WATA BAKWAI CHAPTER 16 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA BAKWAI CHAPTER 16

WATA BAKWAI CHAPTER 16

- - Post a Comment
WATA BAKWAI CHAPTER 16
  Satin su biyu kenan da dawowa daga abuja. Komai na tafiyar musu yanda ya kamata. Saidai prince ishaq baya zama. Sai ya wuni baya gida wanda husna ke bala.in kula dashi a yanzun. Dan ba zataima kanta karya ba. Ta fara damuwa dashi sosai da sosai. Balle data san masu son illata shin sunfi kusa dashi a kano kan abuja. Duk idan yai cikakkun awa biyu a waje bataji ya kirata ba ita zata neme shi taji ko lafiya. * Ta idar da sallar la.asar ta sake kiran prince ishaq wayar shi har lokacin bata shiga. Tun karfe biyu take nemanshi shiru haka. Ta nemi number din Nas shima a kashe. Ta koma dakin prince ishaq din ta kwanta. Gaba daya a tsorace take. Jitai ba zata iya ba ta fito babban falo ta zauna. Num din shi ta kara nema shiru. Tai rau rau da ido. Saboda bata san wa kuma zata kira taji ko lafiya ba. Ta yanke shawarar inhar magrib tayi zata fita akaita gidansu ta dubo. Ta mike kenan ta sake komawa sama yai sallama. Batasan lokacin data karasa inda yake ba da gudu ta fada jikinshi. Riketa yai yana fadin "Easy hussy....." Hawayen da take ta kokarin tarbewa ne taji sun zubo. Ya dagota daga jikin shi yana kallon fuskarta. "I am so sorry wallahi charge dina ya kare. Hankalina ba a kwance ba. I should have call......" Batace komai ba ya sake rungumeta tsam a kirjinshi yana jin wani abu game da ita daya girmi so yana kara shigarshi. Da ita a kusa dashi sai yake jin komai na masa sauki. "Kinci abinci?" Daidai lokacin dayai tambayar ne cikinta ya zabi yai wani kuuu alamar yunwa. Girgiza kai kawai yai ya kama hannunta suka hau sama zuwa bangaren shi. * Tana nan zaune ya fito wanka ya shirya. Suka sake sauka kasa zuwa dining din. Abinci take ci ita. Shikam tana kula da tun zamansu wasa kawai yake da cokalinsa cikin abincin. Abincin dake bakinta ta hadiye sannan ta kalle shi sosai tace. "Gentle what is wrong?" "Kici abincin ki karya huce" Ya fadi maimakon ya amsa mata tambayarta. Dakyar ta kara cokali biyu saboda ji tai abincin ya fita a ranta. Kallonta yai. Da gajiya hadi da damuwa a fuskarshi yace. "Kin koshi" "Na koshi" Ta amsa shi tana mikewa. Magrib sukaji ana kira. Ta kalle shi yace mata suhau sama kawai. Yai musu jam.i dan bayajin fitar ne kwata-kwata. Sai da suka idar da sallah suka gama addu.o.in da zasuyi. Ya juyo ya fuskance ta sosai yace. "Hussy ban dawo ba yau. Saboda muna asibiti da Nas..... " Yana ambaton sunan Nas taji gabanta ya wani fadi. Katse shi tai da fadin "Me ya same shi kuma? Bayaji sauki ba?" Hannunta ya riko yace. "Ki nutsu kiji ni okay? Just calm down" Kai take daga masa cikin kosawa yaci gaba da fadin. STORY CONTINUES BELOW "Tun rand muka dawo yake fama da ciwon kai sosai. Yana ma mumy korafin kanshi kaman ana hura wuta. Sunje asibiti sau hudu dawowarmu. Basu fadamin bane sai yau da abin yai girma" Ajiyar zuciya ya sauke kamun ya ci gaba da fadin. "Yana da wani ciwo cikin kanshi. Buguwane sosai. An bamu 100% tabbacin zai warke. Amman za ai masa aili