WATA FUSKA CHAPTER 12 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 12

WATA FUSKA CHAPTER 12

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 12

  Da k'yar maheer ya shawo kanta ta dawo masa normal, yana fita a gidan tawa anty Nasara waya akan wai taci mata mutunci, sabida taga sun dawo tare, qwafa tayi tace+ "Kinga islam wlhy sekin tashi tsaye akan wannan shegiyar, har fa Abban mu bata bari ba, gaki da tsohon ciki yanzu ai yakai 7 month, ki zauna kina ganin azaba akan wata banza, ki rik'a zubarda hawayenki, k'wacen muji kuma bazamu bari tayiba indai muna numfashi, sannan shima ki dinga cin mutuncin sa kina zaginsa idan har kikaga yana shiga lamarinta, shifa namiji dazaran ka nuna kana tsoron sa shi kenan se raini" Share hawayen ta tayi "Kuma fa anty kosu sophie sun gama d'inkewa da ita, bakiga ba tamkar uwarsu d'aya ubansu d'aya amma nifa koda ace mukad'ai ne agdan basa kulani, ko magana na musu se hantara" murmushin mugunta anty Nasara tayi1 "Had'asu zaki rik'ayi da yayasu, dazaran sun kuskure miki abu d'aya ki saka masa kuka kr har sharri kina mak'ala musu ya musu d'an banzan duka zakiga sun soma tsoron ki" dad'i ne ya kamata ta dinga godiya ita ga mahaukaciya.... *************** Ameen da ummul suna cikin damuwa, rayuwa a b'oye rayuwa ce wacce bazata tab'a yiyuwa agaresu ba, sun shiga takura da matsin rayuwa ita harga Allah ma so takeyi ta gana da iyayenta, gashi kwata kwata Ameen yaki ya yarda suje sokoto akan yana jin tsoro kar Alhj Baba ya kamasu, yaudai kukan sosai ta sakawa Ameen daya sanya bab shiri ya shirya kaita gidan su ya barota cen itada Khadeeja, amma da sharadin bazasu fitoba bare wani ya gansu har se sanda ya nemesu, shi kuwa ya shiryawa kanshi tinkarar Alhj Baba indai ya adana iyalanshi, hakan kuwa akayi sukawa sokoto saukar dare ya kaisu gida, be b'oyewa iyayen ta komai ba dangane da abunda ya faru ya basu kudi masu tarin yawa yae umarni akan lallai karsuje ko ina, Baba iro da akayi tsammanin zeyi masifa tunda yaga kud'i yake washe baki yace ba komai k'addarace Allah ya kiyaye su dana gaba, ansha hiran yaushe gamo Ummul har waya tayi da Nancy sun jima suna hira, koda dare seda sukayi waya babu abinda ta b'oyewa er uwata inda hankalinta ya tashi ta bata shawarwari da adu'o in tsari kala kala kan suyi sallama. ***************** Sabon tane yanzu data waye a turai shan yoghurt duk dare kasancewar batacin abu me nauyi, wannan ne ya sanya ta baje a parlor tana duba laptop tanayin wani assighnment tana kuma kurb'ar shi a hankali, Islam ce tazo tana wani yatsina da wani qaton cikinta a wurin ta kalleta "Mujina yana kan hanya kuma anan zamu zauna, tinda ba gidan uban mutum bane seya b'acemun da gani da wannan shigar" mudubin idanta kurun ta gyarawa zama amma ko d'agowa batayi ta kalleta ba "Ke banza bakyaji dake nake magana, nace nunawa mijina tsiraici da ake tunda be k'yasa ba dakin hakura kin dena kuma yanzun ma ki bashi wuri sabida zezone yaci abinci ya huta" Ko kallonta batayi ba bare ta saka ran zata tanka ta madubin idanta kurun ta zare ta ajiye, warce cup d'in hannunta tayi ta watsa mata yoghurt d'in a fuska da jiki baki d'aya wanda wannan yayi daidai da shigowan sophie da Maheer, da sauri sukayo kanta Maheer yana furta kalmar "Subhanallah Islam kina haukane" mik'ewa Namcy tayi tana yarfe hannaye "Nashiga uku yaa Maheer idona" ta furta tana yarfe hannaye tamkar wacce aka watsawa garin barkono a ido, da sauri yayo kanta ya rik'e kafad'unta, se zabari takeyi tana ihu "Dan Allah ka lashen wannan na idona yanamun zafi" seda ya kalli islam da sophie sannan ya rik'e fuskarta da duka tafukan hannayensa guda biyu ya sanya harshe ya lashe na idanuwanta duka biyu sannan ya zaro hanky ya goge mata fuskarta..k'in bud'e idanta tayi tana meci gaba dayin kukan "Yaa Maheer har yanzu idona zafi nashiga uku zan dena gani" rik'o hannunta ya kumayi "Muje gun wash hand base ki wanke Fuskan ki, da kanshi ya wanke mata fuskar amma fir tace ita zafi takeji, kuma tak'i ta bud'e motan, se sannu sophie ke mata " ke safiyya jeki ki d'akko mayafinta ko abaya haka mu had'u dake mota, gwara muje asibiti kurun" rik'e masa hannu