WATA FUSKA CHAPTER 7 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 7

WATA FUSKA CHAPTER 7

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 7
  Kai tsaye fareedah gidanta ta nufa tae wanka tae salla ta zauna ta qurawa wannan pic d'in ido ita sam ta kasa nutsuwa akan wannan maganar, yaya zaka dauki rayuwar d'an uwanka musulmi ba komai ba? Ko rayuwar arne babu wanda yace ka dauka ka kashe kace kaci bulus maganr nan da daddy keyi akan qyamatar talakan da Anty Nasara keyi har yaje wannan wurin!! Yasha yin fad'a akan korar mutanen datake yi idan sunzo masa, yakance mata yana tausayin ta kar wata rana wannan qiyayyar datakewa talaka ya janyo mata wata musibar, gashi yanzu ta fara gani tunkan aje ko ina, sabida tsabaragen iskanci da sonkai gashi nan ta soma safarar mutane....."Bazan iyaba!!!" Ta furta a sarari da d'an qarfi ladiyo me mata aiki tace "Na'am hajiya, Magana kike ne?" Murmushi ta sakar mata na yaqe tace....a gayawa d'an liti ya shirya zan fita, wayarta ta d'auka tawa Maheer waya yana d'agawa suka gaisa tace "Kana ina ne zamui magana dakai ne" "Shirin zuwa sokoto nakeyi ko ince nama kammala sokoton zani" "Idan na roqi aron awa daya zamui magana ban takuraka ba maganar tanada muhimmanci ne" murmushi ya sakar mata tamkar tana gabansa "Ba komai anty Reedah bari nazo" "Ka zauna kawai ni ganinan tahowa gidan naku" sallamah sukai ya zauna a parlor part dinshi yana nazarin dalilin reedah nasan ganin shi cikin gaggawa haka, yaga dai dazu dazun nan suka rabu, shikamma zewa sokoti shigar dare dan yanzu qarfe biyu ta kusa haka ya zauna wurin 30mns kanta iso........ Quryar dakinsa taja shi mahaifiyarsu nata murmushin ganin ana gudunta da zanje ta wuce dakinta abinta..... Zama sukai sannan ta kalleshi "Sorry lele na b'ata maka lokacin ka ko?" Kallonta yae bece komai ba ta zaro wayar ta, ta lalubo hoton dayake tare da Nancy sunsha kyau kamar ango da amarya an dauki hoton daidai lokacin da dukkansu suka daga qafarsu daya da zummar takawa suci gaba da tafiya kana ko wannensu dauke yake da murmushi a fuskarsa se glowing sukeyi........ A hankali ya karb'i wayar ya qurawa hoton ido hoton ya masa kyau ainun ya burgeshi hanun shi yakai ya miqa dan ya tsarsa d'aya ya tab'a saitin dimple nata d'aya daya lob'a besan yaushe hawaye ya zubo masa ba harga Allah wani tausayin ta yaji ya kamashi sabo fili, farkon b'atanta yakansa hotunanta da videon rwarta agaba ya dinga kalla amma yanayin azabar dayakeji a zuci game da ita ya sanya ya dena amfani da wannan wayar zuwa wata, akwai wani waya dasukai da dare shida ita sanda ya mata hidima a gun finner take mai godiya mistkenly ya danna record sanda suke wayar bemasan ya shiga ba se daga baya dayake duba wayanshi yaji shima yakan kunna ya dinga sauraro gwanin tausayi😭😭....... Kallon sa Anty Fareedah keyi cikeda mamaki ya shagala da kallon hoton amma ya gagara ce mata cikanki!!! Matsawa tayi kusa dashi ta riqe hannunsa d'aya ya d'ago ya kalleta tace "Wacece wannan Mahi?" Ta kirashi da sunan dasuke masa wani zubin ko ince yakusa ya zama sabon en gidan wato mahi...... "Anty qanwa tace, kuma kusan watanni biyu yanzu kenan da b'atan ta, ko bekai biyu saura kad'an....ta b'ata b'at anty wlhy, an nemeta an rasa sama da qasa" qura