a kasar india" Bama tasan hawaye sun zubo mata ba sai da taga ya matso kusa da ita sosai yasa hannuwanshi duka biyun ya goge mata fuska. Hannuwanshi tallabe da fuskarta yace. "He is going to be okay in shaa Allah. Ni dakaina naga file din binciken da sukai" Muryar ta can kasa tace. "Yaushe zaku tafi?" Dan husna kewarshi taji ta soma yi. Yanda take jinma ya danne damuwar Nas. Ganin yanda idanuwanta suka sake kawo ruwa ne yasa shi fadin. "Gobe in Allah ya kaimu da yamma. An gama arranging komai....... " Bata iya tace komai ba. Hannun shi ta cire daga fuskarta tana jingina bayanta da bango. Takai tsahon mintina biyar tana kokarin hadiye abinda ya tokare mata a wuya kamun tace. "Allah ya kaimu goben ya bashi lafiya and........ And..... " Kasa karasawa tayi saboda kukan dake shirin kwace mata. Kallonta yai yana dakuna fuska saboda bai san me yake bata mata rai banda damuwar Nas ba. Kokarin karantar fuskarta yake ba saiya tambaya ba. Ya kasa saida tace. "Ka kula da kanka sosai" "Husnaaa..... " Ya fadi da wani yanayi ya dora da. "Kin dauka zan tafi inbarki ne? Kwana talatin fa. Tare zamu tafi" Wani numfashi da batasan tana rike dashi ba ta saki. Duk da damuwar da yake ji bai hana shi sakin mata wani tattausan murmushi ba. Cikin sigar tsokana yace. "Hawayen missing dina ne nan aka zubdo?" Hannuwanta tasa ta rufe fuskarta saboda wata kunya takeji. Tun tana mamakin damuwarta akan shi harta daina. Prince ishaq dinne akwai shiga rai ba kadan ba. Yanayin kulawar shi da komai. Suna nan zaune shiru har akai isha.i. Ta mike dan ya sake jan su sallar isha.i sai taga ya nufi hanyar toilet. "Ina zakaje?" Ta bukata. "Alwala zan" Ya bata amsa a takaice. "Oh...... " Ta fadi da dariya a muryarta. Hakan ya sashi zaro idanuwan shi dan yagama gane me "Oh..." dinta take nufi. Fuskar shi datai wani ja take kallo. Batasan sanda dariya ta kwace mata ba. Gentle da tusa.2 Abin ne taji shi wani gingirin gin. Ga kunyar da tagani a fuskarshi ta sake bata dariya. Yai tsaye shiru yana kallonta. Bawai dan baya abinda take tunani bane. Yadaiji kunya ne kawai. Kuma taba tan dayaine ya karya masa alwala. Dakewa yai ya soma takawa inda take yana fadin. "Hussy ni kike ma dariya...." Matsawa take tasa hannuwanta tana kokarin tsayar dashi har yakaita bango. Hannuwan ya rike da duk nashi biyun ya matse ta da bangon sosai. Gaba dayanta a jikinshi take. Da kamshinsa daya cika mata hanci. Ya sunkuyo da kanshi saitin fuskarta. Kasa yai da murya sosai dai dai kunnenta yace. "Dariyar me kike?" Jikinta ya dauki dumi. Kafafuwanta na mata kashedin kasa daukar nauyinta. Sumba ya manna mata a fuska da wuyanta ta cikin hijab din dake sanye jikinta. Jiyai abin na neman fin karfinsa. A hankali ya janye jikinshi daga nata batare daya saki hannuwanta ba. Dan ya kula batada wadattacen karfi a jikinta. Daya zuwa goma yake kirgawa cikin kansa. Dan juriyarsa akan husna ta soma kadan. Shi kadai yasan abinda yake ji. Murya a dishe yace. "Wuce mu sake alwala" "Jeka fito tukunna.... " Ta fadi dakyar. Bai mata musu ba ya saki hannunta ya wuce. Bango tabi ta zauna kan gado tana maida