WATA FUSKA CHAPTER 10 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA FUSKA CHAPTER 10

WATA FUSKA CHAPTER 10

- - Post a Comment
WATA FUSKA CHAPTER 10

  Washe gari tayi mamakin ganin an tasheta tun asuban fari kuma ance tayi wanka, 6:30am suka fita susu biyu, mamakinta yanda Maheer da kanshi ke tuk'i agarin kuma babu inda ya b'ata yasan kan garin kamar cikin gidansu.... Wata Makaranta taga sun shiga me d'an karen kyau da tsari, kai tsaye wurin shugaban makarantar sukaje yamai bayanin komai da harshen turanci inda yace sesun mata interview...Ba jinawa aka kammala komai kuma kai tsaye ta lula level 1 a b'angare low a makarantar me sunan Brilliant university makarantar su d'aya dasu Sophie kenan su suna level 3 inda sophie ke bibiyar medicine ita kuma sha'awa ke karantar b'angaren zane zane........1 *************** A waya yake sanarwa Abba k'udirinshi nason dawowa Uk din shima, seda yayi wani dogon nazari kanya amince masa da hakan, yana jiyewa yaron fadawa business irin nashi na rashin lokacin iyali kwata kwata amma yana masa fatan alkhairi. Kwance yake akan kujerar dake parlor d'in yana kallon tv duka tunanin shi da hankalinshi yana gun islam, d'azu dasukayi waya yaji muryan ta cen k'asa alamun tanajin jiki b'oye masa kurun takeyi, baya ga hakan ma yanaso ya kasance tare da matarsa sabida yana missing nata.....Lumshe idanshi yayi ya k'ara budesu a hankali acen k'asan zuciyarsa kuwa yana wani tunanin ne na daban sam ya gagara dena tunanin daya zamto masa tamkar numfashin sa, idan Abin da yakeji gameda islam so ne to lallai ko yana sonta so bana wasa, amma inhar ya kasance abinda yakeji gameda Hafsat shine So to kuwa da banbanci tsakanin so dakuma k'auna sabida ita har cikin jijiyoyin jikinsa yakejinta, tana masa zagaye acikin jini da b'argon sa, takasance itace numfashinaa dayake shaqa yana mata *Son so* wanda babu irin shi, yana mata k'auna wacce mizani yayi kad'an ya aunata sabida duk girmansa ta masa nauyi, yana jin dad'in sauti da amon muryarta tamkar itace ta farko ta kuma k'arshe acikin halittun a irin jinsinta a duniya, tafiyarta tana burgeshi takan d'auke hankalinsa xuwa wata duniyar daban yakanji tamkar bow legs d'inta sunfi na kowa masu irin nata kyau, seyaga kamar kyau ma suka k'arawa tafiyar ta, idan yana kallon d'an siririn hancin ta seyake ji tamkar ya dinga jansa a hankali yana wasa dashi, idanta masu ruwan zaiba aciki yake k'ara narkar masa da duk wani kuzari ya rasa katab'us idan beyi tunanin taba, k'wayar b'akin idanta ke d'auke hankalinsa yayinda ya kalleshi ya hango kanshi aciki, seyaji inama zata bashi aronsu su zame masa madubi dan harga Allah yafi ganin kyawun kanshi acikin d'igon bak'in idan nata, Duk sanda kumatunta ya lob'a kuwa idan tana cin abinci ko dariya kota yamutsa fuska, jiyake yi tamkar yaje ya sanya dan manuninsa acikin ramin yana mata wasa dashi, sumar kanta ke k'ara hura wutar abubuwan dake damunsa akanta, yakanji inama ace ze samu damar shinshinar sumar kan nata, ya shak'i k'amshin kan nata yanayin kwanciyar sumar nata yana nuni sosai da tsantsar tsafta kota yanda yake zuba sheqi......yarasa makama ya rasa madafa, ya ayyanewa ranshi komai nata burgeshi yakeyi daidai da yatsun hannayenta dake zara zara da nails masu kyau farare masu d'igon ruwan zuma a k'asan su, lumshe idanshi ya k'arayi a karo na barkatai, wannan yarinyar tana shirin wargaza masa lissafi,tanaso ta rikita tunaninsa ta tarwatsa masa kansa......da wannan ya miqe domin barin gidan kwata kwata, sabida harga Allah yana so ya yakice ta a ranshi, tasan sirrin islam!! Tasan wacece islam koda yayi nasarar auren ta baze tab'a nasarar zaman lapiyar su, ita islam bazata ji dad'in rayuwarta kishiyarta tasan seda ta gama yawon duniya aka aureta kuma sanin na sosai ba rumours ba, ita kuwa Hafsat zata dinga goranta mata hakan koda wane lokaci kuma yasani a wurin yara ma se ansamu haka ga Islam na shrin soma zazzaga masa yara agida......2 ****************** Matashiyar dake tare da ummul ce tace da ita cikin fusata "Baiwar Allah kinfa isheni da tambayoyi marasa kan gado!! Bake bace mace ta farko data fara zama anan gidan tare dani, kece ta biyar idan ma zaki kwantar da hankalinki ki kwantar dan bakida hanyar fita daga nan gidan, nida kaina na gudu yakai so bakwai amma da k'afana nake dawowa sabida wannan gidan dakika gani duk kyawun shi a jeji ne muke rayuwa, wanda bashida farko bashi k'arshe dubin duniya idan zakiyi bazaki gane komai ba ta inda ze sadaki da wani gari ko k'auye..... Idan kika kwantar da hankalinki kina