IN SO YAKI NE CHAPTER 2 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

IN SO YAKI NE CHAPTER 2

IN SO YAKI NE CHAPTER 2

- - Post a Comment
IN SO YAKI NE CHAPTER 2  SHERATON ULTIMATE HOTELS ABJ+ Motar na tsaya wa driver ya fito ya bud'e musu k'ofa, fitowa Muhseen yayi yana gyara zaman rigar sa yana k'are wa harabar Hotel d'in kallo, duk da cewa duhu yayi k'ayatuwan wajen mara misaltuwa ne, mutane d'add'aya ne ke kai kawo a wajen wasu turawa wasu bak'ak'e abun gwanin burge wa. Jiki ba kwari ta fito sannan ta rungume yarinyar ta tsaya tana kallon shi "What now? What's that look all about?" Ya tambaye ta a fusace. Kai ta sunkuyar k'asa ta sake k'ank'ame y'ar ta kamar wanda za'a kwace. Shige wa yayi gaba tana biye da shi a baya, reception ya nufa suna de bayan shi wannan karon ta sauk'e yarinyar k'asa tana suna tsaye. "Mommy...... I need to pee! Mommy please take me to the bathroom or else i will wet my pant!" Abunda yarinyar ke fad'a kenan tana ta matse k'afafu Matar saida ta juya ta dubi Muhseen, ganin hankalin shi baya kan su yasa ta ce "Shush! Tasleem.... Don't worry we will look around for washroom, muje kafin daddyn ki ya ji ki else we both will pay the price". Tana rufe baki ta ja Tasleem d'in suka bi wata hanya da sauri. "Sir here's your key! Enjoy your stay here!" Receptionist d'in ta fad'a tana murmushi, shima murmushin yayi ya mik'a hannu ya amshi key d'in , juyawan da zai yi ya neme su ya rasa, zo kaga huci da yake yi idanuwan sa look fierce and sharp like a dagger ya dunk'ule hannu yana cije baki yace "This woman never seize to Surprise me! Ina kuma ta je? I just don't understand how she is so dull and stupid! She always does things the way she wanted, and that daughter of her's , i feel like strangling her to death already, she is nothing but a distraction!! I won't spare you today!" Hanyar da suka bi shima ya bi yana dube dube, tsugunne ya hango ta tana gyara wa Tasleem riga, a fusace ya k'arisa zai hau masifa amma se yaga mutane, ita kuwa jikinta tuni ya hau b'ari. Wani shu'umin murmushi ya saki wanda bai kai zuci ba ya sa hannu ya rungumo ta jikin sa harda kissing goshin ta yace "Darling, ina kika shiga? Kin kuwa san yanda na damu? Come on dear muje in ba haka ba zamu yi lattin zuwa partyn". Jikin ta de bai bar rawa ba ya matse ta a jikin sa tun k'arfin sa sannan ya rad'a mata a kunne cewa "Smile...... Sannan kada kiyi zaton na hak'ura, zaki gaya min uban me kike yi a nan, because i don't remember telling you to go anywhere." Murmushin dole ta saki idanuwan ta fal hawaye ita kuwa Tasleem na biye da su a baya har suka isa k'ofar d'akin, room service ne ya shigo da luggage nasu a kan troley ya sauk'e sannan ya fice. Shi kuwa Muhseen take ya maida duban sa gareta kafin ta ankara tuni ya had'e ta da k'ofa ya mak'ure "Uban me kike yi a wajen? Ko kin manta baki da hurumin yin komai ba tare da kin sanar da ni ba? Ina kika shiga?" Kai ta girgiza a susuce tace "Babu inda naje Tasleem ce zata yi fitsari wlhy ba da gangan na bar wajen ba please i am sorry don't hurt me atleast ba a gaban Tasleem ba. Na rok'e ka kayi wa Allah kayi hak'uri bazan sake ba!" "HAH!!!! Kullum de maganar d'aya ce! Bazan sake ba, i am sorry, i won't repeat such mistakes but you end up repeating them again and again LAYLA RASHEED!! Ban san lokacin da zaki waye ba, you are not my type at all! Sannan wannan y'ar taki........." Kasa k'arisa maganar yayi lokacin da ya had'a ido da Tasleem dake ta faman kuka, wajen da take tsaye ya nufa ya durk'usa gaban ta yana mata kallo