[Advertisements⬇️]

AHUMAGGAH CHAPTER 4 - Bankinhausanovels
Mon. Sep 26th, 2022

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

AHUMAGGAH CHAPTER 4

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Bayan sun sallame ni sai na fita dayan site din,Ina tare da ummah Adama har bansan tafiyar shahrul ba.+ Sadaat kam dadin shi yake taji don gani yake kamar tunda khal ya min tsawa agaban abokin sa yanzu kam ai zan fara jin haushin sa Shikuma sai ya samu damar ganina.2 Dan haka ne ma ya kafa hujja da abun d ya faru sai ya dada zuga subaya da cewa shi bawai ya damu dani ba shidai baya son abunda khaldun yake min ne. “Cewar sa Ya za’ayi ina matsayin sister sa kuma ya maida ni mai aikin sa. Subaya dai batace uffan ba dan ta rasa gane musu dukan su. Ni kuwa tuni na warwashe na cigaba da yadda nake yi ma khaldun har ma na mance da wani fushi da nakeyi dashi. Kafin zagowar kwana biyu agidan Nikaina nasan Time dina na khaldun ne him and him alone! Yanzu ko big sis bana cika takura mata bare jahaan da ba shiga tsabgar mu take yi ba. She alwys believe we are good dan in ma munje gaisuwa babu mai nuna mata wani abu musamman ma ni. Hakan dana keyi kuwa ya bada sadat,subaya har da khaldun din ma mamaki with happen that day duk sun dauka zan dan nuna fushi na amma kuma banyi hakan ba.. Ranar sadat yaga bazai iya ba,ina saukowa daga step na ganshi a main falo yana kallo sai na gaishe shi ba yabo ba fallasa Ya amsa tare da dada gyara zaman sa yana kallo na Where are you heading to? A takaice Nace store! Store?a Cikin daren nan ?are u insane ya kure ni da ido kamar he cares for my safety,to ko miye zakije yi kibarshi Let me call the maid,sounding carefree ya fada Nikuwa Dan shiru nayi kafin na furta khaldun yace na kawo masa mango juice kuma na duba babu fresh stock a kitchen store dinsa ina so na duba ne Sai yamin kallon irin ai dama ya sani ko yaushe dai khaldun ne sai ya dan tabe baki bai tanka ba dan Kokarin tashi yayi zai kira maid nayi sauri nace noo sir…thank you sir kar ka damu ai Aiki na ne,and no one is allow up there ..,khaldun zaiyi fada in wata ta je,. Its an oder.. Cikin wani kallon mamaki mai nuna baya jin dadin abunda yake ji abaki na Yace wai dama ke kadaice kike serving dinsa babu wanda yake masa wani abu sai ke? Nace eh,Ba yabo ba fallasa Na gyada mashi kai cike da matsuwa nace zan tafi.. i will just go now Yace hmmm ok,ni dai bance komai ba dai nayi yake zan wuce wuf sai naga ogan ya taso kusa dani babu kunya har kaman zai shaki numfashi na “tsaya, yace yana dada kare min kallo,wani miskillin murmushin dayake sake mun sai da na sauke kaina kasa bazata na dan kau da kai. Yace emm na tuna da wani abu,and it can help you atleast tunda kince ogan naki baya bukatar na kowa sai naki. Amma ni nace dole na taimaka miki sai yayi smiles. ki tsaya anan bari naje ciki na dawo akwai wani mango juice dana sha dazu na kwalba ne but its taste fresh too u can use it ai ko?1 Banso ba amma To avoid his looks and annoying smiles sai nace ok Nan ya shiga wani wajen after like 10 minutes ya taho da mangoe juice a gwalba ya damka min.. Godiya nayi masa bayabo ba fallasa na wuce sama, ya bata min lokaci na dan haka ban tsaya sake duba juice din ba na yi aranging akan tray na fito . A lokacin karfe 9 na dare ya wuce kusan kowa ya shiga turakan sa. Ina bude door na samu khaldun na kan waya sai na shiga zuba mashi drink din a glass cup na mika mashi a hannu1 Shi kuwa baima dube ni ba ina bashi yakai bakin sa ya hau kurba kamar maijin kishin ruwa. Ina daga gefe Me zan gani?a kurba na uku Sai juice din ya dan shake sa har yayi dan gyaran murya Chan kuma sai naga Tari ya farayi kadan kadan daga haka har abun ya dan mike tari bai sake shi ba, kawai Sai ya sake kurban juice din ya aje sauran akan table shi ya koma kan kujeran sa yadan jingina kai kadan Daga nan Shikenan ban sake gane ma khaldun ba… Wani irin tari mai kara ya shiga yi Tsaban tarin daya keyin ma saida ya kashe wayar daya keyi gaba daya ya dafe kirjin sa da tafin hannun sa1 A Take idanun sa suka fara sauya kala suna neman taro ruwa Ina ta kallon shi har zuciya na Gaba daya sai da naji na rude sosai ” sannu, na furta a hankali ina matsowa kusa da shi slowly amma ina jin tsoron kai hannuna jikin sa. Kansa ya lafar akan chair yana dan nishi alaman yana neman tsayar da tarin amma ina abun sosai yaci tura. Dana ga dai bazan iya ba So I guickly grab the glass cup na sake zuba mashi juice din dan yasha ko zaiji sauki,but ina mika mashi sai naga ya riko harda hannu na Gwanin tausayi yana min alaman bazai sha ba. Baki a sake nake binshi da kallon damuwa nikadai na san yadda Hankali na ya tashi sosai,bansan meyasa ba amma bana kaunar ganin sa a wani hali irin wannan Saukar ruwa mai taste din ،Gishiri akan lips dina yasanar da ni cewa hawayen tausayin sa nakeyi Daya ci gaba da tarin A dame na tsuguna kusa dashi na aje hannuna daf na dafa arm din chair din nashi kanshi ya ke kokarin hadewa da gwiwa yana kan tarin ko magana ya kasa fita masa Sannu nake mashi har na dada tsugunawa daf dashi ina bashi baki har ya kwanta akan kafar sa dan shiru ne ya so ya ratsa wajen kafin wani tarin ya kuma taso mashi with full force..,slowly nayi mastering courage na sa hannu a gadon bayan sa na shiga petting dinsa ina shafa shi sosai har tarin ya tsagaita mashi. Nishi yake sauke min, Wani shiru ne ya ratsa wajen sai chan dai ya motsa alaman zai dago kansa sai na mike tsaye a dan tsorace ina kallon shi cike da damuwa Idanun sa yayi luii Ya dan kalle ni ya kalle juice din..cikin sanyin muryan da ban taba ji yayi min magana da shi ba yace me kika sa aciki?Did you really wanna kill me?u hate me ko? Cikin tsananin tsoro da fargaba Na girgiza masa kai hawaye take suka sauko min dan bana jin dadin yadda yake