WATA BAKWAI CHAPTER 9 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA BAKWAI CHAPTER 9

WATA BAKWAI CHAPTER 9

- - Post a Comment
WATA BAKWAI CHAPTER 9





  Babu abinda yakai ciwon rashin wanda ka shaku dashi. Babu abinda yafi tashin hankali sai ya fado maka a rai muryarshi da take cikin tunaninka ta soma dishewa. Saika nemi yanda sautin dariyarshi yake ka manta saboda ya maka nisa. Ya tafi inda zakaje wata rana. Da duk yawan hawayen da zaka zubda da karin tabbacin cewa bazai taba dawowa ba. Sadaukarwa ga duk wanda ya taba rasa wani mai kusanci a tare dashi!!!*1 Tsaye yake kawai ya sakarma kanshi shower.Yanajin yanda ruwan ke bi masa jiki. Idanuwan shi a rufe. Baisan dalilin kukanta ba amman ya tsaya masa a rai sosai. Da ganin yanayin kukan yasan ko menene ba karami bane. Har ranshi dai yana fatan bashi bane sanadin kukan ta. Mutum ne shi da baya son ya takura ko a takura shi. Dan haka tun randa aka kawota sai dole suke magana. Balle daya sake kula da cewar ko magana kan dole take masa ya kara fita harkarta. Yau kukanta ya dawo masa da abubuwa da yawa. Wankan ya fito ya shirya. Fararen kayan dai ya kara sakawa ya nufi dakin husna. * A daddafe tai wankan ta fito. Doguwar riga tasa milk color. Ta daura mayafin rigar a kanta. Hijab taje dauka kaman yanda ta saba zama da ita. Taji kwankwasa kofar prince ishaq. Cikin sanyin murya tace "Shigo" Ya turo ya shigo hadi dayin sallama. Gefen gadon ya zauna kanshi tsaye yana kallonta. Tayi kyau saidai fuskarta ta kumbura da idanuwanta saboda kukan datai. Hijab din ta zura baice mata komai ba. Abokantakar tasu mai rauni ce sosai. Saitai kwari zai hanata saka wannan hijab din tunda ba kalar matan dabai gani ba. "Muje" Ta ce masa. Tashi yai ya karasa daf da ita. Fuskarta yake kallo sosai kaman me neman wani abu. Muryarshi a dake yace. "Kuka kika kara yi ko?" Da sauri ta girgiza masa kai alamar Aa saboda yanda yake sa gabanta ya fadi. Yanda take jin wani shakkar shi na cika mata zuciya. Kallon ta yaci gaba dayi na yan mintina baice komai ba ya wuce gaba. Kafafuwanta ba kwari tabishi har dining room din. Ta zauna. Zagayawa yai ya zauna kujerar dake fuskantar husna. Plate ya dauka ya zuba mata white rice da miyar nikakken nama. Ya zuba plantain a sama ya tura mata. Kanta a kasa taja plate din. Ta soma ci a hankali dan bayau ta fara cin abinci a gaban shi ba. Kawai dai yaune na farko da shi ne ya zuba mata. Tayi mamaki saboda tana masa daukar mutum maijin kanshi da izza amman ya zuba mata abinci. Kamun taci ko rabi ya zuba fruits yankakku a plate ya sake turo mata da fork a ciki. Dagowa tai ta kalle shi. Shima fruit dinne cike yanata ci. Ba yunwa take ji ba ma. Kawai dai tana cine. Ture plate din abincin datai ne yasa shi dagowa ya kalleta. "Me kike nufi?" Ya tambaya. "Nako shi" tace idanuwanta a kasa. Muryarshi a dake yace. STORY CONTINUES BELOW "Tam ki zabi daya. Ko ki cinye abincin nan ko ki shanye fruits din." Yau bata da karfin gaddama ko neman rigima. Cikin raunin murya tace masa. "Nako shine fa" "Just shut up and eat husna. Bana son gaddama, ki zabi wanda zai miki saukin cinyewa." Yana karasa maganar ya maida hankalinshi kan fruits din dayake sha. Da yawan lokuttan da suke daidai ton zama cin abinci waje daya kulewa yake da yanayin cin abincinta. Dan baya son mata magana ne. Ya tsani wasa da abinci duk da shima bawani cin kirkin yake