SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 23 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 23

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 23

- - Post a Comment
SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 23


  Nazeefa ne zaune a 2seater tana mamakin wai sune a wannan babban gidan, Tana cikin tinani faeeza tazo ta katse mata tinanin da takeyi tace dear 6s kije kici abinci mana+ Murmushi tayi tace OK, Dining table suka nufa, Taga abinci Kala Kala, Ga wani kamshi da yake tashi hannu tasa ta dauka cinyar kaza soyayye taci Sannan ta kurba strawberry juice yayi dadi sosai, zama tayi tasha juice din sosai, Mubeen kam duk inda tayi seya bita da kallo cos heart dinshi na beating duk sanda ya ganta, Fita waje yayi ya dakko wayarshi ya kirata yaji wayar a kashe, tsaki yayi sannan ya koma falon Su baffan Nazeefa kuwa da umma hafsatu abincin suma yai musu dadi sosai gashi sun kwaso gajiya dan haka suka zauna suka kwasa girki Nazeefa kuwa tuni daki ta shige, Tana ganin room din tasan bana kowa bane se nata, Dan hanyar shiga room din wani flowers tagani tasan confirm natane, dakin tabi da kallo taga komai sabo! Ga Dan gadonta madaidaici ga wardrobe harda wajen karatu kamar dakunan yaran yan kasar waje, Fadawa a gadon tayi hade da cewa Alhamdulillah, Silar gidan aiki yamun Rana and na koya abubuwa da yawa, Allah kasa mucika dakyau da imani, sannan ta tashi zumbur kamar wacce aka tsungula Toilet ta nufa naga ta wangale baki, ita tunda take bata taba ganin toilet mekyan haka ba kawai taji tana sha'awar yin wanka Dan haka ta shige ta cire kayan jikinta tai wanka ta fito ga mayuka Kala Kala nan ta shafe jikinta se kamshi takeyi Nan ta tino kayantafa kamar na dakin Ummanta, Dan haka ta kwallawa Faeeza Kira Tace Dan Allah ta dakko mata karamin akwatin kayanta na ciki tace Ok nan take ta dakko Nazeefa ta sa wani kaya jallabiya irin na 20K dinnan Wanda mansur ya siyo Mata, Yar Karamar jakarta ta dauka, ta fesa turare sai ta yafa Dan karamin gyalen, kallo daya zakai Mata kasan ta hadu, dukda duguwar rigar da tasa be hana fitowa da shape din jikintaba.. Tana fitowa suka hada ido da mubeen, Gabantane yai mugun fadi amma ta fuske, Zuwa tai kan dining table Tacewa iyayanta zataje wajen Kawarta Ameerah sukace OK Sai kindawo karki dade, Su Mubeen kuwa da faeeza sun zama yan kallo _uhmmm rayuwa kenan fa na gaba ya koma baya duniya makaranta_ Tunda ta fito mubeen Binta da kallo yayi yaji Sam bazai Iya hakuraba, kararaf yayi yace tom muje in kaiki Aranta tace Za'ayita kuwa, Umma hafsatu ne ta katse Mata tinanin da takeyi tace kije yakaiki din, Tai maza ta washe baki tace OK Muje tom aranta kuwa ita kadai tasan me take ayyanawa Fitowa sukai ya bude mata sit din gaba yace ta zaune tace nop, you're my driver so baya Zan zauna KO so kake in zauna a gaba a aza budurwanka ne? Smiling yayi Dan shima yasan Akwai magana a bakinta Fita gidan sukai ya hau kan titi ya Fara driving Ahankali, kallonshi tayi tace malan driver meye haka kayi Abu da jini mana kana tuqi kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki Tsayawa chak yayi yace bazan tuka motar ba kuma ya kulle Ko Ina dan yasan ba karamin aikinta bane ta bude tace zata fita Rantane yai matukar baci tace Kai wani irin wahalalle ne nace maka banasonka banasonka sai shigemun kkeyi ko to wallahi ka saukeni ko na fasama glass din motan da takalmina tana magana