ITA CE QADDARATA CHAPTER 5 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ITA CE QADDARATA CHAPTER 5

ITA CE QADDARATA CHAPTER 5

- - Post a Comment
ITACE QADDARATA CHAPTER 5

  Tambayarki nake kinyi shiru,Imran ya katse mata tunani Tayi sauri ta zabura kanta a sunkuye k'asa,tace Na'am Yace Eh ai kin jini Ta sake yin shiru Ya dakata mata tsawa,zaki bani amsa ko kuwa Murya na rawa tace ni..ni..ma bansan ya akayi auren ba,kawai Babana ne yace ya d'aura mun aure,bayan haka bansan komai ba K'arya kike yi,ki gaya mun gaskiya ya fad'a yana mata kallon tuhuma Gaskiyar kenan Allah Imran yayi shiru yana nazari yace a ranshi hakan na nufin auren dole aka mata kenan,to me yasa Babanta zai aura mata tsoho? i have to find out,Ya d'an sauke numfashi sannan yace Yanzu ina iyayenki ? Murya a sanyaye tace Gidanmu na Garki II, Garki II ya nanata a zuciyarshi,ba dai hakan na nufin iyayenta masu kud'i bane,maybe dai irin masu gadin nan ne,dan bata yi kalar ya'yen masu kud'i ba,but bari na tambayi sunan babanta, Ya sunan mahaifinki ? Alhaji Ibrahim Had'eja Ya girgiza kanshi yace Gud,ya wuce ba tare da ya sake ce mata komai ba Ta bishi da kallo tana mamakin me yasa yake mata tambayoyin nan,dama ya hak'ura da binciken nan,kar yaje ya bincikowa kansa abunda yafi k'arfinsa,dama hausawa sunce kaza wajen tone tonen ta take tonu wuk'ar da za'a yankata,ta kawar da tunanin,ta mik'e Ta cigaba da wanke jeans d'in da k'yar, _duk da cewa taji mai Imran yace na ya fita harkarta,buh tasan halin Yazeed sarai,idan bata wankesu ba sai ta fuskanci mummunan b'acin rai_kwata-kwata bata jin dad'in jikinta,tana yi tana hutawa"" + ""Imran sashen su ya koma,ya watsa ruwa,ya sake shiga cikin manyan kaya,ya feshi jikinsa da turaruka designers masu bala'in k'amshi,Imran ba daga baya ba ta fannin gayu,Yayi kyau sosai,kai kace biki zashi,ko zance,Har yanzu bashi da budurwa,tunda yake bai tab'a soyayya ba,Mata masu ji da aji,sun sha kawo kansu gare shi yayi turus dasu, Yazeed ne mai bala'in son mata kamar bunsuru,kawai shi dai ayi chilling da Yan'mata,Da har Yan'mata yake kawowa gidan,Sai da Imran ya taka mai burki,Yanzu sai dai ya kaisu hotel ko can wani wurin shak'atawa"" ""Noor ta gama wanke jeans da k'yar,ta d'aukosu a bucket,zata je laundary ta shanya,ta hango Imran,ya fito sashensu,Taja ta tsaya,tana kallonshi,shi bai ganta ba Ba k'aramin kyau ya mata ba,a zuciyarta tace Mashaa Allah,Tubarkallah,wannan irin kyau na Imran,Gashi da gayu,tausayi da kyan hali,a gaskiya matar shi ta more,ina ma ace shi Daddyna ya aura mun,da nafi kowa sa'a a duniya,amma inaaa nasan irinsu Imran, ba tsara na bane Tana ta kallonshi har ya wuce parking space,ya shiga mota,ya tada Sannan ta wuce laundary"" ""Yazeed kuwa da ya wuce,sashen Hajiya yaje,Yana huci kamar wani bajimin zaki Hajiya dasu Ihsan na zaune falo, Lafiya Yazeed ya aka yi ? Hajiya ta tambayeshi Yana huci yace Mum can you imagine,nazo marin Noor,Ya Imran ya hana ni har yana murd'e mun hannu,yana cewa in fita harkarta,ita ba Baiwa bace kamar yadda muka