ba. Kallon shi take ya wani hade rai yana tauna fruit din a yangan ce. Dan fa sun zama abokai na wucin gadi bazai sa ya dinga mata wannan shisshigin ba. Fruit din ta dauka ta soma ci. Ta kusan rabi ta ture ta kwantar da kanta a table din. Kallonta yake. With time zata koyi yin duk wani abu da ya umarta. Kyaleta yai bai takurata ba. Yasan limit dinshi. * Satin Nas daya yau a gidansu kasancewar ya kira mumyn shi tace masa yai zamanshi abuja yafi mata kwanciyar hankali. Dan tasan in yana kano bamai kwabarsa. Bamai hana shi fita yawo yaje a samu matsala. Abuja kam tana da tabbacin prince ishaq zai kula da Nas fiye da yanda zai kula da kanshi. Husna ji take kaman sun shekara tare. Yaron ya wani shiga ranta tana jinsa tamkar maheer qaninta sai dai wannan ya girmi maheer. Zasuyi hira. Suyi game. Zuwanshi yasa ta daina wuni da qunci. Da dare zasu sha waya da ammar dinta in kuma yanayin aiki bai riqe shi ba sukanyi chatting. Prince ishaq kaman yanda ta soma kiransa dan a ganinta lokaci yayi da zai zama hakan. Saboda dalilai da dama. Sukan gaisa. Sukanyi hira su uku amman indai su biyune a waje sai su rasa me zasu cewa juna. Duk wani iri kowa saiya daburce. Dan haka suka dinga qoqarin in nas na nan kawai. In baya wajen kowa yai harkarsa. * "Yaya menene idan na fita ni kadai nan ai ba kano bane. Beside babu wanda ma yasan waye ni." Nas ya fadi kaman zaiyi kuka. "In zaka fita wani waje da yake da yawa mutane haka kaman cinema nas you must go with securities.Banson hauka" prince ishaq ya ke maganar cikin qosawa. "I want some normal yaya ka fahimce ni mana. Shisa baso bane banayi inzo inda kuke hakanne yake damuna am 18 fa koda ka manta" "And?" Prince ishaq ya fadi da alamun ranshi ya soma baci. Cikin fuska nas ya kalle shi "hakan yana nufin zanyi yanda nake so da rayuwata. Ba zai yiwu duk inda zani da masu gadina ba kaman wanda za.a kashe" Ya bude baki zai bashi amsa husna tazo wajen.. Kallonsu tai su duka. Tasa akwai abinda yake faruwa. Nas yace mata "anty kice yaya yabarni na fita." Kallon shi tai duk da yana mata kwarjini naban mamaki. Cikin dakiya tace "Kabarshi mana tunda yazo sau daya ya fita" Harararsu yai su duka. "Kibar abinda ba zaki taba fahimta ba. Yaron nan bazai fita gate din farko bama babu masu gadi. Chapter closed" STORY CONTINUES BELOW Yanda yai maganar yasa sukai shiru su duka. Yabar wajen kawai. Nas kaman zai kuka yace "I fucking hate this life!" "Calm down kagane kabishi a hankali." Husna ta fadi cikin sigar ban magana. A hasale nas yace "bazai bari ba anty. Wani lokaci rayuwa bata da adalci. Amman wallahi saina fita" Kamin ta samu bakin magana yabar wajen. Zama tayi abin ya daure mata kai. Meke damunsu su duka biyun. Tasan bata damu da prince ishaq ba amman nas kam dan uwa takejin shi a zuci da jikinta gabaki daya. Wajen minti talatin tsakani taji text ya shigo wayarta. Ta duba taga nas ne. "@silver bird cinema" Kawai yace. "Please take care!" Ta bashi amsa. Bai mata reply ba dai. Tana zaune a wajen prince ishaq ya zo. Kallo daya taima yanayinsa taji gabanta ya fadi. Bata taba ganinsa haka ba. Fuskarsa a hade take idanuwansa sun wani canza launi. A dake yace. "Ina Nasir?" Cikin rawar murya tace yana silver bird cinema" "Dammit!!!" Ya furta yana dukan kujeran wajen saida husna ta tsorata. Kallon ta yai da wani yanayi yace. "Saboda me zaki barshi ya fita? Akan me ba zaki zo