WATA BAKWAI CHAPTER18 KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA BAKWAI CHAPTER18 KARSHE

WATA BAKWAI CHAPTER18 KARSHE

- - Post a Comment
WATA BAKWAI CHAPTER18 KARSHE


  A hargitse suka shiga asibitin. Tana ganin umman prince ishaq ta ruga wajenta tana kuka.+ Sunfi awa biyu zaune likitoci babu wanda ya fito yace musu wani abu. Hankalin kowa a tashe yake. Ko da likita ya fito kusan su duka suka isa wajenshi kaman zasu cinye shi da tambaya. Dakyar ya samu suka nutsu yace musu. "Yana hutawa ne. Ciwukan nashi anyi sa.a ba wani zurfi sukai ba. Ya zubda jini ne shi ya galabaitar dashi" Sai lokacin hankalin kowa ya kwanta. Umma tace azo a tattara kowa ya koma gida dare yayi. Su tafi da husna ma. Abar Nas kawai. Kuka husna ta saka ga shi ta kasa cewa komai. Ganin hakan yasa umma tace abar husna hankalinta zaifi kwanciya. Su duka suka zauna dakin da prince ishaq din yake. Dinkine a hannunshi da wuyanshi. Banda nan babu wani ciwo a jikinshi. Husna taja kujera ta zauna kanta ta dora gefen dagon tana riko hannun shi. Tayi kuka har fuskarta ta kumbura. Bacci kam barawo ne ya saceta. **** Hannun prince ishaq taji saman kanta. Da sauri ta dago ta sauke jajayen idanunta da suka sha kuka cikin nashi. Murmushin shi yai mata kawai. Dan bazai iya magana ba. Makoshin shi ciwo yake masa sosai. Hawaye zatai da idanuwa ya nuna mata alamar baya so. Tako tarbe su. Nas dake kwance gefe ta taso. Yaje ya kira likita. Akazo aka duba shi. Sai bayan ta idar da sallah sannan ta kira gidansu ta fada musu da asibitin da Nas din take. Sukace da gari ya kara wayewa zasu zo. *** Tun da sassafen suke shan baki. Husna kam ba yanda ba ai da itaba ta koma gida ta yo wanka ta sake kaya taqi. Saida umman prince Ishaq tazo sannan tasa Nas ya mayar da ita gida. *** Duk saurin da take yi sanda suka koma mamanta har sunzo sun duba shi sun tafi. Taji kaman zata saka kuka. Waya ta dauka ta kira "Mama ko ki jira in dawo mu gaisa" "Husna zamu dawo gobe in Allah ya kaimu. Kuma su yayanki ma zasu zo da yamma" Ba yanda ta iya. Dole ta hakura. Addu.a tai ma prince ishaq din sosai tukunna sukai sallama. *** Yau kwanan su uku a asibiti. Prince ishaq tunda ya fara samun sauki yake mita shi fa sai a tafi gida. Dole ranar da yamma aka sallame su da warning cewan kar yai stressing kanshi. Ya zauna ya huta sosai. Saima juya idanuwan shi wa doc din dayai hadi da fadin "Zan iya kula da kaina. I know the rules" * Tunda suka dawo gida falonshi ya zauna yanata waya. Husna tana kitchen ta hada masa ginger drink din da yake bala.in so. Farfe sun kifi tai mishi ta zubo ta dawo falo. A plate ta zuba mishi ta zauna ta gyara ta cire kayoyin sannan ta tashi taje ta wanko hannunta ta dawo. Kallonta yai yace STORY CONTINUES BELOW "Sannu da aiki hussy" "Kaine da sannu. Ya jikin?" Ya langabar dakai gefe kawai maimakon ya amsata sai yace "Nas ne ya kirani wai an fara zaman court ne kan shari.armu. Gobe sai naje" Plate din ta dauka takai kusa dashi tana fadin "Allah ya kaimu. Allah ne ya kawo karshen mugayen mutanen nan." Ya amsa da amin. Saida ma taita matsa mishi ya dan kara ci. Tun a asibiti yake cewa kifi yake son ci. Amman kaga yanzun an dafa ya kasa ci. "Menene mama ta kawomun dazun da safe?" Kallon shi tai sosai "Dambun nama ne. An kuma hanaka tauna abu for long" Ya tabare fuska "Ni kam zanci fa" Ta sauke numfashi tace "Gentle ka hakura yana nan na ajiye maka. Idan ka kara samun sauki sai kaci" Ya girgiza kai shi bai yarda ba. "Ki tauna saiki dinga bani" Zaro idanuwa tai. Dakyar ta lallabashi. Shifa a dole sai ta tauna ta bashi. Da