SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 27 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 27

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 27

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 27


  Washe Gari Tun 7 Matar Abdallah ta kira Nazeefa akan maganar gyaran jiki, Nazeefa tace munanan zuwa anjuma tace Alright, tana kashe wayar, Ayyuka tadanyi sannan ta je ta sanar da iyayanta zasuje wajen gyaran jiki sukace bakomai+ Tashi tayi ta shirya sannan ta wuce gidan su Ameerah, koda taje ba wani bata lokaci sukaiba suka wuce gidan Matar Abdallah, suna shiga tace yauwa dama Ku nake jira muje ko? Nazeefa tace ba wani better ne anan gidan tana magana tana shafa cikinta, matar Abdallah ne tace akwai raguwan farfesun da mukai jiya bari na dakko maki kici kinsan Ku amare seda shan romo, Dariya tayi tace kinga matar nan kinsan komai fa, dakko mata tayi taci Ameerah ma taci suka Kora da 5alive sannan suka wuce gidan gyaran amarya! Bangaren mubeen kuwa yana wajen ginin makarantar da akemai, kirjinshi se bugawa yakeyi, Tinaninshi gaba daya yana wajen Ameerah, yanason yarinyar saboda natsuwarta, gata komai tana yinshi cikin Sanyi, Waya ya dakko har ze kirata kuma wata zuciyar tace baka sanar da ita abundake rankaba? Ka jira ta baka amsa Kawai, wata zuciyar kuma tana rayamai anyama zata yarda, yanda yaga kusan komai umurnin Kawarta take bi, Hasbunallahu wa I'imal wakeel yace yamaida wayarshi cikin aljahu, Sannan yai concentrating akan abunda da masu ginin sukeyi Su Nazeefa sunje gidan gyaran jiki, Mansur ne ya dameta da kira, dauka tayi yafara wani magana kasa kasa, ita kanta batasan me yake cewaba tajidai kawai yace dama inganki kusa dani yanzun nan, Uhmm tace Yanata surutanshi batacemai komai ba har ya kashe waya Gyaran jiki akai mata sosai Aranar farko, akace Anan zatai ta zama har se tayi 3days, Dago kanta tai ta kalle me gyaran jikin tace kiyi hakuri Zan koma gida kam yau saboda ban sanar da iyayena ba, Me gyaran jikin tace ba matsala, Wunir ranar body scrub aketa mata se chan yamma akafara mata dilka duka jikinta tace da ace kwana zaki anan da dashi zaki kwana tace badamuwa kimun haka Wajen 7 aka Kara wanke mata jiki da ruwan turare sannan tasa kayanta, aranar farko bakuga yanda skin dinta yai kyau ba se kamshi takeyi, Mansur ne ya kirata tace tana Ina? Tace gasunan waje kaza yace Ganinan zuwa dakkoki tace OK nida Ameerah ne ma yace OK, Ba ai 5 mins segashi yai parking a kofar gidan, tun daga glass din motar yake kallonta yaga ta kara haske sosai Kamar ba itaba, Bude motar sukai suka shiga wani kamshi ya dake hancinshi, kallonta yakeyi kamar wata Aljanah dan kyau datai skin dinta nata kyalle, Gyaran murya tayi, da yake ya gane me take nufi dauke idonshi yayi akanta, Ameerah kuwa nacewa wannan Angon kamar maye hhh.. Cewa yayi dama inasone muje kuga gidan da zamu zauna ya kamata ko? Nazeefa tace yes gaskiya kam Ameerah kuwa tace yakamata amma Dan Allah mubari zuwa gobe yanzu dare yayi 8 fa, Nazeefa ta ce OK Mansur ya kaita gida inyaso goben maje yace OK, Kofar gida ya ajiye