WATA FUSKA CHAPTER 8 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 8

WATA FUSKA CHAPTER 8

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 8
  Yauma kamar kullum Maheer kwance yake acikin bahon wankan sa ya runtse idansa yana nazarin rayuwar duniya...Dukda yake yasan Anty Nasara mahaifiyarsu ta biyo na qyamar talakawa amma sam umma ita bata hakan takan yarda da qaddara sedai kurun bata hulda da talakawa ne ita...komai girman danganta karku idan bakada shi babu ruwan umma dakai sedai idan kazo mata tana haba haba da nan nan dakai, amma ita taje maka batayi fara'arta da haba haba da mutane ya sanya kullum gidan nasu baya rabo da en uwa, sab'anin Maheer da twin dinsa suna qaunar mutane sosai ga fara'a ta mahaifin su dasuka gado ta sosan ma, Matsaloli guda biyu se mutan america su safiya da sha'awa sarakan rashin ji da jiji dakai waisu yaran masu kud'i sune sukafi kowa girman kai a gidan kaf!! Nisawa yae ya qara lumshe idansa yanajin dadin ruwan d'imin dayake cikinsa....rashin memory din Hafsat bashi bane damuwar sa a yanzu,damuwar sa biyu ce na farko dai qafarta yau zasu shiga aiki na biyu kuma rashin maganar ta muryarta kadai yanasi yajita koze samu nutsuwa me sanyi!! Yarasa menene yakeji game da wannan yarinyar abu d'aya ya sani yanajinta har cikin jini,jijiya da b'arqon sa...kai harma qasusuwan sa sunsan da zaman ta acikkn jinjinsa da jijiya sabida sukan amsa suma.....yana yiwa Hafsat Son so!!! Qaunace daga indallah be tab'aji yana sonta da aure ko soyayya ba amma ya kasa fuskantar inda zuciyar sa ta dosa akan hafsat!!!! Haka ya gama wankan sa ya fito ya shirya tsaf ya nufi asibitin..... A kan hanyar zuwa asibitin islam ta masa waya dayike tana sokoto Hafsat tare da Mahaifiyar ta take.....+ "Honey dama cewa zan maka ko za'a d'auke lokacin bikin nanne naga saura kwana bakwai ko IV ba'a kawo ba gidan ma harsun soma mgana" Sajen fuskarsa ya kaiwa laluba kanya qara kame staring yace "Afwan Babyna, wlhy rashin lapiyan hafsat ne ya sanya na shafa gaba d'aya da zancen iv d'in nan amm kuma kinsan abba daddy baze tab'a sauya date d'in aurena ba sabida commitment nasa yagama schedulling da komai akan hakan,so yanzu inaga zan miki transfer seki nemi wani buga iv a garin naku ya buga muku naku na mata, na daurin auren ma daddy ya aiko nine zan aiko dashi but na manta wlhy" Bataji dad'in kalaman saba koda yike itama tanada damuwa sosai akan ciwon hafsat amma tana ganin be cancanci ya shaagala da sha'anin auren ba akan shi ace saura sati d'aya,cikin kasala ta furta "Amma Honey hakan ai ba daidai bane, daga wurinku ake aiko da kati da alawa a al'adar sokoto fa" Haka kawai ya saka mata fad'a "Haba Islam!! Ke bakya ganin ina cikin tashin hankali ne inada patient? Agidan mu wayakeda lokacin zuwa sokoto yin wannan abin, kinga dire al'ada gefe zanwa Ameena transfer koma namai magana asiya komai akai muku ina idan friend dina yazo babu damuwa?" Sekuma ya qarashe maganar cikin sigar rarrashi, hakuri ta bashi sukai sallama akan gobe za'aje akai.... *************** Tunda yaje asibitin ya kasa sukuni cox ana kan aikin qafar basu fito ba, tunawa da yae agidan sa na kano daza'a kawo islam akwai wuraren da babu funiture ya manta ba'a saka ba, tsaki yaja ya kira