Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA BAKWAI CHAPTER 5

WATA BAKWAI CHAPTER 5

- - Post a Comment
WATA BAKWAI CHAPTER 5
Da tunani barkatai a zuciyarshi harya tashi da safe. Tun wajen karfe bakwai daya koma bacci bai tashi ba sai yanzun nan. Yana duba agogo har sha daya tayi. Dakyar ya rabu da katifar yaje yai wanka. Ya shirya cikin wani kaya na karan miski brown. Yayi kyau matuka. Har ya wuce zaiyi dining room din ya tuna da yar mutane da take karkashin kulawar sa bata da lafiya fa. Yaja wani gajeran tsaki sam sam baya son matsala a rayuwar shi. Bangaren husna ya wuce yaga ko taji sauki. Dan bai niyyar daga tafiyar shi ba saboda ita. Yanda aka lika masa aurenta haka aka lika masa tafiya abuja da ita. * Husna kam dayake ba sallah take ba. Tunda ta tashi tai wanka ta shirya cikin wata doguwar riga simple. Suka sha wayarsu da ammar harya shirya zuwa aiki. Dan ya ce mata ya samu aiki a wani gidan mai. Suna gama wayar ta kwanta shiru abinda ya faru tsakaninta da prince ishaq yana mata yawo. Sai taji kaman tanajin kam shi har yanzun kan gadonta. Taja tsaki. Bakin natacce ta fada a ranta. Tanata tunani har bacci ya dauketa. * Kwan kwasawa yai yaji shiru haka yasa shi turawa a hankali yaganta kwance tana bacci. Babu karya tana da kyau. Shi kyan ta baya gabanshi. Gefen gadon ya karasa ya zauna. Ya duba magungunan daya ajiye gefe suna nan yanda suke bata sha ko daya ba. "Yarinyar nan ta rainani" ya fadi a hankali. Sai daya saka aka kawo plantain da fried eggs sannan. Ba inda zai kwashi kaya ya tafi dashi yake fada ma kansa. Hannu yasa ya shafi gefen fuskarta. Da sauri ta bude ido ta sauke shi a fuskarsa. Ganin shi yasa ta saurin tashi zaune tana matsawa. Har haushin yanda take shakkar shi ta ba kanta. Ga jarababben kamshin shi har ya gauraye dakin. Hannu yakai zai sake tabata ta kara matsawa. Bai kobi takanta ba. Ya matsa kusa sosai yaka UK hannu ya taba fuskarta ta rufe idanuwa. Ya taba wuyanta na minti daya yaji akwai sauran zazzabi. Plantain din ya ajiye mata kan cinya da cokali a ciki yace mata. "eat ki sha maganinki" Ya wani hade rai yana kallonta kawai. Husna ta kule. Bata son yana mata shisshigi. Inba naci ba me zai kawo shi dakinta. Girgiza masa kai tayi alamar bata ci. "Ki ci ki sha magani ko kuma ki zauna a dawo ai maki allura. I can't take you ko ina da wannan zazzabin" Ya ce a gajiye. Kaman maganar kawai ta cinye duk karfin jikin shi. A hankali ta dauki plate din. Turawa kawai take badan bakinta nada wani appetite. Dan gara komai da allura. Banda auren natacce babu abinda ta tsana sama da allura.1 Jitai inta kara amai zatai. Ta ture plate din. Matsawa tai ta dauko magungunan. Ta duba yanda zata sha su. Ta ballo saidai ba ruwa kusa. Ga mamakinta prince ishaq ya tashi yaje inda fridge din dakin yake ya dauko mata swan da cup dayake a jiye kan fridge din. STORY CONTINUES BELOW Ya zuba ya mika mata. Saita tsinci kanta da danjin nauyin shi. Ta karba cikin sanyin murya tace. "Nagode" Kai kawai yadan daga mata yanda yakanyi ma wasu cikin hadiman gidan in sun gaishe dashi. Saida yaga ta shanye magungunan. Tana ta yatsina fuska yace mata. "Kina jin ciwon kai?" Ta girgiza kanta. "Dizziness fa? Ko amai?" Ta sake girgiza