YANAYIN RAYUWA CHAPTER 15 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YANAYIN RAYUWA CHAPTER 15

YANAYIN RAYUWA CHAPTER 15

- - Post a Comment
😞YANAYIN RAYUWA😰😭🌸🌸💐💐🌷🌷🌷. CHAPTER15 

 By halimatusadiya saleh ( saliha)🥰 Ba ajima ba,maryam ta shigo dakin rike da kayan zali,ba ma zali tayi, ta musu seda safe. Toilet ta wuce dun sa kayan,mom bata hanata ba, sleeping dress ne riga da wando,tana gama sawa tafito. Kallon ta mom tayi tace " ki samo ki kwanta,da safe muyi magana." Ba musu zali ta haye gadon ta kwanta,tama mom seda safe. Idon ta a rufe,amma bata yi barci ba,duk mom ta lura da itta amma ta basar, dakyar barci ya dauke ta. Da safe ta tashi duk jikin ta ciwo yake,haka ta daure tayi sallah,kafun tayi wanka ta shirya cikin uniform nata. Sede bata sa hijab dinba, daya ke batayi breakfast ba,a falo ta tarar da su,suna shirin yin breakfast,guri ta samo ta zauna. Dakyar take tura abincin,dun bata jin dadin bakin ta,bata dade da fara'a cin abincin ba,sega su ya Umar sun isu gun. Gaban tane yayi mugun fadowa,kujeran dake kusa da itta ya zauna,ya umar ya zauna a gefenshi. Ya Umar ko daya ganta a gun se yaji wani iri, dun haushi ma take bashi,zama yayi,suka gaisa da mom. Ya Usman, ma ya gaishe ta,su khalil ma suka gaishe su. Zali se juya spoon din take ta ma kasa cin abincin,she ko gogan se hararan ta yake,duk mom ta lura dasu. Daukan abincin tayi tasa bakin ta,se kuma ya shaketa,tari tafara yi,wanda yasa hankalin su ya kuma kanta. Shiko Umar kaman baya gun,ko kallon ta bayyi ba,maryam ce ta mika mata ruwa,karba tayi tasha,dakyar tarin ya ragu,ta shi tayi zata bargun. Mom ta kalle ta tace " se inna?" Sun kuyarda kanta tayi kasa tace " na kushe ne." Girgiza kai kawai mom tayi,dun tasan kuta sata taci bazata ci ba. Dakin mom zali,ta wuce, after sun gama breakfast ne,mom tace ma Umar yasame ta adakin ta. Ba musu yabita zuwa dakinta,zama sukayi,zali dake zaune abakin dress mirror,data ga da ya Umar ne mom ta shigo,ya sa ziciyan ta ya tsinke,ta tsorata,kar ya Umar ya gayama mom abunda tace mai. Kallon inda zali take mom tayi tace "in kingama ki juya zamuyi magana." Tana juyawa sukayi ido hudu dashi,yasa tayi saurin dauke kanta. Gyaran murya mom tayi tace " shin zaku iyya min bayanin me yafaru jiya." Gabanta ne yayi mugun fadowa,da sauri ta dago ta kalli Umar nan ma suka kara hada ido,kawar da kanta tayi,zuciyan ta na kan tsinke wa. Duk mom na lura dasu,amma bata ce kumai ba,ya Umar ne ya kalli mom cikin bacin rai ya zayyana mata yanda sukayi da zali. Jinjina kai mom tayi tace " ba laifinta bane,amma ai zali bansamman zakiyi haka ba,na fadade saboda hankalin ki ya kwanta,zali Umar da na e kema y`a tace,kuma bazan muku dole ba,zali kisani sonda muke miki ne yasa nace Umar ya aure ki,bantaba samman zaki ce kina son wani bayan shi ba,kuma kisani gara kisa wannan a ranki,keda Umar mutuka raba,dun haka kuma waye ne yake sonki,to ki gaggauta cire shi a ranki,ki sa soyayyan Umar a ranki,dun yau kuda su yayah suna raye nasan zasu abunda nayi,dun haka kiyi hakuri,da abunda nace miki." Ta fada cikin bacin rai