haihuwa zasu maidaki inda kika fito, dama kwad'ayi ne ya kawoki kuma nasan kinci naki rabon da duk wacce bataci ba bata zuwa nan, sabida haka dan Allah da manzansa ki rufawa kanki asiri ki nutsu ki haife musu yaron cikinki ki huta da rigima" kallon rashin fahimta ta mata, ta rud'e sosai dajin wai yaron cikin ta zata haife musu!! Suwa?... Ta tambayi kanta, bak'in ciki tamkar ze kasheta da rud'u ta kuma durk'usa mata STORY CONTINUES BELOW "Ki taimakeni Naja'atu ki fayyacemun buri har wutsiya wlhy tallahi bansan komai ba game da zuwa nan gidan, hasalima wlhy tallahi ni matar Ameen ce, ba abinda naci nasa...... " Da haka yake yaudarar ku, nidai kuna bani mamaki wlhy, iyayen dayake kai muku kawai na bugi ne, dukkanin wani abu daze muku bana alkhairi bane ba, kukuma mata da iyayenku dazaran kunga me kud'i to ba wani dogon me bincike se aure, yanzu wa gari ya waya? Ki sabi tunda kikazo ta hanyar aure bakida odar barin nan gidan d'in sedai kiyita adu'a....yara kuma dazaran kin haife bakya ganin su kam ko labari sedai kamma kiyi arba'in suke k'ara danna miki wani cikin a huta gaba d'aya" ta karashe maganar tana d'age kafad'unta duka biyu....damuwa sosai ta nuna a fuskar ummul ta soma k'ok'arin kawo ruwan idanta k'asa...."Naja'atu mu kashe Ameen idan yazo semu gudu mana mu taimaki juna, na iya mota semubi duk sawun da tayoyin motar sa suka bi suka shigo" Dariya najan tayi "Bari kiji Ummul kowama kike da suna, wlhy keda ganin Ameen seyazo sake yi miki ciki, abuncin gidan nan ma bansan da yanda yake shigowa ba nida na shekara biyar acikin gidan, sedai nikanga me gadine yake kawo abincin shima da bundigarsa yake yawo sannan duk wata idan za'a kawo kayan abunci me gadin dake kawowa daban, shi kamma bansan wayake bashi abinci ba,kina dai gani daidai da sylinder wannan guda bakwai ne agidan cike da gas, idan na fitar da wanda ta kare bansan yaushe ake daukewa sedai naga an miyar,gulma har bacci nake hana idona ina zuwa leqe amma bani ganin komai, gen din da ake kunna mana da solar bansan yaushe ake saka masa mai ba, hasalima bana ganinsa banjin kukan sa, ba'a tab'a hanani yiwa wata mace bayanin kan gidan ba, nidai kurun abinda na sani zaman iyayena nake a gidan nan" Shiru Ummul ta kasa magana tabbas ta d'akko ruwan dafa kanta, ta kashe kanta da kanta, ta tsoma kanta a uku da kanta.... ************ Islam na kwance a d'akin Umma tun bayan da yayi tafiya agidan take kwana wurin Umma babu tsangwama ba kyara, sema wani tattali na musamman datake samu awurin ta koda wane lokaci.....yau Umma taje meeting bata gidan wannan ne ya baiwa Hajiya Nasara daman shigowa gidan tana wani yauk'i da uban k'aton kai da cikin dasuka mata yawa babu d'uwawu gatanan sekaje wani mayunwacin zaki......taunat cingam takeyi tana yatsina fuska sanda ta shigo d'akin...kallon wulak'anci da raini tawa Islam dake k'ok'arin gaisheta sannan tace "Ke ina Umma?" Sadda kanta tayi k'asa "Tajee meeting ne" ta bata amsa a tak'aice "Kwanciyar me kike mana akan gado magajiya?" Kalmar ta daki k'irjin ta ba kad'an ba wannan ya sanya ta d'ago jajayen idanta daya riked'e mata zuwa ja ta kalli Nasara ido cikin ido amma batace komai ba.... "Dena kallona karuwa!!!" Ta furta mata cikin d'aga murya wanda yayi daidai da shigowa umma d'akin bata san da zuwan umman ba taci gaba "Naji ance kinada ciki wato baki d'auki magana taba ko? Kina gani kamar wasane bazan iya kashe kiba akan wannan cikin? Kina tunanin bazan iya kassaraki ba bazan iya lahantaki ba kenan ko?" "Innalillahi wa inna ilahiraji'un" Itace kalmar da Umma ta furta a sarari "Nasara dama haka kika juya? Dama zaman cikin daula haka kika dawo Nasara? Ganin kinada dukiya kike ganin tamkar ki sab'awa mahaliccinki ba komai bane ba? Lallai kin shayar dani zumar mad'aci, kin kunyatar dani kin tarwatsa tarbiyar damuka baki, yaushe kika koma haka Nasara? Matar d'an uwan naki tome ta miki? Meta kashe miki a rayuwa? Kuma koba itaba wannan kalaman basuyi tsauri ba kuwa? Anya Nasara? Anya bakya gudun sauyin rayuwa?" Shiru batayi nagana ba uwar taci gaba "Fice mun agida, karki kuma dawowa sekinyi hankali, ko a waya karki k'ara kirana sekin yi hankali tukunna kinaji ba" Shiru tad'anyi nad'an k'ank'anin lokaci kanta ce ."ki Gafarceni Umma inshaa Allahu zan kiyaye" hararanta umman tayi "Ki ficemun agida nace ko kuwa?" Sumsum ta fita ta k'udurta aranta seta ciwa islam zarafi acikin ruwan sanyi ........ ***************** Yau dai gaba d'aya Nancy ta tashine cikeda kasala kasancewar tayi mugwayen mafarkai game da ummul, a daddafe tayi shirin school taje ta gayawa su sophie zata wuce abinta tana sauri, Batabi school Bus nasu ba Maheer ne yace ze direta, ya kula sosai da rashin kuzarinta da walwala....kallon ta yayi yana murmushi "Longon beb how far? Menene damuwarki kinyi wani shiru yau ko dimple din ma banga yana magana ba" tamkar yasani kuwa magana takeso tamasa amma ta rasa ina zata soma "Yaa Mahii dan Allah number ummul zaka nemomun awurin Baba iro inaso nayi magana da ita" kallonta yayi adaidai sanda yake lankwasa sitiyarin motarsa don shiga kwana yace "Kanki dawo skul inshaa Allah, zan masa waya sena bani in baki" "Ni A a yanzu nakeso" na furta maganat tamkar zatayi kuka cikin shagwab'a, harga Allah Nancy ko a Nik'afi duk tadowar ta cikin rashin gata tanada shagwab'a, abune dai kawai wanda bakasan kanayi ba, gata da saurin kuka abu kadan kuka abu kadan kuka.....har wani zubin takan bashi takaicin kukan nan shi bayason kuka ya tsaneshi sosai.....kallon ta yayi fuskar nan tamau "Bakida Number d'in Baba iro ke? Idan yanzu yanzu kikeso ki kirashi da kanki danni bazan nemo yanzu yanzu ba tunda ba fad'ar Allah bane ba" shiru tayi nad'an lokaci kan tacr "Kayi hakuri" bece komai ba har suka isa, babu me magana yana direta ta sauka batako kalleshi ba.. ************ Tunda taji bayanin haukan Baba iro taji hankalinta be kwanta da zancen ba, abinda ta tuna ta tab'a gani a motar sane ya fad'o mata aranta, cikin takaici tace da Baba iro "Baba yanzu kunada yak'inin ummul tana k'asar waje? Niba gani k'asar wajen ba amma ana samun nunber na, gaskia da sake wai an baiwa me kaza k'afa ku bincika gidansu yarin mana" k'irjin Baba ne ya doka se'a sannan ya tuna da betab'a tambayar Ameen gidan suba, amma yaga k'anin Baban sa sananne ne shisa be damuba, duk da ya shiga damuwa "To zan bincika gidan nasu Ameenu karki damu, yanda akayi na sanar miki" sallama sukayi ya dire kiran gwawar sa ba k'wari. *Bayan watanni Biyu* Tuni Maheer ya dawo Niger yayinda suke zaman ba laifi itada su fiyya, har mamakin yanayin kudad'en da ake basu takeyi, itama ta acc ake saka mata every month.....Basa shiri da shauty amma da sophie suke mugun shiri itane taketa wayar da ita amma shauty kulljm cikin zaginta wai kwadayine da ita. Yau cikin ummul watanshi Bakwai, amma segashi tana ciwon mara da baya mara misaltuwa, tun tana iya daurewa harta kasa...Naja ce taketa kulawa da ita ashe Nak'udacr haka ta haifi yarinya susu kad'ai ke dumui niyar su, babu sanin kowa tunda ba kowa agidan, haka yarinya tazo Bakwaini, me tsananin kamanni da mahaifinta tayi kyau seda gatanan er mitsila tamkar lomar kishiya, haka Naja tayita tattalinta dama ita ke karbar haihuwa idan aka haihu amma bata taba karbar Bakwaini ba!!! Ko yaya zata rayu? Ko yaya Ameen zeji idan yaji tasha nono, a ka'idar yaran dasuke d'auka sam ba'a bari susha nonon uwarsu tasan kuma shida gidan se nan da watanni biyu idan yasan EDD na Islam ya cika!! Akwai matsala kenan!!! Islam ta k'urawa babynta ido cikeda so da k'auna da kuma tausayi me tsanani!! Bata tab'a kawowa aranta duniya zata mata atishawar tsaki haka ba, bata tab'a kawowa ranta akwai ranar dazata haihu babu dangi a tare da ita, bata tab'a kawowa ranta zata haifi 'ya ba uba ba, ko a mafarki bata zata zata haihu ba asibiti ba, ta samu rauni amma bame kulawa da ita, Bata tab'a zata zata haihu ta rasa romon dataga ana yiwa masu jego ba, tasha ji Baba Azumi na fad'en idan ta haihu kunu zata dinga mata me kyau jikinta yayi k'wari da wuri, tasha ji Baba Azumi na fad'ar zata mata wankan iccen Dogon yaro na ruwa me shegen zafi, Baba Azumi taci burin sanyata a kujerar mata ta dinga turara mata kasanta ance yana maganin tusar gaban da mata keyi bayan sun haihu.....Bata tab'a zata, zata a haihu. Babu uba ko wani jigon dazewa abinda ta haifa Hud'uba da kiran salla ba, Bata tab'a koda a mafarki tunanin cewar zatafi haifi abinda ze rasa sunan da za'a kirasa dashi Ashe Ameenu ninketa yayi baibai ta hanyar sanyawa ainahin fuskar sa *WATA FUSKAR!!* ya danne wata salahar Fuskar da Mummunan *WATA FUSKAR!!* sa lallai tana cikin B'akin ciki, tasha ji yana fad'a cewan Duk sanda ya haifi Namiji ze bashi sunan mahaifinsa na ainahi wato Musa idan kuma Macece ze sanya mata sunan mahaifiyarsa wato *NANA KHADEEJAH* da wannan ta dauki jinjirar ta mata huduba da kanta tana sharar k'wallah lokaci d'aya kuma tana mata kiran sallah ta mata hudu ba da sunan Nana khadeeja....tausayi sosai ta baiwa Naja daya sanya ta kasa daurewa ta sanya kuka.