WATA FUSKA CHAPTER 14 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 14

WATA FUSKA CHAPTER 14

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 14

  Inna kina kallon kuwa Maheer ya soma sauyawa? Bakya kula da yanayinsa tun zuwanki dabashi yace kizoba dase nace wataqil beso kika zoba" Tab'e baki tayi "Waccen mayyar ce dai keso ta zuzuta masa tunani, na mata gargad'i akanshi, bazan lamunci wata banza ta hanamu cin duniyar mu da tsinke ba, gidan talakawa ake kishiya idan ka shiga gidan masu dashi wlhy baka bari wata tashigo maka, Allah ya rufa mana asiri bazamu bari ta tona mana asiri ba, Allah ya sani bazan lamun taba" Gyaran zama Islam tayi "Inna to meye abin yi? Nifa ina ganin kamar dan itama yaje cen gidan da zama, nasan ba'a zama gun me jego amma ina kwana biyunnan duk tare muka yisu, kuma se yanzu ya koma cen" kallonta innar tayi "To wai meye dalilin sa na barin gidan ma dahar kika barsa ya tafi" "To inna kinga cewa fa yayi dani wai tunda kizo yanajin kunya dole ya koma cen" Goron hannunta ta gutsura "Tunda haka yace ki d'auka haka d'inne kuma kinga ai baze yiyu ma ace wai yaje guntaba ga qanninsa agidan, kedai kurin mu sanya ido muna ganin abinda be mana ba, mu tashi tsaye mu nemi mafita" "Hakane Inna dolene ma wannan ai". *************** Ummul se mugwayen mafarkai takeyi da matsafa wai sun farka cikin ta sun ciro mata baby sun kashe babyn itama sun kasheta, mutanen dabatasan ko waye ba amma a mafarkin tana ganin su kamar matsafa da jajayen kaya, abin ya dameta sabida kusan sati d'aya kullum setayi, ta rasa wa zata gayawa wannan maganar, Naja take gayawa tanata kuka " wlhy kinsan Allah hankalina a tashe yake, musamman da mafarkin ke nunamun suna yawan cin galaba akaina, nasani hakk'ine wlhy hakk'in Nanuwa ne yake d'awainiya dani, duk wata masifa danake gani Baba Azumice ta janyomun, sabida tun asali ni. Ameen bani yace yanaso ba yar uwata yakeso k'anwata, amma Babar mu ta dage seda ta juye abun a kaina, watak'il kuma ajalina ta gayyato da hannunta, dan wlhy ina cikin damuwa da firgici....." Nisawa Naja tayi "Anty kiyi hakuri kuma ki dinga adu'a inshaa Allahu lapiya lau zaki sauka kamar yanda yanzu Nana ta girma ta zama big girl haka zaki haife cikin ki lapiya lapiya da yardar Allah" Shiru tayi tana nazarin rayuwar duniya ko banda k'addara akwai hakk'in cin amana kenan haka wani yake da Allah, da zaran ka masa cuta tun a duniya zaka soma fanshewa... Zuwa yanzu Baba Azumi ta soma rikicewa da rashin Ummul, tana cikin tsananin damuwar rashin ta, abubuwa sun soma yi mata yawa gashi dai Ameenu yana iyakar k'ok'arin sa akansu amma ita hankalinta yafi kwanciya akan taga yarinyar ta a kusa da ita..... *************** Duk juyin dazatayi shi take gani take kuma tunawa, ya tsaya a ranta yanayin wasan daya mata jiya, har Allah Allah takeyi daren yau yayi su koma kwanciya wuri d'aya yafita tun safe be dawo ba amma bazatace ga second d'aya daya shud'e batare da tunanin sa aranta ba, a jiyan ya mata abubuwan dasuka tsaya a ranta matuk'a, Ashe dama haka yaa Maheer yake, dama Ashe akwai irin wannan fain cikin da ake cewa yana saka mutum kuka? Ita harga Allah jiya seda tayi k'wallah dayake mata wasan nin dako sanda take k'arama bazata ce ga sanda tayi irin suba, daren jiya har doki ya mata, seda ya tabbatar ya sanyata bacci ma tukunna shiya kwanta nashi baccin tana......... Wuraren k'arfe bakwai ta gota ya dawo gidan, kai tsaye d'akinsa ya nufa, harya shiga ya fito yayi kiran sophie ta kira masa Nancy, cikin mintuna k'alilan segata a d'akin, sanye acikin shigar ta ta alfarma doguwar rigan material me laushi, da akwai aljihu aduka gefen na rigar tayi kyau sosai babu kallabi a kanta, se sumar kanta data zube a k'asa batare data tufe shiba, wanda tsayinsa ya kusa zuwa kan mazaunanta STORY CONTINUES BELOW "Assalamu Alaikum" shine abinda ta furta a hankali, cikeda rangwad'a ta k'arisa a gabansa sanye take da