masa ido tae na wasu en daqiqu bilhaq kuka yakeyi kuwa lallai ta b'aci sabida tun suna yara maheer yakeda qarfin hali wani zubin komai girman dukan dazasu masa baya kuka harya girma kuwa baka ganin kukansa sabida dauriya har wani zubin sukan ce masa Biggest soldier.....hannu takai ta share masa qwallan sa akwai shaquwa me tarin yawa tsakanin sa da Fareedah tare suka tashi shekaru biyu ne a tsakanin su Twin brother take kiranshi shima yace mata twin sister har a waya haka sukai saving number's na juna..... "Twin kuka kuma, menene tsakanin ka da wannan yarinyar da kakewa b'atanta kuka, am pretty sure cewan she's not d first person daka samu labarin b'atan ta" "Anty Reedah wlhy mutunci yaufa muna tare gobe aka ce dani ta b'ata kuma shikenan fa anty ko labarinta babu, gwanda ace ta mutu ai ko" tausayin sa taji "Qawar kace?" Qwallan shi ya sanya yatsa ya d'auke "Qawar islam ce, kuma student d'inane, beside munada shaquwar wuni d'aya a tare, bama wannan ba kallon sister na nake mata tamkar ke da sauran en uwana ina qaunar yarinyar nan" shirune ya ratsa d'akin na wasu en daqiqu ya nutsu sosai yana kallon fuskar ta....muryan reedah ya tsinkaya tana magana "Twin akwai damuwa fa" kallonta yae "Mecece damuwar Twin sis?" Sadda kanta tae a qasa "Anty nasarace tasanya aka........."daga nan ta kwashe komai ta gaya masa tun yana gane zancen ta har ya zamana meji amma kurma sam baya ganewa, babu dalilin aikata hakan agun anty Nasara sabida selfish interest nata kawai seta b'atar da d'an adam qwaya d'aya jal!! Jejin Amanawa!!! Ya nanata hakan a zuci se kuma ya miqe kamar wanda aka tsikara ya kalli reedah " Anty fareedah wannan yana nufin kenan tuni Hafsat ta mutu aljanai ko namun jeji sun cinye ta ko?" Riqo hannun sa tae "Calm down twin pls, inshaa Allahu Allah baze bariba wanda suka kaita cen ai muta nene, suba sun dawo ba? Inshaa Allah yanda suka dawo haka zamu nemota ta dawo itama kaji" duk da AC dake bayarda ni'imtacciyar iska me dad'in qamshi hakan be hana shi had'a gumiba, ya kalleta a karo na barkatai yace a yamutse "Anty Reedah da tana raye aida an ganta tuni kusan watanni biyu fa cur?" Tausayi ya bata ta kula cewar akwai shaquwa sosai a tsakanin su kasa magana tae ya sake cewa "Barinje in gayawa umma wlhy Anty Nasara seta gane kuskurenta har daddy zan kira yaji wannan rashin imanin da ta yi" miqewa tae ta riqeshi "Karka soma zo muje gidanta kabi komai a hankali kaji" haka sukaje gidan a hanya se rarrashin sa takeyi har suka isa.... **************** "Amma anty binta hakan yayi kenan, da islam d'ince se ki mun asarar ta,kina nufin kenan dan abinda nakeso yana talaka bazaki tayani sonsa ba matsayina na d'an uwan ki" harara ta wurga masa "Dan ubanka ninace maka abinda akayi laifi nane? Na samar da reedah dataje ta d'akko ka y'ar akuri ce ta aikata waidan yarinyar taganta karta tona azaci mudin masu garkuwa da mutanene, cewa fa kurun a tsoratar da ita ta fasa auren ka ni meye laifi na sema dana dawo ake gayamun" kallon ta yae cikeda takaici da baqin ciki mara misaltuwa yace "Ba wannan ba yanzu ha d'amu da qawar taki ta nuna mana yaran da inda suka kaita nida kaina zan shiga neman ta da police" da dauri ta d'ago ta kalleshi "Da police kuma kanada hankali kuwa sekaje a riqa