Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAR MAKIYAYA CHAPTER 19

YAR MAKIYAYA CHAPTER 19

- - Post a Comment
YAR MAKIYAYA CHAPTER 19
  Rasheed abunda ka aikata bai yi daidai ba, this family is a very respected family, da baka yi gaggawar k'iran police ba, duk bamu san menene gaskiyar lamarin ba da ka bi abun a hankali......." Abban Habeeb bai kammala maganar sa ba Rasheed ya katse shi ta hanyar d'aga masa hannu kafin yace+ "a bi abun a hankali? Me kake nufi da hakan?? Gosh! Brother na yi zaton kai ka fi ni hankali da tunani, but it seems ba haka bane. Yaya za'a yi ace an kama mutum dumu dumu da laifin kisa sannan kace kar a k'ira police,just because this is a respected family, shikenan se a kyale talaka ya cutu? All evidences are pointing towards Ameer. Kar ka manta wanda aka kashe uba yake a gun y'ata Layla se inda k'arfi na ya k'are". Dad da Abban Habeeb kawai kallon Uncle Rasheed suke yi cike da mamakin sauyawar sa karaf d'aya, babu wanda ya sake furta kalma d'aya a cikin su. ******** ********* ******** Shimfid'e take kan gado Suraj na zaune gefen ta hannun sa rik'e da nata. Habeeb ne yayi sallama ya shigo d'akin jiki a sanyaye yace "Suraj.....wannan wutar kashe ta da kamar wuya, Mai martaba ya samu labarin abunda ya faru as a result yanzu haka yana asibiti, gashi Uncle Rasheed ya sake rura wutar domin ya sa police sun tafi da Ameer for questioning, Suraj komai ya rikice" Suraj bai san lokacin da ya saki hannun Layla ba ya mik'e "Habeeb yaya Uncle Rasheed zai yi haka?" Ihun da Layla tayi ne yasa duk hankalin su ya koma kan ta, Iya k'arfin ta take fisge wa daga jikin Suraj "Ka kyale ni in ga Baba na! Ni ka bar ni Suraj dan Allah ka barni in ga Baba na" Ganin ya kasa controlling d'in ta yasa Suraj ya sake Layla ta fice kamar mahaukaciya. Turus tayi a lokacin da ta isa filin gida, k'afafun ta suka kasa d'aukar ta se zuba gwiwa tayi a k'asa ganin gawar baban ta rufe da zani da tayi. "Suraj! Suraj don Allah ka fad'a min ba gaskiya bane wannan!! Tabbas mafarki nake yi!" Zubaina ce ta rungume ta tana kuka. "Layla ba mafarki kike yi ba! Da gaske ne wannan azzalumin ya kashe Baba!" Se lokacin Layla ta mik'e ta juya tana kallon Suraj dake tsaye jiki ba kwari idanuwan ta cikin nashi kafin ta k'arisa gaban shi ta nuna Gawar Baba da yatsa tace "Dubi! Dubi kaga abunda ya aikata.... Suraj kalli kaga irin kisan wulak'ancin da Ameer yayi wa Baba! Ya kashe min Baba na!!. Kafad'un Layla Suraj ya rik'e yace "Layla! Layla ki nutsu please! Ameer ba shi ya kashe Baba ba! Na tabbata Ameer bazai aikata kisan kai ba,not even in my wildest imaginations" Jin kalaman Suraj yasa se da Layla ta daina gani daidai, ji tayi kamar an datse mata numfashi bata san lokacin da ta fisge jikin ta daga nashi ba ta fara ja da baya tana girgiza kai "Suraj......... M..m..me kake nufi da Ameer ba shi ya kashe Baba na ba?? Kana wajen fa, abunda na gani shi ka gani! Ko kana nufin kace min duk abunda na gani gizo ne ba gaskiya ba ne? Suraj baba na fa! Babana fa ya kashe min!" Suraj ya rik'e fuskar Layla Cikin rud'ani yace "Look Layla, Kar kar ki yi stressing kan ki kin san kina da juna biyu, don Allah ki nutsu ki fahimce ni, kamar yanda yake mahaifin ki nima haka mahaifi na ne, amma wata gaskiyar itace cewa Ameer tabbas ba shi ya kashe Baba ba, Layla na tabbata akwai rashin fahimta." Hannuwan sa ta sauk'e daga fuskar ta,cikin zafin nama ta