Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 3

RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 3

- - Post a Comment
RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 3 Nutsuwa sukayi dukkaninsu suna kallonsa sannan suna jira suji abinda zai fada, "Tunda kun matsanta sai kunji dalilin dayasa nake son raba auren ummulkhair da wannan yaron to zan sanar muku amma ke ummulkhair ki sani bafa zan janye kudirina ba, yazama dole kiyi min biyayya ki hakura da wannan yaron..." Maihaifin nata yafada yana kallonta, bata iya cewa komai ba sai hawaye dake faman bin kumatunta, Mayar da hankalinta tayi ta nutsu wuri daya ta fara sauraron labarin da abbanta yake shirin basu, "Nida alhaji mustapha abokan junane ko kuma nace aminai domin tun lokacin danaje jahar kano karatu muka hadu dashi kasancewar makarantarmu daya sannan ajinmu daya, Mun shaku dashi mutuka komai tare mukeyi, bama rabuwa sai dai idan har hutu akayi, hatta iyayenmu sun san shakuwar dake tsakaninmu, da haka har muka kammala karatun secondary anan muka yanke shawarar cewa zamu dora karatu na diploma a jami'ar bayero dake cikin kano tunda dukkanmu mun samu sakamako mai kyau, Lokacin da muka fara karatu anan nikuma nahadu da wata yarinya yar gidan manyan mutane gidansu yana nan a unguwar rimin kebe, farkon haduwata da ita a kasuwa muka hadu naje siyan takalmi ita kuma an aiketa siyan kayan amfanin gida, daidai shagon danake tsaye tazo tawuce sai jakarta ta fadi bata saniba, Zuwa nayi na dauki jakar nabita abaya har shagon da ta shiga nayi mata sallama nabata jakarta nace mata ahanya ta yasar bata saniba, nan taji dadi tayi murna domin na ga hakan akan fuskarta, Tun kallon farko da nayi mata naga tayi min sosai kuma awurin naji ina sonta,sunanta na tambaya tafada min nima nasanar da ita sunana mukayi sallama bayan ta sanar dani adireshin gidansu, Kwana biyu da haduwarmu da ita na shirya naje gidan nasu anan nasamu kyakkyawar tarba awurinta da wurin iyayenta,mun dan taba hira da ita har nake sanar da ita cewa ni dalibine sannan kuma ba dan asalin cikin garin kano bane, Lokaci kankani muka saba da ita muka shaku soyayya mai karfi ta shiga zukatanmu, ganin mun shaku sosai sannan har mutane sun dan san tarayyarmu yasani nasanar da mustapha maganarta sannan na umarce shi da ya shirya muje nakaishi su gaisa da ita, Aranar mukaje dashi suka gaisa shima ya yaba mutuka da hankalinta da kuma nutsuwarta, haka muka cigaba da tafiya har akayi hutun makaranta anan nabarwa mustapha amanarta saboda ni nayi nisa dan haka nace masa ya runka zuwa yana dubata,hakan kuwace tafaru domin kusan kullum mustapha yana hanyar gidansu wannan yarinyar, Abinda ban saniba ashe shima mustapha sonta yake yi dan haka sannu ahankali ya hure mata kunne yabatani awurinta ya shigar da kansa suka fara soyayya, koda aka koma hutu sai bai nuna mini ba itama kuma bata nuna min ba sai dai ta dan canja min ba kamar daba, Haka dai naci gaba da hakuri domin ina yimata so nagaskiya kuma mai tsanani, Lokacin da muka kammala karatu nasanar mata da zan turo magabatana domin asaka mana ranar aure, bata ki ba tace min to haka shima mustapha nasanar masa, Satina hudu