WATA BAKWAI CHAPTCHAPTER 15 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WATA BAKWAI CHAPTCHAPTER 15

WATA BAKWAI CHAPTCHAPTER 15

- - Post a Comment
WATA BAKWAI CHAPTER 15  A hankali komai yake tafiyar musu. Sauqi kam ya samu wajen nas watanshi biyu kenan cif a asibiti. Dan harya soma musu korafin ya gaji shi kam. Saidai likitanshi yace ba zasu sallame shi ba sai sun tabbatar internal injury din daya samu a kanshi bazai bada wata matsala ba. * Prince ishaq da husna kam da duk ranakun da suke wucewa wani irin shakuwa me karfi ce take kara shiga tsakaninsu. Yanzun kam sai tai kwanaki ma bata tuna da wani ammar ba. Zasu kwana waje daya da prince ishaq. Dan tama saba da duk rikicinsa yanzun. Suje unguwa tare, wasu lokuttan in yasan zai fita ya jima saiya dauketa ya sauketa asibiti wajen Nas suyita hirarsu in ya dawo ya biya ya dauketa su koma gida. * Yauma kaman kullum tana zaune falo tana kallon mbc 3 ya fito jikinshi sanye da farar shadda. Da kyanshi da shaddar suka shigar mata ido. Murmushi tai. Ya daga mata gira hadi da fadin Say it hussy" Ta kalle shi cikin ido tace "mezan fada?" Ya sake fadada murmushinsa. "Kice nayi kyau mana" ya fada yana karasawa inda take ya zauna. "Shaddarka tamun kyau" ta fadi tana dariya ganin yanda ya tabare mata fuska kaman karamin yaro. Ja mishi hanci tai tace "sorry gentle kayi kyau kama fi shaddar" Dariya yai shima ya matsa daf da ita ya sumbaci kuncinta. Ya bude baki zaiyi magana kenan wayarshi ta soma ringing. Yasan Nas ne saboda ringing dinshi dabanne dan haka ya zaro wayar daga aljihu ya daga hadi da fadin "Hello Nas..." "Yaya kuzo ku daukeni an sallameni" ya fadi daga dayan bangaren muryarshi cike da farin ciki. Tare sukaje suka dauko Nas. Su duka ukkun kallonsu zakai ka tabbatar fuskarsu dauke take da farin ciki.+ Sai hamdala sukeyiwa ubangiji. Haka sukaita hira bayan sun dawo gida. Zaka rantse sun shekara ne basu ga juna ba. Sai can husna ta kalli Nas ta sake duban agogon dakin. Karfe tara harta dan gota. Ka tashi ka sha magani kaje ka kwanta lokaci yayi. Husna ta fadi tana kallonshi. Nas ya wani shagwabe fuska. "Nikam kinga wallahi bangaji da hirar nan ba" "Kana son komawa asibiti ne ko?" Prince ishaq ya fadi muryarshi babu alamun wasa. Aikamun husna tace wani abu nas ya mike da saurinshi yabar wajen. Suka hada ido ita da prince ishaq sukai dariya. Miqewa tai itama a kasalance prince ishaq yace mata "ina zakije?" "Daki" ta amsa mishi yanayin yanda yake kallonta na kashe mata jiki. Hannunsa ya miqa mata alamar taje. Batai masa musu ba tasa hannunta cikin nashi ya dumtse nata sosai kamar zata gudu. A hankali yajata ta zauna jikinshi. kamshin sa na wani rikitata. Ajiyar zuciya ya sauke ya saka hannuwansa duka biyun yana riketa sosai. "Hussy naji tsoro sosai" ya fadi a hankali. Shiru tai dan batasan amsar da zata bashi ba. Jin hakan yasa shi ci gaba. "Allah yaga zuciyata ba zata iya daukar rashin Nas ba shisa yabar min kanina." Ya karasa maganar cikin sanyin murya. Hannunshi ta riqo cikin nata tana kokarin gaya masa kalaman da batasan ta ina zata soma hadasu ba. Sun jima zaune a haka. Kamun tace masa "muje mu kwanta ko?" Kai ya daga mata alamar eh. A hankali ta zame jikinta daga nashi tana miqewa. Shima tashin yai tare suka nufi bangarenshi. Kan gado ya kwanta da full kayanshi yana wani tabare fuskarshi me kyau. Husna ta girgiza kai kawai ta shiga toilet ta watsa ruwa. Ta sakko bath robe ta fito. Prince ishaq ta kalla bacci yake Rabin jikinshi akan gado rabi a kasa. Tai murmushi kawai tasan ya gaji. Gama shiryawa tai tsaf tasa kayan bacci sannan tazo inda yake ta zauna ta zuba mishi ido. Zuciyarta na dokawa. Har kasan ranta batason tashin shi. Saidai yanayin kwanciyar