dare tare suka shiga toilet. Ita ta kama mishi ya cire riga saboda hannun shi. Ya cire har single. Dagashi sai boxers. Wata kunyarshi ta saukar mata. Ta kasa hada idanuwanta da nashi. A hankali tasa towel da ruwan dumi ta goge mishi jikin shi tas. Yai brush sannan ya fito. Wani boxers din ta dauko mishi da singlet ya shiga dakin sake kaya ya canza. Ya fito yasa singlet din zuwa wuyansh kawai. Ta taimaka masa ya karasa sakawa. Magunguna ta ballo da cup din ruwa. Ta mika mishi ya wani girgiza kai yana yamutsa fuska. "Bana sha" Zama tai ta kalle shi sosai. "Bangane baka sha ba. Nika karba ka shanye in tashi in wanke singlet din can daka cire" Gani tai da gaske yake baya shan maganin. "Saina narka a ruwa na dura maka ko?" Dariya ta bashi. Ya tsareta da ido yana fada mata zai so ta gwada dura mishi maganin. "Allah in baka sha ba zan kira umma in fada mata" Da sauri ya karbi cup din da maganin ya shanye. Dan yasan umma sarai. Asibiti zai koma ya zauna sai yagama shan maganin. Dariya tai. Ta wuce ta wanke mishi boxers din. Tai wanka sannan ta fito. Sanda ta dawo har yai bacci. Ta zauna gefen shi. Kallon shi take. Bata tabbatar da abinda take ji game dashi so bane. Koma tace ya girmi so. Sai da nas yace mata anjima sa ciwo. Saida taganta asibiti likitocin sun ki fitowa su bata bayanin. Yanda taji numfashin ta na barazar daukewa. Yanda taji tana son taganshi ta tabbatar da lafiyarshi. Indai wannan ba so bane. Bata san menene ba. Saita tsinci kanta da tofa masa addu.o.i tana fatan Allah ya ci gaba da tsare mata shi. *** Yau ake gama zaman kotu shari.ar su prince ishaq. Da ikon Allah dayai alkawarin biwa duk wani wanda aka zalunta hakkinsa. STORY CONTINUES BELOW An nasarar kama masu laifi dumu dumu. An kuma yanke musu hukunci dai-dai da laifukan da suka aikata. Tunda suka fito daga court din jikinshi a bala.in sanyaye yake. Nas ya dafa mishi kafada yana fadin "Yaya komai ya wuce...... " Numfashi ya sauke yace "Nasani nas kawai raina ne bayamun dadi. Duk jimawar nan. Duk abubuwan nan mun riga mun san daga bangaren su Nawaz yake. Amman kamala......... " Yama kasa karasa maganar. Tunda aka kama harda kamala a laifukan nan jikin shi ya gama sanyi. Ko motar su da tai hadari kamala ne ya kwance musu brake. Duk wani motsin dazaiyi kamala da ya yarda dashi shine babban munafukin shi. Kamala shi yai sanadin mutuwar huddy. Shikuma ya so yai sanadin ta Nas. Well Allah kenan. Ga asirinsu duk ya tonu. Ko ba komai daurin rai da rai ne. Shine sassaucin da alkali yai musu. * Gadonta tagama sakema bedsheet. Tana saka pillow case din. Sam bataji turo kofarshi ba. Sai dai taji ya rungumeta ta baya. Kanshi a kafadarta. "It is over hussy. Komai ya kare. We are safe" Hamdala tai wa Mai Ikon Rayuwa da mutuwa sannan ta zame jikinta ta juyo ta kalle shi. "Sarki......... " Gira ya daga mata alamar ta karasa amman sam ta kasa. Sunan shi wani bala.in nauyi yake mata a baki. Janta yai sosai jikinshi. Sumba ya manna mata a wuya. Cikin kunnenta yace "Ina son jin sunana kan lips dinki husna" Kanta ta sake boyewa a kirjinshi tai shiru abinta. Dole ya hakura ya kyaleta. Sakinta yai yana fadin "Jeki dauko hijab dinki zamu fita unguwa" Harta wuce ta juyo tace "Abinci fa?" Ya girgiza mata kai "Na biyo ta gida. Naci nama wajen umma. Kinci wani abu dai ko?" Ta amsa da "Eh naci nima" Hijab dinta ta dauko ta saka. Shi yake tukasu. Saida suka biya ta sahad. Yace mata ta dibi duk wasu kaya na ciye ciye da biscuits. Duk da har yanzun baice mata ga inda zasu ba. Abinda yasa tayi haka ta diba. Basket guda suka cika da