islam tayi "Wlhy k'arya takeyi yoghurt aiba attaruhu bane babu inda zakaje" warce hannun sa yayi "Danla cen ni banson hauka, kinzo kin takurawa yarinya ina agaban idona kika watsa mata kofin yoghurt d'aya a fiskar ta, har a ido kinsan me takeji? Wawiya ma dake bakisan hakk'in d'an adam ba" Kan tayi magana safiyya ta iso da abaya ta zura mata,islam kuka ta saka ta shige d'akinsu su kuwa sukayi hanyar waje yana rik'e da ita har suka isa jikin motar "Yaa ko zaku tafi bani, zanyi bakine wlhy" d'aga mata kurun yayi ya sanyata a baya shima ya zauna a baya driver ne yajasu, seda suka hau hanya da kyau sannan yace "Mesa zakiyi k'arya ki bud'e idanki sabida nasan ba wani zafi dayake miki" A hankali ta bud'e idan nata ta saukesu a kanshi ta shagwab'e fuska, idan kam yayi ja sosai tace cikin muryan kuka "Toni meye laifina da ake wulak'anta ni, ni wlhy hostel zan koma abuna tunda ana kallo take mun wulakanci amma ba'a mata magana" rik'o hannunta yayi "Yaushene tayi ban mata magana ba hafsat? Lallai ne idan zan mata fad'a sekin sani, bata daiji ne amma ina mata fad'a sosai kiyi hakuri, zancen zuwa hostel kuma kema kinsan wannan kina fad'ane kawai" Turo baki tayi "Ai bana ganin ko fushi kana mata, sedai kaje cen ka dinga rarrashin ta, wlhy sena dinga sakata kuka wlhy seta gane shayi ruwane" kallon bakinta yayi yanda take zuba masifa yace "Kinga karki soma tashin fitina kiyi hakuri dan Allah" "Auuu nicema zan tashi fitina ba ita ba? Tab lallai ma" be kara kulataba seda suka zaga gari tukunna suka koma gida, har lokacin fushi takeyi...suna shigowa Islam tazo ta rungume Maheer tana kukan munafunci, ita kuwa ta k'udiri niyyan seta gasawa islam aya a hannun ta....tana sani ta fadi k'asa har tana k'walla k'ara tace "Wayyo Allah na k'afana" har tana rike k'afarta..... Da sauri ya sake Islam yazo ya duk'a "Menene meya samu k'afar?" Tana kuka tace "K'afanane ya bige dana fad'i zogi sosai yakemun" rik'e wurin yayi harga Allah ta bashi tausayi yace "Sannu tashi kije ciki to se sha'awa ko sophie su saka miki man zafi" yunk'urawa tayi kamar zata tashi sekuma ta k'ara k'wallah k'ara tana ihu takoma ta zauna "Wlhy bazan iya tafiya ba ka kiramun sophie ta d'agani" cak ya d'agata zuwa d'akin su sophie har saman gadon ya direta yace sophie ta gasa mata sannan ta saka mata man zafi.... Tun daga parlor suke jiyo ihunta ana k'ok'arin gasa k'afar amma tak'i se dariya suke mata, baro parlor d'in yayi yazo d'akin ita kuwa ta biyo bayansa tana ta faman mita akan iskancine kurun ba wani zafi data keji, shi kuwa ko kallonta beyiba ya shige dama fad'a sukeyi tunda abin ya faru "D'are kan gadon yayi ya karb'i towel d'in hannunta ya kalli Hafsat " ki nutsu kinji Hafsy, da kaina zan miki kuma zan miki a hankali bazan miki da zafi ba ko kad'an a hankali zan miki, haka sukayi cirko cirko suna kallon su yana danna mata towel me ruwan dimi tana ihu sekace wacce za'a cirewa ido....koda akazo dirza man zafi ba k'aramun kuka tayi ba kaikace da gasken taji ciwo, kowama ya gama yarda cewan ciwon taji...takaicine ya sanya islam barin dakin duk yanda taso daurewa seda tayi, shi kuwa ya kasa ya tsare seda tayi bacci tukunna yabar d'akin... Ranar kam islam fushi tayi me zafi,tama dena kula Maheer, shima d'in shareta yayi har washe gari yayi babu mewa wani magana, haka Nancy ta fito da shirin zuwa skul tana d'ingishi ita adole waiga wacce taji rauni, Sophie se sannu take mata suka fita zuwa gate d'in gidan sabida normally sunada skul bus ita ke wucewa dasu to idan kayi late tana barinka sedai wata tazo, dayake yanayin karatun turawa ba irin namune babu ruwansu da d'an wane su kowa yana hawan bus ko taxi.....driver ya d'akko su Maheer shida Islam se cin magani sukeyi dukkansu, tsayar dashi maheer yayi akan su wuce dasu Hafsat, a gaba Sophie ta zauna yayinda Hafsat ta zaga gefen da maheer yake ta bud'e tana ta faman d'ingishi ta shige, Matsawa yayi tana zaunawa ta rik'o hannun shi "Aauucchh yaa Maheer k'afara zafi" kallonta yayi zuwa yanzu ya soma fahimtar hadda raki acikin lamarin na Nancy hannunshi dake tsak'ale a nata ya kalla yace cikeda kasala "Sannu ze dena ne" k'ara matse hannunshi