ITACE QADDARATA CHAPTER 2 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ITACE QADDARATA CHAPTER 2

ITACE QADDARATA CHAPTER 2

- - Post a Comment
ITACE QADDARATA CHAPTER 2

  Noor tami'ke, jiki babu kwari tana sharar hawaye, tana duban Baba mai gadi amma takasa cemai komai. D'akinta na kusa da baba mai gadi,ta tashi ta koma ,ba komai a d'akin sai tabarma da ledarta, ta kaya kala uku su kadai ta mallaka a duniya. Tana shiga tazauna, kan tsohuwar tabarmarta takifa kai da ciny tana aikin kuka. Kuka take tayi tana tunanin sabuwar rayuwar da zata fara yanzu . Muryar mummy ta jiyo tana kiranta Zulum! Faqeer! Noor ta amsa Muryata a dashe, saboda tsabar kuka tace "Na'am momy", Ta tashi tafito da sauri . Mummy ri'ke da k'ugu tace "ga kayana da nasu Sageer can, kije ki wanke, idan kin gama ki share tsakar gidan nan, ki wanke duka toilets na gidan nan, dole kiyi na bankwana", Tayi tsaki tawuce Fuuu..... Noor tace "oo har yau ma da zan tafi ba za'a kyaleni ba?". Alhaji Mamman kuwa da murnarsa ya koma gida, Yana murnar ya samu yarinya budurwa, shal a ledarta, Bai fad'awa kowa ya 'kara aure ba,Ya bari sai an kawo masa Amarya, sannan ya fad'a wa matarsa, dan yasan halinta tsab zata iya lalata auren, kafin a kawota, shiyasa ya bari sai an kawota sannan ya fad'a. Noor sai ana kiran sallar magriba ta gama ayyukan da aka sata, tayi masifar gajiya sosai. Alwala tayi tai sallah, tana ro'kon Za'bin Allah, da abunda yafi zama alkhairi a rayuwarta. Tayi wanka ta chanza kaya dan duk tayi daud'a saboda aikin da tasha. Wasu kaya tasaka, suma dai sunji jiki sosai, wani gurin ya yage, ta d'inke da zare da allura. Wajen Baba mai gadi taje, tana hawaye tace "Baba Nagode nagode da ka sanar da *Asalina*(littafin Zee Yabour), ka fidda ni a duhu, ka bani amsoshin tambayoyin da suka dad'e suna mum yawo a kai, Sannan ina ro'konka ka yafe mun Baba, idan na ta'ba maka wani laifi". Baba mai gadi yayi ajiyar zuciya yace "baki tab'a mun komai ba Noor, kuma ki daina mun godiya haka"Dole in maka godiya Baba, tunda na taso ba mai sona sai kai, ba wanda nake jin dad'i a gurinsa sai kai, kai ka ilimantar dani , a wurinka na sauk'e Al Qur'ani mai girma, nasan hadisai da littafai da dama, ta dalilinki na iya boko duk da ban tab'a zuwa makaranta ba,(D'an shi yasa yana zuwa yana koya mata karatun boko, har ta iya turanci,da rubutu da karatu, Shi kuma shi ke koya mata na addini). "Baba nagode nagode bani da abunda zan saka maka dashi sai addu'a, domin kamin abinda kowanne uba zaiyiwa 'yarsa, kamin abinda mahaifina yakasamin arayuwa, gashi yau za'a rabamu", ta fashe da matsanancin kuka, Baba mai gadi ya tausaya mata sosai yace "Yi shiru Noor ki daina kuka ,In sha Allahu hakan shine mafi alkhairi a rayuwarki ,kiyi imani da 'kaddara ta sharri ce ko ta alkhairi kowanne dan'adam da kaddararsa" Noor cikin shesshekar kuka tace "ni wannan *Itace k'addarata*" Baba mai gadi yace "tabbas itace 'kaddararki Noor amma haquri zaki yi, ki cigaba da addu'a, ki mi'ka dukkan al'amuranki zuwa ga Allah shi zai miki magani" Haka Baba mai gadi ya cigaba da lallashinta yana fad'a mata maganganu masu kwantar da hankali. Har taji natsuwa da