ta sake juyawa ta kalli Umar tace " kai kuma,kada kaga kana da iko a kanta kace zaka wulakanta kadake ta,da gayau se yau inkasake taba zali da sunan duka,to kasani se ka fiskan ci macin rai na,kuma zansamo daddyn ku,akan maganan yayi ya gama gidan sa na upper nan ku tare da matar ka,makarantan ta karasa shi a chan,a lukacin auren hapsat." " Se katashi kabarmin wuri,zamuyi magana da ya'ta." Cikin bacin rai yabar dakin,zali kam ko musi ta kasa,se kuka takeyi,meyasa itta YANAYIN RAYUWAN ta yake zuwa ahaka😭. Cikin damuwa mom ta kalle tace " kiyi hakuri,yata ki dauki kumai amasayin kaddaran ki,insha Allah wata rana zakiyi alfahari da zabin dana miki,fatana Allah baku zaman lafiya." Haka tai tamata kalamai masu kwantar da hankali,har ta hankali zali ya dan kwanta,suka wuce makaranta. Yau tunda taje school,jikin ta ba kuri,ku hirama sama sama sukeyi da zali,kuma kuda uncle kyari ya aika a kirata taki zuwa,har akatashi,ba karamin haushi yajiba,amma yanuna bai dameshi ba. Tunda lukacin ya Umar ya fara bin hanyan da zali zata soshi,wata ran ya dauke ta sutafi shopping,sloon,da sauran su,wataran shike kaisu school. Amma duk abunda yakeyi nan zali kam ku'a jikin ta,ya Usman daya lura da haka ba karamin dadi yajiba,haka mom da dad,gidan da dad yake ginawa ma ankusan gamawa. Yau yakama Saturday kuwa nagida,ummi ce ta ziyar ci zali,suna dakin su suna hira,khalil ne ya shigo yace " Zali ya Umar yace kikai mai abincin shi adaki." Yana fada bai jira amsan taba ya fita,ummi ce ta kalle ta tace " hmmm! Masu miji,se kikai mai ai😜" Turo baki zali tayi tace " banson iskanci,ke waya hanaki auren." Dariya ummi tayi tace" kije de nikam,kafun ta biyoki nan." Zali tace " mtwssss,base ya biyo ba,ni manta wa nake dace wa innada mij." Tabe baki ummi tayi tace " zama ki tuna ai,banza kawai." Tashi zali tayi tafita,ummi na zulayanta,tana fita ummi ta dauki wayan zali,ta hau kallon pic's. Zali na fita ta wuce kitchen,ta hado abinci a flasks da duk wani abunda ze bukata tayi dakin su ya Umar. Da sallama ta shiga,bayabu ba fallasa ya amsa,sede ya Usman baya dakin,zaune ta same shi a kan sofan dame dakin yana lasa waya. Ajiye tray din tayi,kanta akasa tace " inna wuni." Murmushi ya sakar mata yace " lafiya yammatan yayah,ykk?" " Alhamdullilah" ta amsa mai,har yanzu kanta akasa. Jin baisake magana ba,yasa ta tashi zata fita,riko hannun ta yayi yace. " se inna bayan bakiyi serving dina ba." Fada yana sakar mata keller smile dinshi,ba musu ta dawo ta zauna tafara serving din shi. Tana gamawa tace " yayah se anjuma." Kallon ta yayi yace " inna gama waze fitar?" Wani haushi ne taji tace " yayah ummi fa tazo muna tare." " Zamana kike kona ummi?" Yafada yana lasa wayan shi,ba musu ta juya ta zauna,ta ta kure gu daya,se kunguni take ciki ciki,duk ya lura da itta amma ya share ta. By halimatusadiya saleh( saliha)🥰 Love u Fan's,i need u prayers,yar sister na ba lafiya,na gode Allah bar zumunci.