tayi ta kwantar da kanta saman kafad'arshi "Inama ace yau banida test daba inda zani wlhy" murmushi yayi amma shi kanshi beji nutsuwar hakan datayi ba, d'an matsawa yayi kanta ya goce ta d'ago suka had'a ido sunfi 20 secons suna kallon juna ta had'e fuskar nan alamun yaya zakamun haka bece komai ba se k'ara matsawa kusa da ita da yayi ya kasa koda kwakwaran motsi mayar da kanta tayi saman kafad'an nashi ta kwanta tana wani basarwa, islam yi tayi tamkar bata gansu ba, yanzu ta gama hak'ik'an cewa kanta cewar lallai Maheer neman Hafsat yakeyi, idan hakane sun cucesta kuma basu kyautaba ko kad'an.....sannan kuma bazata tab'a yafewa dukansu ba musamman ma ita Hafsat, seta tozartar da ita....... ************* Durk'ushe yake agaban Alhj Baba yana bashi hakuri amma k'ememe mutumin nan ya had'e rai "Kai kana gani kamar kafini wayau ne? Yaushe ma ka taso akan harkar? Wanene kai? Nizaka guda akan matar ka? Dole ka kawomun ita in baiwa maza masu iyawa su mata ciki in biya bashin danaci danni kasan bana asara, mutane da yawa nake huld'an cinikayya na dasu sauran masu cikin na siyar danasu" "Kayi hakuri Alhaj nabaka yarana sunfi 10 wannan iyalin tawa ita nake fatan qarasa rayuwata da ita har abada, nima inaso in samu magazai kamar yanda ka sameni kayi hakuri, zanyi wani auren semu haifa maka adadin dakake buqata kayi yanda kaso dasu" mari ya danna masa seda yaga wutar lahira1 "Da Ummul nakeso, yaranta nakeso na siyar bana kowaba dan ubanka kai harkayi girman dazaka gayamun wai iyali dan kutirin uba" dafe wurin yayi ya mik'e tsaye "Nagaji da kashe yarana, inaji ajikina bawani adopting nasu da akeyi tsafi kakeyimun da yarana,kaima namijine kaje kayita haifar yaran mana kana yanda kaso dasu,koda ba tsafin akeyiba ai turawa kake siyarwa kace, shikenan mu muna musulmai su sutashi a yahudu mucewa Allah me, wlhy nagaji da bauta maka tunda bakai bane Allah, bazan kuma k'ara b'oye maka ba kaji na gaya maka, ka cutar dani ka gurb'ata tarbiyata Allah ya isa" mamakine ya sanya Alhj Baba yin sororo yana kallonshi har yabar gidan ya kasa koda qwaqwarab motsi... ***************** Kai tsaye gidansu Ummul ya nufa, yaje har huci yakeyi yana rarrashinta akan bakin cikin dayake ciki seda yayi mata kuka, ita kuwa Allah Allah takeyi ta fad'a masa tanada shigar sabon ciki, har asibiti taje ma satin cikinta 7, koda ta fad'a masa murna awurinsa ba'a cewa komai sunsha murnarsu susu kad'ai sambarka. *************** Maheer yana cikin damuwa sosai, bayason yanayin islam gata da uban ciki, ta d'auki fushi dashi me zafi kusan kwanaki biyu kenan bata kula sa, gashi batacin abinci yana ganin kamar yanayin yanda Hafsat keyin abubuwa ya dace ace Abba ya bari a sanar wa islam zancen auren nan, besan dalilin Abba na yanke wannan hukuncin ba ace ko yayyunsa babu wanda ya sani, abun yayi yawa amma yazeyi shi awa yace Abba beyi daidai ba haka yayita zarya acikin d'akin shi kad'ai yana neman mafita, daga k'arshe ya kira Umma, itace ta buk'aci ya d'auke islam daga gidan zuwa wani gidan tunda ko rent ne yana halin yin hakan, tunda yake a London gidanne kurun dasu...sosai yayi Na'am da shawarar ta, batare da b'ata lokaciba yasoma shirin neman gidan gadan gadan...ba b'ata lokaci ya samu wani gidan babu nisa da unguwar tasu ak'afa ma sekaje baka sha wahala ba, a parlor ya tadda islam ta had'e rai sosai ko kallonshi batayi ba zama yayi kusa da ita yace STORY CONTINUES BELOW "Haba uwar gida sarautar mata, menene haka na fushi da mijinki har bakya mai magana, yakamata kiyi hakuri, ki kuma fahimci ni Maheer mijin Islam, ina k'aunar matana fiyeda kowa da komai a duniya, ki taimaka ki sassauta mun wannan fushin dan Allah" kallonshi tayi lokaci d'aya ya narkar mata da zuciyarta ta langwab'e masa kanta tana me yimasa k'uri da idanta amma batayi magana ba "Ki shirya kayanki gobe zamu koma sabon gidan mu inda zamu kasance mumu biyu kacal, muci karenmu babu babbaka cox banso ake yawan bata miki ranki" Mik'ewa tayi "Da Gaske zamu bar nan gidan mumu kad'ai mu tafi abunmu" Rik'o hannunta yayi "E mana babyna, banaso aketa b'ata miki ranki ne, gwaramun in d'auki matana mu tafi abunmu" murmushi ta mishi "To yanzu zamu tafi?" Murmushi yayi shima "Gobe da safe zamu tafi babyna inshaa Allahu" Kissing juna suka fara alamun dukkansu suna buk'atar junansu, Sha'awa sarakan gulma dake lab'e sum sum ta wuce d'akinsu tana sand'a.....komai seda ta feshewa su Nancy tanata murna zasu rabu da k'aya , rayuwar hafsat ne ya mugun b'aci wanda har suka fahimci hakan, sophie ta tab'a ta "Baby sis menene, kin b'ata rai" harara ta wurga mata da wasa tace "Kece kanwata fa" bata kulata ba "Mesa kika b'ata rai?" Ta k'ara tambayar ta wayancewa tae "Kurun dai kinsan sabo" tafawa sukayi sophie da sha'awa suka had'a baki wurin cewa "Soyayya" kallon mamaki ta baisu dashi "Kaman yaya ban gane ba?" Harara shauty ta aika mata "Ko makaho yasan keda yaa Mahii soyayya kukeyi, batun yauba muka gano hakan, mu fatanmu ma kuyi aure mu huta da waccen muguwar bafullatanar" murmushi tamusu "Kanku dai akeji, muba wata soyayya damuke, yaa Maheer soyayyar en uwantaka ce a tsakaninmu ta jini, kamar yanda nake daku haka nake dashi" Dariya suka k'arayi "Idan tayi wari maji" sophie ta furta tana me barin d'akin zuwa toilet dake ciki...... ************ Wayan ta ta d'auka takira yaa Mahala be d'aga ba har kiran ya yanke gaba d'aya kusan so biyu, abinda ya faru be hanasu yin waya suyi zumunci ba sedai sukan rarrashi junansu, akan hakan k'addararsu ce basuda yanda suka iya se hak'uri.......kitchen taje ta nemi youghurt ta tsiyaya a cup seda tacikashi fam sannan ta juya wayanta ne yae k'ara adaidai sanda take k'ok'arin danna kanta cikin parlor d'in...cikeda shagwab'a tamkar zatayi kuka ta kara wayan a kunne "Nika rabu dani tun jiya nake kiran wayanka baka d'auka" a d'aya bangaren yace "Haba Hafsat nasani kema kinsan cewar be halatta muke yawan keb'ewa da junaba musamman dakikeda igiyar auren wani akanki, idan wata shawarar kike nema kimun message zan kiraki na baki shawara da kaina" kuka tasoma masa "Haba yaa Mahal, wanake dashi aduk duniya dazan sanarwa damuwana idan bakai ba, ni shikenan kowama ya tsaneni, sekaga kirana ka shareni mena maka" ta karashe maganar tana sharar k'wallah... "Ba haka bane Hafsat, ki fahimci magana na, mijinki bazeji dad'i ba yaga ina waya da matarsa, da ace wata alaqa ta soyayya bata tab'a had'amu ba tokuwa da babu abinda ze dameni, amma yanzu zargi seya shiga kinga seki b'ata aurenki ko" Tanameci gaba da kukan tace "Dukda haka tunda na matsa maka da kira aikasan da wata a k'asa, ni wlhy ka dena sona ko kad'an" shiru yayi sam ta kasa fahimtar sa "Kiyi hakuri kinji, inasu sophie sufa ba wani sanina sukayi ba, ina matsayin d'an uwansu amma basu sanni ba" murmushi ta d'anyi, suna ganinka mana a hoto, abinda har kama ma kakemun da Sophie" murmushi yayi STORY CONTINUES BELOW "Allah ko?" Bata amsa shiba yaci gaba "Menene damuwarki Hafsat?" "Ya wuce kawai karka wasu en damu" beso ya takurata seyace. Kurun "Zan kiraki anjima yanzu ina tuk'i ne" "To Yaa Mahal thanks alot bye" sukayi sallama, kallonta sosai Maheer keyi baya ko k'iftawa.......mik'a mata hannun sa yayi tabi tafin hannunsa da kallo "Wayar zaki bani?" Ya furta cikin dakakkiyar murya "Akan me?" Itama ta furta cikeda tsiwa" bece komai ba ya juya abinshi itama tana mita ta juya zuwa cikin d'akinsu...abinda ya mugun k'onawa Maheer rai, yanaji take cewa wani wai baya santa yanzu tana matar auren takewa wani irin wannan maganar lallai ma sosai Hafsat ta rainashi amma zata ganene wlhy dan baze d'aukar mata ba.....kai tsaye mahal yawa waya .... Bayan sun gaisa yake tambayar sa "Menene yake sanyawa kake waya da Hafsat har yanzu? Zancen haskia mahal banaso ka den plss" Murmushi mahal yayi "Kayi hakuri, koba komai Hafsat k'anwatace, naso Ummul ma ina kallo abokinka yamun k'wace banbita ba, yanzu kuma ka kwace mun Hafsat bance komai seka kirani kace na dena waya da ita, niba jahili bane Maheer ko budurwar dabata aure banbi ba bare kuma matar aure, matar auren ma matar d'an uwana, kasani matsayin duk dasu sophie sukeda a wurina irinshi ne takedashi awurina, hanyar gaskiya kurun nake d'aurata akai bawai muguwar hanya ba ya kamata kasan wannan" Nisawa yayi jikinsa yai sanyi da maganganun mahal "Kasan matane masuda