magana. Bai kula ni ba yayi Kokarin tashi tsaye sai tarin ya sake dawo mishi sai ya koma ya dada zama Har na yunkuro a dame zan taho wajen sa ya tsayar dani da wani irin kallo alama kawai yamin da hannu akan na dauke juice dina na tafi na bashi waje Zuciya ta kamar zatayi amon wuta,I was soo scared and worried a lokaci guda dan bansan ya akayi na dauke sauran juice din daya sha nima nakai baki na na shanye ba.. Wasu zafafan hawayen son shi ne suka gangaro min3 Ina aje cup din ya dago idanun shi Cike da tsananin mamaki sai ya tsaya kallo na Me kika yi? “sautin murya na mai dauke da damuwa nace.i neva wanted to kill you sir…”Ni bansa maka komai aciki ba.. Dama babu stock din ne a kitchen dinka sai na dauko a kasa,ban..ban san meya faru ba but pls dont take it personal sir …na furta cikin rawan murya. Ajiyan zuciya yayi yace hmmm Shi mamaki ma nake bashi,har ya bude baki zai ce na fita sai nima na fara tari. Abu kamar wasa inayi ina kauce idanun sa akaina sai gashi na fara tarin slowly yana karuwa har yazo min kamar kaina zai bude Da shike ni mace ce abun sai ya so y yi min worst fiye da nashi kaina na rike hannu na rike da standing pillar… Shidai Yana zaune yana kallo na har na rusuna kasa rike da kirjina,alokacin da Hawaye suke cike da ido na muka hade ido dashi, cikin sanyin murya nace pls im sorry kayi hakuri ….i dint know…i..i..sai maganan ya ki fita Kokuwa ma na shigayi da numfashi na ina gasping iska ko danyi numfashi da kyau amma kuma nakasa Shikam Bayan mamakin dana ke bashi har Tausayi na sai da ya shige shi,Daga nan Bansan daga ina ba kawai sa naji mutum ya zube ajiki na.. Tallafo ni yayai jikin sa cikin rudewa yana tapping fuska ta da palms din sa yace why did you take it?Ni sa’ar kine da zanyi abu kema kice zakiyi?wai mesa baki da wayo tambayr ki kawai nayi Ni bance nayi fushi dake ba. Dada riko ni yayi a dame gashi yana da kawaici dan haka ya kasa dora hannun sa akan akirjina kai tsaye,see how ure suffering now,wai meyasa kika sha?ya rike ni dam dam amma ya ke furta i knew u wudnt hurt me comn get up and go…1 Nikam Babu bakin amsa shi Sai uban gurnanin nishi na mai nauyi daya ke fitowa yana dada gauraye wajen kirji na na bugu ina nunfashi very slow kamar mai zazzabi mai zafi. Heyy….hey look at me,naji shidai yana dada matsowa amma karshen maganan sa danaji kenan numfashi na sai ya dauke mai gaba daya. Jin bana motsin ya riko ni sosai ya manne ni da kirjin sa kamar mai shirin maida ni cikin sa.. Baya na yake ta shafawa a hankali da duka iyawar sa har baisan iya lokacin daya dauka yana hakan ba Dana dan motsa sai ya dago da ni Wanni irin piecing Look ya bi surar fuska ta da shi for some seconds bai kiftawa,.. sanyin iskan bakin sa ya shiga hurawa akan kwantaciyar halittar suman gaban goshi na da suka kwanta sukayi luguf sabida zufan da ya fetso min a bazata. Gashi har na riko rigar shi agajiye duk na cukuikiya shi,Ji yayi hankalin sa ya tashi,wani tattausan kallo yabi closed eyes dina da dashi a tsanake ya dada tallafo ni yana mai furta “..BAHIYYAH are you alright? …baiji na amsa ba sai ya dada jawoni ya shimfida ni a kirjin sa yana shafa gadon baya na wai ko zan farka na mishi magana,ina dan jinsa kam But Still banda karfin yin hakan,sai nashiga nishi kadan kadan dan hankalin sa ya kwanta Daya lura da hakan sai ya dago ni a hannun sa muka mike tsaye tare ya lafar dani akan kafadar sa. Wayar sa ya dauka ya kira ya sa aka tambaya ma sa maid aka gaya masa inda daki na yake dan shi bai ma sanin inda nake kwana ba. Nikuwa sai layi nake yi ajikin sa ina narkewa kamar kar na tashi tsaban dadin dana keji.2 Daga ni chak yayi Daga nan Site dina ya nufa da ni ya bude dakin ya aje ni akan gado na. His room is 10 times better than mine amma sai daya yayi admiring tsarin sa aransa. Kusa da ni abakin gado na ya zauna Kallo na yake har cikin ransa yana jin tausayi na.. Wato dan na sha poison shine itamaa zata sha ko! This girl is soo anoying…yayi karamin tsaki idonshi yana dada observing tsiraran yatsun hannaye na har Ya riko yatsun nawa zuwa nashi yana massaging gently yana min tausa cike da kulawa,tun ina jin dadi har bacci mai nauyi ya dauke ni Shikuwa kallo na ya cigaba dayi dan Yau ne rana ta farko daya fara jin zai karbe ni arayuwar sa.1 Sai da ya shafi kusan minti 15 sannan ya shiga gyara min zaman pillow akaina yana kallon super cute face dina yana maganan zuci.. “I just have to accept you little angel ure now my family,pub kaman ya bata kalma sai yayi murmushi kadan yace ok my sister…so very innocent and I think you derseve it …Ya sauke ajiyan zuciya ya jawo bargo na mai laushi ya kuma Rufe ni3 Rage min wutar dakin yayi ya juya zai rufe min kofa aikuwa Yana sa kafar sa kofar dakina charaf suka hade ido da saadat da subaya dukan su suna masa wani irin mugun kallo. Dauke kansa yayi sannan ya ja kofar ya rufe bai ma sake kallon gefen su ba yayi yukuri zai wuce..+ Khaldun pls…stop Muryan subaya ya dakatar da shi A take ya jiyo bayabo ba fallasa ya kalle ta.. Dada matsowa tayi tana kallon shi “whats going on here?me kayi ma noor wat did you do to her? Bai amsa ba, wani kallon dai ya watsa mata dan ya lura Hankalin ta adan tashe yake data mashi tambayar Ita kuwa cike da kallon tuhuma ta sake maimaita tambayar nata wanda ya dada jefa shi cikin mamaki sai..Yace kamar yaya, What did i do? “Yessss! Sadaat ya saka baki yana cizan labban sa gwanin ban haushi Akace..mekayi mata?ko kana tunanin bangan ka bane… I saw you with her yanzun nan ka dauko ta a hannu kamar ma bata motsi ko?hmmm ai nagaya miki i bet Dukan ta yayi.. Jin hakan ya dada sa Hankalin subaya ya tashi althi tasan khaldun bai taba dukan mace a rayuwar sa ba. Tamkar marasa aikin yi haka ya dauke su gani yake ma baida lokacin su Wani kallon sama da kasa yayi ma