Ameerah, Nazeefa tace tagode Allah huta gajiya tace Ameen Sannan suka kama hanya, yace My Wife kinga yanda kikai kyau kuwa? Rufe idonta tai dan kunya tace nagode Yace please muje ke kifara ganin gidan da zamu zauna tace OK muje kallonta yai yace I love youuuu Daidai gidan da zasu zauna suka tsaya, da farko gidan su Mansur zasu zauna, tace Love yanaga Kai parking anan? Yace yes an chanza shawarane yanzu nan zamu zauna, Bude gate yayi ya shigar da motar sannan ya kulle, Nazeefa zama bakauyiya tayi dan kyan gidan ya hadu sosai, Kamar ba hannu yai ginin ba, STORY CONTINUES BELOW Tace Masha Allah gidan yayi kyau yace yes, shiga sukai ta ga komai yaji a dakin ga komai da komai ko yanzu aka kawo amarya lafiya lau zasu zauna, Kallonta yayi yace love kinyi kyau, tace uhm, yace ya kikaga gidan tace Gida Masha Allah, Allah sedai nai fatan Allah bamu zaman lafiya da zuria dayyaba yace Ameen, Kusa da ita yazo ya zauna yaji kamshinta na tadamai da hankali, Rike hannunta yayi taji kirjinta na bugun takwas takwas Kallon lips dinta yayi takalleshi batai aune ba taga yakai mata wani Kiss AI Kara rikicewa tayi tafara hawaye Tana Mansur Mansur Mansur please karmui abun da bedace ba Dan Allah, har ze fara romancing dinta Dan idonshi nakan boobs dinta ya tsaya Chak, idoshi yai ja yafara nishi yana kallonta Ita kuma ta rakube a kujera, shiga toilet yayi Kome yai ohonmashi ya fito fuskarshi duk ruwa Tashi mu tafi yace Mata, ta tashi jikinta duk ba kwari tabishi tana hawaye kadan kadan Seda suka shiga mota ya saka AC, Tagumi tai aranta tana meyasa wasu mazan se ahankali ne, Dafata yai ta juyo da sauri tana kallonshi ido cikin ido, tama kasa me zatacemai. Afuwan my love yace mata, ta sunkuyar dakai aranata tace mudai yan mata muna ganin abubuwa kala Kala, Allah dai ya Kara tsaremu Ameen Kallon Agogon wayarta tayi taga karfe 10 na dare Kara tsurewa tai tace wallahi idan naje gida fada za'aimun ace me yasa Nakai 10 a waje, yace To yanzu yazamui? Tace sedai ka kaini gidan su Faeez seba ta ambata Mubeen ba. Yace OK Kaita gidan yayi seda ta fito yace Dan Allah kiyi hakuri akan abunda ya faru wallahi Sonki ne ya janyo haka, da ace ba yanzu zamui aureba wallahi dropping din relationship din zamui cos bazanso na bata miki rai ba ki yafemun, Ka kallonshi batai ba faeez dama already ta kirashi yazo ya bude Mata gate ta shiga Ran Mansur haka ya tafi babu dadi Sam yana Allah ya Kara tsaremu da sharrin shaidan Nazeefa na zuwa gidan ta lalubo number ummanta ta Kira tace tun dazu nake neman layinki dama Zan fada mikine Ina gidan mama Asmau da dare taine kawai muka wuce da faeeza gidan Chan zamu kwana tace to Nazeefa ba komai Allah yayi Albarka tace Ameen ki sanar da babana tace To Yar baba AI yanajin kima, mika mai wayar tai tace baba inata missing dinka, yai murmushi yace Allah yai albarka tace Amen Samun waje tai ta kwanta nan abunda Mansur yai Mata yaketa ta dawo mata, Astagfirullah tace, Sannan tace yajama ma kanshi bazai Kara ganinaba se randa aka Daura mana aure! Shima koda yazo kwanciya kasa samun natsuwa yayi, aranshi me zatace dashi, Yace