mai ban tsoro yace "listen good for nothing! Ki rufa min baki in ba haka ba zan cigaba da dukan Mom d'in ki". Tuni ta share hawayen ta ta nemi waje ta zauna. Juyawa yayi ya dubi LAYLA yace "Na yi ordern abinci kafin y'ar ki ta fara creating scene, nan da mintina talatin ki tabbatar kin shirya kar ki b'ata min lokaci already you have spoiled my mood" yana kai nan ya juya ya sa kai yayi waje. Da gudu Tasleem ta rungume ta tana kuka "Shush..... Ya isa haka stop crying mommy is here! Tashi muje in miki wanka se ki ci abinci na tabbata baby na tana jin yunwa!" Kai ta jinjina yayinda Layla ta kama hannun ta suka nufi Bathroom. Cikin gaggawa tayi komai saida ta tabbatar Tasleem taci abinci tayi nak sannan itama taci, daga nan ta shige tayi wanka. Cikin lokaci k'alilan ta kimtsa tsaf cikin tsadaddiyar doguwar riga turquoise sannan ta d'aura bak'in turban, bata wani yi heavy makeup ba amma Masha Allah tayi matuk'ar kyau. Juya wa tayi ta dubi Tasleem dake zaune tana game "Yanzu yaya zan yi? Ina zan bar Tasleem, gashi Muhseen in ya fara partying bai san ya tsaya ba, Allah kad'ai yasan yaushe zamu dawo, bazan iya barin y'ata a wannan d'akin ita kad'ai ba dole in tafi da ita ko ma me zai min sedai yayi" a zuci take maganar idanuwan ta a kan Tasleem. Hannunta taja suka nufi k'ofar fita bayan ta sa takalman ta. Tun daga nesa ya hango su, rai a dak'ile yace "Oh God! What does this woman thinks, that i will take that girl to a party? At this time of the night! Hah.... Impossible..." Layla na k'araso wa kafin yayi magana ta ce "i promise you Tasleem won't be a burden, ba wajen partin zan shiga da ita ba, zata zauna a mota i'm sure she will be comfortable, kuma nima zan fi sake wa da hakan tunda bazan ji tayi nesa da ni ba, in na barta a nan ko na tafi hankali na bazai kwanta ba, don Allah Muhseen let me take her along" Bai kula ta ba ya shige motar ita ma ta saka Tasleem sannan ta shiga. Duk zagi da tsangwama ta shanye duk dan kar ya chanja mind d'in shi.......1 ******* ******* ******* Habeeb na fita daga sashen Suraj ya koma side nashi cikin sauri "I just hope zasu yi abunda ya dace!" shine abunda ya furta... Living Room ya shigo babu ko motsin mutum don haka ya nufi bedroom d'in shi Kokawa take tayi da zip d'in rigar ta kwata kwata ta kasa rufe wa, ta kai wajen minti uku a haka kafin shigowar Habeeb. Dariya yayi ya k'arisa kusa da ita yace "daga k'arshe de my dear wife zaki amince da maganar da na fad'a miki kwanaki biyu da suka wuce ko? Dubi fa zip ma ya kasa rufe wa. My dear kawai ki yarda cewa kin k'ara k'iba!" Had'e rai tayi ta juyo cike da shagwab'a tace "God!!.....Habeeb na fad'a maka bana so ni babu k'iban da na k'ara, besides in na k'ara ma ai laifin ka ne". Dariya ya sake yi sannan ya janyo ta jikin shi yace "Finally someone is admitting cewa yayi k'iba! But how is that my fault huh?." Murmushi kawai ta sakar masa sannan tace "please help me now, na kasa samun rigar da zata yi fitting d'ina ta yaya zan raka ka party a haka?" Tab'e baki yayi ya kashe mata ido sannan yayi kissing d'inta sannan yace "in that case then lets stay at home, babu riga babu party lets spend the night together! Alone just the two of us, look through the window, kiga yanda sassanyar iska ke busa wa, i believe even the whether is in our favour!" Dariya tayi sannan ta zame daga jikin shi tace "No way! I want to go to the party i really do Habeeby". Murmushi yayi yace "shikenan, ki duba closet d'in ki na ajiye miki surprise and you will love it".da sauri taje ta duba, ruffled gown ce mai