WATA BAKWAI CHAPTER 11 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA BAKWAI CHAPTER 11

WATA BAKWAI CHAPTER 11

- - Post a Comment
WATA BAKWAI CHAPTER 11

  Idanuwansa kawai data kalla ya tabbatar mata da yaji kome take fada.+ Tsaye yake har lokacin ya kafa mata idanuwan na nasa da suke bala.in yi mata kwarjini. Ji take har iskar da take yawo a dakin tsaye take cik. A hankali ya tako ya qaraso inda take. Yanayin yanda zuciyarta ke dokawa ta dauka fitowa waje zatai tsabar kidimewar datai. Bata taba kawoma ranta zai kamata ba. Ko kuma zata ma ji abinda take ji yanzun idan har ya kamata. Baiko kalleta ba. Harya karaso. Hannu yasa ya zare earphone din daga kunnenta. Wayar yazo dauka takai hannu wajen. Ya hada da wayar da hannunta duka ya riqe. Jikin bangon wajen ya turata. Kalar riqon dayai mata a wajen ne yasa batai kiciniyar qwacewa ba. Idanuwansa har sun sauya saboda bacin rai. Bai taba zaton zaiji kishin wata ya mace bayan huddynsa ba. Da huddy baisan kishi kalar wannan ba. Saboda yasan shi kadaine a zuciyarta. A yanzun ma bazaice ga kalar dacin da yake ji a ranshi ba. Yama kasa mata magana. Kallonta kawai yake. Kuma taqi yarda su hada ido. Kanta a kasa da bayanannen tsoro. Ya matsa kusa sosai yana sake hadeta da bangon. Tana jin hucin numfashinsa kan fuskarta saboda kusancin da sukai amman taqi yarda su hada ido. Hannunsa yasa ya dago mata haba. Tako sauke idanuwan nata cikin nasa. Saurin rufe su tai gam. Abinda take gani cikin nasa idanuwan ba zata iya daukar shi ba. Ya mata girma. Dai dai lokacin wayarta ta soma ringing. Karba yai daga hannunta ya duba 'ammar' yagani rubuce jiki da hoton heart qato tsakiyarsa rubuce da 'true love'. Wani numfashi yaja ya fitar dashi. Yakan jima ranshi bai baci ba. Yana duk abinda yasan zai guje masa faruwar hakan. Saboda bai iya shi ba. Dagawa yai ya kara a kunnensa. Hannunshi daya na riqe da husna. Ya janyota ya matseta a qirjinsa sannan yace "Hello" "malam kaba mai wayar abinta" Aka fada daga dayan bangaren. "Mafi munin kuskure da inaji kaf zuri.arku basu taba yinshi ba shine waya da matar aure. Matar kuma ta ishaq" Yanayin muryarshi ya tsorata kafafuwanta har kyarma suke. Badan rikon dayai mata ba dole ta zauna. Ammar kam ranshi ya soma baci yama akai wayar husnar shi taje hannun mutumin daya fi tsana a duk duniya. Dan haka yace "kaine kai kuskuren auren yarinyar da ta jima da miqamin zuciyarta. Ba zata taba sonka ba" Murmushin takaici prince ishaq yai. Yanajin wani sabon ciwuka suna budewa a zuciyarshi. "kai kana sonta kuwa?" Ya bukata da bala.in karfin hali. "Ina sonta son da ba zaka taba iya mata shi ba" Ammar ya fada cikin bacin rai. "Zan iya yarda ka shaqu da ita amman baka taba sonta ba. Daka na sonta ba zaka taba janta zuwa halaka ba. Ni ba qaramin mutum bane akwai dalilai da dama dazai hana na dauki hukunci akanka.........." Katse shi ammar yai da fadin "malami bama son dogon surutu ka saketa mana tunda bata sonka ni take so" Zuciyar prince ishaq har wani daci take ga sabbin raunukan dake ciki suna kara budewa. A hakan ya daure. Cikin kanshi yana lissafa watannin aurensu kamun yace "Zan sake ta! In har bata soni ba nan da *WATA BAKWAI 7* Be a man karka sake kiramin mata har sai wa.adin nan ya cika if not wallahi kaf danginku babu mai gane kurkukun da zan kaika!" Kamin ya bashi amsa ya kashe wayar.Tura husna yai kan gadon dakin ya bude wayan yana qoqarin ciro sim din. Sai lokacin ta taso. "Make shirin yi haka?" Bai kulata ba ya zaro sim din ya karya. "Gentle