+ ******************** Abubuwa sun soma yiwa Baba Azumi yawa sosai, ta soma neman sukunin ta ta rasa, bashi ya mata dabaibayi wanda taketa ci da sunan ummul zatazo amma shiru kakeji tamkar an shuka dusa kwanakin cen gwal d'inta ta eba ta siyar babu yanda ta iya akan zata rage bashi yanzu gashi marasa mutuncin mutane sun taso ta agaba, har yanzu a k'asan ranta ummul take jira ta tabbatar ummul tanacen abunta k'asar waje tana hutawa, bata raba d'aya biyu cikin ummul ya kusa zuwa duniya da wannan take ganin dole su dawo gida.....yau dai kam rana ta b'acewa Baba Azumi sabida tanaji tana kuma gani aka zo aka wuce da ita station akan bashi belinta an gagara karbowa sabida yayan ummul yace shiba ruwanshi yayita gargadin su akan hakan wata er sandar mace har duka ta tik'a mata tsabat haushin datake bata sabida had'e kai masu binta bashin sukayi suka kai k'ararta, taci azaba kan abada belinta, se fad'i takeyi suyi hakuri 'yarta ummjl tazo wai me kudi take aure dansunje yawon shan iskane turai amma dasunzo zata bada, wasu kam kallon mahaukaciya tuquru suke mata. ***** Maheer ya dawo Niger ansha love shida islam se narkewa take wai ita adole me ciki, shi kuwa ko motsin kirki tayi seyaji a ranshi bayan zuwansa da one month suka juya zuwa London inda itama tunda jikinta yae kwari aka soma nemar mata gurbin karatu a turai din inda ta samu nasarar shiga level one a bangaren turancin data faro....dayake su cen abinsu akwai tsari sanda kayi joining college sannan semester ka ze fara.... Tir k'ashi!!! Yau a parlor islam ce kwance tana narka shagwab'a tayi matashin kai da cinyar Maheer dayake biye mata ya sanya hannunsa yana wasa da sumar kanta dake a kwance, ita lallai yau chicken byte takeso, kuma anje siya sunce seda safe gashi 8 yayi, kiran Sophie yayi tazo tace gata "Kin iya chicken byte ne?" Ya tambayeta kanshi tsaye kallon shi tayi ta dan saci kallon islam, a ranta tace wato matarnan tunda tazo muke cikin takura indai tana ganin yaa mahee durun uwa iri iri ko, "Ea bazance ban iyaba amma muma Nancy ke mana, tafi kowa iyawa" jinjina kansa yae "Jeki ki kiramun Hafsatun" juyawa tayi aranta tace so daya mukayi a gaban Nancyn Allah yasa ya kwab'e" tana zuwa ta turo ta, k'irjinta na dokawa ta iso parlor d'in tunda sukazo da islam batada sukuni, tarasa mesa takejinta a takure sannan kuma batason ganinsu kullum.manne da juna tarasa dalilin jin hakan, ada tasan taso maheer amma yanzu ta sani koda a k'afa zasu d'aura mata shi bazata jasa ba sabida sam ita bazata iyaba, tanada wasu dalilai data barwa kanta sani.. "Yaa Maheer sannu da gida" "Yauwa sannu Hafsat, am chicken bytes zakiwa baby, shi takejin ci kuma near by shops dinnan babu wai seda safe suke ta cewa" wani k'ututun bak'in ciki ne ya tasowa Hafsat amma seta kanne tace "E babu damuwa, munada kayan hadin barinje na hada mata" Bece komai ba ta juya tana had'awa tana mita harta kammala ta kawo, agabansu ta ajiye tana kallon islam da wasa irin na ftnds dinnan tace "Maman biyu ga wannan karki cinyemu" murmushi islam tayi sannan cikin isa tace da ita "Kekuwa ina d'an drink dazan had'a da? " miyarda dubanta tayi zuwaga maheer ta shagwab'e fuska "Ni honey kace da ita ta had'amun ko smoothie ne dabashi da wuya nafison Banana smoothie yafi rik'e ciki" kallon mamaki hafsat ta mata shi kuwa Maheer yace "Kinji me tace kije ki had'o kin wani tsayawa mutane akai" zuwa wannan lokacin seda tayi kuka a kitchen tana mamakin sauyawa halin qawarta..... ********** A wannan daren Nancy ta kwana tana bak'in cikin faruwar wannan abin,tasani Maheer baya mata wulakanci shida sophie amma shauty da islam suna yawan kaita mak'ura aciki islam tafi bata mamaki, ita bazata fito ta mata wulakanci ba amma sedai tana mata abubuwan datake so taga sun k'ureta tayi wani abin daze ja mata raini!!! Mamakin wannan halin na islam na cikin damuwar ta......Bazatace Komai ba akan wannan abin tayi alkawari zata jure amma tasan wuyace zata shata ta hango wulakanci tsantsa acikin take taken da islam keyi tun zuwanta, ta dinga mata abubuwa tamkar wata 'yar aiki tana tunzurata zuwa bango, amma ba komai zata jure!!! ********** Duk wani juyin da maheer zeyi tunanin Nancy ne danqal acikin kansa, yana cikin tsantsar damuwa mara adadi, yana kula sosai da yanayin islam da yanayin d'abi'un datake nunawa agaban na Nancy, bayaso ya mata magana ne tazo tana mar wani kallo na daban,yasan mata seya sanya wani abu aranta daze k'ara dagula zaman, yana hango yanayin Nancy da kuma b'acin ran datake shiga duk sanda ta mata irin wannan abun, ya kula ma tun dawowar da yae da islam Nancy walwalarta ta ragu sosai, ya kula kuma takan