dangana tare da mi'ka dukkan al'amuranta zuwa ga Allah. Da daddare aka aiko direba shi k'adai, daga gidan Alhaji Mamman yazo ya d'auki Noor, Ta d'auko yan k'ullin kayanta ta sami Mummy da Daddy a falo . Ta dur'kusa gabansu tace zata wuce, tana neman gafararsu su yafe mata, Ko kallo bata ishesu ba, haka kuma ba wanda ya tanka ta cikinsu, tafi minti goma a zaune agurin, tamkar gunki, ba wanda ya tanka. Da taga basu da niyyar tanka mata , tatashi ta d'au k'ullin kayanta ta fita tana kuka, mai cin rai da bawa dukkan mai sauraro tausayi. Baba mai gadi ya mata rakiya har bakin motar, Suna ta d'agawa juna a hannu, harsuka fita daga layin gidan. tunani ta hauyi da maganganu a ranta. "Ita dai bata tab'a jin, inda aka ce an kai amarya ita kad'ai ba, daga ita sai direba , kuma ba kayan d'aki, ba lefe infact nothing nothing, Wani al'amari sai Allah". Suna parking mota a farfajiyar gidan Alhaji ya tarbesu yana ta washe baki, Noor gabanta ne ya fad'i ganinshi Tsoho tukuf, har yazama mai 'kafa uku, kai duk furfura, amma ahakan aka d'aura mata aure dashi, matsayin miji a gareta. "Subhanallah"! Ta furta a cikin zuciyarta "yanzu wannan shine mijina ?" Alhaji yace ma driver'n zaka iya tafiya, ita kuma ya ri'ko hannunta yana cewa "muje ciki koh?". Hannunta ta fizge, tana hawaye tace "ni ka sakeni". Alhaji ya kyalkyace da dariya yace "Yarinya kenan ni fah yanzu mijinki ne, in ban tab'a ki ba waye zai tab'a ki". Ya sake cafko hannunta, tana 'ko'karin k'wace hannunta, ya damtse shi gamm. Yaja ta cikin gida, Muk'ulli ya fiddo dashi daga aljihunsa, ya bud'e kofar, wani had'ad'd'en falo, suka shiga, sannan ya jata suka wuce k'uryar d'aki,,ya jefar da ita kan gado. Yana kallonta yana lasar baki, Yace "kaiii amma caca tayi wlh, banda caca a ina zan samu wannan santaleliyar budurwa, ga komai Mashaa Allah ba tare da aljihuna yayi kuka ba, amma gashi a banza na sameta". yafad'a Yana kokarin cire rigarsa. Noor ta jawo bargo ta 'kudundune kanta tana cewa "Dan Allah kayi ha'kuri kar ka min komai, Wayyo Allahna!" Ya fashe da dariyar mugunta yace "Haba! Yarinya waye zai samu yarinya kamar ki, ya kyale ke fah matata ce", Ya cire riga yayo kanta kenan,........! Suka ji an bangazu 'kofa da karfi. Hajiya ce ta shigo hannu ri'ke da k'ugu tace "Toh munafuki! Maci amana!, An gaya maka bansan me kake ba ,kaje an baka yarinya a caca kazo kaji dad'i, toh wallahi baka isa ba". Zufa ce ta fara k'etowa Alhaji, duk da cewa akwai sanyin Ac a d'akin murya na rawa yace "yi hak'uri ki saurareni Hajiya" Hajiya tasa hannu ta dakatar dashi tace "Dakata! Ba abunda zan saurara, na riga nasan komai dan haka wuce mu tafi, baka isa ka kwana da yarinyar nan ba wlh". Jiki na rawa ya d'au rigarshi ya nufi hanyar fita. Ta juyo ta'karewa Noor kallo, tayi tsaki tare da nunata da yatsa, tace "ke kuma zanyi lokacinki, kijirani zuwa safiya, zakisan waceceni, zakisan babu macen data isa ta auri mijina tazauna lafiya", ta juya taga Alhaji natsaye yana dubanta, Hajiya ta daka mai tsawa "mai kake jira? wuce mana" Yai saurin zabura jiki na rawa ya wuce. Noor kukan da take ya tsananta, amma ta godewa Allah da ya kawo Hajiya, Alhaji bai mata komai. Tace "Allah ka yafe mun duk da nasan Alhaji mijina ne, Kuma yana da hak'k'insa a kaina amma bazan iya bashi kaina ba". Kuka ta cigaba da yi har kanta ya fara ciwo Anan barci b'arawo ya sace ta.........................! Kiran Sallar asuba ya sata farkawa,Ta tashi ta shiga toilet tayi alwala Tayi sallah ta rok'i Allah abunda yafi zama alkhairi a rayuwarta ""Cikinta taji yayi kuka ""kooooo"" alamun yunwa rabonta da abinchi yau kwana biyu Tashi tayi taje falon tana dube dube ko zata samu wani abu da zata sama cikinta,Wata k'ofa ta gani ta bude kitchen ne Tayi ajiyar Zuciya a ranta tace k'ila in samu abunda zan sa a cikina,Shiga tayi tana dube dube, cupboard duk sai da ta dubasu amma wayam ba komai a kitchen din Dawowa tayi falo ta zauna a fili tace Ya Salaam! Yanxu ya zanyi gashi ba abunda zanci Bayan wasu mintuna tana zaune tayi jigum, taji an turo k'ofa an shigo Wata yarinya ce yar budurwa haka ta Shigo rik'e da tray a hannu Daga gani yar aikin gidan ce , Ta ajiye tray din tace Gashi ,Alhaji yace na kawo miki ""Noor ta mata godiya ta juya ta fita Dankali ne soyayye da k'wai, sai kayan tea tunda aka haifeta bata t'aba cin dankali ko k'wai ba,kai duk wani abu ma mai d'adi bata t'aba ci ba, daga tuwo sai shinkafa ""Ba b'ata lokaci ta fara kai lomomi har kunnenta taji yana motsi tsabar dadin dankali da k'wai da taji,Tace Ashe haka su Mummy ke kwasar d'adi tana ci tana santi ita k'adai + Hajiya ce ta tasa Alhaji a sashen shi(part) sai masifa take mai ""Yanxu Alhaji dan cin mutunci shine zaka je a baka yarinya a caca,ka kawo min ita muyi zaman kishi da ita, yar cikina fah ce yarinyar nan ""Haba! Hajiya ya kike magana haka ai musulunci ya yarda da haka ""Ta daka mai tsawa Dallah rufe ma mutane baki, kai kasan Allah ne,wlhy da kasan Allah da baka rik'a yin wasu abubuwa ba, dan haka ni yanxu ba wani dogon zance ba ka saketa a yau din nan ta koma can gidan ubanta ""Alhaji baki na rawa yace Haba! Hajiya in saketa fah kikace, kar ki manta yarinyar a caca aka bani ita kuma Ubanta abokina ne sosai tare dashi muke harkar cacar nan, kina ganin idan na saketa kwana daya da aure na mai adalchi kenan,sannan sauran abokanmu na caca kallon mai zasu mun maci amana, kuma zasu yi korata daga cikinsu ,kinsan kuwa idan suka koreni shikenan tawa ta qara dan suke had'a ni da manyan mutane mu buga caca ta makudan kudi ""Hajiya ta d'an yi shiru tana nazari sai can tace naji dalilinka, amma ina so kar ka kuskura wani abu ya hada ka da yarinyar,kar ka qara shiga d'akinta, kai ko kallo ma bata isheka ba tana matsayin matarka ce amma kar ka tab'a mata kallon matarka kai kama manta kayi aure a duniya ka d'auka ni kadai ce matarka ""Alhaji yayi shiru yana cewa a ranshi anya zan iya daukar wannan sharudda na hajiya gaskiya sun min tsauri,ina son yarinyar nan kuma ina son mu hada kwanciya da ita dan gaskiya tana da kyakkyawar halitta ""Hajiya ce ta daka mai tsawa kayi shiru kana wasu mazurai ""Murya na rawa yace Umm...ummm na amince A ranta tace kar ma ka amince. nasan maganinka ai,ba ma yarinyar nan ba,ba macen da zata sake burgeka a duniya wlh,Ni kadai ce matarka, dani kadai zakai ta rayuwa ba wacce ta isa ta rab'eka