k'ayataccen murmushi akan fuskarta alamomi sun nuna koda ba bacci take ba to kuwa a kwance take tuni "Barka da dawowa yaa Mahii, kayi hakuri banji shigowar kaba" D'an murmushi ya saka shima ya shagala da kallon ta "Ba komai, dama na dawo a gajiye shine zaki had'amun ruwan wanka a bath tube, ki tayani rage kayan jikina" D'an rintse idanta tayi cikeda jin nauyinsa kanta ce "Babu damuwa" Toilet d'in ta wuce ta had'a masa komai tasha mamakin k'amshin turaren wankan dayake amfani dashi, zataso danin kud'insa tasan koyayane seyayi tsada...tajima a toilet d'in tana gyare gyare kanta fito da towel a hannun tana tinkaro inda yake zaune ko takalmi be cire ba, bata ganewa kansa ba yau ko fara'ar nan babu a fuskar sa ya tsuke fuskar nan tamau dukse ya mata kwarjini sosai ba kad'an ba, tsugunawa tayi ta kwance igiyar takalmin sa ta zare masa su ta cire masa sock's sannan ta d'ago, kasa yin komai tayi bata saba ba bata kuma iyaba, bece komai ba ya mik'e itama seta bisa ta zare rigar dake saman ta kasa,dayike suit ne ajikinsa ta ware masa neck tie cikeda nutsuwa sannan ta soma b'alle masa botiran rigar sa.......... Seda ta cire su tas sannan ta cire na hannun rigar ta zare masa rigar, shidai bece komai ba babu kuma alamun se kulata koya dakatar da ita, nauyi ita kuma takeji jitake tamkar k'asa ta tsage ta shige, singlet d'in jikinsa ta zaro daga kasan wandonsa ta zare masa, se wani kallo yake binta dashi yana lumshe ido alamar gajiya......kallon shi tayi gargasan girjinsa daya wani kwanta luff har zuwa tsagun marar sa yayi k'asa ga packs d'innan guda shida sunsha zane,batada dabaranyi dan bazata iyaba "Kayi hakuri" Da d'an mamaki ya kalleta "Menene?" Shine tambaya daya mata "Bazan iya cirewa ba" lumshe idanshi yayi ya juya "Kibar d'akin kawai" tsaye tayi taga kaman yayi fushi "Kayi Hak'uri yaa mahii, wlhy ba raini bane ban iya bane" hannu ya d'aga mata alamar ya isa sannan ya mata alamar barin d'akin da hannun shi, Jiki a sanyaye ta juya kome ya sameshi oho, dukya sauya tana isowa d'akinsu sophie ta rik'eta "Ke yau kinga idon yaa Maheer, wlhy halin yakeji ni seda ma ya tsoratani da yanda yake magana kodai waccen kojajjiyar ce ta hautsino mana shi" Tabare fuska tayi tamkar zatayi kuka "Wataqil kam, dan cewa yayi na had'a masa ruwan wanka na rage masa kayan jikinsa to kuma sophie tsakani da Allah ni kunya nakeji, fisabilillah wai sena kama na cirewa babba kaya" Dariya tayi "To Amarsu ya kukayi da angon?" K'wallan datake tarewa ya subo mata "Ni nacire sauran wandone bazan iya cirewa ba, nikam nace yayi hakuri shine yayi fushi ya koroni har yana juyamun baya😭😭😭😭" Dariya tabaiwa sophie ta somayi har tana rik'e ciki "Wlhy kinada wawta Nancy, ina mijinki ne? Kin fasan wacece kishiyarki wlhy ki rage wawta da kunyan kin nan, ni wlhy aka auramun Mahal nizanna riqa yi masa wanka ma ba cire kayaba, mujin kine fa, tukunna ma tsaya ina tare kuka kwana jiya mesa bakiqi kwana da shiba?" Kallonta tayi "Sekinyi auren ki gane wlhy da kunya matsananciya sophie, tayaya zan kalli yaa Maheer na cire masa....kai dama bashi bane wani na aura, yayana fa" Dariya tayi "To ki ringa daurewa kina masa abinda yakeso, yaa maheer seku shekara dari tare baki san halinsaba bayasan gadda shi sam, kuma shi ai yaga ke matar sace bakomai bane wannan ai" shiru bata kulata ta qara cewa "Ki tashi kije gunsa ki bashi hak'uri" Ba musu ta mike tana kokarin k'ulle sumar kanta kamar yanda takeyi idan ya dameta seta masa kullin bakar leda..... A bakin gado ta sameshi ya zauna dafe da kanshi dagashi se towel d'ure a qugu, zama tayi kusa dashi tace "Yaa maheer kozan tayaka da shafa oil d'inne ?" D'ago kansa yayi ya kalleta tasha mamakin ganin idanshi yayi jajir, da sauri ta rik'o hannun sa STORY CONTINUES BELOW "Subhanallah yaa Maheer meke damunka" bece mata komai ba se kallonta yakeyi ana haka wayanshi ya soma ringing banza yayi har kiran ya yanke,cen kuma kiran ya k'ara