da gama karatu na tura iyayena neman auren amma koda sukaje sai akace musu ai anbada ita yanzu hakama saura sati daya daurin aurenta, Nashiga tsananin tashin hankali sannan raina ya baci, ana sauran kwana uku bikin na shirya natafi kano wurin mustapha domin ina son nasanar dashi cin amanar da wannan yarinyar tayi min, koda naje banma sameshi ba sai mahaifiyarshi nasamu itace take fada min cewa ai yana can yana shirye shiryen bikinsa wanda za adaura masa nanda kwana uku, har gidansu yarinyar saida tafada min da sunanta anan nagane cewar lallai mustapha amanata yaci shiyasa yayi biris da lamarina lokacin da nake sanar masa da irin canjin da Nagani atare da ita, Tun da nadawo gida daga gidansu mustapha nakwanta rashin lafiya wacce bakomai ke damuna ba face bacin rai ta sanadiyyar haka nahadu da lalurar hawan jini gashi nakasa mantawa da ita koda yaushe acikin tunani nake, Dan haka na shirya daukar fansa na shirya mayarwa da mustapha abinda ya shuka shekaru 30 baya da suka wuce, ayanzu ne zai gane cewar RAMUWAR GAYYA TAFI TA GAYYA ZAFI, domin abinda ya tabayi to gashi zai faru akan dansa, shima yanzu zai dandana bakin ciki irin wanda na dandana abaya..." Dukkaninsu sun razana dajin abinda yafaru, Ajiyar zuciya khairu ta sauke ta kalli abbanta, "Abba hakika abinda abban sawwam yayi maka bai kyautu ba sai dai bai kamata ka hukunta sawwam akan laifin da bashine ya aikata maka ba, idan...." Dakatar da ita mahaifinta yayi ta hanyar daga mata hannu tare da cewa, "Ba neman izininki nakeyi ba dan haka ki rabu dani na aiwatar da abinda najima ina shirin aiwatarwa, sanin kankine saboda sawwam na turaki kano badan wai kiyi karatu ba a,a sai don ina son burina yacika na rama abinda mustapha yayi min, kuma ma ai ni ban saki kiyi soyayya tagaskiya dashi ba, dama cemiki nayi kiyi duk yanda zakiyi kija ra'ayinsa gareki yasoki bance kema ki soshi ba dan haka kima cire ran cewar zakiyi zamantakewar aure tare dashi..." Mikewa yayi zai fita yayunta sukayi hanzarin tsayar dashi, "Haba Abba..." Cewar babban yayansu, Hannu yadaga masa ya dakatar dashi, "Wannan fada tace dan haka dole kubi abinda nace" yana kammala fadin haka yasa kai yafice yabarsu zaune kowa zuciyarsa cikeda sake sake, Babu wanda ya iya magana acikinsu amma ummulkhairi har lokacin bata daina kuka ba, daya bayan daya suka rinka tashi suna barin falon, ganin kowa yabaje yabarta yasata itama tashi tafita anan ta rinka cin karo da yan tafiya wadanda suka zo bikin, kowa sai Allah yasanya alkairi yake yimata ya tafi saboda sunga kaiwa amarya gidan mijinta ya gagara, Dakinta ta shiga ta kwanta shiru taci gaba da kuka tayi kuka kamar ranta zai fita yabar jikinta...... Tashi sawwam yayi yana kallon iyayensa bayan dad dinsa ya kammala bashi labarin abinda ya hadashi da mahaifin ummulkhair wanda komai sai da yafadawa sawwam bai boye masa koda kalma daya ba, "Shikenan dad Allah ya rufa asiri yasa haka shine yafi zama alkairi.." Fita yayi ya shiga dakinsa ya kwanta ransa fal kunci, Wayarshi ya dauka yashiga kiran layinta, har lokacin kuka take amma haka ta daure ta daga wayar, "Matata kuka kike yine? Fada min menene yasaki kuka?" Yace da ita yana