numfashi. * Suna tashi da safe. Sukai sallar subh. Husna ta shiga wanka. Data fito wanka prince ishaq taga yana cire bedsheet. Abin ya bata mamaki. "Gentle da kanka. Da saika bari in fito ai. Ko kasa ai maka" Dagowa yai ya kalleta yace "Um um fa. Bamai shigarmun bedroom. Ni nake gyara abuna in share. Iyakacin yan aiki babban falo shima sai da dalili" Kallon shi kawai take cike da mamaki. Ta girgiza kai tace. "What kind of a prince are you?" Tambayarta ta bashi dariya. Shiru yai mata ya karasa cire bedsheet din. Ya dauka ya nufi fita da alamu zai bayar ne a wanke. Mai husna take shafawa sanda ya dawo. Dakin da suke sake kaya taga ya shiga ya fito da wani zanin gadon da rigunan pillow. Man da take shafawa ta ajiye. Ta mike tana fadin "Kawo kaje kai wankan ka" Ba tare daya kalle ta ba yace "Ki sa pillow case din kawai. I will make the bed" Sanin baya son gaddama ne yasa tai abinda yace din. Ta taya shi suka gyara gadon tsaf. Zaka rantse ba tafiya zasuyi yau ba. Hakan daya fado mata a raine yasata fadin. "Bazai yi kura ba kamun mu dawo?" Yadan yi jim sannan yace "Kamala zaizo asa ledoji a rufe komai" Kamun tace wani abu ya wuce ya shiga toilet. Fita tai ta nufi dakinta tana mamakin kalar rayuwarshi. Yana da jin kai amman nasa kala dabanne akan yanda take jin labarin yaran sarauta. * Ita ya bari ta hada musu kaya. Akwati daya suka dauka. Ta zuba duk wani muhimmin abu data san zasu bukata. Yan kana na kuma ta zuba cikin jakar hannunta. Karfe uku yai mata waya ya turo kamala yazo ya tafi da ita zuwa airport. * Nas take kallo a yanayin shi zaka rantse lafiyarshi kalau. Shi kadai yasan abinda yake ji. "Oh sannu Nas. Allah ya baka lafiya" Ta fadi tana jin duk ba dadi. "Antina amin. Yaya har wani murmushi yake. Nifa nace ya taho dake" Kwalo idanu husna tai cikin mamaki. Tace "Allah sarki kanina nagode" "Idan kun gama ku wuce mu shiga ciki" Prince ishaq ya fadi. Dan bashida lokacin tsokanarsun nan. Bayajin maganar. Karfe hudu jirginsu ya tashi zuw india. + INDIA. A bala.in gajiye suka sauka. Musamman Nas da shi kadai yasan yanda yake ji cikin kanshi. Suna sauka airport ya kira doc din suka sake magana. Zama sukai akazo da motar asibitin aka dauke su. Hankalin shi bai nutsu waje daya ba sai da aka shiga da Nas checking. Yaje yagani da idanuwanshi. Gabanshi sukai sedating din Nas din bacci mai nauyi ya dauke shi. Addu.o.i yai mishi sosai sannan ya fito ya samu husna zaune a waiting room tana jiran shi. Murmushi yai mata. "Gajiya ko?" Ya tambaya yana nazarin fuskarta. Kai kawai ta daga mishi dan bata saba irin wannan tafiyar ba. Ga yunwa na cinta. Akwatinsu ya dauka cak. Husna ta bishi da idanuwa tana mamakin karfin shi. Jan akwatin tai dazun amman harda nishinta. Hannu ya mika mata. Ta kama ya dago ta. Har lokacin murmushine a fuskar shi. Yanda yaga gaba daya husna tai laushi. Lifter suka shiga ta saukar dasu zuwa kasa. Suka fita daga asibitin. Hannun shi damtse danata kaman wadda za.a kwace. * Taxi suka hau. Turancin ba ibdiyan mai taxi din dakyar yake haduwa yace mishi ya kaisu wani hotel mai kyau. Amman indai da mai kyau kusa