cewa wai yayarka me en ta'adda wlhy kayi kadan tunkan ba qanwar uwarka bace ba seka qyaleta ai" kallonta yae har idanshi ya kad'a yae jajir se zare mata su yakeyi ita kanta ta tsorata da yanayinsa ya dauke qafarsa d'aya ya d'aura kan d'aya yace "Anty Nasara ki sani wlhy baki kaimun cenba, na rantse da wanda rayuwata take hannun sa akan Hafsat zan iya yanke jinin dake yawo nawa acikin naki, zan yanke alaqa dake ta har abada, zan rabu dake rabuwa me girma zan nisanceki nisan ci me tsanani wlhy summa tallahi zan tsaneki tsana mafi muni a rayuwa!!! har a wurin Allah banida laifi idan nayi hakan sabida baki d'auki rayuwar d'an adam a bakin komai ba, zan kuma gayawa Daddy zan sanar masa cewar bakida imani yanzu kin sauya daga Fatima Bintar daya haifa kin zamo me kisan kai me gardawa,gwara miki tun wuri ki dawo hayyacinki zan rufa miki asiri na hana en sandan dogo bincike na binne sunanki kimun bayanin su dan naje nemanta da kaina" Mamakin kalaman sa ya sanya ta gaza furta koda kalma d'aya ta hango haqiqancewa a kalamansa iyakar gaskiyar sa kenan fa!! Reedah ce ta tare *look twin beje cenba abin sam ko kad'an beyi nisan daze cenba, ke kuma Anty dan Allah ki had'a mu dasu waike ko haqqi bakya tsoro" nisawa nasaran tae tace ba damuwa zan hadaku dasu yanzun nan amma dai kaikam ka bani mamaki ta yanda zaka fifita wata bare akaina har kana rantsewa akan datse zumuncin mu akanta lallai da mugun abinda ta maka" bece mata kanzil ba harta had'asa dasu. Maheer da police ne suka zagaye kwalawan bayan sunyi nasaran kame su ta hanyar wayau, babban cikine yake jawabin abinda ya faru tirtan tiryan ya qara da cewar+ "Cewa akayi ma mu kashe ta tomu a qa'idar aikin mu bama kisa ko bindiga ma bama amfani da ita qarqari yanki mutum inda mukasan baze mutu ba, shine mukace bama kisa se matar tace mukaita wannan jejin muda kanmu munajin storo seda aka qara dubu dari uku sannan muka kaita bama wani da nisa mukaje da ita ba muka daureta wurin kawai dan mukanmu a tsorace muke, sannan wlhy muba en fashi bane area boys ne kawai mabiya en siyasar sokoton nan" nisawa maheer yae yace "Yanzu kune zaku mana jagoranci zuwa jejin, tunda naji ku kunada dama dama inshaa Allah bazan bari a tsare kuba kuma zan daukeku ayyuka a company d'ina me zaman kaina zan kuma baku jari wanda zaku ja a dayan bangaren ku qara nidai kawai so nake na ganta ne" kallonshi ogan yayi yace "Malam tsakani da Allah zaka sama mana aikin nan ka rabamu da zaman banza, wani zubin abinshan koko ne seya fagaremu ka ganni nan NCE ce dani amma ba aikin yi idan har haka ne zan gaya maka gaskia" dan sandan ne yace "Au kai dama dan qaniyarka qarya kakeyi ba hakan bane" "Bafa qarya nayiba yallab'ai kawai dai wani abu yabiyo bayan mun ajiyeta ne" Riqe hannunshi maheer yae "Wlhy summa tallahi zan cika dukkanin alqawarin dana d'auka kurun dai ka gaya mun gaskia kai harma da qari zan maka wlhy" "Yallab'ai bayan munkai yarinyar nan abu biyu ne ya dawomun a zuciya, na farko dai nayi tunanin idan ta mutu mune da haqqinta na biyu kuma da akwai wani mutum dake so akai masa en mata ya bamu kud'i bansa me suke masa ba amma dai nasan ba kashesu yake ba wani zubin ma mu yake baiwa yaran muje mu mayar dasu inda muka dakko su, wasu bayan wata tara wasu