WATA FUSKA CHAPTER 9 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 9

WATA FUSKA CHAPTER 9

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 9
A hankali ya gangara ya yae parking d'in motanshi, harga Allah baya cikin nutsuwar sa gameda Hafsat, yarasa dalilinsa najin haushin ta akan abinda ta masa abin ban mamaki kuma shine ya rasa meya sanyashi damuwa akan hakan? Ko gun Dr. D'in dayace zeje be biba, ranshine kurin yaji yana matuqar b'aci akan yanda be kula da Nancy ba yau...... Da k'yar ya iya saisaita kansa ya nufi guess house d'in daddyn sa cikin qunan rai,yayi matuqar mamakin jin cewar Mahaifiyar sa ta sanar masa dukkanin abinda Nasara ta aikatawa baiwar Allah yayi fushi me tsanani da har Maheer d'in dayazo d'aurin aure be gaya masa ba daya sani da tuni yarinyar tana waje ana kulawa da ita na mussaman....+ "Yanzu sanar dani wane ci gaba aka samu ajikin yarinyar?" Kanshi aqasa yace anyi nasaran gyaran k'afar harma ta miqe kuma memory d'inta ya dawo normal idan ta k'arajin sauk'i ma aka sallameta zan miyar da ita sokoto" Jinjina kanshi yae ya miyar da dubanshi kan jaridar Daily trust dake hannun shi kamar bazeyi magana ba se kuma yace "Akace baku sanar da iyayenta daga nan gidan aka aikata wa 'yarsu hakan ba,ko miye dalili?" "Ea dama Abba rashin dacewar hakan kurin nagani, bazanso wannan maganar ta fita ba, tunda Allah ya kub'utar da yarinyar, kuma iyayenta ma ba wasu bane basu ma damu ba,ko mahaifinta tunda tazo nan garin basu zo dubata ba, kuma acikin watanni biyun datayi bekira waya so biyar ba yaji ya take ba, hasalima babu wanda yanemi ba'asin sanin inda aka ganta acikin su" kallonshi ya miyar akan Maheer yace "Yace Mahee kai wanine kenan kake gani ko?" Da sauri ya kalli mahaifin nashi ya sani wannan kad'ai ya isa sanyashi ya dinga rigima,muryan shi na rawa yace "Ba haka bane Abba rainane ya b'aci dasu mutane idan basu suka haifi yara ba sekaga ko mutuwa yaran zasuyi ko oho" Gyaran zaman shi yayi "Su waye iyayen nata to?" Kallon Abban shi yayi "A yanda naji dai wai mahaifinta ne ya rasu yabar dukiya me yawa, to ita kad'aice dashi shine se qanin mahaifinta ya auri maman nata ya kuma karb'i dukiyan azuwan ze riqewa yarinya shine fa zaman yaqi dad'i harya saki maman ta ta koma k'asarsu Niger to yarinyar se wahala takesha, yanzu gashi karatun nata ma data gama cin wuyar shi ya lalace sanadiyan haka nazata sunje sun mata defring ashe basuje ba....school d'inda take zuwa wani zubin da k'afa tun daga low cost har D'an fodio" wara ido yae ya jinjina nisan wurin kan yace "Sanda naje sokoto nace zanje naga jami'ar d'an fodio nayi mamakin nisan ta, batada banbanci da jeji ai akwai nisa sosai, harna qosa naga isarmu bazakacemun mutum ze iya zuwa gun da k'afa ba tun daga gwiwa lowcost sabida nasan Gwiwa lowcost ai na sanar maka inada gida acen cen nake sauka idan naje sokoto, da nisa sosai fa" "Allah abba ni shaidane takanje gida da qafa ko tazo da qafa ma, ai wasu mutanen basuda imani" kishingid'a yae kan kujerar dayake kai "Kaima meya hana kaje kamata, ina kace d'alibar kace k'awar iyalanka kuma" "Allah ko abba nazata iyayenta sunje" D'an guntun tsaki yaja "Wanda be baka tranport kaje skul ba kaga alamun ze damune dan bakaje ba, kaida kace basa ma zuwa dubata kuma kace ko a waya basa kira, yaya zakayi wannan tunanin, yanzu abunyi mu had'e ta dasu sha'awa sedai iyayenta suna haqqin sanin me muke shirin yi, sabida haka ka shirya zamuje gobe sokoto" Be isa yayi musu ba dukda ba hakan yaso