sadat din batare da ya nuna alaman wani abu ya taba ransa ba ya juya musu baya dukan su witout saying a word ya sa kafa zai bar su a wajen. Arm din shi subaya tayi saurin rikewa Still muryan ta Cikin bacin rai tace khaldun!!!!,Zan fa hada ka da dad muddin bazaka gaya min komai ba,i want to know now ..i said What did you do to my sister bahiiyya..5 Sai Ya fincike hannun sa slowly ya hade ransa sosai,wani kallon rainin hankali ya bita dashi yana tabe baki looking so arrogant irin ko ajikin sa baisan me ma sukeyi ba. Hakan kuwa na dada basu haushi..a harzuke subaya ta riko hannun sa again tace Why don’t you just talk now?kafara irin shirun kan nan ko? kawai ni ka fada min yanzu kafin na shiga dakin nan na duba da kaina..khal what happen to bahi …her voice was seriuosly cracking kamar zata Yi masa kuka.. Sadat kuwa har wuya yake sai tsaki yake yi shikadai yana jinjina kai Wani Miskilin kallo ya mata na 2secnd Sai da ma ya gyara tsayuwan shi yana mai sakaya hannun shin a cikin aljihun sa kafin yaji aransa zai iya responding. “Aranshi Yana matukar kaunar subaya Amma ya kasa sanin dalilin daya sa bazai taba samun jituwa da halayen mijin ta ba Kuma Yasani sarai sadat yana pumpa ta da maganganu akansa and now she want to react sabida ta nuna tafi kowa sanin yadda yake treating din bahiyya… Wani Karamin boyayyen ajiyan zuciya ya sauke baice uffan ba sai ya dawo ya bude musu kofar dakin da bahiyyar take dukan su suka hango ta a lullube Peacefully tana baccin ta,bai kalle su ba amma tasan da ita kawai yake maganan sa Yace See?she is sleeping kuma ni bansan me kike cewa ba mmm..yanzu zan iya tafiya koko? Dan lumshe ido subaya tayi Tare da sauke ajiyan zuciya Ta Dan kalle shi cikin taushin murya tace toh me kakeyi anan din? I just hope she is alright,sai ta kalle fuskan bahiyyar duk bata jin dadi Khaldun baice uffan ba dan ya tsani raini,batasan duk abunda take fada yanzu ba wanda baya bata masa rai ba,yo shine zata sa agaba da titsiya kamar karamin yaron ta? wani Miskilin murmushi ne ya so ya kufce masa irin gani mugu inna shigo waje ba alheri ba ko. Aransa yace ba laifin ki bane sis nasan wannan shashan ne yake gurbata Miki tunani Amma zanyi maganin sa kwanan nan. Dan Hararar kasan ido ya bishi da shi “Very useless guy..ya furta cikin ransa Sai ya juya ya barsu anan. Subaya da sadat ne suka karasa Shiga dakin suka duba bahiyya,she look untouched har minshari take kamar ta jima akan gado tana bacci. sai abun baiyi ma sadat dadi ba yaso ace yau an kama khaldun da laifi mai karfi akan Bahiyya Sabida yanaso subaya ta daga hankali sosai ta Kai maganan wajen dad dinsu ko Dan araba ta da site dinsa na har abada. Sai gashi Babu wani prove har suka bar daki na ban farka ba… Sadat bai kuma cewa uffan ba har suka koma site din su,wanka ya fada yana mai sakar ma kansa ruwan shower mai karfi yana huci yana maganganu kamar zararre “Naso ace wawan nan ya fadi asalin meya faru akan juice din dana sa masa poison a gaban subaya, mswww but gosh he dindt. toh meya faru ne? ni ko kadan bangane komai ba Bloody bastard!! …Cike da huci mai zafi ya buga hannun shi akan shower wall yana maganan zuci sam ransa baiyi dadi ba.. A cikin dakin kuma Subaya ce akan vanity table tana lailaya jikin ta da night toners sai gashi ya fito daga wankan. Baiko kalleta ba ya cigaba da Tsantsame jikin sa don ayanzu tunanin yadda zai bullo da wani abun duk ya gama sha masa kai Har ta taso ta dafa shi ma bai sani ba. Darling?cikin sanyin murya ta kalle shi “Shikuwa hannun ta yadan sauke kadan yace..What is it?…ya kuma Dan jan tsaki a gajiye ya daure fuskan sa.. Dan shiru tayi kamar wanda tasha jinin jikin ta chan kafin tace Me yafaru ne sadat? Sai Naga kamar hankalin ka baya Nan. Yace Uhh really?I’m just thinking,kuma ma ya wuce dan bana son na cika miki shishhigi akan harkan dan uwanki. A dan dame subaya tace kamar yaya shishhigi? Shikuwa kamar jira yake Nan ya juyo with full attention ya kalle ta. ‘Subayah in fada miki gaskiya?,..Egon sa’ood yayi yawa..he is too full of himself infact He is senseless!1 Aranta Tace what? Shikuwa sai faman zuba yake1 Ko Gani yake kamar don yana comanding 4000 troops a filin yaki sai kowa ma sai ya zamto yana tsoron sa?ni din nan ma na girme shi amma kina ganin yadda yake raina ni,kawai bana son tsayar mashi ne sabida ni nasan darajar ki Ina son farin cikin ki,but Look babe Ya kamata kisa Ido sosai fa,nidai inajin tsoro ma yarinyar Nan bahiyya,i mean she is just a girl bai kamata azuba mashi ido yana cin zarafin ta haka ba ..1 Subaya kam ma bajin sauran bambamin san tayi ba Cike da jin haushin yadda ya zagi khaldun din ta numfasa fushin ta “Amma ai yace babu abunda ya mata and we saw her right?Sadat nasan Khaldun bai amince da ita ba tukun but I know he won’t lie to me Inda yayi mata wani abu da na tambaye shi dazun zai fada min pls try to understand him Khaldun fa kamar yadda ka dauke shi bane..i dont think zai taba iya dukan wata ya mace … So pls relax ka fahimce shi pls. Wani rau da ido sadat din yayi ya mata kallon sama sa kasa”Yeah,..ai dama nasan haka zakice ‘i shud try to understand this fool..sai ya mike tsaye ya harde hannun sa.. Look subaya,am a lawyer kuma nasan menake yi, in ke kin yarda dashi nikam ban yarda da shi ba..Something is wrong with him,tare dake fa muka gansa a bakin kofar dakin yarinyar yana rufe mata kofa has Eva been to that place? Wai Meyasa kike son boye laifin shi ne? Itama mikewa tsayen tayi ta kalle shi tace “Noo darling ba maganan boye laifi bane,dani da kai mun ganta lpyar ta lau..bai bari ma ta gama ba ya ce Toh Ya isah….Ohhh for godsake ki aje wannnan maganan agefe mana, sai yaya in mun ganta haka?does that mean baiyi mata komai ba.? Ai bacci takeyi ko!so how can you be soo sure cewa babu abun da ya faru? Tabe