wlhy Ita kuma zata gane kurenta sai tasan ba macen da ta isa ta auri Alhaji Mamman ta zauna lafiya, duk da nasan a caca aka sata amma har da k'wadayi yasa ta amince, da sai tace ma Ubanta bata son auren,Wato taga mai kud'i zata zo ta huta Bata san ta kawo kanta gidan wahala ba ""Ta tashi ta fita tana haki A bakin kofa tayi kacib'us da Imran zai shiga sashen Abban na shi Ya dan rissina ya gaida mahaifiyar tashi ""Mum ina kwana ?? Lafiya lau Imran Ya dan yi fuskar damuwa sannan yace Mum wai da gaske ne Dad ya qara aure Hajiya tayi Ajiyar zuciya tace Da gaske ne Imran,abun bak'in cikin ma sa'ar Iman ya auro ""A firgice Imran ya kallo mahaifiyarsa yace Wat,abomination wannan ai child abuse ne,Daddy fah is 62yrs and ace ya auri yarinyar yar' 16yrx,haba Daddy me zai sa yayi haka wannan ai mu zai ja ma zagi a gari,Su iyayen yarinyar basu da hankali ne da zasu bada yar' su ga tsoho,sannan ita yarinyar shashashar ina ce da zata bari a aura mata tsoho ""Hajiya tayi k'wafa tace hmm! Kud'i suka gani shine kawai dalilin( *dan yaran basu san sana'ar Ubansu ba wato Caca,kawai sun dauka kasuwanci kawai yake,tunda sunga yana kasuwanci*) Imran yaja tsaki yace ""kaii ! Kaiii! Wai mutane ina zasu da son duniya neh Mtcheeewww!! Ya qara jan wani dogon tsaki kawai ya juya,ya wuce ya fasa shiga sashen mahaifin nashi ""Hajiya tace ai ga irinta nan,haka kurum ka jawowa ya'yenka abun kunya, ka auro yarinyar da ka isa jika da ita Ni ina ma tausaya musu ranar da zasu gano sana'arka ""Ta kawar da wannan tunanin tace bama wannan ba ,kamata yayi na fara tunanin ta ya zan fara cin uban waccar Barorojin(Noor).................... *Waye Alhaji Mamman* Alhaji Mamman asalinsa dan garin Bauchi ne Azare bafullatani ne,Zama ya kawo shi Abuja Matarsa ta farko ta rasu,auren zumunci aka musu, ya'yensu Uku duk mata Salma,Rahma da Maryam yanxu duk sunyi aure da ya'yansu Bayan ta rasu da Shekara biyar ya Auri Halima(Wato Hajiya)wacce itace matarsa har yanxu, itama yar bauchi ce amma a Misau,Hajiya ta gama mallake Alhaji gaba daya sai yadda tayi dashi,tana da masifar kishi da ganin k'yashi bata bari kowa ya rab'i Alhaji daga ita sai ya'yanta,ta zama kamar ita ce mai gidan,Ya'yensu Hudu tare , *Imran* ne Babba shekararshi ashirin da Uku da haihuwa,Kyakkyawa ne fari sol ( _kamar Sid din Roshni@king of hearts LoL_) duk gidansu yafi su kyau,Miskillin mutum ne ko dariya bai cika yi ba Sai murmushi,kuma bai cika son mutane ba,Ya gama degree dinshi akan Mechanical Engineering a Turkey, yanxu haka yana so ya kuma yayi masters, IMRAN hadadden guy ne ajin farko ,kuma d'an gayu ,idan nace na tsaya bayyana muku kyau da had'uwar *IMRAN* sai in dau 3 hours bn gama ba,Mata na daye masa Hajiya ta d'au son duniya ta d'aura masa tana bala'in ji dashi kuma ta d'au dogon buri a kanshi Yazeed ke bima masa 21yrx yana karatu nan Abuja a *Nile Turkish University* Final year yake , Ihsan 18yrx tana *baze university* Level one sai yar autarsu Iman 16yrs Ss2 a Al-amin international school Kan yaran duka a had'e yake,kuma familyn suna zaune lafiya sai dai yadda Mahaifiyarsu ke controlling mahaifin nasu, abun na damunsu tun ba IMRAN ba yafi kowa jin