WATA FUSKA CHAPTER 16 KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 16 KARSHE

WATA FUSKA CHAPTER 16 KARSHE

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 16 KARSHE
Maheer ya shiga damuwa sosai 
akan Ummul, kwana biyu ma Hafsat bata ganshiba, yana tare da Ameenu suna gabatar da wani muhimmin bincike, har sun cafke yaran Alhal Baba kusan hud'u, da Alk'awarin basu Naira miliyan goma su duka su rarraba indai suka fad'i inda take, sun samu amsar tambaynsu da wannan.....amma sesuka ci gaba da tsaresu akan sesun tabbatar an ganta tukunna zasu sakesu.......+ *************** Islam tasha mamakin yanda yae, d'akinsa taje babu alamar ya d'auki suturunsa amma babu wasu dagacikin kayan dayake amfani dasu na toilet ko wani abu makamancin hakan, babu laptop da sauran kayan aikin sa, me hakan yake nufi? Ta tambayi kanta, bame bata amsa wannan ya sanya ta juya akalar tunanin ta zuwa neman anty Nasara..... Ringin biyu ta d'aga wayar cikeda isa tacr "Sanadiyanki an hanani huld'a da kowa na zuri'ar mu, kin cuci halacci dason dana nuna miki mesa zaki kirani yanzu?" Ta k'arashe maganr da tsawa sosai "Kiyi Hak'uri anty Nasara wlhy ba laifi na bane ba, ko yanzu ina cikin tashin hankali, Inna na tace na rufewa maheer k'ofar tunda baya dawowa se dare, shine yai mun yaji motocinsa ma kaf basa gidan, dan Allah gayamun yaya zanyi" wani sanyi ne ya ziyarci Anty Nasara dama bil haq takeso ta wargaza auren, kan kuma tazo kan nanuwa dole seya auri wacce takeso ya aura d'in "Kefa shine matsalar ki, bakida aji ko kad'an, namiji idan yace ze miki yaji aike seki dakawa shege barkono, wlhy dazaran yayi kwana biyu bezoba ki tattare komatsanki ki tafi gidanku seya nemeki da kanshi tabb" Nisawa tai "Anty wlhy bazan iyaba, zandai iya shareshi amma ba zancen zuwa gida kam" tsaki taja ta kashe wayan gaba d'aya........bin wayan da kallo Islam tayi, ta fara tunanin wasu abubuwan game da Anty Nasara, bafa jahila bace iya, kodai da biyu take santa? Amma ko menene zata gano bakin zaren...... ********* Yau dai jkin hafsat yayi sauk'i sosai harta soma en harkokinta, ganin nutsuwa ya shiga jikinta ya sanya umma tayi kiranta a parlor ta zaunar da ita, ta soka magana cikeda nutsuwa... "Hafsat kinsan dai cewar koda babu auren Maheer akanki ke 'yata ce ko? Allah ne ya banike kuma nagode masa, ba dole d'anda ka haufa acikinka shine d'anka ba koda wane lokaci Allah ze iya had'aka da yaro naka na kanka, to da wannan nakeso kibi hukuncina kimun biyayya" Tunkan a fad'i hukunci k'irjin ta ke masifan dokawa, amma ta gaza furta wata kalmar, gyaran zama Umma tayi kan tace "A yanda na kula zaman lafiya tsakanin keda islam baze tab'a samuwa ba har abada, dalilan dazasu hana zaman lafiyan sunada yawa sosai a tsakanin ku, na farko dai kinga ni dake da kowa yasan cewan Islam tayi yawonta me muni kantayi aure, daga cikin mutanen dasukayi shaidar hakan kece mafi kusanci da ita kinfi kowa sanin wacece islam, da wannan hankalin kishiya baze tab'a kwanciya ba ace kishiyarta ganau ce ba jiyau ba akan karuwancin da kayi kafin aure yakuma kasance wai ka dawo ka auri mijinta, a iya hasashena iyalin Maheer bazasu tab'a zaman lafiya da had'in kai muddin kikaci gaba da kasancewa matar sa!!""" Da sauri Hafsat ta d'ago ta kalleta sabida yanda zancen ya doketa duka me tsanani, kawar da kai Umman tai gefe alamun itama ba'a san ranta take furta wannan maganar ba kantaci gaba "Abu na biyu babu gaskiya ko kad'an ace mijinka ya aure k'awarka bada sanin kaba, kuma k'awance ma irin naku da islam, kinga duk inda akabi akaje aka dawo bamuda gaskia kuma mun zalinci yarinyar nan, nayi shawara da en uwana, da kuma abokanaina makusan tana akan cewar idan har ana so Maheer ya samu kwanciyar hankali da iyalansa tokuwa se an raba auren ki dashi" zamane ya gagari Hafsat ta mik'e tsaye cikin zare ido da firgici lokaci d'aya gumi ya soma tsatsafo mata , janyo hannunta umman tayi zuwa kan kujerar a kusa da ita tace "Hafsat dan Allah ki tausayawa rayuwwar maheer, kar kwaramniya tayi masa yawa aka tsufan dole ya taso masa, keda bakida tsatso dashi ki bani goyon baya muce da Abba bakya sanshi a raba aurenku koda bayaso kodan kwanciyar hankalin dukkan ku" Duk yanda hafsat taso daurewa setaji kalama umma tamkar an watsa mata gaushin wuta a zuci, bata raba wannan zancen na umma da labarin ranar mutuwar taba, kanta ne ya soma sara mata amma ta gagara furta wata kalmar...murya na rawa umma tace "Karkiga kamar ina nuna sonkai ne, keda kike ta gari kece mace ta farko dazan sowa maheer amma kinga idan nace ya rabu da Islam mun cuceta ne" kallonta yanzu kam hafsat tai ido cikin ido, ita kanta umman ta hango tashin hankali shinfid'e a fuskar hafsat d'in.... *********** Sosai Ummul ke faman yin nak'udar tsaye, koda wane lokaci cikin zullumi take da tashin hankali, ga wata k'atuwar bayarbiya dake yawan danna mata hannu ajiki da sunan wai karkato da kan baby zuwa k'asa, tana ansar uwar azaba akan hakan........ Su Maheer batare dayawa kowa sallama ba yabar garin kano zuwa chad inda shida Ameenu suka samu goyon bayan jami'an tsaron chad d'in, da taimakon yaron Alhj Baba suka isa gidan.... Tunda Ummul ta samu damar sakawa me tsaron k'ofar datake ciki maganin dasuke saka mata ta dinga bacci se kuma baccin ya sureshi......... Matsalarta masu gadin k'ofar, hakan baze hanata neman mafita ba harse ta cimma burinta na barin gidan, zuciyarta ce take azalzalar ta akan lallai tabar gidan inba hakaba su hallakata ita da d'an cikinta, duk wanda ya sace mutum harya bari ya ganshi kuma ba manufar alkhairi bane a ranshi toko tabbas ze aikata kisa akan wannan mutumin kodan gudun tonuwar asirinsa akan lamarin......... Tana zuwa k'ofar parlor taga ba kowa, wannan ne ya bata damar soma tattaki cikin sanda da zumar barin gidan gaba d'aya, tafiya takeyi cikin sand'a har tazo farfajiyar gidan tana tafiya tana waige waige, me gadin data hango ne ya miyar da gabansa gabas yana rik'e da bindiga ya bata damar sauya akalar tafiyarta zuwa back yard na gidan ta b'uya, acikin shuke shuken furan nin dake zagaye da bayan gidan ta b'uya atakure ga maran ta yana mugun murd'a mata sosai se gumi take had'awa.....batafi mintuna ashirin da b'uya a wurin ba taji ansoma d'aga murya ana nemanta...duk duka gigice wani har kusa da ita yake be ga ko alamar taba, wannan ya sanya ta k'ara tsorata sabida taji suna cewan yace da zaran an ganta indai ta gudu to a harbeta!!!!!..... Kaf masu tsaron gidan ficewa sukayi daga gidan zuwa nemanta haik'an!!!! Sun tsorata sosai da rashin ta har me gadin, jn shiru ya sanyata fitowa tana ganin k'ofa a bud'e ta arce dama da yamma ne..... Koda su Ameen suka iso babu kowa agidan gasu da tawagar en sanda, a tsammaninsu an musu munafurcine an sanar da zuwansu amma kankance kwabo meye harsun dawo gidan gasu aciki su a waje, haka aka dinga harbi suda police an kashe kusan fiye da rabinsu, sannan aka damk'e sauran amma tashin hankalin shine babu Ummul babu alamar ta........hankalin Ameen yayi mugun tashi har baya ganin meye a gabanshi, kuka ya somayi sabida last hope d'inshi kenan, baya tsammanin bayan iyayen kud'in daya kashe da kuma zurfafa binciken dayayi akwai wani binciken daze k'arayi akan lamarin Ummul, a yanda yake lissafi EDD d'inta saura kwanaki uku in hakane watak'il tama rage EDD d'in ta haihu an kashe masa ita an kashe kuma Babyn ta, yasha kuka da k'yar Maheer ya rarrashe sa............. Ummul kuwa koda ta fito taga acikin garine tan gararas se kurun ta arce..... Tayi tafiya me nisa, abinda yafi bata wahala shine cikinta, ga kuma babu mejin yarenta se d'aid'aiku gashi france suke amfani da ba English ba, ta kula mutanen garin ma basuda tausayi mafiya akasirin su, tayi kuka harta godewa Allah, ga dare yayi ga yunwa, ga ciwon baya ga batada ko sisi!!!! ************ Mik'ewa kurun Hafsat tayi batare data ce kanzin ba ta mik'e da gudu zuwa d'akin ta.... Rufe d'akin tayi ta soma kuka tamkar ba gobe, tayi kukan harta gaji sabida harga Allah a matsayin macuciya tale kallon umma, seda aka gama yaga mata rigar mutun ci sannan ace za'a saketa?" Kiran wayan maheer tai amma baya tafiya ko nan da cen, batada labarin ya tafi chad ma....rana kam wuni tai tana kuka a d'aki ko abinci bata nema ba, bugun duniya umman tayi amma tak'i ta bud'e d'akin. *************** Tafiya ummul keyi batare datasan ina take wurga k'afar taba, yunga ga azabar tafiya, ta kulama ta soma barin cikin garin zuwa jeji jeji..... Karene ya bita da gudun fanfalak'i se surfafa gudun takeyi tamkar ba gobe, karo tai da wani abun atake ta fad'i wurin a sume!!!!! Mom Nu'aiym Fan's kui hak'uri, munata bikine nima ba haka nasoba ko kad'an wlhy, amma kuyi hakuri inshaa Allah tunda gobe wunine kawai zakuna samun daily update. ..dan Allah ku gafarci er mutan galadanchi love u.. Kife rub da ciki ta fad'i, wanda k'aran data k'walla ne ya janyo hankalin wata mace da mijinta dake k'ok'arin wucewa acikin mota akanta, ganin mutum a kwance ya bashi daman yin reverse ya parka, shida matarsa a tare suka fito daga cikin motar, karen da yai tsaye akanta ya sona korewa kan su birkitota, sunyita jijjigata amma ko motsi sema jini da matarsa ta kula yana bin jikinta, yarensu ta masa suka kwashe ta suka juya acikin gari.........