islam "Honey ina wuni yaya anfito aikin ne?" Ga alama tunkan su fara magana harya qosa da maganar "Ammm cewa nayi kin iya tuqi kuwa?" Bataji dad'in yanda yae ba amma jiki a sanyaye tace "Ea na iya amma automatic kawai ban iya manual ba" jinjina kansa yae kamar tana ganinsa "Kije gidan cen tunda key yana hannun ki ki shiga bed room d'ina ki duba a drower mirror akwai key's na motocin gidan farar jeeb dinda ke gidan kawai ce auto seki dauketa, idan ackin qannenki maza wanda ya iya tuqi seki bashi benz black sabida hidin dimun gida ke kuna ga naki hidima, sannan kuma gobe zan aiko kamala dukkanin abu nawa dayakeda muhimmanci agidan nan ze kwashemun shi zuwa sabon gidanki na sokoto, ku koma wannan gidan keda en gidanku da kowa ma, amm sannan kuma akwai d'akuna biyu acikin gidanki na kano dava komai aciki yaya kikeso ayi dasu, a zuba wane color zan kira company tun ban manta ba, amma se kuma nangidan shima daki biyune da furniture sauran tile ne kawai me za'a saka zanwa wani company magana a sokoto yazo yae wannan gyaran" Godiya taita masa kantace "Dan Allah Maheer hidimar nan tayi yawa ka taimaka kabarshi a hakan zamu saka anan din, Allah ya saka da alkhairi yabar qauna na kanon ma inda aka gyara ya wadatar" Shiru kamar bazeyi magana cen se kuma yace.. "Amm dan Allah salaha karkice zakiyi bidi'o in nan wlhy samun lapiyar hafsa ce a gabana, ki taqaita zanzo iya dinne kinji babyna, idan zakiyi jmahagulgulanki kiyi amma karkice ban zoba" Numfashi ta fesar ."Dinner da walima kawai zanyi karka damu, se magaana ta gaba yaya zancen tariya sokoto ne ko kano" gyaran zamansa yae "Kano za'a kawoki Mana ai nanne garinmu, abu na biyu sokoto sabida nan nakeyin aiki dole mu koma sannan na sanar dake bazaki ci gaba da karatu bako? Zan miyar dake wani skull daban bansan wannan yawon" haka taita binsa da toh har sukai sllam, annan ta durqushe taita kukan wahalar data daukarwa kanta... Lapia lau aka wa hafsat aikin qafar anyi nasarar daurin sedai fa dawuya be karkace ba se wani hukuncin na Allah. *************** Yau Ameen da ummul suna zaune a parlor ya hade girar sama data qasa, tamkar be taba dariya ba ummul ta kallesa tace "Yaa Ameen banida lapia ciwon mara nake da yawan tashin zuciya gashi daga zaran na zauna kome nake se bacci" wani annashuwa da annuri ya bayyana a fuskar sa na lokaci d'aya ya kalleta "Auu haba, barin kira miki Familu Dr. Dinmu ko" kallon mamaki take masa yanda ya sauya to ciwon nata ne abun murna, haka Dr. Yazo ya duba ta ya tabbatar cikine da ita 2 months mamaki ya kama Ameen shida yake da saurin gane ciki, kodan tayi period se biyune ya sanya yake tunanin babu, ya kalli Dr. Din "Takan yi period fa yallabai yazace ciki har 2 months?" Murmushi Dr din yae "Zata dena ne wasu matan sukanyi hakan, so kawai ta dena aikace aikace cikinta baya so shisa take ciwon mara" ranar murna awurin Ameen ba'a magana aikam hafsat har abinda ba'aso seda aka mata!! Kanta ya d'aure ta soma tunanin anya nrman haihuwabaure da watanni biyu hankaline kuwa? Amma dai dukda haka zataga qarshen abin. Bayan sun kammala wayar ne kuma tana tsakiya da kukanta mahaifiyarta ta shigo ta zauna gefen gadon ta kalleta+ "Salaha lapiya dai? Kukan me kikeyi ne haka?" Share hawayentabtae tace