IN SO YAKI NE CHAPTER 4 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

IN SO YAKI NE CHAPTER 4

IN SO YAKI NE CHAPTER 4

- - Post a Comment
IN SO YAKI NE CHAPTER 4  Da kyar take d'aga k'afa sam jikin ta babu k'arfi, babu abunda yake flashing a kwakwalwan ta se yanda Suraj ya kusa raba ta da iskar da take shak'a, bata tab'a tsintar kan ta ba a irin wannan yanayin, gumi ne yake karyo mata tamkar wanda tayi gudun marathon, kitchen ta shiga ta a daddafe ta bud'e fridge, water bottle ta d'auka tana bud'e wa ta kafa a baki hannu yana b'ari shi kanshi ruwan kasa rik'e wa tayi ya kufce daga hannun ta ya malale a wajen ita ma zame wa tayi a wajen ta zauna ta jingina bayan ta da fridge sannan ta had'e kai da gwiwa tana hawaye+ "why? Why did i have to fall in love? And that too with Suraj? Miye Laifi na a ciki don ina k'aunar ka? I wish that you reap my heart from my chest! Da ya fi min wannan halin da nake ciki? Na yarda abunda na aikata ba daidai bane, hanyar da na bi bai kamata ba but everything is fair in love and war! I just wanted you lo love me just love me Suraj, that's all i need and nothing else!" Duk Maganganun ta Suraj yana ji don ya jima tsaye a kanta, sosai ya tausaya mata, he felt guilty na halin da ta shiga. Zama yayi gefen ta yana kallon yanda ta nutse fuskar ta cikin tafin hannun ta hannun shi na rawa ya d'aga ya d'aura a kafad'an ta, a razane ta d'ago suka yi ido hud'u dukannin su babu wanda ya furta ko da kalma se jerin kwalla dake tsere a kan kunchin su Langab'ar da kai Suraj yayi sannan yace "I......i.aa.....Am SOOR...RY". Wani bugu zuciyar Meenah tayi, tsikar jikin ta ya tashi ta d'an ja da baya don ta k'ara fuskantar Suraj, domin ji tayi kamar a mafarki, ta sani sarai Suraj is not the apologising type.. Cikin Sautin kuka ya sake Maimaita abun da ya fad'a a baya. "I am SORRY! For everything! For hurting you! For hating you for wasting three years of your life, for troubling you! Don Allah ki yafe min I have hurt you times without numbers, i don't even know how you manage to smile all those years ! Na yi realising cewa your love is pure and true. Actually akwai wata wanda ta gaza yin juriyar da kika yi, ballantana tayi irin abunda kika yi. Please forgive me" Kuka Meenah ta saka sannan ta mik'e ta fice daga kitchen d'in, Mik'e wa Suraj yayi ya bi bayan ta "Meenah please stop!". Amma kafin ya sake d'aga k'afa jiri ya ja shi tuni ya zube k'asa tamkar mara rai. K'aran da taji yasa ta juyo, da kyar ta iya jan numfashi tsabar firgici, da gudu ta nufo shi tana k'iran sunan shi "Suraj! Wannan wanne irin wasa ne? Look! Ka yi apologising kuma na yafe maka but please get up if not bazan tab'a yafe maka ba for troubling me again! Ka bani hak'uri amma kuma gashi you are still troubling me! Get up you! Draman naka ya isa haka bani da wani sauran k'arfi a tattare da ni don Allah". Gani tayi bai ko motsa ba don haka ta sake rikice wa "Ba kowa ne a nan? Please help! Ganin ba wanda ya zo ta sauk'e kan Suraj daga cinyarta ta nufi k'ofa da gudu. "Mubeenah hurry please, zan yi latti yau muna da board meeting na tabbata Suraj har ya isa " Ameer ne ke magana yayinda Mubeenah ke bawa Iman abinci. Mik'a Iman tayi a nanny sannan ta mik'e ta d'auki jakar ta "Fine then lets go in ba haka ba bazaka kyale ni ba i'm sure." Basu ankare ba Meenah ta shigo ko sallama babu tana kuka, da kyar ta iya nuni da yatsa direction na sashen su tace "SssUraj! Please help! Suraj! ...." Kafin ta gama rufe baki Ameer ya jefar da jakar shi ya nufi k'ofar fita , ita kuwa Mubeenah k'ok'ari tayi na nutsar da Meenah kafin suka fita zuwa shashen nasu. Khadijah ta fito rik'e da Boboh ta ga shigar su