zauna skul ko bata komai har yamma sabida batason ganin abubuwan da islam keyi sam ya kula tana cikkn damuwa abun yana damunsa!!! Yau kusan wata d'aya da sati biyu kenan da haihuwar Ummul yarinyarta tayi girma sosai bazakace bakwaini bace, tayi kamar mahaifinta yamkar an tsaga kara, ita kuwa uwar se rama takeyi tamkar kud'in guzuri a tsorace take kwana sabida labarin dataji a bakin Naja akan kwace jarirai da ake a wurin iyayensu bata kuma san ina kaisu ba, shak'uwa me tsananin yawa ta shiga tsakaninta da Naja, taji labarin iyayenta aka dauka akan zaman dole takeyi anan kusan shrkaru biyar rabonta da gidansu, da iyayenta da dangi, tayita kokarin gusuwa amma ba hanya......+ Hankalin Ummul baya jikinta EDD da aka bata kan azo da ita nan sauran shi sati biyu kacal, hakan yana nufin kenan zasu rabata Da NaNan ta zasu k'wace ta daga hannunta tosu kaita ina? In hakane tun yanzu ya dace ta keci jejin kota nemi dabarar yi sabida akwai matsala, ga mikin ta na haihuwa har yanzu da saura sabida rashin magani koda na hausa ne tana cikin tsananin damuwa me yawa ba er kad'an ba. *************** A parlor su sophie ne ke zaune suna hirarsu har Nancy wani zubin zakaga suna raha gaba d'ayansu tamkar basa gallaza mata, yauma hakan ce en matan uku se hira suke suna shewa dukkansu acikin kayan bacci masu wando iya gwiwa da riga me gajeran hannu amma tanada tsayi har socks suka sanya sabida ana tab'a sanyi a garin babu me d'ankwali acikin su, ita nancy ma tsawon sumar kanta daya sauka har cen bayanta ta tattaro zuwa gefen kafad'arta ya sauka ta gaban qirjinta, tana sanye da madubi sabida matsala da idanta ke bata akan yawan duba takarda suna hiran tana dannan wayanta.....zuwa wannan lakacin ta zama 'yar gida sun gama sakin jiki da Maheer ta cire shi aranta babu abinda take mai kallo se yayanta uwa d'aya uba d'aya, gidansu ne anan suke zaman hira musamman idan yaa Maheer baya nan.....islam ce ta shigo tana yamutsa fuska su sophie suka kalleta atare suka hada banda Nancy "Sannu anty kin fito" murmushi ta musu "Nafito en uwa ya kuke?" Murmushi sukayi shauty tace "Qalau muke anty" kallonta Nancy tayi da murmushi a fuskarta "Isy baby how body" ta furta tana gyaran zaman madubin idanta, yamutsa fuska islam tayi "Yadai kamata kisan banbancin da dakuma yanzu, matsayin yayarki nake inda kikazo agolanci fa yayan su nake aure, ai ya dace ki ajiye qawancen mu nada ki gayar dani yanda kikaji kowa yayi bawai ki kirani da sunan raini ba tsabar izgili, amma bari yayan yazo zance ya miki magana ki san yanda zakimun magana, kina b'atamun rai gako Dr. Yace adena b'ata raina" sophie ma yau taji haushin wannan wulaqancin da islam kewa Nancy ita kuwa Nancy batace komai ba ta tattare yanata yanata tayi hanyar d'aki,tsaki ta bita dashi ta zauna wurin data tashi, ta tabbatar maganar da Anty Nasara ta fad'a Gaskia ne, wato dai Nancy ta manta halacci auren mijinta takeso tayi ko, itako kozatayi yawo tsirara bazata tab'a bari mijinta ya auti vergine ba gwara ya auro magajiyar karuwai, ko Umma ta gano bata santa arayuwa duk sunfison Nancy da ita tunda suke shirin auramai ita dabadan anty Nasara ba dabazama tasan miyan da ake yiba, amma ba komai wuya zata sanya ta gudu da k'afanta tabar gidan!!! Suma duksu sophie se suka bi bayan Nancy, a d'akinta suka sameta sophie tace "Mesa wai ke adinga miki abu bazaki yi magana ba, me anty islam ke nufi dake zata rik'a kiranki agolar, ko agolancin kike aiba gidan ubanta bane itama" Murmushi tayi tace tana kallon sophir "Ku manta da ita sophir duniya taga ta samu shiyasa, a turan nan Allah sa yaa Mahii ya samu wata matar ya aura" ta qarashe maganar tana dariyar mugunta , sha'awa d'aka mata duka tayi a cinya STORY CONTINUES BELOW "Ke Banza ce wlhy, duk abinda ta miki ke dariya ma kike, ni wlhy duk abinda na miki ada sharrin shedan ne dakuma zuga kiyi hak'uri na fahimci kinada hak'uri da girmama mutane, uwa uba gashi kina koya mana karatun Allah harma mun gayawa Umma wlhy kuma tana jin dadi, mukace dama kece matar wancen se ikon tsiya" Tana murmushin ta tace.. "To meye duniyar shauty? Duk idan ka kwantar da hankalinka dudu kwana nawa ya rage maka a duniyar? Ko yanzu seka iya mutuwa wlhy ku barta duniyar ce akanta ita har yanzu ni bazan tab'a kulata ba wlhy" haka duka zauna sunata mita haushin Islam fal aransu basuda labarin Anty Nasara ce ta ingizota take wannan izgilancin takuma tabbatar mata su Abba sunce ita zasu aurawa Maheer....... **************** Mahal se yanzu ya gano yanason Nancy da kanshi yaje gun Baba iro ya karb'o