Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA BAKWAI CHAPTER 6

WATA BAKWAI CHAPTER 6

- - Post a Comment
WATA BAKWAI CHAPTER 6
  Yanayin tsari na garin abuja ya burgeta matuqa.+ Zataso ace da ammar dintane sukazo dataji dadin zuwan. Bude musu mota akai. Tana fitowa takalli yanayin ginin gidan batasan "wow" ta subuce mata ba. Zagayawa tai dan zatonta zaa bude bayan motar ne su dauki kayansu. Ganin ta tsaya yasa shi fadin "Muje mana" "Zan dauki kayana ne" ta bukata tana masa kallon da yake fassara wannan wacce irin tambaya ce? Kallonta yai sosai kamun yace. "Muje za.a shigo maki dashi" Ganin ya wuce abinsa yasa tabi bayanshi Tsakiyar wani qayataccen falo suka isa. "Za.a nuna miki bangarenki. Inkina buqatar wani abu hadiman gidan zasuyi miki" Ya fada mata. Bai jira amsarta ba ya wuce. Wata ce tazo ta rakata har bangarenta. Wajen ya hadu dan duk tsanar mammalakin gidan datai bai sa yaqi burgeta ba. Wanka tayi dan tagaji sosai tunda bata samu tsarki ba balle tace zatai sallah. Ta duba wayarta ammar bai dawo online ba har lokacin. Ta soma kewarshi. Tunawa tai ashe fa kausar na abuja. Wani murmushi ya qwace mata. Wayarta ta dauka ta kirata. Bayan sun gama gaisawa tace "Ke er uwa ina abuja fa" "Wooo bani address zan shigo gobe in shaa Allahu" kausar ta fadi cike da farin ciki. "Ta dora da meye sirrin? Rabon da inji muryarki haka harna manta husna." Dariya tai tace "kausar kin cika zolaya akwai labari saikin shigo ke dai" "Ba damuwa kimin text din address din fa karki manta." "Zan miki yanzun in shaa Allah." Husna ta fadi. "Tam ina jira" kausar ta ce sukai sallama. Ajiyar zuciya ta sauke. Yunwa takeji dan haka ta yanke shawarar sauka qasa ta tambayi address din gidan nan ta tura ma kausar. Daya daga cikin hadiman gidan ta tambaya suka fada mata. Zuwa tai inda aka shirya musu abinci taci wanda yai mata. Bataga natacce ba baya gabanta kuma. Ba.a shigo mata da akwatinta ba tun dazun dan kayan jikinta ta mayar. Ta tsani yanda kamshin nataccen nan yake manne dasu. Sama ta koma tai kwanciyarta dan ammar ya dawo online. Hira sukai tayi bata sake fitowa ba har qarfe goma na dare. Tasan Ammar ya tafi kallon ball yace mata suna da wasa. Ko ya dawo ma ita dai bai kirata ba kuma bata neme shi ba. Duk da gajiyar dake jikinta baisa bacci yazo mata ba. Fitowa tai daga dakin baccin zuwa qayataccen falon dake saman nasu. T.V ta kunna. Channel din yana kan star movies. Bata canza ba dan tasan suna saka films masu kyau sosai. Wani horror ne mai tashin hankali. A tsorace take kallon amman ta kasa tashi ta sauya tashar ko ta kashe. Lokacin da suka gama sha biyu saura. Sai yanzun take dana sanin kashe qwayayen wajen da tayi dan ta dauka ba zata ma fito ba. Ga gidan yayi wani shiru musamman data kashe t.v din. Sanyin AC bai hanata jin zufa ba. A hankali take tafiya zuwa dakinta. Wani abu taji taci karo dashi ta saki wata irin giggitacciyar qara. * Sai juyi yake kan tanqamemen gadonsa ya kasa bacci. Dan yanzun wahala yake masa tunani baya barinsa bacci. Nas ya kira yaji lafiyarsa sukaita hira. Yana fada masa ya shirya fa dan suprised din da zai masa ya kusa. Dariya yai duk da sautinta ne kawai yakan fita ya manta yanda launinta yake a xuci. Sukai sallama. Fridge din dakinsa ya bude duk apple din daya samu ciki ya cinye shi