saurarenta domin yagama fahimtar cewar kuka take yi, "Dad yabaka labarin abinda ya hadashi da abbana?" Ta tambayeshi cikin kuka, "Ehh yafada min, nifa nayi tsammanin wani babban abune ashema wai akan mami ne fadan..." "Ehhh akaine" tabashi amsa tana share hawayen fuskarta, "To share hawayenki, kidaina kuka kinji" "Tayaya zan iya share hawayena sawwam?" Tafada tana kuka, "Daurewa zakiyi, kinji matata, kicire damuwar komai aranki, ina sonki bazan iya rabuwa dake ba" "Dagaske?" Ta fada tana murmushi, "Dagaske nake, kin ganni nan babu abinda yake damuna sai son kasancewa da matata, bana son ganin komai sai kyakkyawar fuskarta, bana son jin komai sai kamshin jikinta, gaskiya bazan boye miki ba ina bukatarki..." Hannu tasa tarufe fuskarta tana murmushi, "Kai ana ta shirin yanda za ayi adaidaita kai kuma ta wannan kake.." "Hmm amma dai kin san dole na bukaci matata ko?" "Hmmm hakane" "To kin gani, wallahi hakurina yakusa karewa..." "Ka kara hakuri dai dan Allah kaji mijina..." Ajiyar zuciya ya saki, "to dan yimin kiss naji" Bata bashi amsa ba ta shiga aika masa da zazzafan kiss wanda yafara kokarin ruguza masa dodon kunne.... 2 days later... Kokari sawwam yayi ya cire damuwa aransa,hakan da yayi ba karamin dadi yayiwa dad dinsa ba domin ya tsammanci cewar sawwam yacire khairi daga cikin zuciyarsa, Ganin zaman gidan baya yimasa dadi yasashi kawai komawa office yaci gaba da zuwa aikansa, sannan idan ya tashi kuma sai yawuce wurinsu Abdul, baya komawa gida sai misalin karfe tara nadare, da zarar ya koma kuma kusan kwana suke suna waya da ummulkhair, Ita kanta ummulkhair ta danyi jarumta wajen rage damuwar dake ranta. Yau kimanin sati biyu da bikinsu shida ummulkhair, abuja aka turashi shida abokan aikinsa, har ya shirya zai tafi sai yaga kuma bazai iya tafiya batare da yaga lonely dinshi ba, Bauchi yafara zuwa, misalin karfe 12 narana yasamu ya isa, lokacin da yafadawa ummulkhair zuwansa rasa yanda zatayi tafita tayi gashi abbanta ya hanata koda leka kofar gida, Tana nan zaune tanata sassaka yanda zatayi sai dabara ta fado mata ta tuno cewar an kwantar da kawar mama a asibiti, Tambayar mama tayi cewar zataje dubiya, bata hanata ba amma ta gargadeta akan tadawo da wuri kafin abbanta yadawo, Wani material tasaka pink da bakin hijabi har kasa tafita, acan tsohon titi tasameshi yayi packing akasan wata bishiya yana jiranta, "My lonely ai nayi zaton ko bazan samu ganinki ba.." Murmushi tayi tana kallonsa yasha kananan kaya gashi kamshin turarensa duk ya cika mata hanci, "Nasamu nafito dakyar..." "To yakike, ya gida, ya missing dina? Ko bakiyi ba?" Murmushi tasaki ta dauke kanta, "Missing dinka sosai ma, bafa na iya yin bacci.." Hannunta yakamo acikin nasa, "Idan dagaske kike to nuna min nagani sai na tabbatar" Jin ya matso jikinta yasata boye fuskarta a kirjinsa, "Nuna min mana nagani, kodai dama bakiyi missing din nawaba kawai dadin baki kike yimin?" Kanta ta girgiza ta dago tana kallonsa, kiss takai mishi a kumatunsa, "Shikenan?" Ya tambayeta yana murmushi, kai ta daga, "To ni bari kiga yanda nayi missing dinki" Rungumeta yayi ajikinshi yafara laluben bakinta......, Sake matseta yayi ajikinsa, "In