gaskiya muma maza munada matsala mudinga kokarin kiyayewa, Muna Dannewa, Juyi kawai yakeyi a gado dayan zuciyarshi kuma tana fadamai yayi missing dinta cos she has soft skin daga gani zatai......! **** Washe gari tun Asuba yake kiranta taqi picking daga karshema kashe wayar tayi, bayan sun kammala Hajiya asmau da faeeza suka taho gidan tare dan nan zasu zauna har se angama biki, Koda suka zo gidan Nazeefa sanar da iyenta tai Chan zata zauna har se Ana gobe bikin zata dawo sukace to bakomai a kula tace Tare da faeeza zamu tafi, sukaji dadi Sosai Tafiya Chan gidan su Ameeran sukai suka hadu, koda sukaje Ameerah se kallon Faeeza take jitai tanason yarinyar Dan sau tari suna yawan hada ido Ameerah dai tace wannan waye? Nazeefa tace laaa ban fada mikiba kanwar saurayinkine mubeen ko ince kanwar mijinki! Amirah tadanji kunya Faeeza tace Sist Nazeefa da gaske budurwan ya mubeen ne? Tace wallahi da gaske nake Faeeza tace wow she's beautiful wallahi, nan take ta Kira mubeen tace yaya gani ga budurwanka Mamakine ya kamashi yace budurwata kuma? Aina kikaganta? Tace yes budurwanka gamunan muna tare da ita Nazeefa ta fadamun Ajiyar zuciya yai yace Alhamdulillah sannan ya kashe wato. Anyima accepting soyayyarshi, Wow. Tashi sukai suka tafi gidan gyaran amarya sukabar Nazeefa achan, Su koma suka tafi kasuwar Dan siyayyan abunda sukeso Misalin karfe 11 na safe mubeen ya shirya ya tafi tsohon gidan su Ameerah yaga Kofar is locked, Kara zuwa yai yadawo kusan 3times still Kofar a kulle wani Yaro ya tambaya yace ai kusan kwana 3 kenan basanan sun tashi Mubeen yace OK Kiran Kanwarshi yayi yace kuna inane? Tace muna kasuwa yayi, yace Nazeefa fa tace tana gidan.....se bata karasaba yace Ameerah fa tace gatanan! Mika Mata wayar, ta amsa suna magana yace nazo bakwanan wai kuntashi? Tace ohh wlhi abun ne yazo kasan bana zama sai yasa yace OK, Zamui magana anjuma tace dear Sannan ta mikawa Faeeza wayarta Bangaren Mansur kuwa yayi Kiran duniyar nan wayar Nazeefa a kashe Oh My Nazee yace! Please switch on ur phone Ina son jin muryarki, nai dariya nace wazai fada mata😹 Kiran wayar yaketayi a kashe, bude Gallery dinshi yayi yaga pics din da sukai tare, idonshi nakan boobs dinta ta Fara lashe baki yana cewa I can't wait ki zama mallakina, I love youuuuuuu TOFAA Tun Ana jibi bikin yan uwa na nesa suka fara zuwa, gida kam ya cika da jama'a kowa se neman Nazeefa yakeyi sedai ace batanan,+ Bangaren gidan su Mansur kuwa shima iyalan Me martaba Sarki duk sunzo ciki harda hassan da hussaini, Su suhailat kuwa ance baza a zo da suba suna chan sunata fada tsakaninsu, Anata shirye shirye amma Sam hankalin Mansur yai matukar tashi yau kwana daya bege beloved dinshiba, Damuwa ya shiga sosai, kuma beson kowa yason halin da yake ciki, Su Hassan se damunshi sukeyi ina amarya sedai yace Na boyeta banso aganta Lol Daki ya shiga yanata neman numbernta gaba daya ta kashe, Aranshi yace Nazeefa so kike ki kasheni! Bangaren Mubeen kuwa hankakinshi kwance, Yana faran ciki Ameerah ta amsa soyayyarshi Dan haka ya tashi ya shirya, kiranta a waya yai tamai kwatancen