dan yau babu komai cikinsa sai shi. Fitowa yai ya dibi wasu dan dare yayi balle ya sa akawo masa. Mamaki ya cika shi ganin duk an kashe wutacen lungun. Yama manta natacciya tana rayuwarsa ma gabaki daya balle kuma a gidan. Tafiya yake dan ya lalubo switch din ya kunna. Yaji wani abu ya kawo masa karo kuma an saki qara. Tamkar wanda aka dauka aka watsa duniyar tunani zuciyarsa ta budo masa wani yanayi: **** **** Ta baya ya lallabo ganin bataji tafiyarsa ba. A hankali yasa hannu yaja jelar kitsonta guda daya data sauka har gadon bayanta. Wata qara ta saki a razane hadi da juyowa. Shi kansa ta bashi tsoron riqeta yai dam a faffadan qirjinsa yana shafa bayanta. "Huddyna kin cika tsoro daga tsokana." Cikin tabararta tace "Yayana kaban tsoro sosai." * Iya tsoro kam husna ta tsorata numfashinta har barazanar daukewa yake yi. Rungumeta taji anyi cikin wani faffadan qirji. Qamshinsa taji tasan shine. Natacce ne ya tsoratata haka. Kanta yake shafawa "huddyna kin cika tsoro daga tsokana." Ya fada batare daya sani ba. "Huddy?" Ta nanata a zuciyarta. "Ammar" zuciyarta ta sake furta mata. Idanuwansa a rufe suke yanajin duminta dan singlet ce kawai a jikinsa da boxers. Sai dai akwai wani abu daya banbanta. Wannan ba kalar turaren huddy bane. Jin an ture shi yasa zuciyarsa ta sake shi daga duniyar tunanin data watsa shi. "Ya salam" ya furta dai-dai lokacin data kunna hasken wajen. Idanunta ta sauke cikin nashi. Da gudy tabar wajen. Dafe kai yai? Why? Meyasa zuciyarsa take masa haka ne? Saboda me zata dinga kaishi irin wannan wajajen dai-dai lokuttan da qaddara zata jeho masa natacciyar yarinyar nan. Jikinsa ya hada da nata duk da yana qaryata cewar yaji wani abu. Amman abinda ya qona masa rai ba damuwa dayai da natacciya ba son ganinsa da batayi. Sai kace wani dodo ko wanda yake da abin qi a jikinsa. Jibi yanzun tana kunna hasken wajen suka hada ido sai tayi tamkar wadda tai kuskuren kallonshi tabar wajen. Fasa daukar apple din yai ya koma daki ya kwata kawai. Husna kam dakinta ta koma.+ Kuka take sosai. Ya zatai ma ammar haka? Wannan cin amana ne. Tunda tasan natacce ne. Kamshin shi kawai taji tasan shine. Bata manta yanayin qamshinsa ba tabari ya rungumeta a qirjinsa. Yanayin rungumar dayai mata batasan ya zata fassara shi ba. Tanajin sawun hannuwanshi akan bayanta har yanzun. Tana jin dumin jikinsa gauraye da nata. Da sauri ta miqe ta shiga toilet. Bathtub ta shiga bayan ta cika shi da ruwa. Soso da sabulu tasa ta durje ko ina na jikinta har ya soma radadi ko zata wanke abinda take ji. Sai dai ga mamakinta yanayine daya samu waje daram cikin zuciyarta bawai iya jikinta bane. Da ace zuciyar nan zata ciru. Data fito da ita ta wanke ta tas. Ta goge ko menene ya dasa mata a ciki. Saboda bata son shi sam. Tai kuka harta gaji. Tunawa tai wayarta a silent take da sauri ta janyota. Missed calls na ammar har 26. Text messages guda 10. Maganar dayai mata a whatsapp 53. Tana cikin dubawane kiransa ya sake shigowa. Da sauri ta dauka "Nawan" Wani nannauyan numfashi ya sauke da har taji ta cikin wayar. "Ina kika shiga haka?" Ta tsani kanta ta tsani qaryar da bakinta yake shirin furta masa. "Bacci ne ya daukeni nawan wayar na silent yanzun na farka naga kana kira." Ta karasa maganar cikin sanyin murya. "Wlh naji tsoro sosai babyna babu tunanin da baizomin ba. Gashi kincemin kin bishi abuja. Husna mutuwa zanyi idan na rasa ki. In ya tabamin ke zuciyata fashewa zatayi wlh kishi kasheni zai husna" Ya qarasa muryarsa na rawa. Hawayen dake bin fuskarta ta goge cike da tausaya mishi. Dayasan abinda ta bari ya faru yanzun........ Da sauri tace "kana karyamin zuciya in kana tunanin zan hada shimfida da mutumin dana tsana. Ni taka ce nawan. Kai kadai bazan taba hada maka jiki da wani ba gara an dauki gawata da hakan ya faru." "Hmm husna ba zaki gane me zuciyata takeji ba inba kashe auren nan kikayi ba naga kin zama tawa tunani kawai zai iya kassarani." Sun jima suna waya kamin suyi sallama. Washe gari tana yin sallar asuba ta koma bacci danko wanka batai ba. Baccin ne a idanuwanta sosai. Wayar kausar ta tasheta wajen goma da yan mintina. Ta fada mata tana hanya. Wanka tayi ta shirya kanta cikin doguwar riga simple ta sakko qasa ta zauna. Hadiman gidan ta fadama tana da baquwa su shirya mata wajen cin abinci na falon sama. Kausar na sallama ta tashi da gudu taje ta ruqunqumeta tana tsalle tsalle. Dariya take sosai "yau mun banu husna kaman wata yarinya." Dai-dai lokacin da prince ishaq ya sakko daga benen. Kausar ta ganshi ita kam husna tsalle tsallenta take yi. * Tunda ya fara sakkowa yake jin dariya da tsalle tsallen husna. Kallonsu yake da mamaki a tsahon ganin da yake mata ko murmushinta bai taba gani ba. Kullum fuskarta kaman zata saka mishi kuka. Sai kuma hawayen tan nan da baya so. Inta fara zubo dasu har wani ciwon kai yake shirin kamashi saboda dagula masa lissafi take. Sai yau tana ta dariya. Baisan murmushi ya qwace masa ba ma. Sai yaga ta qara kyau.1 Ohh ya fada a zuciyarsa yarinyar da ta tsane shi ya zauna yana ganin ta qara kyau kenan ma ya lura tana dashi. Kauda kansa yai. Muryar kausar qasa qasa tace "dan ubanki ki nutsu." "Wai me kike kallo husna ta fadi tana juya." Lokaci daya fara.ar da take fuskarta ta dauke. Tsikar jikinta ta wani tashi duk da ta janye idanuwanta daga fuskarsa zuwa qirjinsa. Yanayin dumin qirjin ya fado mata a zuciya ta girgiza kai tamkar tana so ta batar da abin ta hakan. Hannun kausar ta damqa da niyyar janta suhau sama ganin natacce ya nufo inda suke. Amman taqi. Cikin qasaita ya iso inda suke. Murmushi ya dora a fuskarsa. Cike da girmamawa kausar tace masa "barka da warhaka." "Barkanki" ya amsa yana dorawa da. "Mungode da ziyara" Murmushi kausar tayi tace. "Bakomai Allah ya kara girma" Kai kawai ya daga mata ya wuce abin shi. Husna ta jata suka wuce suma. Kan hanya taketa faman masifa "meye na wani gaishe dashi harda girmamawa. Ai wlh kin bani haushi ba kadan ba.A hakan ma sai uban yangar tsiya" Shiru kausar tai mata saida suka sami waje suka zauna sannan tace "husna kinsan ko waye shi din? Naga alama baki sani ba koh?" "Kinga nifa baya gabana asalima ke nake jira kizo kiban shawarar yanda zan kashe auren nan. Ammar ya dawo." Sakin baki kausar tai tana kallonta. "Ba canai ki tsaya kina min wannan kallon kaman na samu haukaba nace miki ammar ya dawo yanzun haka ko yau da safe munyi waya dashi." Husna ta fada tana kallon kausar cikin fuska. Girgizata kausar tai tace "Husna kina da hankali a jikinki kuwa? Kin manta kalar tashin hankali da muka shigane? Tabbas kin manta da har kike son mayar