hankad'a Suraj yayi baya har saida Habeeb ya rik'e shi daidai lokacin su Mom suka shigo gidan, su kansu sun tsorita da yanayin Layla, se lokacin Baban junaidu ya tsoma baki "Kin ga abunda nake gudu tun farko kenan! Shi Mai dukiya da Mai mulki ba abun yarda bane, a ko wanne lokaci zai iya sauya wa, d'an uwansa ya kashe min d'an uwa na amma domin su kare darajar gidan su da mutuncin su babu abunda baza su iya aikata wa ba, domin darajar su da kimar su tafi musu komai a rayuwa. Kuma zaki gani, Mai laifin ko kwana d'aya bazai yi a rufe ba, duniyar da kika kai kan ki Layla shi yayi sanadiyyar ran Baban ki, da baki auri Surajo ba da har yanzu kina rayuwar ki cikin farin ciki! Yanzu ga sakamakon nan, d'an uwana ya mutu..." Suraj ne ya katse shi ta hanyar fisgo Layla jikin shi, fuskar sa sharkaf don zufa yace "No Layla! Don Allah kar ki saurare shi! Kawai yana k'ok'ari ne ya sauya miki tunani, abunda kawu yake fad'a ba haka yake ba, sannan Auren mu bamu yi shi bisa kuskure ba, muna k'aunar juna, Layla don Allah ki fahimce ni" Fisge wa ta sake yi a karo na uku ta nuna shi da yatsa! Kar ka sake tab'a ni Suraj, kawu gaskiya ya fad'a! Duk laifi na ne!! Laifi na ne da na bari ka shiga rayuwa ta, Suraj da ace bamu had'u ba da bazan fuskanci irin matsalolin da na fuskanta a rayuwa ba, naga tashin hankali, Suraj kayi tunani mana Ni tunda na taso ban san wata rayuwa ba da ya wuce kiwo, duniya ta k'arama ce amma babu abunda na rasa a cikin ta, farin ciki, kwanciyar hankali komai ina da shi amma tun ranar da ka shigo rayuwa ta nake ganin tashin hankali, Farko Ameer, sannan Saeed yanzu kuma Ameer ya kashe min Mahaifi ya raba ni da farinciki na Suraj duniyar ka ta tarwatsa min tawa duniyar baki d'aya! Kawai ka fita bana son ganin ka! Suraj in ka farka daga mafarkin da kake yi na cewa Ameer ba shi ya kashe Baba ba se ka dawo, kawai ka fita!!.... "Layla! Meye haka kike fad'a? Suraj fa mijin ki ne, kada zafin rashin Baban ki ya sa ki zauce". Mom ce tayi maganar amma Layla ko kallon inda take bata yi ba se cewa ma tayi "Suraj ka fita daga gidan nan ko ni ma in kashe kai na!!" Wani bugu k'irjin Suraj yayi take jiri ya d'ebe shi saida su Dad suka rirrik'e shi, fice wa suka yi daga gidan yayinda Layla ta zube k'asa tana kuka. Ranar aka Kai Baba makwancin sa, Uncle Rasheed da shi aka yi komai a wajen, Baban Junaidu kuwa ya hana su Dad ko da Sallatar gawar Baba balle zaman makoki. Ameer kuwa yana chan ana ta interrogating d'in shi amma, amsa d'aya kawai yake bayar wa "Ba ni na kashe shi ba". ******** ********* ******** Layla tana kwance kan gado a duk'unk'une duk ta kod'e tsabar kuka Uncle Rasheed ya shigo, zama yayi bakin gadon ya dafa kan ta da hannun shi, jin haka ta tashi zaune tana share hawaye. "Y'ata....... Abunda ya faru ya faru kuma baza mu iya sauya k'addara ba, Ina so ki manta komai, Zaman ki a nan kawai sabon ciwo zai tada miki ina so in d'auke ki mu tafi, kiyi nesa da nan, zaki fi samun kwanciyar hankali. Na sani cewa duk da ni ne asalin mahaifin ki, bani da matsayin da baban ki yake da shi a wajen ki, amma ni ma ina so in gan ki cikin farin ciki, ina so in nuna miki k'auna wanda ban samu daman nuna miki ba a baya. Ki biyo ni mu tafi, wajen da baza ki yi nadaman zuwa ba, sabuwar duniya sabuwar rayuwa." Kuka Layla ta fashe da shi ba tare da ta amsa shi ba, ya dad'e yana zaune a wajen kafin ya mik'e yace "Y'ata in har kin yanke