kusa da asibitin yakai su nan. Haka kuwa akai wani dan hotel yakai su. "Hotel ka mubarak" baiyi nisa can da asibitin ba. Kuma yana da dan kyau. Husna sai dai idanu dan tagama gajiya gabaki dayanta. * "Yunwa ko?" Ya fadi yana zama kusa da husna. Kai ta daga mishi ya bata fuska alamar baya so. Hakan ya sata cewa "Eh yunwa fa" Mikewa yai. "Barin samo mana abinda zamuci" Kwanciya tai kan gadon kamun ya dawo. * Yanayin yawancin abincin yagani yasan da wuyar gaske ya ciyu wajensu. Dan haka ya siyo musu kaji da lemuka. Kwankwasawa yai ya tura da sallama ga mamakin shi husna har tai bacci. Badon yunwar da take jiba sam da bai tashe ta ba. Ajiye kayan yai a kasa. Ya zauna gefen gadon. Hannunshi yasa ya shafa kuncinta. Ta ture hannun shi tana sake gyara kwanciyarta. Hannuwanshi yasa duk biyun ya dagota kaman yarinya karama. Ya tallabota jikinshi. A hankali yake jijjigata yana fadin. "Hussy mana. Tashi kici wani abu" Sake langabewa tai jikinshi. Ya lumshe idanuwa yana jin wani yanayi da yake wahalar dashi. Ya sauke numfashi yana sake girgizata. Amman ina gajiyar datai tasa baccin yaci karfinta. Yana son ya tasheta da salonshi sai dai shi zai wahala. Yanda yake ji ma a yanzun kawai ya ishe shi. Dakyar ya samu ta tashi kaman zata saka mishi kuka. Ya kama hannunta zuwa toilet. Ruwa ya zuba mata yace ta wanke fuska da bakinta. STORY CONTINUES BELOW Ya sake riko ta zuwa bedroom din. Zaunar da ita yai tana wani murza idanuwa da hannuwanta. Ta wani burge shi. Ya nutsu yana kallonta kamun ya dauko ledar ya bude musu. Tare suka ci. Tana gamawa ta lallaba tahau gadon ta kwanta. Prince ishaq sai da yai wanka sannan yazo ya kwanta. Matsawa yai sosai kusa da husna yanajin wani abu na fisgarsa. Adduo.i yai musu ya dora kanshi a kafadarta yana sauke numfashi. A haka har bacci ya dauke shi. * Da safe da suka tashi. Tana jinshi yana kiran yan gidansu suna gaisawa. Saita tsinci kanta da jin wata kewar mamanta ta rufeta. Yaushe rabon da ko taji muryarsu. In sun waya da maheer ne takan ce ya gaishe mata dasu. Ita ta kasa kira. Su kuma tasan fushin sune bai gama hucewa ba shisa basu neme ta ba. * Magana yake ta mata yaji shiru. Karasowa yai ya zauna kusa da ita. Ya taba mata kafada hadi da fadin. "Hey.... " Dagowa tai ta kalle shi tana sauke numfashi. "Tunanin me kike?" Ya tambaya yana tsareta da idanuwanshi. "Bako..... " Hannu ya daga mata alamar baya son ji. Shirun kuwa tai. Sosai ya kalleta cikin fuska sannan yace "Feel free idan ba zaki iya gayamun damuwarki ba. But yau yaza ma na karshe da zakimun karya" Mikewa yai dan haka kawai yaji ranshi ya baci. Yasan bashida matsayin da zaice saita fada masa komai dake damunta. Yana dai fatan wata rana tazo da bama saiya tambaya ba zata fada mishi. Husna taga alamar ta bata mishi rai. Bawai gaya masa ne ba zata iya ba. Bata son damunshi ne da damuwarta. Hidimomin shi sun masa yawa. A hankali tace "Ba haka bane gentle bana son damunka ne fa" Agogon shi yake daurawa baice mata komai ba. Tasan yana jinta hakan yasa ta ci gaba. "Yanda kake waya dasu umma ne ya sani missing nawa family din. Shine kawai" Yanda