haushi, ya rasa yadda zaiyi ya lurar da mahaifin nashi ya zama namiji,yasan cewa shine mai gida,Shine shugaba a gidan ba mummy ba,shi ke da damar bada order a gidan abi ba Mummy ba.......................... Noor da ta gama breakfast,ta tattara kwanukan ta d'au tray ta fito A tsakar gida taga mai shara ,Ta tambayeshi Dan Allah ina ne kitchen ?? Ya mata nuni da hannu ""Kitchen ta shiga ,taga masu aiki nata aiki,bayan ta gaisa dasu ta ajiye kayan a sink,ta juya zata fita kenan, taci kaci karo da hajiya ""Ina kwana ?? Ta gaishe da Hajiyar tare da d'an rissinawa ""Da ban kwana ba da zan kika ganni munafuka,to bari kiji ba hutu kika zo yi ba,matsayinki d'aya da wa'innan masu aikin,ta nuna su da yatsa,ke sunma fiki daraja a gidan,sannan ni ba kishiya aka kawo mun ba yar'aiki aka kawo mun, dan haka ki gaggautawa jyyawa ki wanke wadanda can kwanukan da kika ci abinchi,dama sauran da ke wurin idan kin gama ,ki sameni falo na gaya miki sauran ayyukanki ""Hawaye Noor ta fara,a ranta tace anan d'in ma ban huta ba,ni dai haka Allah yayi rayuwata cikin k'unci da wahala,wannan *itace kaddarata* ""Ta juya kan masu aikin Wacce shegiyar ce a cikin ku ta kai mata breakfast ""Lami muryar na rawa duk ta gama tsorata tace Al...Alhaaaa.....ji ne yace na a kai mata ""Ina so wannan ya zama na farko kuma na k'arshe,matsayinku d'aya da ita a gidan nan ,kai har ma kun fita matsayi a gidan nan Kun jini ku ""Suka amsa da ""toh Hajiya Ta fice+ ""Noor wanke-wanken take tana kuka ""Masu aiki da gulma,d'aya daga cikinsu tace ba kece amaryar da Alhaji yayi ba ""Noor ta g'yada kai sama ""Lami tace ke kuwa me ya kai ki auren tsohon ""Noor cikin muryar kuka tace Mahaifina ne ya aura mun shi ""Sauran masu aikin guda biyu suka tab'e baki,suka ce tabd'i wlh ke kika yarda ""Lami ce tace "'Allah sarki! Sai kinyi hakuri gidan nan,dan ba Hajiya ba ya'yanta ba,duka basu da kirki wlhy,baka shiga hancinsu ba ma sun ma,toh ina ga ka shiga gonarsu dan haka sai kinyi haquri da juriya ""Sauran biyun suka ce wlh kuwa, dan har kin fara bamu tausayi ""Noor ko uffan bata ce ba, wanke-wanke kawai take a ranta tace ni ba wata wahala da zata razana ni, dan ba irin wacce ban sha ba a gidanmu,bak'in cikina tsohon da aka aura mun,rabani da Baba maigadi,da kuma rashin mahaifiyata Masu aiki nata hira abun su,ita dai Noor bata sa musu baki ba Da ta gama wanke wanke, ta tambayi Lami ina ne sashen hajiya Lami ta jata, ta nuna mata ""Hajiya na zaune da ya'yenta mata(Ihsan da Iman) a k'yatattacen falonta suna hira ""Noor tayi sallama ta shiga, Ta duk'a tace Na gama hajiya ""Ihsan tace wacece wannan Mum, ko sabuwar mai'aiki ce aka kawo ""Hajiya ta yatsina fuska tace wai itace yarinyar da babanku ya aura ""Iman da Ihsan a tare suka ce Wat!! Wannan d'in suka nuna ta da yatsa ""Hajiya tace ita fah ""Ihsan tace watz wrong wif Dad da zai auri yarinya kamar wannan,gaskiya Daddy bai kyauta mana ba ""Iman tace Jibe ta fah kazama ma da ita,daga gani yar matsiyata ce,ji kayanta duk sun yage,kyau kawai daddy ya gani ya auri wannan yarinyar ""Ihsan tace ni wlhy duk ma ta cika mun hanci da wari,sai d'oyi take, ta tashi ta d'auko air freshner tana feffesawa