ka bari kai baka san darajar so bane?" Ta fada tana goge hawayen da suka zubo mata. Ko inda take bai kallaba. Saboda baisan me zai iya mata ba. A yanda yakejinsa komai ma zai iya yi. Wayar ya doka da bango ta tarwatse. Ya tsaya ya dafe kanshi da hannuwansa duk biyun. Yau shine wani yake fadawa maganar da duk ranshi yaso. Yau shine aka tozarta. Tozarci mafi muni. Abubuwa da yawa sun faru da rayuwarsa. Sai dai babu wanda ya taba darajarshi irin nayau. Bai isheta ba ta hada masa da zagi cewar baisan darajar SO ba. "Akanme zaka fasamin waya? Saboda me? Kasan yanda..........." Bata qarasa ba ya dauketa da wani irin mari da saida taga wani haske da wasu kana nan taurari.1 Ta dafe kunci tana kallonshi. Komai ya tsaya mata. Muryarshi a dake yace "Da aurena akanki husna? Da darajata zakina waya da qato cikin gidana! Qarqashin ikona. Saboda bakisan daraja da haqqoqin aure ba ko? And you dare have the guts to question me? Wallahi bansan tsanar da kikaimun tai girma haka ba" Tsugunnawa tai a wajen tana wani irin kuka. Ya qare mata kallo kawai yana dana sanin wannan auren. Tun farkon shi yasan babu komai sai fitina a ciki. Da karin matsaloli a wajen shi. Fita kawai yai yana doko qofar da qarfi gaske. * Tunda husna take bata taba zaton akwai randa zataji kunyar wani dan adam kwatankwacin tayau bama. Taji ta muzanta. Maganganunsa sun sosa mata rai shisa taso tai tabarmar kunya. Sam marin dayai mata bai dameta ba. Domin ta cancanta yai mata fiye da wannan hukuncin. Ta jima da sanin cewar abinda take bashi da kyau saidai ta kasa dainawa. A kwanakin da suka wuce ta daina kiran ammar saboda tanajin kaman bata kyautawa aurenta. Saidai shi inya nemetan bata iya share shi. Bata san ta inda zata fara ba. Me zata soma gyarawa? Laifukan zunuban da suke kanta taji sun wani danneta lokaci daya. Da sauri sauri take maida numfashi. Tunanin mutuwa da kwanciyar kabari ta ziyarci zuciyarta. Tunanin yanda ta biye son zuciyarta da tunzurar shaidan ta aikata laifi mai girma. Astagfirullah ta shiga jerowa tana wani irin kuka. Bata san da wanne irin ido zata kalli prince ishaq ba.Falon kasa ya sauka. Baya son ya shiga dakinshi dake cike da hotunan huddy yaga abinda kaddara ta ja masa.+ Fuskarshi na cikin hannuwan shi yana maida numfashi. Bai taba zaton akwai ranar da zai daga hannunshi wa mace ba. Saidai kuma bai taba zaton abinda ya faru yau zai taba faruwa ba. Hakama ciwon da yake jin zuciyar shi nayi. Yasan ya tsaneta a farko fine. Saboda yana dauka auren kwadayi tayi dashi. Amman wannan bai isa ta hukunta shi ta wannan hanyar ba. Asalima yanzun abinda yake ji game da ita shi kanshi bazai fassara shi ba. Baisan abinda ya kamata yayi ba. Jikinshi har wani kakkarwa yake. * Saida tai kukanta mai isarta sannan. Ko fuskarta bata damu data wanke ba. Ta riga da ta gama yanke ma zuciyarta. Zuwa zatai ta bashi hakuri. Zuwa tai wucewa zuwa bangaren shi. Kaman ance ta kalli kasa ta hango shi. Jitai zuciyarta ta sake karyewa. Da wanne idon zata kalle shi? Me ma zatace ne. * Yanajin zuwanta. Bai dago daga yanda yake ba. Saboda baya son ganinta sam sam a yanzun. Tsugunnawa tai gabanshi a kasa. Ya bude fuskar shi ya sauke jaijayen idanuwanta akan ta. Kasa hada ido tai dashi saboda wani kwarjini da kunyarshi data cika mata zuciya. Kafarshi tazo rikewa ya matsar da sauri yana fadin. "Don't..... Please ki tafi kawai" Girgiza kai tai tasa hannu tana goge hawayen daya zubo mata. Cikin kuka tace. "Dan girman Allah kayi hakuri. Ka yafemun......" Ji yake kaman tana