d'auketa, What! Imran da kanshi ta fad'a unbelievable Wlh Mum nima nayi mamaki Ta kad'a kai tace barni dashi zai zo ya sameni,sai ya gaya mun dalilinshi nayin haka,sannan Noor na nan a matsayin Baiwa,ba wanda ya isa ya kareta gidan nan wlh,kaje ka mata duk abunda kaga dama,idan ta maka laifi ka hukuntata son ranka,Baiwarku ce,Baiwar gidan ubanku ce Ihsan ta tsomu bakinta tace to akan me ma,Ya Imran zai kareta,shi da ko son ganinta ba yayi Iman tace nima shi na gani Hajiya tace kaiii kuma kira mun yar'iska in k'ara tabbatar mata da matsayinta a gidan nan Iman ta mik'e ta fita kiranta"" ""Noor ta dawo d'aki kenan,Iman ta shigo rik'e da k'ugu tace fito munafukar Allah,jibe ta sumi-sumi Noor bata ce komai ba,tsaye kawai tayi tana kallon Iman Dallah! Kin wani tsare ni da kallo kamar tsohuwar mayya,wuce muje Mum ke kiran ki Tayi gaba,Noor tabi bayanta"" ""Sai da Hajiya ta k'are mata kallo sama da k'asa,Sannan ta juya kan Yazeed tace yi mata marin da kayi niyyar yi,Imran ya hana ka Noor gabanta yace Rass,ta tsani a mareta,dan a ganinta, ba cin mutuncin da yawuce a mareka,but ita kullum cikin marinta ake,ba mai ganin mutuncinta ko darajarta Yazeed yayi dariyar mugunta,ya taso da zafin nama,Ya d'aga hannu ya falla mata lafiyayyan mari Sai da taga Stars,kanta ya fara juyawa,tana ganin jiri,mari ne ya mata na mugunta da k'arfi Hajiya tace yawwa da kyau,gata nan ka mata horon duk da kaga dama,Baiwarku ce,ki daina tunanin cewar da Imran yayi ke ba baiwa bace,kin tashi daga Baiwa,kina nan a matsayinki ,duk da cewa ba a yak'i aka ciyo ki ba,amma kinsan inda aka ciyo ki,har gara a ciyoka a yak'i,akan inda aka ciyoki Da mamaki suke kallon Hajiya,Yazeed yace bamu gane ba Mum,kamar ya? Hajiya tayi saurin shan kwana tace ina nufin an aurota a banza,hausar tawa ce baku gane ba Ohh woo suka had'a baki gaba d'aya Noor hawayen bak'in ciki kawai take,ta rik'e kunci,a zuciyarta tace banda Allah yasa ina da zuciyar imani,yadda kuke azabtar dani d'in nan,da na tona yadda ubanku ya auroni"" ""Yazeed yace kin wanke jeans d'in da na baki ko kuwa ? Na wanke Ya d'an yi murmushi yace haa....God save you,but duk da haka,ban gama dake ba,i have to punish you for delaying,and making Ya Imran to shout at me Addu'ar neman tsari daga azzalumai ta fara karantowa Ji kawai tayi wayarshi na ringing Hello baby! Wata Babe ta fad'a Ohh Suzy,hw re u Fine,ina ta jiranka a Ibro hotel tun d'azu Ohh sorry baby,on my way Yayi hanging-up Ya nuna Noor,da yatsa yace ki jira dawowata Yana ta sauri,ya d'au car key d'inshi yace bye mum en sisters Suka ce masa byee Hajiya tace ke tambayar Su Ihsan,ba wani aiki da zaku sata ? Ihsan tace ni dai babu Iman tace nima babu Hajiya tace ok! Oya tashi kije ki ba flowers ruwa Wani sanyi taji a zuciyarta, ta furta Alhamdulillah! a ranta, da Allah ya mata tsari da Yazeed,ba flowers ruwa duk mai sauk'i ne"" ""Imran Garki II ya nufa,bai sha wahalar gane gidansu ba,tambaya d'aya yayi aka nuna mai gidan,kasancewar mahaifinta sananne ne a unguwar Yayi horn,Baba mai gadi ya taso ya bud'e