SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 25 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 25

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 25

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 25  Nazeefa daki ta shige ta rasama wazata kira ta sanar dashi wannan abun farin ciki, Chan kawarta Ameerah ta fado mata, Nan take ta kirata ta sanar da ita cewa Goben nan za'azo maganar aurenta kuma tana gani bikin ma kadan za'a saka, Ameerah tace Wow amma nayi farin ciki sosai sedai kash Wallahi naso ki aura mubeen cos he's madly in love with you,+ Nazeefa ce ta tabe baki tace ki ki aureshi mana, Ba abunda zanyi Dashi inada Mansur Dina, Ameerah tai dariya tace Nazeefa Allah ya shirya mana ke, Ta zunburo baki tace Ameen, Sannan tace gobe fa kizo please kuma inbadamuwa ki sanar dasu mama suma suzo kunga nan inbanda iyayan su Mubeen bamusan kowa ba, Ameerah tace dear Frnd karki damu zamuzo inshaa Allah, Sannan ta katse wayar, Bajewa akan gado tayi iskar fanka na shiganta ta ko Ina, aranta tana tinanin Ikon Allah kenan wai Yar aiki yau gashi ta zama abun rububi ga maza, Mik'ewa tayi ta shiga dakin ummanta, Babanta ta samu ya dawo Umma na sanar dashi abun farin ciki, Alhamdulillah yace, Dakko wayarshi yayi ya Kira mahaifin mubeen yake sanar dashi akan gobe dukansu suzo, Mansur ze turo Da magabatanshi Alhamdulillah dad mubeen yace sannan ya Kira matarshi da yaranshi duk ya sanar dasu, Mubeen na zaune amma wani kullutun Abu yaji ya tsayamai a zuciyarshi, ji yake tamkar mafarki, Kara tambayan mahaifinshi yake da gaske ne kuwa? Faeez kuwa kallon Dan uwanshi yayi tabbas ya tafka Babban kuskure, Kasa zama mubeen yai, daki ya shiga room dinshi ya kulle, Gabanshi se fadi yakeyi, shi yanzu yazaiyi da son da yake mata, zaro wayarshi yai a aljihu ya Kira number ta, Batai picking ba, Text ya tura mata kamar haka, _Salam zinariyar mata, Wallahi har gobe inasonki, Karki bari sonki ya illatani kiyi hakuri ki aurene ni nafi dacewa dake_ ya tura Mata Nazeefa kuwa shugowa daki tayi ta tino da kawarta dinnan ta garinsu, Kauyen karfi tace bari na kirata na sanar da ita, sai wata zuciya kuma tace mata, in kin Kirata Me zakice mata bayan ba'a tsayar darana ba Dan haka kawai ta fasa kiran nata, alamun Anmata text dagani Dan haka ta bude ta karanta Gabantane yai mugun fadi tace waye ke shirin ruguzamun farin cikina, Calling din number tayi akaqi picking, Mubeen na kallon wayar na ringing ya kasa dauka cos besan mezaice Mata ba Kira take tayi sedata Kira kusan sau 5 sannan aka dauka, Mubeen ne da wani irin voice yace Hello swt Heart, Yana magana ta gane voice din waye Dan haka ta soma magana, koba swt hrt ba, Kai wai wani irin Mutun ne, duk abunda nai maka Baka dandara bako wallahi karka fita harkata sena wulakantaka, Mubeen najin haka yai tsaki, Yace se kinyi regretting wallahi, kisa a wulakantani, idan ma saurayinki ya zigaki ki haka zaki dana sanine Kuma mind you KO kinqi ko kinso you're my sys ta hakika so kiyi duk abunda zaki, Na fita daga rayuwarki daga yau inkinga na sake kiranki Ku kulaki ki mun duk abunda zaki, Badai *SO* ya janyomun hakaba? To dagayau na cire sonki a zuciyata yai tsaki Sannan ya chanza murya daga na fada zuwa sanyi murya yace Kuma naji abun alheri, Allah ya Baku zaman lafiya, Allah yasa ayi damu Tunda ya Fara magana Nazeefa batace komai ba. Yana kashe wayar bin wayar da kallo tayi abun na Daure Mata kai Jikintane ya Fara rawa, itafa tanason Mubeen amma Mansur already ya Riga ya zama jinin jikinta, halaccin da yai Mata ba abun da zata sakamai kamar ta zama matarshi, Tinani daban daban ta tsundama yi, Idontane yai jajir kamar tace ta fasa auren ma gaba daya Haka dai ranar ta wuni ba wani farin ciki da walwala a tare da ita Tsintar kanta tayi tanason karajin voice din mubeen din, wata zuciyata tace karma ki kuskura ki Kira Dan zai Iya fada miki mag ana Bangaren Mansur kuwa se rawan Kafa yakeyi a shi dole ya kusan zama ango, Suhailat da jamila kusa tun a gidan sukai baran baran sukaci mutuncin juna ba Wanda ya sani. bakin ciki kamar ya kashesu, Nan Take nadama ta zo