Hankali Mahal amma idan bakaji dadin magana naba kayi hak'uri ba wani abun nake nufi ba" gyaran murya Mahal yayi "Koda baka kurani bama nizan kiraka ayau nayi niyyan hakan, inaso kasani Hafsat shekarunta kusan 20 yanzu ta mallaki hankalin kanta, baze yiyu ace kana tauye mata hakkinta ba matsayinta na matar aure, koda umarnin Abba ne rufe maganar amma ka duba lamarin, aure ba abin wasa bane, nasani Abba shi gudun fitina yake agarin daba kowa amma fa kayi kokarin koda a b'oye ne ka nuna mata itad'in matar aurece, na tabbatar ka fahimceni sarai...abu na gaba kuma dama inason namaka waya akan sophie, yarinyar tamun inaso zan aureta ina fatan zaka tayani yak'in neman zab'e" Dariya Maheer yayi "Kai mashaa Allah amma naji dad'in wannan maganar taka sosai, zanma sanarwa daddy" murmushi shima yayi "London d'in zanzo zuwa nxt week nida ummy na fa, kabari na soma kafa gwamnati tukunna tunda ka kwacemun budurwa dama dole ka bani kanwarka" Sosai suka dara kansuyi sallama ran Maheer yayi fes...message daya shiga wayanshi ne ya mayar da hankalinshi kan wayan "Inaso zamuyi magana by 1:am mu had'u a wurin motsa jiki" Hafsat ce tamasa wannan sak'on seda yaje d'aki wurin matarsa duka soye yayi wanka ya tabbatar tayi bacci sannan ya rufo dakin yama rufeshi ta waje ya nufi wurin, da k'arfe 12:56 am ya isa wurin ga mamakinshi tarigashi wurin.....a hankali ta tako tamatso daf dashi har suna jiyo numfashin juna da bugun zuciyar junansu, suka k'urawa juna ido na kusan mintuna biyu batare da waninsu ya gajiya da kallon d'an uwan saba, kowa da abinda yake sak'awa a ranshi mamakin ta sosai yakeyi yanda ta k'ware a iya kafe mutane da ido batako k'iftawa watak'ila hakan baya rasa nasabane da yawan sanya nik'afi ta kuma rufe idanta da gilashi... Anata b'angaren kuwa idanuwan sane ke hana nata motsawa duk sanda taso yin hakan, duk lokacin da idanuwansu suka gauraya tokuwa tabbas bazata iya janye nataba seya janye nasa, wani uban magnet ne ke manne su wuri d'aya da idan har yaci gaba da kallon ta tokuwa ita sam bazata iya d'auke nata idanba.....shine ya soma magana batare daya janye idanshi anata ba, cikin sanyin murya ya furta "Hafsat lafiya dai kira cikin daren nan?" Tattaro duk wani courage nata tayi tace har lokacin idanta na cikin nasa "Sabida niba mace bace, kokuma aurena yanada banbanci dana sauran mutane ne?" Be fahimci kalamanta ba "Subhanallah Hafsa, meya kawo wannan maganar me kika gani? Ban fahimce kiba" k'ank'ance idanuwan ta tayi sosai "Bazan kiraka acikin dare ba sabida ni banida kwana ko?" Se yanzu ya gane inda zancenta na farko ya dosa amma seya gaza furta wata kalmar se bakinsa dake motsi alamar da akwai abinda yake so yace...taci gaba da magana "Dolene ya zamar mun idan har inasan nayi magana dakai mijina sena b'oye, idan ba ahaka ba matarka bazata bari ba, dole ne nabi dare sabida in ari halin b'arayi in rufawa tsufana asiri kar a cimun mutunci in gaza ramawa bakuma nida me ramamun" yasani sarai dashi take cen cikin mk'oshin daya bushe masa qayau ya lalubor kalmar "Haba hafsat wannan wace irin magana ce?" Gyaram tsayuwarta tayi ta hard'e hannayenta asaman k'irjin ta tace "Banida iko da hurumin sanin cewar zaku bar gida kaida matar ka awurinka sedai a bakin shanun tallah, niba mace bace yaa Maheer, banida wani buri kenan arayuwa? Dan ban aureka asan rainaba bashi ke nuni dacewar banason aurena ba, bashi ke nuni da cewar na shiryawa kaina rayuwar zawarci ba, bashi ke nuna cewar zab'in iyaye ba Alkhairi bane ba, dan Allah be bani auren wanda naso aura ba bashi ze nuna cewar wai zab'in Allah kuskure bane, watakila wanda nakeson ba kuskure bane arayuwata, dan daddy yacr aurenmu ya zama sirri har zuwa wani lokaci sekuma yace dakai dukkanin hakk'okina ka wofintar dasu?" Gaza furta koda kalma d'aya yayi k'ara taku biyu tayi izuwa daf dashi ta kunce hannayenta data hard'e ta rik'o hanshi biyu "Ashe banida hakk'in tab'a jikinka kamar yanda islam keyi agaban kowa, ace ban cancanci a bani shinfid'a asaman k'irjin kaba, ni banida damar da za'a waremun lokaci na aci abinci atare dani,ajani salla, amun hira koda a waya matsayina na matarka ban cancanci ko d'aya