Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAMUWAR GAYYAH CHAPTER5

RAMUWAR GAYYAH CHAPTER5

- - Post a Comment
RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 5
K'arfe biyar da rabi sawwam yafarka, ummulkhair ya kalla wacce ke kwance gefenshi ta cure jikinta wuri guda,+ Hannunshi yakai kan goshinta ya taba, duk zufa ta tsatssafo mata kamar wacce take zaune atsakiyar rana, Tashi yayi ya shiga toilet ya tsaftace jikinsa yafito, zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi kamar kankara sai zallar farin ciki dake wanzuwa acikinta marar yankewa, Idonshi akan khairi ya dauko kayanshi yasaka, gaban gadon yaje ya dagata ahankali ya gyara mata kwanciyarta, fuskarta yabi da kallo yana murmushi saboda baccinta take hani'an kamar ta shekara batayi ba, Sai da yabata wani zazzafan kiss a kumatunta sannan yaja bargo ya lullubeta yafita masallaci. Karfe shida da yan mintuna yadawo cikin dakin amma har lokacin ummulkhair bata tashiba asalima ko juyi bata yiba tana nan a yarda yatafi yabarta, Gefenta yaje ya kwanta ya dagota zuwa jikinshi ya rungumeta, "My lonely yau kin tabbatar da abinda nadade ina fada miki cewar zan baki daddadar rayuwa duk ranar da muka kasance tare, Gashi yau Allah cikin jin kansa ya nuna mana wannan lokacin, Allah yayi miki albarka khairi,Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya albarkacemu da 'yaya masu albarka, Ina tsananin sonki ummulkhair and bazan taba daina sonki ba har karshen rayuwata, babu abinda zai rabani dake...." Sharrr hawaye suka fara bin kumatunsa, ita dai khairi kamar a mafarki take jin maganganunsa kasancewar bacci take yi sosai, Rungumeta yayi sosai ajikinshi har bacci ya sake tafiya dashi bashi ya tashi ba sai da misalin karfe tara saura, Mamakine ya kamashi ganin har lokacin ummulkhair bata tashiba, tashinta yafara yi ahankali, "My lonely..., my lonely rana tayi bakiyi salla ba.." Sake gyara kwanciyarta tayi ta juya baya, bai hakura ba yasake komawa gefen datake yana shafar fuskarta, "Tashi mana yanmata na..." "Um, um ka kyaleni" "Sai yaushe zaki tashi to?" "Yanzu..." Tabashi amsa har lokacin bata bude idanuwanta ba, Ganin bata da niyyar tashi yasashi kyaleta yafita, motarshi ya dauka ya nufi gidansu, lokacin da yashiga ko dakinsa bai shigaba ya nufi falon Mami, tana cikin kitchen ita da mai aikinta suna hada breakfast, Daga bakin kofa ya tsaya yafara gaida mami, kallo daya zaka yiwa fuskarsa ka fahimci irin tsananin farin cikin da yake ciki, "Sawwam har ka tashi?" Mami tace dashi tana fara'a, "Ehh wallahi Mami" yabata amsa yana sosa keyarshi saboda yasan mami ta rigada ta fahimci komai, "Mami kawo natayaki..." "To zo ka debi wannan flasks din ka kai kan dining ka jera" Da murmushi akan fuskarshi yakarasa cikin kitchen din yafara diban flasks din yana kaiwa kan dining, mami sai kallonshi take in banda murmushi babu abinda yake yi shi kadai, Girgiza kai Mami tayi ita dinma wani farin cikine yake ratsata domin farin cikin sawwam shine farin cikinta, Tare suka kammala shirya breakfast din har dad ya shigo cikin shirinsa na zuwa office, Fuska dauke da fara'a da walwala sawwam ya gaidashi, shi kansa dad din sai da yayi mamaki saboda yajima baiga fara'ar sawwam haka ba, Cikin farin ciki sukayi karin kumallon suka kammala, lokacin da dad zai fita har farfajiyar gida sawwam ya rakashi, Yana