baki kawai subaya tayi tace …hmmm toh Sai ajira gobe ai aji daga bakin ta A zafafe ya mayar mata amsan “Nikuma Ina tabbatar miki da za kiji sabanin labarin daga wajen ta,domin ina da tabbacin khaldun din naki yayi ma yarinyar nan wani abu…kawai bazai fada miki ba. “Cike da damuwa subaya ta sauke ajiyan zuciya,tace ok, enough sadat khaldun is my brother and i realy trust him, Yakamata mu aje maganan nan haka ..shikenan,ni zan tambaye bahiyyan gobe…so Can we go to bed now? Tsaban haushin data bashi Wani tsaki mai sauti yaja kasar wuyan sa yace “im not in the mood..ya dada harde ransa Ya bude closet Yana kokarin jawo pjamas dinsa zai fice Sa murmushi tayi Cike da mamaki Tace Sadat ka sassauta haka pls dont take this too personal Sai ya tsare ta da hannu yana jefa mata mugayen yatsine yana bambami Ni kar ki ishe ni Naji ai Khaldun is your only Brother shi kadai ne yake da iko dake,sai kuma ki kirashi yanzu ku kwana tare am out. A hargitse ta dada dagowa cikin mamaki tana cewa meyayi zafi haka? Ko kula ta baiyi ba ma ya ja mata kofa aka barta tana kiran sa Sadat..darling.. sad…duk yanajin ta hakan bai kula ba ya bar site din mai gaba daya. Iya bayani tayi mashi amma Gaba daya daren yaki ya saurare ta She slept unhappy zuciyan ta cike da zimman warware wannan matsalan.1 Tasan Kuma hanya daya ne kawai zai jawo hakan shine intaji bayanin abunda ya kawo khaldun site din bahiyya a gobe And why was she uncounsious?.. Washe gari da safe ma Iya kokari sadat yayi dan ya nuna mata laifin khaldun amma dashike bata gani da idon ta ba so tana tsoron sake tuhumar khaldun kai tsaye batare da taji nashi fashin bakin ko na bahiyya ba *** Bangare na kuwa da safe ina farkawa na Shiga toilet a gurguje na dauro alwala nayi sallah Banmayi wanka ba a tsaban yadda naga time ya tafi so ban tsaya ko ina ba sai site din khaldun I started making his breakfast nomally araina ma ko tunanin abunda ya faru da ni jiya banayi. Bread halwa da south indian egg masala nayi sai dai na rasa wani irin juice zan hada masa,gaba daya cike nake da tsoro dan bansan asalin musababin abun da daya sa shi tarin a jiya ba. But i think That mango juice was poisoned ko hala yayi expire ne oho? Ni dai tunda na tashi naji ni garau sai bandamu ba.. But Dan na kaucar da irin wannan matsalan sai na tuno da wani recipe din smoothie wanda da hannu na ma zan iya yinsa ba sai nayi amfani da wani processed drink ba. Da sauri na bude fridge na fara dube duben ingredient din hada shin. Nan na dauko ayaba guda daya na saka a freexer na kara masa karfin sanyi don kuwa so nake ayaban yayi kankara sosai. Anan na fito da green matcha tea powder na debe kopi daya,na hado da ground flax seed rabin tea spoon da kopi guda na fresh almond milk. vanilla extract dina na gefe and finally sai na dauko cocunut na yi shredding dinsa yayi kyau na hade su waje guda cike da kwarewa na hada abunda ake kira “Cocunut matcha smoothie” Its soo yummy and pleasant to the eyes ga dan uban qamshin shi daya cika min hanci har bana jin qamshin sauran abunda na soya. Ko da naje ina shirya tray din jan dinning bansani ba ashe Tsaye yayi daga baya na yana ta kallo na Nasan dai Ya danji dama dama dayaga na warke but his face wasnt showing any emotion. Bansan yana baya na ba Dan haka da muka ido sai nayi saurin kau da idanuna cikin sanyin jiki hade da tuno duk abunda ya faru jiya tsakani na dashi,wani boye murmushi na nayi sannan nace ina kwana? Sama da kasa ya kalle ni,ko ya amsa ko bai amsa ba oho,dan ni dai banji ba. Zama yayi idanun sa na kan wayar sa yana latsawa. Nikuwa Cucunut macha Smothie din na fara serving dinsa a cup dan haka ya dauki cup din batare da wani tamtama ba ya shiga kurban abunsa. Abun ya matukar bani bani mamaki Does that mean khaldun sa’ood ya yarda dani?Ko dan yaga nima nasha drink din ne?Nidai Sosai naji dadi araina Toh har na juya plates kenan zan zuba mashi sauran abincin Sai naga ya dago fararen idanunshi Ya kalle ni sai ya kuma juyawa ya dubi seat din gefen sa “Sit…ya furta yana kure ni da wani makalallen kallon aji mai tafe da kasaitar data kafa tarihi araina. …tuni mamaki ya balbale ni don bansan ko naji abunda ya fada da kyau bane ko banji ba. But wait oo Did he just asked me to sit with him? Ai naji ance babu mai zama dashi anan sai jahan dan ko abokinsa shahrul dayaxo ma banga ya zauna da shi anan ba.1 Tsaye nayi ina murda hannu cikin rudani,ina dai so na tambaye shi dan nayi clarifyng Amma kuma nasan khaldun baiya maimaita magana so i just took the risk sai na matso kusa da shi na ja seat din na zauna a dan dofane. Shikam Baima sam inayi ba,Looking very calm yaa aje Cup din smothie akan table..ya kalle fuskata dake dan sunkuye. Da wani irin daddan husky voice dinsa Yace Serve!! Banma san lokacin da na dago ba. But Ganin tuni ya dauke kansa ya mayar kan wayar sai nima na shiga serving dinsa daga inda nake a xaunen Halwa bread din na fara ajewa kafin na bi da South indian egg masalan agefe Ganin yayi rabin smoothie dana sa yasa na kara zuba mashi wani shidai Baice min uffan ba har nagama. Daga nan Wayar sa naga ya aje agefe sai ya turo min plates din abincin gaba na. Tsoro yasa nayi rau rau da idanu na,..tunani na ko abunda nayi jiyan ne za ayi min hukunci..but i tot he has forgiven me, a take naji na shiga rudani ma fara tunanin ko dai bai yarda bane? Ban ko gama haukar tunani nan ba naga ya juya another plate ya aje agaban sa a cikin salon da banyi zato ba naga yana serving kanshi da kanshi.. Waje idanuna suka fito suna rau rau da kansu ina ta satan kallon shi baima san dani ba,duk mamakin shi ya kure min tunani barin ma Yadda naga salon daya zuba abincin a plate dinsa simplified and classic cikin iya tsara space tamkar tsohon wanda ya kwarance a aikin dafe dafe wanda ko ni nasan