shawara ki same ni a chan fada, jibi zan koma Newyork kuma bazan iya barin ki cikin wannan yanayin ba, ina tare da ke a ko yaushe. Kuma ki sani ko ma waye ya aikata wannan laifin iya k'arfi na se na sa ya wulak'anta a rayuwa, shima se ya fuskanci hukunci in Allah ya yarda!". Yana kai nan ya fice Layla ta bi shi da kallo...... "For a moment i taught i was dreaming Habeeb! Yanda Layla ta sauya karaf d'aya, the fire i saw in her eyes proves clearly that she hates to see me! Ban tab'a tsammanin cewa Layla bazata saurare ni ba, she doesn't even trust me anymore! Habeeb Layla cewa tayi komai ya faru saboda na shiga rayuwar ta ne, Bazan iya cire Layla daga rayuwa na ba, ita zuciya ta ne, babu shakka Habeeb bazan iya jure rashin ta a kusa da ni ba, ka bar ni in je in same ta , zamu yi magana a tsanake i'm sure zata fahimce ni bazan bari Layla ta datse soyayyar mu ba".. Rik'e shi Habeeb yayi yace "Suraj please, ka dawo hayyacin ka, Layla kawai shock ne na rashin Baba ya same ta, ka bata lokaci ta dawo hayyacin ta, sannan a wannan yanayin naka ta ina zaka fita zuwa gidan su Layla! Bazan bari ka fita ba a haka, kana buk'atar hutu. Nasan Layla kalaman ta sun yi kaushi amma ka sani in da kai ne a gurbin ta you would do the same. Yanzu fa k'arfe takwas na dare bazan bari ka fita ba Suraj." Daga nan Suraj bai sake furta kalma d'aya ba Habeeb ma haka yana zaune gefen Suraj. Mom ce ta shigo d'akin ta ajiye wayar Suraj sannan ta dubi Habeeb tace "Habeeb please stay here tonight, i don't want him to be alone". Kai Habeeb ya jinjina suka yi sallama da Mom sannan ya dawo ya kwanta bayan ya kashe wutar d'akin. 12:00am Hasken farin wata ne ya hasko d'akin iska yana shigo wa mai dad'in gaske, kallon bud'add'en windon yake yi kafin ya mik'e ya nufi bakin windon ya tsaya, duk iskar nan tana dukan jikin shi sanyin yana ratsa shi ko kad'an bai damu ba. Duk abunda yake yi Habeeb yana kallon shi cikin tausaya wa. Washegari Tare Suraj da Habeeb suka fito ganin fuskokin su kad'ai ya isa ya bada shaidar cewa babu d'aya daga cikin su da ya runtsa, Mom ce kad'ai a falon ta tafka uban tagumi har suka k'arisa inda take "Good morning Mom". Suka fad'a a tare, Kai kawai ta girgiza tana k'are musu kallo kafin ta ce "Fuskokin ku sun tabbatar min babu wanda ya runtsa a cikin ku, why?". Murmushin dole Suraj yayi kafin ya mik'e yace "Ta yaya zan iya barci cikin d'akin da babu komai cikin sa se d'umbin duhu? Ta yaya zan iya runtsa wa a kan gadon da aka shimfid'e shi da k'arangiya?, Mom ina so in yi magana da Layla! I'm sure abunda ya faru jiya ba daidai bane, Layla kawai ta girgiza ne saboda rashin Baba, yanzu zan je in same ta we will solve this problem once and for all!... Suraj na gama rufe bakin shi suka ji an bud'e k'ofa, duk a tare suka had'e baki wajen furta sunan ta "LAYLAA!!!...." Suraj bai damu da cewa Mom na tsaye ba yayi hugging Layla kamar zai had'e da ita, ko motsi Layla bata yi ba, tamkar itace haka ta tsaya ganin Suraj bashi da niyyar sake ta yasa ta sa hannu ta ture shi daga jikin ta sannan ta nad'e hannuwan ta a k'irji. Suraj sam sam bai damu da reaction d'in ta ba se ma cewa da yake yi "I know she will come back! Layla nasan zaki dawo, nasan bazaki iya fushi da ni na tsawon lokaci ba, Layla shin kin san halin da na shiga a dare d'aya tak da bakya kusa da ni? Idan na kasance cikin damuwa kullum kina tare da ni ,amma jiya kin kwace