shekara wasu har shekaru biyu suke kan mu maidashi, tose nayi tunanin na kai masa ita amma kuma nayita kiran wayarsa a kashe, ban taba sanin inane gidan saba kullum a hanya muke had'uwa....dukda haka senaje na dauketa koda naje ta suma a wurin amma haka na d'akko ta na kaita wani gidan mu na daureta kullum ko bayan kwana biyu nikanje sedai shekaranjiya naje batada lapia sosai, kamar ulcer ne da ita kwana biyu babu aiki ba kudi banida abun siyan mata abinci banjeba, inaso in sake ta ta tafi amma ina tsoron sena saketa oga me en mata ya dawo" Cakumo rigar sa maheer yar "kanada hankali kuwa yaya zaka daure mutum ka kwana biyu bakaje ka bashi abinci ba, to waima tukunna ita kadaice kenan a gidan koda me kula da ita?" Riqewa maheer hannu yae yaji maqura yace "Kayi hakuri yanzu muje cetonta shine yafi" sakeshi yae tare da tunkudashi yace ku tashi mutafi wlhy idan wani abu ya sameta duk sekun gane wlhy" haka suka d'unguma dukkansu har anty Reedah dake biye dashi kamar jela har sokoto ta bishi sanida en iskan a sokoto suke...... Da kanshi ya bude gidan ya kasa hakuri ya warce key d'in a tare suka shiga dukkansu wasu nabin wasu haka ya miqawa ogan key ya bude d'akin ya shiga shima yabi bayansa wasu police suka tsaya da wasu yaran a waje.......d'akin duhu sosai, Maheer jikinsa har rawa yake garin laluben fitilar wayarsa haka Anty Fareedah ma,hasken fitilar d'akin ya soma mamaye d'akin wannan ya baiwa Ilahirin mutanen d'akin damar fuskantar gabansu, Seda maheer yae baya sannan ya sake wayar hannunsa Nancy ce kam amma kamar ba itaba tayi baqi abin baqin ciki da takaici ma a tsaye aka d'aure ta kashi da komai anan takeyi kuma doguwar rigar dake jikinta dukta nannade a jikinta d'akin se tashin wari yakeyi na kashinta da fitsarin da takeyi...Maheer beko kalli kashin ba yae kanta da taimakon ogan suka kunce ta amma seta biyosu lago tana shirin fad'uwa riqeta maheer yae ya janyeta daga wurin najasar amma bega alamun akwai numfashi a tattare da ita ba, Se tsakar gida ogan ya kama masa suka kaita Maheer tamkar nagoye yake kuka hatta fareedah kuka takeyi police uku ma acikinsu kuka suke, lokaci daya nadama me tsanani ta saukarwa oga, ya kalli Maheer yace da kun shigar da ita bayin nan an dauraye mata jikinta bazamu iya fita da ita a haka ba, jikinta duk kashi" harara maheer ya wurga masa ya kalli fareeda yace "Twin tayani duba pulse d'inta dan Allah" Dayake dama fareedah medical doctor ce wannan ne ya basu damar dubawa tabbas akwai sauran numfashi ajikinta sedai she's too weak....kallan shi tae tace "tana buqatar taimakon gaggawa amma dole seda wanka babu asibitin dazamu nufa da ita haka, gashi bazata iya yiwa kanta ba harga Allah ni bazan iya taimakontaba, tunda gidansu anan yake mukaita gida kawai" kallonta yae "Banason sunan gidanmu ya b'aci twin, bazan kaita gida a haka ba dole seda wani plan, kinga police suje station da azzaluman nan ke kuma muje gidana ki gani... Hakan kuwa akayi islam yawa waya yana nemanta a gidansa da gaggawa dolenta ta hau adaidai ta rigasu gidan suna zuwa yaja hannunta ciki " ki nutsu babu lokacin dazan miki bayanin wani abu a yanzu maza jeki ciki zan kawo miki Hafsat tana buqatar wanka k mata mu kaita asibiti tana buqatar taimakon gaggawa" kallonshi