ta karasa maganar da wani sanyin murya yasa shi fadin "Crap" Cikin kanshi. Dan baima san yanda akai tunanin suje gidansu baizo masa ba. Ya kamata ace koda sau dayane sunje tare ma. Yaga kalar family dinta ya gaishe dasu. Batare daya juyo ba yace mata. "Zamu kirasu anjima mu gaishe dasu. Idan mun koma gida zamuje" Dan kunyarta ma yaji ta wani saukar masa. Gaskiya bai kyauta ba. Ko da sanda aka bashi ita baya so. Wanda yai maka karamcin aura masa yarka ya cancan ci mutuntawa. "Allah ya kaimu" Ta furta. Baya son maganar don haka yace "Mu tsaya mu karya ko sai munje wajen Nas?" "Muje din. Kaga munbarshi tun jiya karya farka bakon waje" Juyowa yai ya kalleta alamar ta shirya. Ya kuma daga mata kai cewar ya ji me tace. Wani hade fuska tayi yanda yakanyi. Cikin kwaikwayon muryarshi tace "Bana son magana da kai. Ka bude bakinka ka amsani"1 Towel din dake gefenshi ya dauka ya cilla mata a fuska. Yana rufe tashi fuskar da hannuwanshi. "I love the way you blush" Husna ta fadi tana sake kwashewa da dariya. Kunyar shi na bata mamaki. Sai kaga fuskar nan mai kyau tayi wani ja. Bata ga tahowar shi ba saboda dariyar da take. Jinshi kawai tai kusa da ita sosai. Dariyar ta tsaya mata a wuya. Idanuwanshi ya zuba mata. "Kika ce menene?" Ya fada can kasan makoshi. Ji tai jikinta ya dauki dumi duk wata kalma ta tsaya mata. Fuskarshi ya matsar kusa da tata. Tanajin numfashin shi saman fuskarta. Ya wani ja iska yana lumshe idanuwa. Gaba daya yagama saukar mata da kasala. Sumba ya manna mata a wuya da kumatu da kan hancinta. Tayi luf da ita. Tanajin yanda jikinta ke amsa duk wani sakon da yake tura mishi. Hannu yasa ya zagaye mata lips sannan ya saka hannun a baki yana tasting kalar man leben data saka. Dakyar ya samu ya mike. Yana azabtuwa da yanda yake ji din nan. Sai dai inba tabbatarwa yai da son shi a zuciyarta ba. Bazai iya wuce fiye da yanda yake yin nan ba yanzun. Ko baki bazai iya hadawa da macen da bata son shi ba balle a wuce hakan. "Tashi ki shirya mu tafi" ya fadi yana maida numfashi. Yanda ta amsa "Uhummm" Din dakyar ya sa shi dariya. Yana kallon yanda take sunkuyar dakai a rashi yace good. Yanzun ta sa yaji kunya. * Suna isa asibitin kuwa Nas yace yanzun ake shirin kiransu saboda za.a shiga dashi aiki. Prince ishaq ya kalla idanuwan shi cike da wata kaunar yayan nashi yace. "Yaya ka yafemun. Just incase ko da wani....... " Girgiza masa kai prince ishaq yake. Muryarshi a dake yace "No Naseer. No and i mean NO bana son ji. Allah zai baka lafiya munyi addu.a" "Antina" Ya fadi yana maida hankalin shi kan husna. Kuka take. Nas yace "Haba mana super anty. In kina haka wazai kulamun da yayana" Hannu tasa tana kokarin goge hawayen fuskarta amman ta kasa. Prince ishaq ne ya kamota. Tako yi luf jikin shi tana kuka. Dakyar ta samu nutsuwa ta dago. Tace "Kanina Allah yasa a fito lafiya. Allah ya baka lafiya" Ya amsa da amin. Suna kallo akazo aka tafi da Nas din. Shi kanshi prince ishaq daya tambaya akace masa awanni takwas za.a dauka ana aikin. Sai da yaji jikinshi yayi sanyi. Nan suka zauna husna ta kwantar da kanta saman cinyarshi. Shikuma