goga masa gishi a sabbin ciwukan dayaji. "Dan Allah ki kyaleni. Just leave me the hell alone!" Duk da ba hayaniya yake ba. Muryarshi a dake take. Bude baki zatai ya katse ta da fadin. "Kibarni husna, laifina ne dana kasa sauke hakkokin ki da Allah ya doramun. Na biyewa son zuciyata. Hukunci na ne wannan........." Da alamaun gajiya sosai a muryarshi. Ga tunani ya masa yawa. Shima ya gane kuskuren daya aikata. Ko da baya son husna bai kamata dan yana gudun karin matsala yaki sauke hakkokin da Allah ya wajabta masa ba. Bai kamata ace yaki duba darajar ibadar da take cikin aure. Shisa Allah yai masa wannan jarabawar. Ya kuma dora masa wani azababben kishin husnar. Yanda husna ta yanke ma zuciyarta duk abinda zaiyi zata jure ta bashi hakuri. Zata sake gwadawa wayar shi dake ajiye jan table din wajen ta shiga ringing. Ko kallonta baiba harta tsinke. Ta kara daukar wani ruri. Ya duba likitan Nas ne. Dagawa yai yana addu.a Allah yasa ba wata jarabawar bace. Karawa yai a kunne yai shiru. Dakyar ya iya amsa sallamar da doc din yai masa. "Nas ya bude idanuwan shi. Saidai baiyi magana ba. Nasan zakaso ka sani......... " Baima bari ya karasa ba. Ya ajiye wayar ya lumshe idanuwan shi yana mika Godiyarshi Ga Allah madaukakin Sarki Mai Ikon rayuwa da mutuwa. Husna ya kalla badon ya daina jin bacin rai ba. Ko abinda ya faru ya wuce. Sai don girmab labarin daya samu yanzun ya danne komai. Hakan yasa yace mata. "Nas ya bude idanuwan shi" Fuskarta ta goge tana hamdala. Mikewa tai muryarta can kasa tace bara in dauko hijab. "Kiyi me?" Ya tambaya yana mata wani kallo daya sata jin ta tsani kanta da abinda tayi. A rauna ne tace. "Muje wajen Nas....." Girgiza kai yai sannan yace. "Believe me, after dazun Nas bazai so ganin ki ba..... " Wasu hawaye suka zubo mata. Ta goge su tace. "Ban roke ka karka hukuntani ba amman ka dubi girman Allah karkai mun hakan da haramtamun ganin Nas" Wuce ta yazo yi saboda yanda take neman karya mishi zuciya. Hannu ta riko masa tana fadin. "Allah idan bakaje dani ba. Ko ta katangane zanbi inba a budemun gate ba" Taso ta bashi dariya ya share. Hannun shi ya kwace yace. "Fine. Karki batamun lokaci" Kusan da gudu ta wuce shi ta hau sama. Ya girgiza kai murmushi na kwace masa. A wannan lokacin ne yasan ko da baya son yarinyar nan gaba daya. Ya soma sonta. Saboda jiyai ya yafe mata. Har zuciyarshi ya yafe mata. Rokar musu gafara yake wajen Allah na laifin da su duka suka aikata. * Har sukaje asibitin ko inda take bai sake kallo ba balle tai tunanin zai mata magana. Saidai sanda suka je Nas din harya koma bacci. Canjin da zaka iya gani an samu da idanuwa shine da kan shi yake numfashi. Babu taimakon komai saina Allah. Zama sukai. Prince ishaq can nesa da ita. Sai take jinta duk wani iri. Mumyn Nas ya fara kira ya sanar da ita da kanshi ci gaban da aka samu. Sannan ya kira umman shi. Sun jima suna waya da ita sannan ta bukaci ya bata Husna su gaisa. Kallonta taga yayi sannan ya tashi ya karasa inda take a dake ya mika mata wayar yace. "Umma nason magana dake" Gabanta taji ya fadi. Hannu na rawa ta karbi wayar. Tai sallama ta gaishe da ita a ladabce. Zata iya jin fara.ar umman ta cikin muryarta tace "Ya mai jiki kuma" A sanyaye ta amsa da. "Alhamdulillah umma" "Allah ya kara sauki. Dan Allah ku kula. Ki rike amana, kinga kalar rayuwar da baban yake fama....." Wata kunya taji don amana ta dade da watsar da ita. Ta daure tace. "In shaa Allah umma. Mungode Allah ya kara girma" Ta amsa da amin tai musu addu.a sosai sannan