kayan ciye ciye. Ya biya kudin suka koma mota. Ga mamakin husna hanyar estate dinsu taga ya nufa. Murmushin datai mishi har ranshi ya jishi. Tama kasa magana dan murna. * Ba karamun dadi su mama sukaji ba. Babban falonsu suka zauna. Bakowa gidan sai mama. Duk suna islamiyya. Abbansu kuma yana kasuwa. Duk abubuwan da aka kawo masa. Dambum nama kadai yaci. Shima dan yaji dadin na kwanaki da maman ta kawo masa. "Mama dan Allah aisha tazo in anyi hutu mana" Cewar husna Mama ta amsa ta da "Wai husna islamiyyar kuma fa. Kinsan suna hadda" "Mama sai a dinga kawota kullum ai" Prince ishaq ya fadi yana ma mama murmushin dayakasan siye mutane dashi. Kwarjinin shi yasa mama ta yarda cewar zata fadama abbansu idan ya dawo. Suna shirin tafiya su aisha suka dawo. Maheer ne ya fara shigowa da sallama. "Anty husna" Ya fadi muryarshi da mamaki da kuma farin cikin ganinta. Ai aisha najin haka da sauri ta ture shi ta karasa ciki. Da gudunta ta fada jikin husna tana ihun murna. Mama tace "Oh ni aisha ki nutsu dan Allah. Baki iya gaida mutane bane" A ladabce suka gaishe da prince ishaq din ita da maheer. "Su maheer ko adan leqo ni" Husna ke mishi mita. Sosa kai yai a kunyace yace "Zanzo in shaa Allah." Hira suka dan taba kadan. Mama tace ya isa haka. Sun tsaida su ga yamma tanayi. Prince ishaq yace ma maheer ya biyo shi mota ya dauko musu abu. Kamun su dawo mama ta shiga kitchen ta ciko musu wata rubber da dambun nama. Sai turarukan wuta taba ma husna. Ganin lodin ledojin da maheer ya shigo dasune yasa mama salati. Cewar hidimar tayi yawa. "Mama ai kune da hidima" Inji prince ishaq. Addu.a tai musu sosai. Har mota su aisha suka rakasu sannan suka koma gida. Husna wani dadi ne da farin ciki fal zuciyarta. Suna shiga mota tace "Nagode sosai gentle. Nagode da karamci" Kallonta yadanyi ya maida hankalin shi kan tukin. Murmushi ya kwace mata. Kawai ya wani kalleta ya basar. Prince ishaq akwai jin kai. Da zata ce masa yana jin kai. Ko ta kwaikwayi abinda yai yanzun. Zakaga fuskar nan tai ja. Wai shi yaji kunya. Da gudunta ta ruga ta sameshi a dakinshi yana kwance yasaka laptop a gaba yana aiki bayanshi ta dare ta zauna abinta ta sakalo hannayenta ta wuyanshi ta kwanta ta furta+ "Gentle kausar ta haihu ansa mu baby boy" Laptop din ya janye gefe daya. Ya kamo hannunta ta sakko daga bayanshi. Ta zauna gefen shi. Wani yanayi yakeji. Daman ace babyn nan nasu ne. Da ba karamun dadi zaiji ba yau. Da murmushi a fuskarshi ya ce. "Ma shaa Allah. Allah ya raya babyn da mumynshi" Ta amsa da amin kamun yace "Yaushe ne suna?" "Yau aka haihu kaga Friday suna ze kama" bata fuska yayi yace "To yaushe zaki tafi saboda nasan Wanan satin me zuwa ayyukane kaina barkatai bazan samu damar binki abj ba" "Thursday zantafi indawo Sunday" Zaro ido yayi yace "Hussy kwana uku kenan fa ko?" Rau-rau tai da idanuwanta. "Please gentle. Kausar ce fa" "bazan hanaki tafiyaba kinsani, amma hussy kwana uku fa. Ko dan ke ba zakiyi kewata ba?" Murmushi tamasa tana dora kanta a kafadarshi. Ita kanta tasan a daddafe zatai kwanakin nan. Ko bikin gidansu da akai. Dadewa take batai bacci ba. Ta saba duk juyin da zatai ya gyara mata kwanciya a jikinshi. "Gentle kayi hakuri zan dawo saturday.Wallahi nima zan kewarka sosai." Matseta yayi tamkar wani zai kwace masa ita. Yai shiru kawai. Kwanakin daya rage musu yake kirgawa. Yanajin da husna ta soshi da bata soshi ba. A karo na farko a rayuwarshi zai karya alkawari. Da bazai taba iya hakura da ita ba.1 Koda kuwa ba za.a samu wani ci gaba ba a zamansu. * Da kanshi yaje yai mata booking tun kamun