tana kokarin Cire takalminta Dayaga da gske take tuni yai unlock din motor ta samu ta fito tana wurga Mai harara Shikam mubeen na tsaye ya rasa irin zuciyar Nazeefa Mansur kuwa se juyi yake a kan gado ga frnds dinshi maza da mata harda Abdallah a ciki zagaye dashi, Yan matan wajen se iyaye suke ko akwai wanda zaice yanaso cos duk wacce kuga gani a wajen son Mansur turaki takeyi *** Nazeefa kuwa napep ta Tara tace akaita gidansu Mansur, tana zuwa tace me nepep ya jirata tambaya zatai, Zuwa tai ta tambaye gate man din wani hospital aka Kai Mansur Da yake ya ganeta nan take ya sanar da ita sunan Hospital din harda room din da yake tace OK nagode Yima me nepep din magana tai yakaita hospital din yace angama Tafiya kadan sukai suka Isa asibitin Ciro 1000 tai ta bashi yace ga chanji tace kabaari kawai, yanata jinjina mata yana sa mata albarka tafiyan da befi abaka 250 amma tabashi 1000 lalle yau akwai sa'a Da sauri ta shiga asibitin hankalinta a tashe, batasan wani yanayi zataje ta sameshi ba Kai tsaye ta shiga room din da aka kwatanta Mata, Sallama tayi gaba daya yan dakin suka juyo suna kallonta, Wani kamshi kawai yake tashi, ahankali ta karasa gadon da yake kwance Riko hannunshi tayi tace Mansur, idonshi a kulle, jiyai anrike hannunshi ya fara bude ido ahankali Bude idon da zaiyi kenan sumai 4 eyes da Muradin zuciyarshi Kashe mai ido tayi ta sakar Mai wani murmushi, yunkurin tashi yayi tamai alamu da Nooo ya kwanta kawai Abdallah kuwa kallonta yayi yace sannu da zuwa madam Tace yauwa amininmu ya jikinmu? Yace jiki da sauqi hajjaju Gaba daya yan wajen maida idonsu sukai wajen Nazeefa se a lokacin suka kare mata kallo sosai gaskiya yarinyar ta hadu, Matan wajenma sunsan ta hadu bare mazan wajen Watace Ta ce Abdul 6ter mansur ne KO? Murmushi kawai yaimata yace she's more than a 6ter Kowa yai tsuru tsuru yanason jin dangartakar dake tsakaninsu Mansur da nazeefa kuwa kallon juna suke Kamar zasu hadiye kansu, Dan mansur ya ma manta beda lafiya wani Iron kallon yake jefa mata hade da kashe ido Abdallah ne yadan buga gadon da Mansur yake kwance Se a time din ya tina akwaifa mutane a dakin🤣 Kowa a dakin tsuru tsuru yayi yanason jin wani dangantaka ne ke tsakaninsu+ Nazeefa ajiye jakarta tayi, Sannan tacewa Abdallah yaci abinci kuwa? Yace aa rabonshi dacin abinci tun jiya fa OK tace Ina abincin? Aka nuna Mata, dakkowa tayi ta fara feeding dinshi ahankali, kowa abun ya Bashi mamaki, seda ta tabbatar ya koshi sosai sannan ta bashi ruwa hade da magani tasha tace please yana bukatan hutu kubarshi ya huta Watace tai dariyar sheqiyanci tace woo Ina ganin soyayya, halan ke budurwansa ce KO? Kafin Nazeefa ta bata amsa Mansur karaf ya amsa Mata yace ba budurwa ta ba ce, jinin jikina ne kuma inshaa Allah ita zata zama uwar yarana very soon, Matan sunajin haka suka Fara zunbure zumbure, daya bayan daya sukabar dakin Dan takaici da bakin ciki, sauran frnds dinsu maza kuwa sukacemai congrats daga gani ya sama abokiyar rayuwa Dan tanada hankali sosai Anan ta wuni se chan dare ta koma gida, ganinshi datai kamar an soka mata kibiyan sonshi itadai tana kaunar bayan Allah nan *WASHE GARI* Mum da dad din Mansur suna asibitin sai Abdallah, Dad ne yace Yau zamui baki fa daga masarautan Mu ta Chan tunda na fada musu Mansur beda lafiya hankalinsu ya tashi, Mansur yace" Abba za azo dasu Hassan da hussaini amma KO? Dad yai murnushi yace yes hardasu