mai gate,Bayan sun gaisa yake tambayarsa mai gidan na nan Baba mai gadi yace eh! yana nan ciki Shiru Imran yayi yana k'arewa gidan Kallo,har yanzu ya kasa yarda nan ne gidan mahaifin Noor saboda had'uwar gidan Ya nisa yace Baba Dan Allah waye Ibrahim had'eja a gidan nan ? Baba mai gadi ya d'an yi murmushi yace Ai shine mai gidan Toh Baba dan Allah tambaya ta k'arshe in baza ka damun ba, Ina saurarenka yaro Imran yace shine mahaifin wata yarinya Noor Baba mai gadi yace Eh shine,ita ce Babbar yar'sa wani abu ne A'ah ba komai,kawai kace ana sallama dashi Baba yace toh toh Imran yayi shiru yana nazari yace yanzu ace wannan shine gidansu Noor,amma iyayenta suka kaita ba kayan arziki,gaskiya akwai wani abu a k'asa Baba mai gadi ne ya katse mai tunani,Yace ka shiga ciki Ok toh nagode Falon da ya shiga,ba k'aramin tsaruwa yayi ba,Aljannar duniya,babu abunda babu na more rayuwar duniya,shi dai mamaki kawai yake Masu aiki suka kawo mai abun motsa baki Jim kad'an Daddyn Noor ya fito,da ka ganshi kaga mai ji da naira Ya bashi hannu suka gaisa Sannan ya samu wuri ya zauna,Yace d'an samari sai dai ban gane ka ba Imran ya d'an yi murmushi tare da sosa k'eya yace D'an gidan Alhaji Mamman ne Toooo tooo na gane,yana lafiya dai ko Daddy ya fad'a Eh lafiya lau Toh madallah,shi ya aiko ka ne A'ah bashi ya aiko ni ba,nazo akan maganar yar'ka ne Noor Ya'ta Noor kuma,ai ni yanzu bani da wata ya' Noor,dan yanzu ta tashi daga hannuna ta kuma hannunku Eh Baba,nasan da haka amma maganar da zamu yi tana da amfani,da ka tsaya ka saurareni Daddy ya b'ata rai yace kaga d'an samari,indai maganar Noor ce,bana son ji ka tashi,ka fita tun girma da arziki,kaje ka sami Ubanka shi ke da iko akanta bani ba Yana fad'ar haka,ya tashi ya bar falon Imran ya bishi da kallo,kallon mamaki,Me Daddy da mutumin nan ke nufi,ko shakka babu akwai wani b'oyayyen al'amari tsakaninsu,Ta ya za'a ce Uba baya son maganar yar'sa,kuma duk kud'insa ace ya bar yar'sa a tsiyace,cikin yagaggun kaya Kuma me zai sa Daddy ba zai saketa ba,tunda baya sonta,baya kulata Ya salam! Ina zan samu amsar tambayoyin nan, Ya dafe kanshi Da k'yar ya iya mik'ewa,jiki ba k'wari Yai sallama da Baba mai gadi tare da bashi 1k Ya kama hanyar gida,da tunani barkatai a k'wak'walwarshi""................ Yana driving yana tunani,Anya yarinyar nan ba laifi tama iyayenta ba,shiyasa suka barta hka,toh ina mahaifiyarta? Ga dukkan alamu akwai abunda ita kanta yarinyar ke b'oyewa,dole in bugi ruwan cikinta inji me ye take b'oyewa,bana son aurensu da Daddy"" + ""Noor na watering flowers,tana wak'e wak'enta kamar yadda ta saba a gidansu,damuwa fal a cikin ranta Imran ya fito daga mota ya hangota,Ya Salam! Ya furta sannan Yace ba xasu tab'a bari yarinyar nan ta huta ba,yanzu kuma waya sata watering flowers,ina fatan ba Yazeed bane coz in shine sai ya had'u da mummunan b'acin raina wlh, Ya k'arasa inda take, Wa ya saki wannan aiki? Ya tambayeta Da saurin ta juyo,charaf idonsu ya had'u,gaba d'ayansu sai da suka ji fad'uwar gaba,Tai saurin sunkuyar da