kai dan ya soma isarta. Shi ba likita ba ya tsare da tambayoyi. Mikewa yai ya karasa daf da ita. Hannu yakai ya sake tabawa yaji yanayin zazzabin. Ta janye fuskarta.1 Wani abu ya tsaya mishi a wuya. Ya rasa dame yarinyar nan take ji. Baya son ta zame masa kayane dan suna setting kafarsu abuja bashi da lokacin wannan shirmen. Share ta yai ya matsa ya taba kumatunta. Ganin yanda bata so ne yasa shi dora hannun kan wuyanta. Yabarshi akai fiye da yanda yake bukata dan kawai ya takurata. Tadai ki kallon shi harya dauke ya fita. Zanin gado husna ta janyo ta goge kumatunta inda ya taba ta kuma goge wuyanta. Amman da yake kaman yanda Allah ya zuba masa naci haka ma duk abinda yabar mata ajiki yake da naci.1 Yaki fita sam. Ta ki daina jin dumin hannunshi da yanda tsikar jikinta ke tashi. A fusace ta sakko daga kan gadon ta je wajen dressing mirror dinta. Duk wani collection na turare da take dashi saida ta feshe dakin dashi. Jin turarukanta sunki korar kamshin nataccen nan yasata bude akwati nan da kayan kwalliya ne kawai a ciki da turaruka lefenta datai ma kanta alkawarin ba zata taba ba. Tunda bata son mai kayan ba kuma tason abin hannun shi. Kala uku ta bude daka gansu kasan masu bala.in tsada ne. Ta feshe dakin. Sannan taji yamata kamshi na daban. Tana komawa kan gado ta kwanta ammar na kiranta. "Assalamu alaikum tawan" Ya fada tanajin fara.arshi cikin muryarshi. Ta amsa da murmushi a fuskar ta. Yanda yaji muryarta ya sashi tambayarta lafiya kuwa. Tace. "Nawan zazzabi nake danyi fa" A rikice ya shiga jero mata tambayoyi. "Ya Rabb. Yanzun ya jikin? Kinsha magani? Ko sai kinje asibiti? Husna ko....... " Dariya tai ta katse shi da fadin. "Ya kira likita an dubani har gida. Yanzun ma yazo yaban magani ya fita" Lokaci daya muryar ammar ta sauya. Can kasan makoshi yace. "Husna karki soma son shi. Karya tabamun ke, husna in baki kashe auren nan ba wallahi zan iya mutuwa. Ki tausayamun"1 Muryarta a tausashe tace. "Relax nawan. Ka yarda dani mana. Ni bansan meyasa ya aureni bama. Wallahi bai damu dani ba. Bai taba yunkurin tabani ba." Wani dumi taji inda ya tabata dazun tamkar waje na neman karyata zancenta. Ta kuma tuno yanda ya riketa da za.ai mata allura. Duk da dumin zazzabin da take ji bai hanata tuno nashi dumin ba. Haka ta samu ta kwantarma da ammar hankali da sake jaddada masa alkawurran da bata san yanda za.ai ta cika shi ba. * Kan kujerar falon shi ya zauna yai shiru. Kanshi ma ciwo yake. Yana so ya hada kayan tafiyar shi gobe duk da yanada kaya acan. Amman akwai yan abubuwan dazai hada saboda yanayin tsaro. Ko da kwana hotel zai kamasu ba komai na can din yake son amfani dashi ba dul da cewar sababbi ne. Wani lokaci yakan godewa halayya irin ta ummarshi da duk matsayinsu tai kokarin koya musu yin abubuwa da dama dakansu. Takance kar matsayin da Allah yai musu ya saka su girman kai ko wulakanta na kasa dasu. Su dauka cewa matsayinsu wani abune mai nauyin gaske da Allah zai musu tambaya akan yanda suka rike shi. Duk da haka kamala ya kira dan ya yarda dashi sosai. Shi yasa ya hada mishi duk abinda yake bukata. Ya kuma ce shine zai kaisu Abuja goben in shaa Allah. Dan haka kawai yake son canji. A mota zasuyi tafiyar. Rabon shi dayai tafiyar fin awa daya a mota harya manta. Ya sanar da kamal baya son security saboda hakanma na janyo hankalin mutane akan su. Normal yake bukata ko da ta rana dayace. Yana son yayi abu kaman yanda kowa yake yi. Yana son ajiye prince ishaq a gefe yai abu a ishaq dinshi zallah. Tun wajen karfe tara ya gama shiryawa Sai dai baisan ko ita ta shiryaba ko bata shirya ba. Fitowa yai babban falo ya sami hadima daya dabai san sunanta ba don ba damuwa yai da hakan ba.