a falon ""Noor wasu hawayen bak'in ciki ne yazo mata,wannan cin mutunchi haka,duk da tasan bata sa turare(dan bata da shi,kuma bata da kud'in siya) amma bata wari ""Ihsan tace Gaskiya mum kisan yadda zaki yi da wannan yarinyar ,ba zai yiyu ba ace wannan kazamar,k'aramar yarinyarce kishiyarki ba ""Hajiya tayi dariyar mugunta tace ""ku kwantar da hankalinku,kunsan halin mahaifiyarku bazan tab'a zuba ido ina kallon yarinyar nan,a cikin gidan nan tana hutawa ba,ba ita son kud'i ya sata ta auri tsoho ba,tazo ta huta,toh wlhy sai ta gwammace kid'a da karatu ""Iman tace yawwa mummy gwara a koya mata hankali,Wlhy sai kinyi regretting auren mahaifinmu,Shegiya kamar aljana ""Keee!! Hajiya ta kira Noor a tsawace ""Noor ta d'an zabura tace Na'am Ina so ki saurareni da kyau kiji abunda zan gaya miki Na farko ki tattaro kayanki ki dawo d'akin masu aiki,Sannan daga yau kin koma baiwa a gidan nan ,ba mai aiki ba *Baiwa*, ba wasu ayyukan da zan cire miki nace su zaki rik'a yi, duk aiki da ya kama yin shi zaki yi, Iman ! Ihsan! Ga *baiwa* nan sai yadda kuka yi da ita ""Yes! Mummy shiyasa muke sonki *Imran* da *Yazeed* ne suka shigo a tare Ina kwana mum? Suka fad'a a tare Lafiya lau my two luvly sons Suka samu wuri suka zauna Kujerar da *Imran* ya zaune, ita ke facing Noor Idonshi caraf suka kai kanta ,kanta a sunkuye tana hawaye, Yace ""kee lafiyarki ?? Me ya sameki kike kuka ?? _Bai ma san wacece ba ,hakanan ya tsinci kanshi da tambayarta_ Har a lokacin bata d'ago kanta ba,kuma bata tanka shi ba ""Hajiya tace au kuka take ,tun yanxu har kin fara kuka, ashe nan gaba sai hawayenki sun k'are ""Imran yace Who is she ?? ""Hajiya tace Matar babanku ""Imran yaja tsaki yace Toh me take anan, i guess da part dinta ""Kiranta nayi na gaya mata matsayinta a gidan nan,dan daga yau ta koma *Baiwa* ,nafi k'arfin nayi kishi da k'azamar nan ,yar cikina ""Imran ya tab'e baki,irin ko ohon nan(i dnt care) dama yasan za'ayi haka, yasan halin mum din tashi Ya mik'e yace Dad na nan ko ya fita ?? Yana nan ka duba part dinshi,wani abu ne ? ""Ok , i need to talk to him about my job( ina so na mai maganar aiki na) ""Hajiya tace toh Allah yasa a dace Yace Ameen ya fice ""Yazeed yace dama ita ce wannan,wlh sai na huce takaicin jiya a kanki,dama ina ta rok'on Allah yasa na had'u dake ""Hajiya tace me ya faru ne ?? ""Yazeed yace Allah mum kar kiso kiga yadda friends d'ina ke teasing d'ina jiya,wai Babana ya auri yarinya wacce ya isa jika da ita ""Hajiya tace ai ga irin abunda ake gudu kenan,yanxu gaka gata,ka mata duk abunda kaga dama ""Yazeed yayi murmushi irin na mugunta, yace haaaa!! Ba dai tana gidan nan ba, kuma ta tashi daga matsayin matar daddy ta koma Baiwa, hmmm zanyi lokacinta, yanxu ina da lectures Byee mum and sisters ""Iman da ihsan suka ce bye Bro sai ka dawo ""Hajiya tace Allah ya bada sa'a ""Ya amsa da Ameen ""Ihsan ta mik'e tace kee!! Biyoni baya,akwai aikin da zaki mun ""Iman tace in kin gama nata nima akwai nawa ""Muryar a dashe Noor tace Toh ""Jiki a sanyaye ta tashi tabi bayanta.....................

Post a Comment for "ITACE QADDARATA CHAPTER 2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...