ba, had'e ta dasu sha'awa na nufin komawar ta london kenan gaba d'aya da zama da karatu toshi yaya ze rayu babu ita a rayuwarsa?....seda abban yace "Ka tashi ka tafi mana",tukunna ya miqe,yana godiya yabar parlor d'in. *************** *Bayan kwana biyu* Har akayi discharging na hafsat maheer be k'ara komawa asibitin ba, abun duk ya dameta Islam da kanta tayi mamakin hakan duk sanda tace asibiti driver ke kaita tayi tambayar harta gaji amma be kulata ba, yau da akayi sallamar Reedah tana wurin kasancewar me gidanta ya sanar mata za'ayi sallamar, da suka gayawa maheer ma se cewa yayi akaita gidan umman shi, sunsha mamakin bece gidan islam ba, amma haka suka d'unguma har islam d'in. Hannu bibbiyu umma ta tarbesu aka kai hafsat b'angaren da aka ware mata kusa dana su Shauty da sophie har ta k'ara jin sauk'i su kuma sukayi k'awanya a parlor suna zuba zance Umma se washewa islam baki tabke tana sakota a hira ita kuwa kunyarta sosai takeji ta kasa sakin jikinta, su sophie se yatsina suke an kai musu ita kusa dasu sufa basuga dalilin nanuk'e musu datayi ba yarinya se san abun duniya sun tsaneta wlhy..... Maheer se bayan isha ya shigo gidan, bayan sun gaisa dasu Reedah ya buk'aci sanin inda take aka gaya masa tana can sama...kai tsaye saman ya haura ya k'wank'wasa d'akin a hankali, cen k'asan muryanta tace "Bismillah, wanda seda ta fad'a so uku tukunna ya jiyota, ya turo k'ofar a hankali ya shiga, kallon sa tayi dan batayi tsammanin ganin saba ta sare akan ya tafi abunshi kenan " Sannu da zuwa yaa maheer" shine abunda ta fad'a kanta a k'asa...Fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "Yauwa ya jikin ki?" "Da sauk'i Alhamdulillah" zama yayi akan gadon cen nesa da ita "Ga sabuwar waya na siya miki dan taki ko labari, nayi k'ok'arin miki welcome back na layukanki duka biyu sedai d'ayan na Airtel dole sekinje da kanki wannan na mtn gashi nan banma gwadaba amma bari na gwada akan wayan yanzu" murmushi tayi "Allah ya k'ara girma na gode sosai" Be kulata ba har messages suka fara dira akan wayar daga kunnawa kai idanshi yae akan wata number data turo message yafi so 20 se shigowa sukeyi ba adadi ya tsaya cak!! Akan lambar ya soma bud'awa ("Nayi kewar rashin ki nayi kukan nisan dakika mun nayi dana sanin rashin zame miki dan sandan ciki domin baiwa lapiyarki kariya, nayi sake dakika zamto acikin halin rashin tuna komai gaki kwance k'afa a karye Allah ya baki lapiya...Naki me k'aunarki Mahal") Wannan shine saqo na farko dayayi tozali dashi a wayar ("Babu a duniya me iya sanya na nisanceki ki warke ki dawo gareni muyi auren mu na soyayya...Naki Mahal") ("Ina kukan rashin ki, ina keawarki abar sona, Allah ya tashi kafad'unki") haka messagea suka dinga shigowa sama da kasa na Mahal ya zauna harya manta da wanzuwarta agun seda ya gama karanta su tsaf!! NA K'ARSHEN ne yafi tsorata shi ("Labarin samuwar lafiyar ki ya riske ni daga gun Mahal!! Naji ance kin warke ina nan zuwa gareki soon tawan, bazan rayuba idan baki abar sona, ina fatan kiga saqon nina") wato dama Mahal shiya miyar wani sha ka tafi? Lallai ma wannan yaron yazo da salon raini, mik'ewa yayi yana kallonta, ta tabbatar ba haka idanshi yake sanda ya shigo ba to meye damuwar? "Bana son wannan sim card d'in bazakiyi amfani dashi ba, zan siyo wani da safe, ki rik'e wayar a gunki" kai tsaye yacire layin a wayan ya ajiye mata wayar, cikin rauni tace "Amma yaa Maheer naga layin ya hau lapiya, kuma komai nawa na school da bank da komai dashi nake using" wata