amma bata kawo akanta wani abu ba har saida taga Ameer ya fito da Suraj ba shiri ta nufo inda suke Ameer ya dube ta yace "Yawwa khadija please ki min wannan alfarman, zan kai Suraj asibiti, ki k'ira Habeeb ki sanar da shi abunda ke faruwa, kice ya d'aga board meeting d'in, and kin san Boboh yana fama da fever kwanakin nan, zai fi kyau ki zauna a gida" Kai ta girgiza ta dafa kafad'an Meenah tace "He will be alright inshaa Allah, kar ki damu" kai Meenah ta jinjina kafin ta shige motar Ameer ya tuk'a Suka tafi.... @Maleek Holdings... Yafi missed calls goma a wayan Habeeb amma sam baya Cabin d'in shi ballantana ya gani. Tafe yake yana surutai "Yaa Ilahy! Me yasa har yanzu basu iso ba? Suraj ,Ameer, Mubeenah! Of all days su rasa ranar da zasu yi latti se yau? Already saura five minutes a fara meeting bari de in k'ira Suraj in ji inda yake" Aljihun sa ya laluma amma bai ji waya ba, k'afa ya buga yace "Damn! Wayar ai tana office d'ina " Hanyar Cabin d'in shi ya nufa kai tsaye, yana shiga yaji wayar tana kan ringing, bai b'ata lokaci ba wajen d'aga wa "Thank God Ameer! Yanzu ma k'iran ku zan yi, kun iso ne? Time yayi already......... Katse shi Ameer yayi da cewa "Habeeb!... Suraj yana asibiti" Wani zabura Habeeb yayi yace "WHAT!!!?" Ameer ya sake fad'in "Suraj collapsed completelyHabeeb, na kawo shi asibiti , ni kaina ban san dalili ba har yanzu likita na kan shi, ka bawa board members hak'uri and postpone the meeting if possible ba kwana kusa ba ma" Habeeb bai ma k'arasa jin maganganun Ameer ba ya katse wayar ya fice da sauri, Secretary d'in shi ya tura zuwa meeting Hall d'in da sak'on shima ya fice ya nufi hanyar asibitin infact ji yake kamar ba zai isa ba, all he wanted is to see his dear brother Suraj. ****** ******** ******* "Muhseen don Allah kayi hak'uri but dole in kai Tasleem asibiti, zazzab'in ta yayi zafi sosai, have mercy on my poor child na rok'e ka, i promise i won't cause you any trouble, i can drive zan tuk'a motar ba sai ka zo ba." Kamar bai san tana yi ba haka Muhseen ya cigaba da kwanciyar sa harma da juyi. K'afar sa ta rike ta durk'usa a bakin gadon tace "In kana yi wa Allah ka bud'e k'ofar nan Muhseen, Tasleem is in pain please ka tausaya mata na rok'eka." A fusace ya d'ago ya rafka wa Layla mari wanda hakan yayi sanadiyyar fitar jini daga bakin ta, amma ko ta kan marin bata bi ba tace "Ka dake ni iya yanda kake so amman don Allah Muhseen ka dubi yanda y'ata take b'ari". "Ohhhh! Wai me yake damun ki ne? Use your common sense please! In y'ar ki bata da lafiya what has that got to do with me? How is it my problem Laylah? Na farko de ke kad'ai ce mallaki na, da kece ba lafiya i will do my best , but that girl is not mine, alfarma kawai nake mata hakan ba yana nufin zaki takura min bane. Akwai kud'i a wajenki i am sure kiyi amfani da su ki kai ta asibiti before it's too late sannan ki bar ni nayi bacci in peace kin san party d'in jiya yanda ya gajiyar da ni.." Mik'ewa tayi ta d'auki mayafinta rolling tayi sannan ta d'auki Tasleem da kyar bayan ta d'auki jakar ta, juyawa tayi ta k'are wa Muhseen kallo tayi kafin ta juya ta fice ta tura masa k'ofa , babu abunda take se hawaye tana isa reception wasu ma'aikata biyu suka taimaka mata kafin tace wani abu har sun kawo ambulance nasu aka sa Tasleem ita ma Laylah tare suka tafi zuwa asibitin ......... (True love has the habbit of coming back!) Kuna ganin Suraj yayi abunda ya dace da ya yi accepting Meenah? Shin asibiti zai zamo sanadiyyar Had'uwar Laylah da Suraj a karo na farko bayan tsawon shekaru bakwai? In hakan ta faru Habeeb zai zauna a kan bakan sa na ganin Laylah bata yi magana da Suraj ba ko kuwa zai