WATA BAKWAI CHAPTER17 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA BAKWAI CHAPTER17

WATA BAKWAI CHAPTER17

- - Post a Comment
WATA BAKWAI CHAPTER 17


  Yauma bayan sun shirya sai da suka fara biyawa suka ce ma Nas zasu je yawo in sun dawo zasu biyo.+ Idan doctors din sun yarda wajen shi ma zasu kwana. "Go do your romantic yawo. Nikam am fine. Bama saikun dawo ba munyi waya" Nas ya fadi yana musu murmushinsa yana jin dadin ganin yayan na shi cikin nutsuwa da walwala haka. Saida suka dan kara hira tukunna suka fita. Mai taxi din da suka hau yana gane turanci dan haka prince ishaq yace yakai su inda ake bada renting din mota. Aikam shi ya rakasu. Kasancewar ba yan kasa bane yasa da suka biya kudin renting din motar. Saida ya bada passport dinsu shida husna. Insun dawo da motar a basu abinsu. Sai da suka shiga ne suka dauki hanya husna tace masa "Ina zamuje ne wai? Ka wani kama mota kaman kasan gari" Dariya yai ya daga mata kafadu yace "Mu dauki hanya kawai muga gari. Duk inda muka gaji mu dawo" Rigimar shi din nan tana bata mamaki a lokaci daya tana burgeta. "Kawai ina son yanda nake da damar fita duk inda nake so ba wani fargaba. Ba kallon mudubi ko wasu na biye dani" Ya fadi cikin sanyin murya da yasa ta jin wani abu ya tsaya mata a wuya. Sam rayuwar su bata mishi adalci wani lokacin. Daurewa tai tace "Mu na bin gabas saboda tafi sa.a" Baisan lokacin da dariya ya kwace masa ba. Itama dariyar tai. Suka dauki hanya. Duk inda ya burge shi su fito su gani. Idan wajen siyar da abune su duba su siya wanda yai musu su fito. Sosai yawo suke abinsu. Wani waje suka tsaya inda suka ga masallaci. Gashi nan maza da mata. Fita sukai suka shiga. Sukai alwala. Husna ta wuce inda matan ke bi. Tai sallah. Ta riga shi idarwa ma ta fito wajen motar tana jiranshi. Saida suka shiga yace "Wallahi ji nake kaman muyi zaman mu kar mu koma gida fa" Ta kai hannu ta ja mishi kumatu ya ture yana dariya. * Yamma tayi zagayen gari kawai suke. Hadari ya hado. Iska aka fara sosai hakan yasa shi samun wani waje sukai parking. Zaman su sukai cikin motar shiru. Ya jingina da kujera yana kallon husna da take danne dannenta a waya. Ruwa ya tsuge ba shiri suka rufe gilasan motar. "Yau zamu kwana anan kenan" Cewar husna A kasalance yace mata "Inji waye da ruwan nan ya tsagaita zamuyi tafiyar mu abinmu" Ba ai mintina ashirin ba ruwan ya soma daukewa ya kalle ta yace "You see... " Murmushi kawai tai masa suka kama hanya. Ko tafiyar mintina goma basuyi ba motar ta fara wani slow kamun ta dauke. Suka kalli juna shida husna. Bude motar yai ya fita zaka rantse da Allah yasan abinda ya samu motar. Yana bude murfin wani hayaqi na fitowa da yasa shi rufewa da sauri yana tari. Husna ta fita da saurinta. Ta kalle shi yana kore hayakin da hannu yana tari. "Mechanic gentle. Meye matsalar motar ne?" Ta tambaya cikin tsokana tana danne dariyarta. Hannuwanshi ya ajiye. Yana kallonta fuska a hade. "O. M. G....... " Husna ta fadi tana wata dariya harda dafa mota. Gaba daya hayaqin ya bule mishi a fuska. Bakine har goshin shi kaman wanda kurar gawayi ta bata. Dariya take sosai cike da mamaki yace mata "Wai meke baki dariya. Mun makale a wajen nan kina dariya ko hussy" Dakyar ta iya hadiye dariyar tace masa bakomai fa. Tsaye sukai jikin motar suna jiran wani yazo wucewa ya taimaka musu. Husna ta kauda kai gefe dan data kalli prince ishaq dariya kara kamata takeyi. Wani