+ ************** Anty Fareedah ta kira a waya inda take shaida mata aiki takeyi zata nemeta daga baya, dukda yanayin muryan hafsat kurin ya isa ya nuna mata cewan da matsala sosai.....!!! A gaggace ta kammala ta patients sannan ta koma office dayake mallakinta ta danna masa key, farar rigar dake kan kayan jikinta ta zare tukunna sannan ta bud'e fridge ta d'akko ruwa a roba da cup tazo ta zauna ta tsiyaya tasha....zafi ake a agarin tana ganin tamkar idan Allah yaso ruwane ze sauka akwai alamun hadari a garin sosai kuma. Wayanta ta zaro ta danna wa Hafsat kira tana d'agawa ta soma yi mata kuka wiwi akan abinda umman tace da ita, ta zayyane mata komai a waya..ta k'ara da cewan "Anty Fareedah seda aka gama yagamun budurcina sannan a miyar dani k'aramar bazawara dan Allah da manzan sa ki baiwa Umma hak'uri wlhy koda banasan Maheer ni ban isa nace inason aurena ya mutu ba, dan Allah ki taimakeni" shiru ne ya ratsa wayan na wuccin gadi, kan Fareeda ta nisa tace "Nasan da maganar amma ban tab'a zata umma zata d'auki muguwar shawarar k'awayenta ba, da alama anty Nasara ce ta taje ta gaggaya musu labarin cikin gida dayike batada hankali, amma yanzu bari muwa tufkar hanci....Zan kira Abba kaina a tsaye in fad'a masa komai" Nisawa tai tana sauke ajiyan zuciya a hankali "To Anty Nagode sosai Allah saka da Alkhairi" kashe wayoyin sukayi yayinda Hafsat ta kwanta a rigingine tana kallon saman d'akin,abubuwa dayawa sun cunkushe mata, tunda ta had'u da Maheer abubuwa gaba d'aya suka tarwatse a rayuwarta, da farko dai karatunta a sanadin maheer ya tarwatse, k'awancenta da islam ma a sanadin maheer ne ya tarwatse, rabuwarta da gidansu sanadin maheer ne, duk talaucin gidan ubanka yafiye maka rab'e rab'e har ciwo tai na fitar rai akan shi, an mata auren dole akan Maheer ga wannan ciwon daya taso mata haik'an duk a sanadin maheer...yanzu ya k'arb'e mata abu mafi girman daraja a wurinta sannan seta dawo bazawara akan shi?!! Kenan ya tattare duk ya tab'arb'are mata rayuwarta ya gurb'atar da ita? Lallai tarayyarta da Maheer ba alkhairi bace... ************* Da gaggawa aka karb'eta zuwa d'akin masu haihuwa a asibitin, cikin kuma lokacin dabe wuce mintuna arba'in ba ta haifo yaranta biyu duka maza, abu mafi tashin hankali shine jinin ta daketa tsiyayewa harta fice a hayyacinta!!! Jikin Ameen ya soma ficewa tunanin maheer, zazzab'i sosai yakeyi lokaci d'aya ya fyad'e ya rame, wuraren sha biyun dare ya soma jijjiga wanda ala dole Maheer da wasu yaransa suka kwasheshi zuwa asibiti.....Neman taimakon jinin da ake ne ya zowa Maheer a kunne akan wata baiwar Allah me cikin da aka tsinta kuma ta haihu lafiya amma tanata zubar da jini ana sanya jinin yana ficewa, kalmar an tsinta ne yaja hankalinsa zuwa wurin wanda ya nemi ganin matar yanaso ya taimaka aikuwa yana zuwa se Ummul ya tarar rai a hannun Allah, beyi k'asa a gwiwa ba wurin gayawa Ameen da har lokacin be gama kammala mutum ba, ai kam tare suka koma dukda bashida lafiya, suka nuna evidence na cewar su en uwantane wannan ma shine mijinta, har hotunansu a tare seda suka nuna dake kan wayar Ameen tukunna aka masa bayani akan matuk'ar wai ba emergency theater aka mata ba aka cire mahaifar gaba d'aya to tabbas da akwai yuyuwar itama arasa ranta, be tsaya wani b'ata lokaciba sukayi signing aikam aka wuce da ita wurin opertion d'in.. Ba k'aramun dad'ine ya lillib'e Ameenu ba dayaga yaranshi maza har biyu kyawawa sosai. ************ Islam ta tsorata ainun ganin kwana biyu babu Maher d'inta babu labarin sa, hankalin ta yakai k'ololuwar wurin tashi akan rashin sa, zuwa yanzu ta gama amanna ta kwantar da hankalinta akan Hafsat kurun shine mafita agareta su zauna lafiya tunda yake mijinta ba wulak'anci yake mata ba, tana cikin tashin hankali yanzu idan Maheer ya saketa waye ze aureta? Ai ita a duniya ta gama kad'ewa kuma har abada bazata auru a wurin kowa ba, ta yanke shawarar zuwa gun Hafsat tukunna ta bata hakuri wannan ne ya sanya ta shirya fita itada babynta zuwa gidan Abba. Babu laifi ta samu kyakyawar tarba awurin umma, inda kai tsaye ta buk'aci ganin Hafsat kuma umman tace taje tana sama, zuwanta k'ofan d'akin yayi daidai da fitowan Hafsat a shirye nasan zuwa gidan