ki fadamun ba?" Ta bude baki zata amsa shi dan bata ga fa yanda zata fara hana Nas fita ba ya katse ta da fadin. "Forget it" Ya dauko wayarshi kenan. Nata wayar ta soma ringing ta dauka nas ne. "Hello qani yadai?" "Wasu ne suka biyoshi sun ji masa ciwo yanzun haka muna bayan silver bird qarqashin wata mota wannan ne number din qarshe takan kiransa dana gani shisa na kira" Kallonshi kawai tai da bayanannen tsoro cikin idanuwanta fuskarta da alamun tashin hankali ya karbi wayar. Magana sukai da kowaye yake riqe da wayar nas din. Prince ishaq ya miqa mata yana tafiya ta tsayar dashi da "Kana tunanin zaka tafi kabarni anan? Cikin damuwa yace "ki zauna saboda yanayi na tsaro" "Wlh saina biyoka aiba qaninka bane kai kadai" Babu yanda zaiyi kuma baya son yawan surutu a wannan yanayin. Dan haka yabarta taje ta dauko alkyabba ta dora kan kayan da suke jikinta. Gabanta faduwa kawai yake. Jami.an tsaro ne tako ina suke zagaye dasu banda wanda yai waya su isa wajen. Husna bata san kuka take ba saida taji abu nabin kuncinta. Jini ne kaman an yanka qaramar dabba a gurin. Da gudu su duka suka karasa wajen Nas din. Girgiza kai prince ishaq yake cikin tashin hankali ya riko Nas jikinshi da bayama numfashi a rikice yake fadin. "Nas banda kai. Please ka bude idanuwanka" Husna na tsugunne gefe "Nasirr" ta kirashi cikin muryar kuka. Baima san tanayi ba. "Ya mutu koh?" Take tambayar prince ishaq. Shiru yai ya kyale yarinyar nan. Dan shima zuciyarsa zafi kawai take masa ba zata iya daukar wani rashin ba.Na huddy kawai ya ishe su. Wai me mutanen nan suke nema dasu ne? Duk akan mulki. Mulkin da in an tona zuciyoyinsu ba qaunarshi suke ba. Ya Allah! Yake fada a zuciyarsa ya dora da Allah ka tausaya mana. Nas yake jijjigawa. Kasa ya ajiye shi kamun ambulance din da aka kira ta karaso. Hannun shi ya dora kan zuciyar shi yana dannawa. Lokaci daya abinda ya faru da huddynshi yake masa yawo akai. Iska ya soma ba Nas ta baki yana jijjiga shi amman a banza. Baiga amfanin karatun shi ba. Ya kasa saving hudeesa yanzun ma ga Nas. Tare suka shiga motar asibitin su dukansu tare da nas. Kuka husna keyi kaman zata shide ganin qoqarin da likitoci suke tun daga cikin motar na ganin ya farfado amman abin yana neman gagara. Prince ishaq ya kalleta sai yaji zuciyarsa tayi wani irin yanayi. Hannunta ya riqo bata hanashi ba dan bama a hayyacinta take ba. Matso da ita yai jikinsa tako ruqunqume shi dam. Duk da halin da suke ciki bai hanashi jin wani abu na daban ba. Kuka take har lokacin amman wannan karon a qirjinsa take yanajin yanda jikinta ke jijjigasu gabaki daya. Saiya tuna masa lokaci mai nisa. Hannunsa yakai kaman zai riqota amman yana tunanin hakan. Wata zuciyar tace kayi ko babu komai tanajin halin da qaninka yake ciki. Hannuwansa duk biyun yasa ya riqe husna yana lallashinta. A haka har suka isa asibitin. Hana su shiga akai dole suka tsaya suna kallo ta window. Ganin yarinyar mutane na shirin sume masa yasa shi janyeta daga wajen window din suka zauna.Tana maqale jikinsa har bacci ya dauketa. Anfi awa biyu wani likita ya fito daga dakin da Nas yake. Tashin dayai ne yasa husna bude idanuwanta dan yama manta tana jikin shi. Girgiza masa kai likitan yai. Wani jiri yaji ya dibe shi.........! Bango ya dafa dan ya kusan faduwa. Husna ce tai karfin hali cikin rawar murya ta ce ma likitan.