+ Har qasa ta tsugunna kanta a sunkuye tace "fatan yarima ya tashi cikin qoshin lafiya?" Lafiya ya amsa a taqaice mulkin na motsa masa. Yana son ya tura a ce mata ta fito sai dai yana gudun zata iya fadar magana a gaban hadimansa. Baya qaunar yarfi da harkar yada girma duk da bawai son matsayin nasa na yanzun da na gaba yake ba. Da kansa ya taka zuwa bangaren ta ya nufi dakinta. A hankali ya qwanqwasa. * Husna kam tunda ta tashi taji jikinta babu zazzabi sam. Tadai yi wanka ne tasa aka kawo mata soyayyen dankali tadan ci. Tasha magungunanta dan bata da bukatar natacce yazo ya maimaita abinda yai jiya. Dan ta kula namiji ne shi da yake yin abinda yaso babu kuma wanda ya isa ya hana shi inya tashi. Chatting suke da ammar a whatsapp dan jiya da dare ya sata tai downloading sabo. Taji an kwankwasa kofar. A zatonta asabe ce ta dawo kwashe kayan data kawo dan haka tace "Shigo" Tura qofar yai tana kwance da wayarta a hannu ta dago. Saurin sadda kanta qasa tayi tana ci gaba da danna wayarta. Wannan nataccen nema sai dai ya gaji da tsayuwarsa a wajen ya shigo ko ya koma. Chatting din da take da ammar ya fiye mata komai na gidan nan. Shi kullum yaita fama da kaya kaman wani dan sarki. Duk da tsanarsa da tai baya hana mayyar zuciyarta ganin yayi kyau. "Ki fito mu tafi." Ya fada cikin wannan muryar tasa ta yanga. Sai lokacin ta tuna yaune yace mata zasu tafi abuja. A kasalance tace "ba zani ba aina fada maka" Wani abu yaji ya tsaya masa a wuya. Inda ba.ai masa umarnin ya tafi da itaba sai dai kawai taga bata ganinsa. Zuciyarsa ta dibe shi ta watsa wani lokaci can baya. **** **** "Yayana ni fa saina bika......yai dariyarsa "huddy kiyi haquri ba dadewa zanyi ba kwana uku kawai Kuma zamuyi waya" Ta sake goge hawayen dake bin fuskarta "bana so kanamin nisa." Sauke numfashi yai "huddy ke kinmin nisa ai" ya fadi a zuciyar tasa. A fili kuma yace "banson jan magana ko bacin rai. Umarni ne na cewar na tafi dake.Ki shirya nan da 15 minutes. I don't want to drag you myself, don't tempt me " Ganin bata da niyyar cewa komai yasa shi ficewa. Ita yanzun kam me zai bata mata rai bayan tana manne da ammar a whatsapp....wuni suke hira ko yana office ma haka da dare suna manne yana rikitata da voice notes dinsa. Da batai niyyar shiryawa ba sai wata zuciyar tace yanzun in ma baki tashi ba dawowa zaiyi. Kuma ta tabbata tsaf zai aikata abinda ya fada. Maganar ma da take yi dashi lokacinta take bashi. Tashi tayi ta sake kayan jikinta. Wani karamun akwati ta dauka badan tasan menene a cikin shi ba. Gara ma ta bishi abuja din dan ya sake tabbatar da baya gabanta. Mayafi kawai ta dora kan kayan jikinta taja akwatinta zuwa falo...inda wata daga cikin masu aikin tai saurin zuwa ta karbar mata. Fita akai dashi. Natacce