shigowa wannan karon janyota yayi yana lumshe jajayen rinannun idanuwan sa...ya d'auka tare furta "Assalamu Alaikum" A d'ayan b'angaren kuma Umma ce "Alaikassalam Mahii" "Na'am Umma ina jinki" "Cewa na maka ka sauyawa yarinya suna daga Hafsat zuwa wani sunan daban karka kasance namiji me haddasa fitina a gidansa, matarka takirani a waya tanata kuka, sanin kankane ba macen dazataji dad'i ace anmata kishiya bata saniba kuma da k'awarta, har kullum ina maka gargad'i akan yin adalci a tsakanin matayenka, Abbanka yanada dalilinsa na cewa kar a gaya mata yanzu, gudun fitina yakeyi kuma yasan halin mata su tashi hankulansu agarin daba nasuba basuda kowa" "Umma kiyi hak'uri ai nace zan sauya sunan inshaa Allah" "Sannan takirani yanzu ma akan wai kabar gidan zuwa gidan su Sophie, meye dalilinka nayin hakan? Baka gudun tayi zargin wani abu kota gano wane abun" Ranshi ya matuk'ar b'aci dandai Umma ce "Umma bazan iya kwana gida d'aya da sirikata ba wlhy, kana bazan iya zama awani wurin ni kad'ai ba, ki k'yalesu kurun suna kuma da kikace a sauya mata seki zab'a danni harga Allah bansan wani suna dazan baiwa babyn ba" Nisawa Umman tayi tasani sosai Maheer yanason sunan daya zab'a d'in nan takuma sani bazeji dad'in haban ba amma matar safa? Suna zaman lafiya idan ta gano sunan kishiyara aka sakawa babyn ta yaya zataji? Ai suma seta d'aukesu mutanen banza ... "Autan maza kayi Hakuri, ka baiwa yarinyar nan suna Aisha kaga itace mahaifiyar Abban ku semu sakala mata sunan daya dace ana kiranta dash shida kanshi zeji dad'in hakan, inshaa Allahu" "Babu damuwa Umma zanna rik'a kiranta Mamaa Allah yasanya albarka" "Ameen autan maza, Allah yamaka albarka, kayi hakuri nasan halinka da zuciya dakuma yawan ciwon kai idan ranka ya b'aci dan Allah kayi hakuri, kakuma nemi hanya me sauk'i ta gayawa matarka aurenka da Hafsatun idan kun dawo, naji ance nanda kwana 30 zasu kammala jarabawa suyi hutu seka tarkatasu ku dawo gida anan semu sanarwa matar taka" Nisawa yayi "babu komai Ummana yanda duk kikeso haka zanyi,albarkanki kurun nake nema" Albarkan ta sanya masa ta masa godiya sosai sannan sukayi sallama, kanshi dake sara masa ya danne da duka hannayenshi guda biyu jikinsa harya soma rawa tsabar macin rai, baze iya yiwa ummansa musu ba, kisane kurun zata sakashi yace bazeyi ba, amma Islam ta gama rainashi wlhy, shi zatawa iskanci da wulak'anci takai k'ararsa gun iyayensa abinda yafi tsana, bazata masa magana bama setaje ta gayashi da iyayenshi lallai ma Salaha....... Duk se Nancy taji wani iri batajin me umma ke cewa amma ta fahimci akan sunan baby ne...... Rintse idanta tayi ta kai hannunta sama waits nashi ta zagaye "Meyake damunka Zauji?" "Ba komai ki kawomun coffee" zuwa tai ta had'o ta kawo masa,da kanta ta bashi coffee din me zafi yasha sosai, sannan ya nemi gadon ya kwanta luff dashi, kasa barinsa tayi shi kadai taje ta rage kayan nauyin jikinta zuwa nashan iska, tadawo d'akin da wayarta a hannu, kai tsaye gadon ta d'are ta soma daddan na masa bayanshi da kafad'un shi yana jinta amma ko motsawa beyi ba, sabida harga Allah yanajin dad'in tausar seda taji ya soma minshari sannan ta rufe shi da duvet, tana shirin kwanciya ta huta wayanta yayi k'ara, lambar London ce amma batada lambar, a sukwane ta d'ag kiran "Bak'ar ashana k'ona gari, kina ganin kamar kinci galabane da kika sanya aka sanyawa 'yata sunanki? To na nuna isata na kira sirikata for ur information yanzu sunan yarinyata Aisha, banza karuwa mebin mazan mutane er tasha, uwarki ta k'are a karuwanci kema acen zaki k'are wlhy keda mijina har abada er dandi er dadiro yar kwararo haihuwar kan titi kawai" Ba kad'anba kalaman islam suna k'ona ran Hafsat tace "Yanzu islam ni kike jifa da muggan kalamai irin wannan mena miki? In isheni akan mijinki, wai idan har inason auren na mijinki ne ke kin isa ki hanani auren nashine? Wlhy so dubu yafi ganin k'ima na dake, ke kin manta inda aka