+ "Ya dai?" Ya bude baki zai magana wata Nurse ta fito da gudu ta kirashi.Ai bai saurare su ba ya koma ciki. Prince ishaq gani yai bazai iyaba. Husna yabari tsaye ta jingina da bango ya tura kofar ya shiga. Ihu zasu fara masa ya fita, ya zaro I.D card dinshi ya nuna ma daya daga cikin likitocin. Safar hannu kawai suka mika masa. Baima damu da saka abu ya toshe hancin shi ba. Na.urar dake gefe ya kalla. Addu.o.i yake karantawa dan gaba daya yagama karaya. Bugun zuciyar Nas cikin dari yana kan sha biyar. Yana tsoron taba shi. Saidai yasan bazai taba yafewa kanshi ba inhar bai kokarta da wani abu ba. Rayuwa da mutuwa duk yana hannun Allah. Wani irin ciwo ne gefen kanshi da har kashin wajen kana hangowa. Aikin shi ya ci gaba dayi tare da sauran likitocin na dinke dinken ciwukan dake cikin shi. Yankan wukane. * Husna kam da taji su shiru. Karasawa tai wajen glass din tana kallon su. Kanta wani irin ciwo yake yi. Ga hawayen daketa zubo mata. Bata taba ganin tashin hankali kwatankwacin nayau ba. Prince ishaq take kallo yanata kai da kawowa. Batasan iya awannin da suka dauka ba. Sannan suka fito. Da sauri ta karasa inda prince ishaq yake. Idanuwanshi sun wani canza launi. Sai taga harya rame saboda tashin hankali. Da idanuwanta take rokon shi yace mata Nas lafiyar shi kalau. Yace mata bai mutu ba. Jikin bangon ya jingina a hankali ya zame zuwa kasa ya hade kanshi da gwiwa. Husna ta tsugunna gabanshi. Hannunta na rawa ta dafa kafadarshi. Dagowa yai ya kalleta kyawawan idanuwanshi cike taf da hawaye. Mayar da kanshi yai ya hade da gwiwar shi. Yanda numfashin shi ke fita ne tasan kuka yake. Jitai zuciyarta ta sake karyewa itama zama tai kusa dashi. Batasan me zatai masa ba saboda batasan me yake jiba. Idan har ita dabata hada komai da Nas ba tana jin wannan dacin a ranta. Shi kuma me yake ji. Hannuwanta ta saka kan kafadun shi. Prince ishaq kam wani abune ya tsaya mishi a wuya. Wani irin ciwo zuciyarshi take masa. Kirjin shi ya masa nauyi. Saboda har yanzun zuciyar Nas bata da karfi. Huhunshi bashida karfin taimaka masa wajen numfashi sai da na.ura. A minti daya komai zai iya tsayawa. Yanajin duk abinda yake samun kowa laifin shine. Shi ake turo ma kashe di. Yakamata ace ya janye daga karbar mulkin nan dayai. Tun akan huddy baiji kashe din ba. Gara ya rasa komai. Abar masa kaninsa. So yake wani ya rike shi ya lallashe shi. Har cikin zuciyarsa so yake wani ya girgiza shi yace masa komai zai zama lafiya kalau. Nas zai ji sauki. Za a daina kokarin kashe su saboda za.a kama koma wanene su samu shaida a hannun su. Jin hannuwan Husna kan kafadarshi yasa shi dagowa. Ganin hawayen dake bin fuskar shi ba karamin girgiza husna yai ba. Tasan maza manya na kuka in abun yakai inda yakai. Amman yanayin prince ishaq yakan nuna zai iya daukar komai duniya ta jefe shi dashi. STORY CONTINUES BELOW Zai iya jure duk wani kallo da kaddara zatai masa. Batasan lokacin datasa hannu tana goge masa fuska ba. Hannuwanta ya ture alamar ta kyale shi baya so. Kai kawai take girgiza masa tana maida hannunta tana ci gaba da goge masa fuska. Zamanshi ya gyara. Wani irin karyewa yaji zuciyarshi tayi. Hannuwanta ya ture ya dora kanshi kan kafafuwanta. Tsayawa tai tana kallon shi na yan mintina kamun ta dora kanta akan bayanshi. Su dukansu kuka suke. A wannan lokacin ba tare da saninsu ba abinda suke ji ya kulla alaka. Kaman yanda aurensu ya kullu a bisa kaddara