anty Fareeda sabida cewam datayi tazo....murmushi islam ta sakar mata wanda ya matuk'ar bata mamaki, rabon dataga fuskar islam da irin wannan murmushin tun suna school tanaga, kasa miyar mata da murmushin baya tai se zura mata idanta da tai tana nazarin ta, ba tun yauba tasan halin islam ciki da waje, ta san kalan murmushinta na yak'e kona gaske koma na mugunta, babu shakka duk sanda kaga wannan kalan murmushin shinfid'e a fuskar islam toko tabbad da gasken takeyi to meye haka kuma? Anya zata yarda da ita kuwa? Kodai umma ta gama yi mata bayanin raba auren ne? Shine take murna taci galadaba akanta? Idan haka ne ma bari tai mata na yan duniya itama.... "Sannu issy baby, daga ina haka?" Ta fad'a tana me hak'waran ta cikeda k'arfin hali, amma ga mamakin ta setaga islam ta k'ura mata ido tamkar me nazarin wani abu, se kuma ta matso daf da ita ta rik'o hannun ta "My Nancy kuka kikayi? Meya sameki ne?" Ta sani duk yanda takai ga b'oye damuwarta tabbas seya bayyana a idon islam, dukda haka gani tai tamkar islam d'in tasan komai dukan cikinta ne takeyi taji ta bakinta, wani irin k'ululun bak'in cikine ya tado ya tarnak'eta da arayuwa tanaga bata tab'a jin irin shiba tanaga, had'iyar paracetamol ne tayiwa k'ululun kanta d'ago ta kalli islam sosai "Menene ya ragu acikin gurb'ata rayuwata da kika sanya hannu akayi dabaki sani ba islam? Menene kuma ya saura acikin rayuwata da kike hari shima? Dukkanin shirin dakikayi akaina ai ya tabbata ko? Kinsan komai islam, abu d'aya nake gaya miki shine dukkanin abinda kai wa waninka nan ko cen sekaga sakamako, kuma wlhy wannan karon kam, na shirya d'amarar yak'i da koma waye akan mujina, wlhy summa tallahi, mahaliccin sammai da qassai ne kad'ai ya isa ya rabani da mijina" kallon mamaki islam ke binta dashi harta kai aya, da k'yar ta lalubo kalmar "Meyayi zafi haka Hafsat? Ni na isa na rabaki da maheer? Abinda ma na kula dashi shine sam kwanciyar hankalina dana aurena seda sanya hannunki zeci gaba da wanzuwa, farin cikin mijina kece ina ni gangancin cewa zan rba aurenku? Kumama ni awa dana isa na raba auren ku keda mijina? Nayi k'adan wlhy idan ma akwai wani abin dake faruwa ki yarda dani bansan komai ba, dq zuciya d'aya nazo miki, na dena d'aukan zigan kowa inasone muyi zaman lafiya" Harara Hafsat ta danna mata tukunna taja gajeran tsoki tayi hanyar gangarowa daga sama, kanta ne yai wani irin mugun sara mata ta dafe wurin islam tayi tsaye kurun tana binta da kallo, luuuu taga zata fad'i ta gangara ya sanya islam sake jakar hannunta ta bita da nufin tarota lokaci d'aya tana k'walla k'ara da kiran sunan ta, k'addara ta riga fata domin kuwa atare suka shiga gangarawan seda duka gama gangarewa gaba d'aya, babu d'aya daga cikinsu dake motsi Umma data wanko da gudu itada da masu yin hidima agidan sukai cirko cirko.... Anwa Ummul aiki susscesfully an cire mahaifan gaba d'aya ta huta, sedai bata farfad'oba dayike an mata alluran bacci....'yan biyu se cancara qarar yunwa sukeyi dole aka soma musu da madara karsu jigata......+ ********------******** Dukkansu sun kasa yin komai se kallonsu dasukeyi, hankalin Umman ya tashi ganin su a haka, tana zargi ko fad'a ne sukayi harya kai suka fad'a daga saman,sophie dake bacci acikin baccin tajiyo kururwan su wanda yasanya tai hanzarin tashi ta sakko itama, itane tai jarumtar zuwa ta d'aga hafsat amma t kasa, tadai kula tana numfashi amma sam bata cikin hayyacinta, ita kuwa islam jini ta hanci da baki...hankalin kowa ya mugun tashi da taimakon securities na gidan aka wuce dasu asibitin su Fareedah inda umman da kanta ta mata waya, cikin gaggawa aka karb'esu aka shiga duddubasu..... Hafsat kam ciwon tame yai mugun tashi se kuma islam data samu targad'e a kafad'anta da kuma k'afanta se buguwa datai ba laifi tad'anji ciwo sedai ba masu hawalan warkewa bane...kowa yarigada ya gama cewan islam ce taja tajata fad'a suka fad'o a tare se tsine mata ake, har aka kwana biyu suna asibitin ga kuma babu wanda aka sallama, amma ita islam da magana da komai tanayi har tashima dukda raunin k'afarta yayinda Hafsat ke cikin tsananin rad'ad'i da azabar ciwo sabida har yanzu batamasan inda take se dogon bincike akeyi akanta kasancewar tanada matsalan da ake neman ciwo kanta tun farko. *Bayan kwanaki biyu* Kwanansu hud'u aka sallami islam, inda hafsat har lokacin shiru ko motsi, abincinma ta NG tube ake bata, sosai take shan wuya abubuwa sun mata nauyi a zuci........ Yau su maheer suka dira Niger ta jirgi suka zo a kano suka sauka, kai tsaye gidan islam suka nufa har ummul da Ameen, a d'ayan part d'in suka sauka gidan akwai tight security ya sanya suka sauka acen, beko lek'a wurin islam d'inba dama ya sanya kuku ya dafa abinci da komai ya fice, yana matuk'ar so yaga Hafsat, yana sani ya shareta be sanar mata zancen tafiya ba sabida yasan condition nata tabbas zata shiga damuwa. A sukwane ya shiga cikin gidan, yaje d'akin umma batanan, ya duduuba parlor na sama dana k'asa bata ban. Kai tsaye ya juya d'akin Hafsat, ya d'anyi knocking shiru kanya tura k'ofar d'akin ya shige da sallama d'auke a labb'ansa, ganin ba kowa ya sanya shi juyawa yana tunanin ko tasamu sauk'ine sun soma fita, a k'ofar d'akin yaci karo da Gimbiya me aikin gidan, zubewa tai tana kwasar gaisuwa cikin k'aguwa ya d'aga mata hannu ya kuma ce "Ummana da Hafsat fa?" Kallon shi tai.... Tana rik'e baki "Yallab'ai dama baka san abinda ya faru ba?" Gyaran tsayuwar sa yae cikeda mamaki, ko kan su taso yai waya da ummansa amma bata sanar masa komai ba, anty fareedah ma bayan ya iso sunyi waya amma komai batace masa ba "Meyene ya faru kuma?" D'an jim tai batai magana ba seda ya daka mata tsawa "Danla malama dake ake magan nace gayamun dalla dalla meya faru ne?" Cikin rawan jiki ga tulin munafurci na cinta, dan sarai taji uwar na gayawa k'awayen ta besan miyan da ake shaba tace "Yallaba'i dama fa umman kane naji tana rok'an Anty hafsat akan wai su had'e kai acewa me gida bata sanka araba auren, injin umman wai bazasu barka ka nutsu ka samu kwanciyar hankali ba, kuma sannan islam ita takeda tsatso dakai dan haka ita ta hak'ura kawai dakai karka tsufa da wuri akan tashin hankalinsu, to daga sannan dai ban kuma jin d'uriyan anty Hafsan ba, sedai naji umman tanata dukan k'ofar d'akin ta tak'i ta bud'e se da yamma sosai Anty islam tazo tanemi ganin hafsat d'in akace tana sama, to dagacen dai dambe ya kaure a tsakaninsu suka gangaro daga saman nan har k'asa bame motsi, Alhamdulillah ita anty islam an sallameta jiya daga asibiti dan ta samu sauk'i ita anty Hafsan dai ko d'azu danaje asibiti kai abinci da driver gwanin tausayi ta hanci ake bata abinci" ta k'arashe maganar cikin share k'walla alamun tausayi" yama rasa mezaice mata ko kuma wane tunanin zeyi be tsaya cewa da ita komai ba ya sakko daga matattakalar benen da gudun fanfalak'i zuwa mota, body guard d'insa naganin sa suka bankad'e masa murfin mota kai tsaye convey suka rufa masa baya da kusan mota biyar tasace a tsakiya suka bar harabar gidan me k'atoton gate har round about ne aciki, tafiyan kusan mintuna uku kansuje gate nan take ha wangale kansa sukai waje...dama yanada guards nashi baya buk'atar yawon dasune sam yanzu ma akan Alhj Baba ne basusan ta ina ze bullo musu ba...kai tsaye office d'in farida ya wuce, beko wani tsaya knocking ba ya bankad'e k'ofar, ita da umma ne da mijinta suna tattaunawa, dukkansu mik'ewa sukayi tsaye ganinsa yace cikin sauri "Fareeda Hafsat fa? Tana inane yanzu" labb'anta sun gagara sanar masa tana ICH (Intensive care Unit) tana kwatanto hankalin sabyanda ze tashi inhar itama d'azu da akai refering nata can tasha kuka shifa dake tsananin san matar sa? Ta gaza furta masa kalma d'aya kowa se kallonsa yake, tunkan tai Magana yaji zuciyar sa ta tsinke ya gagara tsayuwa zubewa a wurin gaba d'aya seda mijin fareeda ya rik'esa "Ka kwantar da hankalinka matar ka tana nan, amma bazamuji k'warin gwiwar sanar maka ba harseka bamu nutsuwarka ka kwantar da hankalinka gaba d'aya....kallon sa kurun yakeyi baya ko k'iftawa tamkar ze cinyesa haka yakeji " inajinka tana ina yanzu?" Seda Dr. Ya g'yara tsayuwarsa sannan yace "ICH" Mik'ewa yai tamkar wanda aka tsikara ya nanata kalmar ICH a bakinsa sekace me koyon magana, da riverse ya juya da gudu zuwa wurin baya ko ganin gabansa, dukkansu da gudu suka rufa masa baya, har suka isa an hanashi shiga se cizge cirge yaje yanda yaganta daure da ox da glass ita kad'ai batasan inda kanta yake ba, ya kalli umman sa "Umma keda islam ne ko, kina kallo islam ta wurgo mun ita daga saman ita tanacen tana hutawa amma Hafsat na na nan tanashan bak'ar hawala ko, ummana nine fa mahee d'inki yaushe kika dena san farin cikina? Naji komai daya faru a wurin Gimbiya, yaya yarinya batada lafiya kuma kin sani, da aurenta kaman daga sama kice araba? Wlhy ni idan babu hafsat arayuwa ta banga amfanin taba ma, ita kuwa islam kinsan tayi attempting kisa daga farko yanzu kuma kin dawo kin bata damar ke b'ancewa