kyau bak'i a rataye, da gudu ta dawo tayi hugging Habeeb har suna zubewa a k'asa "Hahah! KHADIJAH....What...... Me haka kike yi, dubi kin jefar da mu a k'asa, come on! Je kiyi sauri ki shirya else we'll be late". Dariya tayi sannan ta mik'e ta nufi bathroom, Habeeb ya bita da kallo yana murmushi kafin shima ya fara shiri.... A tare suka sauk'o daga bene hannun Khadija cikin na Habeeb se hirar su suke na masoya, come see perfect match. Mubeenah da Ameer na suka yi sallamah hannun Mubeenah rungume da yarinya da bata wuce shekaru uku ba. "Aha! Khadijah i was wondering if zan iya barin Iman a nan, her nanny is not home tayi tafiya so bazan iya barin ta ita kad'ai ba". Mubeenah ta k'are maganar da Murmushi "Ji Mubeenah da wata magana, nan da chan ai duk d'aya ne, besides Boboh ma yana barci a ciki kuma akwai nannies lets put my princess to bed" cewar khadijah Nan suka koma ciki a tare , Mubeenah ta kwantar ta sannan suka fita..... Note; Khadijah itace matar Habeeb Mubeenah itace matar Ameer Tasleem y'ar Layla ce Muhseen shine mijin Layla Iman ita Yar Mubeenah da Ameer ne Boboh, mai sunan Suraj ne kuma d'an Habeeb da khadijah... Zaune ta hango shi cikin mota ya jingina a jikin kujera idanuwan sa a lumshe, k'arisa wa tayi ta bud'e k'ofar baya tayi zaman ta a owners kamar bata san yana ciki ba, duk iyayin ta yana ji se da ya jira ta zauna comfotably, idanuwan shi a lumshe ba tare da d'agowa ba yace "Me kike nufi?, nayi miki kama da driver ne ko me?" Murmushi tayi kafin ta matso jikin kujeran shi tace "Suraj... In kai ba driver bane me yasa ka zauna a wajen sa? Party fa zamu je kamata yayi ace kana gefe na, sanin kanka ne ni bazan zauna a gaba ba that doesn't sound classy to me at all, ka bar driver yayi aikin shi kawai!"+ Fita Suraj yayi daga motar a fusace ya bud'e inda take ya shiga sannan ya fisgo ta daf da shi ita kanta saida ta tsorita da idanuwan sa hasali ma kasa had'a ido tayi da shi a karo na biyu "Ki saurare ni Meenah! Naga alama baki karanci halayya na ba har yanzu, rawan kan ki yayi yawa, kin manta cewa wannan gida na ne, mota na ne sannan ke kanki a k'ark'ashi na kike! Ina da daman da zan yi abunda na so, yau ban ga daman zama a baya ba, sannan bana ra'ayin wani driver ya tuk'a ni in kin ga hakan bai miki ba don kina da daman d'aukar wata motar ki tafi driver zai kai ki but in de da ni zaki tafi believe me ba ki isa ki sa in yi abunda ban yi niyya ba i hope i have made myself clear?" Murya k'asa k'asa tace "Yess" Sannan yayi wani shu'umin murmushi yana gyara hannun rigar shi ya ce "Good , so now kina da zab'i ki shiga gaba ko ki chanja mota". Yana kai nan ya fice ya koma drivers seat yana kallon ta daga madubi, rai a b'ace ta d'auki purse d'in ta ta fice gami da banke k'ofar motar da k'arfin tsiya har saida suraj ya tsorita, gaban ta dawo ta zauna cike da k'unci ba tare da ta kalli inda yake ba "Oh my goodness! Sweetheart irin wannan rufe k'ofa haka? Ai nayi zaton glass d'in ya fashe, barin baki shawara. Nan gaba do not vent your anger on my car saboda ina ji da motar sosai" Kalaman Suraj sun k'ara b'ata mata rai amma bata kula shi ba se ma murmushin yak'e da ta sakar mishi had'e da harara. Shi kuwa fuska fal murmushi ya tada mota ya fice daga harabar gidan....... @party... Taro ne na masu hannu da shuni, y'an siyasa, jarumai da sauran su, a very high profile party! Motar Suraj na tsaya wa aka bud'e masa k'ofa ya fito da murmushi Kusan tare su Habeeb ma suka iso, Suraj ko ta kan Meenah bai bi ba ya wuce yana gyara rigar sa ga media se d'aukar hotuna