gidan yace gashinan zuwa, Tace OK Ba'ai 30mins ba se gashi ya iso gidan, kiranta yai a waya ta fito, bayan sun gaisa yace ya shirye shirye? Tace Alhamdulillah sannan yace Ina Mai kara Godiya da Kika amince da soyayyata, Allah ubangiji ya barmu tare tace Ameen, Mansur ne ya danno motarshi kan layin su Ameerah, tun dada nesa Mansur ya gane mubeen ne a wajen Dan haka ya fasa zuwa wajen Ameerah, aranshi yana wato nan wajen ya lallabo ko? AI gwanda hakan badai Nazeefa na ba kam, Hakanan ya juya yaso Yaje yaji meke faruwa, wata zuciyar kuma tacemai ai kasan abunda Kai Mata, Samun waje yayi yai parking yana mai nadamar abunda yai mata ga wani feelings dake damunshi, shidai ayi ayi a daura auren nan ya huta lol, Da sauri ya tada motar ya karasa gida, Daki ya shiga ya bude fridge din dakinshi ya dakko lemon yasha Dan feelings din da yakeji ra ragu, Hassan da hussaini suka shugo, zuru zuru yai da ido sukam sunsan manufarshi kwashewa da dariya sukai, Hassan yace Ango Ango! Mansur ya harareshi yace wlhi kun fiye sa ido, Dariya sukai sukace Kai kuma ka cika zalama ba! Yace eh din. Barin dakin yayi saboda tsiya suke tamai,Kiran abokinshi yayi Abdallah yace yana Ina? Abdallah yace Ina gida yace ganinan zuwa, Koda yaje gidan Ina amarya yace? Yace ta raka Nazeefa wajen gyaran jiki, Mansur yace OK, dama inata kiran wayartane a kashe kadan kiramun matarka se taba nazeefa mui wayar yace OK, kiranta yai jikinta na rawa da Iya kwarewa cikin salo da yanga tai picking, hello Sweet Heart "Yace yes my love, yace Ina Nazeefa tace gatanan, yace kibata mansur ne keson magana da ita tace OK Kara Mata wayar tai a kunne taji muryar Mansur, Gabantane ya fadi tadai daure suka gaisa seta Fara hello hello banji kamar network prblm Mansur yace please kinajina, Tuni tai cutting din call din, tama kashe wayar Matar Abdallah gaba daya ta ajiye a jikinta tace zai Kira network ne Mansur sororo ya tsaya amma yai ta maza bece komai ba, yace Abdallah zo muje mu amso dinkinmu dazu tailor din ya kirani yace OK Muje sukai tafiyarsu *** Cousins din Mansur ma sunzo maza da mata, A cikinsu akwai Ummie tana bala'in Son Mansur Dan ita Sam bata yarda da Mansur zeyi aureba, cos suna yawan waya komai take so yana Mata, ita ta aza sonta yakeyi...toofaa Koda suka zo gidan kiranshi a waya tai tace Ina kake munzofa, yace da gaske sist tace zanma karyane hardasu Aisha, maryam da rukky, Yace ganinan zuwa yanzun nan naganku Tace OK Ba'ai 30mins ba yadawo, yana shugowa yaga yan uwa sun zauna se hira sukeyi, ummine ta mike tamai oyoyo ta rungumeshi, Gidan aka fara Ango ango Kakarsune ta fito tace Ina angon yace tsohuwa mai ran karfe, kindai qi mutuwa se kinga aurena KO Tace yoo nan gani nan bari danma bance dani za'a daura auren ba, suka kwashe da dariya, tace Ina kishiyar tawa Yace na boyeta saboda irinku, karku goga mata tsufa, tace Yaro a sannu dai, haka suketa hirarsu har dare tayi, Still yanata kiran amaryanshi waya a kashe Hakanan Mansur yai kwana biyu besa Nazeefa a idonshiba, ita ma dukda tanason ganinshi hakanan ta hakura, deep inside her heart itama tasan tana