lambar wayarta, Yau ma kamar kullum aikin ne da aka saba sakata na wahala takewa islam wai kunu zatasha dama an aiko garin kunu daga gida sabida tanaso, tana kawowa ta ajiye akan centre table islam ta soma rigima "Ni Honey nace kadena sanya Hafsat tanamun abu,bansan meya shiga tsakaninmu ba ta tsaneni yanzu sabida Allah kunu haka da ruwa yaushe ze riqen ciki gashi taga bana iya cin komai" kallonta Maheer yayi ya sani neman fitinane kurin "Adama me kaurin ne?" D'auke kanta tayi "Nafasa shan kunun abari kawai na kwana da yunwar" tasani baze lamunci barin ta da yunwa ba yanda yake tattalin cikin nan tamkar ranshi,tallafota yayi "Noo Baby karmuyi haka dake plss, ki bari yanzu taje ta dama me kaurin sekisha kinji" yamutsa fuska tayi "Nise naji dama ace peppersoup ne na kaza danasha romon inci naman" "To yanzu ayi peppersoup d'in?" Gyad'a masa kanta tayi, akwai house girl agidan har biyu ita ya kwallawa kira har yanzu nancy tana a tsaye , wayanta ne ya soma ringing bata san Number ba, juyawa tayi tana daukar kiran "Yaa Mahal dama kana nan? Lallai ma ai nayi maka fushi wlhy" shine kalmomin daya miyar da duban Maheer zuwaga Nancy k'irjinsa yana dokawa "Ba waninan yaa Mahal wlhy Allah nayi fushi, amma ina abu yanzu barin gama zan kiraka" Bata k'ara kallon subama tawuce d'akin su sophie yanzu kamma har zama d'akinta ta dena yi sesu kwana a tare suna zuba shagalin su tama rage damuwarta akan Islam takula batada hankali. *************** Bayan sati biyu Yauce ranar cikan EDD na Ummul kuma yarinyarta ta cika watanninta biyu a duniya tayi kyau abinta tayi qiba ta murje sedai abin tausayi bata da ko rigar sakawa a duniya ko pant batada sabida ba'a tanada ba, kullum acini. D'ankwalin ummul take har ciwon mura tayi sosai amma babu maganin bata da taimkon Allab taji sauk'i tunda aka soma tab'a k'ofar shigowa gida suke a rud'e da kanta taje ta neki kwali ta shinfid'a d'an kwalaye aciki takuma saka Nana ta sanya wani kyalle tanaji dana gani ta d'aure bakin 'yarta ta d'auki kwalin ta sanyashi ackkin store dake gidan na kayana abinci cen bayan buhun hunan shin kafa, kullum haka sukewa jinjirar har yau Allah yasa yazo ita ta bud'e masa k'ofar gidan tana ganin shine ta fad'a jikinsa tana ta kuka,dama haka suka shirya. "Yaa Ameen wani laifin namaka ne? Menamaka a rayuwa? Ka gudu kabarni anan dabansan ko ina bane, na rasa inda zan dosa arayuwa, har k'addara ta sameni bakazoba yaa Ameen" d'agota yayi ya kalleta daga samanta har k'asan ya yamutsa fuska "me kike nufi? Ina kika kaimun yaron cikinki...kuka ta k'ara fashewa dashi " ka zauna zan maka bayanin komai, mana da waccen muguwar abinda tamun datana kulani daban shiga tashin hankali irin wannan ba yaa Ameen" Lokaci guda ya shiga rud'u da tashin hankali me yawan gaske, ya zauna yana kallon ta tace "Bayan daka tafi ka barni anan bako sallama ya Ameen, ranar da dare kasan ciki da kwadayi na tashi ina neman yoghurt babu agidan nan ga wannan Najar batako kulawa dani yanda kace.....shine fa na fad'i a kitchen lokacin cikina watanninsa bakwai kacal*Haske writer's Asso Yau kusan wata d'aya da sati biyu kenan da haihuwar Ummul yarinyarta tayi girma sosai bazakace bakwaini bace, tayi kamar mahaifinta yamkar an tsaga kara, ita kuwa uwar se rama takeyi tamkar kud'in guzuri a tsorace take kwana sabida labarin dataji a bakin Naja akan kwace jarirai da ake a wurin iyayensu bata kuma san ina kaisu ba, shak'uwa me tsananin yawa ta shiga tsakaninta da Naja, taji labarin iyayenta aka dauka akan zaman dole takeyi anan kusan shrkaru biyar rabonta da gidansu, da iyayenta da dangi, tayita kokarin gusuwa amma ba hanya...... Hankalin Ummul baya jikinta EDD da aka bata kan azo da ita nan sauran shi sati biyu kacal, hakan yana nufin kenan zasu rabata Da NaNan ta zasu k'wace ta daga hannunta tosu kaita ina? In hakane tun yanzu ya dace ta keci jejin kota nemi dabarar yi sabida akwai matsala, ga mikin ta na haihuwa har yanzu da saura sabida rashin magani koda na hausa ne tana cikin tsananin damuwa me yawa ba er kad'an ba. *************** A parlor su sophie ne ke zaune suna hirarsu har Nancy wani zubin zakaga suna raha gaba d'ayansu tamkar basa gallaza mata, yauma hakan ce en matan uku se hira suke suna shewa dukkansu acikin kayan bacci masu wando iya gwiwa da riga me gajeran hannu amma tanada tsayi har socks suka sanya sabida ana tab'a sanyi a garin babu me d'ankwali acikin su, ita nancy ma tsawon sumar kanta daya sauka har cen bayanta ta tattaro zuwa gefen kafad'arta ya sauka ta gaban qirjinta, tana sanye da madubi sabida