kanta,shima ya kawar da kansa gefe A hnkli tace Hajiya Ya d'an yi shiru,Yace ajiye,ki biyoni Ta ajiye tiyon ba musu,tabi bayanshi Can bayan gidan yaje da ita,akwai wasu kujerun roba masu kyau a wajen,ya mata nuni da d'aya yace ta zauna Tana d'ari d'ari dashi ta zauna,kunyarshi take ji kuma at d same time tana shakkar shi,kwarjini yake mata,bata so yace tayi wani laifi Ya murtuke fuska ba tare da ya kalleta ba,ita kuwa tana satar kallonshi,masifar kyaunshi take gani kuma bata gajiya da kallonshi Yace ki saurareni da kyau,bana son k'arya,na tsani k'arya,duk wanda ya mun k'arya ina tsanarshi,tsana mai tsanani Dan haka tambayoyin da zan miki yanzu,ina so ki gaya mun gaskiya,idan kika mun k'arya,na gano k'arya kikai mun,zan tsaneki fiye da yadda kike zato, Gabanta ya fad'i, _ita idan kowa duniya zai tsaneta,ya tsaneta amma banda Imran,hknn taji bata so ya tsaneta,ta bashi wani matsayi mai girma a zuciyarta sbd shi kad'ai ne,bai tab'a mata wani abu ba ,na cin mutunchi tunda tazo gidan,Allah yasa kar ya mata tambayoyin da ba zata iya bashi amsa ba_ Maganarshi ta katse mata tunani,ki saurari tambayoyin da zan miki,ki bani amsa Me ya had'aki da mahaifinki da baya son ko maganarki? Ina mahaifiyarki take,da ta bari kike fuskantar rayuwar k'unci haka? Noor tayi shiru sai hawaye,ya fama mata inda ke mata ciwo,rashin mahaifiyarta da tsanarta da Ubanta yayi _Har ga Allah bana so asan babana ya tsane nine sbd wani dalili da ya sab'awa addinin musulunci,da yadda ubana ya ma mahaifiyata korar kare sbd ta haifeni,bana so girman Ubana ya fad'i a idon kowa,ko na mai k'aryar dalilin da yasa Daddy baya son maganata,nasan har duniya ta nad'e bazai samu ainihin dalilin ba,sbd ba wanda ya sani daga ni Daddy,mummy sai Baba mai gadi,sai fa mahaifiyata kuma cikinsu bbu wanda zai sanar dashi_ Ya katse mata tunani da cewa kina tunanin k'aryar da zaki gaya mun ne,oya go ahead and lie to me Ta girgiza kanta tace A'ah ba k'arya zan ma ba,zan gaya ma gaskiya _Mahaifiyata bata gidanmu,tun tasowa ta ban santa ba,ban san inda take ba, a wajen matar babana na tashi,ita ce bata sona take azabtar dani tasa Daddynah ya tsane ni_ ta k'arasa maganar tana kuka Sosai ta bashi tausayi,kuma ya girgiza da jin bayaninta Kina nufin baki tab'a ganin mahaifiyarki ba,tun tasowarki ? Tayi nodding kanta alamar Eh Gaba d'aya ta gama kashe mai jiki,duk haushinta da yake ji na auren daddysu,ya nemi ya rasa a zuciyarshi,Amma shi abunda ya kasa ganewa me yasa Daddynsu ya aureta,ita knta tace bata sani ba,babu wanda yasan wannan dalili sai Babanta da Daddynsu,anyway yanzu tunda ya gano ba laifinta bane,zai je ya gayawa su mummy, su daina azabtar da baiwar Allah, Ita km Noor sai kuka take Daina kuka kinji,share hawayenki Kina so ki cigaba da auren Daddy? Ta girgiza kanta,kina so ki koma gida Tace Eh _Dan tafi so ta koma gidansu,akan ta cigaba da rayuwa gidan nan a matsayin matar Alhaji_ Shikenan kar ki damu In shaa Allahu zaki koma gidanku,tashi ki tafi d'aki,ki bar watering flowers d'in Tace toh,Nagode Ta tashi tafi,shima