ranar tafiyarta abuja. Ta gama shiryawa tsaf. Shi zai kaita airport ya wuce gidansu. Ya wani tsaya jikin bango ya tabare fuska. "Gentle please. In kana haka da fuska yazan in tafi" Takawa tai ta karasa inda yake tsaya. Hannuwanshi ta riko bai hanata ba. Kawai ya zuba mata idanuwanshi ne. "Gentlee manaa..... " "Kawai bana so ne. Bana sonki da nisa haka har kwana biyu" Ji tai harya kanta ya soma ciwo. Ita kanta badan kausar bace bamai ja mata tafiyar nan. "Ginger dinka na fridge" Ta fadi kaman ginger din data hada mishi zai rage masa missing dinta. "Ki aika mata da ginger din ni ki zauna" Dariya ya bata. Shima kuma sai abun ya bashi dariya. Janta yai jikinshi yau hugging sosai. Ji yake kaman ya maida ta cikin jikinshi kawai ya boyeta. Dakyar ta lallabashi suka fita. * Tana isa abuja ta samu ana jiranta a airport. Saida ta shiga mota sannan ta kira prince ishaq din. STORY CONTINUES BELOW Hira sukai tayi har saida taje kofar gidan kausar tukunna. Tace zata kirashi anjima. Kausar kaman tai me dan murna. Ta bala.in jin dadin zuwan husnar. Nan suka shiga hidima basu samu zama ba sai dare. Hira suka sha sosai danma kausar akwai gajiya a jikinta. Hakan yasata bacci da wuri. Husna ta tusa babyn a gaba tana ta kallo. Yaron abun sha.awa. Lokaci daya son mallakar nata yaron ko yarinyar. Sai dai bata san rana ba. A yanayin zaman su da prince ishaq. Wani ajiyar zuciya ta saki tana jin kewar shi. Waya ta dauka zata kirashi kenan. Saiga kiranshi ya shigo. Tana dauka yace mata "Hussy na kasa bacci kuma nagaji sosai" Ji take kaman ta rungumo shi ta cikin wayar. Ko tai tsuntsuwa ta je kano. "Nima inata missing dinka" Shirun shi yai mata tasan shi sarai. Bai gaji bama wasu lokuttan magana na masa wahala. Balle yanzun dayagaji. Labarin baby ta shiga bashi. Saidai yace mata umm. A haka har taji shiru. Sumba ta manna ma wayar sannan ta kashe. Ta ajiyeta gefe tai addu.a sannan bacci ya dauketa cike da mafarkin prince ishaq. * Anyi suna komai yaji husna sai fama take da babyn tamkar ta had'iyeshi. Daukar hoto tayi ta turawa prince Ishaq ta whatsapp aikuwa tasha mita taje tana ta kwalliya. Shi anbar shi shi kadai. * Washe gari tun takwas ya kirata ta shirya dan kuwa jirgin karfe goma zata bi. Kausar ta karbi wayar suka gaisa. Yai maga Allah ya raya. Ta mishi godiyar kayan babies da suka sha. Da husna zata tafi. Fada kausar ta kara yi mata sosai. Ta kwantar da hankalinta. Ta zauna lafiya da mijinta. Dariya tai dan ko kausar bata fada ba. Ammar ya zama tarihi a wajenta. Akwai bangare na zuciyarta da bazai taba manta shi ba. Saboda ta soshi so na gaskia. Yanzun duk wani fata na ci gaba da rayuwarta prince ishaq take gani. * A gida ta same shi. Ya wani basar saboda hadiman da suka shigo mata da akwatinta. Suna barin wajen ya karaso ya rungumeta. Kamshin shi take shaka. Da yanayin matseta dayai yake nuna mata yanda yai kewarta. *** Sam ya kasa bacci. Yana rike da husna. Zuciyarshi cike fal da wani yanayi daya kasa fassarawa. Wani irin daci yake ji. Daren yaune kawai ya rage masa WATA BAKWAI din daya diba ya cika. Sam bacci ya kaurace ma idanuwanshi dan haka ya dauro alwala yazo ya jero sallah raka.a hudu. Zama yai ya bude Qur.ani yana karantawa. Daya idar yai addu.a ya roki gafarar Ubangiji na banzatar da duk hakkokin aure da Allah ya dora masa dayai yabiye son zuciyarshi. Ga alkawari daya dauka cikin bacin rai. Alkawarin da baya zaton zai taba iya cikawa. Duk da yasan hukuncin rashin cika alkawari. Har asuba yana zaune wajen yana sake sake a zuciyarshi. Saida ya sako alwala ya fito. Husna ya taba a