haka kaddarar data fada ma Nas ta kulla alaka a tsakanin su.1 Sun shafe wajen awa daya a hakan kamun husna ta tashi daga bayan shi. Ta daukama bacci yake taga ya motsa. Bayanshi tadan bubbuga muryarta a dishe tace. Ka tashi. Bai mata musu ba ya dago daga jikinta ya sauke mata idanuwanshi da suka kumbura. Abinka da farar fata. Fuskar tai ja. Kayanshi duk jini ne. "Muje gida kai wanka ka sake kaya" Ta fadi muryarta na rawa. Dan bata so hankalin shi ya dawo jikinshi yaga jinin dan uwansa. Girgiza mata kai yai alamar a.a.Dan gani yake yana tafiya daga asibitin Nas mutuwa zaiyi. "Ina wayarka" Ta bukata. Hannunshi yasa a aljihunshi ya dauko wayar ya mika mata. "Wazan kira ya dauko maka wasu kayan?"Ta tambaya. Karbar wayar yai ya lalubo lambar kamala. Muryarshi dakyar take fita yagaya masa ya kawo masa kaya. Yasa a shiga dakin husna ma a dauko mata a hado musu da kafet din sallah. Mintina wajen Ashirin tsakani kamala ya shigo dan saida aka kira prince ishaq sannan suka barshi ya wuto. Yana kawo musu. * Wani kofa ya bude kusa da dakin da Nas yake ciki. Kujeru ne da wani gadon a ciki. Sai kofa ta glass datai connecting zuwa dakin da Nas yake ciki. Nan yabar husna zaune tana kallon yanda gaba daya jikin Nas yake jone da wasu na.urori. Addu.a ta shiga karantowa tana masa fatan samun sauki. Kayan jikinshi kawai ya cire ya ajiye su nan kasa cikin toilet din ya sakar ma kanshi shower. Jin shi yake wani sama sama. Haka ya saka kayan da aka kawo masa ya fito. Kallon shi husna tai. Yana tsaye gefe duk da a hargitse yake yayi kyau cikin black jeans da riga fara. Gashin a harmitse ga suma yana da ita baka duk tai coil. Tashi husna tai ta karasa inda yake. Saman goshin shi da gefen fuskar shi jini ne. Ruwa ya jika shi ya zama kaman lokacin ya goga. "Me kai hakan?" Ta tambaye shi. Idanuwan nan ya zuba mata kaman bazai amsa ba sannan yace. "Wanka" Hannu takai zata goge masa jinin dake fuskar shi ya kauce fuskar shi. "Bana son gaddama" Ta fadi cikin yanayin muryar dayakan mata amfani dashi wasu lokuttan. Ita kanta mamakin yanda take son kula dashi take yi. Dan yau ya zame mata kaman wani yaro karami da yake matukar bukatar kulawa. Kallonta kawai yake dan a yanayin da yake ji kwakwalwar shi bata da lokacin tunani. STORY CONTINUES BELOW Hannun shi husna ta kama taja shi zuwa toilet din. Bai mata musu ba ya bita. Towel din dake ajiye sabo fil cikin leda ta bude. Ta jika da ruwa ta soma goge masa fuska dashi. Rufe idanuwanshi kawai yai yana jinta. A gefe daya kuma yana fata da addu.ar samun sauki wa Nas. Hannuwanta sun soma gajiya saboda ya mata tsaho da yawa. Sanda ta gama goge masa fuskar tsaf har wani nishin wahala take. Jin ta kama hannunshi yasa shi bude idanuwanshi. Janshi tai takai wajen kujerar. "Zauna to in fito" Ta bukata. Wani kasalallen kallo yai mata yace. "I am not a kid husna....." Wani guntun murmushi tai masa ta juya zuwa toilet din. Alkyabbar dake jikinta ta cire ta rataye. Kayan daya ajiye ta saka cikin wani bucket dake gefe ta cika shi da ruwa. Sabulun data gani ta fasa ta soma wanke su. Saidai sun rigada sunyi stain. Haka ta wanke iya yinta ta dauraye ta rataye su. Alkyabbar ta mayar ta fito ta zauna gefen shi. Kanshi ya kwantar a kafadar husna. Muryar shi can nesa yace mata. "Ina jin tsoro sosai" Cikin sanyin murya tace masa "komai zaiyi dai dai in shaa Allah.Babu abinda zai same