ban iya ba… Yana gamawa kuwa ya dada gyara zaman shi,Loma biyu yayi masu kyau kafin ya dago ya kalle ni,..fuskan sa adan daure Yace Eat”..arude nayi saurin cewa ok.. Hannu na tuni ya daga spoon da fork din amma ban iya komai da shi ba sai mu kaji sallama akan mu. Jahan ce da kanta ta shigo dan haka a take nayi yunkuri zan mike tsaye Ban ma lura da shigowar subaya da saddat ba sai da khaldun ya balla min wata hararar daya maida ni kan seat dina batare da niyya ba. Spoon da fork din na dauka idanuna a kasa na shiga juya abincin cikin fargaba Dukan su fuskan su sai da ya nuna alaman mamakin ganin mu a hakan To top it all ga abinci agaba na. Jahan was like is this for real?ta dan kalle mu da kyau dukan mu.. Na dada sunkuyar da kaina cike ladabi da sanyin murya nace good morning mum. Sai Ta dan dafa kafadata da sauri ta dago ni nikuwa sai cire idanu nake tsaban bugun kirji na,noor are you ok?u r suposed to be on ur bed,Ashe jiya baki ji dadi ba shine bazaki zo ki fada mun ba ko? A yadda tayi min maganan cikin tsananin kulawa Duk sai Na rasa me zance mata sai kawai nayi mata shiru Cikin kasaita mai nuna sanyin bacin rai khaldun Yace mum pls Alaman an yi distrupting din breakfast dinshi kuma baiji dadi ba. Jahan dai Batace masa komi ba ta narka masa kyakywan idanun ta akan nashi lips din ta dauke da miskilallen murmushi mai masa alaman ya dakata mata Yana dauke idanun shi ta dan dafa shi Kasa kasa tace mashi ayi hakuri ..dole ne ya sani na zo nan khaldun,i need To check on my doter. A dan yangace yace not now mum..karya wa muke yi and i need my space. Wannan maganan da su subaya ya ke Nikuwa wannan phrase din nasa na karyawa “muke yi” yasa na dago da kyau na kalle shi Jahan Tasan halinshi sarai dan haka bata tsaya maimaita abunda subaya da sadaat suka fada mata akanshi da safen ba. Itama Zama tayi tare da mu Cikin ido ta dube shi calmy tace Aaban,are we good?da kamar zai amsa sai ya basar abincin shi ya cigaba da ci bai ko kula ta ba,ta kalle shi ta dan kalle ni.. Sai tayi murmushi. Sadat ma ya kalle subaya itama ta kalle shi abun ya matukar basu mamaki Wani shiru ne ya ratsa wajen kowa da abunda yake sakawa aransa A Bazata khaldun ya sake Wani miskilillan murmushi wanda ko lips dinsa basu san yayi shi ba sai ya kada kansa batare daya sake daga idon sa ba. Allah kadai yasan meke gudana aransa a time din Abincin sa yake ci ya hade ransa,sadat daya ga nayi tsuru tsuru bana iya motsi agaban sa’ood da jahan sai lafe ta kunne yace ma subaya ta je ta dago ni a tsakiyan su,… looking like he cares da razanar da nayi Babu musu kuwa subaya ta karaso dan ita kadai tasan wahalar data sha wajen shawo kansa da safen nan Tana kuwa dafa ni khaldun ya balla mata wani mugun harara,amma da shike taga jahan agaban su sai ta share shi tace min get up little sis wa yace miki kizauna anan din zo muje daki,…a hankali na dago na kalle ta sai naga ta na kokarin jawo hannu na. Wani karar Stop it din da mukaji sai da yasa ta sake ni da sauri ta kalle shi adan tsorace,pls let her have her breakfast….sai ya dan saukar da murya ya bita da kallon dagaske yake wani mamaki ne ya turnuke subayan har ta kasa cewa komai sai kallon shi data keyi itama… Agefe kuma bakin ciki,haushi da rudewa ya hana sadaat cewa uffan subaya kamar zatayi kuka ganin dik na razana,jahan dake lura da shi tace pls ka barsu su tafi mana naga kamar ma bacin komai takeyi ba Bai jira ta karasa ba ya dago spoon dinsa ya debo abincin yana kallon jahan din yace zata ci mana.. Sai ya juya gare ni cikin jan aji ta salon yin wasa da tunanin su, nan ya kawo abincin dai dai setin baki na a hankali yace min open5 Chak wajen ya dauke da ji.. Rawa ma baki nan ya fara yi tun kafin na bude shi,yau nidai naga takaina yau ga khaldun of all ppl wai zai bani abinci abaki,.2 slowly na bude baki nawa ya sa min spoon din ban ko iya taunawa ba na gumse shi dan mamaki da rudani ya hana zuciya ta sakat And More than anyone awajen zuciyan sadat kamar zai fice daga kirjin sa tsaban bakin ciki.16 Jahan kam murmushi tayi,ta mike tare da cemin idan na gama break in nazo tana nema na. Ban iya amsawa da words ba na gyada kai,am sure jahan ta fahimci halin da nake ciki alokacin sai bata juyo ba har na dena kallon ta Subaya gaba daya ta kasa kamu kan tashan. Dan sosai sadaat ya zugata da safen ma har suka je wajen jahan da magana akan abunda ya faru jiya gashi khaldun sai juya abubuwa yake. ayadda suka juya ma jahan labarin ta dauka ko zata zo ta samu bahiyyya na kwance awani hali Sai gashi khaldun is set to suprise them ..babu wanda ya yi tunanin zaiyi abunda yayi yanzu Khaldun ya cigaba da bani abinci abaki har hawaye suka gangaro min tsaban tsoro ban ma sani Subaya tayo shiru akan mu dan ko uffan baice mata ba bare ma ya kalle mijin ta Daga nan Bamu ma san lokacin da sadaat din ya fice ba,sabida inda za’a bude kirjin sa aga bacin ran dake ciki da tabbas gobara ne zai tashi awajen Da ya rage saura mu ukun,wani kallon barazana yamin ataikaice alaman naci gaba da ci da kaina shi ya gaji,dan haka yana mika min spoon din ya tashi ya haura sama ya barmu nida big sis munyi lumui muna bin bayan sa da ido. A gurguje ta dan kalle ni tace are you alright? Uhmm kawai nace Na gyada kai kafin na sunkuyar da kai ina tare hawaye na. Jira ni anan Ina zuwa…kafin na dago ma ta haura sama ta bi bayan sa. Kofar dakin shi ta nufa Tayi knock bai kula ta ba,sai ta turo door din ta shigo mamaki ma ya bata da taga gansa A Zaune hankalin sa nakan wayar sa yana latsawa Sau daya ya daga ido ya kalle ta ya dauke kansa ya cigaba da abun da yake yi Kallon 2 seconds tayi mashi tare da sauke ajiyan zuciya sai ta taho ta zauna kusa dashi cikin sanyin jiki Da taga bai kula ba,Wani irin marairace fuska tayi zata dafa shi ya ja jikin sa ya kau da