hankali ta bude ido. Baice mata komai ba ya zauna abinshi. Yana kallo ta tashi ta shiga bandaki. Shi yaja musu sallah. Suka idar sukai addu.o.i. STORY CONTINUES BELOW Wanka ya shiga yayi. Ya dawo gefenta ya kwanta ya lumshe idanuwanshi. * Zaton husna bacci yake yi. Tabon dake jikin wuyanshi na ciwon da aka ji masa tasa hannu tana tabawa. Yana jinta yai luf abinshi. Hannun ta ya ci gaba da mishi yawo a fuska. Harta gaji bacci ya sake daukarta. * Lalubawa tai gefe bataji prince ishaq ba. Ta bude idanuwanta. Baya dakin banda kamshin shi babu komai. Tashi tayi ta shiga wanka. Data fito dakin sake kayanshi ta shiga. Dan akwai kayanta da yawa dakin shi. Atamfa ta dauka riga da zani simple. Ba wata kwalliya a fuskarta sai dan jan baki da ta saka pink. Ta san duk inta saka shi sai prince ishaq ya sa hannu ya dangwalar mata. * A babban falon su na sama ta same shi yana kwance. Gefen shi ta zauna hadi da fadin "Ina kwana" Cikin sanyin murya yace "Kin tashi lafiya?" Ta amsa da "Alhamdulillah" "Ka taso muje muyi breakfast. In kuma kana son wani abune in shiga kitchen in dafa maka" Girgiza mata kai yayi. Dan bayajin zai iya sakama cikin shi wani abu. Gabanshi ma faduwa yake tun safe. Sosai ta kalle shi. Tasan akwai damuwa tattare da yanayin shi. "Meke damunka?" Shiru yai saida ta dauka baiji ta bama sannan ya amsa da "Kije kiyi breakfast dinki hussy" Kasa ta sauka ta matsa saitin fuskarshi. Idanuwanta ta sauke cikin nashi. "Ba abinda zai iya shiga cikina in baka fadamun meke damunka ba" Wayarshi ya lalubo da take gefe ya bude key din. Calendar ya bude ya nuna mata kwanan wata. Da rashin fahimta tace "Gentle bangane ba" Zaune ya mike ya sakko da kafafuwanshi. Wani iri yake ji. Kaman zazzabi zai saukar masa. Muryarshi can kasa yace "Hussy idan nace ina sonki banma abinda nake ji a zuciyata adalci ba sam" Zuciyarta ke dokawa. Tsalle take. Ta sha karantar soyayyarta a idanuwanshi da yanayinshi amman bai taba fada mata ba. Rawa take da tsalle a badininta. A zahiri kuwa idanuwanta ne kafe cikin nashi. Yaci gaba da fadin "Yau naima Ammar alkawari husna. In bakice kina sona ba zan.......... " Shiru yai ya dafe kai. Dan kalmar ba zata karasu ba wajen shi. Furtata a zuciyarshi kawai wani zafi yake ji. Muryarta na rawa tace "I choose you gentle. Ina sonka. Ina sonka sosai"2 Dagowa yai kallonta yake. Kunnuwanshi na amsa maganarta. Wayarshi ya karba ya bude key din. "Samun number dinshi" Batai musu ba ta karba ta saka mishi. A loudspeaker ya saka. Ringing take ya daga hadi da fadin "Hello" Wasu hawaye husna taji. Ta jima da yima ammar bankwana a zuciyarta. "Hello ammar" Husna ta fadi. Wata ajiyar zuciya ya sauke "Husna..... Ki yafemun dan Allah. Ina mijinki? Bansan ta yanda zan nemo ki ba. Husna munyi kuskure sosai....... " "Ammar" Prince ishaq ya fadi. "Dan Allah ka yafemun. Ka yafe mana. Karka saki matarka......." "Na yafe maka ammar. Allah ya baka wadda tafi husna. Nagode sosai. Daman mun kira ne muyi maka fatan alkhairi" Wani tausayin ammar din yaji har zuciyarshi. Saboda yasan yanda zafin rabuwa da abinda kake so yake. Garama shi lokacin mutuwa ce ta rabasu. Ace a aura mata wani. Bama zai soma hango ciwon abin ba. "Ka riketa da amana. Ka sota sosai. Ka zamana mai yafe mata inta maka laifi. Ka sata cikin farin ciki......" Kasa jiran amsarsu ammar yayi. Ya kashe wayar. Kami husna prince ishaq yai. Ya dagota ya zaunar jikinsu. "I love you hussy" Bude baki tai zata amsa shi ya hada bakinshi da nata. Da sumbar daya manna mata zuciyoyinsu suka hadu. Abinda duk basu da kalaman da zasu fada ma juna ya hadu a lokacin. Ringing din wayarshi ya dawo dasu hayyacin su.