suka samu ya ko tsaya. Babban mutum ne amman yanajin turanci sosai. Shi ya duba musu motar sukai masa godiya sosai suka shiga suka tafi. Sam bai kula da bakin dake fuskar shi ba. Duhu harya fara sanda suka maida motar. Taxi suka hau suka koma hotel dinsu. * Husna ta kalle shi yanata shagwabe fuskarshi duk baki baki a jiki ta sake kwashewa da dariya. Kamota yai tana kokarin kwacewa ya matse ta jikinshi yana fadin. "saikin gayamun me kike ma dariya" Jan shi tai wajen mudubi ta nuna masa fuskarshi. Ya zaro idanuwa sannan ya kwashe da dariya shima. Hannunshi yasa ya shiga goge fuskarshi yana dariya. "Hussy ke ko...... " "bakai sarkin gyara ba shisa nai shiru ai....... " Gani tai bai gama gogewa ba tace "Akwai fa...... " Yasa hannu ya ske gogewa. Ta girgiza masa kai alamar baiba tana matsawa gab dashi. Hannuwanta takai cikin nutsuwa ta na goge masa. Kallonta yake. Itana tsayawa tai tana kallon shin. Hannunta daya nakan fuskarshi. Kama hannun dake fuskarshi yai da dayan hannu. Ya riko ta yana dora goshin shi saman nata. "Husnaa...... " Ya ja sunanta muryarshi can kasa. Ta kasa amsa shi saboda gani take tana bude bakinta babu abinda zai fito sai karar bugun da zuciyarta take. Koma manene take ji a game da prince ishaq babbane. Yanayi ne da bata taba sanin akwai shi ba. Yanayi ne da babu kalaman da zasuyi adalci wajen bayyana shi. Hannunta ta kwace daga nashi ta dora shi kan wuyanshi yana sake hade goshinsu tare. Lumshe idanuwanta tai tana jin kamshin shi na shigarta yana kara saukar mata da abubuwa masu yawa. A hankali suna goge wasu hotuna na rayuwar ta ta baya ba ma tare data kula da hakan ba. Basu san iya lokacin da suka dauka ba. Dan prince ishaq sam baya son yanayin nan ya wuce. Saboda komai na yanayin ya masa. Haka ya hango rayuwar shi babu hayaniyar mulki a cikinta. Dakyar ya kamata yajata zuwa kan gadon. Kwanciya yai sannan ya rikota jikin shi. Ko kayan jikinsu basu sake bama balle suyi tunanin yin wani wanka. Kwanciya sukai shiru abinsu. Sun jima haka sosai kowa da abinda yake ji. Sallar isha.i suka tashi sukai. Babu mai bakin magana. Wannan karon da suka koma kwanciya. Juya bayanshi yai yana jin wani zazzabin wahalar abinda yake jurewa na saukar mishi. Ya lumshe idanuwanshi dayaji ta matso jikinshi ta kwantar da kanta a bayanshi. Dumin numfashinta a kan wuyanshi. Bai juyo ba a haka yai musu addu.a. Yana jin yanayinta bacci ya dauketa. Ya samu ya janye jikinshi ya shiga toilet ya sakar ma kanshi ruwa mai sanyi shine kawai saukin shi. Alwala ya dauro dan baccin yaga alamar zai wuyar ya samu wajen shi. Rayuwa ba ta da wahala. Yau satin su uku a india. Kullum daga wajen Nas babu inda suke zuwa sai yawo abinsu. Da wucewar duk wata dakika ta ranakun nan da shigar wata shakuwa ta ban mamaki tsakanin su.+ Tare da mulkin dake jiranshi ya hango rikici kwance. Sai dai bai hango shigowar husna rayuwar shi ba. * Randa aka sallami Nas sauran kwana biyu kwanakin da suka diba ya cika. Dan yaji sauki ne sosai. Karfin addu.ar da ake. Taxi suka dauka su duka ukkun. Tare suka koma hotel din aka kama ma Nas nashi dakin kusa da nasu. * Prince ishaq ya dawo daga duba Nas ya shigo yace ma husna ta fito suje waje. Bata musa mishi ba duk da dare ne. Ta dauki mayafinta suka fita. * Kasan hotel din suka shiga wani dan bakery suka siyi coffee suka fito. Takawa suke suka samu wani lilo babu kowa a wajen. Zama sukayi akai. Prince ishaq ya soma rocking