matsala da idanta ke bata akan yawan duba takarda suna hiran tana dannan wayanta.....zuwa wannan lakacin ta zama 'yar gida sun gama sakin jiki da Maheer ta cire shi aranta babu abinda take mai kallo se yayanta uwa d'aya uba d'aya, gidansu ne anan suke zaman hira musamman idan yaa Maheer baya nan.....islam ce ta shigo tana yamutsa fuska su sophie suka kalleta atare suka hada banda Nancy "Sannu anty kin fito" murmushi ta musu "Nafito en uwa ya kuke?" Murmushi sukayi shauty tace "Qalau muke anty" kallonta Nancy tayi da murmushi a fuskarta "Isy baby how body" ta furta tana gyaran zaman madubin idanta, yamutsa fuska islam tayi "Yadai kamata kisan banbancin da dakuma yanzu, matsayin yayarki nake inda kikazo agolanci fa yayan su nake aure, ai ya dace ki ajiye qawancen mu nada ki gayar dani yanda kikaji kowa yayi bawai ki kirani da sunan raini ba tsabar izgili, amma bari yayan yazo zance ya miki magana ki san yanda zakimun magana, kina b'atamun rai gako Dr. Yace adena b'ata raina" sophie ma yau taji haushin wannan wulaqancin da islam kewa Nancy ita kuwa Nancy batace komai ba ta tattare yanata yanata tayi hanyar d'aki,tsaki ta bita dashi ta zauna wurin data tashi, ta tabbatar maganar da Anty Nasara ta fad'a Gaskia ne, wato dai Nancy ta manta halacci auren mijinta takeso tayi ko, itako kozatayi yawo tsirara bazata tab'a bari mijinta ya auti vergine ba gwara ya auro magajiyar karuwai, ko Umma ta gano bata santa arayuwa duk sunfison Nancy da ita tunda suke shirin auramai ita dabadan anty Nasara ba dabazama tasan miyan da ake yiba, amma ba komai wuya zata sanya ta gudu da k'afanta tabar gidan!!! Suma duksu sophie se suka bi bayan Nancy, a d'akinta suka sameta sophie tace "Mesa wai ke adinga miki abu bazaki yi magana ba, me anty islam ke nufi dake zata rik'a kiranki agolar, ko agolancin kike aiba gidan ubanta bane itama" Murmushi tayi tace tana kallon sophir "Ku manta da ita sophir duniya taga ta samu shiyasa, a turan nan Allah sa yaa Mahii ya samu wata matar ya aura" ta qarashe maganar tana dariyar mugunta , sha'awa d'aka mata duka tayi a cinya STORY CONTINUES BELOW "Ke Banza ce wlhy, duk abinda ta miki ke dariya ma kike, ni wlhy duk abinda na miki ada sharrin shedan ne dakuma zuga kiyi hak'uri na fahimci kinada hak'uri da girmama mutane, uwa uba gashi kina koya mana karatun Allah harma mun gayawa Umma wlhy kuma tana jin dadi, mukace dama kece matar wancen se ikon tsiya" Tana murmushin ta tace.. "To meye duniyar shauty? Duk idan ka kwantar da hankalinka dudu kwana nawa ya rage maka a duniyar? Ko yanzu seka iya mutuwa wlhy ku barta duniyar ce akanta ita har yanzu ni bazan tab'a kulata ba wlhy" haka duka zauna sunata mita haushin Islam fal aransu basuda labarin Anty Nasara ce ta ingizota take wannan izgilancin takuma tabbatar mata su Abba sunce ita zasu aurawa Maheer....... **************** Mahal se yanzu ya gano yanason Nancy da kanshi yaje gun Baba iro ya karb'o lambar wayarta, Yau ma kamar kullum aikin ne da aka saba sakata na wahala takewa islam wai kunu zatasha dama an aiko garin kunu daga gida sabida tanaso, tana kawowa ta ajiye akan centre table islam ta soma rigima "Ni Honey nace kadena sanya Hafsat tanamun abu,bansan meya shiga tsakaninmu ba ta tsaneni yanzu sabida Allah kunu haka da ruwa yaushe ze riqen ciki gashi taga bana iya cin komai" kallonta Maheer yayi ya sani neman fitinane kurin "Adama me kaurin ne?" D'auke kanta tayi "Nafasa shan kunun abari kawai na kwana da yunwar" tasani baze lamunci barin ta da yunwa ba yanda yake tattalin cikin nan tamkar ranshi,tallafota yayi "Noo Baby karmuyi haka dake plss, ki bari yanzu taje ta dama me kaurin sekisha kinji" yamutsa fuska tayi "Nise naji dama ace peppersoup ne na kaza danasha romon inci naman" "To yanzu ayi peppersoup d'in?" Gyad'a masa kanta tayi, akwai house girl agidan har biyu ita ya kwallawa kira har yanzu nancy tana a tsaye , wayanta ne ya soma ringing bata san Number ba, juyawa tayi tana daukar kiran "Yaa Mahal dama kana nan? Lallai ma ai nayi maka fushi wlhy" shine kalmomin daya miyar da duban Maheer zuwaga Nancy k'irjinsa yana dokawa "Ba waninan yaa Mahal wlhy Allah nayi fushi, amma ina abu yanzu barin gama zan kiraka" Bata k'ara kallon subama tawuce d'akin su sophie yanzu kamma har zama d'akinta ta dena yi sesu kwana a tare suna zuba shagalin su tama rage damuwarta akan Islam takula batada hankali. *************** Bayan sati biyu Yauce ranar cikan EDD na Ummul kuma yarinyarta ta cika watanninta biyu a duniya tayi kyau abinta tayi qiba ta murje sedai abin