shi." Muryarsa can qasa yace "inajin tsoro sosai husna sunyi sanadin rabani da huddy. Bansan me zancewa su umma ba" Sai lokacin ta kalli fuskarsa. Abinda tagani ta tabbatar ba zata taba mantashi ba har qarshen rayuwarta. Saita samu kanta da sa hannu ta taba fuskarsa. Tana son da duk wani abu da take dashi ta nuna masa komai zaiyi dai dai. Idanuwansa dauke da nisantacciyar damuwa. Tun ba yanzun ba husna ta kasance mai tausayi ko ga dabbobi ballantana kuma en adam. Hankalin prince ishaq ya koma can wani waje wani lokaci. * Riqe yake da hannun huddy suna jiran ambulance tazo ga mutane da suka dabaibaye su. Duk ciwukan da suke jikinshi basu dame shi ba. Huddyn sa yake ji ita kadaice damuwarsa. Duk wani kokari da zai iya ta fannin aikin shi a banza yake saboda baida kayan aiki. Ciwon dake gefen wuyanta yanata zubar jini. Rigar dake jikinshi ya cire dagashi sai singlet. Ya danne mata wajen a rikice yake fadin. "Stay with me huddy. Eyes open. Karki kulle su" "Yaya" ta fadi cikin murya mai dauke da ciwon da takeji. "Huddy dan Allah kiyi shiru karkice komai sannu yanzun taimako zaizo" Yake fada yana tarbe hawayen dake son zubo masa. Bata saurare shi ba tace "yaya karka barsu su sake dauke mana komai. Karku bar musu mulkin da basu cancanta dashi ba........" Tari ya sarqeta wanda tun tanayi harta soma na jini. Hankalinsa ya qara tashi ya tallabota jikinsa "huddy don't give up on me please ki taimaka" Murmushi tai masa "I love you yaya" "Na sani huddy nima ina sonki da yawa dan Allah karki barni." Baiga amfanin karatun shi ba a yanzun. Saboda bashida abinda zai taimaka mata dashi. "Damn....." Ya rasa inda zaisa ranshi yaji dadi. Hannunta ta dago wanda da alamun fuskarta ba matuqar dauriya taiba don azabar da take ciki. Ta taba kuncinsa a hankali tace "karka mantani. Ka zama cikin farin ciki yaya kamin alqawari" Yanzun kam hawaye ne suke zuba a idanuwansa rabon shi da hakan harya manta. "Na miki huddy na maki alqawari. Murmushi tai "La ilaha Ilallah........." Ta karasa muryarta na sarkewa.Lumshe idanuwanta tayi sannan komai ya tsaya cik! Ganin yanayin fuskar shi yasa husna girgiza shi ta dawo dashi daga dogon tunanin da yake yi.+ Dafe kanshi yai cikin hannuwanshi yana maida numfashi da sauri da sauri. Wayar shi ya dauko. Baisan me zaice ma su mumyn Nas ba. Husna ya kalla idanuwanshi bayyane da duk tsoron da yake ji muryarshi na rawa yace mata. "I don't know what to tell them, mumyn nas ta dauka zan kula dashi........" Kasa karasawa yai ya dafe kanshi kawai yana jin kaman ace kasa ta bude ya shige ya huta da wannan nauyin da yake kanshi. Husna bata san me zatace masa ba ko kuma taya zata rage masa abinda yake ji. Wayarshi ta soma ringing. Ya duba umman shice. Kai ya shiga girgizawa kaman tana ganin shi. Hakan yasa husna duba wayar ta ga wayake kira. Dagawa tai ta mika masa. "Kai mata magana kawai. You can do this" Jikinshi babu wani kwari ya kara wayar a kunnen shi yai shiru. "Babana kana lafiya?" Umman ta fada da rauni a muryarta. Sai yaji ya samu wani dan karfi kadan jin muryarta. Cikin karfin hali yace. "Mungode ma Allah umma...... Mumy fa?" Yanajin ajiyar zuciyar data sauke sannan tace. "Tun dazun kamala ya fada mana abinda ya faru. Mai martaba yace adan dagata tukunna muzo saboda yanayin tsaro. Ita tace tunda kana tare da Nas tabar ma Allah komai" Lumshe idanuwanshi yai yanajin kaman mumyn Nas