fito ne dazaki rik'a kirana karuwa, kijimun iskancin banza wai bayarbe keceda inyamuri kafiri, bari kiji islam wlhy kika k'ara kirana kina zagina sena nuna miki baki sanni bq tukunna, halacci ne kurun nakeyi ina qyaleki bawai don ina tsoron kiba,k'wacen miji kuma zakiga yanda akeyinshi wlhy banza shasha.... " Uwarkice banza, nace matsiyaciyar uwarkice banza, mugayen buzaye masu bak'ar aniya, wlhy sena sanya an lahanta miki rayuwa akan maheer mayya kawai, ko a lahira idan ana aure bazaki tab'a aurar maheer ba bare kuma a duniya ana zaune, shegiya er tasha" tsaki nancy taja ta katse kiran.......kai tsaye Anty Fareeda ta kira, tana d'agawa ta saka mata kuka "Anty Fareedah ni dan Allah kicewa Abba a miyar dani school a kano, wlhy na tsani zaman garin nan islam ta sakoni agaba Anty Reedah bata bari inashan iska, yanzu ta kirawoni har ummana seda ta zaga tana cemun karuwa waye waye" Nisawa Fareedah tayi Aiki kuwa yagano islam tabbas, amma ke Hafsat ki dena damuwa, umma tamun magana ma akan sunan baby nina qara bayarda goyon bayan a sauya, yarinyar sekin tashi tsaye makissaciya ce,ki dena kuka ina kan aiki yanzu anjima zan kiraki" sallama sukayi ta zauna tanata kukanta seda ta gaji bacci ya kwasheta a wurin... Maheer dake baccin sa sama sama yake jiyo sheshekar kukan Hafsat, ita arayuwa ta tsani fitina, dame yinshi ranar dukda islam ta gano Maheer mijintane kenan seta hallakata kasheta ma zasuyi ita da uwarta, Har lokacin idanshi jajir yake kamar gaushin wuta, dak'yar ya samu sassauci ya saukesu akanta "Hafsat Lapia dai?" Dagowa tai sukayi ido biyu,ta k'ara shagwab'e fuska "Toba islam baceba taketa xagina,Har Umnana take cewa karuwa,waini karuwa ce waye waye,Allah kuwan nina gaji da wannan abin,ka miyar dani gida nayi makarantan acen" Dafe kanshi ya k'arayi dake barazanar tsage masa ya tsani fitina, wannan Islam tazame masa rigima arayuwa, ko yanzu yasha fad'an daya mugun b'ata masa rai gun Abba akan islam, wai mahaifinta tasa yakira Abba akan wai tanaso ta sanya suna amma an hanata sakawa, shine Abba ke fad'a akan ba'a sanar masa ta zab'i wani suna ba dabaze hana a saka mata ba, ya bada umarni tare da bada damar a saka sunan da uwar keso.....yasha fad'a akan soma nuna rashin adalci har yana ik'irarin raba auren sa da Hafsat tunda ita dama baso takeyi ba, danshi yayi idan baze adana zamtowa hafsat matarsa for d tme bng ze raba auren....tunda yaji qazafin da suka masa yaji gaba d'aya daga islam din har iyayensa sun sire masa, yasani be bata zab'in sunaba amma bata ce dashi ga wanda takeso ba, yana mamakin ma yanda ta lalubo sunan mahaifiyar Abba danshi maganat br tab'a had'ashi da ita ba, baya ma raba d'aya biyu inshaa Allahu Anty Nasara ce.....gyaran kwanciyarsa yayi zuwa zama ma ya janyota jikinsa.. "Hafsy na kiyi hak'uri kinji, komai yayi farko zeyi k'arshe, kuma wannan muguwar kalmar datake jifanki dashi zan mata magana karta k'ara sam bazan lamunci wannan furucin akan princess naba" Lafewa tagi ajikinsa "Ni Yaa maheer Allah seka miyar dani Nigeria, Islam ta sakoni agaba, auren ma nawa akanta yazama kaman dodo, se b'oyewa akeyi,kuma ace ta hanani sukuni ni idan aka barni anan Allah bazanyi karatu ba" Shagwab'ar nan ta Hafsat tana burgeshi, sumar kanta ya soma shafa mata "Kinga Princess hakuri zakiyi, ke kinga alamun zan iya rayuwana bake aciki? Tayaya zan bari kimun nisa ne wai? Idan kika koma Niger duk wasu harkoki nawa kin dakatar dasu, ki kwantar da hankalinki bazan bari ta k'ara miki irin wannan ba zan mata fad'a kinji" K'ara matsawa tayi jikinsa sosai yana kakkamashi "Idan ta k'ara zagina nina ramawa zanyi, dan kawai taga ka mata ciki ta haihu se wulak'anci nima ai zan haihune" murmushi yayi "Ko mesa yanzu hafsat ke wawta oho?" Abinda ya fad'a kenan aranshi kanya nisa yace "Ea fa hakane, kema zaki samu babyn ki, kuma akan sunan danace na baiwa yarinya hafsat kiyi hakuri wani uzuri ya taso da dolene seya