itada Hafsat again, ga sauran abinda kuka ragemun nan a kwance, wlhy umma ban tab'a zata zakimun haka ba, amma shikenan" kowa yai shiru yana sake sak'e a xuci yayinda ya juya kurun zuwa gidan islam cikin rashin kuzari, har aka isa bema sani ba seda tukunna suka ankarar dashi k'arasowar tasu ya fito, kai tsaye ciki ya nufa yaci karo da 'yarsa a hannun maid ya karb'eta yanata masa wasa tamkar ba komai a ransa yayi missing d'inta sosai, islam dataji sallamar sa ta fito seta tsaya kurun ta kasa ce masa komai, bed room nashi ya shige ya kwantar da 'yar ya rubutawa islam takarsar sakinta ya fito da babyn ya baiwa maid d'in ya bita d'akinta, mik'a mata takardan yai ta gagara karb'a a gefen ta ya ajiye ya juya mata baya "Ga takardar sakinki nan, ban sakeki dan bana sankiba, Allah ya sani akanki nasan meye so kuma har gobe ina sanki, sedai bazan zauna da macen dake iya yin kisa ba, 'yata kije da ita sekin yaye ta tukunna ,zan k'arb'o abata, dummanin abubuwan dake ciki Gidannan danke na siya ki tattare ki tafi dashi har motoci dake mallakinki, zan turo miliyan biyar a acc naki kimun renon 'yata, ki shirya da safe za'a maidaki sokoto" Wata uwar k'ara ta k'walla tahau magiya har waje ta bishi amma be saurare taba!!! ....ko saki nawane akawa baiwar Allah, ko zaman ze k'ara dawowa oho.....muje zuwa Jikin islam har rawa yakeyi sanda ta dawo cikin gidan, takardan data barshi akan gado ta d'auka amma ta gagara bud'ewa, tunawan datai da umma me ya bata damar juyawa tana d'ingishi da k'afarta ko 'yarta bata tsaya karb'a ba ta juya a sittin, da kanta tai tuk'i zuwa asibitin da takardan a hannunta, bata tsammanin ganin kowa a ICH wannan ya bata daman zuwa office na fareedah dan kuwa anan ta barsu, koda taje kuwa tai sa'a suna nan, wurin umma taje ta durk'usa da k'afufuwan ta tana kuka "Umma dan Allah ki tallafeni ki ceceni ki kuma agajeni, Maheer ya sakeni umma kinga takardan daya bani wai inaso zan yi kisa harso biyu, wlhy umma k'addarane ya fad'o damu nida Hafsat amma wlhy garin ceton tane ma nima na fad'o, ki cewa maheer ya taimakeni ya miyar dani d'akina wlhy shine farin cikina dan Allah kimun tallafi" Tunda Islam ta soma magana umman ke kallonta ta gagara koda motsi, ko ba komai ta tsorata da yanayin yaronta d'azu be tab'a mata kwatankwacin yanda yae ba d'azu hankalinta yakai k'ololuwar b'aci tama rasa me zatace, yanzu mezata cewa Abba idan yaji? Farida ce tai k'arfin halin karb'ar takardan ta bud'e ta soma karantawa da sauri wata wawiyar ajiyan zuciya ta sauke ta zauna dafe da kai kantace "Saki d'aya ne Umma, dan Allah awa tufkar hanci, dan gaskia wannan ya zama hauka, daga faruwar abu bakada ilimi akanshi blindly kurin ka sako saki, an gayawa Maheer aure abun wasa ne wai? Ko kuma muya mayar shashashai? Ubanwaye ma yace dashi islam ta wurgo Hafsat d'in? Ita ta wurgo ta kuma suka fad'o a tare? Gaskia umma bakwa duba lamarin rayuwar maheer yanda ya dace abubuwa yakeyi gaba gad'i, ko zancen auren nan na hafsat haka yae iskancin nan yazo ya narke kuka amince masa batare dakoda jin ra'ayin yarinyar ba, wannan kurin ya isa ya haddasa fitina, tun wuri gwara a kirashi wlhy a nuna masa kuskurensa" Nisawa Umman tai kanta rik'o hannun islam "Baze k'ara aikata wannan kuskuren ba inhar dai nice na haifesa, sannan ki koma gidan ki yanzu karnaji zancen kin tafi gidanku, karma ki gaya musu wannan mugun labarin, zanga maheer d'in ai" Godiya islam tayi sannan ta nemi komawa hanyar gida.... ****------**** Maheer kai tsaye asibiti ya koma, Wurin da Hafsat take yaje ya tsaya wurin glass daze rik'a hangota, se k'wallan dake wanko masa ziyarar ba zata yake zubarwa, yayinda sakin dayawa islam ya masa tsaye a wuya, yana wa islam wani irin so dabaya tunanin amma tab'a halittar irin sa, tafiyar da yai yabar nata gida yasha wahalan rashin ta, har mamakin kansa yakeyi ya daurene kurun sabida yanuna mata iya karta, yanaji ajikinsa idan yaje gidan zuwa anjima ze dakatar da ita akan tafiyar da tai niyan yi....ya kasa barin hafsat ne tausayinta yakeji kamar me, baiwar Allah tun tasowar ta a wahala take har yanzu...yana tsaye a wurin ya kusa da sauyawar yanayin kwanciyarta alamun ta motsa, be b'ata lokaci me tsawo ba ya juya zuwa officr na Fareedah don sanar mata acen ya tarar dasu rai a b'ace, umman ma ta had'a fuska be damuba ya gayawa Fareedah a gaggauce suka fita zuwa ICH d'in.. Dr. Sam yarigasu isa wurin sabida shi dama yana aikin yamma ne, taimakon gaggawa ya bata ganin tayi regaining