tana murmushin yaqe "Dad'i nakeji zakuji dad'in rayuwa ta dalilina akan auren da zanyi Inna, Maheer ne ya bamu gidansa daya tashi yace mu zauna anan garin, be furta yace kyauta bane amma dai yace mui mooving ciki Inna bakiga gidan ba ya had'u wlhy gidan masu kud'i ne fa" murna innar ta shigayi tana rarrashi akan abin farin cikine ta dena kuka kantace da ita "Dama Nikuwa salaha cewa nai zancen kawo kayan lefe naji shiru har yanzu, en uwa sun soma tambaya kinsan mutane" Murmushi tayi "Bam masa magana ba tukunna amma barin masa waya" Yana wurin Hafsat ya kasa ya tsare seda yaga farfad'owarta yana tsakiyan mata sannu yaji qarar wayansa.....Ganin islam ce ya sanya ya fita waje "Baby" shine abindabya furta bayan d'aga wayar "Ina wuni honey?" Yana murmushi yace "Lapia lau my baby, hafsat fa ta farfad'o" se yanzu ta gane dalilin dinga fadan shi d'azu akan bega hafsan ta farfad'o bane, farin cikinsa yanzu kuma akan ta farfad'o ne "Alhamdulillah Allah ya qara mata lapia" shine abinda ta furta tana murmushi "To Babyna how far meye a qasa" sakon barkwancin da yae ne ya sanya ta saki jikinta takumaji sanyi a ranta, itadai tana matuqar qaunar maheer... "Honey dama cewa nai zancen kayan lefe najiku shiru kasan a nan kafin biki ake kawo wa" Dafe kansa yae shap yama manta "Dan Allah baby kuyi hakuri, kinsan Allah wlhy na manta ana lefe a aure ma, kumafa umma na kullum setayi maganar ranar da twin tamun magana ranar aka samu labarin hafsat duk wannan abun ne ya mantar dani yanzu kinsan meze faru,barin wa umma waya inyaso kinga sena kiraki back yanda mukai" Bataso jin hakan daga gareshi amma setace. "Ba komai dear, sena jika" haka ta ajiye wayar ta kalli mamanta "Ammm Inna wai akwai shirin dasukeyi amma ze kira mamanshi yaji inyaso seya kirani muji yaushe zasu kawo" murmushi uwar tayi "To kuma zancen kud'in saka lalle da wankan amarya shifa yaya za'ayi? Ko kaya zasu kawo ne?" Nanma yaqe tayi tace "Na manta dubu dari ne ya bayar suna nan acikin jakana" Gud'a uwar tayi ta karb'i kud'in tafita waje tana murnar an musu qoqari ta samu kudin yin kayan tuya na gara!!... **************** "Ummana yaya maganar kayan lefen nan ne wai, kinga ni na shafa wlhy" Dariya tae har yana jiyo sautin muryanta tace "Mahi auren nan sekace dole aka maka, waya tab'a manta kayan lefen matarsa? Kaga nifa enkai lefe nakan hanyar sokoto yanzu ma haka sun mun waya akan suna kan hanyar shiga layin su a unguwar....dama Fareedah bata sanar maka ba tare fa suka tafi, itada qawata da qanwar mahaifinku" Daria yae "Nayita neman layinta beje ba kuwa, to Allah ya qara girma ummana nagode sosai".. Kallon kayan aketayi ana mamakin had'uwarsa da uwar dukiyar da aka narka zani babu na qasa da dubu 25 komai yaji, tsayawa fad'ar dukiyar dake cikin kayan lefen ma bata baki ne, Islam tasha mamakinsa har taji kunyar hakurin data kasayi tayi kiranshi sabida kamma su gama wayar aka soma sallama ana shigo da kayan. STORY CONTINUES BELOW Agurguje plss Auren Maheer da Islam dai Babu wasu bidi'o i da akai se dinner se kuwa gagarumar walimar data daddage ta shirya me qayatarwa, Maheer yai qoqarin zuwa gun Dinner wacce ta haska bilhaq anja dala an cuci naira kuma manya manyan en kasuwa sunzo anci ansha an wakita, islam kam