ganin dad yafita yakoma wurin mami, "Mami zanje natafi, nabar ummulkhair ita kadai" Murmushi mami tayi tana harhada masa food flasks acikin wani dan madaidaicin kwando, "Lafiyarta dai kalau ko?" "Mami lafiya lau take" "To ka gaisheta dakyau, ga abincin" Karba yayi yajuya ya fita yana fadin, "zata ji mami". Sawwam bai jima da fitaba ummulkhair ta tashi, zama tayi tana kallon ko ina nacikin dakin da kallo, take kuma abubuwan da suka faru suka rinka dawo mata daya bayan daya, Mikewa tayi ta lallaba ta shiga bathroom ta yi wanka bayan ta gasa jikinta da ruwa mai zafi, Fitowa tayi daure da towel ta nufi dakinta, kaya tasaka riga da skirt na shadda kalar ruwan kwai, Salla tayi sannan tayi musu addu'ar samun zaman lafiya itada mijinta, tana idarwa ta mike ta dan gyara fuskarta tafita falo, Abincin da sawwam ya kawo mata jiya shi ta ciro daga cikin fridge, ko dumamawa batayi ba ta zauna taci ahaka saboda yunwa takeji, Kan doguwar kujera takoma ta kwanta bayan ta kammala cin abincin, bata jima da kwanciyar ba sawwam ya shigo hannuwansa dauke da kaya, Kayan ya ajiye akan center table yana kallonta, "Ba zakizo kiyi min sannu da zuwa ba?" Zaune ta tashi tana murmushi sai dai takasa hada ido dashi, "Sannu da zuwa..." Kafada ya makale alamun bai yarda ba, "Nidai sai kinzo kinyi min sannu da zuwa sannan zan amsa" Murmushi tayi idonta yana kallon kasa gashi takasa tashi taje inda yake,karasawa yayi ya zauna akusa da ita tareda kamo hannuwanta yarike cikin nasa, "Kin tashi?"kai ta daga masa, "Kinsha bacci.." Kallonsa tayi sai kuma tayi saurin kawar da kwayar idonta kafin su hada ido dashi, "Ga abinci mami ta bayar akawo miki, taso muje nabaki" Girgiza masa kai tayi, "na koshi" "Me kikaci?" "Abincin jiya" Murmushi yayi ya tsaida idonshi akan fuskarta ya lura duk maganar da take masa tana yine idonta akasa batare data kalleshi ba yasan kunyarsa takeji yanzu, niyyar tsokanarta yayi yakai hannunshi kan zif din rigarta, cikin sauri ta rike hannunsa tana kallonsa, "Meya faru?" Yace da ita yana murmushi kasa kasa, "Babu komai" "To zomuje ki kwanta ki huta" Kai ta girgiza masa alamun a'a, murmushi yayi ya shafi gefen fuskarta, "My lonely matsoraciyace duk kinbi kin tsorata daga jiya kadai, sannan wannan kunyar babu inda zata kaiki garama ki cireta" Bai barta tayi magana ba ya mikar da ita tsaye yakamata zuwa bedroom dinta, kwantar da ita yayi ya zauna agefenta yana yi mata tausa har bacci ya dauketa yana ganin haka shima ya kwanta akusa da ita. Ranar dai tare suka wuni agida baije ko inaba dama ko office bashida niyyar zuwa, sai da dare yayi sannan suka fita tare, gari suka dan kewaya sannan yadawo da ita gida ya koma gidan mami, sai da yajira suka ci abincin dare tareda dad,har sai da yaga dad din yashiga part dinsa sannan yayiwa mami sallama zai tafi, "Ka gaisheta, sannan dan Allah sawwam ka kula da ita sosai kaji, kaga dai irin halaccin da tayi maka" "Insha Allah mami zan kiyaye" Lokacin da yaje gidan yasamu har ummulkhair ta yi shirin bacci ta kwanta adakinta, "Badai har kinyi bacciba?" Yafada yana shafar kumatunta, "Nadai fara, kadawo?" "Ehh nadawo, tunda kin kwanta bari naje nayi wanka" "To sai da safe" tafada tareda gyara kwanciyarta, "Wanne irin sai da safe? Ai zan dawo, ko yau korata kike?" Shiru tayi tana jinsa bata amsa ba, hannunta ya kamo, "Zo mutafi dakina" Kafada