conciousnes nata, dama sun bada 24 hours ne idan bata farfad'o bama suna ganin se wani ikon Allah, idan kuma ta farfad'o Alhamdulillah....to 1 hour ya rage 24 hours din ya cika shisa ma yazo dubata, yaji dad'i sosai ganin ta farfad'o sedai batai masa magana ba, se binsa da kallo takeyi haka aka hana musu shiga su Maheer Fareeda ne kurun ta samu damar shigowa inda taketa murna dan suna shirin fidda rai da ita ne.. ****----*** Alhj Baba ba k'aramun tashin hankali yake cikiba, ganin babban mutum ya matsa lamba akan anemo masa shi, Abban Maheer ya matsa matuk'a akan neman sa, wannan ne ya sanya ya gudu daga Nigeria gaba d'aya zuwa Ghana tafiyan dabesan ran dawowa ba sabida da asirinsa ya tonu gwara a tsinta gawar sa......Ga cutar dayawa d'an uwansa (Mahaifin Ameenu") sabida rikon amanar aminun ya bashi amma yaketa hallaka masa 'ya'ya yasan hakki kadai seyaci qaniyar sa. STORY CONTINUES BELOW Su ummul kuwa ita da Ameen kamar su cinye junansu, jin kansu sukeyi tamkar sababbin had'uwa duk motsi idanshi yana kanta, Neman iyayen Naja ya sanya a gaba kuma inshaa Allah ze gansu ne sedai bashi da kanshi ke neman nasuba ya sanya ne amasa bincike. ****-----*** Maheer yasha fad'a sosai a wurin Umma, kuma Hafsat da bakinta ta fad'i yanda komai ya kasance tsakaninta da islam, hasalima islam ta fad'one garin ceton ta daga fad'owa ita, yaji haushin kanshi na yanke hukunci cikin fushi kuma batare da buncike ba ya baiwa islam hak'uri inda yai shirin ganin ya had'e kan matan sa da yardar Allah kuma baze k'ara baiwa wani damar daze shiga tsakanin suba... Hafsat dai ana asibiti har lokacin jiki se adu'a yak'i dad'i an kasa gano bakin zaren... Maheer duk a rikice yake, yasha mamakin islm ma dabata masa fushi ba, dan kuwa dayaji musababbin faruwar abun duk seyaji kunya da nauyinta ya matuk'ar kamashi... Dafe kai Maheer yai, lamarin na Hafsat yana d'aure kanshi, se tayi kaman taji sauqi da rana se kuma dare nayi zazzab'i ya kuma lullub'eta, ga komai taci amai take kelamawa, bata masan ganin abinci, tayi wani mugun fari ta rame sosai sumar kanta kurin ke k'ara tsayi se uban goshi, islam ce keta kaikawo a wurinta tunda yake Ummul ba lafiya ne da itaba, ita kanta Baba Azumi da Naja ke kulawa da ita "Yanzh Anty Fareeda meye mafita, kodai zan kwashe tane mu tafi london a dubamun ita yanda ya dace, naga anan komai nata sekuce normal amma ciwo yak'ici yak'i cinyewa yarinya dukta rame, nida akace mamanta zatazo ma dukse naji kunya wlhy, kartazo taga 'yarta kaman ana d'ebanta ana miya" D'an murmushi Fareedah tai dabekai zuciba ta kalleshi sosai "Maheer Hafsat fa cikine da ita, alamomi da yawa sun nuna mana hakan, bana tunanin wanin ciwon ne daya wuce haka, yanzu haka d'azu da kaina nakai jinin ta lab, za'a mata syrum pregnancy test" kallonta yai da murmushin yake shima "Kai Anty Reedah ni se kika bani dariya wlhy, ciki dai sekace almara, nifa tunda taji wannan ciwon rabona da ita, abu so d'aya kurin" kan tai magana an soma knocking na k'ofar office d'in izinin shigowa ta bayar aka shigo, Lawal ne me aiki a lab datace idan result ya kammala ya kawo mata...karba kurun tai ya juya tana dubawa ta soma dariya "Lallai k'anina ka iya aika aika, yanzu yarinya ko amarci batasan dad'in saba zaka mata haka, cikin ma me wahala irin hakan nan, to kadai gani cikin satinsa shida da kwana hud'u" wara idanshi yae wato wannan sati ukun datai a asibiti duk azaban cikine, amma be tab'a kawowa kanshi hakan ba ciki da wuri haka...shi d'inma dariya yai "Anty gaskia wasane" Dariyan taci gaba dayi "Wlhy ba wasa bane ba, ni dariya ma kake bani wlhy, koda yake tsarin Allah ya zarce na kowa, Allah ya bata lafiya yanzu kam se a duba cikin, sabida tayita shan magungunan dabe dace da itaba" haka suka zanta sosai akan hakan,yamma aka kaita hoto ciki lafiyan sa qalau, gogar tamu dama ashe ta fahimci hakan sabida al'adanta daya dena zuwa tun bayan da suka sadu da Maheer batai magana bane sabida kunya, ranar taga tarairaya kuwa, umma ma da abin yabata kunya ai barin d'akin tai gaba d'aya.. ********---******** *Bayan wata d'aya* Tsakanin Islam da Maheer babu wata damuwa, hafsat kuwa tana gidan umma gashi kuma hutu ya kusa k'arewa, umma ta hanashi matarsa wai batada lafiya koda yake hakanne, ganin ummul ba k'aramun dad'i yawa Hafsat ba, har kukan dad'i tai mara iyaka.....dukda yake ummul tabi hasken *WATA FUSKAR* ne dake k'ark'ashin fuskar Ameen me tsananin duhu ada ta cuci kanta da kanta, hakan baze hanaka tausayin taba