min duk wata dama da nake da ita na kasance wa tare da ke a lokacin da kika fi kowa buk'atan hakan, with just a snap of a finger you snatched away that right from me Layla." Duk turancin shi Layla ba ji take yi ba ko kula shi bata yi ba balle ta san yana wajen , a lokacin Uncle Rasheed ya shigo, turus yayi da yaga Layla, ita kuwa wajen shi ta nufa, ta d'au lokaci a tsaye kafin da kyar ta bud'e baki tace "Na amince, ....... Na amince zan bi ka mu tafi tare Abbah!!" Wani victorious murmushi Uncle Rasheed ya sake sannan ya janyo Layla jikin shi yace "Allah ya miki albarka my daughter! , kije ki shirya mu kama hanya don tafiyar da nisa". Haura staircase Layla tayi yayinda Uncle Rasheed ya nemi waje ya zauna "What the hell is going on here??" Suraj ya furta,cikin kid'ime wa. Uncle Rasheed ya d'ago kai ya kalle shi kafin ya mik'e yace "Tafiya zan yi and i am taking my daughter along with me." Iya girgiza Suraj ya girgiza da kyar ya samo kalaman da zai furta "You are taking away my wife from me? My better half! Matar tawa zaka d'auke ka tafi da ita, ba fa sakin ta nayi ba sannan tana d'auke da juna biyu. Or have you fogotten that she's pregnant with my child? Who are you to make such drastic decision??" Cikin tsawa Uncle Rasheed ya ce "ni waye???? NI WAYE KAKE TAMBAYA?? ina tunanin ka manta cewa Layla is my daughter! Y'ata ce ita jinina ! Ina da right a kan ta, zan d'auki y'ata in tafi da ita kuma no force on earth can stop me! Kada ka sake questioning d'ina Suraj i can see ka manta manners d'in ka ...... Daidai lokacin Layla ta fito sannan a Lokacin Dad da Abban Habeeb suka shigo falon tare da Ameer. Murmushin takaici Uncle Rasheed yayi kafin ya yi nuni da su Dad yace "Look! Dubi yanda son kai ya mamaye ku baki d'aya, wanda yayi kisa ko awanni ashirin da hud'u bai cika ba a jail kun sake shi, ko ba shi ne Ameer d'in da ta dalilin shi y'ata ta dinga fuskantar matsaloli ba tun had'uwar ku? Wane alkhairi Ameer ya tab'a yi maka kai da kanka Suraj? Amma saboda Son kai ka zab'i wannan munafikin a kan matar ka". Suraj da ya gama kid'ime wa ya girgiza kai ya nufi inda Layla take tsaye ya durk'usa kan gwiwar sa ya had'e hannuwan sa yace "Look Layla! Kin ce had'uwar mu dake shine silar faruwar matsalolin ki, na yarda, tun had'uwar mu na rabaki da duniyar ki mai tarin farin ciki da kwanciyar hankali ,shima na yarda, amma Layla ni kuma abinda kike k'ok'arin aikata min ba farin ciki kad'ai zai d'auke min ba har rayuwa ta tana cikin had'ari, k'ok'ari fa kike ki rabani da mata ta, da d'ana, ku ne fa duniya ta...." Durk'usa wa Layla tayi a gaban shi kafin tace "ba a son rai na ba zan tafi Suraj domin bazan so in raba ka da duniyar ka ba kamar yanda ka fad'a amma a duk ran da naga fuskar wancan azzalumin zai dinga tada min sabon ciwo na rashin baba, bazan iya zama k'ark'ashin inuwa d'aya da wanda ya kashe min Mahaifi ba Suraj." Suraj ya girgiza "Layla na sani cewa mun shiga matsaloli daban dalilin Ameer, na sani Ameer ya cutar da ke na sani Ameer zai iya yin komai don jin dad'in shi Amma Ameer d'in da na sani bazai tab'a aikata kisan kai ba, bazai aikata ba,Layla ya kamata ki tsaya mu bi al'amarin nan a tsanake" A fusace Layla ta mik'e gami da ja da baya kafin ta girgiza kai tace Har yanzun dai kare shi kake yi , Baba na aka kashe amma kai bai dame ka ba ta d'an uwan ka kawai kake yi saboda haka bazan fasa ba nima tafiya zan yi." Uncle