kansa gefe ,..Khal…pleasse Aaaban..muryan ta yayi rawa tun kan takai gaba Yace ya isa haka subaya,meye ne kam kuke takura ni i realy dont want to be angry today. tace toh ka fada min mana? Whats going on ina nufin menene ya faru tsakanin ka da bahiyyan? Bai kalle ta ba Yace nothing. Tace and today? Khaldun,kowa yasan kai kadai kake cin breakfast,so why ..Hannu ya daga mata tun ma kafin ta karasa yana kallon ta cikin azalzalan masifa… Kin cika tambaya subayah,dole ne sai kin san komai?Ok fine she drank some mango juice,sai ya shake ta and then she faint shiyasa kika ganni da ita jiya and today we are just having Normal breakfast,kina da matsala da hakan ne?Whats wrong with that?. Adan tsorace ta dago ta kalle shi bakin ta har na missing step zatayi magana ya mike tsaye cikin bacin rai Wai Meyasa duk abunda nayi sai ya dawo miki fitina why…ya dan daka mata tsawa sai datayi hadiyan yawo Wani hawaye mai sanyin nuna razanar karar nasa ta sake mashi dan Gaba daya ta kasa motsi sai ta sunkuyar da kanta kadan cikin shessheka Tsaki yaja ya nufi bakin door ya bude “Look just Get out ya mata nuni da hanya Bata motsa ba tace toh Kayi hakuri dan Allah .. I just wanted to know,nan ta shiga gaya masa abunda sadaat yake dora ta akai tun jiya Juya kansa yayi yana cije labban sa cikin jin haushi, gashi Har cikin ransa ya tsani ya ganta a hakan,but he is so pissed right now ita kanta tana bashi haushi dan ya tsani janjana magana bare uwa uba yaranta.1 Kukan sa baiya so din take faman yi 2 seconds look ya bita dashi tana kan matso hawayen,tare da sauke boyayyen ajiyan zuciya ya dawo kusa da ita ya riko hannun ta cikin nasa”Come here… ya jawo ta ta mike tsaye kusa da shii wani kallon so da kauna ya bi cryng face din ta dashi yasa palms dinsa ya shiga goge mata yana binta da wani irin sanyin kallon kauna gaba daya sai da ya kashe mata jiki sai ya jawo ta jikin sa kadan ya rungume ta ya fara lallashin ta yana petting din ta. A kunne ya furta its ok ba fada nake maki ba,rainin ki ne ya ishe ni..ina duk kin gaji dani ne,to im going Subayah ni sam bana son fitinan ki.6 Wani cukuikiya shi take dada yi tana shiga kirjin sa da wani irin shauki ta yadda dukan gabobin sa suke amsawa da irin son data ke mashi Lunshe ido yay yana sauke ajiyayyan numfashi “Mutum Sai shegen son kuka kamar wata yarinya bayan kinsan bana so ko? Lafewa ta kara yi a shagwabe Tana share hawayen ta Cike da marairaicewa Tace im soryyy khal nifa bana son ranka ya baci ne..bai bari ta dora ba…yatsa yasa abakin ta yace shusshhh Duk abunda kike so a duniya zanyi miki shi Ina dai Kina so na karbe ta a matsayin sistar mu ne ko? Ta dada lafewa jikib sa Ta gyada kai Will you be happy if i do that? Tayi murmushi tace yeess “Dan karamin ajiyan zuciya yayi ya kissing hannun ta da goshin ta yace,its ok so be it; subaya I have accepted her komai ya wuce yanzu?2 Wani kankame sa ta da dayi ta gyada kai tana murna har cikin ranta tana masa godiya Tace I love you! Yace I love you too Go now,kijira ni a wajen mum akwai abunda zan fada miki Sai Ta tsaya kallon shi Murmushi mai kyatrwa ya mata cikin wasa ya ce no more tears? Tuni ta goge saura hawayen ta ta mayar masa faffadan murmushi tace ok am waiting sai ta fice. Dan karamin lumshe ido yayi kafin nan ya cigaba da abunda yakeyi Kan kace kobo ya shiga tattare tattaren sa,masu mashi aiki ne suke faman jigila suna fitar masa da kayan sa waje.. Lokacin nikuma har na tattara dishes din naje kitchen ina wankewa,sai dai gaba daya zuciya ta cike yake da tunani kala kala,bansan meyasa yau din kwata kwata bana jin dadi araina ba. Aiki na ma cikin qwiyuwa nake yinshi ,and I almost foget that jahan tace naje na same ta dazun,da abun ya fado min sai nayi saurin maida hankali kan aikin Dama so nake nayi wanka na dada tsaftace kaina kafin naje. Bangaren subaya kam murnan jin khaldun ya amince dani a matsayin yar uwansa ya sa ta kasa hakuri Site din jahan taje ta shiga bata labarin abunda yace.+ Jahan murmushi kawai take tayi aranta tana jinjina murdadden hali irin na danta tasan Bazai taba yin abu direct ba Wani bin har tausayin macen da zai auro ya zauna da ita take. Cikin hirar su da subaya sai ga kiran alhaj hamood. Anan subayan ta kejin ashe cewa da khaldun yayi zai tafi ya bar ta ba wasa yake yi ba dagaske ne. Khaldun sa’ood zai tafi chan iran dawlan kakkanin sa watoh iyayen mahaifin sa.. Bayan ya dade baije bama gashi yanzu wani muhimmin Aiki ya hada shi da sojojin india rajiskhan iran da duk wani karamar yankin data shiga tsakanin wayannan kasashe2 Dan haka zaibar gida nigeria na kusan shekara 4.4 A Take jikin subaya ya mutu sai taji wani iri aranta Sai dai kuma inda sabo ta saba dan haka koda akayi confirming maganan tafiyar sa awajen jahan sai ta daure bata ce komai ba. Ni kuwa ina chan daki ina kan dresing kaina,dan da shike yau banyi wanka da safe ba sai naga zaifi dacewa nayi wankan kafin naje ansa kirar jahan. Puss pink ember gown dan dai dai da jiki na na saka,sai na goga light pink oily chapet a lips dina,ban wani shafa turare dayawa ba dan haka mutum bazai ji qamshin da jiki na take yi sai yana daf da ni.. Wajen jahan na nufa dan haka Tafiya ta nake yi shiru akan tsari Ban lura da wanda yake biyo ni abaya na ba Shikuwa khaldun tun daga saukowar sa a akan step din shigowa shashen ya zuko qamshin jikina sai ya dago idanub sa ya sauke akaina yana ta kallo na He loves keeping straight face,dan haka babu alaman daya nuna cewa qamshin jikin nawa ne ya burge shi,toh whats he looking at dan ko ni ban isa nace na sani ba. Da shike waje daya muka dosa sai Motsin takun sa a daf dani ya fargar dani. Gefe na koma na rabe alaman na bashi hanya,. Banyi tsammanin zai kalle ni ba sai gashi har mun hade ido. Dauke kansa yayi da sauri ya dan shige gaba nikuwa