ta makale, "a'a" "Wai yau abin tsoro nazama ne? Dakin nawa ma tsoronshi kike?" Sake kwanciya tayi tana turo baki, "Zo mutafi maza my lonely dina..., Allah muna zuwa baccinki zakiyi" Da lallami da komai yasamu ta tashi tabishi zuwa dakin nashi, wanka ya shiga ita kuma ta hau kan gadonshi ta kwanta, kafin yafito daga wankan har tayi bacci,murmushi yayi ya shirya ya matsa kusa da ita ya rungumeta, "Shine kikayi bacci kika barni baki jirani nazo munyi hiraba" "Indai wannan hirarce nayafe" yaji tabashi amsa, murmushi yayi ya sake kankameta tamkar zai mayar da ita cikin kirjinsa. Ahaka har sukayi sati daya, kullum mami ce take basu abinci shi dad ma sam bai san sawwam baya kwana agidan ba saboda yana ganinshi kamar da, sai dai wani lokacin idan ya nemeshi cikin dare sai mami tace yayi bacci saboda yasha maganin mura, sam dad bai taba ganewa ba shiyasa hankalinsa ya kwanta musamman ma da yaga shi kansa sawwam din shima hankinsa ya kwanta. Tunda ummulkhair tazo gidan yau kwana goma kenan sai yau sawwam zai fita office amma da kullum agida yake wuni suna soyayyarsu shida khairi idan dare yayi kuma sufita su zagaya gari, Yana kwance yana bacci ta shigo taci kwalliya sosai, daga shi har ita har sunyi kiba a yan kwanakin da suka dauka tare, Bakinshi ta tsotsa da nata tana dariya, "sahibi kafasa fita aikin ne?" Kamota yayi zuwa jikinsa ya rungumeta, "ban gama baccin bane" "To katashi kayi wanka ko ka makara" Jin zata zame ta gudu yasashi bude idonshi, "ina zakije?" "To bakaine kaki tashiba" Tashi yayi yana kallonta, "natashi, shikenan?" Kai ta daga masa taja hannunshi, wanka ya shiga ya fito ta shiryashi yafito fes dashi, breakfast ta gabatar musu sukaci sai da ya sammata soyayyarsa mai tsayawa arai sannan ya mike domin fita, babu zato yaganta tafara zubar da hawaye, Rungumeta yayi yafara lallashinta, "My lonely nima ba ason raina zan tafi nabarki ba amma sai dai zanyi miki albishir guda daya, kema acikin week dinnan zaki koma makaranta" Tsalle tayi ta rungumeshi ta fara kissing dinshi a wuyanshi, "Nagode sahibina, Allah ya kiyaye hanya.." "Shikenan kuka yakare..?" Yafada cikin tsokana, murmushi tayi ta daga masa kai, bayanshi ta dale, ahaka yafita tana goye abayanshi har sai da yaje wurin motarshi sannan ta sauka tana dariya, shima dariyar yake ya bude motar ya shiga, "Zan iya tafiya?" Ya tambayeta, kiss tayi masa a baki tana dariya, "Zaka iya tafiya Allah ya tsare min kai har ka dawo" "Amin my lonely, sai nadawo" Tana tsaye tana kallonsa har yafice daga gidan, ciki takoma duk sai taji gidan babu dadi saboda sawwam baya nan ita sai yanzune ma tasan ta shaku dashi ashe da shakuwar da sukayi a makaranta ba shakuwa bace shirme ne, yanzune suka shaku shakuwa irin ta zuciya da zuciya, yanzune take sonshi soyayyar da Allah ne kadai yasan adadinta, Tana zaune tanata missing dinshi har yamma tayi, ta idar da salla kenan taji sallamarshi, fitowa tayi ta rungumeshi sosai tana murna,kallonta yayi tayi kwalliya tayi kyau sosai abinta, Kugunta ya rike yana hada fuskarshi da tata, "Kinyi bakuwa" Saurin sakinshi tayi ta kalli bayanshi, alawiyya tagani tsaye tana murmushi, da gudu ta tafi ta rungumeta, "Ashe tare kuke? Wallahi ban ganki ba" "Dama taya zaki ganni" alawiyya tafada tana dariya, zaunar da ita ummulkhairi tayi ta kawo mata abinci, sannan taje ta gabatarwa da sawwam