tausayi bata da ko rigar sakawa a duniya ko pant batada sabida ba'a tanada ba, kullum acini. D'ankwalin ummul take har ciwon mura tayi sosai amma babu maganin bata da taimkon Allab taji sauk'i tunda aka soma tab'a k'ofar shigowa gida suke a rud'e da kanta taje ta neki kwali ta shinfid'a d'an kwalaye aciki takuma saka Nana ta sanya wani kyalle tanaji dana gani ta d'aure bakin 'yarta ta d'auki kwalin ta sanyashi ackkin store dake gidan na kayana abinci cen bayan buhun hunan shin kafa, kullum haka sukewa jinjirar har yau Allah yasa yazo ita ta bud'e masa k'ofar gidan tana ganin shine ta fad'a jikinsa tana ta kuka,dama haka suka shirya. "Yaa Ameen wani laifin namaka ne? Menamaka a rayuwa? Ka gudu kabarni anan dabansan ko ina bane, na rasa inda zan dosa arayuwa, har k'addara ta sameni bakazoba yaa Ameen" d'agota yayi ya kalleta daga samanta har k'asan ya yamutsa fuska "me kike nufi? Ina kika kaimun yaron cikinki...kuka ta k'ara fashewa dashi " ka zauna zan maka bayanin komai, mana da waccen muguwar abinda tamun datana kulani daban shiga tashin hankali irin wannan ba yaa Ameen" Lokaci guda ya shiga rud'u da tashin hankali me yawan gaske, ya zauna yana kallon ta tace "Bayan daka tafi ka barni anan bako sallama ya Ameen, ranar da dare kasan ciki da kwadayi na tashi ina neman yoghurt babu agidan nan ga wannan Najar batako kulawa dani yanda kace.....shine fa na fad'i a kitchen lokacin cikina watanninsa bakwai kacal, shiru tayi yana kuka yace cikin tsawa " ina jinki mana kinyi wani shiru seme dan cikinki wata bakwai" tana sharar k'wallah tace "To shine sena soma nakuda me tsanani nikadai a d'akin sedaga baya tazo koda tazo yaro ya gama wahala, ana haifarshi ya mutu, neman duniya na maka har gidan naso in bari amma banga hanyaba, haka muka hak'a rami muka binne gawar yaron yanzu kusan watanni biyu kenan" wata iriyar shak'a ya kai mata ya cafko wuyan rigarta seda ta yage ma, idanshi duk yayi waje yace "K'arya kikeyi wlhy sekin fitomun da cikin jikinki, watak'ila ma yanzu kika haihi muje in gani" yajata giri riri zuwa d'aki se rantse rantse take akan wlhy bakwainin ta haifa!!! *********** Mahal da Nancy kam kullum suna maqale a waya kowama ya fahimci hakan har su sophie ke tsokanar ta akan NaHal 2k19, bata kulasu dai ita kurin yana d'ebe mata kewar er uwarta ne yasa take kulashi ma, kuma dai ina laifin me sanka... Yauma kamar kullum zaune take a saman matattalar benen dake cikin sabon gidan dasuka koma a london din, tana wayarta da Mahal se raha suke abinsu, Maherr dake bayanta yana sauraren wayar dasuke lokaci daya ta bashi takaici me tsanani, ya kalleta tana zaune tana wasa da sumar kanta tamkar ya rufeta da duka yakeji, yayi tsammanin daya sakko ta ganshi ta dena wayan amma ko gezau batayi ba, ta kurin ce "Sannu da fitowa yaa mahii" ko kallonta beyi ba, dama ace tasan yanda yakejin sonta a ranshi data masa adalci, da ace tasan yanda take da matsayi a zuciyarsa data rufawa kanta asiri ta dena sauraran kowa, dama ace tasan bashida niyyan yafewa waninsa ita data dena baiwa kanta wahalar sauraran wasun shi..... Harya wuce ya dawo yace "Ke ajiye wayar ki sameni garden yanzu" Mik'ewa kurin tayi taje ta sanya hijab har lokacin tanakan wayar seda ta kusa isa garden d'in sannan ta ajiye wayan...sosai ya kalleta kallo me tattare da tarin ma'anoni yace cikeda kasala "Menene tsakaninki da Mahal ne, kullum kuna maqale a waya" murmushi tayi "Bafa komai yaa mahee wlhy, kurin dai muna gaisawane he's just a friend nothing more nothing less" Shiru yayi kafin yace "Hafsat inason ki, so nakeyi in aureki kuma ba wasa nake ba da gaske nake, har raina ina k'aunar ki sosai, ina miki son so daban tab'a yiwa wata 'ya mace a duniya ba, dan Allah ki amince dani ki aureni" wani kallon tuhuma ta bishi dashi bata tab'a kawowa zezo da wannan haukan ba, kowace k'addarar zata had'ata kishi da Islam oho? Har abada bazata tab'a aurar Maheer ba har duniya ta ninke kuwa, ko da ta kula ba wani so aranta se zallan burgeta da yanayinshi keyi yanzu kuwa kallon yaya kurun take masa,sewani haushi dayake bata yanda islam ta mayar dashi wani soko agabnshi take cin zarafinta, batace dashi komai ba ta wuce ciki da gudu batada amsar bashi ita kam.... ************* Har sunkai ciki ya dawo yana k'wallawa naja kira anan yajiyo kamar kukan jarirai kallonshi ya miyar daidai kofar kitchen din inda yakeda yaqinin nan ne yaji kukan juya akalar tafiyarshi yayi zuwa cikin kitchen d'in.....

Post a Comment for "WATA FUSKA CHAPTER 10"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...