ya maheer, ashe ayanayin yanda aurena dakai yazo ban cancanci rarrashi ba.....Ashe ban cancanci kulawaba yaa maheer kasani nima macece dukkanin abubuwan dana fad'a dama wanda ban fad'a ba suna raina nima inaso ina buk'atar tattalin nan danaga kanawa islam koma fiye, kana fad'ar soyayyar nan tawa a baki komenene yake kashe maka jiki kake kasa nunamun ita a sarari" shiru yayi ya kasa magana se janyota da yayi zuwa faffad'an k'irjinsa ya kwantar da ita...yana patting bayanta a hankali, besan dalilin saba na zama dolo wawa agaban Hafsat seya kasa yin magana ko wace irice agabanta, seya zamto mara wayau idan suna tare yakan kasance cikin, tsananin shauk'in ta idan suna tare....daidai sautin kunnenta ya rad'a mata "Kiyi hakuri, wlhy kinada dukkanin matsayin dababu wata macen dake dashi awurina, banida burin daya wuce in faranta miki, Allah ne shaidana idan farin cikin islam shine babban dalilin dayasanya zan d'auketa agidan to kekuma kwanciyar hankalinki shine abu mafi soyuwa agareni, wanda shine babban dalilin d'auketa agidan, abubuwan da idanuwanki ke gane miki na tabbatar kina daurewa ne kurun badan kin soba bakya cikin kwanciyar hankali, nasani k'azantar dukda baka ganiba tsaftace wannan ne ya sanya na yanke shawarar sauya mata wuri sabida ku nesanta da juna dan Allah kiyi hak'uri" matseshi tayi sosai ta hanyar zagaye hannayenta a bayansa tace "Babu komai na fahimceka mijina, hukuncin ka daidai ne, amma fa ka sani ina buk'atar kulawarka,kuma idan ka tafi ka rik'a kawo mun ziyara zanfi kowa farin cikin hakan" matseta shima yayi Inshaa Allah sekin gaji dani, kin sakani a farin ciki Hafsat, dole kema ma saka miki da fin abinda kikamun, ki sani wannan kulawar da kika bani ya wanzar da farin ciki me yawa a rayuwata Allah ya miki albarka kinji" sunfi 10mns rungume da juna sedaga baya ya d'agota ta fuskancesa ya sanya hannu a hab'arta ya sumbace bakinta sosai ya tsotse sa, har suka kusan fad'uwa bazatace bataji daban ba to waye ita da maheer ze sarrafata ta kasa zama garin tuwo!! Zama sukayi suna hira se wuraren asuba suka rabu da juna... Washe gari suka bar gidan shida islam komai nasu suka kwashe, ita kuwa ta kira anty fareeda ta gaya mata tayi yanda yace gama abinda yace, dama anty fareedah tasan da maganar auren, Umma da kanta ta gaya mata kuma takula da shigewar da nasara kewa islam ko a waya, shisa itama take tattalin Hafsat. Kema Hafsat sekinyi hakuri da abubuwa da yawa yanzu, idan kika biyewa zafin bakyason Maheer kece zaki wahala, karki kuskura kiyi tunanin yin zawarci da k'uruciyarki kada kuma ki bari amiki k'wacen miji sabida wlhy ke zaki wahala, k'awarki 'yar duniya ce kuma ta fahimci wani abu yasa take miki hakan, karki bari a fahimci akwai aure tsakaninki da Maheer dan idan Aunty Nasara ta sani yanzu kuna london kece zaki wahala, Anty Nasara yayatace amma koni ina tsoron mugun halinta, wannan ya sanya nace ki rike adu'a da azhkhar, ki kuma hakura da kalmar baso a aranki ki rungumi mijinki, koba komai ke baki san komai ba akan tarayrayar maza ita kishiyraki fa? Meye bata saniba meye bata iyaba? Ki kama kanki ki kama mijinki ki cire wannan zancen na yayi amfani da kud'i wurin aurenmi kinjini ba" D'an turo baki tayi "Anty Fareedah agabana yake wani kakkama matarshi, yana mak'ale mata amma ni ko oho, su dinga bani wahala sekace jaka shimafa basona yake ba, so kike yace ninake binshi ina zubar da ajina, ko jiya Allah banso nayi abinda kikace ba banaso ne kurun ranki ya b'aci" Dariya Antyn tayi "Hafsatuwalle kenan, kina bani dariya wlhy ninasan wannan k'unk'unin da kikeyi duk kishine ba komai ba, kina so kina kaiwa kasuwa" Tabare fuskarnnan tayi tamkar suna tare "Haba mana anty wane irin kishi kuma niba wani kishi wlhy, yanzu fa dazasu wuce konemana beyiba se fitowa nayi babusu a gidan kuma ko waya be nemeniba, ni ai sanda mamana ke sokoto tana auren Baba iro naga raba kwana akeyi ko" Sosai anty Reedah tagano Nancy cike take fam da uban kishi da soyayyar da batama san tanayiba.......murmusawa tayi "Kece zaki kirashi da kanki kimai shagwab'a akan be nemekiba, da k'afarsa ze dawo, haba mana k'anwata ni rgimar nan dukni akewa alhalin