ta qarayi "Wace hafsan? Tsawa ya mata " Nace bamuda lokaci salaha!!!" Bata qara magana ba, wlhy dataga hafsat bata gane taba seda yace Nancyn kice a haka fa Salaha, wlhy an cutar damu" tsayawa tae yace "haba salaha ki mata wankan nan wlhy bamuda lokaci sannan kuma kinga bata numfashi da kyau" A haka islam na kuka tawa Hafsat sab'i yakai bakwai seda taga ta soma haske sannan ta barta haka anty Fareeda ta kira suka dawo da ita dakin suka saka mata kaya wanda yauma da ake neman kayan da qyar aka samu doguwar riga abinda kullum akwai kayan kyauta yau aka rasa se rigar maheer aka sanya mata, aka shafa mata mai da komai sannan fareedah tasa akai rushin nata zuwa asibitin uduth, a gaggawa suka karbe ta sannan suka samu nutsuwa kad'an mota Maheer ya kira islam yace "Islam ki nustu kiji abinda zan fad'a miki, kuma ki sani wannan sirrine bana buqatar koa gidanku ki fad'a, sannan kuma ki sani abinda zan fad'a miki ya shafeki ne dakema bazan sanar miki ba" kallonshi tae amma batace komai ba yaci gaba "Duk kanin abinda ya faru da Hafsat ta dalilin kine" da sauri ta kalleshi alamun bata gane ba....atake ya bayyane mata komai har qarshe yace. "Bani buqatar sunan yayata ya fito sabida haka zan adana wannan maganar se Nancy taji sauqi gaba d'aya, sena nemo wani plan dazan fada kina jina ko?" Nisawa tae har tana qwallah tace "Amma wlhy an cuci Hafsat wai kasan na kula da qafarta d'aya daga qasanta kamar a karye take😭😭 karaya tsohuwa kuma dan hargun yayi baqi, dukda batasan inda kanta yake ba wlhy na kula cewar tana yamutsa fuska duk sanda na taba wurin kuma, duka qafafun guda biyu sun kumbura suntum se qyalli sukeyi wataqik dukanta sukayi a qafar" kallonta yae shima qwallan dayake tarewa seda ya zubo sannan yace "Islam a tsaye suka d'aureta kusan watanni biyu dole qafafunta suyi hakan ai, wataqil inaga ba karaya bace ba dai wani abinne karki damu kinji?" Gyada masa kai tayi tanata kuka, yau kad'ai maheer ya kamo kafad'un islam yana ganin wannan ne kawai ze sanyaya masa zuciyar sa gani yakeyi tamkar haqqin Hafsat ze dinga bibiyar zuri'arsu ne har qarshen ta . ************** Seda doctor yaja numfashi sannan kalli Maheer yace cikeda tausayawa "kaine mijinta?" Kallonsa Maheer yae ya kalli islam da fareeda sannan yace "Ea nine mijinta" doctor yace "Babu damuwa in fad'i abinda zan fad'a agaban wa ennan?" Daga masa kai kurun yae alamar e baze iya magana ba jikinsa har rawa yake yi sosai akan hakan, doctor yaci gaba "Ranka ya dad'e nayi mamakin yanayin abubuwan dake damun matarka har haka kanada arziqinka amma baka d'auki wani matakin ba, da farko dai yunwa tayi mata illa me tsananin wahalar magan cewa har indorscopy se an mata domun gano menene matsalar cikinta idan ta farfado, na biyu kuma tanada tsohuwar karayar da zance tafi wata daya ba'a dorata ba harma ta soma rube k'afarta ta dama, wanda ko shakka banayi dole se an yanke qafar, abu na uku kuma bata cikin hayyacinta jininta yayi mugun hawa, pcv dinta kuma is very low, yanzu zaka saka mana hannu ne a takardar cire qafar tata sabida a gaske bamason aikin ya wuce sati sabida qafar tanata ci karta qara sama tunda a qasane kawai, qarayar wurin ankle d'inta ne" kasa magana maheer yae ganin komai yake tamkar a mafarki yanzu kam har