muguwar harara ya wurga mata, cikin d'aga murya yace "To nace bazaki yi amfani dashi ba ko kinada ja ne!" Nan da nan idanta ya kawo ruwa "Kayi hakuri ba haka nake nufi ba, abari da safe akawo sabon" seyaji kuma duk beji dad'in hakan ba daya mata amma bece komai ba ya fice daga d'akin... ************ Bayan ya tafi kuma dukse ya kasa nutsuwar sa, ya gigice ya d'imauce ya rasa meke masa dad'i yafa kasa gane inda zuciyar sa ta dosa gameda Hafsat, abu k'alilan ya fusata sa akanta, abu kad'an indai ya shafeta yake susutar dashi wani zubin, yau kam be tab'ajin kwatan kwacin azabar radad'i da zafin zuciyaba kamar irin wanda yaji yau ganin saqon nin nan, yana mamakin wanann dama Mahal son ta yakeyi yake masa wayau? Lallai ma yaron nan.... Islam ma bata ganewa komai ba yau din dasuka je, sabida yasha mur baya ko magana,beko kwana a d'aki d'aya da ita ba Tunda su ummul suka bar sokoto batajin dad'in rayuwar ta, idanda za'a kasheta kuwa bazata fad'i wane garin take ba, abin mamaki gidan datake zaune daga ita se Ameen ace wai wayarta an sace ba wannan bane abun mafi mamaki shine Ameen yaqi ya kawo mata new phone kullum k'aryar ya manta yake abubuwa sun masa yawa, abu mafi ban takaici shine yanda yake ficewarsa ya barta ita kad'ai kamar mayya danma Allah yasa akwai wata matashiyar yarinya me riqa mata aiki, babu abu guda d'aya data nema ta rasa agidan amma bata cikin nutsuwar ta, ga karatuntama yabi ruwa ada bata damuba sabida ta samu auren me kudi amma a yanzu ta soma nadamar yin auren gaggawa, data bari seda ta hada kwalin degree dinta data more wa rayuwarta amma yanzu gashi gadai dukiya amma ko wayar hannu ta gagareta, abin duniya ya dameta sosai takeso taji muryan Baba azumi amma abu ya gagara!!!+ Baba azumi kuwa cewa tayi wai ance idan anje qasashen waje ba'a samun lambar mutum watak'ila suna london, da wannan haukan duk wanda ta samu setace masa ai sun tafi london yawon shak'ata wa...sedai fa aljihu ya soma yi musu k'asa dan tunda aka kai ummul Ameen ko tsinke be kuma basu ba, gwara ummul takan basu amma itama yanzu shiru tunda batanan, bill kawai na wutar gidan yasoma gagarar su, Abin duniya ya dami Baba iro yayinda Baba azumi ke cewa idan sun dawo zata warke har tana cin bashin kud'... Baba iro ganin hakan bazata yiyuba ta sanya ya shirya zuwa kano dubo Hafsat, daganan yayi k'aryan shima ciwo yayi baida ko sisi kuma ko Allah zesa richest man in africa ze bashi kyautar koda shinkafa da taliya ne, haukarshi d'aya daya dena zuwa aikin shinkafar dasuke da amininsa danyaga ya samu ku'di da wannan yawa maheer waya zezo, shi kuwa daya gayawa mahaifin sa sesuka dakatar da tasu tafiya akan zasu jira shi......... ************* A parlor ya tadda Hafsat da sha'awa da Sophie da kuma Umman sa, suna hira amma banda Hafsat ta takure wuri d'aya tana zaune a k'asa ta mik'ar da k'afarta da akawa aiki, sanye take da jar doguwar rigar material me santsi, ba d'ankwali akanta ta zubar da gashinta data tufke dukya cakud'e wuri d'aya sabidar rashin gyara amma daka ganshi kaga na fulanin usul......akwai kwalli a fararen dara daran idanuwanta a lips dinta kuma pink lip balm ne ta saka daya kusa hadewa da kalar fatarta....idanta ta sauke a kansa bayan ya zauna suka gaggaisa Shauty ce tace dashi.. "Yaa Mahii wai Hafsat ce tace mu raka ta salon, amata gyaran gashin kanta,shine nace ta bari kazo tukunna sabida ba escort agidan" Be ansataba wannan ya baiwa kowa damar mik'ewa yabar wurin ciki kuwa hadda hafsat data mik'e cikin dabaru