suke, rai a dak'ile ta bud'e k'ofar ta fito tana kallon Suraj da ya ma kusa shigewa Hall d'in, Habeeb ya ga abunda ke faruwa don haka kawai ya girgiza kai ya rik'e hannun khadija suka shige haka ma Ameer da Mubeenah. Action d'in Suraj ya janyo maganganu a gun y'an jaridu wato gossip magazines. "Happy anniversary Brother!" Suraj ya fad'a gami da rungume Hon. Sufyan Khalil . Shima hugging d'in Suraj yayi yace "Thank you Bro! naji dad'in zuwan ka, despite being a busy man, still ka samu lokacin attending, wannan ba k'aramin abu bane a waje na!.......meet my beloved wife Zarah". Murmushi Suraj yayi kafin yace "Hi mrs. Sufyan Happy Anniversary! And nice meeting you". Ita ma zarah murmushi tayi tace "Thank you and its a pleasure meeting you too". Haka ma su Habeeb suka yi wishing Sufyan kafin kace me party ya d'auko dad'i kowa yayi grouping wasu na discussing business, wasu politics wasu kuma gossips musamman ma matan wanda kowa takara take da y'ar uwarta wajen ganin ta kece raini, Meenah ta shige cikin mata y'an uwanta masu aji top class se gossips ake yi amma idanuwan ta kan Suraj da activities d'in sa. Mubeenah da khadijah kuwa suna tare suma da nasu hirar. Kayan ciye-ciye se wanda ka zab'a....... A tare suka shigo hannun shi guda sak'ale da kunkumin ta daga baya daga ganin murmushin fuskar ta kasan na yak'e ne shi kuwa tun daga k'ofa Muhseen ya fara aikin sa na kashe wa mata ido daman chan haka yake sharholiyar sa. A tsorace take k'are wa wajen kallo, sosai wajen yayi kyau ya k'ayatu. sosai Layla taji dad'in shigowa cikin jama'a domin in a idon mutane ne Muhseen bai cika yi mata rashin mutumci ba hasali ma yana nuna mata so kamar ya had'iye ta in ma zai yi halin nashi toh y'ar k'asa-k'asa yake yi saboda kar a gano shi. Sake Layla yayi da fara'ar sa ya nufi inda Sufyan ke tsaye tare da su Habeeb STORY CONTINUES BELOW "Haaappyyy Anniversary Partner!" ya fad'a lokacin da ya k'arisa inda suke gami da ware hannuwan sa suka rungume juna "Hah!! Thank you partner! Naji dad'in zuwan ka! Yaya kake , yaya Newyork? " Sufyan ya tambaya "Well Newyork na nan yanda yake nima kuma yanda nake babu wani abu sabo, as usual Work, parties , business ,women!! " Duk Sufyan da Muhseen suka bushe da dariya kafin Sufyan yace "You will never change partner! Kai da mata...... Ina Madam ne yaya ban ganta ba ko de baka taho da ita ba?". Tab'e baki Muhseen yayi kafin ya juya yana d'an dube dube yace "tare muka zo, you know how middle class she is, yanzu haka tayi wani wajen she likes being alone." Kai Sufyan ya girgiza yace "Goodness me! Muhseen maganar matar ka fa ake yi yaya zaka yi degrading d'in ta haka?" Murmushi Muhseen yayi ya dafa kafad'ar Sufyan yace "Listen Partner, kana magana kamar baka san ni ba, Muhseen ne fa! You know i prefer hot spicy girls, and LAYLA is nothing close to those type of girls!" Jin kalmar "Layla" da Muhseen ya furta yasa k'irjin Suraj dukan uku uku tuni ya sauk'e glass d'in drink da yakai baki ya juyo yana kallon Muhseen. Amma se ya kawar da tunanin da ya zo kan shi da sauri ya kurb'i drink d'in a ranshi yace "Zai yiwu ba LAYLA ta bace, besides mata da yawa suna da wannan sunan, its possible kawai suna taci, but somehow i feel so restless"... Sufyan ne ya dafa kafad'ar Suraj yace "Brother! Me kake tunani haka? Anyways Meet my business partner and friend Muhseen! He just arrived from Newyork sannan zai zauna a nan na wani lokaci saboda parnership da muke yi, Muhseen wannan shine Suraj Abdoul-Maleek CHAIRMAN, MALEEK HOLDINGS, A trendsetting industrialist