna don yanzu sosai su ke dasawa da Ummi saika rantse wani abu bai ta6a giftawa tsakaninsu ba. Bayan an gama gyara yaran wadanda sak kamannin mahaifinsu suka dauko, aka miko musu. "Masha Allah." Cewar Dakta Ridwan wanda ke rike da macen yayinda Haidar ya matsa ga Hajiya yana kallon namijin. Faruk ya kuramusu idanu yana kallo cike da sha'awa da tsananin so da kauna, burinsa ya yi tozali da Umminsa wacce ta haifa mishi wadannan kyawawan halittar abin so da kauna. Koda suka shiga, kasa daga idanu ta yi ta dubesu haka kawai ta ji tana kunya musamman ma ganin har Hajiya Babba aka zo. "Madam sannu, kin kawowa Hajiya miji, Daddy kuma mata ko?" Cewar Haidar, akayi dariya. Faruk dake rungume da macen ya saci kallon Ummi saidai bata ko kallo inda ya ke ba, murmushi ya yi yana ji kamar ya hadasu duka ya rungumesu. Ko awa uku ba'a cika ba, su Baraka da Jidda duk aka iso har babban Yaya. Haka suka cika daki mai lamba hudu wanda aka bawa Ummi don ta huta. Faruk da kansa ya kira Gombe ya sanarwa Malam Balarabe da Gidado, wannan abu ba karamin dadi ya yi musu ba. Dada ta hau shirin tahowa Abuja don daman ta ce ita da zuwa Abuja sai idan Ummi ta haihu. Ana gobe suna yan uwa duk suka zo har mutan Kano da Gombe, Amina ta so zuwa saidai babu dama don ita kanta tana fama da jikinta, Binta itama ta yi farinciki sosai don itama ga kusa aure lokacin. Yara suka ci suna Afra da Afreen, da yawa tsoffin suka kasa maimaitawa. "Dan nema, za ka zo ka sameni, idan ba mugunta ba mene na saka sunan da bamu iya fad'i ba sai kace sunan aljanu?" Cewar Hajja kenan lokacin da sukayi waya da Faruk, banda dariya, babu abinda Faruk ya yi. A karshe suka gaisa da Modibbo wanda ke kwance ba lafiya har lokacin. Dakyar ya amsa wayar kafin su yi sallama. Sati biyu da haihuwar Ummi, Dada ce awajenta tana kula da ita, alokacin ne kuma aka soma bikin Ikram da Gidado wanda babu abinda Ummi ta halarta a ciki bisa umarnin Faruk, acewarsa yaushe ma ta haihu da zata soma fita? Haka aka yi biki aka k'are, Ihsan itama ta zo daga Adamawa anan gidan Ummi ta yada zango, sosai Ummi ta ji dadi, tsakanin Ihsan da Faruk zumunci na yan uwantaka ke wanzuwa ba kamar a baya ba da ya ke daddauremata, hatta Badiyya kishiyarta ta zo wannan karon. Haka aka kammala bikin Ikram aka mik'ata Jar Kwami, gidan da Gidado ya gyarashi kaika rantse cikin birnin Gombe ne don daman ko kadan basu da matsalar wutar nema. To me zai dameta tana tare da masoyinta? Bayan Ummi ta yi arba'in babu inda kafarta bai taka ba itace har Gombe, a wannan lokacin ne kuma Faruk ya biyamusu Umarah, har hawaye ta yi don tsabar farinciki. *** *** *** BAYAN SHEKARU UKU DAN ADAM STORY CONTINUES BELOW Mace mai shekaru ashirin da daya mai tsohon ciki na hango sanye cikin kananun kaya riga iyakar gwuiwa da dogon wando, kanta nade da mayafi tana bin wani kyakkyawan yaro wanda ya ci riga marar hannu da wando karami na shan iska, yana gudu yana dariya rike da 'yartsana tana binsa da tsinken tsintsiyar kwakwa. Wata kyakkyawar yarinya da aka nade gashinta da ribbon tana biye da ita tana murza idanu baki a ta6e lamun kuka ta yi. "Afreen! Afreen! Ba zaka tsaya ba wai?" Saidai kamar k'ara tunzurashi ta ke ya hau zagaye falon, a haka Uban ya fito daga sashensa yana dubansu, ganinsa yasa Afreen rugawa gareshi ya rungume kafafunsa. "Papa kaga Maama pho?" Ya fada cikin gur6atacciyar hausarsa. Daidai lokacin da ta karaso a fusace ta daga zata kai mishi bugu, Faruk ya rike hannunta. Ta dubeshi tana huci. "Allah kuwa FAR HAS karka hanani, tun dazu ya ke ta sanya yarinyarnan kuka don ya ga bata da hayaniya duk ya bi ya takura rayuwarta. Bata yartsanarta tun kan na 6ata ranka." Murmushi Faruk ya yi ya daga Afreen cak ya sanya a kafadarsa suna