ainun, ga k'uruciya ga rashin mahaifa, dama Allah yasota da idan Rahama tanada yara har uku sedai fatan Allah ya raya mata su..... *Bayan wasu en kwanaki* Har lokacin babu alamar umma zata sakowa maheer matarsa, wannan ne dalilin dayisa sam ya kasa dukuni, zuwa yai gidan Anty Fareedah ya sanar mata shifa yanason matarsa ta tare agidanta kan su koma, hutu ya k'are tawa umman magana, tasha dariya kanta kora masa bayanin damuwarta akan hukuncin Abba akan Anty Nasara, nan suka yanke shawarar baiwa Abban hakuri, hakan kuwa akayi yace ya wuce su kuma suka d'unguma zuwa gidan ta, acen kana ganinta kasan taji dad'in ganin su sun jima sosai suna magana har shawarwari suka bata da kuma Nasiha taji dad'in hakan ta sakko daga mugun dokin data hau na cewan setaga bayan auren maheer da 'yayan talakawa, ta bashi hak'uri sosai inda tace da safe da kanta zatawa Umman maganar Hafsat har gidan zataje..... ************* Umman tacene bazata baiwa Maheer Hafsat ba seya mata kayan lefe, shikuma shap ya manta da hakan aikam shida yayyinsa mata suka zage suka nunawa dala rashin mutunci mara k'arewa ciki kuwa hadda kyautar motoci k'waya biyu.......gidansu na sokoto suka kai kayan gaba d'aya inda Baba iro se washe bakinsa yake inda Baba azumi da ummul ma tazo da en tagwayenta, Ameen da Maheer ana cewa Ameen Ameer, Maheer kuma Babul kasancewan yafisa jiki, haka nan Ameen yaji sakawa yaran sunayen nan nasa dana abokinsa awani bangaren kuma aminin sa😀😀..... Koda akace za'a kaita gidanta ranar wata juma'a tasha kuka, k'arara ta nunawa Anty Fareedah tsananin tsoron datakewa maheer, rarrashi sosai tasha daga gunsu itada Anty Nasara kan daga bisani a kaita gidan ta, cikeda mugun tsoro take zaune agidan, sanda ya shigo ma sosai ya mata kamada yanda take ganin mazan littafi na zuwar ma matayensu, jikinta se karkawa yakeyi sanda ya zauna a kusa da ita, be b'ata lokacin saba wurin aika mata kyakyawar ajiyan zuciya lokaci d'aya kuma ya sauke kyakyawan ajiyan zuciya, batace masa komai ba harya kai hannunsa saman mararta, d'an cikinta ya soma danno kai yana murmushi yace "Amarya inaso zan gaisa da babyna, yaya kenan" Bata gane me yake nufi ba, amma seta tsinci kalamansa da sanya fad'uwar gaba!!!! "Kafasan ina ciwo ko, kasan banida lafiya ya maheer, yaya kakeso jik.......bata k'arisa fad'an maganar taba ya manne bakinsu wuri d'aya, tun tana tattureshi har yae nasaran kashe mata jikinta, aikuwa lafiya lau yabi da abarsa yau dukda yasha kuka kam sabida a tsorace take amma bata wani ji zafi bama. Seda komai ya lafa ya bita da kallo, mata ko wacce da baiwarta a rayuwa, idan yace islam rake ce sarkin ruwa da zak'i mexe cewa hafsat? Yama rasa wacce ce acikin matansa zece tafi wata abu d'aya ya sani dukkaninsu suna matuk'ar gamsar dashi, kuma alfahari dasu, acikin mazaje bakowane yakeyin tsantsar sa'ar da yae ba......" Sannu Beautiful yau dai ba zafi ko?" fuskarta da rufe da tafukan hannayenta duka biyu alamun jin kunya matuk'a..... ************ Rayuwar girmama juna akeyi tsakanin dukkanin ahalin na Maheer, tubdaga kan gidansu har kowa ma, Sophie da Mahal auren su ya kusa ga cikin hafsat ya tsufa, shauty ma tasamu wani saurayin daze aureta yaron aminin mahaifinsu cikin kwanciyar hankali suke zuba love wanda atare gaba d'aya za'a ha'da ai bikin, su dama daga wannan hutun sun kammala karatun su. Lafiya lau Hafsat ta haifi yaronta namiji me kyau, da tsananin kamanni da maheer ko kadan be dakko taba... Murna awurin maheer ba'a magana sam...yaro yaci sunan Abba ana kiran shi da Abbi.. *Bayan shakaru biyu* Babu shakka zaman lafiya yafi zama d'an sarki, yanzu kam islam da Hafsat amintarsu ta k'ara ta ninka ta dawo fiyr ma da da, bazaka tab'a cewa sud'in kishiyoyi bane, a london duk sun kusa kammala karatu islam dai ciki har yau shiru ga babu an girma haka Hafsat ma, maheer anyi k'iba sosai sejinsa yakeyi wasai sabida ya had'e kan matansa ababen sansa. Alhj Baba dai Anyi neman duniya babu labarinsa, har yanzu Allah shikad'ai ya baiwa kansa sanin inda yake kai jariran dayake garkuwa dasu an hakura ma an shareshi tunda yake yanzu ummul dame gidanta suna zaune kalau. Naja kam babu labarin iyayenta, da wannan Ameen ya aureta tazo ata biyu, dole ummul ta hakura tunda kuwa batama haihuwar yanzu, wannan shine aminta da *WATA FUSKAR* dukda yake k'addara tarigayi fata dama. *Tammat bi hamdillah*

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 16 KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...