ta kashe wayar ta mika masa. Karba yai ya koma inda yake ya zauna. * Yau ko da kamala ya kawo musu kayan ciye ciye. Kowa daban daban yaci. Basu koma gida ba sai dare da doc ya tabbatar masa allurai da magungunan dake aiki jikin Nas ba zasu bari ya farka dan ranar ba. Saboda kwakwalwar shi na bukatar wadataccen hutu. Suna isa gida suka hau sama. Yana shirin nufar bangaren shi tace. "Gentle......" Bai juyowa ba amman ya tsaya da tafiyar da yake. Hakan yasa ta fadin. "Dan Allah ka yafemun. Nayi kuskure mai girma. Ka yafemun..... " Yanajin tayi shiru yaci gaba da tafiya abin shi. Yana son sosai ta gana kuskuren abinda ta aikata. Ya kuma yarda da ita cewar ba zata sake ba kamun nan ya soma goge mata wannan yaron a zuciya. Ta lumshe idanuwanta ta bude su hadi da sauke wani dogon numfashi. Bakomai zata ci gaba da kokari tunda ita ta aikata laifi. Dakinta ta wuce itama. Rigar jikinta kawai ta sake dan sunyi isha.i a asibiti. Ta kwanta. Allah sarki rayuwa. Bata taba zaton zata juya da ita ta wannan fannin ba.+ Wasu hawaye masu dumi taji sun zubo mata.Sai yanzun girman laifin datai yake dawo mata. Ina hankali da iliminta ya tafi take waya da namijin da ba muharraminta ba da aurenta. Inalillahi wa ina ilaihi raji.un. Wasu maganganu suka dawo mata a daren da za.a kawota gidan prince ishaq. "Husna baki taba bijirewa umarni na ba sai akan auren nan. Ba don bama son yaron da ke kike so bane muka hana shi ke. Sai don mu mun hango abinda baki hango ba. Aure an daura. Ki dauka hakan shine alkhairi a rayuwarki. Inhar kikai abinda kika kaso auren nan Allah ya isa tsakanina dake!!!" "Ya Allah" Ta furta tana sake juyi kan gadonta maganganun babanta na dawo mata. Ta rasa yanda akai komai ya juya mata haka. Lokaci daya farkon abin ya dawo mata. * Husna itace yarinya ta uku cikin yaya biyar da Alhaji abdullahi da matarshi Haj. Baraka suka mallaka. Babbar yarsa mace ce wato haj.fatima. Tana da aure harda yara uku. Sai namijin dake bi mata Aminu. Da shima yana da aure. Sai husna. Akwai tazarar shekaru kusan bakwai tsakanin su da aminu. Maheer sai autarsu aisha. Baban su dan kasuwa ne. Estate guda gare su da gidaje ashirin cif a ciki. Family dinsu ke cikin wajen gidaje goma sha biyu. Sauran ne kawai baki. Sun samu wadatacciyar tarbiya da ilimi na addini dai-dai misali. Husna tagama secondary school da shekaru sha bakwai tai Nasarar samun gurbin karatu a kano poly inda take diploma dinta akan computer science. * Ba zata manta haduwarsu ta farko ba da ammar. Kaya tai loading harda system cikin wata jaka. Tun daga gida mamansu tace mata hannun jakar bazai dauki nauyin data loda masa ba tai gardama. Aikam tai sa.a hannun jakar ya tsinke. Kasancewar bamai zip bane komai yai kasa. System dinta kadai ta iya tarewa. Komai ya watse kasa. Jitai kaman ta saka kuka dan takaici. Bama tasan ta inda zata soma tattara su ba. Ta tsugunna ta soma da maths set dinta. Kaman daga sama taji ance "Dole kiyi bari wannan books din sun maki nauyin dauka" Dagowa tai suka hada ido. Murmushi ya qwace mata. Shi ya tayata ta tattara komai. Haduwarsu ta biyu islamiya zataje anan ne taji sunan shi yaji nata har sukai musayar number. * Ammar kam shine babba gidansu sai kannensa maza. Babansu ba wani mai hali bane. Rufin asirin Allah. Lokacin da ya hadu da husna yana level 2 bawani girman kirki ne dashi ba. Cikin watanni biyu sukai wata irin shakuwa taban mamaki saboda duk wani abu da yake bukata a wajen mace husna ta hadashi. Ba fara bace can. Tana da wani hasken fata mai