kasancewar zuwanta gidane ta dena using k'arafa, suka nufi sama zuwa bed rooms nasu, har zata shiga d'akin ta Shauty tace "Ki hakura, mu gidanmu ba irin naku bane, bama fita seda tsaro amma idan zaki iya fita ke kad'ai to, dama waze saci talaka yaci wuya" ta fahimceta sarai amma batai magana ba ta juya zuwa d'akin da aka ware dominta kawai tana sharar k'wallah, gidansu zata koma sabida batacewa kowa zata zauna gidan masu kud'i ba bare a nemi yi mata wulak'anci, bayan ya gama maganar da zeyi da mahaifiyarsa ya haura saman ,dakin su sophie ya lek'a yace da ita "Ke ku tashi muje na kaiku nida kamala, da akwai inda zamuje" mik'ewa sukayi suna murna zasu fita an kwana biyu zaune agida tamkar garar kunya...ya juya d'akin Nancy ya shiga da sallamar sa, tana zaune kan gado tayi tagumi " ki tashi muje na kaiku salon d'in" kallonshi tae dama a shak'e take "Ka kaini ni kad'ai nida ko an saceni dama cen talakaceni babu ma me d'aukana, amma karkaje da k'annen ka a sace su" Ne fahimcetaba yace "wannan wace irin magana ce?" Ganin be dace tace masa ga abinda ya faru ba yasanya tace "Naji sunce ba escort a gidan" tsaki yaja "Shi kuma Allah fa? Akwai inda babu shi?" Shiru batace komai ba, waya ya ajiye mata da layi aciki "Ga sabon layin kinan" Batace komai ba ta mik'e taja mayafinta wani yalolo kalar material din jkinta ta rataya a kanta tabi kusa dashi tayi hanyar waje batare data d'auki wayar ba, binta yayi da kallo she's showing attitude waz wrong with her? Ya ayyana a ransa kanya d'age kafad'unsa duka biyu ya d'akko wayar yabi bayanta, har k'asa ta durk'usa "Umma zamuje wankin kai" murmushi maman tayi wannan shine tarbiyan datakeso a wurin yaro hannunta ta riqe "Allah ya kiyaye ya tsare hanya dan Allah kuyi adu'a kafin ku bar cikin gidan" shiru su sophie sukayi sunata yatsina haushin Hafsat sukeji "To Umma inshaa Allah zamuyi" Daganan suka wuce. Dukkansu A baya suka zauna har Maheer yayinda kamala ke tuk'i, a kusa dashi sophie ce se chat takeyi da wani friend d'inta dake london, yana kallon ta amma beyi magana ba har suka isa salon dasuke zuwa yana diresu ya baiwa Hafsat 10k ya juya shida kamala d'aukar mahaifinta daya iso yana tasha. ***************** Dogon jawabi mahaifin Hafsat wato Baba iro ya rattabo game da rashin kud'insa wanda ya kara akan hakance ta hanashi zuwa duba hafsat, ya k'ara da bayanin rashin lafiyar sa itama aka masa jaje Abba yace "Am to Allah ya sauwak'e, dama koda baka zo ba ni dakai na zanje a yau dinnan akan maganar Hafsat d'in, labari ya riskeni cewan kai k'anin mahaifinta ne shine naga dacewar neman izininka, idan babu damuwa inaso zan dauki rik'on ta hannuna harma ina shirin zan had'ata da yarana suje inda suke karatu su k'arisa nasu acen tunda ance wanda takeyi anan yarigada ya lalace amma fa idan babu damuwa" Wani dad'ine ya kama Baba iro shikam ina ruwanshi da inda zata rayu indai zata zame masa jarinsa na rayuwa? Seme dan an kaita wata k'asar shidai burinshi ya had'a alak'a dasu kowace irice ya samu na cefane, Banda Allah ke k'addaro abubuwa aida yace mafarki yake sabida ko a tv beyi tsammanin zeyiwa Alhaji Ali dala wannan kallon ba bare har suyi magana me tsayi haka ba harma ace ze karbar masa rik'on 'ya "Haba ranka ya dad'e meyasa zaka rok'eni ma, Hafsat ma ai 'yar kace wlhy fatana insan a hannun datake amma kafi karfin hakan a wurinmu, nabaka ita halak malak har abada, ko aure ka d'aura mata batare da izinina ba bazanji komai ba dan kuwa kai ubanta ne" Abba mutum ne me matuk'ar