damu." Ganin tayi shiru tana wani kumbura fuska yasa kausar ci gaba da fadin "da aurenki kike waya da gardi???" Cikin bacin rai husna tace "karki sake kiranshi da gardi. Bana qaunar mutumin nan ko na qaramin lokaci. Idan na zauna dashi son ammar kasheni zaiyi. Na tsane shi kausar dole ne na rabu dashi na auri wanda zuciyata take muradi." Husna ta karasa tana goge hawayen da suka taru a idanuwanta. Girgiza kai kausar take cikin tashin hankali: "kin samu tabin kwakwalwa. Kuma kina gab da saka ammar da duk masu sonshi cikin tashin hankali da rudu. Husna kinsan wa kike aure?" Ta qarasa maganar cikin rawar murya. A zuciya husna tace wai natacce din nan waye shine? Fine a yanzun tasan yanada alaka da sarauta ko dan cikin gidansu data gani. Saidai bai dameta ba. Tunaninta bai taba je mata wajem bama. A fili kuwa girgiza mata kai tayi alamar a.a. "Prince ishaq" kausar ta fadi tana ci gaba, "dan sarki kabeer. Wanda yake jiran gadon mulkin garin kano.Husna zaki jefa rayuwar ammar cikin garari inhar ya gane abinda kike. Meyasa ba zaki haqura da ammar bane ki zauna gidan aurenki? Ba kowacce qaddara ake sauyawa ba." Wata irin dokawa zuciyarta take. Idanuwanta cike taf da hawaye tace "kausar ki taimakamin wlh bazan iya haqura da ammar ba. Nayi qoqarin hakan na kasa." Hannunta ta riqe tana fadin "husna babu yanda zamuyi da Hukuncin Ubangiji, ammar ba mijinki bane." Fisge hannunta tai a zuci tana fadin babu wanda ya isa ya rabani da ammar ko sarkin ne ma da kanshi ballantana dansa.Saina kashe auren nan ko ta yaya. A fili kuwa ta goge fuskarta tace Allah yai mana jagora mubar maganar nan kausar sai wani lokacin. Tashi muje ko breakfast banyi ba. "Hmm mudai je nikam a qoshe nake." * Kausar ta wuni gidan. Da zata tafi ma ta sake ma husna kashe di. "Kinga ki rufa mana asiri husna. Har yanzun su abba basu gama hucewa dake ba. Karki jawo wata sabuwar matsalar" Fuska babu walwala husna tace. "Nafa jiki da kyau. Yanzun yaushe zaki kara dawowa? Ko nice zanzo?" Fito da idanuwa kausar tai tace. "Rufamun asiri. Ni yar ubana. Duka satinki nawa da aure daza ki soma yawo. Zan dawo in shaa Allah" Dariya husna tai tace. "Yasan da hakan ya jajibo ni har abuja" Girgiza kai kawai kausar tai ta wuce tana fadin. "Sai munyi waya" * Falon kasa tai zamanta tana ta kallo. Kamun daga bisani ammar yazo online su sha hirarsu. ** Satinsu uku kenan abuja. Husna zata iya cewa tun ranar da sukai karo da natacce. Magana bata sake hadasu ba. Zasu hadu ko a falon sama. Ko na kasa tana zaune. Ko wajen cin abinci. Tun satun da sukazo sau uku a haduwar da sukai zai taba fuskarta da goshinta yaji ko da zazzabi. Badai magana yake mata ba. Wasu lokuttan idan yazo ya ganta a zaune babban falo shima zai zauna. Sai dai taji idanuwansa na mata yawo alamar yana kallonta. * Prince ishaq kam hidimomin shi kawai yake. Yanajin dadin yanda natacciyar can bata damun shi. Bata zame masa kaya ba kaman yanda yake zato. Asalima ya sake kula haduwarsu sai dole. Kawai dai bashida lokacin batawa ne akanta a yanzun. Amman daya dan samu time dole in yana waje ta dinga kallon shi indai tana son zaman lafiya. Badon ya damu da ita bane. Aa kawai ya damu da ta girmama shine bai kuma son dalili ba.

Post a Comment for "WATA BAKWAI CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...