kyau. Da manyan idanuwanta tubarkalla. Bakinta da hancinta kaman ita ta zaba. Yakan mata tsiya wani lokacin cewan tsayinta bazai wuce damtsen hannun shi ba. Dan kuwa gajera ce da jiki madaidaici. * A shekaru biyu da dori da sukai da ammar duk wani wanda yake tare da ita yasan shi. Duk wani buri na rayuwarshi husna ce. Duk wani mafarki na har abadanta ammar ne. Lokacin data hada diploma dinta ne babansu ya bukaci yaron da take so ya turo manyan shi. Labarin ya daga musu hankali saboda ammar a lokacin yake shekarar shi ta karshe a karatu. Yana da gidan da zasu zauna. Saidai bashida sana.ar da zata rike su. Ko da magabatan shi suka zo basu boye ma baban su husna ba. Sun sanar dansu bashida wata sa.a saidai yana matakin karshe na karatun shi. Sam babansu husna bai musu alkawari ba. Asalima yabar magana ne kan cewar in har yarshi ta samu tsayayye nasu dan bai samu sana.a ba zai aurar da ita. Babu kalar tashin hankalin da basu shiga ba. Husna ke karfafa masa gwiwa cewar saita kula wani ne za.ama ganshi a aura mata. Saidai batasan me kaddara ta rubuta mata ba. * Lokacin da ammar ya tafi bautar kasa ne. Kasancewar estate dinsu yana kusa da gidan wazirin kano. Husna ba zatace tasan wata alaka dake tsakanin babanta da wazirin kano ba data wuce makwabta ka. Asali ma basu ko taba shiga gidan ba. Saidai su wuce shi in hanya ta kama. * Bata san da kaddarar data hada babanta da wazirin kano ba. Alaka ce data samo asali sanadin makaranta. Tare sukai primary school. Lokacin da mai martaba yazo masa da bukatar a samo ma danshi yarinya mai hankali. Ba sai yar sarauta ko yar wani mai kudi ba. Yarinya yar babban gida. Yar manyan mutane. Wazirin yaranshi duk mazane. Macen shi yarinya ce dabata shige shekara goma ba a lokacin ne yaima baban husna magana akan nema ma prince ishaq auren yarshi idan ya amince. Yaji dadi sosai da wannan girmamawa da yai masa dan haka ya amsa shi. * Husna ba zata manta wani yammacin ranar juma.a ba. Kwance take suna waya da ammar. Kasancewar yanzun sai suyi sati biyu ma zuwa uku basuyi waya ba. Wani kungurmin kauye ne yake bautar kasa. Sai yahau abin hawa tafiyar awa daya da wani abu ya shigo gari dan ya samu network yaji muryarta. Aisha ta shigo dakinta tace mata tazo babansu yana kira. Kaman zasu sakama juna kuka sukai sallama. Tun a hanya ta rasa me yasa take jin gabanta na wani faduwa. A haka ta karasa falon babansu ta gaishe dashi. Mamanta ma tana nan. Bayan sun gaisa a ladabce babanta ya sa magama a nutse. "Husna kasancewar ina da tabbaci akanko yasa na amsa neman aurenki jiya da dare. Yau din nan zasu kawo komai. Idan an dade wata biyu..........." Tun daga wajen kalmar "Aurenki" kunnuwan husna suka daina jin wani bayani. Komai ya daskare mata. Zuciyarta na wani mata nauyi. Lumfashinta taji yana shirin daukewa. Cikin tashin hankali tace. "A.a baba.... Wallahi bana son shi.... Mama karku mun haka......." Daga ranar tashin hankalinta ya fara. Babu kalar haukan da batai ba amman a banza. Aka kwace mata wayoyi duka. Wata biyun nan da yan kwanaki shi ya rage musu su cimma burinsu ita da ammar............! **** **** Wani nauyi da zuciyarta tai mata ga numfashinta na fita sama sama yasata tashi zaune. Addu.o.i take karantawa dan Allah ya bata karfin halin hana zuciyarta maidata rayuwarta ta baya. Mayar da ita watanni biyu na rayuwarta da suka fi kowanne kunci. A haka bacci ya kwasheta da mafarkai kala kala.

Post a Comment for "WATA BAKWAI CHAPTER 11"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...