taba?" Ya rada mata a kunnenta, Cikeda kunya ta girgiza masa kai, "Yauma hanani zakiyi, nida halal dina? Bari kigani.." Cusa kanta tayi ajikinshi saboda tagane abinda yake nufi, Sai da ya nuna mata salon soyayyarshi sosai sannan ya kyaleta yana murmushi, "Bari natafi karki sa nayi shigar dare.." Jitake kamar kada ya yatafi yabarta,hawaye tafara yi sharrrrrr, cikin kuka tafara yimasa magana, "Allah ya kiyaye hanya, dan Allah sawwam karka rabu dani, karka tsaneni dan Allah karka ce zaka sakeni, wallahi ina tsananin sonka.." Sake rungumeta yayi yana shafar bayanta kamar wata jaririya, "Ummulkhair nayi miki alkawari zan kasance dake bazan rabu dakeba domin kece rayuwata, saki kuma indai nine maiyi to har abada bazan yiba.." "Allah yakaika lafiya, idan kadawo zaka biyo tanan?" Murmushi yayi yana kallonta, "kina son nadawo ne?" "Ehh" tabashi amsa, "To zan dawo naganki, kije kitafi gida" Sakinta yayi tafara kokarin zuge zif din rigarta tana harararsa, "Nayi laifine?" Ya tambayeta yana kashe mata ido tareda yimata dariya, Baki ta turo ta bude kofar motar ta fita aranta tana jin cewar tasan zatayi missing dinshi sosai, dariya yake mata har tabar wurin ta tsaya abakin titi tana tarar mai keke napep, Mahaifinta dake tsaye abakin titi shida wani abokinsa wanda suka hadu suna gaisawa sunyi packing din motocinsu agefe sai kawai yahango wata tafito daga cikin wata bakar mota mai bakin gilasai kamar ummulkhair, gabansa ne yafadi domin ko tantama babu itace, yana ganin ta shiga keke napep yayi saurin yiwa abokinsa sallama ya shiga motarsa yabi bayansu...... Qarasowar su da mai napep yayi dai dai da qarasowar Abba, Da sauri ta baiwa mai napep ďin kudinsa tayi cikin gida jikinta na rawa, Tun a waje yake kwala mata Kira, tana jinsa bata amsa ba har ya qaraso, mama na jinsa ta fito, 'Uban Waye naga ya ajiyeki bakin titi, 'yayan maryam ne, xasuje kasuwa da budurwarsa shine ya ajiyeni acan na qaraso, dama Muna can tare a asibiti, Ya sauke ajiyar xuciya kana ya juya da sauri, Numfashi taja haďe da lumshe idanuwanta, 'God save me.... 'ya Mai jiki mama ta tambayeta, 'Mai jiki da sauqi, tayi cikin ďaki da sauri, kayanta ta soma cirewa kana ta shiga toilet domin watsa ruwa, 2 days~ Ranar da sawwam ya dawo sai da ya tsaya a inda suka saba haďuwa, ya kirata a waya, Ta duba Abba yaje masallaci mama Kuwa ta shiga sallah, ta ďauki takalminta saďaf saďaf ta fice da sauri taji daďin da ko yayyunta bata gani a hanya ba, Tana xuwa ta shiga motar tana sauke numfashi, ya kalleta, 'gudu kika yi hala? Tayi far da ido tana kallonsa, 'wane irin gudu kuma sai kace yarinya, 'ai bakida Banbanci da yarinya naga sai maida Numfashi kike, Ta janyo hannunsa ta ďora kan qirjinta, 'kaji ynda xuciyata ke bugawa, ina tsoron Abba ya ganni ne, ranar fa yaso ya gane sai da ya bini a baya, Ya janye hannunsa yana kallonta, 'ni ai naganshi tare da wani tsaye, ban gayamiki ba Kada hankalinki ya tashi nasan ki da tsoro, da fatar bai taba min lfyr jikinki ba, ya faďa yana tattaba jikinta, Ta girgixa kanta tana kallonsa, ' bana son abinda xai sami wannan jikin ki kula da shi sosai, ta gyada kai tana kallonsa, Yasa hannun ya mintsini bakinta, 