🙏🏻 😞 YANAYIN RAYUWA😰😱🌸💐💐🌷🌷🌸🌸. By halimatusadiya saleh( saliha)🥰 Fara cin abincin yayi,chan ya dago ya kalle ta yanda tayi ya matukar bashi dariya,murmushi yayi yace " Kin ci abinci ne?" Bata dagoba tace " ehh" Bai kara ce mata kumai ba,se da yagama cin abincin,kallon ta yayi yace " Gyara wurin,se ki fita da kwanukan." Ba musu ta tashi,ta fara gerawa,kasa kasa tace " mutum ne yana cin abinci kaman yaro,mtswww." Tafada taja tsaki,bata san ajita ba,ji tayi yace " Ki kasani koni yaron ne?" Gaban tane yayi mugun fadowa,marairai cewa tayi tace " Dan Allah yayah kayi hakuri bada kai nakeyi ba." Yace " to dawa,ko mu ukune a dakin nan?" Bata kara magana ba,dun tasan intayi kuskure kadan ze hukun tatane. Kallon ta yake yi har tagama,ta dauka zata tafi,har ta issu bakin kofa yace " I will call u,saura kikashe wayan." Batace kumai ba,ta fita, kitchen ta fara wuce wa ta ajiye tray,kafun ta wuce daki. A kwance ta samo ummi,data gaji da jiran ta,ummi na ganin ta,ta ya galla mata harara tace " Hmmm! A hakan ma wai ba'asonshi amma andade,inana sonshi ya kenan,kin ajiye ni kinyi tafiyan ki." Hararan ta zali tayi tace " banson iskanci, ni nace kijiran,imma na dade mijinki ko mijina?" 🤣🤣 Dariya ummi tayi tace " a'a,manya masu miji eyye,ai daman bance mijina bane." Tace " kima fada man kigani." Hmmm! Su zali masu miji manya. A haka suka ta hiran su har la'asar yayi,sukayi sallah,inda ummi koh tayi shirrin kumawa gida. Dakin mom,sukaje tayi mata sallama,inda mom tayi mata kyauta mai yawa,harda kudin machine 2k,ummi tayi ma mom godiya,kafun suka wuce zata tafi. A compound na gidan,suka tarar da ya Umar da ya Usman suna hira,gaishe su sukayi,za su wuce,ya Umar yace " Ku jirani mukai ta gida kawai." Basu musaba suka jira shi,tun fitan su ya Usman hankalin shi ya kuma kan ummi,amma se ya dake kaman ba shiba,dun ganin kar kanwan sa ta gane,but ya Umar ya lura da hakan. A parking space suka saya jiranshi,cikin gida ya shiga ya dauko key,ba wani mata lukaci ba ya fito. Ya ma ya Usman sallama,ya shiga muta suka fita,a gaba zali ta zauna,ummi koh tana baya. Har gida suka kai ummi,suka mata sallama. A hanyan dawowa, driving yake amma hankalin shi duk yana kanta,motan yayi shiru,ganin shirun yayi yawane,yasa ya kunna wakan umar m Sharif na ta kamani ta kamani alsarki soyayya. Duk abunda yakeyi,tana ganin shi,amma bata kulashi ba,haka har suka issu gida,ba wanda yacce da wani kalla. Yana parking ta fita,ido kawai ya bita dashi,har tashiga kafun shima ya shiga ciki. Maryam ce kadai ta samo a falo,zama itta ma tayi suka shiga kallo,ba'a jimaba shima yashigo,ko ta gunda suke bai kallaba ya wuce dakin su. Kallon su keyi har seda aka kira sallan manghrib kafun suka wuce dakin su,dun yin sallah,aunty hapsat na dakin mom. Maryam ce ta shiga dakin su ya Umar,tace musu daddy nakiran su,ba bata lukaci suka tashi suka nufi dakin daddy. Sallama sukayi,amsawa yayi hade da musu izzinin shiga,shiga sukayi suka samo guri suka zauna,gaishe sa sukayi ya amsa cikin fara'a. Dan shiru sukayi na san lukaci,kafun dad ya dube su yace..... Sorry for short post🙏🏻 By halimatusadiya saleh ( saliha)🥰

Post a Comment for "YANAYIN RAYUWA CHAPTER 15"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...