a gabanshi tai maganar. Yana kuma jin nauyin girman da ta dora masa. "Allah yasa umma. Kuyita addu.a shi kadai Nas yake bukata a yanzun...... " Yanda yai maganar ne yasa tace masa. "Ya Naseer din?" Yasan ma.anar tambayarta saboda yajita a muryarta. Bataso kai tsaye ta tambaye shi idan su saka rai da tashin Nas ko kuma su soma shiryama zuciyarsu hakuri dashi. "Umma zan kiraki in an sami wani ci gaba" Ya fadi yanajin yanda ta furta. "Ya Allah.... " Kamun ya kashe wayar. Dan yana tsoron tambayar datai masa. Tun da suka shigo asibitin nan yake kokawa da zuciyarshi kan wannan tambayar. Jiyai cikinshi ya wani kulle ya gyara zaman shi ya dora kanshi a cinyar husna yai shiru kawai. Kyale shi tai. Tunda batada hanyar da zata rage masa abinda yake ji. Wacece ita da zata hana shi yin abinda yaji zai iya ya samu saukin zuciyar shi. * A asibitin sukai sallar isha.i. Duk yanda likitoci suka bashi magana kan cewa yanayin Nas a yanzun stable ne. Suna kuma addu.a da fatan ya tsaya haka a kuma samu ci gaba kin yarda yai. Da kanshi ya dudduba Nas din dabai masan duniyar dayake ba. Har lokacin bugun zuciyarshi ba wani karfi. Saidai yana dan karuwa da uku zuwa hudu kan dazun sai kuma ya sauka. Amman yaki yarda daya tafi yabar Nas din. Kallo daya zakai masa kasan cewar shi kanshi yana bukatar hutun amman yaki yarda ya tafi gida. STORY CONTINUES BELOW Husna ya kalla yace mata. "Idan kamala ya zo kawo blankets ki bishi ya mayar dake gida" Girgiza masa kai kawai tayi. Dan batajin zata matsa kafa daya ma batare dashi ba. Bawai dan bata taba kwana ita kadai sai yan aiki a wannan katon gidan ba. Saidan wani sabon tsoro daya shigeta da kuma son ta zauna kusa da prince ishaq din. Ga tausayin shi daya addabeta. Bazai iya wani surutu mai yawa ba. Dan haka ya kyale husnar. Shima yafi son ta zauna. Yana bukatar wanda zai kula dashi. Tunda ummar shi tayi masa nisa babu wadda zai juya ya kalla yadanji karfi karfi sai husnar. Dakin su suka bari suka shiga inda Nas din yake kasancewar dakin tankameme. Can gefe husna ta shimfida musu bargunan manya masu matukar laushi suka zauna shiru. * Nan inda husna take zaune bacci ya dauketa. Shi ya kamata ya kwantar da ita ya lillibe ta. Addu.o.in tsari ya tofa mata sannan ya koma ya zauna. A haka ya kwana kanshi hade da gwiwarshi. Da duk shigowar da wani likita zaiyi duba Nas tare zasu duba shi. Da asuba saida yai wanka yayo alwala yazo da niyyar tashin husna ya samu ta tashi. Toilet ta nufa itama wankan tai ta saka kayan da aka kawo mata jiya batai amfani dasu ba. Sanda ta fito prince ishaq harya idar da sallah hana zaune yana addu.o.i. Sallar tai itama. Taima Nas addu.ar samun sauki ta koma kan bargunan tai zamanta. Shima nan ya koma kusa da ita ya zauna. Saida taji cikinta na ihu ne ta tuna rabonsu da abinci tun na jiya da rana. Dayan dakin husna ta tashi ta shiga. Prince ishaq kam da ido yake binta. Kayayyakin ciye ciye da kamala ya kawo musu kiya ya zuba a fridge din wajen ta dibo. Fresh milk da snacks ta dibo masa fruits dan a yan kwanakin nan ta kula yana son su. Kome take da ido yake binta. Yana kallo ta miko masa fresh milk da burge. Kai ya girgiza mata dan tun jiya yake jinshi wani iri. Kallon wannan tarkacen ma jiyai amai yake ji. Kyale shi tai tadan samu taci burge guda daya da fresh milk. A hankali tace. "Kaci wani abu please. Ko fruit dinne" Kanshima ciwo yake