+ Saida yai kokarin saita kanshi tukunna ya daga. Mumyn Nas ce tana nemanshi kan maganar komawar Nas makaranta. Saida ya sake sumbatar husna sosai sannan ya fita badan yaso ba. A wajen ta kwanta tana jin wani yanayi na daban. Son shi na kara shigarta. * Bai dawo gidan ba sai yamma likis. Yana shigowa ana sallar magrib dan haka ya fita masallaci bai dawo ba sai dayai isha.i. Jan husna yai dakinshi. Yasa ta sake yin alwala suka gabatar da nafila raka.a biyu. Wanka ya shiga. Ya fito husna ma ta shiga. Mai ta dauka zata shafa ya taso ya rike hannunta. "Nafi sonki haka please" Ajiye man tayi ya jata zuwa kan gadon. Hannunshi ya dora saman kanta ya karanto Addu.ar da Manzon Allah S. A. W yace ayi. ‘Allahumma Inniy as’aluka khayraha wa khayra ma jabaltaha alayhi, wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alayhi.’ Itama husna yana sauke nashi ya dora nata akanshi tana fadin. ‘Allahumma inniy as’aluka khayrahu wa khayra ma jabaltahu alayhi, wa a’uzu bika min sharrihi wa sharri ma jabaltahu alayh.’ Hannuwanta ya riko ya kalleta sosai yace. "Ina addu.a da fatan gina zama da rayuwa ta amana dake husna. Bana bukatar komai daga gareki da ya wuci yarda da aminci" Sauke numfashi tai tace "abu biyu nake rokonka gentle. Ka zama abokina ka zama mijina. Ina son duk randa nake da matsala da mijina inyi magana ta fahimta da abokina" Kai ya jinjina yana fahimtar duk maganarta "Bazan miki alkawarin komai ba husna. Zan iya kokarina" Bai bari tai magana ba ya hade bakinshi da nata. Daren ranar tasha addu.a da albarka. Ya samar musu da wata nutsuwa taban mamaki. * Shi fa yace ta tashe shi karfe goma. Zaije wajen mai martaba. Gashi yanzun shigowarta daki na uku kenan tana tashin shi yaki tashi. Zama tai kusa dashi. Sumba take manna masa ta ko ina na fuskarshi da wuyanshi. Bude idanuwa yai ya fisgota ta fado kan gadon tana dariya. "Gentle dan Allah yi hakuri. Tun dazun inata tashinka kaki ka tashine fa" Bai saurareta ba ya soma aika mata da saqonni cikin salon shi dake tsaya mata a rai. Tun tana masa magiya harya kashe mata bakin magana. * Sanda ya fito wanka tana kwance. "Hussy ki tashi. Yunwa fa nake ji" Tana jinshi gaba daya yagama gajiyar da ita. Tai shiru kaman tana bacci. Gefen gadon ya zauna. "Bara mu kara wani round din....." Kamun ya karasa ta duro daga gadon ta nufi toilet ya kwashe da dariya. Bedsheet din ya cire ya dauko wani ya sake. STORY CONTINUES BELOW Da kanta ta sauka kasa ta hado mishi plantain da soyayyen kwai da ruwan Lipton. Tasan baya son madara a tea. Ajiye mishi tai. Ya kamo hannunta. "Zo inji kalar lipgloss din nan" Kwace hannunta tai tana fadin "Sai mai martaba ya aiko fadawa an dauke ka a kafada ba ruwana" Dariya yai sosai. Ya kyaleta. Yaci abincin shi. Bayanda baiyi da itaba tace ta koshi. Taci nata da yana bacci dazun. Mikewa yai yana fadin "yanzun amun a dawo lafiya ko?" Langabe masa kai tayi. "Gentle inzo mu tafi? Zanje in gaishe da umma" Ya girgiza kai alamar aa. Bude baki tai zata sake magana yace "Ba inda zaki fa. Bana son baby na yasha rana" Rufe fuska tai tana fadin "Gentle ka bari please. Cikina ba komaina cikin shi" Kamota yai yana shakar kamshin ta da take cewa ya zama iri daya da nashi tunda turaruka daya duke amfani dashi yanzun. Yakan mata gardama dan shi ji yake nata kamshin daban yake. *** Abinci suke ci suna taba hira. Ta dauki nama ta saka abakinta. Kawai sai ji tai gaba daya kamshin naman ya da taste dinshi ya mata wani iri. Dakyar ta karasa tauna shi. Tana hadiyewa taji wani