'shi bakin baya mgn ne, sai dai kita gyada kai kamar kurma, Ta tunxuro bakin cikin jin xafin mintsinar da yayi mata, 'oh sorry dear da xafi ko? nan ma gyada kai tayi, Ya janyota sosai xuwa jikinsa, a hankali ya xira harshensa cikin bakinta, a Yanxu ta soma sabawa da wannan itama sai ta shiga maida masa martani, sun jima a hakan kafin ya saketa, ya gyara mata hijab ďinta ya qara haďa fuskarsa da tata, 'Ina son ki khairi, ta lumshe idanuwanta xuciyarta nayi mata sanyi, itama tana jinsa har cikin ranta, 'Yanxu idan ka tafi Kuma sai yaushe xaka dawo? 'I don't know too, duk ynda hali yayi, tayi shiru tana kallonsa, yaja hancinta, 'kinaso na dawo da wuri ne? ta gyada Kai tana kallonsa, 'kimin Abinda xai sa nadawo gobe ma, 'Tace menene, Ya matsa yayi mata raďa a kunne (na tabe bakina Ina kallon Ummi Aysha) Rufe fuskarta tayi da tafin hannuwanta tana murmushi, 'kin amince? Ta girgixa kanta, shima murmushin kawai yayi, Sun ďauki lokaci suna hira kafin yabarta ta tafi, sai da yaje gidansu maryam suna tare sai ga qaninta yaxo nemanta gidan ba shiri suka fito, Sanda taga Abba a bakin qofar gida sai da gabanta ya faďi, 'kai Nafi'u Ina ka sameta? 'gidansu maryam na ganta, Ga mamakinta baice komai ba ya juya cikin gida, ta sauke numfashi tabi bayansa. Tana shiga mama ta soma mata faďa sosai akan yawan fitar da take a ynxu Wanda ada batayi, Abba ma yasa bakinshi, tanajinsu bata tanka ba, batada matsala a ynxu tunda taga sahibinta koma menene suyi tayi, Abinci taje ta diba kitchen tadawo tsakar gida tana ci, yanayinsu da sawwam take tunawa sai faman murmushi take ita kaďai a tsakar gida, tana haka wayarta ta soma ringing, tana ganin shine tayi Saurin karata a kunneta, 'badai ka isa ba, 'Nooooooo na tsaya hotel ne gobe xn qarasa, hope kina lfy, 'lfy kamar ynda kake, 'kinsan yanda nake kuwa, Ina matuqar buqatarki a kusa dani, ta juya tana waige waige bakowa, 'kayi haquri watarana muna tare har xaka gaji dani, 'baxan gaji da ke ba bakisan ynda nakejin ki a xuciyata bane, 'I feel what you feel, kayi haquri, 'haquri idan nagaji da yinsa xnxo na ďauke kine mu gudu, Fitowar Abba yasanyata yin shiru jikinta na soma rawa, 'baxaki bini ba shiyasa kika min shiru, tayi Saurin cewa 'A'a qawata baxan xo ba ke kixo gobe sai ki tayani haďa kayana, ni hr ynxu bnsan matsayina ba mai aure ko marar aure, Abba ya juyo yana kallonta har xaiyi mgn sai Kuma yasa kai ya fice, Ta sauke ajiyar xuciya, taji sawwam na dariya 'dariya ma kake shikenan, 'ni xaki maida Mace saboda Abba ne ko mama, 'Abba ne, 'OK we talk later xn shiga wanka...... Bayan sati biyu basu qara haďuwa ba olways suna kan waya, tun lokacin bata qara fita ba ko qofar gida ma bata xuwa, sai Abba ya qara yarda da Ita yasan baxata iya cin amanarsa ba, Ranar da sukayi waya ya gayamata xaixo, tayi shirinta ta feshe jikinta da turare Mai sanyin qamshi kana taje inda Abba, 'Abba xnje duba Farida ta haihu gobe suna baxan iya shiga taro ba saboda bakin mutane, 'yace hakane ummu, yasanya hannu a aljihunsa ya ciro kuďi yabata, 'Gashi sai kibawa Mai jego ko, ta karba tana godiya kana ta tashi ta fice da sauri, Hotel ďin daya sauka nan suka nufa, sunyi planning yanda xasu gudu idan Iyayen sunqi saukowa, sun sha soyayya kamar kada su rabu, Yaxo maidata sunyi Sallama kenan ta fita motar, yana kallonta ta baqin glass ďin motar tana tafiya, sai ya sauke glass ďin da sauri ya Kira sunanta, duk akan idon Abba yana hangosu daga inda yake xaune, Tana juyowa ta saki murmushi, yayi mata kiss a tafin hannunsa ya hura ta iska xuwa gareta, 'I love you.... 