musu inama basu musgunawa Nazeefa ba, araina nace komai rubutacce ne dama inaku ina Mansur turaki hehehe he's a high Class guy, ba irin naku bane lol Washe gari, Tun Asuba su Nazeefa suka tashi suka Fara gyaran gidan, Faeeza kuwa tun da ta sama labarin tun jiya ta tattaro kayanta tazo gidan, Nazeefa taji dadi sosai, Komai tare sukai a gidan, Chan anjuma saiga iyayan Mubeen dashi kanshi mubeen da faeez,+ Gaishesu tayi gaba dayansu suka amsa, sannan ta sauke Idonta akan mubeen Idon da su nazeefa suka hada da mubeen taji gabanta na mugun faduwa, Kallonshi tayi dakyau taga yadanyi kiba yayi kyau irin ustazan nan, ga gashin gemu da saje sun karamai kyau ga wani kamshi da yakeyi Tunda ya shugo gidan bayan sun hada ido be sake kallonta ba, dan yasan she's now someone's property, Dan haka fitama waje yayi ya sama wani garden yasa Earphone a kunnanshi yana saurarar karatul qur'ani Mum da ummanta da faeeza kuwa suna ta shirye shiryen abunda zasu Tara baki, Nazeefa kuma kasa sukuni tayi setaji tanason Ganin Mubeen she's missing him balle kuma abunda tai mai jiya yaji Sam bedace ba, as he said ita Yar uwanshine ko ba soyayya akwai Yan uwantaka na jini sosai, wata zuciya tace kawai ki manta da komai, Ni kuma nace Anya kuwa it's too late ay Fita tayi ta sameshi inda ya zauna tace Sannu da hutawa bro, Idonshi a rufe yanajin dadin karatun alqur'anin bemasan da mutun a wajenba Tabashi tayi yana bude ido sukai 4eyes subanallah yace hade da mikewa Kallo cikin ido sukai sosai, Yaji wani iri yarrr ajikinshi, Hade rai yayi yace meya kawoki nan? Bakya tinanin yan uwan wanda zaki aura su ganki anan? Zunburo baki tayi tace uhmm Ina ruwana to ai Kai Dan uwanane, daga mata Kai yayi yace for sure ni dan uwankine but ya kamata Mu dinga kiyaye wani abun, mikewa yayi ya barta a wajen tabi bayanshi da kallo taji kamar tabishi Mubeen Sam ya chanza anya shi yai mata text jiya kuwa? Wata zuciya tace yes shine mana Yana zuwa bakin gate yaci Karo da Ameerah da mahaifiyarta, Tsugunnawa yayi ya gaisar da Maman Ameerah tai gaba Tana karewa gidan kallo, lalle Masha Allah gidan ya hadu sosai, Nazeefa kuwa bin mubeen tai da kallo tana wajen a zaune, kasa motsi tayi Dan wani kallon soyayya da taga yana wurga ma Ameerah ita kuma Ameerar na murmushi, Nazeefa mutuwar zaune tayi, Jitai kwalla na shirin zubo mata wata zuciyar tace don't cry ki daure Mik'ewa tayi taje taiwa maman Ameerah sannu da zuwa ta rike hannunta sukai cikin falo din, Mubeen kuwa da fita zaiyi amma tunda yaga Ameerah ta shugo ya fasa fita ya koma inda yake ya zauna abunshi ***** Maman Ameerah ta shigo gidan, Nan Nazeefa tai introducing dinta tace mahaifiyar Ameerah ce, kunsan iyayanmu na da bajan class ko Kai Dan wanene Ko Kai matar me kudine su ba ruwansu hira suka shigayi kamar dama ansan juna sosai Maman Ameerah tace Masha Allah gida yayi kyau Allah yasa wqjen zamane sukace Ameen Nazeefa kuwa bata wani sakewa Ameerah fuska kamar da ba saboda tana kishi lol, nikam nace meye na kishi bayan kowa ya sama nashi Bini bini Mubeen na tura ma Ameerah love text ta karanta tamai reply su iyayan ba wanda ya lura amma Nazeefa idonta nakanta Duk taji zuciyarta bata mata Dadi cos she's confuse jitai kamar ta kira mansur tace ta fasa auransa Dan wani zugi da taji Zuciyarta na Mata Suna Zaune dai Chan kusan 1.00PM saukaji horn din motoci mubeen tashi yayi yaje ya bude musu suka shugo da motarsu Nazeefa kuwa tanajin horn din taji dadi a ranta amma daki ta shige Tana fadin Alhamdulillah, Kiran Mansur tayi tace harsunzo fa, Murmushi yayi yace Masha Allah *** Nan iyayan Mansur suka gabatar da kansu akan sunzo Neman aurar diyarsune kuma suna rokan alfarma sunaso ayi bikin nanda Sati biyu Mahaifin Nazeefa tace Eh to amma gskiya yayi kusa ina laifin asa one month saboda shirye shiyen da za'ai Sarki Dad din su hassan yace karsu damu in ma batun kayan dakine da sauransu duk su zasui kawai suna rokan Alfarmane cos Dr yace ai gaggawar Bashi abunda yakeso Dad din mubeen Yace to bakomai, Allah yai mana jagora sukace Ameen An yanke sadakin Nazeefa 500K, Nan ake zube masu shi, Sannan SARKI