jamila da suhaila zasuzo wacce naso a hada auranku Mansur dai na kwance bece Komaiba, Amma gaba daya yaji gabanshi na mugun fadi Sallama sukaji, gaba dayansu suka waiga, Nazeefa ce ta shugo sanye da hijab har kasa se hannunta rik'e da basket Ahankali ta karaso ta tsugunna tagaisheshu, Dad da mum suka Kara tabbatar da natsuwan yarinyar Sukaji ta Kara shiga ransu sosai, Ahankali tace yame jiki? sukace jiki Alhamdulillah, Tace Allah Kara sauqi sukace Ameen Suna zaune kowa yayi jum a dakin, wayar dad ne yai ringing yana dubawa yaga SARKI, kallon maman Mansur yayi yace gasunan sun karaso, Nan take fuskar Nazeefa ya chanza dan ta tsana taji gabanta na fadi tasan surely wani abun ne zai faru, Kallon mum tayi tace zantafi mum Maman Mansur tace bazakije KO inaba ki tsaya yan uwan Mansur zasuzo Ku gaisa mana, Daurewa kawai tayi tace OK ta sama waje se innalillahi wa Inna ilaihir rajiun take ambatowa a a zuciyarta Sallama Sukaji suka amsa sannan mutanan suka shugo Kallo daya nazeefa tai musu tagane wanchan Sarkine, da Hajiya bilkisu da Hassan da Hussaini da Jamila da suhaila, Mikewa tayi tare da fadin innalillahi wa Inna ilaihir rajiun Mezan gani! Gaba daya suka maida hankalinsu wajenta, Hajiya bilkisu ne Ta kalleta tace kamar nasan fuskar nan Dukansu suma sukace tabbas sunsan face dinnan amma sun manta inda suka sansu Nazeefa hawaye ta fara tace tabbas kunsanni, NAZEEFA Ce wacce Sarki ya kawoni gidanku Jamila Da suhaila Nan suka Fara tari suna zare ido, Nazeefa tace hmm Suhaila kenan da jamila Hajiya bilkisu shuru tare tana mamakin chanzawan Nazeefa, Hassan da Hussaini kuwa suma kallonta sosai sukai sukace Nazeefa kece Ashe zamu sake haduwa wallahi munyi kewarki sosai meya kawoki nan wajen dama kinsan mansur ne? Iyayan Mansur kuwa suna tsaye suma sukace duk bamu gane komai ba dama kunsan tane? Nazeefa ta sake kallon suhaila da nazeefa, Nan take sukai tsure Tsuru, Hajiya bilkisu kuwa hararar Nazeefa ta so mayi tana makira, Allah ya Isa tsakanina dake Mansur ne ya mike daga kwanciyar da yake yana Mum Metai miki Nazeefa ce Tace Eh din itafa, kaga wannnar yarinyar! Nazeefa tace Alhamdulillah, Hajiya kiyi hakuri Bazan daukar kazafin da wa ennan makiran yaran nan suka kulla mun ba Nan Mum Mansur tace meke faruwa ne dama kunsan tane? Sarki dai na zaune, Yana mamaki Nazeefa tace Mum Bari kiji duk abunda ya faru yanzu inada bakin magana Hajiya Bilkisu tace karku saurareta karya takeyi Sarkine yai Mata magana yace, Tai shuru, Mum Mansur ita kuma Tace Fada mana meye faru? Mum mansur ne tace Nazeefa fada mana meya faru? Nazeefa ta Fara ba mum din Mansur labari tace mum kintuna time din Da mansur ya kawoni gidanku? Mum Mansur tace na Tina Nazeefa,+ Nazeefa tace ai daga gidansu nake, ta nuna suhaihat da Jamila tace Su sukai mun sharrin wai na sace gwalagwalan Hajiya, Mum Mansur dafa kirji tayi tace Subhanallah, how comes kikaje gidansu? Nan Nazeefa ta bata labarin Gwagwar mayar da tasha agaban Su suhailat, jikinsune ya fara rawa, Hassan kuwa harararsu yayi yace munafukai Anan dai Nazeefa ta basu kaf labarinta, Sarki yai shuru yana nazarin Wani Abu Hajiya Bilkisu kuwa hawayene ya zuba a idonta, Tace yanzu kina Ina Nazeefa? Nazeefa tace da temakon Mansur naga iyayena Ina tare dasu, Mum Mansur kuwa ta qarajin tausayin Nazeefa Ashe yarinyar Tasha wahala, Mum mansur ne tace Hajiya Bilkisu infada miki Ashe babanta babban Dan kasuwane qilama