Rasheed ya ja hannun Layla zasu fita Dad ya tare su yace "Rasheed! Don't you dare! Yaya za'a yi ka raba mata da mijin ta alhali suna k'aunar junan su? Misunderstanding ne kawai kuma zamu sasanta i am not letting you take my daughter anywhere!".. Jin kalaman Dad Uncle Rasheed ya kwashe da dariya kafin yace "YOUR DAUGHTER?!! Wai kai Abdoul_malik har kana da bakin k'iran Layla y'ar ka? Ko ka manta cewa ita ce de wannan Y'AR MAKIYAYA, k'ask'antacciya da kake kyamata? In kun manta zan tuna muku cewa a ranar auren Suraj da Layla ni kuka rok'a na zama uban ta saboda auren ya d'auru saboda matar ka tana gudun in ka gane Layla talaka ce bazaka yarda da auren ba, sannan a kan Auren Layla saboda k'iyayya da kayi mata har d'an ka kayi wa jini da majina, duk wannan ban manta ba saboda haka baka da hakk'in k'iran ta y'ar ka. Now get out of my way Abdoul_malik!! Uncle Rasheed haka ya ja Layla suka tafi ko juyo wa bata yi ba yayinda Suraj ya kasa ko da d'aga k'afa a wajen balle bud'e baki........ Hello beutiful ppl! Very soon the story of y'ar makiyaya book one is coming to an end! What do you think about this touching episode ,kuna ganin Layla ta yi daidai kuwa? Plus in ba Ameer ne yayi kisan ba toh waye ?? Afterall all the evidence is pointing towards Ameer.. Ameer k'arisa wa yayi gaban Suraj ya zuba gwiwa kan shi a k'asa yana kuka "Na shaa yi maka abubuwa na ban haushi da takaici, na sha munafurtan ka sannan na saka ka cikin damuwa iri daban daban yet you are standing firm to prove my innocence, ban tab'a tausaya maka ba se gashi ka tausaya min, babu wanda ya yarda da cewa ba ni nayi kisan nan ba se kai, Suraj above all, kayi sacrificing soyayyar ka, farin cikin ka duk saboda ka cece ni. Ka bar ni nima na saka maka kyautata war da kayi min, zan fita na bar gidan nan, zan yi nesa da Belel da kuma kai na tabbata in Layla taji haka zata dawo gare ka Suraj, kuma ina rok'on ka don Allah ka yafe min laifukan da na aikata maka a baya na gane kuskure na".+ Suraj ba tare da ya furta kalma ba ya d'ago Ameer yayi hugging d'in shi kafin yace "Babu inda zaka je Ameer, tafiyar Layla ko dawowan ta wannan decision d'in ta ne yanzu, mu bata lokaci am sure she will come to her senses, amma Suraj instead of ka yi nesa da mu me zai hana ka zauna ka gyara alak'ar ka da mutanen gidan ku? Dukannin mu zuri'ah d'aya ne babu banbanci a tsakanin mu, change your life for good, ka nemi yafiyan wad'anda ka yi wa Laifi. Ni kam na yafe maka duk abunda kayi min, Ameer no matter what, you are my brother, jini na ne kai." Ameer kasa d'ago kai yayi har Suraj ya juya ya bar wajen ya nufi d'akin sa cikin sauri numfashin shi yana sama sama, yana shigo wa d'akin ya banke k'ofar ya rufe kamar wanda ya zauce haka ya dinga wurgi da duk abunda ke gaban sa, ya zubar da kwalaben turarrukan dake gaban dressing mirror duk suka tarwatse ko kula bai yi ba cewa ta kan kwalaben ya hau ya wuce, babu abunda suraj bai tarwatsa ba a d'akin saida d'akin ya koma babu masakar tsinke, duk ya yayyanke hannuwan sa. Ameer fice wa yayi daga falon yana kuka ya nufi sashen sa, ko bi ta kan mahaifiyar sa bai yi ba ya shige d'aki ya danna makulli ya rufe. Bayan kusan awanni biyu Mom ta dubi Dad tace "Bari na je na ga Suraj, i hope ya samu barci" Habeeb ma mik'ewa yayi ya bi bayan ta. A hankali ta murd'a hannun k'ofar sannan ta tura, abunda ta gani yasa saida ta zube k'asa, cikin