tayi kyau na nunawa sa'a Maheer duk yanda ka kalleshi zaka tabbatar yana cikin kwanciyar hankali,nutsuwa da ni'imtaccen farin ciki mara misaltuwa shida kanshi shaidane akan tabbacin son dayakewa islam, dukkanin abubuwan dayaji yakuma gani akanta babu daya da yae tasiri akansa ya manta dasu tamkar yanda ka manta rayuwarka ta quruciya ko kuma tamkar wanda bema tuna komai ba na dangane da rayuwarsa ta jarin taka, yayi murna matuqa da aurensa, yanzu damuwarsa d'aya hafsat dabata magana har yanzu inda yake cikeda tsoron akan bayanin da aka masa kan cewar idan basui hankali ba maganar ma se an dawo fresh cox ko kashi takeji bata fadan zatayi da susuce ta lalace ta zama wata kala wata iri abin tausayi Yana ganin cewar duk abinda ya sameta ta dalilin sane domin akansa aka mata, shisa yake ganin haqqinta yana rataye ne a wuyansa, zuwansa sokoto ma be barota da kowa ba mahaifiyarta ta koma Niger sabida mujinta ya matsa en uwanta na sokoto anyi anyi Baba azumi taqi zuwa ita acewarta ummul ma batada lapia.... So Wata er aikin gidansuce larai kurun tare da ita hankalinsa duk kashi 30 yana gunta dukda murnar dayake ciki a qauyan su aka daura auren inda manya manyan en kasuwar duniya sukazo aka daura auren islam da Maheer amarya ta samu kyautar mota kusan 5 awurin daurin auren daga wurin abokanan mahaifin maheer se murna mahaifinta keyi haka washe garin d'aurin aka wuce da amarya agidanta dake kano. ******************* Amarya duk inda hankalinta yake baya kwance kasancewar rashin adanar budurcinta zuwa gidan mijinta, a tsorace take da abinda zeje yazo fad'uwar gaba ya sanyata ramar wuni uku kacal shigowarsu gidanta na sunna ya qara gigitar da ita ainun!!! Haka en rakiyar amarya suka watse zuwa masaukin da aka ware musu aka barta ita kad'ai qwallin qwal!! Girjinta be dena bugawa dukda gyaran data samu daga Anty billy... Batasan yaya mijinta ze kalletaba ba akan wannan abin..tana nan zaune har Allah mad'aukakin sarki ya kawo Maheer da tawagarsa amma sesuka tarar ba qawayen amarya ko d'aya wannan ya basu dama baiwa amaryar kudin siyan baki 500k suka juya... A wannan daren sukai alwala da sallar nafila, sosai darajar islam ta qaru agun maheer ganin cewar tasani sosai akan addinintabya mata nasiha sannan ya bata wuri domin ta kintsa amma abinda ya bashi mamaki haryaje ya dawo bata sauya kayan ba tana takure a hijabin da tae sallah dashi, zama yae ya kamo hannun ta yaji wani asalin laushi me d'aukar hankali da sanya nutsuwa, murza hannun ya somayi a hankali hannun acikin tafinsa gumi yakeyi "Babyna yaya, bazaki sauya kayan jikinki zuwa na bacci ba mu kwanta?" Kallanshi tae se ta kawar da kanta, jikinta rawa yakeyi ya kula da hakan sabida hannunta dayake riqeda se karkawa yakeyi,ya kula hankalinta baya jikinta kuma ga dukkan alamu bata cikin nutsuwarta ko kad'an,alamu ma sun nuna cewan a tsorace take....bayaso ya saka a ransa cewan wai dalilin yawon datai ne takejin tsoro wannan ya sanya ta tattaro nustsuwarsa shima ya janyota jikinsa, mamakin yanda jikinta ke rawa gabaki d'ayansa yakeyi, amma seya kawar "Yau ina tsiwar ne eee matana? Ina tsokanar ina bakin duk sun tafi kema kinsan bawai sassauta miki zan ba, barin lalubo miki kayan baccin ki ko?" Runtse idanta tae, yaje