nasan ka tab'a jin labarin shi" K'are wa Juna kallo Suraj da Muhseen suka yi kafin Muhseen ya tab'e baki ya mik'a wa Suraj hannu, shima Suraj a gadarance ya Mik'a hannun sa suka yi shaking, Muhseen ya saki murmushi yace "Hi! Mr. Maleek... I have heard a lot about you, its a pleasure meeting you!" "pleasure is mine.." shine kalmar da ta fita daga bakin Suraj yayinda ya cigaba da hirar sa da Ameer. Muhseen ya ja Sufyan gefe yace "Wai wannan me yake tak'ama da shi? Mutane da dama suna mutuwar ganin na had'a hannu da su amma har zan fara mik'a masa hannu for a handshake ya nuna gadara! Sufyan this friend of yours is surely playing with fire!" Sufyan ya zaro ido waje yace "Oh please Muhseen! Kar kace haka, Suraj yana da muhimmanci a wannan partnership d'in kada kayi abunda zai sa mu rasa Billions . Suraj haka yake daman just forget it" Duk abubuwan da suke fad'a yana kunnen Habeeb kawai kallon su yake yi shi kuwa Suraj bai ma bi ta kan su ba ballantana yaji me suke yi...... Tafiya take a hankali tana taku d'add'aya su kansu Matan saida suka sha jinin jikin su ganin irin dukiyar da ke jikin ta da kuma kyau da Allah yayi mata. K'awar Meenah ta ce "Oh my God! She is wearing that piece of jewellery! Wanda muke maganar shi yanzun nan, in ban manta ba jiya ya shiga kasuwa, that necklace is worth millions! Wacece ita?". Wata ma daga gefe tace "and that gown! It's designed by Moschino last week na gani a fashion magazine in fact yana daga cikin top three designes. Naji ma an ce Ita ce LAYLA Matar Muhseen Ali, she is hot like her husband!!." Tab'e baki Meenah tayi ba tare da ta furta kalma ba se ma wani takaici da ya taso mata saboda a kullum itace talk of the town, sannan ko wanne party se an yaba shigar ta amma karo na farko yau duk yan k'ulin nata sun haukace a kan wata macen da basu san ko wacece ba. Hakan yasa ta mik'e a fusace ta bar wajen rai a b'ace. Ganin ta tashi ya tabbatar musu cewa Meenah was jealous don haka suka bushe da dariya hakan ma sake k'ular da ita yayi, bar ta nufa ta d'ale kujera ta bawa kowa baya "One glass of rapsberry drink please" Ta fad'a tana dafe kai...... Gefen Su Mubeenah ta zauna gami da yi musu sallama, cike da fara'a suka amsa mata sannan ta d'auki wayar ta tana buga game. Duk abunda Muhseen yake yi idanuwan ta yana kan shi. A hankali tace "Dube shi kamar mutumin kirki, acting so freely ji yanda yake hira, ina ma ace haka yake ko a gida, Muhseen ina ma ace ban had'u da kai ba? Ina ma ace baka shiga rayuwa ta ba, you are not like him at all, shi ya kasance mai kulawa da ni and you!.... You are just the total opposite, ya nuna min k'auna a zahiri da bad'ini kai kuma babu abunda kake nuna min se k'angin bauta da ka sa ni a ciki. SURAJ ina ka shiga ne? Shekaru da dama amma har yanzu babu abunda ya chanja daga irin k'aunar da nake maka, ban sani ba in daidai ne abunda nake yi but Muhseen is nothing to me when it comes to you Suraj. Where are you!!!".. She'shek'ar kukan ta ne ya janyo hankalin su Mubeenah, taso wa suka yi zuwa inda take, khadija ta dafa kafad'ar ta tace "Lafiyan ki kuwa? Me yasa kike kuka haka that too at such a party, is there anything we can do to help?" ta k'arisa maganar tana mik'a wa Layla handkerchief. Hannu ta sa ta karb'a sannan ta share hawayen nata da shi sannan ta saki tsadadden murmushi tace "Ba komai, just lamuran rayuwa and all, nagode da kula wa". Murmushi Khadija tayi sai tace "duba! Nima mace ce y'ar uwar ki, idanuwan ki kad'ai sun isa su nuna cewa kina cikin damuwa, ki d'auke ni a matsayin k'awar ki ko