dinsu. Husna tace "Gentle karka yaddo mu fa" Dariya yai. "Kin cika tsoro" Saida ta kurbi coffee dinta sannan tace "Um um fa ba tsoro bane. Da gaskiyata" Shiru sukai "Nagode husna" Ya fadi kaman daga sama. "Godiyar me kake mun?" Ta bukata dan ita bataga dalilin yi mata godiyar ba. Itama ya kamata tai masa godiya. Na fargar da ita dayai daga halaka. Na zama dalilin shiryawarta da iyayenta. Hannun shi ta riko. Sannan yace "Nagode sosai husna. For everything" Shiru tai dan batasan me ma ya kamata tace masa ba. Su. Jima sosai a wajen suna zaune ya a rocking dinsu kan lilon kamun yace mata "Dare yanayi mu koma ko?" Mikewa tai. * Washe gari su uku suka fita harda Nas din. Siyayyar tsaraba sukayi. Nas sarkin shiririta. Yaita basu dariya. * Da daren ranar suka hada komai nasu washe gari karfe takwas a Airport tai musu. Karfe tara jirginsu ya tashi zuwa gida nigeria. *** NIGERIA Wannan karon harda mumyn Nas akazo tararsu. Da wasu yan mata su biyu da husna bata taba gani ba. Dayar bakace sosai. Amman tana da kyau. Dayar hasken su zaizo daya da Nas. Bama su bi takan husna ba. Farar doguwa mai matsakaicin jiki ce ta rike nas din tana wani irin kuka. "Am okay. Everything is ok billy" Nas din ke fadi amman kaman ma ba jinshi take ba. Sai da suka sa husna hawaye. Sakin nas tai takama hannun prince ishaq. Hannu yasa ya goge mata hawayen yana girgiza mata kai. "He is okay. Komai zai wuce" Husna dai kallon su kawai take. Ya saki hannun yarinyar daya kira da billy ya janyo husna yace mata. "Hussy ga sister na bilkisu. Tana karatu ne a saudi. Ga dayar kuma fauziyya. Su duka suna karatu ne a saudi. Billy ta gama ita fauzy ne da saura" Murmushi taima husna tace "Mungode sosai da karamci. Welcome to the family. Muna farin cikin shigowarki" "Nima nagode bilkisu" Gaisawa sukai da fauzy fuskarta babu yabo ba fallasa har hakan yasa husna kallon prince ishaq. "Karki damu haka fauzy take da kowa. Baki ga nima kai kawai ta daga mun ba?" Murmushi husna tan dan ta fahimci fauzy irinsu daya da prince ishaq miskilanci. Dukansu gidansu prince ishaq din suka sauka. * Nan ma suka kwana. Saboda maganar bikin billy da duka saura sati biyu. Dan tun tana saudi aka sa rana. Husna da kanta ta kira gidansu ta fada sa bikin gidansu prince ishaq din.+ "Mama ba zaki zo ki ganni ba" Cewar husna Tanajin dariyar maman nata ta cikin waya tace "Husna nikam inzo in miki menene. Idan naji kina kafiya ma ya wadatar" Husna ta langabar dakai tamkar tana ganinta cikin sanyin murya tace "Tam shike nan mama. Ki gaishe mun da abba" "zaiji in shaa Allah. Ki kula banda sakarci husna. Kiyita hakuri zaman yau da gobe sai da hakuri" Ta amsa da "In shaa Allah mama zan kula. Sai anjima" Gaba daya tagaji da kalaluwan abincin da suke ci. Tuwo ma take marmari ita. Dan haka ta tashi da kanta. Tasa asabe ta rakata store. Shakare yake da kayan abinci. Ta dauko semo leda daya tasa aka rakata kitchen din da bata taba sanin hanyar da yake ba. * Asabe ta tayata. Gyaran cefane tai markada a blender. Tuwo tayi miyar danyar kubewa da kaji. Ta saka a warmer abinta tasa asabe ta dauko mata zuwa bangarenta. Saida tabari cewar a bare mata ginger a markada sannan ta wuce. Sallar Asr tayi. Ta fito ta kima kitchen din ta hada ginger drink ta zubo a jug tasaka kankaru ta fito. Tana zuwa babban falo prince ishaq na shigowa. Ga hannuwanta duk kaya. Sallamarshi ta amsa. Ya tako inda take ya na kokarin karbar