ya bude jerin akwatunan daya gani ya nemo wata riga me tsantsi ya dawo.... Tanaji tana gani ya cire dukkanin kayan jikinta ya zura mata wannan, yauce ranar farko data somajin kunyar wani namiji arayuwa, sanda aka qwace mata budurcinta batasan ya akaiba, sanda ta fada bariki babu tsoro ko kunya a tattare da ita!!! Kashe fitilar dakin yae ya zare jallabiyar jikinsa ya dare gadon sannan ya janyota jikinsa hannunsa ya shinfid'ar ya d'aura mata kanta a saman hannun nasa suna fuskantar juna, hannunsa daya ya sanya ya zagaye bayanta a hankali ya shafi bayanta wanda wlhy babu qarya acikin ni'imtaccen dad'in dayaji da had'uwar jikinsu da shafar dayawa bayanta...runtse idanta tae jikinta se rawa yakeyi tana sauraren yanda yake sarrafa jikinta san ranshi, Maheer sam ya manta a wacce duniyar yake baya tunanin ya tab'a kasancewa akan ni'ima me kwantar da hankali sama da wannan, Murzarta yakeyi tako ina baji ba gani, Kasa hakuri yae sabida beso fara yin wani abu da ita ba yau, amma tunda ya had'a jikinsa da nata ya tabbatarwa kansa Islam d'insa ta daban ce, lalubo bakinta yae ya kai masa cafka, yau kawai duk jarumtar islam seta gagara aiwatar da komai tayi lago se yanda yae da ita, haka ya kaiwa dukiyar fulaninta cafka!! Ya dinga murzanshi a takaice dai seda ya yae mata jiga jiga ita kuwa ta kasa komai banda rawa da jikinta keyi babu abinda take iyawa, koda yazo domin gaabatar da aiwatar da shirin bayan gabatarwa seta sanya masa kuka sabida anan take ganin tagama wulaqanta, yauce ranar farko da islam ta tabbatar wa kanta ta wulaqanta rayuwarta na wofintar da Kanta awurin mazajen bariki, dama ace sanda akai mata fyad'e ta barwa Allah wataqil dabata tsinci kanta acikin wannan halin ba......1 Kwanciya yae ya janyota ajikin sa "My islam karki mun haka mana, ki barni in karbi haqqina idan kikamun rowa wurin wa kikeso inje? Ke kadai gareni islam na jima ina jiran ranar nan,ranar dazaki samto mallakina inyi yanda nakeso dake" Shiru ta masa ya kai harshensa a kuncinta ya lashe qwallan datakeyi sannan ya koma ruwa duk yanda taso ta kame kanta seda ya cimma burinsa da manufarsa akanta, a wannan lokacin daya samu nutsuwa jiyakeyi tamkar ya miyar da ita ciki, Ya kansance cikin farin ciki mara misaltuwa, haka ya dinga mata sambatu yana saka mata albarka me tarin yawa....nauyi da kunyar sa suka dirar mata ta kasa koda motsi haka suka kwana yanata daukinta yayi abu d'aya yakai so biyar, da asuba da kanshi ya mata wanka yana mata fi'ili akan bakinta da ya mutu ita kuma se mamakinsa takeyi bata tab'a koda mafarki tunanin zata samu tarairaya haka daga wurin gwarzon mazajen taba, shuya yane bed sheet ya turashi cikin ingin wanki ya sauya wani, kuma ya hanata aikin komai daga gidansu aka kawo break fasat da kanshi ma ya bata taci.... Se yamma ya qara yin waya gidan nasu aka kawo abinci, sukaci sannan suka nufi asibiti wurin Hafsat.... Bayan sun tsaya yamata umarni da taje ciki yana zuwa, kifa kanshi yayi saman Staring motar tasa ya runtse idansa, yana da damuwa sosai akan yanayin daya riski Islam, ya sani ya shiryawa hakan kuma ya tabbatar wa kanshi ya samu gamsuwa me tsanani a tattare da islam to amma ya rasa dalilin damuwar sa akan riskarta matsayin cikakkiyar budurwa, yana