kuma bani nakar zomon ba" "Ni se anjima anty" Dariya tayi "To anjima zaki kirani koni na kira" "Duk yanda akayi anty, nafa gaya miki sun tafi abunsu kuma ke dariya ma kike ni wlhy kowama ya tsaneni, ace wai yaa Maheer yafison islam dani, ya dauke matarsa har yana ce mata wai bayaso ake bata ranta shisa ze dauketa" Rigiman hafsat na baiwa fareeda mamaki, idan ka ganta kamar bazatayi ba "Kinga kiyi hakuri gaskiya be kyautaba, zanmq yi masa fad'a akan hakan kinji" "Ni bance amar fad'a ba, kurun dai kice dani be kyautaba shikenan" murmushi ta qarayi. "Be kyautaba gaskia kiyi hakuri kinji" "To Anty nagode bye bye" kashe waya fareeda tayi tanata kwasan dariya, k'uruciya masiface kana kishi bakama san kanayi ba Allah shi kyauta. **************** Be ragewa ummul komai ba gameda yanda sukayi da Alhaj Baba, ya qara da cewar " Ni nasan Allah dole ya jarabeni da masifu iri iri ummul, seda k'arfin gwiwarki nake nema ki bani, gwarin gwiwa ki kasance tare dani komai rintsi, ina cikin ibtila'in rayuwa, nasha auren mace in kuma barta da wasu k'artin banzan suna yanda sukaso da ita, abun yana masifar damuna sosai yanzu, gashi kema anaso a tattab'amun ke, wlhy tallahi ummul zan iya kashe duk wani namiji daze tab'amun iyalina, bama keba babu mace koba matata ba dazan zura ido ayi fasikanci da ita, nasan halin Alhaj Baba idan yayi niyyan yin abu, kuma nasan kema kinajin tsoro sabida haka tunda kunada en uwa Niger inaso ki koma cen keda Naja da Ummami" tausayi ya bata ta shafi kanshi "Zan koma duk inda kace mijina, ina fatan zaka kula da kanka, kuma kana yawan yin istigfari dan Allah, kasan Allah yana yafewa bawa zunubinsa komai girmansa indai ya tuba ya dena gaba d'aya" Rungumarta yayi STORY CONTINUES BELOW "Zannayi Ummul inshaa Allah, karki damu kedai kawai ku kularmun da kanki......Had'e bakinsa da nata yayi, basu suka sararawa junaba seda suka tabbatar sun gama gamsar da junansu sosai da sosai, sannan suka wanka atare suka kwanta, dama a guess house na gidan su Ummul yake kwana tun zuwansu... Du Baba iro badu musantawa Ameen ba, se adu'a da duka masa, seda ya cika mata acc nata da kudi masu yawan gaske sannan da kanshi yakaisu Niger gun mahaifiyar Hafsat, kwanansa bakwai tare dasu sannan ya juyo ya d'auri anniyar yin yak'i da Alhaj Baba koda ze rasa ransa ne wurin yak'in neman enci..... *********** Yau dai kosu Sophie sun gano yanda Hafsat ke k'unci tun tafiyar su Islam da yaa maheer, ko magana ka mata se fad'a se tsokanar ta suke suna k'ara tunzurar da ita akan sun kasa gane kuncin me takeyi, har kuka seda tayi ta rasa dalilin kukanta....su islam kuwa anacen ana iyayi a sabon gida, an kasa an kuma tsare se shagwab'a ake mannawa Maheer shi kuma ya biye mata se yanda tayi dashi, ta mantardashi duk wata damuwa se soyewa sukeyi, gata da ciki watanni bakwai amma se jarabar tsiya, shi har mamaki take bashi wasu lokutan..... Yau tunda sukazo ko skul batajeba se soyayya aketayi dukta gama tatsewa Maheer ruwan jikinsa, yayi lagwaf, bacci yayi se magrib yanayin sallah sukaci abinci sukayi isha se suka kara adana kansu acikin lallausan duvet bacci ne me nauyi yayi awon gaba dasu basu suka farka ba se asuba, anan ake rigimar kuwa cox a b'angaren Hafsat kwana tayi tana zuba uban kuka babu k'akk'autawa, shikenan ita an aureta an mayar da ita banza, an hanata auren Mahal sannan kuma anzo ana cutar da ita wlhy zata rama ne, Anty Fareedah ma wayau take mata tafison d'an uwanta akanta, ta mayar da ita jaka banza anzo duk anbi an tsaneta, meye amfanin wannan auren? Tayi bakin ciki sosai, kan daga bisani ta baiwa kanta magana akan tahak'ura kurun. ************ Maheer bashi yazo gidan ba se bayan kwana biyu, gaba d'aya islam ta hanashi fita ko company bejeba so biyu yana cancelling meeting nashi, Allah ne shaidarsa Nancy tana cikin ransa, har kunyan ganinta yakeji, Da sallamar sa ya shiga gidan, suna zaune susu uku, ko wacce sanye da riga iya cinya suna shan fresh milk, dukkansu wasanninsu suke suna raha amma banda Hafsat tayi shiru tana dannan wayanta, da Ummul take chat, su sophie atare suka had'a baki wurin gayar da maheer amma sam Nancy ko d'ago kanta batayi ba