nashi kan na saman kafadarta. Suna jiran hukuncin Allah. Anyi ma Nas aiki cikin nasara. Komai na tafiya yanda ake so da yardar Allah.1 * Yau satin su daya kenan a india. Suna zaune a hotel room dinsu prince ishaq yai zaune shiru. Husna na cin cookies tana game din datai downloading a tablet dinshi. Taga shirun shi ya wuce misali ta dago tace "yadai?" Da wani yanayi a idanuwanshi da ta kasa fahimta yace. "Kinsan sai yanzun nai tunanin kasar nan babu wanda yasanni. Banida wani matsayi sai na koma tawa kasar......" Kallon shi take da mamaki ya ci gaba da fadin "Zan iya kome nake so. Zan iya rayuwata free hussy" Yanayin da yake maganar ya sata fadin. "Me kake sonyi? Kamun mu koma?" Murmushin nan nashi yai mata har dimple din fuskarshi ya fito. "I wanna have fun. Naseer is ok. Ina son living sauran days dina kamun in koma gida to the fullest" Wayar husna ta saka a key. Ta ajiye cookies din gefe tana fadin "Tashi ka shirya to. Muje wajen Nas mu tafi yawo" Mikewa yai ya nufi bathroom. Ta girgiza kai. Yanda yanayinsa yake cike da farin ciki ya mata dadi. Kome yake sonyi ita kam zata taya shi. Kaman yanda ya bata kwarin gwiwa ta kira iyayenta. Dan jiya tai bacci wanda ta jima bata yishi ba. Taji muryar iyayenta. Ta gaisa da kowa. Sun sa mata albarka. Har kuka sai da tai dan farin ciki. To name ita ba zata taya shi ya samu nashi farin cikin ba. Tana nan zaune ya fito. Itama ta tashi tayo wanka. Doguwar riga ta saka loose tai rolling mayafin akanta. Duk da babu kwalliya a fuskarta ta mishi kyau sosai. Fita zasuyi tazo gabanshi ta tsaya. Hannuwanshi ta riko ta sauke idanuwanta cikin nashi. So take yaga yanda tai nadamar abinda tai masa. Muryarta na rawa tace "Har yanzun baka ce ka yafemun ba gentle. Nayi kuskure mai girma nasani amman.......... " "Na yafe miki husna. Na yafe miki tun kamun ki rokeni" Batasan lokacin sata rungume shi ba. Dan ji tai kaman ya sauke mata wani katon nauyi. Hannuwanshi yasa ya rungumeta na wasu dakikai kamun ya sake ta. * Sai da suka biya wajen Nas. Dakyar ma yake musu magana saboda magunguna sun fara dibarshi. Saida yai bacci tukunna suka fito. Su kansu basu san inda zasu je ba. Hannun ta na cikin nashi. Hanya kawai suka diba. Duk titin dayai musu su bi. Wani ad husna tagani na poster din wani film. "O. M. G wallahi ina mugun son actor din can..... " Ta fadi tana nuna ma prince ishaq. Kallon guy din yai. "Vijay yayi fa. Kyanshi wani nutsatse ne. Kaga inyai dariya..... " STORY CONTINUES BELOW Mintsininta yai a hannunta da yake rike dashi. Hakan ya katse mata magana ta kwace hannu tana fadin "Ouchhh gentle mana.... " Fuskarshi daya murtuke ta kalla. "Muna tare ne kike kiran wancan tikeken katon nada kyau?" Kwashe wa tai da dariya. "You are jealous...... " Tace tana ci gaba da dariya. Kuma ya wani murtuke fuska zaka rantse bai taba dariya ba. Da gasken kishi yaji. Ya za ai ma suna tare tace wani nada kyau. Son vijay din ya mata sauki. Nashi ne mai wahala. Wucewa yai abinshi ta bi bayanshi tana dariya. Wajen ice cream ta gani da sauri tace "Gentle ice cream" "Nagan shi ai" Ya fadi yana ci gaba da