missing dinshi sosai But yazatai hakan shine daidai saboda gudun aikata aikin dana sani, tasan Mansur sosai idan suna haduwa yana yawan Mata maganganu balle kuma yanzu idan yaganta AI kara rudewa zaiyi... Ameerah da Mubeen a yan kwana biyun nan sun bala'in shakuwa Kana ganinsu basai ance maka lovers bane idonka zai baka amsa! *** Ana gobe za'a daura aure Nazeefa ta bude wayarta, tana budewa Mansur ya kirata, Picking tai cikin yanga da kasaita tace hello cikin sanyin murya A gigice yace my princess Sannan yai ajiyar zuciya yace Please kiyi hakuri Dan Allah inganki I'm badly missing you! Tace uhm Bata sake cewa komai ba hakuri yaketa bata sannan tace to sedai kazo anjuma da dare, Wani ajiyar zuciya ya sakeyi yace OK my one and Only Fitowa yai tsakar gida anata hada hada yaci Karo da ummie, Tadan tsuke fuska yace what's wrong my sist? tadan juya taga ba Wanda ke kallonta ta Fara hawaye tace bakai bane! Yace zo muje ki fadamun waya tabamun kanwata, Fitowar waje sukai ya dauka mota suka tafi yace muje kisha ice cream ko? Da yake marainiyace yana sonta sosai dan tana bala'in bashi tausayi, ta zumburo baki tace ni ba ice cream nake soba Kai nakeso yaya! Kai nakeson aura meyasa zakaimun haka Jiyai maganar tamai nauyi, Kasa tada motor ma yayi, tsayawa yai yana kallonta yace ummi, na dauke as a sister nefa, Wannan abun da kikaga inayi nafifitakine akan kowa, Kinsan sauran har haushi sukeji ko? Sannan yai shuru Fashewa da kuka tayi ta sauka a motar taje wajen kakansu, Tanata Mata kuka! Shi ko Binta da ido yai kar fa ta kwanto mai ruwa Dan za'ai drama ne wallahi, Tsaki yayi yai ficewarshi Ummie kuwa in banda kuka ba abunda takeyi, dakyar kakansu ta lallasheta tai shuru Gidan su Nazeefa suma ya cika fal, yan uwa da abokan arziki kowa ya hallara, wajen 4 Nazeefa suka shugo gidan, All eyes on her tai bala'in yin kyau kamar balarabiya, sassanunku tace musu kowa Binta da ido yayi Dan wani kyau datai Shiryawa sukai suka wuce inda zasui bridal shower, Anyi cake, Meat pea, samosa da pepper meat ga drinks na roba da ruwa ansha anci Masha Allah, Kowa Cewa Nazeefa take tayi kyau Bayan sun gamane suka koma gida, misalin karfe 8 na dare saiga Mansur Kiranta awaya yai ta fito da kayan bridal shower din, Kura mata ido yai, Yana Anya kuwa nazeefa ne! Shugowa tai ta zauna fuskarnan babu Fara'a ta gaisheshi, ya amsa yace haba Mata na nace afuwan fa! Uhm tace, juyawa da zatai sui magana dukansu sukaji wani irin a jikinsu, Dan Nazeefa ma kasa motsi tayi, hannunta ya rik'e yace dear kinyi kyau sosai, tsintar kanta tai ta kasa cemai komai, Dayaga batada shirin ma magana, yace kawai nazo nagankine kuma kinyi kyau nizan tafi sai gobe Zamu hadu!!! Gabantane ya fadi tai saurin dago kanta suka Kara hada ido Sauka tai a motar jikinta duk ba wani kwari, Shikam yai tafiyarshi yana smiling Kome yake ayyanawa aranshi shi yasani tana shugowa gida tai kwanciyarta bacci yaqi zuwa itama ko tinanin me takeyi ohon Mata Mansur bayan ya koma gida ya bude part dinshi ya shiga, Samun Hassan da Hussaini yayi har sunyi bacci Dan haka ya shiga dayan dakin ba