tsaban bugun da zuciya keyi sai da na kusan minti 10 ina tsaye ina ta tuno da wulgawar kyakwan fuskan sa sanda har ya kure bana ganin sa ban lura ba sai chan kafin na tattaro kaina na biyo bayan sa. Da sallama na dan yaye curtain din da zimman ganin sa shida jahan sai wayam naga ba kowa acikin hall din. Dada shigowa nayi ina dube dube amma shiru banji motsin kowa ba,dada kutso kai nake yi ina bin palourrs din ta dakii daki gashi wajen ba kadan ba Ganin shiru yayi yawa sai na juyo da zimman zab fice,wani sanyin iska ne mai dan karfi ya buso ni dana ke takowa ta hall way yana faman daga transparent curtains to a chan bayan site din na hango big sis subaya tana xaune tana ta dariya alaman anan suke Dan kadan na dafa glass wall din na yaye curtain din ina kallon murmishin ta Haka kawai naji wani irin dadi acikin raina danaga tana cikin wannan yanayi I just love seeing her happy,sai dai bansan meyasa na tsani mijin ta har cikin zuciya ta ba.2 Hankalina ya fara bani cewa baya kaunar khaldun and he is not so caring with big sis. A tunani na yanzun ma ba bazai wuce da shi take tare ba,hmm big sis is realy in love with him,and its so unfurtunate that sadat shine farin cikin ta..amma da za’a bi ra’ayi na i feel like he dosnt even derseve her.1 Ajiyan zuciya na sauke zan sake labule naji kaina ya wani sara,bugun kirji na ya karu. Wani daddan Qamshin jikin khaldun mai rudarwa na shaka Ban wani jira ba na waigo a fixge har ban sani bana fado jikin shi da kyar na dan daddafe na chakumo rigar sa Ido na a lumshe nayi shiru ina jin tafiyar hannun sa a baya na daya sa ya tallafo ni Ban iya hade ido da shi ba cikin marairacewar murya nace Sorry.. Yace baki da aikin yi ko?sai Ya sake ni a hankali ya na kallo na Sai Na girgiza masa kai ina dan matsawa gefe، tabe baki yayi ya wuce daf jikina kamar zai gogu dani dan na kara matsawa, hannu yasa ya yaye curtain din shima ya shiga kare ma big sis kallo Go get me something to eat “Derset Nace ok…k Da sauri nayi yunkuri Zan wuce yace i want that thing ! Ban fahimce that thing din ba sai Na juyo a slow motion,ina kallon shi har yanxu idanun sa nakan kallon waje. Ban dai ce komai ba Na tsaya ina mutsu mutsu kamar munafuka Har zan yanki draw na tafi sai naji yace Wancan abun da kike dafawa shahrul yam balls…shikadai ma its ok Hehehe yau kuma? amma ai da shahrul ya yabeni akan yamballs din cewa yayi bai masa dadi Ba Ko gama assimilating voice dinshi banyi ba yayi dismising dina da cewa “Be fast about it, Kawai sai na nufi kitchen ina ta famar murmushi Doya na feraye na tafasa kafin na shiga hade haden da nasaba domin yin hadaddiyar yam balls mai flaked fish.. Da shike ina ta tunani kala kala,sai na dan bata lokaci ban gama hada shi a tray ba saiga mai aikin gidan ta shigo,tace min khaldun yace chan baya zan same shi Nace toh dana kimtsa sai na biyo ta bayan da tray din a hannu,anan din ma a cikin wani garden suke ga khaldun tare da subaya,sai umbrella swing a chan yana motsawa shikadan sa wanda ya tabbatar min cewa dama su uku da jahan Aarah suke xaune Anan sai dai banganta ba har sai da na iso daff na hango ta achan nesa tana ta waya dukan su basu lura da ni ba.. Tsayawa nayi nadan rabe jikin wire wall dib ina satan kallon wasan da khaldun yake ma sister sa subayah Neva in my life have i eva seen him this free,tunda nake dashi sai yau na taba ganin geniune murmushin sa Subaya Sanye take da english wears rainbow top da rim jeans ta daura cute hair band akan suman kan ta sai tayi fresh sosai kamar wata yar shekara sha bakwai. akan farar doki yar madaidaiciya ya daura ta shi yana jan siddin daga kasa ita kuma tana masa hira yana mata murmushi Sai Dada matse ido na nake ina so naga ko murmushin nasa zaifi haka dan motsawar dimples dinsa ne dama alamar,but he still remain geek,i just wonder if har na mutu zanga wani kakrawan dariya akan fuskan sa. Thy both look happy nima sai naji dadin hakan,ashe bansan da cewa yawanci dama idan zai tafi haka sukeyi sukan ware lokaci makansu na junan su ba . Duk dama ni ba jinin su bane amma sosai Naji dadi da banga sadaat anan din ba Ko da ba’ace ba Nikaina nasan bana son abunda khaldun baya so Am naturally getting attched to his emotions Ganin jahan ta sauke waya a kunnen ta yasa nayi maza na fito daga bayan wall din na karaso Ya Nooori… Subaya ta kwalla min kira muryan ra shake da dariya da farin ciki I cant help but to smile back,ina aje Tray din yamballs din san sai nayi waving inta at same time ina karasawa zuwa wajen jahan. Har kasa nakai zan rusuna ta ruko ni calmy da irin kallon ta mai kafa tasiri azuciyan mutum. Sanda ta dago kaina ta dora min light peg a goshi kafin tayi min adduan tsawon rai. ‘Shikuwa khaldun sau daya ya kalle ni ya kau da kansa amma bai wani hade rai ba. Jahan ce ta fara bude abincin dana kawo masa A ranta tana wondering ba dazo da safe subaya tace mata khaldun ya amince da ni ba? Kafin ma ta kammala wannan tunanin sai tagan sa yana sauke subayan shi daga kan doki kamar yar baby tana kyalkyale dariya. Hannun shi ta rike suna tahowa sai na naga jahan ta girgiza kai tayi murmushi tace min zauna bahiyya,ban musa ba na zauna shiru kusa da ita Cos khaldun is giving me a hot fun to watch…Ashe haka yake?Waye zaiyi tunanin zai bar wata ta rabe shi bare ma ya mata wasa har haka. Rungume ni da big sis tayi ya fargan dani,sai na riko ta nima muna dan maida ma juna murmushi. ‘Yana zama ya jawo yamballs din gaban sa,jahan kuwa dan son taji bakin sa sai tace ai na dauka mani kika kawo bahiyyyah..nayi murmushi cikin jin kunya nace ah’a dama nashi ne. Tace emmm so Khal,ya dan dago kamar baby ya mata kallon tayi shiru bayason surrutu,hakan kuwa ya cinye abunsa bai bada kowa ba… Big sis Subaya ma data gama sa rai zai bata koma yace suci tare amma sai yayi