ganin hakan baya rasa nasaba ne da kasancewar sa me tsananin kamun kai da kame jikinsa ga matan banza, ya sani Fasiqi se fasiqa amma a wannan lokacin yana kyautata zaton banda wacce ta tuba! Yana kallon islam a matsayin mace mafi tsarki aduniya baya jeranta ta a matsayin fasiqan mata, kasancewarta kamilalliya a yanzu Allah ne ya masa zab'inta kuma shine yawa alqawarin bazata tab'a ganin wani wulaqanci daga wurin saba danwai be sameta a matsayin budurwa ba, yawa kanshi alqawarin har abada indai ta wannan b'angaren ne bazata tab'a ganin wata alama daga gun saba ta rashin jin dad'i koya wulaqanta tata ba har abada......cikin damuwa yace2 "Allah ka sanya islam ta shiryu kenan har abada, dazan samu wannan dana riqe islam har abada,idan zan iya bada shaida a lahira dasena bayar da ita acikin mata mafi salihanci na duniya"...... Kashe motar yae ya fita waje ya nufi d'aki, acen ya tarar da islam zaune tayi tagumi ita kuwa Nancy ta qurawa tv dake d'akin ido tana kallon wani film...gashinan an sato wani yaro yanata tattalin qwacewa shima seya raja'a da kallon cen kuma se aka qwalawa yaron kwalba akai nan take ta qwalla qara me tsanani ta had'e da dafe kanta, atare sukai wurinta suka ririqeta se ihu takeyi, Islam kuwa itace tae qarfin halin fita waje neman Dr., a d'aya b'angaren kuwa likitan dayake wani dakin duba patient qaran dayaji ya gayyato sa zuwa d'akin, seda sukai karo da islam da sauri yanufi kan Nancy ta gagara nutsuwa ta kwantar da hankalinta se ihu take, cikin gaggawa ya sanya aka kawo masa allurar bacci ya danna mata kana ya nemi ba'asin yanda abin ya faru....Bayani Maheer ya masa, yae murmushi ya dafa kafad'ar sa " karka damu inaga mun soma samun nasara zata samu memory d'inta, hopefully ma yadawo gaba d'aya" Nisawa Maheer yayi1 "Allah yasa hakan, daka duba qafanta naga tayita jijjiga" Nanma murmushi yae "Lapia lau qafan take karka damu kaji" bece komai ba ya miyarda dubansa zuwa gareta yana nazarin yanayinta,se yamutsa fuska takeyi dukda bata cikin hankalinta alamun akwai abinda ke damun ta..... *Bayan sati hud'u* Acikin wa en nan satitiitkan Hafsat ta samu sauqi sosai, kuma tana magana sedai abinda muke tsammani na dawowar memory d'inta abin ya faskara ci gaba d'aya ne ta soma yin magana, kullum Maheer da islam wurinta suke wuni zamu iya cewa rayuwar amarcin Islam ya k'arene awurin sintirin asibiti da jinyar Nancy, Baba azumi dai taqi zuwa haka Ummul laulayi takeyi me matuqar bata wahala yayinda take samun tsananin kulawa awurin Ameen....Batada kowa se islam da Maheer su kad'ai ta sani su kad'ai take gani, acikin satin nan d'aya jal gaba d'aya islam bata zuwa asibitin sabida zazzab'in datakeyi, damuwa sosai take ciki akan yanayin yanda Aunty Nasara ke mata wulaqanci da nunin wariyar launin fata, a shekaranjiya ta sanar mata karta yadda tayi ciki ta haife musu dan tsohuwar karuwa tayi kukan wannan maganar harta godewa Allah amma sam bata gayawa Maheer ba, wannan dalilin ne ya sanyata jin zazzafan zazzab'in daya kwantar da ita, tayi dana sani me tsanani na halin rayuwar data aikata a baya, ta kuma kasa sanarwa kowa dama ace Hafsat d'inta nada lapia dama ace 'yar uwace bata rasa tunanin taba data gaya mata ko zata samu sassaucin abin da