kowa ya shiga wanka dan wani zafin da yakeji,+ Ummie kuwa sist din mansur itama ba bacci taiba tana ganin ya shiga dakin ta biyoshi, yana fitowa daga wanka yaga mutun a zaune! Kura mai ido tai sosai kamar zata cinyeshi, shikam janyo jallabiyarshi yai Yai kokarin rufe jikinshi Meye haka yace lafiyarki kuwa, meya kawoki nan dakin, fashewa da kuka tai yai maza ya zira rigarshi yazo yana lallashinta akan tai hakuri meke faruwa! Bangaren Nazeefa kuwa kasa bacci tayi don haka ta Kira wayar Mansur, Dubawa yai yaga Matarshi ne yai maza yai picking yace" yes love ya kike, tace lafiya lau ganinan inata missing dinka, Ummie najin haka ta Fara wani uhm uhmm kamar zatai kuka Karaf a kunnan Nazeefa tace Love kai da waye haka? Kame kame ya fara yama kashe wayar, Nazeefa tuni taji zuciyarta na Mata zafi, kiranshi vedio call tayi yaqi picking Hankalin Nazeefa ne yai matukar tashi, tace tabbas sautin kukan Mace naji, Me Mansur yakeyi da mace a daki! Kallon agogo tai taga kusan 11PM Kara kiranshi tai taji wayar ma gaba daya a kashe, Tashin hankali tace tai tagumi tinanin Allah yasa ba wani abun sukeyiba, Wato sai yasa idan yazo yaita kalle Mata jiki, Wato dama Dan is........Wata zuciyar kuma tace don't even think of this Wani Ajiyar zuciya tai se hawaye keta zubowa a fuskarta! Bangaren Mansur kuwa gaba daya hankalinshi ba kwance yakeba Dan ummie budemai wuta tai tace Wallahi seya aureta!!! Shin wacece ummie! Ummie Yar uwar Mansur ne, Da babanshi da mamanta uwarsu daya ubansu daya, cikin yan uwanshi kaf sunfi shakuwa da ummie saboda tanada Dan sauqin Kai, kuma duk Wanda yai mata magana bataji amma tana balain jin kunyar Mansur, Shi kuma Mansur Allah yamai kwarjini, duk budurwan data ganshi setaso ace dama shine mijinta saboda yanada siffar cikakkun maza, In fact he has all the quality that a lady need from a man! Sai yasa mata ke bala'in sonshi So Ummie tun tana karama mahaifinta ya rasu da son Mansur ta taso cos duk abunda take bukata shi yake mata, last year da zasuje hajji yace sam bazai jeba saida ita, haka suka tafi cos Yawancin family sun aza soyayya suke shi kuma deep inside his heart tausayine kawai ba soyayya sukeba Koda zasu taho sedatai wa mum dinta kuka itafa tanason Mansur, tace Mata tai hakuri zatasan yanda zatai kawai Dan hankalinta ya kwanta Ummie, is just 20 years amma tanadan girman jiki, she's wise, gatada ilimi sosai Dan a abroad tai karatu, so Tarbiyarta se ahankali atakaice kenan! *** Nazeefa kasa bacci tai ga wani irin ciwon Kai dake damunta! Kokarin fadin innalillahi wa Inna ilaihir rajiun take tayi tasamu bacci yadan kwasheta Bangaren su Mansur kuwa duk a tsorace yake, karma wani yazo ya gansu, Allah yasa ma su Hassan sunyi bacci daya shiga uku da tsiya Ummie ne ta taso ta karaso kusa dashi, tace muna magana na fada maka sedai ka zaba daya KO ka aureni ko kuma yanzun nan kaga ikon Allah tana magana tana kokarin cire kayan jikinta, WAIT Yace mata, Wani zufa na ketomai, aranshi yana wasu matan fitinane Wallahi, aw shuruma Kai Bari kagani...... Rufe fuskarshi yai yace Zan aureki.....Tace mene? Yace Zan