'Love you too muah ta tura masa itama, Yayi murmushi ya maida glass ďin motar kana ya fice xuciyarsa cike da farinciki, Hankalin Anna yayi matuqar tashi, yaushe khairi ta xama yar iska, bama Wannan ba yaushe ta fara masa qarya tun yaushe ma suke haďuwa da wannan yaron? ya tashi yabita da sauri, Tana shiga gida gyalenta kawai ta ajiye, ba xato ba tsammani ta soma jin duka ta ko ina ajikinta, Da waya yake dukanta sai ihu take, mama taxo da sauri ta kwace ta hannunsa, 'metayi kake dukanta haka, idan kajimata ciwo da wannan bulalar fa? 'gwanda na jimata ciwo da ta kunyatani idon jama'a, Ashe bata rabu da wannan yaron ba, tun yaushe kuke tare Ina kuke haďuwa ne, Khairi ta boye bayan mama tana kuka tana duba jikinta, bulalar harta kwanta mata, 'Haba Alhaji ya kamata a sassautawa yarannan haka tunda suna son junansu, laifin iyaye bai kamata ya shafe su ba, badasu xakayi *Ramuwar gayya* ba tsakaninku Iyayen, 'ke kimin shiru kina Goyon bayanta ne tor wallahi daga yau karna qara ganin qafarta a waje, ba qawarkiba ko qanwar uwarki taxo nan kika rakata bakin gida sai ranki ya baci ballantana kije ganin mai jego, shashashar banxa kawai, Mama tayi shiru amma kalamansa sun mata xafi, har xai fita ya juyo yana kallonta, 'bani wayarki nan, ba musu ta miqa masa jikinta na rawa, ya fice sai mamakin abinda idonsa ya gane masa yau yake, idan labari aka xo masa baxai yarda khairi xata iya haka ba, ya yarda namiji shike bata Mace, tunda gashi khairi bata masa biyayya ta koyi yimasa qarya hartana bijire masa duk saboda ďa namiji, ďakinsa ya nufa ya sami takarda da Biro yayi rubutu akai kana ya fito yabawa ďaya daga cikin ya'yansa yaje ya kaiwa mahaifin sawwam, Wasiqar bata samesa ba sai a Washe garin ranar , Yayi mamakin da jin wai sawwam bai saki khairi ba gashi har mahaifinta yana baraxanar maka su a kotu idan har bai sake ta ba, Sosai Ransa ya baci wato sawwam ya raina masu hankali, Koda mami taji batun batayi mamaki ba dan taga take takensa yayi yawa akan tafiye tafiye Kuma ta taba kamasa yana waya da khairi bata damu ba saboda farincikinsa shine nata, ita da xasu sasanta kansu subar yaran da tafi kowa farinciki, Sawwam na xaune a ďakinsa da laptop a hannunsa dad ya shigo, ba xato ba tsammani yaji saukar Mari a kuncinsa, Ya dafe kuncin yana kallonsa cikin tsananin mamaki, 'ni xaka rainawa wayo kace ka saki yarinya alhali baka sake taba, me kake nufine? Sawwam ya ajiye laptop ďin gefe ya tashi yana kallon mahaifinsa, 'Dad let's bygone be bygones, abinda ya riga ya wuce ya xama past dad, abinda ke tsakaninku iya kune , mu miye laifin mu anan dan Allah dad kuyi haquri kubarmu mana, 'Baka isa ba sai ka saketa a yau ko ranka yayi matuqar baci.......

Post a Comment for "RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...