shima nasa abincin,hannunta yaja ya hadata da jikinsa, "Nifa ke kadai nake bukata ba wani abincin ba" ido ta kwalalo, "Haba sawwam bakaga munyi bakuwa bane, kabari mana tatafi" Dariya abin yabashi saboda yanda yaga ta zaro ido, "To naji..." Cakulkul yafara yi mata tayi saurin kwacewa tagudu tana dariya, Wurin alawiyya takoma suka fara hirar yaushe gamo, "Khairi kinyi kyau wallahi kuma gashi kinyi kiba abinki" Dariya ummulkhair tayi, "nikuma wallahi bana ganin kibar, shima sawwam kullum sai ya tsokaneni wai nayi kiba" "Gaskiya kinyi kiba, shima sawwam din naga yayi kiba, da alama kuna kulawa da junanku" Dariya ummulkhair tayi suka cigaba da hirarsu da alawiyya,har dare suna tare sai da akayi sallar isha sannan sukaje itada sawwam suka mayar da ita gida. Acikin satin ummulkhair takoma makaranta tafara zuwa lectures, kullum tare suke fita da sawwam yasauketa sannan yawuce office, Gidan mami kuwa tunda ta tare bata jeba saboda suna tsoron kar dad yaganta, ganin haka yasa ita mamin ta shiryo tazo, basu jima da dawowa gidan ba suna kitchen tana girki sawwam yana tayata saiga mami tazo, ko sallamarta basuji ba saboda hira suke yi, tana bashi labarin wasu yanmata da sukayi fada akan saurayi a makaranta yau, "Kema fa kin taba fada akaina" yafada cikeda tsokana, "Ai ko yanzu da kake mijina bazanyi fada akanka ba balle da a matsayinka na saurayi" Dariya yasaka "wallahi karya kike, yanzu idan nakawo miki budurwata da dambe zaki kamata" "Haba dai sai kace wata gara.." "Allah kina kishina sosai nasani, duk daren duniya fa sai kin fada min kalmar so sannan kike yin bacci, au ashefa wani lokacin bakya sanin kina fada, jiyama dan bakiji abinda kika fada bane ko kina son ji in fada miki? "Banda sharri dai" tafada tana murmushi, "Babu wani sharri, kedai kam nasan idan baniba sai rijiya" Kafin tabashi amsa ya lallabo ta bayanta ya rungumeta yana yi mata rada, "nima idan bake ba sai rijiya, ki gama girkin nan muje kibani tukwici.." "Haka dai.." Tafada tana tureshi, "Idan kika hanani wurin yanmata na zan tafi, ohh Allah sarki khairina rannan da kika yimin rowa nace zan je wurin yanmatana fa rudewa kikayi harda kukanki kina cewa dan Allah sawwam karkaje wallahi zina babu kyau, dan Allah kar kaje su bata min kai..." Ya karashe maganar yana dariya, Dariya itama tayi ta debi ruwan da take fere dankali ta watsa masa, "Kuna inane?" Suka jiyo muryar mami, "Lahh mamice tazo, dan Allah dauko min hijabina" Kafada ya makale yana dariya, "sai dai kifito haka" Rikeshi taje yi ya goce ya gudu yana mata dariya domin wata yar rigace kamar shimi iya cinyarta kalarta pink, "Mami sannu da zuwa" sawwam yafada bayan ya zauna akusa da mamin, kallonsa mami tayi dagashi sai short nicker da riga mai gajeren hannu, "Yawwa sannu ina ummulkhairin?" "Mami taki fitowa wai kunya take ji" Zaninta dake kan kujera ya dauka ya mika mata cikin kitchen din ya fito, dole haka ta daure tafito, kallo daya mami tayi mata ta fahimci tana dauke da juna biyu amma su dayake yarane duk cikinsu babu wanda yasani, "Mami sannu da zuwa" ummulkhair tafada cikeda kunya, "Yawwa sannu, aiki ake tayine?" "Ehh mami" Mikewa tayi ta shiga daki ta sako hijab tafito ta kawowa mami kayan motsa baki, Cike da kunya ta gaisar da mami, cikin fara'a da kauna Mami ta amsa mata tana tambayar ta babu wani abu ko, "Babu komai mami" ta amsa