masa. Bayason magana at all. Dan haka ya karbi apple din data bashi. Gutsura daya dakyar ya hadiye yana wani yatsine fuska. Kula tayi kaman jikinshi nadan kakkarwa. Kallon shi tai sosai. Idanuwanshi sun shige ciki sunyi wani kanana. "Are you okay?" Ta tambaya. Daya daga mata kai alamar eh, sai kuma ya gigiza mata kai alamar a.a dan jinshi yake wani irin sama sama. Apple din dake hannunshi taje karba. Taji wani zafi fiye da yanda takanji jikinshi. Da sauri takai hannu ta taba fuskarshi. Wani irin zazzabine rufe dashi. Ido ta zaro tace. "Baka da lafiya. You are burning up" "Lafiyata kalau" Ya fadi yana kauda kai gefe. "Baka da lafiya bara wanj doc ya shigo" Husna tace tana kallon shi. Batare daya kalli inda take ba yace. "Bana wani bukatar doc saboda lafiyata kalau" "Ka cika gardama" Ta bashi amsa. Kallonta yai cikin fuskata yace. "Kin cika son jan magana" "Bafa kada lafiya" Ta maimaita tana kallonshi cikin idanuwa wannan karin. Yatsina fuska yai a dake yace. "Bana son jan magana and bana bukatan doc" Shiru tai kawai. Ta kula ba wai saurararta zai ba. Dakyar ya iya mikewa saboda jirin dke kwasar shi dan ba karamar dauriya yake ba. "Ina zaka?" Ta tambaya. Baice mata komai ba ya wuce ya fita. Numfashi ta sauke. Batabi bayanshi ba. Yanda baison takura ta saka mishi ido kawai. * Allurar zazzabi akai masa data sake taimakawa wajen kara mishi jirin dayake yi. Da doc din yaga prince ishaq yaki saurarshi kan cewar kodai ya yarda ya kwanta asibiti ko kuma ya koma gida ya huta dan stress ya mishi yawa yasa shi biyo shi har dakin da Nas yake. Husna yaima magana yace prince ishaq din na bukatar hutu. "Ka kira azo a dauke mu kaje gida ka huta please" Ta bukata muryarta a tausashe. Girgiza mata kai yai hadi da fadin. "Ba inda zani" Dafe kai husna tai. Taurin kanshi ya soma gajiyar da ita. A nutse tace. "Nas bazai so kai masa haka ba. Zaiso ka zamana mai kwarin gwiwa yanda zaka kula dashi sosai. Ba ka yarda Allah bane mai bada lafiya?" Shiru yai kanshi a kasa yana saurarenta. Ganin hakan yasa husna cewa. "Duk zaman nan da muke bashi Nas yake bukata ba. Addu.a yake bukata. Please muje gida ka huta.... " A gajiye ta karasa maganar. Yana tsaye inda yake. Kyale shi tai kawai. Ga mamakinta waya taga ya zaro daga aljihunshi. Ya kira kamala. * Saida suka shiga mota prince ishaq ya kalleta na wasu yan mintina. Hannunta ya riko dayasata juyowa ta kalle shi. "Nagode. Nagode sosai da komai da kikai mana" Batace komai ba sai wani dan guntun murmushi datai masa. A haka har suka karasa gida. Kowa bangarensa ya nufa. Saida tai wanka sosai tai brush sannan tama tuna da wayarta. Falon kasa ta sauka nan tabarta kan kujera jiya. Ta dauka ta nufi dining. Irish ta dan ci da soyayyen kwai sannan ta koma sama. Key din wayar ta bude. Gabanta ya fadi. Har ga Allah ta manta da ammar a kwana dayan nan. Hakan ba karamun mamaki ya bata ba. Ya kirata har ba adadi. Ga messages da yawa. Ji tai bata bukatar wani sabon ciwon kan. Ba zata iya magana dashi ba. Text ta tura mishi ta fada masa kanin prince ishaq datake fada masa ne yai accident. Zata kirashi. Ko tsofaffin sakunan daya bar mata bata duba balle ta jira taga reply din dazai dawo mata dashi. Ta kashe wayar ta ajiye gefe. Bacci ya dauketa cike da mafarkin Nas da rayuwa irin tasu.

Post a Comment for "WATA BAKWAI CHAPTER 9"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...