son karamci arayuwar sa yana son mutum me kyautata masa, duk yawan dukiyar sa idan kamasa kyauta yanaso, wannan ne dalilin dayasa en k'auyansu ko mangwaro ne suke zuwar masu dashi idan zasu zo sabida sun kula yana san Alkhairi komai k'ank'an tarsa....washe bakin sa yayi ya hau godiya Baba iro har mamakin sauqin kansa yake mutum me dukiya irin wannan amma ace d'an wannan abin yana godiya haka, yarinyar dabata wuce zama 'yar aikin gidan saba amma dan kawai ze rabasu da wahalar ta yake godiya ai sune da godiyar....shine yahau yin godiya har babu iyaka... ****************** Daga baya ne aka had'ashi da Hafsat da kanshi ya mata bayani kuka sosai ta saka masa akan ita bazata zauna ha lallai seta bishi zuwa gida, yace semester dayace zatakai abubuwan asibiti ta yarda tayi carry over amma yabarta ta koma sokoto, dayaga rarrashi bazeyi ba ya zazzageta har yana cewa tana masa bak'in ciki ze samu arziqi ta hanyarta, haka suka rabu ba dad'i kamar zata mutu batasan ta yaya zatayi rayuwa acikin wannan d'inbin mak'iyan? Kaf gidan Anty Reedah da Umma ne kurin ke nuna mata so ita waccen Nasarar ma bata taba ganin taba kuma tsoronta takeji tunda taji wannan labarin abakin Islam. ***************** Dukkanin ahalin Alhaj Ali sun taru a babban parlor gidansa ciki kuwa hadda Anty Nasara, bayan dogon bayani akan hafsat ya shaida musu rik'onta ya dawo hannun sa sabida haka ta zama 'yar uwarsu be yadda akomai su ware taba har a 'yan uwa a nunata amatsayin 'yar sa... Agaban sa kowa yayi haba haba da zancen amma ana watse taron Anty Nasara ta had'e kan k'annen ta ta zuga su akan aci ubanta, Fareedah ce kurun tayi ta fad'a bata cikin su, su kuwa Anty Nasara tajasu suka sameta a d'akin ta ta idar da salla....kai tsaye wanka mata mari Nasara tayi seda taga wutar lahira "Matsiya ciya er isa, kinzo dole sekinci arzik'i ko? Kinaso lallai sekin shafa mana talauci ko? Toki sani wlhy wuyace zata saka kibar gidan nan da k'afar ki" kuka ta saka sosai me ban tausayi har bayan dasuka wuce bata dena kukan ba Ummul dai yau ta shirya zuwa yawon zaga garin dabatasan wane garin bane, dan haka ta fito da hijabin ta sanye tana neman hanyar daze sadata da gate d'in gidan tayi hanyar waje abinta kan Ameen ya dawo.... Tana k'arasawa taga gate d'in a k'ulle ta ciki mamaki ya kamata ta shiga waige waige, idan har aciki aka rufe toko tabbas da akwai wanda ya rufe d'in tunda Ameen baya nan me hakan yake nufi kenan? Tasoma shiga ko kwanto game da al'arin Ameen, ga alama ma babu wani gida a kusa dasu bata hango roof ata saman gidan ganin tunanin ta baze k'areta da komai ba ya sanya ta juya kawai zuwa cikin gidan kanta yana matuk'ar sara mata tana cikin k'unci da bak'in ciki da takaicin kalar rayuwar datakeyi.....+ *************** Islam tanaso tace zataje gun Hafsat amma bataga fuska ba agun maheer, hasalima tun daga ranar bata k'ara ji yayi maganar hafsat ba, takula yaji haushin abinda ta masa......Haka ta daure ta kirasa a awaya "Honey dama zancene dan Allah kozanje na duba hafsat?" "Ok kamala yana zuwa nanda 30 mns" shine abinda ya fad'a tare da katse kiran... Bata wasu en damu ba dai tace "Nagode honey" Bece k'ala ba ya datse kiran...ranshi a matuk'ar b'ace yake dukkanin abinda Anty Nasara ta aikatawa Hafsat a kunnen sa yana ji, kasa tsayawa jin sauran yayi islam ma ya d'auki wayar tane sabida ya kula rashin walwalarsa ya sanyata acikin damuwa, ita kuwa Anty wlhy dashi take zancen!! ************* Be nemi Hafsat ba yabar gidan gaba d'aya koda islam