amai ya taso mata. Da gudu ta tashi ta nufi dakinta. Prince ishaa ya bi bayanta yana fadin "Lafiya. Hussy....... " Bandaki ta shiga ta dinga kwara amai kaman yan cikinta zasu fita. Tana gamawa ya zuba mata ruwa ta wanke bakinta da fuskarta. Kayanta ya tayata cirewa yanata zabga mata sannu. Dakyar tace masa ya fita abinshi zata iya yin wanka. Dole ya kyaleta dan hussyn tashi har yanzun kunyarshi na dawainiya da ita. Tana fitowa wanka sai zazzabi. Kamun kace meye jikin nan rau. Cayai ta tashi suje asibiti takiya. "Me yasa kai ba zaka dubani ba?" Shiru yai. Ya fada mata ya ajiye aikin shi tun randa huddy ta rasu. "Huddy zata so ka ajiye aikinka ne? Gentle ita kanta lokacinta ne yayi. Kaman yanda namu zaiyi muma. Inhar ba zaka dubani ba karka sake mun maganar zuwa asibiti" Tana karasa maganar taja blanket ta rufe ta juya mishi baya. Ya lumshe idanuwanshi ya bude su. Kan gadon yahau sosai ya kamota. "Hussy please ki tashi mu tafi asibiti. Kinga baki da lafiya" Ture shi tai. Duk da jirin da take ji zaune ta tashi. "Akan me ba zaka koma aikinka ba? Ni ka rabu dani. Daka damu dani ai da ka dubani da kanka" Baya son matsala sam sam. Baya son rikici. "Are we fighting?" Ya tambaya yana zuba mata idanuwanshi dake shirin wargaza mata duk abin da tai niyya. Sauke nata idanuwan tai. Tasan meye ba yaso ta soma hawaye. Tasa hannu tana goge fuska. Gaba daya ta dagula mishi lissafi. Hannu yasa ya tallabi fuskarta. "Husna please dan Allah karkimun haka" Idanuwanta cike taf da hawaye ta kalle shi. STORY CONTINUES BELOW "kamun alfarmar nan gentle. Ka koma aikinka idan ka zama sarki ba ajiyewa zakai ba?" Sakinta yai ya tashi ya fice. Addu.a husna take har ranta Allah yasa ya koma aiki. Dan Nas ya bata labarin yanda yake bala.in son aikin shi. Tun randa hussy ta rasu a hannunshi ya tsorata. Prince ishaq kam daya fita wajen dakin. Jikin bango ya jingina. Ajiyar zuciya ya sauke. Ya jima yana tunanin komawa aiki amman jikinshi sanyi yake yi. Kamun ya kara kasawa ya dauko wayarshi daga aljihunshi. Dr. Abdul ya kira ringing daya ya dauka. Kalmar shi ta farko shine "welcome back Dr.ishaq" Murmushi ya kwace mishi. Yace "Gani nan zan shigo yanzun" Bai jira amsarshi ba yaje ya fito da husna. Saida ya tabbatar mata dashi zai dubata kamun su isa "Royalty hospital" Da hadin gwiwa ne na su uku. Prince ishaq da kanshi. Dr Abdul sai Dr.muneerat da babbar gynecologist ce. * Da kanshi yaima husna duk wani abu da ake bukata. Hamdala ya shiga yi ganin husna nada shigar ciki sati biyar. Zuwa yai ya dauketa suka tafi gida. Duk da zazzabin dake jikinta bai hana shi nutsar dasu wata duniya ba. Cewan shi celebrating yakeyi. * Wani irin laulayi husna take mai wahala. Kome taci sai ya dawo. Duk wani taimako da kula da take bukata tana samu daga wajen prince ishaq. Catai mishi ya kira gidansu a kawo mata aisha ko dai ba zatai mata wani aiki ba. Idan ya tafi asibiti abinshi sun zauna. Fur yace saidai ta kira da kanta. Shi kunya yake ji dayace bata da lafiya za.a gane ciki ne da ita. Itama ba zata iya fada ba dan haka ta hakura. Ko in sun waya mama ta tambaye ta haka take cewa suna lafiya. Haka taita fama bata dan fara samun sauki sauki ba saida cikin yai wata hudu tukunna. A haka komai yake tafiyar musu a nutse da kwanciyar hankali da wata irin kauna mai burgewa. *** Zaune take da tikeken cikinta tanata faman cin cookies prince ishaq ya shigo. Sam bataji shigowarshi ba. Tsayawa yai yana kallonta. Dariya ta bashi. Dariyarshi taji ta dago kai ta kalle shi. Kokarin tashi take ya karaso da sauri yana fadin "Hussy me zakiyi