saduda?? Don samun amsoshin tambayoyin nan ku kasance da cigaban wannan labarin...... Tsaye Habeeb yake ya nad'e hannuwa a k'irji ko kyafta ido baya yi yana kallon Suraj dake kwance helplessly a gado, baka jin komai se k'arar na'ura da kuma sheshe'kar kukan Meenah wanda ke zaune ta gefen gadon hannuwan ta cikin na Suraj d'in. Likita ne ya gama dube duben sa sannan ya dubi Habeeb yace "Mr Habeeb ina son magana da kai, come to my office". Kai Habeeb ya jinjina yace "Sure!". Kusan a tare ma suka fice . @Dr's Office+ " Actually na k'ira ka nan ne to warn you about Mr Maleek's health!" Wani bugu k'irjin Habeeb yayi nan take ya gyara zama yace "Me yake damun Suraj? What is it? I hope it's not worst?" "Relax Habeeb, It's just that health d'in shi ya kamata ya zama first priority nashi but it seems bai damu da kiwon lafiyar shi ba, lately blood pressure d'in shi ya hau sosai, sannan ya yi loosing a lot of blood dalilin yankan dake hannun shi, an yi sa'a blood group naku d'aya, still he is depressed and stressed. Ina so in baku shawara , i will advise you as a family to do your best and keep him happy, k'aramin b'acin rai barazana ce ga rayuwar shi , shi yasa mukayi recommending bed rest na kwana biyu, ba aikin office ba meetings, nothing! Let him just rest" Kai Habeeb ya gyad'a kai Suka mik'e tare da doctor sannan ya mik'a masa hannu suka yi shaking "Thank you doctor, we will do our very best insha Allah, thank you". Ameer ne tafe da prescription na wasu magunguna da zai siyo, kukan da ya jiyo ne yasashi tsayawa chak ya dubi gefen shi na hagu , k'usurwan bango ta samu nan ta mak'ale ta had'e kai da gwiwa tana rafka kuka, har Ameer zai wuce kuma se ya d'an yi tunani don haka ta nufi inda take ya d'urk'usa a gaban ta yayi mata sallama A hankali ta d'ago ai kuwa suna yin ido hud'u duk suka mik'e a tare kamar wad'anda aka mintsina "A...Ameer??" Ta k'ira sunan shi muryar ta duk ta dishe "Laylah! Laylah me yasa kike kuka? What happened? Me yasa kike zaune a nan, on bare floor? Me ya kawo ki asibiti?" Shi Ameer a tunanin shi Laylah ta san Suraj yana Asibitin amma amsar ta ce ta bashi mamaki "Ameer, Tasleem ce ba lafiya ni tsoro nake ji kar wani abu ya sameta, in hakan ta faru bazan yafewa kai na ba" Ameer cike da mamaki yace "Tasleem? Wace ce Tasleem??" Kafin Laylah ta bashi amsa Ameer yaji an dafa kafad'ar shi. "Tasleem is our daughter". Kalaman Muhseen ne yasa Ameer juyawa da wuri don yaga mai maganar "MUHSEEN ALI?" Ya furta cike da mamaki Muhseen ya zaga zuwa b'angaren Laylah ya rungumo kunkumin ta sannan yace "Yess! Ni d'in ne de, and this is my lovely wife LAYLAH! Sannan Tasleem is our cute daughter". Wani Bugu k'irjin Ameer yayi da jin kalaman Muhseen, idanuwan shi suka yi ja tsabar takaici bai san cewa yayi squeezing prescription d'in dake hannun shi ba. Laylah taka yanda Ameer ya sauya karaf d'aya hakan ya bata tsoro, gashi ita ta ma rasa dalilin da yasa Muhseen ya zo asibitin bayan tun farko ya ce bazai zo ba. Ta tabbata wani sabon shirin ne na musguna mata ya had'a. Muhseen ne ya kawar da shirun ta hanyar cewa "By the way ina Mr Suraj Maleek? Jiya had'uwar mu was not quiet a pleasant one, zan so mu zauna da shi mu tattauna" Wani d'an murmushin Takaici Ameer yayi kafin yace "Well.... Suraj yana nan lafiya, as you can see i'm in a hurry, in bazaka damu ba i will take my leave". Ameer bai jira me Muhseen zai ce ba ya juya zai bar wajen, jin muryar Habeeb ne yasa shi ya tsaya chak. "Ameer!... What is wrong with you? Tun d'azu ko maganin baka siya ba? Suraj zai farka any moment from now doctor yana ta jira fa". Maganganun Habeeb ne yasa saida Laylah ta kusa zame wa k'asa Muhseen