cikin jin kunya, shikuma sawwam dake kusa da ita sai mintsininta yake tayadda Mami ba zata ganiba,hannunshi ta buge ta mike ta canja wuri tana harararsa, Mami bata wani dadeba sosai tace tafiya zatayi saboda dama ganinsu kawai tazo yi, tare suka fito suka rakota, kallon sawwam tayi tace, "Ina fata dai baka matsa mata ko? Kaga juna biyu gareta idan kafiya matsa mata dayawa to cikin zai iya zubewa..." Dukkaninsu mamakine ya kamasu, ga kunya mai nauyi data rufe khairi, "Mami ciki kuma?" Yafada cikeda mamaki, "Kai baka saniba ba ko saboda kana shirme, juna biyu gareta mana, Allah dai yaraba lafiya" "Wallahi mami bata gaya minba boye min tayi sai yanzu nasani da kika fada" "To Allah yaraba lafiya, kuma ku kula sosai banda shiririta" "To mami..." Ita dai ummulkhair takasa magana sai sawwam ne kadai ke amsawa, har mami tatafi bata bari sun kara hada idoba, Yana ganin fitar motar mami yaja hannunta suka koma ciki, "Shine kika boye min?" "Wallahi nima fa ban san dashiba nidai kawai nasan tunda nazo gidan nan banyi period ba" Rungumeta yayi yana murmushi, nan kuma yashiga tsokanarta.... "Maman yan biyu ce ko?" "Yan uku" tafada tana turo baki, "Idan ma hudu kika Haifa min wallahi ina so, gaskiya ke hadamammiya ce har kinyi ciki, koda yake nagane bakya son wata tazo tafiki samuna ko?" Tureshi tashiga yi, "ni kyaleni naje nakarasa girkina" Tashi yayi yabita yana murmushi, "mu karasa tare dai tunda dama tare muka fara" Tana jinshi ta rabu dashi sai murmushi da takeyi aranta tana ta mamakin wai har sun kusa samun baby ita da sawwam lallai abin babu wuya awurin Allah... *** "Yau zanje nagano yarinyar nan" mahaifin khairi yafada yana gyara babbar rigarsa, Mama dake tsaye kamar zata saka kuka tace "Allah ya kiyaye hanya, kagaisheta" "Zataji" shine kawai abinda yafada yasa takalminsa yafice,binsa mama tayi da ido amma duk zuciyarta babu dadi saboda rabata da yarta da akayi, Karfe 12 suka shiga garin gombe, kai tsaye gidan dan uwansa suka wuce sunci Sa,a sun sameshi agida bai fita ko inaba, Saida suka gaisa aka dan jima sannan abban khairi yadubi yayansa, "Ina ita wannan yarinyar take? Kallonsa yayansa yayi, "wafa?" "Ummulkhairi mana" yafada yana fara,a, "Ai bata zoba" "Haba yaya, nifa nakawo yarinyar da hannuna" "To ai tun wannan turowar da kayi aka tafi da ita shikenan rabonmu da ita" "Ni? Da yaushe?" Baban ummulkhair yafada cikin tashin hankali, "Banfa gane abinda kake son fada min ba, kaine fa ka aiko aka tafi da ita.." "Yaya wallahi ban san wannan maganar ba..." Tashi yayansa yayi ya leka cikin gida yana kwallawa umma kira, tana zuwa yafara magana, "Zoki jiye min wani abin al'ajabi, kinji wai bashine yaturo aka tafi da khairi ba" Shiga rudani umma tayi jikinta yana rawa, "Alhaji ka gafarceni wallahi banyi haka dan in bata maka ba, dan Allah kayi hakuri" "Me kuma yafaru?" Alhaji mukhtar yafada hankali tashe, "Alhaji wallahi ba shine ya turo atafi da itaba mijinta ne..." Zunbur abba ya mike arazane, "wai kuna nufin khairi bata gidan nan? Tana ina?" "Tana kano gidan mijinta tun kimanin watanni uku baya da suka wuce" Mamakine karara ya bayyana a fuskokinsu amma shi abban khairi bayan mamakin ma harda tashin hankali, ko takansu bai sake biba ya saba babbar rigarsa yafita yana cewa, "Wallahi yau ko ani ko a mahaifin wannan yaron, bazan yarda ba sai sun sakar min yata, yata