jug din. Ta fito masa da idanuwa tace "Gentle rufamun asiri kar hadimanka sugani ina saka future king aiki" Dariya kawai yai yace "Nikam kibani abin nan. Ba aiki zan ba. Ya burge ni ne zan sha" Da sauri ta wuce tana fadin bafa abinda zan baka ka taho muje ka dan huta sannan. Ya wani tabare fuska yana binta. Bangarenta suka nufa yasa rikici ai shifa sai ya sha abin nan na cikin jug. Dole ta zuba mishi yasha yana neman kari "Gentle zai kulle maka ciki. Please muje kayi wanka tukunna" Hannun shi ta kama taja shi bedroom dinta. Da kanta ta tayashi ya cire alkyabbar shi ya shiga toilet. Dakinshi taje ta dauko masa wani yadi marar nauyi fari. Ta feso mishi collections din turarukan shi ta dawo. Harya fito ta bashi kayan ta sake fita. Ko minti biyar baiba ya fito falonta ya zauna yace mata "Yunwa nake ji fa" Ya fadi dan duk ranar sunata hidimar auren billy. Bai samu zama ba. "Me zakaci? Sai inje in dibo maka" Ta bukata dan bata tunanin zaici tuwo. "Duk abinda zakici" Ya fadi. Ta ce "um um fa. Ni nagaji da kalaluwan abincin nan. Na shiga kitchen nayi tuwo miyar kubewa" Ai gani tai ya gyara zama yace STORY CONTINUES BELOW "amman kin taimaka husna. Kisan rabon da inci tuwo anyi shekaru? Da umma tana mana tun kamun in tafi karatu" Kallon shi take da mamaki tace "Wai da gaske zakaci tuwon?" Daga mata kai yake yace "Nikam ki zubo mun hanjina yana kullewa" Xuba musu tai. Suka sauka kasa kan kafet. Tai mamaki sunci tuwon sosai. Suka shanye lemonsu. Prince ishaq nata mata santi. "Husna gobe ma ki dafa mana wani abu. Na gargajiya" Da dariya a muryarta tace "Zakaci dambun shinkafa" Ya jinjina kai yace "Ban tabaci ba. Amman komai kikai nasan zaiyi dadi" Hira suka shigayi sosai kan abinci. Itama sai taji dadin yanda taga yaci Ta godema Allah taima mahaifiyarta addua data tsaya taga ta koyi girki. Ta dauka niyya a ranta daga ranar kome take zata shiga kitchen tunda ga yan tayi ta dafa ma mijinta duk abinda yake so. Da dare haka yace mata lemon dazun ya masa dadi sosai. Batace komai ba ta tashi taje kitchen ta kara hado mishi wani. Kissing dinta yai a goshi da kumatu. Nan dakinta ya kwanta yace bazai iya zuwa dakinshi ba yagaji sosai. *** Kwanci tashi babu wahala wajen Allah. Ga bikin billy yau saura kwana biyu. * Zaune ya sameta a parlour d'in kasa ta kurawa wayarta ido tana chat da khausar sai uban murmushi takeyi harma batasan yashigo ba. Kamshinsa ne daman take gane shigowarshi dashi. To yanzun kamun ya fita ya gama dakunata itama kamshin nasa take. Ko da taji shi ya cika mata hanci ma ta dauka na jikinta ne daya rungumeta sanda zai fita. Tabayanta ya zago ya warce wayar juyowa tayi gaba daya ta kalleshi. Murmushi tai tace "Gentle yaushe ka shigo?" Dariya ya saka ya wuce abinshi yana fadin "Kinata danna waya ina zakiga shigowata" Mikewa tai ta bishi tana fadin. "Gentle ka tsaya mana. Kaifa nake jira daman" Side dinshinsuka wuce. Ya ajiye wayar kan gado. Yana wani dakuna fuska shi a dole fushi yake. "Waya fad'a maka banji shigowar kaba,naji fa bayan kamanta fushi nake dakai kafita bansaniba" Juyowa yayi ya kalleta kawai ya wuce dakin sake kaya. Ya fito "Ki shirya, umma tamun waya komai naki yana can wai kije tun yau" Wani murmushi ya kwace mata "Inje in dauko hijab dina?" Janyo ta jikinshi yai ya furta "Kina murna zaki barni har kwana wajen hudu. Ko kewana ba zakiji ba ko?" "Waya gaya maka ni baruwana duk inda zakaje zan bikane" Murmushi