kisanshi, Wani Alhaji Nalado Wanda duk garin nan shine Me shugo da flour mekyau Chan shekarun baya? tace eh Naji shine mahaifinta? Mum mansur tace shine kuwa, Sarki innalillahi wa Inna ilaihir rajiun yace, yarinya kiyi hakuri ki yafe mana Hajiya bilkisu ma Matsowa kusa da ita tayi tace Yar Mu please kiyafe mana, Wani Ajiyar zuciya Nazeefa tayi idonta ya cika da kwalla, tace nayafe maku Hajiya ai ba laifinku bane laifin Jamila Da suhailat ne, Duk Su suka sa muku kiyayya na a zuciyarku Nan Jamila da suhailat kunya ta rufesu kamar su nitse kasa, Sunataba Nazeefa hakuri suma, Hussaini yace munafukai a chan gida bana tabajin kuna fadan akan kun siyar da wani gwal ba kuna fada akan kudi da nazo na tambayeku ai nunamun kukai ba komai, yanzu gashinan Asirinku ya tono Nan suka Fara inda inda munafukai sak cos magana ma sun kasa, Mansur ne yai wani ajiyar zuciya gaba daya hankalinsu ya koma kanshi, Kakarin amai yake tayi shi beyi aman ba kuma be dena kakarin ba Seda aka Kira doctor sannan ya dubashi yace sunyi yawa a dakin a arage surutu, kuma yanason bacci Dan haka gaba dayansu suka fita, Reception suka sama waje suka zauna dukansu kowa da abun da yake sakawa a zuciyarshi Nazeefa ce kadai da Abdallah a dakin, Riko Hannun Mansur tayi tace please ka kwantar da hankalinka, kar abunda kaji sunmun yasa hankalinka ya tashi, ni na yafe musu har abada kaji habeebe nah Murmushi yayi yace are you sure tace yes, ni kawai abunda nakeso dakai shine ka kwantar da hankalinka I'm yours forever inshaa Allah, Kara riko hannunta yayi ya damke sosai yana mata wani irin kallon ga eyes dinshi kamar yanajin bacci, Itama kashemai ido tayi tace Sorry my love, KO zakasha ruwane, wayau tamai cos rike mata hannun dayayi gam tasan be daceba Daga kai yayi ta dakko Mai ruwan Swan medan sanyi ta sa Cup ta bashi, Yasha sosai yace love naji Dadin ruwan nan fa cos kirjina har yadanyi sanyi, tace yeah nasan kanada bukatane Kuma KO lafiyanka lau is good kadinga shan ruwa akai akai Bin lebanta da ido yayi yace Wow hakane gimbiyata Tace how are you feeling now yace Alhamdulillah tace Masha Allah Abdallah ne na gefe yana kallonsu, Tsantsan so sukewa junansu, Nazeefa a hospital din ta wuni se Chan yamma ta koma gida Koda ta koma Gado ta fada se tinanin MAN Dinta takeyi, time din kuma Su mubeen sun koma Chan gidansu Umma hafsatu ne da malan nalado suna Zaune a falo suna shan A.C se TV a kunne kana ganinsu kasan suna cikin jin dadi Nazeefa ce ta fito sanye da doguwar riga kanta ba dan kwali se wayarta a hannu, Gashin kanta ya kwanta, Zuwa kusa da ummanta tayi tace Dan Allah gobe inaso gobe kuje Ku gaida Mansur please Malan Nalado ne yace mamata ina dankwalinki taba kanta tayi tamarairaice kamar Wata karamar yarinya tace laaa bansaniba Ashe ya fadi Babanta yace OK kidinga kula dai, Kuma Allah yakaimu goben zamuje da murna ta tashi ta shige Daki ta fada kan gado, kawarta Ameerah ta Kira tace kee nadawo fa, gobe pls ki shirya zamuzo Mu daukeki Love of my life ba lafiya Ameerah tai wani ihu tace yaushene nai tinaninki Ashe kindawo, Allah yakaimu goben, Kawata Tace Ameeen Nazeefa kuwa bayan ta fada gado, lafewa tayi ta bude gallery din wayarta, kallon pics din mansur ta fara tsintar kanta tayi tana smiling sosai ahaka bacci ya kwasheta Muje Zuwa.

Post a Comment for "SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 23"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...