tazo shi yabar gidan, A d'aki ta samu Nanuwa tana kukan ta juyin duniya tayi amma tak'i sanar mata me aka mata, sema daga baya takewa islam magana ta roki a karb'o mata kayanta daga kano gaba d'aya..... **************** Bayan isha ya shigo part d'in nasu,kai tsaye d'akinsu ya nufa su yaran su sophie, bayan sun gayar dashi ya kallesu fuska a had'e "Zuwa nayi in gayamuku naji dukkanin abinda Nasara ta sakaku kukayi ina tsaye jikin k'ofar d'akin kuma ke shauty na tabbatar kin ganni ko? Toku sani wlhy dama kunsan halina, kuskure daya naji kunwa yarinyar cen Allah ne kadai ze rabani daku, danjin zataje london tare daku bashi zesha a kitsa muku mugun abu kuma ku dauka ba, ina gargadin ku akan fita harkar ta idan ba hakaba zan muku mummunan hukunci kuma zan gayawa Abba ya miyar daku Bayero university duk a huta" Am batar za'a maidasu nan yafi komai d'aga musu hankali suka hau ban baki da ban hakuri....daganan d'akin Nancy ya wuce ya tarar islam na ciki suna tare, bayan sun gaisa yace da islam "Zamuje gida ki sauka k'asa kiwa Umma sallama" Ba musu tawa hafsa sallama ta sauka ya fuskance ta sosai "Na sanarwa Baba iro ya bayarda kayan ki dake kano duka, credentials dinki kadai nace ya turo a motan haya gobe, to ma driver daya kaishi ze dawo dasu,koda wani matsalar ne? " Ni a gaskiya da akwai sababbin kayana fa danakeso acikinsu, kayana na bikin ummu da komai fa yanacen, hijab dayane anan kuma babu Niqafi" kallon mamamki ya mata yace "To Nancy ba anan sena siya miki wani kayan ba" mik'ewa tayi ta soma doddoka k'afanta a k'asa "Wlhy Allah ni inason kayana, dan annbi kace a kawomun" shiru yayi nad'an lokaci kanya zaro waya ya kira Baba iro akan a hado da wasu daga cikin sababbin kayanta da kuma takardun sannan nikafanta amma banda hijabai.....Ba msu yace to ya kalleta "Ya isa,hijaban ki shirya gobe zakuje da islam kasuwa seku siyo ko kuwa?" Shiru tayi secen tace "Yaa Maheer inason inga ummana dake Niger kan in tafi inda kukace" Dariya ta bashi wai inda kukace😀 ..... STORY CONTINUES BELOW "Nanda kwanaki uku ki shirya nizan kaiki da kaina" murna tashigayi har ya hango hakan zataje Niger, Sophy ce ta rugo d'akin "Yaa Maheer wai kazo inji umma, anty islam daga tasha agwaluma taketa kelaya amai harta kasa tashi ma" Yariga ta fice a d'akin da gudinshi yaje k'asa, be damu da umman dake kusa da islam ba ya d'ago ta zuwa jikinsa, kallon umma yayi sabida neman k'arin bayani tace "Kaga waifa agwaluma yaran nan kesha shine tana ganinshi tayi zallo abata, anan gidan ko girkinmu batasanci sabida kunya har nayi mamakin agabana take cewa a samma ta abu nasan islam da kunya, shine fa tanashn biyu se naga ta ruga tun tana zuwa ta dawo harta gagara yanzu na share wanda tayi anan acikin minti biyar tayi yakai so hudu fa" kansu karayin magana se wanin aman, duk ajikin maheer tayishi be kulaba yakira fareedah, kai tsaye asibitin su aka kaita, gwajin farko ya nuna zaman ciki daram na wata d'aya da satuka uku harda kwanaki.....Murna a wurin Maheer ba'a ko maganar ta, kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin farin ciki, ita uwar rakiyar wato Nancy ma har mamaki yake bata yanda ya sake yau se nisha di yake yi Islam se nan2 ake yi da ita tamkar ze maidata cikin sa....an samu nasarar tsayar da aman ma har ta samu bacci abinta. ************** Yaso suje tare da islam Niger amma umma ta hana azuwan ta dawo gunta tunda batada lapiya, sophie da sha'awa su musu rakiya tunda kwana uku ne kurin zasuyi...... *************** Sokoto