Ya basu 1Million yace in akwai abunda zata buka ta sukace sungode Sosai Da zasu tafi aka basu sha Tara ta arziki da tukuici 50K suma suka amsa sukace sungode Anyi komai angama ansa bikin Nazeefa da M.T Two weeks, Mubeen yaji dadi amma ta wani bangaren na zuciyarshi yanaji inama shine angon da yafi kowa murna SARKI kuma washe gari suka kuma gida, Koda suka koma ya kirawo su suhailat da Jamila yai musu fada sosai akan mugunta da sukai wa Nazeefa, shifa muganci idan anmaka Allah na daukaka kane, yanzu dai sungani da idansu, Hajiya Bilkisu kuma tace sam suhailat bazata zauna a gidan ba, dama Yar kanwartace tace zata Mai data Chan wajen uwarta ita kuma Jamila tunda tsintar ta akai kota fito da miji ko a aura mata daya daga cikin masu gadin gidan, Hanjin cikinsune ya kada se rokan Su Sarki sukeyi akan suyi hakuri yace Sam inyai magana be chanzawa, To su suhailat da jamila Dama duk Wanda ya aikata sharri kanshi yake dawowa, Se a dau dangana *** Mansur kuwa tunda akasa bikinsu be zama kullun yana kasuwa siyo wannan siyo wanchan Ita kuma Nazeefa Kudin sadakin da aka kawo tace babanta ya siya Mata mota, Lallabata yayi yace AI se a zagemu keda zaki aure yanzu inake Ina sayan mota, Idan Dan kinyi namiki alkawarin Zan Sai miki kuma companies Dina Zan Baki Daya halak malak Wanda kudi zasu dinga shugo miki direct Rumgume mahaifinta tayi, Tace nagode abba, Yace bakomai diyata, Nan take Ameerah ta fado mata arai taji ya kamata fa Su duba Mata, wata zuciyar kuma nacewa karki wani dubata Ita da take shirin auren Mubeen dinki, A'uzubillah ta ambata a zuciyarta ta kawar da shaidan din da yakeso ya hanata aikata alheri Kara gyara zama tayi tace Abba Dan Allah koba yanzuba idan kanada hali inaso ka taimaka kawata dinnan ka gyara musu gida kuma ka temaka musu Da abincin ci Dan Allah Abba Murmushi yayi Dan kyan halin yarshi yana burgeshi akwaita da son temako, Yace karki damu anjuma KO gobe zakuje da mamanki taga gidan Yeehhhh tai tai ihu kamar wata karamar yarinya, seda ihunta yasa ummanta ta fito tace me ake tataunawa bansaniba, Samun waje tayi ta zauna Nan mahaifin Nazeefa ya sanar da ita Komai Alhamdulillah tace aiko Kamar kinshiga raina nima seda nai tinanin abun, Nan sukaci gaba da hira irin happy family dinnan gwanin sha'awa *** Washe Gari Nazeefa da mahaifiyarta sukaje chan gidan su Ameerah, Umma hafsatu ta tausaya musu sosai cos suna bukatan temako Haka ta dawo gida jikinta a sanyaye, Tace Malan munada hali Allah ya hore mana kuma ba wata hidimar yara garemuba gaskiya a chanza musu gidane kawai yafi, inda suke KO ance za a gyara still ya musu kadan Malan Nalado yace tabbas hakane zamu bincika Mu sai musu daya inshaa Allah tace Madallah **** Bangaren Mubeen kuwa son Ameerah se Kara ruruwa yakeyi a zuciyarshi amma tsoronshi daya shine shin zata yarda ko aa, Koma akwai wanda take sone, Allah kadai yasani Yana cikin tinanin nan ne Malan haruna me gini ya kitashi yace gashinan anfara sauke Kayan gidan yazo ya gani Dan haka ya ajiye tinanin da yakeyi yahau motarshi ya tafi Chan filinshi Blocks da yashi da siminti da sauran kayayyakin gidi aka sauke Sun auna a kalla za'ai Classes kusan 30 kasa 15 sama 15 se babban masallaci ga wajen wasan yara da parking space yalwatacce Yace Alhamdulillah Tunda already An Fara foundation na ginin a ciki gaba kawai nan ma'aikata sukaci gaba da aikinsu Bangaren Ameerah itama tasha tambayan kanta akan kallon da mubeen yake Mata danme yake kallonta, Da zaran ta tinashi sedai taga tana smiling for no reason lol Nace Su Ameerah an kamu ba'a saniba Lol Cos time to time yana kiranta suna kuma exchange texts sedai batasan manufarshiba Suhailata da jamila Kuwait a masarauta labari ya watsu akan sharrin da sukaiwa Nazeefa, Kowa be ganinsu da mutunci, kowa takasu yake yanda yakeso Mansur kuwa bini bini ya kira waya yaji ya lafiyar gimbiyarsa take, He's madly in love with her, Love texts kuwa turoshi yake akai akai cos sonda yake Mata kamar ya cinyeta yakeji lol Muje Zuwa

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 25"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...