ne ya fito daga side dinsa sanye da alkyabba ruwan hanta mai cizawa da wata irin hula akansa. Bata so ta tsaya zuciarta ta misalta mata kyawunsa. "Ungo" ya fadi.....hannunsa ta kalla daya miqo mata batare data yarda ta kalli fuskarsa ba. Alkyabba ce mai kalar tasa sai dai wannan akwai ado na mata a jikinta. "Ki saka saboda zamu fara biyawa ta gida sannan mu wuce." Karba kawai tayi. Bata son magana mai tsaho na hadasu inba dole ba. Tanajin idanuwansa na binta har ta saka ba tare data kalle shi ba tace "muje" Gaba daya kamshinsa ne cike da alkyabbar jikinta. Ta kuma tsani yanda hancinta ke jin dadin kamshin. Gaba ya shiga ta bishi a baya har zuwa wajen motar (Range Rover) wata fara mai kyau. Bude musu akai ta shiga shima ya shiga baya. Har suka isa gidan babu wanda yacewa kowa komai. Ita tana ta chatting da ammar abinta. Dan haka bata kula da komai ba sai tsayuwar motar data ji. Aka zo aka bude musu qofa suka fito. Ya zo kusa da ita ya tsaya. "Na iya lokacin da zamuyi a cikin gidan nan kiyi pretending komai normal ne a tsakaninmu." Ya fada cikin muryar da takanji yaima yan aiki. Cike da mamaki ta kalle shi. Bata dai bashi amsa ba duk inda yai nan take binsa suna tafiya. Tana kallon yanda mutanen cikin gida suke tsugunnawa tun kamin ya qaraso inda suke suna gaishe dashi amman ko kallon arziqi balle taji ya amsa. "Ana gaishe dakai ko baka ji?" Ta buqata. Bai bata amsa ba.. Taji haushin kanta ma datai masa magana. Wani irin daki suka shiga da saita wuni a tsaye a wajen bata gama qarema kyawunsa kallo ba. Ya zauna kan daya daga cikin manyan kujerun dakin. "Ki zauna" ya furta a hankali yana nuna mata waje a kusa dashi. Bata musa ba ta zauna. Wata kyakkyawar mata ce magidanciya ta shigo dakin cikin shiga ta alfarma. Sai taga matar ta mata wani irin kwarjini. Kasa taga ya sakko ya tsugunna itama bata san lokacin databi yanda yai ba. Saida matar ta zauna tukunna ya gaishe da ita cike da girmamawa...itama gaishe tan tayi....da fara.a ta amsa musu sannan taga ya koma kan kujerar ya zauna...itama tayi hakan. "Babana an shirya kenan?" Ta buqata. Cikin tausasawar murya yace "yanzun zamu wuce nace saimun biyo ta nan mun gaishe dake." "Aikam ka kyauta sosai ba zaka je da ita taci wani abu ba kuma kudan zagaya ciki?" "Uhm uhm umma sai dai ko inmun dawo muna sauri ne kinsan ba jirgi zamu bi ba" ya fada yana miqewa.. Saita tsinci kanta da sake tsugunnawa tace mata mun tafi. Addu.a tai musu sosai. Kamun su kama hanya su fita. Motar suka koma. Daga su sai driver din. Tun dazun take mamakin yanda cikin motar yake. Ba ta inda driver din zaiga me sukeyi saboda akwai barrier a tsakaninsu. Hannu prince ishaq yakai ya taba goshinta. Ya sake taba kumatunta sanna ya koma cikin kujerar ya zauna sosai. Husna kam batai mamaki ba. Kadan da aikin wannan bakin nataccen. IPhone din shin ya dauko ya saka headphones yana sauraran wakokin larabci na Rashid Al Majeed.