mik'ewa yayi ya bar wurin"" ""Kan y'ar katifar ta ,ta kwanta,zuciyarta cike da farin ciki,finally zata bar gidan nan,zata koma gidansu duk da tasan can ma ba dad'i take ji ba,buh ta gwammace can da nan Imran hak'ik'a kai mutum ne,kuma kana da hali mai kyau,Allah ya saka maka da alkhairi, Da ta tuna in tabar gidan ba zata sake ganin Imran ba,sai kuma taji ba dad'i Allah sarki! I will miss yhu wlh although bn saba dakai ba,bfr ko magana baka mun,ko mgn zaka mun sai da fad'a,but care d'in da ka nuna mun kwana biyu,naji bana son rabuwa da kai"" ""Yana shiga falon Hajiya,bata ko tsaya ya gaisheta ba,ta rufe shi da fad'a Akan me zaka hana Yazeed marin Noor,har kana cewa ya fita harkarta,ita ba baiwa bace Imran ya d'an yi murmushi yace Mum kenan,Dalilina na yin hka ba komai bane,illa na dawo daga office,naci karo da Noor a sume,na d'auketa na kaita asibiti,likita ke cewa damuwa ta mata yawa,idan ta cigaba da shiga damuwa,zuciyarta zata iya bugawa ta rasa ranta Hajiya tace toh sai me in ta rasa ranta? Akan me ma zaka d'auketa ka kai ta asibiti ta mutu a wurin,ina ruwan wani Da mamaki yake kallon mum d'inshi bai san rashin imaninta ya kai haka ba,Yace ta mutu fah kika ce Mum Eh ta mutu Imran ranshi ya fara b'aci yace gaskiya mum bazan iya bari yar mutane ta mutu ba,afterall itama ba da son ranta aka mata auren nan ba,yarinyar da ko mahaifiyarta bata sani ba,a hannun kishiyar mamanta ta tashi,ya kamata ace an tausaya mata Wato ta gaya maka labarin k'arya ka yarda,me ye had'inka da ita da har zata baka wannan labarin, Mum ni dai duk ba wannan ba,pls ku bar yarinyar nan ta huta,taji da abunda ke damunta Hajiya a fusace tace ba za'a barta ba,Imran ka fita a idona,kuma ka fita hanyar yarinyar nan in baso kake ka fuskanci mummunan b'acin rai ba, Imran yace naji zan fita harkarta Mum,but please kisa Daddy ya saketa,ta koma gidansu kowa ya huta Idan da ace zai iya sakinta,da tuni ya saketa ta bar gidan nan,dan ni kaina bason auren nan nake ba Da mamaki ya kalli Hajiya yace dan me bazai iya sakinta ba? Imran me yasa kake son shiga hurumin da ba naka ba, Toh Mum plxx one last favor,Dan Allah Dan Annabi tunda Daddy bazai iya sakinta ba,ku barta ta zauna peacefully har ranar da Allah zai kawo rabuwarsu da Daddy, Nan kuma ne baka isa ba,aiki ne dole tayi shi Ya d'unkule hannunshi,ya buga a d'ayan tafin hannu yace OMG ,Zuciyar shi ta kawo wuya,bai sake cewa komai ba sbd yasan mahaifiyarshi ce idanal yace zai k'ara magana zai iya fad'in ba dai dai ba,Imran akwai Zuciya Buga k'ofar falon yayi ya fice Hajiya ta bishi da kallo,tace Ikon Allah,ku ganmu da yaro,kayi ka gama ,Noor ce dai sai ta cigaba da bauta a gidan nan ko zata mutu"" ""Kamar ya had'iye zuciya ya mutu haka yake ji,tsabar yadda zuciyarshi ke tafasa D'akinshi ya shiga ya rufe kanshi da key,yana huci,yana magana shi kad'ai, _daga yau nayi alk'awarin zan kare ki Noor,i won't allow any harm to come to yhu,bazan bari kowa ya cutar da ita ba,zan kula da ita sai inda k'arfina ya k'are,ba wanda ya isa ya hana ni,kuma zanyi iya