dayai zata iya saka mishi ciwon jiki. Dabara tazo mata nata kamashi ta juyashi ya kwanta kan gadon sosai. Kafafuwanshi ta kama daqyar ta cicciba su ta dora kan gadon tana uban nishi. Komun nauyin baccin dayake kana tabashi saiya farka. Husna na tabashi ya tashi saidai ya rufe idonshi kawai yana jinta da nishin da take. Dariya na son kubce masa. Sake juyashi tai daqyar ta kama hannunshi ta zare alkyabbar dake jikinshi. Ta sake mirgina shi ta zare dayan hannun. Gefe ta zauna tana maida numfashi. Ta kare mishi kallo. A ranta tace Allah ya kera mazaje a wajen nan. A fili kuma fada take tiqa a hankali. "Mutum shi badan dambe ba yabi duk ya tara tsoka. Yanzun da ace baida qiba kamar ni juyashi kawai zan in rage mishi wannan kayan nauyin.1 Ai shikenan ka huta. Saikaita baccinka da wannan shaddar nikam dai nagaji" Prince ishaq baisan lokacin da dariya ta kubce masa ba. Husna ta zaro ido. Lokaci daya ta hade fuska2 "ashe kana jina daman" Pillow ta dauka ta kwada masa a kirji tana fadin. "Kasa inata nishi kana jina kai lamo" Ta sake kwada masa a fuska ya tare yana dariya. Kwace pillow din yai ya rama. Husna ta dauki dayan pillow din ta sake kwada masa. Fadan pillow suka ci gaba dayi inta kwada masa ya rama. Yanata mata dariya. Gajiya tai ta ajiye ta kwanta gefe tana maida numfashi. A hankali yakai hannu ya juyo da fuskarta ta kalle shi. Idanuwanta ta sauke cikin nashi tako yi saurin maida nata kan kirjinsa. Murmushi yai. Yanajin dadin yanda idanuwansa ke da tasiri akanta. Bata jure kallonsu. Sauka yai daga kan gadon ya shiga toilet shima ya watsa ruwa ya fito. Ya shiga dakin canza kaya ya fito daga shi sai boxers da farar singlet. Ya hau gadon ya kwanta yana janyo husna zuwa jikinshi. Kaman ko da yaushe sai da taji wata kasala ta saukar mata. Ta kasa sabawa da yanayin nan. "Nagaji da abuja" yace mata. Hannu tasa ta danna mishi kumatu daidai inda dimple dinshi yake. Sannan tace "mukoma gida mana gobe indai babu wata matsala" Ya jinjina kai yace "haka nake planning nima nasa kamala yai booking mana" Saida safe tace mishi tana rufe idanuwanta. Addu.o.i yai musu kamar koda yaushe ya sumbace ta a kumatu da goshi sannan yace mata "Allah ya tashe mu lafiya" Washe gari tunda wuri suka hada abinda suke bukata. Dan husna ma akwatinta datazo dashi shi tadan zuba wasu kayan.+ Wasu kuwa nan tabarsu. Daga prince ishaq har nas babu abinda suka dauka sai kayan jikinsu. Jirgi sukabi zuwa kano. Karo na farko a rayuwar husna data taba hawan jirgi. * Daga airport mota suka samu ana jiransu aka dauke su zuwa gidan su prince ishaq. Husna taga karamci ranar. Takuma ga duk yan uwan prince ishaq masu kyau saidai duk basukai shi kyau ba. Sun jima sosai gidan dan nan sukai sallar la.asar. Komai husna takeyi a kunyace take yinshi. Haka kawai ta tsinci kanta da jin nauyinsu. Musamman mahaifiyar prince ishaq din. Hakan umma ta kula dashi yasa ta kira prince ishaq din tace "Babana kazo ku tafi gidanku ko?" Da murmushi a fuskarshi ya amsa mata ya maida dubanshi zuwa kan husna yace ta taso. Har kofar falon aka rakasu sannan suka fita zuwa harabar gidan inda motar su take ajiye. Bude musu akai suka shiga. Sai bayan an rufene husna tace "gentle banga nas bafa har zamu tafi." "Yana can bangarensu. Zaizo har gida indan Nas" ya amsa batare daya kalle taba. Kanshi ya jingina da kujera yai shiru. Ta kalle shi yau sarautar ta motsa kenan ta fadi a ranta. Duk da yangarshi a jininsa take. Wani lokaci tana kula in sarautar ta motsa magana ma kan dole yake yinta. Sai su wuni shiru saidai yai ta amsata dakai kome zatace inyai kokari yace mata um ko um um ko hmm.

Post a Comment for "WATA BAKWAI CHAPTCHAPTER 15"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...