+ Ita kam husna suna hira ne da ammar sai dai idan network ya dauke ta tsaya saiya dawo. Can yace "Tawan me kike yine haka?? "Muna hanyar abuja" Ta bashi amsa. "Abuja???" Ya rubuto da alamar tambaya. Tasan mugun kishi irin na ammar koda yaushe saiya tambaya ko natacce yana da kyau tace masa mummuna ne shisa ta kara tsanarsa. Shirun dayaga tayine batai reply ba yasa yace "ke dawa zaku je abuja? Kuma me zaku yi?" "Nima ban saniba ammar haka yace mu tafi ta bashi amsa." Yafi mintina goma bai bata amsa ba sannan yace "husna dan Allah karki bari ya tabamin ke kar ki so shi....ki taimakamin ki kashe auren nan."2 Wasu hawaye taji zasu xubo na tausaya musu. Hannunta na rawa ta rubuta masa "yanda bana sonshi shima haka bazaimin komai ba...kayi haquri saina kashe auren nan munyi rayuwarmu." "Zanso kina kusa dani yanzun zanyi shirune ina kallon kyawun idanunki masu nutsar dani cikin wani yanayi." Ya rubuto. Ta sauke ajiyar zuciya,yama zata fara zaman aure da wani ba ammar dinta ba mai nuna mata soyayyarsa. Battery dinsa ne ya dauke. Don haka ta sauka akan whatsapp din tana nazarin yanayi na hanyar abuja dan bata taba zuwa ba. Jingina tai da kujerar. A hankali ta juya kanta ta kalli natacce. Ya lumshe idanuwan shi da alama bacci yake. Taja dan karamin tsaki a zuciyarta tana fadin bacci da headphones. Batasan me yasa take jin inta bar masa bata kyauta ba. Hannu tasa ta dauki wayar da take ajiye kan cinyarshi. Yana jinta saboda ba bacci yake yi ba. Ta dauki wayar tana swiping dayake ba password ta bude. Pause ta sakama wakar da yake ji ta ajiye masa wayar inda taganta. Bude idanuwansa yai ya juyo inda take, a kasalance yace. "Saboda me zaki tsayarmun da waka?" Shegen shisshigina mana ta fada a zuciyarta. A fili kuma shiru tai ta kyale shi. Dan bata da abinda zatace masa.2 Kunnawa yai ya sake komawa yanda yake. Itama shirun tai batama san sanda bacci ya dauke ta ba. Jiyai ta kwanto masa kan kafada. Ya bude idanuwanshi, daman yasan wannan natacciyar kaya zata bala.in zame masa. Kamata yai a hankali ya kwanto da ita kan cinyarshi dan yanayin yanda take yana ganin jikinta zai iya ciwo in ta jima a hakan. Kallonta yake da wani yanayiba zuciyar shi da baigane ba. Kawai kuma ya basar. Gajiya yai shima yaso ya zame kujerar yadan kwanta sai dai bayason motsa wannan natacciyar. Yanda bayason a tashe shi in yana bacci haka bayason ya tashi wani. Saman kafadarta ya dora hannayensa ya dora kanshi. Shima baccin ya dauke shi. * Husna tana bude idanuwanta kamshin shi ya cika kata hanci. Abu taji a kafadarta. Takuma ji dumi sosai inda take kwance. Sai lokacin ta kula da yanayin da suke. Kawai sai taji kasala ta saukar mata. Motsin datai ne ya sashi bude idanuwansa. Muryarshi da take a bude ta sake zama wata babba saboda baccin daya tashi. "Dagani to, tunda kin tashi" Ya fada. Lallai ma husna ta fada a ranta. Shima fa a jikinta yake kwance dan rainin hankali zaice ta wani daga shi. Ita bama tasan me take kan cinyarshi ba bayan alkawarin datai ma ammar dinta. A kufule tace. "Ka dagani tukunna" Murmushi ya kwace masa. Tashi yai daga kafadarta. Ya zuba mata idanuwansa da bata so saboda yanda suke saka ta ji. Gefe ta matsa ta wani daure fuska har taso ta bashi dariya ma. Kujerar ya saukar ya kishingida sosai ya koma baccin shi. Husna ma rakubewa tai can gefe ta koma bacci. Bata tashi ba sai da suka karasa cikin garin abuja. Ta glass din motar take kallo tana yaba kyawun

Post a Comment for "WATA BAKWAI CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...