kasance an sauya, amma na miki alqawarin indai inada rabon tara 'ya'ya anan gaba, inshaa Allahu zan miki Takwara" Murmushi tayi "Babu komai, dama mamanta ta gayamun bazata bari asaka ba, kuma banji komai ba kaima tafika Gaskia, sunan kiahiyartane fa, ayi haka" Dariya yayi "Halinki nakeson babyn ta d'akko shisa, amma ko yanzu ina mata fatan ta dawo kamar ke" Murmushi ta k'arayi "Yaa Maheer dan Allah idan bazaka damuba na tambayeka mana?" "Ba komai Bismillah ina jinki" "Meyake damunka? Kasan idanka ya sauya launi zuwa ja, yanayin ka gaba d'aya ya nuna kana cikin damuwa kana kuma jikinki yayi zafi alamun kanada zazzab'i, iskar nimfashin kama ta sauya zuwa d'imi, menene damuwar? Bayan zazzab'in nan na tabbata akwai abinda ke damun ka na b'acin rai" Nisawa yayi STORY CONTINUES BELOW "Zazzab'i ze tafi inshaa Allah, B'acin rai kuma kam tabbas akwaishi, sedai fatan Allah ya yaye, karki damu Angel komai ze wuce" Lafewa tayi a k'irjinsa "Bazan tab'a dena damuwa ba muddin kana cikin wannan halin mijina, tayaya zanyi walwala alhalin kai kana cikin damuwa? Yaya zanyi walwala alhalin kai kuma kana cikin hali Rashin lapiya, zancen ciwo kasha magani, b'acin rai kuma kayi hakuri komai yayi zafi maganinsa Allah, kana yawai salatin annabi komai zezo ya wuce kamar ba'a yiba" Mamakin hikima irin na yarinyar yakeyi,harta fahimci halin da yike ciki, bashida abokin daze fad'awa damuwar sa, amma bazezo ya soma yin maganar wata da wata acikinsu ba, abinda ke tsakaninsa dako wacce daban "Nagode miki da yawa Hafsy na, kin kasance mace me hikima da sanya salama a zuciyar mijinki, ina miki son so hafsat, bana so kike sakawa ranki wani abu akan soyayyata agare ki, wlhy ina sonki sona gaskia na tsakani da Allah, komai zan iya yi a kanki muddin be sab'awa shari'a ba, ki taimaka ki soni Hafsat, ki taimakeni kar a rabani dake, dukda bazan sanar dake zallan abinda ya faru ba, amma ki sani har barazanar k'wacemun ke akayi yau, a raba aurena dake na har abada, inda koda zan mutu bazan musaba akan abinda banji ba ban gani ba, wannan zazzab'in na tunanin rasaki ne, dan nasan halin Abba tsaf ze raba auren, ni kuwa rabani dake tamkar rabani da rayuwata ne" D'ago kanta ta k'ura masa ido na 'yan dak'ik'u hak'k'a tafara sabawa da Maheer, kulawan dayake bata ya sanya ta soma yin wata muguwar shak'uwa dashi, babu inda take samun nutsuwa aduk fad'in duniyar nan sama da kwanciya saman k'irjinsa.....lumshe masa idanuwanta tayi tana murmushi "Koda zasu kasheni ni dama nida mijina mutu karaba ne takalmin kaza, bame rabani dakai Maheer kaine jigon rayuwata, Babu amfani acikin rayuwata idan ka mata k'aura ....kadena damuwa akaina yaa Maheer, ni takace har abada" Ba k'aramun dad'i kalamanta suka masa ba, ya gagara furta wata kalma, se murmushi yakeyi, a hakan ma ya wadata koda bata furta masa kalmar soba wannan kad'ai ya ishesa k'warin gwiwa inshaa Allahu, a daren yau seya mayar da ita cikakkiyar mace, Abba yayi hakuri baze lamunci rayuwa babu hafsat acikiba. ************* Ameen yana zaune yana baiwa ummul abinci abaki aka fad'o musu acikin d'akin na hotel dasuka kama, tashin hankaline wanda ba'a saka masa rana ya ziyarcesu dukkansu, mik'ewa yayj yana zare ido ganinsu da bindigogi "Malam lapiya dai me kuke buk'ata?" Kwad'a masa bakin bundiga wani daga cikinsu yayi kai tsaye ya zube wurin a sume,Ummul da qatoton cikinta tayo kansa nan take suka bad'a mata wani powder wanda atake ta zube awurin, d'auketa sukayi sukabar hotel d'in gaba d'aya..... ****************** Ameenu se farkawa yayi ya ganshi yashe acikin d'akin, ummul da wayanta da jakarta da komai suna wurin, abincin dayake bata dukya tarwatse agun, wata uwar qara ya k'wallah ya furta "Ummul!!!!!" Da iya kacin k'arfinsa , tamkar wani zararre haka ya zauna yana kuka, yayi ma ishinsa kan yakai ga hukumar 'yan sanda ta Niger har hotel d'in anga shigowar su an kumaga fitarsu da ita sedai a cctv ne da aka duba, kuma abinda yafi d'aga masa hankali shine shima ya shaqi wannan powder cix tun daren jiya karfe 8 da en mintuna abun ya faru amma segashi ya farka tara na washe garin ranar, idan hakane report d'ayakai baida wani amfani dan ya tabbatar sunbar cikin k'asar ta Niger......Yaje ya gayawa Naja da Innan Hafsat, ya sanar musu su kula da Ummimi, Zeje Niger yasan Alhj Baba ne da wannan d'anyen aiki ........ *********** Ummul kuwa koda ta farka seta ganta a kwance saman wani faffad'an gado me kyawun Gaske, d'akin yayi sosai amma se ita kad'ai ba kowa, shiru tai tana tariyo abubuwan dasuka faru, kanta kai ga karshen tunaninta har an banko k'afar an shigo, wani dattijo ta gani cikin shiga ta kamala kallo d'aya zaka masa ka tabbatar shi babban mutum ne, kazalika duk wanda yasan Ameenu dazaran yaga wannan ze tabbatar sunada alak'a ta jini sosai, murmushi ya mata "Sannu 'yata kina lapiya?" Kasa amsashi tayi ze zare ido takeyi "Kiyi hak'uri kina Niger na maidoki chad, mijinki Ameenu nine ubansa, babu abinda zanyi da lpiyarki, bashina yaci be biyani ba, shine naketa renon wannan cikkn naki, har gashi yanzu ya shigo wata na takwas, shine na d'akko ki, domin kuwa yaron cikinki dashi zan fanshi bashina dayaci, idan Allah yasa kinada sauran shan ruwa agaba, zan barki araye kici gaba da haifamun 'ya'ya kobada Ameenu ba, koni zan iya miki ciki da kaina ko yarana, idan kuma bakida rabo kina haihuwa zan kasheki, idan kikayi gaddama ko yunk'urin guduwa wlhy tsaf zan harbeki, bari ma kiji, na baiwa masu tsaronki dama dazaran kinzo guduwa su harbeki, Ameenu kuma kedashi har abada anan chad zaki zauna har k'arshen rayuwarki" yaudai kukan ma ya gagari Ummul, abu d'aya ta sani Ta ari *WATA FUSKAR* wacce ba tataba ta siyowa ajalinta, tanaji ajikinta a hakan zata mutu, ace da aurenka wani gardi tsoho yana ik'irar'in ze maka ciki koya saka wasu su maka, dabata ci amanar Hafsat ba watak'il da k'addarar nan bata fad'a mata ba, yauga inda son abin duniya ya janyo mata musiba...Baba azumi ta cutar da ita sosai ba kadan ba wlhy ..harya yabar d'akin ko motsin kirki bata yiba, seda wani ya shigo ta rok'eshi akan tanason hijabi da sallaya ba jimawa kuwa aka kawo akwati da kaya da yawa da hijabi da sallayar, aka tambayeta abinci shikam ta kasaci ko kadan kuka kuma yaqi zuwa sam!!! ************** Sosai ya had'e fuskar nan ba alamun wasa, islam dukse jikinta yayi sanyi "Honey dan Allah kayi hakuri" kallo ya wurgo mata cikin b'acin rai "Mesa zakimun k'arya, ki had'ani da iyayena? Yaushe mukai zancen suna kikace ga wanda kikeso, a rayuwa nafi tsanar mutum me mun karya fiye da kowa, haka kawai zaki had'ani da iyayena, ki sani wlhy ba'amun k'arya an sakawa yarinya Aisha fine! Amma ki sani nine ubanta kuma wlhy kinyi kad'an ki nunamun fin k'arfi ko iko akanta,lastly duk wani abu daze shiga tsakanina dake nan gaba ya tsaya iya mu, kika kuskura kika k'ara kai k'arana awurin koma waye wlhh sena nuna miki iya karki!" Yana kaiwa nan ya fice abunsa be jira cewar taba, har kuka tayi tana son Maher amma yaya zatayi?..... ************ Bata jira ya aiko kiranta ba ta shirya cikin shigar ta me d'aukar hankali ta nufi d'akin sa....harta kai k'ofa sophie tace "Lallai ma su Nancy wuyanki yayi k'wari, sena gayawa Adda islam abinda kikeyi da mijinta" Murmushi tayi ta juyo "Point of correction mijinmu dai ko?" Dariya suka saka sha'awa tace "Dan Allah yau akashe mana arna, ataya annabi yak'i mana, an tsaya ana baya baya, tsoron islam ya hana a baiwa muji hakk'in sa" Dariya tayi "Allah ya tsareni inji tsoron wannan wawiyar, kuma yau duk sekunsha mamaki na, en iska abinda kuke sonji kuma bazaku jiba dan bazan fad'a ba wlhy" Dariya suka saka atare "Mune 'yan gashi aje dai idan tayi wari maji" Bata kula suba, yaran nan azo amusu aure tafada a zuci tana murmushi........ Ba b'ata lokaci mutumina ya jasu salla raka'a biyu kacal, ya musu adu'a sannan ya fuskanceta "Hafsat yau inaso zan sauke nauyin daya rataya a wuyana na mujinki, inaso in sanya hannu atakardar zamtowarki cikakkiyar mace, nakumasan keba yarinya bace kina kuma da iliminki na addinin daidai gwargwado, bazan miki dole ba, idan baki shiryaba daganan har nan da shekaru goma komafi zan iya jiranki harki shiryawa hakan" Sadda kanta tayi kasa tana wasa da 'yan yatsunta....sosai takeso tabashi amsa akan ta amince amma da wane bakin? Zata iya kuwa? Ko zasuyi shekaran annabi nuhu agurin bazata ita furta masa kalma ko d'aya ba!!!! Batai aune ba taji hannunsa a saman nata, yace Ehm Princess? Bakya buk'ata ne? Bakyaso ki kasance tare da mijinki? Idan hankalinki be kwanta ba karkiji shayin komai ki fad'a namiki alk'awarin zan barki harse sanda kika buk'ata, abu d'aya nakeso ki saka a ranki ina cikin tsananin buk'atar ki a yanzu" Har lokacin batace komai ba, bata kuma kalleshi ba se murmushi datakeyi matsowa yae daf da ita "Princess hafsy sarautar ya motsane ko azumun magana ne kikeyi?, Nace inaso in kasance tare da matana ko rowa za'a mun" wannan kalmar daya fad'a kansa tsaye daf da kunnenta ne ya sanya ta shige a k'irjinsa tana b'oye fuskarta aciki, ya kula sosai takejin kunyar sa yana son mace me kunya, tana daga cikin matayen dayake daraja darajarsu akoda yaushe, yasha fad'awa Kabeer baze auri mace wacce batada kunya ba se gashi yanzu Allah ya bashi....rungume abarsa yayi gaba'aya ya sanya hannu d'aya yana patting bayan ta a hankali "Princess kunya na kikeji? Ehm? Bani amsa mana kunya na kikeji?" K'ara cura kanta tayi a k'irjinsa, d'agota yayi ya zare mata hijabinta, lumshe idansa yayi yana godewa mak'agin wannan halittar, se k'ara shige masa takeyi in d name of kunya😂😂😂... Nan kuwa bata saniba kashe wa gogan jiki take k'arayi, numfashinsa se hauhawa yake sakamakon dadd'an k'amshin turaren ta me sanyi da sanyaya zuciya, a b'angarenta kuwa itama hakance kwanciyar hankali tare da nutsuwa me tarin yawa take samu a wannan k'amshin na jikin Maheer ko kad'an bata so ta rabu da jikinsa, sunyi shiru dukkansu na kusan mintuna uku kowanne da abinda yake sak'awa a ranshi, shine yai jarumtar furta1 "Ki d'agani mana muje kan gado" Kotak'i kotaso zamanta ajikinsa yayi matuk'ar tasiri agareta, bata shirya fitar kalmomin ba seji tayi sun fito a bakinta, a ranta take sak'a hakan batada labarin kalaman zuci sun fito "Inajin dad'in k'amshin dake fita ajikinka yaa Maheer, dan Allah ka barni" murmushi yayi "Tozan barki ajikina harse sanda kikace kin gaji, amma dukda haka muje kan gado nand'in gajiya zakiyi" seda ya bata amsa ta ankare da abinda tace, kasa motsi tai seda da kanshi ya mik'e ya d'agata chak zuwa kan gadon, zare jallabiyar jikinsa yae kana yawa kansa masauki a akan gadon tallafota yayi jikin ta rufe idanta tai yaja dogon hancinta ya sauke idanshi akan black lips d'inta asalin na buzaye shisa koda wane lokaci koda bata shafa lipstick ba yake kyau sosai yayi brown seyayiwa farar fatarta kyau matuk'a, Murmushin dayake kan fuskarsane ya fad'ad'a ganin yanda take rufe ido yanzu, ashe dama rainin na k'aryane dacen har mamakinta yake yanda take cire ma ta daddage ta k'ura masa na mujiya ido cikin ido "Ki kalleni mana Princess" murmushi tayi "Idan na kuskura na sanya idona anaka bana iya janye nawa, wani magnet ne inaga dakai a ido, idan ina kallonka bana iya janye idona sedai ko idan ka soma janyewa....idanma ba kallon ka nake ba idan idona yana a bud'e se magnet na idanka ya janyo nawa zuwa kanka nika barni a haka" Wasu lokutan setayi kaman bata surutu wani zubin kuma se kaga tana zuba tamkar ba ita ba "Naji nine me magnet d'in,amma kefa meye naki? Nifa dazaran kina wuri to bana shakka ko waye a wurin sena biki dana mujiya nake jin sauqi, nutsuwa ta gaba d'aya tattarewa take ta nemawa kanta mazauni a gunki, ke kuma wannene magnet naki?" Murmushi tayi kantace wani abin wayanshi ya soma ringing....janyota yai ya kara a kunne bayan ya d'aga kiran