fareeda kuka takeyi sun gagara cewa da likitan komai se kuka har maheer din, mijin fareeda ne ya kira dama yace zezo sokoto shima dayake babban likitane, ta fice ta daga wayar tana kuka take sanar masa...... Haka Maheer be baiwa doctor amsa ba kuka yaci qarfinsa yaje mota yafi 30 mns yanayi, daga baya yaje dakin da aka ajiye Hafsat anan ya tarar da islam na kukan ta riqe hannun Nancy, shi dinma ya gagara rarrashinta zama yae ya qurawa fuskar nansi ido,se yamutsa fuska nancy keyi harse dimple nata ya lob'a, shafa fuskarta yae yace1 "Ki yafemun Hafsat, duk ta dalilina kika shiga wannan halin" haka ya dinga surutai yana kuka islam ta kasa magana se kuka take qwalawa harna tashin hankali shima maheer haka......Assalamu Alaikum...masoya kuma makaranta wannan novel din ina me baku hakurin abinda zan fada, dan Allah kuyi hakuri daga page 20 na jiya nadena baiwa kowa daga farko, inasha wahala wurin turawa gaskia, dan Allah dukmeso ta nema a group kotaje wattpad nagode sosai da qauna.*+ *Maman Ramly wannan shafin nakine kyaita, ina godiya sosai da comment* Haka Anty Reedah da mijinta Dr. Muheeb suka shigo suka samesu, ya kasa ya tsare tamkar ya rungume ta yakeji ita kuwa islam ta kifa kanta jikin gadon tanata kukanta a hankali.......Hannun Maheer d'aya tsaqale acikin na patient d'in yanzu kam qwallan ma ya gagara yi se numfarfashi yake saukewa da sauri da sauri itakam Hafsat batasan ina kanta yake ba oxygn mane aka sanya mata, kallon muheeb yae ya saketa da sauri yaje wurin shi ya riqe masa hannu "Ka taimaki baiwar Allah nan muheeb banaso acire mata qafa qaramar yarinya ce muheeb, dan Allah ka dubi maraicinta ko aure batayiba ace a gundule mata qafarta waze aureta?" Rungumeshi Muheeb yae "Calm down Twin kaji, komai zezo da sauqi na nemi transfer ma zuwa asibitin frnd dina me zaman kanta ta qashi dake kano, ni kasan ba ainahin wurin qashi nake ba amma nasan sosai akan bangare, zan duba qafar kuma yanzu da condition dinnan idan muka dauketa komai ze iya faruwa se dole an ciwo kan numfashin ta, abu na gaba shine ka sanar wa iyayenta cewar ka kama mutanen dasuka saceta sedai ka boye sunan yayarka dana qawar ta kakuma ce zaka dauki mataki akansu karka fadi wani dalili se bakasan komai ba faqat" binshi yae da kallo shikuwa ya sakeshi yaje ya duba qafar.....tabbas karaya ce ta wurin Ankle dinta sedai wannan karayar bazata wuce sati uku ba, kuma a yanda yaga hoton babu wani nama dataci sosai sedai fa tabbas koda zasu gyara qafar har abada bazata tab'a dawowa normal ba seta dan karkace idan akayi sa'a karkacewar bazata nuna ba amma idan akai rashin sa'a sedai yazamana qafar ta karkace yanda ze nuna sosai kamar me dingishi ko kurkuwa ma dan idan daya tafi daya tsyi dole seda sanda.....dafe kanshi yae cikin bacin rai anty Nasara tayi aiki irin na jahilai kuma jakai, talakan data raina yafita har a wurin Allah indai ze fita jin tsoron Allah......waigowa yae ya bayyanawa Maheer abinda yake hange ya qara da cewar "Abari amma Dr. Sunusi yazo muji nashi tunda a wannan gefen guru ne yafini sani, sabida haka ka shirya muje gidansu hafsat a gaya musu abinda ya dace su sani sannan aga yanda zamui mu koma kano da ita amma gaskia dole se anyi amfani da private jet na Abba wurin daukarta" Hakan kuwa akayi Baba azumi se gwatsina takeyi akan qaryane seda sukaje taga yanayin hafsat itama seda tae qwallah jin an daureta a tsaye kusan watanni biyu ga kuma yanda jan buzu ya dawo kala kala ajiki, Mahaifiyar hafsat kasa kuka tae se zare ido takeyi dukta rikice........ ***************** Maheer ga mahaifiyar hafsat a asibiti amma ya kasa ya tsare yaje ya riqe hannunta yanata mata addu'a yana tofa mata yana ganin kota farka a firgice zata tashi dukda likitan ya sanar masa abincin dasuka bata ta hanci ya taimaka mata zata farfad'o anytime soon.....amma cire ox da aka daura mata,ganin haka ya sanya ta koma qaramin dakin dake farkon shigowa cikin dakin.... Hannunta ta motsa kad'an dayake yana riqe da hannun seya kaiwa wurin kallo ya dawo da dubanshi zuwa gareta a hankali ta bud'e idanta qura masa idanta tae na wasu en daqiqu batare data qifta ba shi dinma kallon ta yake har yana washe baki ya matsa daf da ita ya tallafi kanta "Sannu Hafsat ya jikinki kin farka, inane yake miki ciwo sannu kinji yanzu kin dawo gida komai ya wuce ki kwantar da hankalin ki" kallon sa tae alamun bata fahimtar komai ya kalleta sosai ya fara sunsuno wani abin, saketa yae yaje ya kira Babarta itama tazo tayi maganar harta gaji amma shiru hafsat ba amsa se kallon su takeyi tamkar wasu wawaye.......Ana haka ummul ta shigo itada Ameen, sukai kanta amma ga alama ba wanda ta gane se kallon mutane takeyi, fareedah ma da Muheeb dasuka gama kaiwa qarshen neman hanyar kaita kano suka shigo......da kanshi muheeb ya dubata yanda yaga kowa ya zagayeta har islam itama tazo amma batawa kowa magana ba se kallon su takeyi "Lost of memory!" Ya furta a hankali bayan ya gama tab'a kanta dako ina amma bata ko damuba se binshi takeyi da ido, wannan yarinyar taga rayuwa ya furta a sarari, cikin gaggawa ya nemi hoton qwalwa batare daya musu bayani ba kiran wani dr. Kurun yae ya qara dubata sukazo aka tafi da ita hoton Kai.... Tunda aka gayawa maheer da sauran mutane cewar a kai ake hangen matsalar se suka rikice, abin ya daurewa kowa kai ga ummul dama tana cikin damuwa, Ameen kullum sesunyi fad'a yana cewa ya auretane danyaci riba da yaran dazata haifa amma wata biyu shiru babu ciki, tana mamakin sa ko shekaru biyu tayi batai ciki ba aibata cancanci hakan daga gareshi ba zaman su yaqi dad'i, har yana cewa dole tasan yanda zatai da samu ciki inba haka ba akwai damuwa cox bazeyi asaran kudinsa a banza ba...... Maheer ko yanzu mota ya koma yarasa meyasa yakeji kamar ana cewa za'a kashe shi duk sanda akace ga abinda ke damun hafsat, kwana biyu ma beje lecture ba, yanzu baya iya koda qwalla ne akan Hafsat tun ranar dasuka baro gidan nasara take kiransa baya d'auka sam!! Har dakanta taje ta gayawa ummansu abinda tae tare da yin qarairayi ta kare kanta umman tamata fada amma ta yarda bada hannunta akawa er mutane hakan ba....Abba ne kawai besan miyan da ake shaba sabida baya garin. ************* Bincike ya nuna qwalwar hafsa babu inda ya tab'u amma fa tayi lossing memory dinta gaba d'aya wanda suke saka ran ya dawo bada jimawa ba, a wannan ranar suka wuce kano domin yiwa hafsat aikin na qafar......

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 7"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...