k'ok'arina dan ganin na raba aurensu da Daddy,akan me zai ce bazai iya sakinta ba,bayan baya kula da ita ya barta tana wahala,Wane irin Uba,Uwa da yan'uwa ne dani, da basu da tausayi ko kad'an a zuciyarsu,Allah ina rok'on ka shiryesu,ka ganar dasu hanya madaidaiciya_ Ya mik'e ya bud'e fridge,ya d'auko gorar ruwa,yasha ko ya rage jin zafi a zuciyarshi Ya kwankwad'a sannan yayi ajiyar zuciya yace *Zan kare ki Noor* *Zan kula dake* *Bazan sake bari wani ya cutar dake ba ko mahaifiyata ce kuwa*""Har dare Imran na d'aki bai fito bh,tunani ne birjik a ranshi,ta yadda zai taimaki Noor Kwan!kwan!kwan! Yaji ana mai knocking bakin k'ofa,tsaki yayi yace Waye Yazeed yace Nine bro Ya aka yi? Ka dai bud'e hot hot See Yaxeed idan na bud'e k'ofar nn,naga shirme ne ranka zai b'aci Eh! Na yadda Imran ya taso ya bud'e mai k'ofa,ya juya ciki Yazeed ya biyo bayanshi yana mik'a mishi wayarshi yace kalli wata babe bro, Bata had'uwa ba Dan Allah Wani dogon tsaki Imran yaja,yace dama abunda zaka gaya mun kenan,wai kai yaushe zaka yi hnkli,kaji tsoron Allah Yaxeed,baka da aiki sai bin mata, Yazeed ya fara gunguni yace haba! Yaya baka tsaya kaji me zance bh,wannan fah aurenta xanyi Na dai gaya maka kaji tsoron Allah Yaya ni fah ina tsoron Allah Fitar mun a d'aki Ya fita yana gunguni yana cewa kai! You re always negative wlh Imran ya tashi ya k'ara sa key ya rufe d'akinshi"" ""Su Hajiya duk ranar basu k'ara waiwayar Noor ba,amma hakan ba wai yana nufin sun bi abunda Imran yace ba,they are just planning me zasu mata,irin azabar da xasu d'and'ana mata,su nuna mata Imran bai isa ya hana su dealing with her ba Hajiya na tak'amar ita ta haifeshi so she has right over him,su Yazeed na tak'ama Hajiya na bayansu"" ""Noor da taga basu bi ta kanta ba,tana ta murna A tunaninta Imran ya musu magana shiyasa suka k'yaleta,yanzu jira kawai take ace Alhaji ya saketa Dan burinta yanzu bai wuce na Alhaji ya saketa ba"" *8:00am* *Ana sanyi sosai har buji ake* ""Engr.Imran ya shirya tsaf zashi office,yana aiki a wani company da ake Generator,Shine Accountant,Sosai yake samun kud'i Sashen masu aiki ya nufa,bakin k'ofar d'akin Noor ya tsaya,yana tunanin ya shiga ko kar ya shiga,yana so yaga lafiyarta kawai wata zuciyar tace toh me ye just ka shiga,ai lafiyarta zaka duba"" ""A hankali ya tura k'ofar d'akin,ya shiga Tana kwance kan sallaya(daga gani Sallah ta gama barci ya d'auketa a nan),ta takure wuri d'aya alamun sanyi take ji, D'akin ya dudduba yaga ko zai ga bargo,yaga babu ko bedsheet,katifar da take kwana a kanta ma hknn take wayam A ranshi yace yanzu duk sanyin nan haka take kwana ba bargo infact ko ma bedsheet babu a katifarta,Wacce irin zuciya ce da Mum haka,da bata da tausayi ko kad'an Ya juya ya fita,d'akinshi ya koma Ya d'auko d'aya daga cikin bedsheet d'inshi tare da blanket Ya rufe ta da bargon,sannan ya shimfid'a mata bedsheet Ya kalleta,yaga yadda taja bargon ta k'udundene,yayi murmushi ya fita,Yana mai masifar jin tausayinta"" ""Noor barcinta kawai take sha,ta lume cikin bargo"" ""Tunda sassafe