yamata yace "hargun mai martaba saikin bini?" Waro idonta tayi suka kwashe da dariya dukkansu.... STORY CONTINUES BELOW * Biki ya kankama yau ake kamun Amrya Billy da Angonta saeed. Amarya da ango sunsha kyau a taheer guest palace ake bikin kamun. Hussy tashirya tayi kyau iya kyau domin kuwa takanas ta kira belleza, tazo tamata makeup kuma ba laifi tamasifan yi kyau, blue and yellow tayi bawani mayafi ta yafaba. Ashoeke ne blue nakai da na yafawa a kafad'a tayi kyau matuka kai kace itace Amaryar. Prince ishaq ta kira a waya dan yace inta gama shiryawa shine zai kaita. Ga yan gidansu duk za.a tafi gaba daya amman yakiya. Kallonta ya tsaya yanayi domin kuwa ta masifar masa kyau. Murmushin dake karawa fuskarta kyau ta sakar masa tace "Gentle I'm set" janyota yayi jikinshi yashaqi kamshinta mai dad'i ya furta "Hussy anya kuwa zan barki ki fita ahaka kinga yanda kikayi kyau kuwa? Wurin fa da maza" Langwabe kai tayi ta furta "Gentle ba dakai zamuba aiba wanda ma zai kalleni ansan ni matar prince Ishaq ce da anganni" baice komaiba ya sake ta dan yaga mutane nakai kawo. Mota suka shiga. * Wurin ya matukar kayatuwa domin kuwa komi yaji sam barka. kallo ne ya koma sama sanda prince ishaq ya shigo shida hussy domin kuwa sunsha kyau shikuwa sai shan kamshi yake ala dole ana Kallar masa hussyn shi. Ahaka taro ya watse .... * Washe gari dinner akayi a guest house na mai martaba. Nanma sunsha kyau matuka amma antaru sosai wurin ba kama hannun yaro. Zaune prince Ishaq yake shida hussy,shifa duk inda take yananan manne da ita. Wani friend d'inshi zahar yamai waya kancewar yana waje yazo yashigo dashi. Ya nata duba wanda zaisa yaje ya shigo da zahar din bai samu ba. Dan haka yace ma hussy. "Yanzun zan dawo. Karkije ko ina fa" * A hanya taro mutane yayi yawa shikuwa yau mulkin yakeji ahankali yake rabe mutane yana wuceww harya kusan isa gate din da zai sadashi da waje. Ji kawai yayi an cakamai wuka hannu kara yasaka ya dafe wurin dagowar dazaiyi yaga ko waye. yaga ankuma daga wukar zuwa kirjinshi da sauri ya kai hannu dan ya kare. Ya same shina wuya. Ya rike shi dam ya soma ihun kiran mutane. Hankalin mutanen kuwa ya soma yo kansu. Jirin dake dibar shine yasa mutumin ya kubce masa. Amman ina an nasarar damke shi. Prince ishaq kam kasa ya tafi luuu. Ya sume saboda jinin dake zuba jikinshi. * Hussy ta taso domin ta dubashi kasancewar taga wayanshi dayabari kan table nata tsala ihu,da alama wanda yafita ne yashigo dashi basu haduba. Wayar hannunta taga tana ringing. Ganin Nas ne ta dauka tun dazun take mitar bata ganshi ba. "Hello kanina" "Anti fito waje please yanzun nan" Yanayin muryarshi ya tsoratata. Da gudu ta fita waje. Taga komai ya hargitse ga yan sanda sunzo. Nas ta hango ta kara Sa wajen shi. Baice mata komai ba ya kama hanya tabishi. Mota suka shiga gidan baya su dukansu. Sai lokacin take ce masa "Me ya faru. Ina gentle?" Shiru yai kawai. Gani tai yasa hannu yana goge fuskarshi. Ai nan take kuka ya kwace mata. "Dan Allah naseer ka fadamun kome ya same shi" Dakyar ya sauta muryarshi yace "Wani ne ya ji masa ciwo. Amman komai ya kusa karewa. An kama mutum daya yau" Ai tun daga kalmar "ciwo...... " Ta daina fahimtar komai. Kuka kawai take suna hanyar asibiti. So take taganshi ta tabbatar da lafiyarshi kalau. Babu abinda zai samar mata miji.

Post a Comment for "WATA BAKWAI CHAPTER17"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...