bazata zauna dashi ba"..... Alhaji mukhtar yayi Saurin tsaidashi,+ 'karkaje ka raba wannan auren Abinda Allah ya rubuta ba Wanda ya isa ya hanashi, ko ba komai yarannan suna son junansu, 'idan mutum yayi ma ba dai dai ba, ka haqura kabarshi, ai *Alheri danqo* ne saka mashi da alherin kai kuma sai kaga kyakkyawar sakayya, kayi haquri kabarshi kabar komai ba komai ba abinda ya riga ya wuce ya tafi sai kubawa xuciyarku haquri amma Sam *Ramuwar gayya* bata dace da ku ba, 'kayi haquri yaya idan har nabar masu yarinyar sunci Lagona kenan, an karbemin budurwa an karbemin yarinya, 'Tun asali can ba matar ka bace, ai matar mutum kabarinsa, ya dubi yayan Ransa a bace, *'Matar waye*? Sun dai ci amanata ne, kuma bawai ina son ta bane har ynxu kawai Ina so na rama abinda suka min ga yaron sune, 'Sam bai dace ba, Kada ka kuskura karaba wannan auren na khairi domin yaran suna son junansu, Kada ka shiga haqqinsu akan abinda basuda laifi akai, tunda baka jin magana kaje can kacigaba da gabar da kake da mahaifansa, Abba ya sa Kai ya fice yana gunguni shi baiga abinda xai hanasa karbo yarinyarsa ba sai ya saketa, Yana fita gidan motarsa ya shiga Ransa a bace kai tsaye Kano ya nufa, baisha wahalar neman gidan su mahaifin sawwam ba kasancewar yana da address ďin gidan. Dad da Mami na xaune a falonsu lokacin suna tattauna Mgnr su Kan sawwam ne, yaga yaron ya daina xaman gida ina yake xuwa tunda ya bincika gurin aikinsa an tabbatar masa da lallai yana xuwa, 'Tace duk inda yake xuwa baxai wuce gurin abokansa ba kuma hakan yafi saboda xai rage damuwa sosai da kaďaici shi kaďai a ďaki, 'hakane ba laifi tunda yana xuwa gun aikinsa, sai a fara nema masa auren Rukayya kada abarshi haka ba mata, Gaban mami ya faďi tun bata kai ga magana ba sai ga mai gadi ya shigo, ya gaidasu cikin girmamawa, 'Alhaji kana da baqo a waje, Dad ya dubesa, 'Waye shi, 'bai gayamin ba amma dattijo ne kamar irin mu, 'kaishi falon baqi... kodai shigo da shi nan ďin, Maigadi ya fita da sauri bai jima ba sai gasu tare, Suna haďa ido dad ya tashi da mamaki yana kallonsa, mami Kuwa kusan ruďewa tayi, 'me Kuma kaxo yi gidana? 'in banda ya'ta har akwai abinda xnxo yi a Wannan gidan naka, Dad ya juya yana kallon mami data daburce kafin ya maida kallonsa garesa, 'wace ya'kuma, ko kayi batan kaine, 'wannan tambayar yaron ka ya dace kayiwa, ya'ta naxo abani a yau ďinnan, yaje ya sami guri ya xauna, jikin dad na soma rawa Ransa ya baci Kada xarginsa ya xama gsky sawwam yana tare da khairi ne, A dai dai wannan lokacin khairi na kwance a jikin sawwam tayi matashi da cinyarsa, 'tashi mugani cikinnan ya qara girma, ta qara narkewa, 'wai kai kullum aka cema yake qara girma ne, kullum sai kace xaka duba kagani idan ya qara girma, 'tor shikenan gyara xn duba lafiyar cikin, 'yaushe Kuma ka xama likita bn sani ba, 'ni likitanki ne ai, barama kigani.... kafin tayi mgn ya kware rigar ya kara kunnensa a cikin yana saurare, kallonsa take cikin so da qauna kome yayi yana burgeta, sai ya dubeta da murmushi, 'kinji me yace.... Tayi far da ido cikin tsananin mamaki kafin tayi murmushi tana shafar fuskarsa, 'banda qarya sahibina, wata uku ne fa ko mutum bai xama ba, Ya bata fuska alamar yayi fushi, Tayi murmushi haďe da sumbatarsa a gefen kumatunsa, 'yi haquri gayamin inji, yaja hancinta yana kallonta da murmushi, 'baby abinci yake so abashi dan haka muje ďaki, ya soma qoqarin ďaukarta, taqi bari suna haka wayarsa ta soma ringing, yana ganin mamice ya sauke numfashi haďe da Kara wayar a kunnensa, 'kana ina ne? 