aka kira Hajiya k'anin babanta ya rasu,ba shiri suka kama hanyar zaria(garinsu),ita,Alhaji ,Yaxeed dasu ihsan,Imran na office bai sani ba"" *11:20am* ""Noor ta farka taji ta cikin bargo Tai saurin tashi zaune,tana kallon bargon mamaki take waye ya lullub'eta da bargon nan mai kyau,takai dubanta ga katifarta taga bedsheet shimfid'e Shiru tayi tana tunani,can zuciyarta tace mata tabbas Maganar da Imran yama su Hajiya ne yasa suka chanza,gashi har rana ta fito ba'a tashe ta ba Murmushi tayi,wani d'ad'i ya ziyarci zuciyarta D'akin ya game da wani daddad'an k'amshi turare Ita dai ji take kmr tasan mai k'amshin turaren nan amma ta kasa gane waye Mik'ewa tayi ta shiga toilet ta kuskure bakinta dan bata da brush,aswaki kawai take kullum(tun tana gidansu,hak'oranta tas suke farare kamar tana sa musu toothpaste),tayi wanka da sabulun(Giv) na lami ne da ta mnta,amma Noor tun tasowarta bata wanka da Sabulu sai fah sabulun wanki ,idan tayi wanki ya rage ta d'auka"" ""Yagaggun kayanta tasa,ta fita kitchen dan tambayar masu aiki,wa ya lullub'eta a cikinsu,ta mata godiya Suna ta famar aikinsu Noor tayi sallama ba wanda ya amsata Ta sake yi, suka mata banza,hkn ya tabbatar mata sun jita suka mata banza Murya a sanyaye tace Dan Allah wa ya rufeni da bargo cikinku ya shimfid'a mun bedsheet Tsaki Abu taja,tace kuji wannan wa zai rufe ki kuwa Suka b'arke da dariya ,suka ce amma ke anyi yar' rainin hnkli wlh,wa kika ajiye da zai miki wannan Ko kin manta matsayinki ne a gidan nan,Baiwa ce kefah ba kowa ba Wannan ya fad'a mata bak'ar magana,wannan ya fad'a,haka suka dinga gasa mata bak'ak'en maganganu Wani bak'in ciki taji yazo ya tokareta,ace gidan mijinka,masu aiki na maka wannan cin mutunchi,ita wannan ba zaman aure tazo yi ba,bauta aka kawota Wasu zazzafan hawaye taji suna kwaranya daga idanunta Ta juya ta fita daga kitchen d'in D'aki ta koma tana ta kukan bak'in ciki da tunanin wa ya shimfid'a mata bedsheet/ya rufe ta da bargo,ta dai san yaran gidan nn ko nasu basa shimfid'awa balle su shimfid'a mata toh ko waye? Ko aljani ne? Cikinta taji yayi k'uuu,alamun yunwa rabon da taci abinchi tun tafiyar Lami,Tace wa kanta yanzu ina zan samu abinchi,nasan masu aikin nan bazasu bani abinchi ba,Allah sarki lami Allah ya jik'anta ba don ta mutu ba Kamar wasa taji cikinta ya murd'e,k'irjinta na zafi, Nan ta rik'e cikinta tana kuka,tana kiran sunan Allah Bargo ta jawo ta k'udundune,tana ta murd'e murd'en ciwon ciki"" ""Tana nan kwance har azahar,tayi kuka har ta gaji,idonta duk sun kumbura,fuskarta tayi jajir kunsan farin mutum Su Hajiya har lkcin basu dawo ba Imran ya dawo gida lunch,dama gida yake lunch Yana parking motar shi straight d'akin Noor ya nufa(ya gani tana nn k an sata wani aikin)"" ""Shesshek'ar kuka yaji,a rud'e ya yaye bargon,yana tambayarta lafiya? Wani abu aka miki? Kamar daga sama haka taji muryarshi,ba tare da ta tashi zaune ba Tace cikina ke ciwo, A hnkli ya furta Ya Salam! Tashi muje asibiti,xaki iya tashi ko na kira Abu ta kama miki Murya a sanyaye tace zan iya