tafiya. Ganin zasu wuce yasa tace "Saimun zakai fa" Tsayawa yai ya dora hannayen shi a kuqu yace "Mu koma wajen poster din vijay ki fada masa ya sai miki"2 Rau rau tai da ido tace "Yi hakuri. Kawai yana burge ni fa. Kama fishi kyau" Murmushi ya kwace masa. Dan yasan sai dai yafi vijay kyawun zuciya da hasken musulunci. Kama hannunta yai suka tsallaka wajen ice cream din. Guda uku ya sai mata ita kadai. "Kai baka dauka ba fa" Ta fadi tana dandana na hannunta. Ta wani lumshe ido dan bata taba shan ice cream mai dadin shi ba. Ya girgiza mata kai yana kallon yanda take shan ice cream din yana burge shi. Sha kaji da dadi sosai fa. Kamun yace wani abu ta mika masa. Saboda ya mata tsaho yasa ta mika hannu sosai. Ta ko dangwala mishi a hanci da kumatu. Da sauri yakai hannu yana gogewa. Baya son sanyi. Cokalin ya dauka ya dibo ya dangwala mata a fuska. Da sauri ita ma ta goge tana fadin "Bana so fa. Sai ka samun danqo. Ni ka sha karyai melting" Kadan ya diba ya sha. Yace mata "Umm ba laifi" Ta zaro ido "Wallahi da dadi sosai. Bakinka bashi da taste" Gira ya daga mata duka biyun alamar shi dinne bakin shi ba taste. Jiranta yai ta shanye ice cream din sannan. Tace mishi "A karo mu tafi dashi" Ya girgiza mata kai yana fadin "Ya isa haka. Sai kinyi mura ko?" Yanayin yanda yai maganar ne kawai yasa tai shiru ba don ta koshi da ice cream din ba. Fitowa sukai suka sake mikar hanya. Aikam suka shiga wani layi kamar mini market. Ana saide saiden abubuwa a wajen. Wasu bangles ya hango sun mishi kyau sosai. Yaja husna wajen. Ya taba yana cema mutumin. "I want this and that. How much" Da alama banda wanda prince ishaq ya taba da wanda ya nuna da hannu bai gane me yake nufi ba. "ve kitane hain?(nawa suke?)"1 Husna ta tambaya da yasa prince ishaq ya tsaya kallonta cike da mamaki. "teen hajaar ma'am" (dubu uku) Mai saida bangle din ya fada. "Antim mooly? (gaskiya kenan?) "Yes ma'am" Juyawa tai ta kalli prince ishaq tace "Ka dibo kudi saiya bamu canji tunda ba sanin kan kudinsu mukai ba" Cike da mamaki ya dauko wallet dinshi ya mika mata. Ta dibo kudin ta bashi Ya basu guda biyun da prince ishaq ya nuna ya dibo canji. Sai da ta kamo hannun prince ishaq suka fito daga kasuwar. Kwace hannunshi yai ya tsaya "Daman kina gane wannan jagwalgwalon hindi din kika barni da mai taxi dazun?" Dariya tai tace "Kadan kadan ne fa. Kuma shima dan hindi ne. Mai taxi din dazun urdu yake yi. Ka taho mu tafi" Ya maqale kafada. "Kafafuwana sun gaji. Mu sami taxi mu koma hotel dinmu. Ban labarin yanda akai kike ji" Matsawa tai ta tsaya kusa dashi sannan tace "Ina ganewa sosai saboda ina yawan kallon film dinsu masu translation. Amman kadan kadan nake rikewa fa" Kallonta yake tana kara wani burge shi. Haka suka ci gaba da labari har suka koma hotel dinsu. Wanka yai ya fito. Itama tayi. Sukai ordering nama da lemo dan sun gwada cin kalar abincinsu rannan basu ji dadin shi ba. Ita husna ma kadan taci. Dan duk a hanya yaita siya mata tarkacen duk da tagani tace tana so.

Post a Comment for "WATA BAKWAI CHAPTER 16"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...