suka fara zuwa, tasha mamakin hakan a gidansu suka kwana d'aya, se washe gari suka doshi hanyar niger anan tasamu damar daukar abubuwan ta masu muhimmanci datake buk'ata bata kuma samu matsala dasu fiyya ba tun zuwansu washe gari suka wuce Niger...... A hanya se Bacci Nancy keyi gashi itane agaba, kamala kejan motar yayinda maheer da kannensa ke bayan motar a zaune, haka har suka isa garin Niger atare.....Mahaifiyarta taji dad'in ganin ta takumayi farin cikin jin tabar hannun azzaluman cen, tayiwa maheer godiya sosai, seda sukayi adadin kwana kin su sannan suka juyo zuwa kanon dabo inda koda suka karasu Nancy ta samu visa na zuwa london karatu inda tare da Maheer d'in zasuje se yaga yanda za'ayi ta samu komai cox ko maganar admission ba'ayi ba sesunje sabida k'urewar lokaci! ******************* *London* A babban birnin london sukawa kansu masauki a wani k'ayataccen gida me kyau tsarin ginin turawa yayi kyau sosai, 3 bedroom flat ne se wani cute parlor dake hade da kitchen da dining d'insa, Har yanzu dai Maheer baya sakewa Nancy, yayinda su kuwa su sophie suke matuk'ar jin haushin ta akan niqafin datake mannawa, sun tabbatar a london tayi kad'an tayi yawo acikin sa shisa ma suka gayawa maheer ya mata magana. Kallon sosai ya mata bayan daya kirata yace da ita cikin isa "Niqafan nan dakika zo dasu dole ki ajiyesu, bazasu lamunta ba anan kam, su komai da camera sukeyi kar wani ya aikata wani abu zargi ya tabbata akanki tunda face dinki a rufe yake, ya kamata ki sani nanba gida bane, tunda yake dama fuskar ki ba al'aura bace ba seki hakura da wannan aqidar" shiru batace masa komai ba yaci gaba "Kin fara pure English yanzu wanne zakiyi anan?" Kallonshi tayi idansu suka gauraya lokaci d'aya k'irjin dukkansu ya buga, ta kasa d'auke idanta akan nasa, shi d'inma ya rasa dabarun yi ayau idanshi akanta baya ko k'iftawa, murmushin dabasuda niyyan yiwa juna suka sakarwa juna kan daga bisani yace "Yaya dai sefa ince sekin biya kud'in wannan kallon, kinga fine boi kin wani kafeni da ido" shagwab'e fuska tayi "Allah ni yaa maheer ban kalle ba, kaine ma kake kallona shisa har kaga ina kallon naka" dariya ya d'anyi "Kin sani dai matana batada k'aton goshi ni banason mace me qaton goshi" tabare fuska tayi ta tunzuro baki "Ni yanzu kawai se a rik'a cemun wai me goshi,bayan nasan wlhy ni nafika kyau so dubu" Besan dalilin jin yanason ci gaba da wasan ba, seya tsinci kansa cikin nisha d'i yana k'ara fad'ad'a fara'ar sa yace "Oho dai nidai banason k'aton goshi da wani k'aton kanta a wurin" dariya itama tayi ta zauna da kyau "Yaa Maheer yanzu wane course zanyi wai?" Murmushi ya mata "Ke kika zab'i English dacen?" Girgiza kanta tayi alamar aa tace "Noo Law na saka ban samu bane" gyaran zaman sa yae "Kijewa law d'in mana ko kuwa?" Haka dai yayi convincing nata ta yadda zata yi law din.... A wannan daren kasa bacci Maheer yayi ya gama k'udurcewa kansa cewar lallai seya mallaki Hafsat!!! Ya fahimvi ba wani zagaye santa yakeyi sona hak'ika bawai na wasa ba, to Amma ta yaya? A yanda yakeji ze koma Niger ya ajiye aikin lecturing ya dawo ya rik'awa Abba wasu harkokinsa na nan, daga nan ya dakko islam tazo itama taci gaba da karatunta, babu sassaucin daze samu a nesanta kanshi da Nancy face siyan fashewar zuciyar sa!!!! Tayaya zaman nan ze yiyu? Anya ba yanzu muka fara wasan ba kuwa? Da alama akwai sauran rina a kaba.

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 9"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...