aureki tace zuwa yaushe? Yace zuwa nan da kamar 5 years, wani dariya tai tace banyardaba AI gwanda kawai Kai...... Ranshine ya baci sosai yace Wallahi zanje na sanar da su mummy ga abunda kikace nace zan aurekiba ba shikkenan ba!.. Tadan tsorata saboda bata taba ganin fushin shiba, ajiyar zuciya tai, sannan ta kuramai ido kamar zata cinyeshi Yace saiki fitan mun a daki KO? Murmushi tai tace Zan fita Allah yakaimu goben Zonan yace Mata mezai faru goben? Tace bakomai Yace Wallahi gobene daurin aurena inji wata magana KO wani Abu wallahi zaki sani, Kallonshi tai ta fita batace komai ba Tana fita ya kunna wayarshi, Kiran Nazeefa yai tama Fara bacci tai dauka Zuciyarta na Mata kuna, Tace kungama? Dogon Salati yaja yace ki tsaya Kiji Tace ba abunda zanji malan seda Safe, Ina fatan mata biyu za'a daura maka aure dasu gobe KO? Kasa ma magana yai itakam ta kashe wayar gaba daya a zuciyarta tace za'ai drama ne wallahi Shi kuma Mansur Tsaki yai yace Wallahi wasu cousins din ma bala'ine saisu hanaka farin ciki arayuwa, Senayi maganinki yace Kiran ummie yai a waya cikin Daren yace kinga abunda kikajamun KO? Tace aww bari nadawo semui maganar dakyau Yace wallahi Kika kuskura naga kafarki a part dinnan saikin sani sannan ya kashe waya Yasan halinta sarai zata iya zuwa yai maza yaje inda su hassan suke kwance shima ya kwanta, zuciyarshi duk ba dadi, nai dariya nace Dama kana tsoro Wajen 3AM ne bacci ya kwasheshi, **** Asuba nayi kowa ya tashi aka fara hada hadan daurin aure saboda 9:AM Za a daura anan Chan gidan su Nazeefa suma, Hada hada aketayi abun se Wanda yagani, Nazeefa qin tashi tai wanka tayi, seda Ameerah tai da gaske sannan Ta tashi amma idonta yadan kumbura, nan tsoffin gidan suketa tsokanarta ke kikace kinaso, da bakici kina soba da ba a baki shiba, sedai tai murmushi kawai Bayan an daura aure, Mansur kuwa rawan jiki yaketayi, Ciro wayarshi yai yai Mata text kamar haka you're officially Mrs Mansur, kallon text din tai batace komai ba Ameerah ne ta janyota tace wai meke damunki, kawata please ki sake jikinki Dan Allah, kodai wani abun ne Nazeefa batace komai ba illa kirkiro murmushi datai tace wani abun nake tinawa, amma ba komai Gidan ne ya Kaure da gud'a ga ango ga ango, gaban Nazeefa ne ya fara fadi, fuske wa kawai tai ta fito kallon cikin ido sukaiwa juna ya sakar mata da wani murmushi, jitai ta Kara sonshi Nan aka fara daukan hotono, Nazeefa sai zuwa take tana chanza kaya **** Bangaren ummie kuwa tana gida bakin ciki ya isheta, taso ace Mansur ne ze fara auranta, dakko wayarta tai ta shiga WhatsApp taga Mansur yai status Budewa tai taganshi har yai uploading hotarshi da amarya, yasa Alhamdulillah what a blessed day, Finally she's mine! Kara kure ma Nazeefa kallo tai tace Ina ya Mansur ya samo balarabiya, shegiya tanada kyau fa! Setai comment da hmmmmm she's beautiful Shikam Mansur Se nan nan yake da amaryarshi, 4 suka wuce hall cos da event din da za'ai Daga chan za a wuce da amarya gidanta!!!!!

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 27"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...