'gida, 'kaxo ynxu tare da khairi, Kafin yayi mgn ta tsinke Wayar, ya dubi khairi yana gayamata abinda mami tace, 'ko xa'a rabamu ne, 'bana tsammanin haka qila tayiwa dad bayanin komai kuma xai fahimce mu ne, tashi ki shirya, Ta tashi a sanyaye ta nufi dakinta, duk shirinta ba kuxari a jikinta, hijab ta sanya fuskarta ba kwalliya ta fito, ya dubeta dai dai ya fito cikin nasa shirin, 'chab ina xaki bini a haka, sai kace wacce ke xaune cikin takura, yaja hannunta suka koma shi da kanshi yayi mata kwalliya harda Jan baki Kuma tayi kyau sosai, da kanta ta ďaura kallabi, yabata gyale yana kallonta tayi kyau sosai, 'Haba ko Kefa, xamu gaida surukai xakije da wannan shigar, Ta rungumeshi tana murmushi kafin ta kai masa kiss yayi Saurin riqeta yana kissing ďinta sosai, sai da ya gaji dan kansa kana ya saketa, Ga mamakinsa sai yaga ta turo bakinta a shagwabe, 'bai isheki bane? Ta make kafada tana nuna masa Jan baki akan mirrow, Tayi murmushi haďe da shafa kansa, 'sorry dear, yaje ya ďauko ya qara sa mata kana suka fita daga gidan. Tun a bakin gate gabanta yayi mummunan faďuwa ganin motar Abba, ta dubi sawwam dai dai lokacin da yake parking motarsa, ya kalleta yana faďin, 'menene naga duk kin tada hankalinki, 'motar Abba yaxo ya tafi dani ne, shima gabansa ya faďi, 'impossible, fito muje ba abinda xai faru, baxasu rabamu ba ina sonki, Ta fito jikinta a sanyaye suka shiga gidan, nan Iyayen maxa suka hau faďa sosai kowa nayi kan yaronsa da faďa Kamar xasu dake so, kowane ransa a bace sai kumfar baki suke cikin tsananin fushi, Khairi ce kawai ke kuka gurin, mami da sawwam kuwa bacin raine kwance a fuskarsu, 'ki tafi muje, kin gama xama dashi sai inga ynda xaixo ya qara ďaukarki, Ga mamakinsu sai sukaga khairi taje gaban dad ta riqe qafafuwansa tana kuka, 'karka bari ya tafi dani, ina son sawwam dan Allah kada ku rabamu kabawa Abbana haquri, A lokacin sai jikin dad yayi sanyi, tausayin yaran yakeji har cikin ransa, yayi shiru bai yi mgn ba, Mami tace ba ynda xa'a raba aurensu, sawwam baxai saki khairi sai dai kaje da Ita tayi ta xama a gabanka, idan ta haihu ka maida mana yaron mu ka riqe yar'ka, Sai sukaji mgnr wata iri banbarakwai daga Abba har dad, khairi nada ciki kenan, Abba yaxo a fusace ya fisgota, tana kuka take kallon dad aganinta shi kaďai xai iya cetonta, 'please dad....... Abba sai janta yake, tayi saurin riqa hannu sawwam shima a ynxu hawaye yake, Abba ya juyo yana kallonsa, 'kai sake min yarinya bana son shashanci, ba musu sawwam ya saketa, Tanaji tana gani Abba ya rabata da sawwam, ya sanyata a mota ya fice da sauri, Sawwam ma ďakin sa ya nufa ransa a bace, ya bugo qofar ďakin ji kake gam kamar xai ballata.... 