kuma sister and tell me me yake damun ki". Kai Layla ta d'ago ta kalli Khadija tace "Na tabbata kina da aure, sannan daga gani kina cikin matuk'ar farin ciki! Toh zan baki shawara, duk girman laifi da mijin ki yayi miki,duk girman kuskure da ya tafka toh ki samu wani gurbi a zuciyar ki da zaki yafe mishi ko da zai d'auki lokaci to forgive him completely ki cije ki daure! Na koyi darrusa da dama a rayuwa, a lokacin da yace in bashi dama k'i nayi a k'arshe turar shi ta kai bango ya zartar da hukuncin da har in mutu bazan yafe wa kai na ba i will keep regretting it till the end of my Life, duk wannan saboda kuskuren mutum d'aya tak!" Mubeenah da khadijah suka kalli juna sannan suka maida duban su ga Layla ba tare da sun fahimci inda maganar ta tanufa ba. Murmushi tayi musu sannan tace In bazaku damu ba i will go and check on my daughter". Daga nan ta mik'e ta wuce ta bar wajen suka bi bayan ta da kallo...... Kallon shi take tamkar zata had'iye, duk motsin shi tana gani. Murmushin fuskar ta kuwa se k'ara fad'ad'a yake yi, Langab'ar da kai Meenah tayi tana juya kujeran da take kai tana kad'a glass d'in hannun ta mai d'auke da drink har lokacin idanuwan ta kan Suraj suke. Tun Suraj bai fahimci hakan ba har abun ya fara damun shi don haka ya dubi su Sufyan yace+ "Ammm... Excuse me please, be right back". Yana kai nan ya nufi inda take zaune har lokacin kallon sa take yi. Cikin ranta take cewa "Come Sooraj! Come..! Ko ba komai zan ji ka a kusa da ni na wasu mintina duk da ma de nasan zuwan naka yana nufin FIGHT is on!" Table d'in gaban ta ya buga da hannun shi, hakan yasa ta yi firgigit ta mik'e tsaye, Matsowa yayi daf da ita yace "Ya dai y'ammata? Ya da kallo haka? Please take it easy kar idanuwan ki su fice daga socket nasu" Hannuwa Meenah ta sa ta sak'alo wuyan shi sannan ta ce "I'd be glad in idanuwa na zasu fice daga socket nasu dalilin kallon ka, you know Suraj....... Ban yi laifi ba ko kad'an don na kalle ka after all you are damn H...O.....TT..! NO! YOU ARE EVEN HOTTER....." Murmushi Suraj yayi shima ya rik'o kumkumin ta yace "Humph!.....nice try y'ammata! I know the fact that i am HOT! don haka ki gwada wani abun daban ba wannan ba, charms d'in ki ba zai yi aiki a kaina ba because i know i am already charming!". Yana kai nan ya fisge hannuwan ta daga wuyan shi amma Meenah sai tayi yunk'urin fad'uwa k'asa ganin haka yasa Suraj yayi saurin tarbo ta "Hmmmm.....Kulawa haka da yawa? Ashe de akwai soft spot a zuciyar ka". Meenah ta fad'a hannuwan ta rik'e da nashi ?" Sake ta yayi ya gyara rigar shi kafin yace "Baby... Do not be overwhelmed! Acting kawai nake yi, duba ki gani , look around you, these foolish people think we are in love so kawai kema ki cigaba da acting kar ki rayu cikin mafarkin ki na cewa Suraj Abdoul-Maleek ya damu da ke, in da a wani wajen na daban muke da na bari kin rantab'u da k'asa se kika yi sa'a muna cikin taro, kin san Hoooot guyss like myself bamu cika son rab'ar irin ku ba, dube ki fa Meenah...... Gaki gajera, look at the size of your boobs.... Well they are too tiny! Boobs like these basu burge ni ..... And your face! Too oily duba har kyalli take, i prefer sparkling eyes, oh and your lips.....Lab'b'an ki sorry to say there is nothing sexy about them! A wanne k'asar kika koyi make-up? " Suraj yana maganar ne a hankali with so much pleasure da murmushi d'auke a fuskar shi musamman ma da yaga idanuwan Meenah Sun ciko da hawaye duk da cewa ita ma bata daina murmushin ba saboda kar mutane su gane, "Ya isa haka Suraj! Enough! You have