Ok tashi muje,Sannu Da k'yar ta mik'e,tana tafiya da k'yar har suka kai mota,ya bud'e mata k'ofar baya,ta shiga ta kwanta,ya mayar ya rufe Ya koma driver's seat yaja mota"" ""A asibitin sai makyarkyatar sanyi take,Sweater(rigar sanyi)dake jikinshi ya cire ya mik'a mata Yace gashi kisa Da mamaki take kallonshi snn ta girgiza kanta tace A'ah Yace karb'a mana Da k'yar take magana sbd zafin ciwo tace ya za'a yi nasa sweater'nka, Ya d'an murtuke fuska yace ki karb'a,bana son kilibibi Jiki a sanyaye ta karb'a,ta rik'e Da d'an tsawa yace sa mana Sannan jiki na rawa tasa coz taga ranshi ya fara b'aci ita kuma abunda bata so kenan"" ""Likita bayan ya dubata ya d'an yi gwaje gwaje,Yace Ulcer ne da ita Imran bai yi mamakin jin tana da Ulcer ba,yasan za'a rina,tsab mum zata iya hana mata abinci Likita ya rubuta magungunan ulcer,tare da cewa ta rik'a cin abinchi,da shan irinsu madara da maltina haka"" ""Imran da ya siya magungunan,shopping mall ya biya Ya siyo katon d'in Maltina biyu,Family size madara d'aya,madarar ruwa katon d'aya,milo,sugar,biscuit,Yoghurt,katon na swan water(ruwan gora) Ya kuma biya restaurant ya siyo take away na jollof rice with chicken, Ko da suka isa gida,shi ya kwashi kayan da kanshi,ko tsinki bai bari ta d'auka ba,har d'aki ya kai mata, Kawai gani tayi yana shigo da kaya,ita mamaki ma ya hanata yin magana,sai da ya gama shigo da kayan,ya samu wuri ya zauna,ya jawo leda take away,ya bud'e ya tura gabanta,Yace oya ci Ba tare da tace uffan ba,ta fara ci,duk da tana jin kunyarshi,hakan bai hanata ci ba, sbd yunwar da take ji,Sai da ta cinye tas Ya jawo kofin dake gefen katifarta,ya bud'e maltina ya zuba a ciki tare da juye gungun madara d'aya(na ruwa) Ya mik'a mata,ta k'arba ta kafa kai ta shanye, Snn ya b'allo magani da ruwan gora,ya bata tasha Ita dai binshi da ido kawai take tana mamaki"" ""Ya mik'e yace kayan nn naki ne,ki rik'a ci,kina shan magani akan lkci,nasan ba lallai ki rik'a samun abinci kullum ba,but zan ma masu aiki magana su rik'a kawo miki Har yasa k'afa d'aya waje A hnkli murya can k'asa tace nago........ Yai saurin katse da cewa No need"" ""Noor tana magana a fili lallai Imran mutum ne,tunda nake ba wanda ya tab'a mun irin abunda Imran yamun sai fah Baba maigadi da ya ilamantar dani,Allah yayi shi mai tausayi, ina ma ace haka sauran yan'uwanshi suke,ko shakka babu d'azu ma shi ya rufeni da bargo,k'amshin turarenshi ne naji d'azu Zuciyarta taji tayi fari k'al,kamar an zuba mata k'ank'ara a zuciya Allah ya saka maka da Alkhairi Imran,Matarka ta more wlh Ya Allah! Ka raba aurena da Alhaji ka bani miji mai irin halin Imran,inma da hali mai kama dashi,dan Imran nada kyau,ina son namiji mai irin kyaunshi Wata zuciyar tace mata baki da hankali,kina a hakan zaki samu miji kamar Imran,ai sai dai mummuna ko tsoho, Kawai sai taji hawaye ita dai bata da madafa,Allah kad'ai ne gatan ta,sai fa Imran yanzu dake neman taimakon rayuwarta.................

Post a Comment for "ITA CE QADDARATA CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...