'Dad yace duqawa wada baxai hana ya tashi ba, ni nayi masa laifi saboda ke, xnje na bashi haquri saboda yaran, suna matuqar son junansu, 'Mami tace sai muje tare a gobe kaga yarinyar nada ciki kar yaje ya salwantar dashi, munason cikin da farincikin sawwam, 'Nima haka nake tunani cewar dad. Khairi Kuwa kuka take sosai acikin motar bai kulata ba har suka xo gidan, idanunta sunyi jawur luhu luhu da su, Da gudu ta shiga cikin gida tana kuka, kukanta ya fito da mama daga kitchen anan ta sameta tsugunne riqe da cikinta sai amai take kwararawa kamar xata amayarda hanjin cikinta, Mama sai sannu take mata cikin tausayawa yarinyar, taje ta kawo mata ruwa, 'sai dai ki mutu amma kin gama xama da wannan yaron cewar Abba yasa kai ya fice da sauri, Khairi ta riqa ta tana kuka, 'mama ki taimakeni, mama kibashi haquri ya maidani inda sawwam, Mama ta riqata suka shiga ďaki, yinin ranar komai bata ci ba har dare duk ynda mama tayi da Ita taqi taci komai, yayyunta maxa ma sai tausayamata suke suna rarrashinta taci taqi kasancewar ita kaďai ce Mace a gidan duk maxa ne shiyasa suke sonta, Har goma na dare taqi taci komai, mama ta damu sosai sai taje ta gayawa Abba, 'ai ba'a fushi da abinci kibarta xata nemeshi dan Karan kanta ko dan cikin dake jikinta, 'cikine da Ita Alhaji? ta tambaya cike da mamaki, 'cikine da Ita wai injisu Iyayen yaron, koma dai menene tagama aurensa, idan ta haihu xn kai masu abinda ta haifa shikenan, Mama ta girgixa kanta kawai cike da takaici tabar ďakinsa wannan rayuwa dame tayi kama, 'ummu.. Ummu.. ta soma kiranta, can qasan maqoshinta taji ta amsa, 'tashi kici abinci ba dan niba sai dan abinda ke jikinki, bakisan xaman ki da yunwa xai iya janyo masa matsala ba, idan ya xube mijinki baxai ji daďi ba, Khairi ta ďan dubeta tana share hawayen fuskarta, 'mama ni sawwam nake so, 'kici abinci tukunna xamuyi Mgnr, 'bana iya cin komai ynxu sai tea, 'shikenan bara na haďa maki, Tea mai kauri ta haďa ta kawo mata ta bata, 'inbaki bread, ta girgixa kanta, biscuits fa, nan ma a'a, cake fa, ta yatsina fuska kafin ta girgixa kanta, 'haka xakisha ruwan tea bada komai ba ai baxai riqa cikin ki ba ummu, 'mama ya isa, tasa kai ta shanye tas, sai ga xufa na karyo mata sai wani ajiyar xuciya take, ta cire rigar jikinta, 'mama tace ko xakiyi wanka ne? Ta gyada Kai tana kallonta, mama da kanta ta haďa mata ruwan wanka taje tayi ta fito tana kallon maman dake xaman jiranta, 'mama bakuda ďan wake a gidannan? 'ďan wake ynxu ummu, Ina xn samu, Khairi ta xauna tana yatsina fuska, 'mama kimin kona garin rogo ne kona flour, Mama ta tashi tana faďin inaji kamar da akwai flour gidan bara na duba ingani, ni xama bai sameni ba tunda an haďa ni da lalurar Mai ciki ta fice.... Tana fita khairi ta dauki wayarta ta Kira Alhaji mukhtar cikin kuka take sanardashi duk abinda ya faru, 'kiyi shiru ki kwantar da hankalinki bai isa ya rabaki wannan auren ba, tunda ni har nayi masa mgn bai jiba Gobe xnxo da aminin babanmu nasan shi dole ya isa da shi, Tayi godiya sosai xuciyarta fal da farinciki, ta kira wayar sawwam bata shiga sai ta ajiye wayar. * Washe garin ranar da sassafe Alhaji mukhtar yaxo gidan tare da wani dattijo aminin babansu suna kiransa da baffa, Faďa sosai yayiwa Abba har sai da yayi danasanin abinda ya aikata, Ana haka sai ga dad mami da sawwam, Nan aka taru aka sasanta Iyayen bayan faďa da nasihohin da baffa yayi masu, 'a koda yaushe ka xama mai yafiya domin kaima a gurin Allah mai laifine, Suka yafe juna tare da miqawa juna hannu suka gaisa haďe da rungume junansu cikin farin ciki, shekaru da yawa rabonsu da hakan, Basu ankara da sawwam da khairi basa gidan ba sai da suka soma nemansu, tuni sun kama hanyar Kano sun bar Iyayen.......

Post a Comment for "RAMUWAR GAYYAH CHAPTER5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...