said enough please leave! Ka tafi ka bar nan!" Dariya ya sa sannan ya sunkuyo yayi mata kiss a kumatu sannan ya rad'a mata magana a kunne "don't cry baby, kin san ban son ganin mace tana kuka, hakan yana tab'a zuciya na soooosai..." Juya wa yayi ya kyale ta a wajen yayi tafiyar sa Habeeb ne ya dafa kafad'ar shi ya ja shi gefe sannan yace "What was that? I don't believe you Suraj! Zaka iya mayar da kowa mahaukaci a nan wajen amma banda ni, na sani cewa babu kalma guda d'aya mai dad'i da ka fad'a wa Meenah, na san bak'ak'en maganganun da ka b'oye a bayan murmushin nan, Suraj ka sassauta wa baiwar Allah ta samu sukuni please!... Wlhy kai mugu ne." Dariya Suraj ya bushe da kafin yace "Tunda de ba kai nayi wa muguntar ba ai tazo gidan sauk'i, ni bari ma kaga in fice in sha iska this party is quite boring" Habeeb de kawai kallon sa yake har ya fice daga hall d'in sannan ya maida duban shi ga Meenah dake k'ok'arin b'oye hawayen ta, ita ma mik'e wa tayi a fusace ta bar wajen. Tafiya take cikin dogon Hallway d'in se lokacin ta fashe da kuka ta sa gudu, band'aki ta shiga ta rufe k'ofar ta dafe Wash basin ta sunkuyar da kanta tana kuka, maganganun Suraj suna dawo mata d'aya bayan d'aya ta d'ago kai ta dubi madubi ta dad'e tana k'are wa kanta kallo se chanja pose take yi, Boobs d'in ta take kallo harda adjusting kafin ta wanke fuskar ta tace "Enough now Suraj! Ya ishe ni haka! Nayi Hak'uri na tsawon shekaru uku but now i am fed up, yau d'in nan,......a wannan daren you will be mine ko ka k'i ko ka so! Sedai daga baya duk abunda ya tafasa ya k'one.. " STORY CONTINUES BELOW Powder ta ciro daga purse nata ta gyara make-up d'in ta sannan ta fice daga toilet d'in ta koma hall d'in da ake party.... ***** ****** ****** Layla na fito wa ta nufi inda motar su take ajiye, bud'e wa tayi ta lek'a, amma bata ga kowa ba "Tasleem .... Tasleemm!!" Ta fito tana k'ira duk hankalin ta a tashe... Waya yake yana tafe se ji yayi kamar kuka, da sauri ya juya ya dubi inda take zaune ta had'e kai da gwiwa tana kuka. Katse wayar yayi at once ya k'arisa kan bench d'in da take zaune shima ya zauna a gefen ta "Hy!" ya furta fuskar shi d'auke da murmushi D'agowa tayi ta kalle shi baki a tab'e tace "H...ii". Da sauri Suraj ya ja da baya a firgice yace "LAYLAH!!".... Mik'e wa tayi ta matsa kusa da shi tace "Me yasa kake tsoro?" Kawar da kai yayi gefe kafin ya kalleta ya kwaikwayi muryar ta yace "Me yasa kike kuka?" Dariya tayi sannan ta zauna daf da shi tace "I am hungry and thirsty and sleepy! I can't sleep without my mommy". Fuskar tausayi Suraj yayi yace "awwwn.... How sweet! Ina mommy take? Suna party da Daddy, ni kuma ina jiran su a mota" Kallon agogon shi yayi yaga k'arfe goma da rabi na dare, cike da mamaki yace "Kamata yayi ace by now kin kwanta, dare yayi sosai. Come with me, zan samo miki abinci. Da murna ta mik'e hannun ta rik'e da nashi ya kai ta restaurant na cikin hotel d'in da suke, kujera ya ja mata ta zauna sannan ya tambaye ta me zata ci Kamar wanda aka mintsina ta ce "NOODLES!!..." Daga shi har waitress d'in saida suka yi dariya yace "One bowl of Noodles and two glasses of orange juice". Ita kuwa se murna take tana kad'a k'afafu. "Ban san me yasa ba amma ina ji tamkar ina da wata alak'a da ke, idanuwan ki tamkar na Layla, kamar photocopy d'in ta? Why did i feel restless all of a sudden?" A cikin zuciyar shi Suraj ke maganar yayinda ya k'ura wa yarinyar ido, yayi zurfi cikin tunanin shi hakan yasa bai ma san an kawo abincin ba, ita kam har ta fara aika wa ciki..... "Suraj!.....Su...." Habeeb