rawar murya ta k'ira sunan sa "SSSURAAAJ??" Da gudu Habeeb ya shige d'akin yayi k'ok'arin d'aga Suraj dake sume ya maida kan birkitaccen gadon kafin ya d'auki waya ya k'ira likita, Mom kuwa duk tabi ta rud'e take ta kwalla k'iran Dad "ABDUL_MALIK!! Abdoul-malik!! Jin k'iran sa da Mom tayi yasa ya yi saurin mik'e wa ya nufi sashen Suraj. Ganin yanayin Suraj yasa hankalin Dad ya tashi matuk'a. "Look at My son Razia! Dubi yanda d'ana ya koma, har nema yake ya hallaka kan shi and all this because of a girl! In Layla bata buk'atar Suraj a rayuwar ta ya kamata Suraj ma ya farka, he needs to start afresh, nasan bazai iya manta Layla ba cikin sauk'i but haqqin mu ne muga mun sama masa farin ciki, he can't continue like this! In aka kammala case d'in nan zan d'auki d'ana mu bar nan mu kuma yi nesa da duk wani abun da zai tada masa hankali ko ya tuna masa da tashin hankalin da ya shiga!" Mik'ewa Mom tayi kafin ta ce "Toh amma Layla fa? Kana sane da cewa har yanzu ita matar Suraj ce sannan she is pregnant with his child". Daidai lokacin likita ya shigo ya gama examining Suraj, duk inda yayi Rauni saida yayi treating sannan yayi masa wata allura "Akwai damuwa da kuma gajiya a tarttare da shi yana buk'atar hutu, in so samu ne a raba shi da current environment d'in da yake ciki hakan zai taimaka masa sosai wajen samun nutsuwa." cewar Likita Habeeb ya fita tare da Likitan yayin da Mom tasa aka sauya wa Suraj d'aki domin wancan d'akin ya gama zama messed up. Bayan driver ya fita da likita Habeeb ya juyo zai dawo kwatsam yaga hayak'i ya turnuke wani Balcony daga sashen su Ameer "Hayak'i kuma? Wancan ba d'akin Ameer bane??" Habeeb ya tambayi kan shi, don ya tabbatar ya ruga zuwa sashen nan ya shige main falo ko kallon inda Maman Ameer take bai yi ba ya haura stairs ai kuwa da kyar aka samu Habeeb ya b'alle k'ofar, tsabar tiririn da ya doki fuskar Habeeb saida ya fad'i k'asa ma'aikatan wajen suka d'aga shi da kyar. Cikin rud'ewa Habeeb ya kwalla k'iran Ameer amma shiru kake ji gashi wajen ya turnuk'e Habeeb ya kutsa kai ba tare da ya damu da yanda wutan yake ci ba, kwance ya iske Ameer kamar matacce, haka ya ciccib'e shi ya fito da shi, kafin kace me har ambulance ta iso, shi kanshi Habeeb ya kasa kyakkyawan numfashi hakan yasa aka sa mishi Oxygen mask suka nufi asibiti. Fire sevice ne suka yi nasaran kashe wutan, Mom ta ma rasa ta inda zata fara on one hand Suraj on another hand Habeeb da Ameer. Umma Hauwa aka bari ta kula da Suraj Mom suka tafi asibiti domin duba halin da Habeeb da Ameer ke ciki. K'arfe sha biyu na rana Suraj ya farka, jiki ba kwari ya tashi daga gadon ya ziro k'afafun sa k'asa kafin ya k'are wa d'akin kallo. "Mom, Habeeb!!" ya kwalla musu k'ira , jin babu wanda ya amsa yasa Suraj ya mik'e, se lokacin yaji zafin ciwon dake k'afar sa, da d'ingishi ya fito , ko ina shiru babu motsin su Mom har ya isa living room inda ya iske Umma Hauwa zaune. "Ina suka shiga? Me yasa ban ga kowa ba?" Suraj ya tambaye ta. "Ranka shi dad'e Suna asibiti, Ameer yayi k'ok'arin kashe kansa ta hanyar banka wa d'akin sa wuta, a garin ceton shi Habeeb ma ya fad'i saboda shak'ewar numfashi...... Bata k'arisa maganar ba Suraj ya zari key d'in mota ya fice daga falon kamar zai tashi sama don sauri, a d'ari ya matsa motar ya nufi asibiti....

Post a Comment for "YAR MAKIYAYA CHAPTER 19"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...