dariya. Ganin haka yasa Ummi ta k'ulu, ta yi kwafa gami da jan hannun Afra su wuce. Faruk ya riko kunnen Afreen har saida ya saki yar kara da dariya. Yaron ba dai wayo ba. "Bigboy meyasa ka ke takurawa Bebina ne? Duk maganar da zanyi ba ka ji ko? Zamu 6ata fa." "Na daina Papa, ka yi hakuli." Ya ja kumatunsa kasancewar Afreen tubarkallah akwai k'iba don har yafi Afra jiki. "Oya muje ka bata hakuri." Suka nufi wajen Ummi wacce ta dannowa Afra game a wayarta ta mik'amata. Ko kallonsu bata yi ba, Faruk ya sauke Afreen, ai kuwa daman jira ya ke a guje ya je ya mikawa Afra 'yartsanarta kafin ya soma raba idanu yana kallon wayar Ummin don a rayuwarsa yana son ya ganshi yana danne-dannen waya duk kuwa da cewar ba iyawa ya yi ba. Abin yaso bawa Ummi dariya sanin halin dannata saidai ta danne. Ya dubeta kamar wanda ya yiwa Sarki k'arya. Faruk ya na dariya ya dan sanya yatsa cikin kunnen Ummi ta yi saurin tarewa tana dariya. Bayan sun tsagaita ya ce. "Kinsan fa abinda dannaki ke so ki ke mishi yanga ko?" Ta dan tsuke baki. "Allah kuwa shine abin ban haushi." "Na daina Maama, ki yi hakuri." Ya fada yana mai dafa kafafunta. "Please Ummina ki yi hakuri bazai k'ara ba ko?" Ta yi murmushi kafin ta rungume dannata ta sumbaci goshinsa. "Is ok my son, Maama ta hakura." Ya hau tsalle sannan ya dane cinyarta har ta danyi k'ara sakamakon dan bugun cikinta da ya yi, da sauri Faruk ya dagashi cak. "Afra, tashi ku je dakin Maama ku yi game din amma banda danne-danne kunji?" "Toh." A guje suka mike suka yi dakin, ya janyota jikinsa ta kwanta saman kafadarsa. "Ina sonki Ummina." Ta lumshe idanu tana murmushi, shekarunsu uku da aure amman har gobe tana jin kalmar nan tamkar sabuwa fil a kunne da gangar jikinta. "Kasan me FAR HAS?" Shima idanunsa lumshe ya amsa. "Sai kin fada Ummina." Ta kara rungume hannunsa. "Inajin dadi aduk sadda ka cemin I love you." Ya yi yar dariya. "Zanyita ce miki har sai zuwa komawarmu ga Allah, ki tayani addua, Allah Ya bani ikon farantamiki har karshen rayuwata." Ta dago ta dubeshi shima ita ya ke kallo har suna shakar numfashin juna, kai ta girgiza gami da shafar gefen fuskarsa. "Ni kuwa menene ba ka yimin ba ma a yanzun FAR HAS, ka nunawa duniya cewa nima ina cikin yan Adam masu girma da daraja, ka yimin dukkan wani abu na rayuwa, ka barni na samu karatu har gashinan zan zana jarabawar wucewa jami'a, me zanyi gareka banda addua da kyautatamaka. Ni nake ganin ma kamar banyi maka wani abu ba..." Ya girgizamata kai cike da jin shaukin sonta da kauna. "Ke ki ka yimin kuwa Ummina, tunda har ki ka amince da aurena ki ka zauna da ni bisa amana har kika haifamin Afreen da Afra kin biyani Ummina, ga kuma bebina mai zuwa nan gaba,( ya shafi cikinta), kinmin komai kina bin umarnina kina nunamin kauna ta hakika, ai kuwa kin biyani." Ta yi murmushi, wayar Faruk ta yi kara ya daga, Abubakar ke sanarmishi haihuwar Ihsan haihuwa ta biyu, farinciki ya cikashi don daman yaronta na fari Badiyya abokiyar zamanta ta barwa wacce itama cikin ikon Allah yanzun ta ke dauke da juna biyu. Ummi kanta ta yi farinciki don takanas ta kira Ihsan suka shiga hira kafin Abubakar ya kar6e wai ta takurawa matarsa daga haihuwa, don yanzu Abubakar ya nutsu sosai ya bar dukkan mugun dabi'u cikin nufin Allah. Faruk ya mike gami da miko mata hannunsa, ta dubeshi ya kashemata ido daya. Ta bishi da murmushin da ya fi so daga gareta, kafin ta sanya hannunta cikinnasa suka nufi sashensa....!!!! Tammat Bi Hamdullah...!!! Godiya da Yabo sun tabbata ga Ubangijina da Yaban ikon rubuto muku labarin DAN ADAM, tsira da amincinSa su tabbata ga Annabi sallalahu alaihi wasallam.

Post a Comment for "DAN ADAM CHAPTER 37 KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...