haka. Kina son wahalar mun da baby" Tabe baki tai tace "Ai yanzun fa komai baby. Sannu da zuwa fa zan maka" Dariya yai. "Na hutar dake. Ya kuka wuni. Inata kiranki baki dauka ba" Sai lokacin ta tuna can daki tabar wayar. "wayata na daki gentle. Nikuma ina nan" Hira suke kadan kadan tace masa ya tashi yaje ya watso ruwa ga abinci ma baici ba. Tashi yai. Dan ba karamar gajiya ya kwaso ba. Yau asibitin nasu cike yake da mutane. * Harya fito tana nan zaune inda ya sameta. Kujera ta dafa tana mikewa dakyar. Yana tsaye yana kallonta. Dan yasan hali. Dayaje tayata zatace bata so. Inbai sa.a ba ma ta tusa rikici ya mayar da ita kaman wata tsohuwa gani yake ba zata iya komai bane. "Gentle dazun......... " Wani amsawa taji kugunta yayi daya katse mata maganarta. Ji tai abin nayi ne ta saka salati. Da gudu prince ishaq ya karaso inda take. "Ya Rabb hussy. Sannu.." Kamata yai ya zaunar. Sun sha karbar haihuwa. Amman data zo kanshi sai yaji komai ya kwance mishi. Wata damqa da husna tai mishi tana salati sai da yai zaton ta tsage masa kashi. Dakyar ya samu ya dauko wayarshi ya kira umma. * Kamun suzo husna ta haifo yaronta kato dashi. Shi ya yanke cibi. Baiji komai ba ya rungume danshi a jiki yana jin kaunar yaron na wani shigarshi. Kiran sallah yai mishi a kunne sannan ya riko husna suna ma Allah godiya tare. "I love you husna" Yake ta maimaitawa. Duk da gajiyar dake jikinta bai hanata sumbatarshi ba. "I more than love you my prince my gentle" Takai mintina sha biyar tana neman takalmin ta rasa inda yusra ta jefa shi. "Yusra ki zabi wani mana duk takalman kin nan dan rigima sai wannan zaki saka?" "ana la 'urid 'an airtida' bedhm albaed (ni bana son wani)" Yusra ta fada. Husna ta lumshe idanuwanta. Dai dai sallamar prince ishaq. "Amira(gimbiya)" Jikinshi yusra ta makale tana fadin. "Abba aqul laha lileuthur ealaa hadhayiy (kace mata ta nemo min takalmina" Kallon shi husna tai tace. "Ka dinga yima yarinyar nan yaren da nake ganewa" Yusra ya kalla yace "adhhab waleubb mae yasir(jeki yi wasa da yasir)" Fita tai batare da musu ba. Ya karasa inda husna take ya dora hannuwanshi akan kafadarta. Sumbatarta yai a hankali yana shanye duk wani fushi da take da yanayin kaunar shi. Ture shi tai tana maida numfashi. "Seriously gentle in baka gida ni kake bari da wahala. Daga ita har yasir. Garama Nur" Dariya yai yace "Kibarmun yara na. Idan na sake ajiye wani a cikinki zan dinga mishi hausa" Zaro idanuwa tai tace "Gentle ka rufamun asiri. Duka watan yassar nawa? And beside yara ne saika gaji dasu" Murmushin sa yai. Yasan kishi ne yake cinta. Dan a cewarta ya taba ganin sarki da mata daya? Hanci ya ja mata yace "Hussy please mana. Banfa zama sarkin ba. Idan na riga mai martaba mutuwa fa?" Bakinshi ta rufe da hannunta tana girgiza masa kai. "Kar in kara ji" Rungumeta yai a jikinshi yana fadin "Tam kema karna sake jin hangomun rayuwa da wata matar bayan ke. Kin yarda?" Kai ta daga mishi. "You are my now and forever hussy" Ya fada yana hada bakinshi da nata sukaji an buga kofar "Mami. Yassar na kuka" Cewar Nur(dayake hakan suke kiranshi. Shi yaci sunan mai martaba) Da sauri prince ishaq ya saketa. Hannu ta saka ta goge mishi jan bakinta daya bata mishi lips tana fadin. "Gentle ka shiga toilet din su yusra ka wanke fuskarka duk jan baki" Mudubi ya kalla yaga ba komai fuskarshi ta riga da ta goge. Juyowa yai ya nufota yana fadin "Hussy zo nan?" Da gudu ta fita daga dakin ya bita..........!!! ALHAMDULILLAH.

Post a Comment for "WATA BAKWAI CHAPTER18 KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...