takeji...... *************** Maheer yayi wata shaquwa me tsanani da hafsat da har bayason zuwa sokoto kullum idan zeje seyasha fama, ganin tana masa rigima ya sanya yau yace baze ma sanar mata ba ya shirya ta tafi abunshi ya barta da islam, se dare ita kuma ta barta da Inna wacce dama hayarta sukayo domin tana kwana tare Hafsat d'in.....kwana biyu hafsat bataga maheer ba ta soma yiwa islam rigima akan yaa maheer kamar yanda taji qannin sa na fad'a idan sunzo mata dubiya... Da q'yar islam ta shawo kanta ta dena rigimar hadda kukan ta kuwa, abun ya matuk'ar dami islam, ta kasa gane alaqar zuciyoyin biyu, shima a b'angarensa hakanne ko waya ya kira Hafsat ze fara tambaya' yauma kamar kullum tana tsakiya da tunanin nan wayarta ya shiga ruri ko bata duba ba tasani Maheer ne ko daga yanayin waqar dake tashi....karawa tayi a kunne bayan data d'aga kiran a hankali ta furta STORY CONTINUES BELOW "Assalamu Alaikum Honey" murmushi "Amin wa Alaikissalam Baby na ya gida"? Murmushin tayi itama " Alhamdulillah" "Ina Hafsat da jikinta?" Kallon Hafsat d'in tayi a ranta tace "Ni bazece ya nake ba se hafsat? A sarari kuma seta furta " Taji sauqi Alhamdulillah" washe baki yayi "Ki bani ita muyi magana" bataso hakan ba dama kenan ba ita ya kira ba? Badan ita ya kira wayar ba kallon hafsat din tayi ta mik'a mata wayar tana murmushin k'arfin hali....Bata karb'a ba kuma bata kula taba wannan ya sanya tace "Yaa Maheer ne zaku gaisa ki karb'a mana" kallon ta tayi ita ma "Bazan yi magana dashiba bayan ya tafi wani wurin ya barni kuma yace muyi magana bazan yiba nidai" Haushine ya ishi islam na sosan ma ta kalli wayar kanta daqile kiran tasoma k'osawa da wannan iskancin itakam ma gani takeyi tamkar memory d'in Nancy ya dawo rainine kawai dacin zarafi koda ya k'ara kira bata d'aga ba tamai banza Hafsat kuwa ta sanya kuka sekace wata jinjira baqin cikine ya sanyata barij asibitin batamawa hafsat sallama bama, ta barta da inna cena gwamatse masu bazata iyaba salon wulaqanci kawai. **************** Washe gari ma Islam bataje asibitin ba da Maheer ya kira tace masa batajin dad'i shikuwa ya rasa dalilin daya sanya zuciyar sa take azalzalar sa akan yaje gun Hafsat wataqil hakan baya rasa nasaba da cewar da aka masa Hafsat ta soma yin tafiya da kanta kuma Dr. Ya tabbatar masa ta soma samun memory d'inta dan an sanar masa tasoma tambayar en uwanta su Baba azumi dasuke en iska basu zauna jinyar taba Ummul ce kad'ai me yawan kiran waya gashi batada lapia sosai laulayi takeyi kamar me.....Jikinsa har mazari yakeyi akan yaje ya ganta.....kai tsaye asibitin ya wuce daga zuwan sa garin na kano, yaji dad'in ganin ta tana tafiya da qafarta kuma lapia lau ba laifi tayi daidaito da y'ar uwarta sedai tak'i sake masa fuska gaba d'aya ta b'ata ranta...zama yayi kusa da ita ya kamo hannunta "Lil sis menene kuma na fushi? Na kikkira kinqi ki karb'i wayan mu gaisa" kallon sa tayi "Ba komai" ta furta a taqaice da murmushi d'auke a fuskarsa yace "Kinsan Ni lecturer ne a makarantar ku udus dake sokoto, baze yiyu na dinga jeka ka kawoba kano zuwa sokoto akwai nisa sosai" "Udus kuma?" Ta nanata a sarari se kuma ta lula a duniyar dunani...kamar kuma wacce aka tsikara seta warce hannun ta ajikinsa "Innalillahi yaa Maheer