burus dasu haka har ta gama kumbura fuska bai yi ma kowa tayi ba..ita kuwa jahan babu abunda take sai dariyar draman sa a cikin ranta. Daya gama yace Alhmdullhi sai na kawo hannu na dauke plate din abun mamaki sai naji yace min “thanks” murmushi kawai nayi,zuciya ta fall da jin dadi har na shiga kitchen ban sauke a hannu a kan fuskata ba. Haka kawai natsinci kaina cikin nishadi. Bayan tafiya ta ne yake fayyace ma jahan cewa ya amince dani a matsayin bahiyya hamoods amma da shike bashi ya sani aikin ba shiysa bazai iya cewa na dena ba Har jahan ta dan tsokane sa,cos looking at the way he eats my yamballs tasan inhar kama zuciya ake nufi to taste din abincina ya riga ya xuciyar sa. Nikuwa shirme na na tsaya yi a kitchen fuskan khaldun keyimin gizo,ga plates din ma agabana ko wankewa banyi ba Karfe 12/00 jirginsa zai var nigeria,dan haka sukayi bankwana da su big sis sai ya hauro sama zai shirya. Ina ta shirme ban hankara ba naji inuwar mutum abaya na,a dan birkice na juyo na kalle sa,cikin sanyi muryan da bansan dashi ba nace masa meya keso,ya fada min zan kawo mashi daki Yamin alaman kar na damu”Scoof kawai yayi daya kare min kallo,sai ya wuce ya bude fridge ya fito da mixed red and black fruit juice ya aje akan couch,.bai saba da shiga kitchen ba Dan haka ya shiga dubawa ko zai ga cup din da zai zuba drink dinsa so i quiclky open one of the drawers na fito da clean glass cup na bashi.. Ina tsaye naga ya zuba yana sha a yangace har sau biyu,inda zaka ganmu a lokacin zaka dauka wani magana zamuyi amma aje min komai yayi anan ya fice abun sa. Wani dadi naji Kamar ankashe ni,sauran wanda yasha din ma dauka na nemi setin bakin sa nima inasha There ia no daubt that am crushing on him har cikin raina ba fara jin wani sabon bakon al’amrai game dashi.1 Shikuwa dakin sa ya nufa after like 30minutes ya fito a shirya tsaf cikin true blue mens suit na giorgio armani. Dai dai ina saukowa zan shigo kenan Wayyoh ubangiji na,dan dana gansa daga nesa shima yana saukowa sanda na koma da baya na rungume bango .. Wani Lumshe ido nayi tsamm ina sauke nunfashi kamar rai ne yaga rai He looks so gentle kamar ba shi din ba sai naji na fara raina ma kaina agaban sa haka kawai nayi sauri naje daki na. Wardrobe na bude na shiga neman kayan da zan saka mai dan armashi a gurguje don nasan wayar dayake yi ayadda ya saba zai iya daukar sa minti sha biyar. Naci sa’a kuwa har na gama yan shafe shafen na mammatso jiki na acikin wata pure royal blue fitted gown mai fallen neck na fito bai gama ba. Wato irin kyaun danayi Ni kaina sai da naji wani irin fargaba da nake saukowa ahakan don sosai kalar kayan ya dada haska farin fata na. Sai dai Kunya ya rike ni asaman step inaji big sis subaya tana cewa ai ban sauko ba ajirani aje airpot din tare dani Da naga alaman jahan zata iya shigowa wajen sai na sa tafin hannu na na rage karfin pwder dana bula kafin na taro kwarjini na fito sarari. wani irin kallon 2minute silence suka jefe ni dashi dukan su biyu sai na rage taku na ina sum sum ina kaucewa idanunan su Subaya tace wooow..what a beautiful angel. Ita kanta bata san matse arm din shi take faman yi dan ya kalle ni ba Kinga yadda kayan nan ya miki kyau kuwa? Sake shi tayi ta kamo ni tana cewa ai nafada maki sexy dreses is for sexy models like you. You look exctly like aishwariya rai Dawuri Khaldun ya tabe baki,dan saida ya kalle subaya kafin ya Wani karkace yabini da sanyin kallo Kwayar idanuwan shi ya kafe surar jiki na dashi har na iso daf ina amsa big sis shikam da alaman ma baisan kallo na yake ba3 haka kuwa baice min uffan ba har jahan ta zo ta same mu Muka fita rakashi nidai naji jahan tace khaldun zai tafi amma bansan ina zaije ba kuma bantambaya ba,firr yaki muje aiport din dan haka agida muka rabu, Da ni dashi Sai satan kallon juna mu keyi yana dai kau da kai Gashi kusan irin kalar kayansa nima nasa,da big sis ta nace akan mana pics dan dolen sa ya tsaya kusa dani kuma yayi murmushi3 Nidai Allah Allah nake wayar bigsis din ya shiga hannu na ko zan mallake hoton da ya shiga convoys dinsa One last look danayi ma tinted din sai da jiki na yabani cewa yana kallo na kuma yana min murmushi Dawowar mu ciki muka zauna a falo tare da jahan kowa yayi zugum tana dan saisata subaya da tuni ta fara daga hankali ta har jikin ta ya fara daukn dumi. Kowa acikin mu yanajin zafin tafiyar san,sai dai kowa da yadda yake fama da nashi azuciyansa Jahan karan kanta ma dauriya take yi,don bata wani sabawar da kowacce uwa takeyi da danta ba. Rabin girman sa ba hannun ta bane,godiayn Allah ma tasan danta khaldun yana matikar kaunar ta Sai subayan itama,nikam ba a magana don kuwa nawa harda boyayyen ciwon son shi araina wanda bai bayyana min kansa ba. Muna cikin jimamin rashin sa na kwana biyu saiga gen hamood ya kira, dama shikam yasan subaya sarai da son daga hankali sai ya sa aka bata wayar yana lalabarta da maganganu masu dadi Anan nima nake jin ashe ma jahan tana da kishiya awani kasar kuma nan khaldun zai fara zuwa Tun Ranar haka nakeyib bacci cikin tunanin sa da kyar rashin khaldub agidan yabi jikina Dan kafin na sauko watar da zan yi waec shirintan sadaat ya gama kure min hakuri na. Kullum sai nayi claiming rashin lpya suke kyale ni,wani bin har na kanji nakai karan sa wajen jahan amma kuma bazan iya ba dan bansan me zan ce ba. Toh ranar da zamu shiga watan fara exams a wajen cin abinci jahan ta bani wasu papers tace na sa hannu Bansan cewa takardun shedan zama bane akasar london. Dan har angama tsaramin karatu na da duk hidiman rayuwa ta achan ban sani ba Jahan tace min tunda khaldun baiya nan big sis da mijin ta saadat sune zasu kaini dan haka sune guardians dina ko da naje makaranta.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published.

[Advertisements⬇️]