bare ya saka ran zata gayar dashi, ganin haka ya sanya yace dasu "Ku barni da Nanuwa, zamuyi magana ne" Mik'ewa sukayi amma sophie sarakan gulma ajikin k'ofar d'akinsu ta mak'ale....ko kallon sa batayiba ya zauna kusa da ita ya rik'o hannunta tana zaune akan kujerar ko motsi batayi ba, gashin gemunsa ya sanya a bayan wuyanta yana gogawa a hankali, tsikan jikin ta ya miqe, lokaci d'aya taji saukar wata muguwar kasala lumshe idanta tayi ta bud'esu a hankali, d'ayan hannunshi ya sanya ya shafi k'irjinta zuwa wuyanta, sannan ya d'ago fuskarta suka fuskanci juna, Idanuwan su suka gauraya dana juna, idanta harya soma ja yana shirin kawo ruwa, mekenan batada zarafin ramawa ? Meke sanyata kasala? Mesa bata iya yi masa rashin m, mesa yazo mata ta wannan sigar dabazata iya hanawa ba, suna kallon juna kowa da abinda yake sak'awa a ranshi yace Nanuwa lagonki kenan, kina cika bakine kurun amma kinfi kowa bukatana......muryanshi kaman baya iya magana yace "Kiyi hakuri Nanuwa, zazzab'i nake tunda mukaje cen, ko nemana bakiyi ba, kema kinsan bayanda zanyi in kasa koda kiranki ina lapiya, kyau ace ai kinemeni da kanki" har yanzu cikin idanshi take kallo ta kasa gaskata zancen sa takuma kasa k'arya tashi, shikuwa bakinta ya d'auke masa hankali kasa hakuri yayi seda ya manna bakinsa da nata wuri d'aya, ta kasa katab'us batada k'arfin hanasa, bazatace tana manta wancen ranar ba, harshenta ya lalubo ya soma tsotsa a hankali, har yana mata wani numfarfashi wanda shine yake k'ara kashe mata jiki, yanayin qshin da numfashin ke fitarwa yana k'ara kasheta gaba d'aya batada yanda zatayi daya wuce ta rike masa waist d'inshi sabida tasoma kasa iya rik'e kanta, janye bakinta tasoma k'ok'arin yi amma ya hanata, sake harshen yayi ya sanya nashi harshen ya lashi lips nata, ya dawo ya sumbaci wuyanta, saketa yayi suka k'ara manna idanuwansu acikin na juna, sam bata iya d'auke idanta a nasa, k'wallan idanta ya sakko tace dashi da k'yar "Ka dena kallona dan Allah" murmushi yayi "Kema ki dena kallona" yau kawai ta d'auke idanta a nashi da k'yar, amma ta kasa nutsuwa ji take idan yana kallonta tamkar yana jona musu wani magnet ne da dole seta kalleshi, d'ago idanta ta k'arayi a hankali ta gauraya a nasa, har yanzu ita yake kallo, kanta ya janyo ya sanya harshe ya lashe mata wannan hawayen dake ambaliya a idanta,ya k'ara manna bakinsa a nata, kuka tasoma yi masa yanzu kam, abinda bata saniba wannan kukan ne yake jinshi wani irin daya sanya ya kasa d'auke bakinsa anata ya soma shafa cinyar ta, da k'yar ta kwace idan nan dukya sauya tace "Kayi hakuri karfa ka manta su safiyya suna nan fa" Dafe kanshi yayi ya saisaita nutsuwar sa, besan yanda za'ayi ya yadena kai hannunshi jikinta ba, bashi bane yake wannan shaukin akanta, gangar jikinsa ne ke masa izgilan cin nan, harga Allah yashiga tsoron yanayin zamansa da islam, kiss kurun dayawa Nancy ranar idan yana tarawa da islam seya sanyo tunaninta a zuci tukunna yake samun gamsuwa "Kiyi hakuri bankiraki ko a wayaba, bazan k'araba banji dad'i bane shisa kinji" lumshe idanta tae ta qara budesu akansa kasala ya dirar mata, batasan meye feelings ba Allah be d'oro mata se yanzu "Babu komai, Allah ya baka lapiya nizan shiga ciki bacci nakeji" D'an yatsanshi ya sanya yana mata yawo a cinya "Kiyi baccinki asaman jikina Nanuwa kinji" ta kasa koda qwaqwaran motsi se kallonshi kurun datake yanameci gaba da yi mata yawo a cinya!!!! Sophie mamaki ya kamata taje d'aki tanawa sha'awa gulma, aikuwa suka had'a rai sunsan brother su bashida neman mata, shine kenan ya sanya taketa bakin rai, ashe iskanci take koya masa?.... Ya dade tare da ita a parlor sedaga bayane ma yawuce, tana shiga dakin sha'awa tamata kwal, wai ita er iskace zata iskanta musu yayansu kowa yasan shi mutumin kirki ne waye waye...... Tayi kuka tamkar zata mutu amma ta rasa kalmar yi musu magana.......bayanin mema zata musu su fahimceta? Ai babushi wlhy, ga abinda yaja mata nan, wannan muqun muqun ya isheta, zuwa tayi ta kira anty Fareedah ta fayyace mata komai...

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 12"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...