dama kaine ka sanya aka satoni ko, dan Allh ka kaini gun su Baba azumi mena maka a rayuwa" Wasa wasa dai da k'yar da sid'in goshi Dr. Ya kwantar da ita da alluran bacci se hamdala sukeyi ta samu memory d'inta back...sedai Beji dad'in hakan data zata ba amma ba komai ze jira farkawar ta seya mata bayani. ************ *Bayan kwana d'aya* Islam da Maheer atare suka shigo d'akin, ga maheer ranshi a b'ace yake da islam akan rashin zuwanta asibiti kwana biyu, sarai ya sani lapiyan ta qalau yakula kishi ne ke d'awainiya da ita dukda yasan akwai kishi amma be dace tayi tunanin kishi akan Nancy ba sabida shi ba komai aranshi akanta se alkhairi kuma kwanaki da yawa tayi tana aikin lada, sadaukarwar data qara mata k'ima da daraja agunsa kwana biyu kuma se wani banzan kishi ya sanya ta b'arar da ladar ta na jinya....Babu wata walwala a tattare da islam amma ganin Nancy na kallonta ya sanya lokaci d'aya ta sake fuskarta tana fara'a taje ta rik'e hannunta sannu Nancy yaya jikin naki? Murmushi Nancy tayi "Lapia na qalau naji sauqi sedai inata ganin jiri, me kikeyi anan tare da Maheer" kallon Maheer ta juya tayi sannan tace "Waya ce dake Maheer ne ya sanya aka saceki ne wai, kinga yayanki beji dad'in maganar ki ba, bakida lapiya kusan watanni uku kina kwance har loosing memory d'inki kikayi shisa kike ganin komai a haka ki kwantar da hankalinki zakiji bayanin komai idan kika k'ara samun sauqi, amma kan nan ki dinga yiwa Maheer adu'a shine sanadin samuwar sauqin ki da taimakon Allah" Batai magana ba, se shine ya kalli Islam "Baby ungo key jeki mota nabar wayana d'akko mun" karb'a tayi da hannu biyu ta juya ya zauna a kujerar dake fuskantar inda take kwance "Hafsat yaya jikin naki?" A maimakon tayi magana seta d'auke masa kanta gefe d'aya, be qara cewa da ita komai ba ya zauna kurin yana nazarin ta har Islam ta shigo da sallama a bakin ta, miqewa yae ya karb'i wayanshi sannan yace "Baby barinje gun Dr. Zamuyi wata magana ne, da wuta na biyo tanan din idan na gama dashi idan kika gama zaman asibitin sekimun waya na turo miki driver yazo ya d'aukeki" kwanciya tayi asaman faffad'an qirjinsa "Mesa yau kawai zakace bazaka dawo duba qanwar kaba" murmushi yayi "Daddy yazone dole na ganshi yau bansan se yaushe zamu zauna ba, idan yana gari koke dakike matana bakida guarantee xaki ganni bare kuma k'awarki" Bataji dad'in maganar daya fad'a ba kanshi tsaye agaban Nancy amma setayi yak'e "Idan dai zan kwana a saman qirjin kan nan toba damuwa, Allah ya tsare" Be qara kallon Hafsat ba ya fice abinsa..... Ko kalma qwaya d'aya tak bata rage ba daga cikin abinda ya faru ta sanarwa Nancy, kuskuren ta d'aya shine Maheer be sakata aikata aikata hakan ba na biyu kuma bashida niyyan sanar mata cewan Antyn sa Nasara ce ta sanya amata wannan aikin, acikin labarin ta sanar mata zancen aurensu da maheer da dakatawar karatun ta itama....Nancy tayi kuka tamkar ba gobe, ta godewa Allah daya kub'utar da ita amma taji storon jin wai 'yan uwan Maheer suka kuskureta da islam suka mata abinda aka mata tunawa da abinda ta gani a jejin ne ya sanyata soma karanto adu'a tare da rufe idanta.

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 8"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...