yana me k'ara matseta ajikinsa "Maheer wlhy ina cikin tashin hankali, Anzo har hotel an sumar dani an sace mun Ummul da tsohon ciki, Alhj Baba bashida imani Maheer, ko kasheta ze iyayi ayanda yakejin haushina, bansan me zanyiba, idan ma da hukuma nace zan had'ashi banida hujjan cewa shine kuma kaga asirinmu nida shi duk ze tonu tunda banida wata madafa, sefa ta wurin rabbu sabida nina me laifi ne" Zabura Maheer cikin tashin hankali "Subhanallah Ameenu, kagani ko kaga abunda nakewa gudu ko, yanzu da tun farko ka turo ta nan da babu abinda ze sameta, Niger ai ba garin b'uya bane ba, beside kanata zarya sati biyu kazo ka koma dole na gaya maka su sanya maka ido, yanzu kaga amaimakon kaika cutu 'yar mutane ce aciki bakasan halin datake ciki ba" Kuka ya saka masa1 "Wlhy na yarda maraici bala'i ne da inada iyaye na a raye meze sanya wannan azzalumin ya d'aurani akan gurb'atacciyar hanya irin wannan? Yanzu gashi banida mafita, ka taimakamun da mafita Maheer banida wani danasan ze fad'amun Gaskiya sekai Maheer, wlhy ummul tausayi take bai matuk'a, ga Nana Ummimi ma ita ba wani girma ba gashi tasha ciki, gaba uwarta a tare da ita, bansan ko itama yazo kanta ba" "Ka kwantar da hankalinka Ameenu, babu abinda ze sameta itama jinjirin kurun yake so ta haifa masa, yanzu shawara biyu zan baka idan ma babu kud'i a hannunka nizanyi komai na visa ka had'o wannan Najar da Jinjirar suzo mun nan London dough dai ba jimawa zan dawo amma gwara basa k'asar, kai kuma ka lafe akan maganar Ummul, karma ka nuna masa kadamu da d'aukewan daya mata, hikima kurin zata iya dawo maka da matarka amma rigima sam bazatayi ba, ina kacemun kadena kuje masa yanzu ka kanje gunsa har kuna gudanar da kasuwancin ku shima yadena maka maganar laifin daka masa, to kaima lafe masa ci gaba da binsa kamar ba'ayiba harmu gano bakin zaren" Nisawa yayi "To Maheer inshaa Allah zanyi yanda kace, amma Naja da Ummimi har ma na kaisu wurin wani abokina dake Ghana yanada kud'i sosai kuma akwai security sosai a gidansa, munyi magana akan ba inda zasuje Matsalar su d'aya Ummimi dake yawan tambayar mamanta, ta dinga kuka akan Ammy Ammy" Nisawa Maheer yai "Ka rik'a yawaita adu'a kana sadaka ana maka, inshaa Allah komai ze daidaita, ka kuma sanarwa iyayenta" A raunane yace "Na sanar dasu, yanzu haka Babarta tana kwance a asibiti hawan jini ya kwashe ta, se ciwo take akan 'yar wlhy duk na damu" ban baki yashiga yi seda ya kwantar da hankalinsa had'e da shawarwari sunfi 40mns a waya, Nancy dukta rud'e kan sui sallama "Yaa maheer meya samu Ummul na ne, jiyan ma seda na kirawo wayanta amma bejeba meya sameta ne?" Tausayinta yaji ya janyo hannunta yace "Hafsat ki saurareni kiji mezan gaya miki, dama na sanar akan matsalar da Ummul da Ameenu ke ciki to shine shekaranjiya se aka.........ya kwashe komai ya gaya mata, aikam kuka ta sanya masa wiwi wai ita 'yar uwata.....janyota yai jikknsa ya dinga rarrashi da ban baki, a haka hartayi bacci a jikinsa se sauke numfashi takeyi da k'yar alamun baccin ma ba a dad'in rai take yinsa ba sosai ya shiga damuwa.1 ******** Washe gari kuwa koda ya tashi harta bar d'akin, da tsananin ciwon kai ta farka akan damuwa, tanata mafarkin 'yar uwarta, last call nasu ma video call ne har aka bata mamanta taga k'aton cikin ummul se dariya take mata tana cewa tayi k'aton hanci ta zama k'atuwa....tana buk'atar kad'aicewa sabida ta samu yin nazari, be takurata ba ya shirya ya wuce abunshi gun islam, sallamar farko da fad'a suka fara wai jiya ya tafi da wuri kuma ko waya me yake nufi da ita, ya mata ciki ta haihu ze wulak'antata aiko laplfiyan baby ya kira yaji, Hakuri ya bata had'e da yi mata 'yan wasanni kan ya shawo kanta suci gaba da hirarrakinsu na soyayya tsakanin miji da mata se Allah kankace kwabo sun gama daidaitawa kamar ba'ayiba...

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 14"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...