ya sake matse ta a jikinshi. Yayinda Habeeb ya ja Ameer suka bar wajen, shi asali ma Habeeb bai gansu ba . Kasa rik'e hawayen ta Laylah tayi musamman da taji Habeeb ya ambaci Suraj ba lafiya. Tuni ta fara karkarwa cikin ranta tace "Miye haka yake shirin faruwa? Tasleem da Suraj a asibiti at the same time?? Wannan wacce irin jarabawa ce??". "naga alama duk inda na sake na baki freedom se kin b'ata min rai ko?" Muryar Muhseen ne ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga a firgice ta d'ago tana kallon fuskar shi ba tare da ta san me ya fad'a ba. Matse ta yayi a jikin shi kamar zai had'e da ita, sannan hancin shi na gugan nata murya ciki ciki yace "Instead ki fitar da yarinyar ki cikin ruwan sanyi ku taho asibiti, duk da cewa kin d'auki makullin mota seda kika yi creating scene a hotel, kin k'ira ambulance kina kuka duk kin wani rud'e, kafin na ankara ko ina ya d'auka kowa na nuna ni, na shirya zan fita zuwa party amma saboda Press da ke neman na fad'a kinga inda na k'are! I ended up in this bloody hospital !! Wannan karon rik'on da yayi mata ya yi k'arfi sosai don yanda ya sake matse ta. Daidai lokacin Laylah ta had'a ido da su Habeeb da Ameer dukkanin su babu wanda ya iya motsa wa ko da inch tsabar takaici, don haka Laylah tayi iya k'arfinta ta fisge kanta daga rik'on da Muhseen yayi mata, a lokacin ne Habeeb suka fice daga wajen kowa yana sak'e sak'e a ran shi. Tsugunne tayi a wajen tana hawaye shi kuwa Muhseen yayi tafiyar sa ko ta kan Tasleem bai bi ba ballantana lamarin rashin lafiyar ta.+ ...... "Habeeb i'm sooo tired of lying down all day! Please mu fita in d'an zagaya duk k'afafu na bana jin dad'in su" Suraj ya k'are maganar yana k'ok'arin sauk'a daga kan gadon . Da sauri Habeeb ya rik'e shi yace "kayi hauka ne? Yaushe ma ka bud'e ido da har kake neman fita? Dubi jikin ka duk babu kwari, ka bari tukunna likita ya duba ka, Ameer ya tafi yayi magana da shi likitan". Ba musu Suraj ya koma ya kwanta sannan ya jingina da pillow tare da taimakon Habeeb. Tab'e baki yayi sannan yayi rolling idanuwan shi yana kallon Habeeb dake zaune a kujera ta gefen shi yace "How disgusting! An wani ajiye mutum se wani tarairaya shi ake kamar mai nak'uda, Habeeb pleeeese let me go out! gadon nan mintsini na yake wlhy." Wayar dake hannun shi ya ajiye idanuwan sa cikin na Suraj da wani irin serious look , nan da nan Suraj ya had'e gira yace "Miye hakan? Wannan wanne irin kallo kake yi min haka? It's not like nayi maka sata Habeeb i was simply just asking for some fresh air, shine zaka tsare ni haka da ido? Habeeb ya kad'a kai da slight murmushi yace "Kawai de mamaki kake bani, kai da kanka kayi sanadiyyar kasancewar ka fa a nan asibintin and yet you are complaining... Trust me in ka k'ara complaining se nayi smashing fuskar ka da takalmi na! God!! Wlhy Suraj wasu lokutan you are so annoying. I just don't understand why you will hurt yourself saboda wanda bai damu da kai ba, bai ma san kana existing ba a duniya you keep on hurting yourself again and again shin mu baka damuwa da irin halin da zamu shiga idan baka farin ciki? We are brothers Suraj! We've got each others backs all the time, baka son kaga mun shiga matsala amma kai kullum kana jefa kanka a ciki. Kana tunanin in kayi hakan ran mu zai yi fari ne? No! Not at all Suraj, zan rok'eka don Allah Suraj ka gyara for our sake atleast." Kai Suraj ya jinjina ba tare da ya furta komai ba ya lumshe idanuwa yana murmushi kawai. Shiru ne ya gauraye d'akin kai kace ba kowa a ciki Suraj bai ce qala ba shima Habeeb ko tari bai yi ba se ma daukar wayar sa da yayi yana buga game. Shigowan Ameer da Meenah ne yayi breaking silence d'in "Hey! Ya kake? Ya duk naga kun yi shiru?" Ameer bai jira amsar su ba ya buga tsallen sa ya haye gadon da Suraj ke zaune, ai kuwa ba shiri Suraj ya nad'e k'afafun sa da wuri yana dariya Shima Habeeb dariyar tsallen yayi yace "Ameer lafiyar ka kuwa? Miye haka?" ya karishe maganar yana dariya. Ameer kuwa bai bi ta kan su ba ya fiddo wayar sa ya fara surfing. Meenah de na tsaye ta rik'e k'arfen gadon hakan ya bata damar fuskantar Suraj, shima kallon nata yake a ranshi yace "Ko kad'an bana jin soyayyar ki a raina Meenah, i just pity you! Sannan bana so in yi hurting naki saboda makahon son da kike min, ni kad'ai ne zan iya fahimtar zafin so, saboda haka i will pretend to love you domin ki samu sukuni a ranki. In nayi hakan zan faranta miki kuma nima zan samu sukuni a raina cewar ban tauye miki hakkin ki ba as my wife i will do my best to keep you happy". Duk maganganun nan a ranshi yake yi bai ma san likita ya shigo har yana masa magana ba. Nad'e hannuwa doctor yayi a k'irjin shi domin har ya gaji da yi masa magana. Dariya ce ta kufce wa Habeeb yace "Sorry about that doctor" ita de Meenah kai ta girgiza tace "Ya Habeeb zan wuce masallaci time na sallah yayi, ku ma zai fi muku ku tafi ku yi sallah coz ban san duniyar da Suraj ya mak'ale ba, he's so weird." Ta k'arashe maganar da tab'e baki sannan ta fice. Doctor kuwa murmushi yayi ya dafa kafad'ar Suraj a wannan karon ne ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga, da murmushi ya dubi doctor yace "Finally! Tun d'azu kai nake jira ai." Dariya doctor yayi yace "ni d'in ma kai nake jira, thank God ka dawo hayyacin ka, anyways babu wata matsala de ko? Ba hajijiya ba ciwon kai? " Gyara zaman shi Suraj yayi kafin yace "Matsala kam akwai, kuma in na cigaba da zama a nan all day taruwa matsalolin zasu yi i am serious". Duk ya basu dariya musamman doctor saboda yanda ya ke magana a hak'ik'ance. "Alright what's the problem Mr.Maleek?" Snapping yatsun shi Suraj yayi sannan ya nuna doctor da yatsa yace "Tambaya mai kyau! Matsalar ita ce _ na gaji da zama, i am tired of this room i need fresh air saboda haka ina so in d'an fita in sha iska faqat". Kai doctor ya jinjina yayi y'an dube duben shi yace "da ina tunanin se gobe zan sallame ka but seems like komai is normal zan yi prescribing wasu magunguna se ku iya tafiya, Mr Habeeb please se ka tuna da maganganun da mukayi sannan a kiyaye. Mik'e wa Habeeb yayi suka yi shaking hands da doctor haka ma Suraj ya mik'a masa hannu likita yayi masa Allah k'ara sauk'i ya fice. Habeeb da Ameer suka juya a tare suna kallon Suraj da Murmushi kafin suka bushe da dariya sannan duk suka rungume Suraj dake zaune "Kai! Me hakan kuke yi! Ku shika ni dallah chan kun bi kun wani mak'ure ni so kuke na koma gidan jiya ne" Suraj ya k'arishe maganar yana bugan k'irjin Ameer da hannun shi. Kamar walk'iya haka yaga wucewar ta, wani bugu zuciyar shi ta fara tamkar wanda za'a yanka daga kaga yanayin fuskar shi zaka ga mamaki a shimfid'e k'arara, da kyar ya sauk'e k'afar shi daga kan gadon ko takalma bai sa ba ya nufi k'ofa, Habeeb na rik'o hannun shi ya juyo suka had'a ido da Habeeb d'in , hankalin Habeeb ne ya tashi da yaga kwalla a idanuwan Suraj d'in "Suraj control yourself! Miye haka ka gani ina kuma zaka je ko takalmi babu?" Tambayoyin da Habeeb yayi masa kenan se lokacin Suraj ya iya bud'e baki yace "Na tabbata ita na gani! Habeeb yanzu naga Laylah ta i am sure it's Laylah, k'ofar nan a bud'e, naganta ta wuce i'm sure it's my Laylah! Habeeb lemme go please ka barni in ganta ka sake min hannu Habeeb"......

Post a Comment for "IN SO YAKI NE CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...