ne ke kwalla masa k'ira kafin ya k'ariso inda yake zaune Dafa shi yayi yace "What on earth are you doing here? Babu inda ban duba ba, wace yarinya ce wannan a ina ka samo ta kuma?". Kafin Suraj yace komai yarinyar tace "TASLEEM....! Sunana Tasleem!" ta k'ura wa Habeeb ido "Inna lillahi wa inna ilaihir rajee'un!" Habeeb ya furta a zuciya ba tare da sanin maganar ta fito fili ba Yace "Allah mai halitta, in ba don wannan yarinya ce ba da se in ce Laylah ce". Ya fad'a a zuci kafin ya sakar mata murmushi ya dubi Suraj yace "Sufyan yana neman ka it's like magana ce a kan partnership, Suraj i don't trust them both saboda haka kaima ka kula, that Muhseen looks very cunning to me" Kai Suraj ya jinjina yace "Ina sane Habeeb, muje kawai kar ka damu nasan abunda zan yi". Juya wa yayi ya shafa fuskar Tasleem yace "ki cinye duk, it's all yours" Kai ta jinjina tayi murmushi Sannan ya dubi waitress d'in yace Ku bata duk abunda ta buk'ata, sannan ki kula da ita and send me the bill" "Yes sir!" Waitress ta amsa sannan Suraj ya juya yacigaba da tafiya. Tun k'arfin ta Tasleem ta rugo da gudu ta rungume Suraj tace "Thank you Daddy!!".. Chak Suraj ya tsaya, ji yayi kamar an watsa masa ruwan sanyi ya kalleta yace "DADDY??". Tasleem ta girgiza kai tace "Eh! Da ina kuka ka sa nayi shiru, kuma ka siya min abinci kayi ta min dariya, only a daddy can do that right? Toh kai ma daddy na ne". Kissing goshin ta yayi ya saki murmushi yace "je ki k'arasa cin abincin ki sannan in kin gama ki koma ki jira mom d'in ki, she might be worried in ta gane bakya cikin motar" Kai ta jinjina ta koma da gudu wajen cin abincin ta cigaba da ci....... "Ameer wollah wannan party sam babu dad'i it's soooo boring" Suraj ne ke magana idanuwan shi a cikin na Muhseen, shima Muhseen kallon Suraj d'in yake yi duk da cewa ba a kusa suke da juna ba amma duk sun fahimci cewa they do not quite like each other. Suraj yacigaba da kallon Muhseen har wani k'ank'antar da idanuwa yake yi kafin yace "Ka san miye? Habeeb infact i am starting to hate that Muhseen for no reason! Ji nake kamar akwai wani abu mallaki na da ya sace min, something very precious and important! Sannan bana son irin kallon da yake min i hate that ". Wata dariya Habeeb ya saki kafin ya tab'e baki ya dubi Suraj yace "Something important! Suraj kai yanzu akwai wani abu important da kake da shi wanda bamu sani ba? Menene wannan??" Kawar da kai Suraj yayi gefe sannan ya saki classy murmushi kafin ya ce a ransa "actually there is Something important in my life, zai yiwu ta manta da ni, zai yiwu ta cigaba da gudanar da rayuwar ta cikin jin dad'i, zai yiwu bana cikin duniyar ta amma gaskiya d'aya ce Layla har yanzu kece abu mafi muhimnaci a rayuwa na, i wish zan gan ki one last time, ina da tarin tambayoyi da nake son ki amsa min su, me yasa? Why did you leave me? Me ya baki kwarin gwiwar da kika samu shekaru bakwai da suka wuce? Me yasa kika yanke wannan hukuncin?" Habeeb ya zuba wa Suraj ido ganin ya fad'a cikin zurfin tunani. "Bro! Whats all this now? Sufyan yana son magana da kai muje mu same shi maganar tana da muhimmanci kamar yadda yace". Sake lume wa Suraj yayi cikin kujerar da yake kwance kafin yace "In yana da magana mai muhimmanci shi ya kamata ya zo ya same ni, ba ni zan je wajen sa ba, Habeeb the least you can do is to let me enjoy this party, ku je ku yi magana da shi in zaku iya amma ni kam ina nan!". Kai Ameer ya girgiza yana dariya kafin ya mik'e tsaye yace "Ni dai zan tafi wajen Mubeenah kun san nayi k'ok'ari, it's not easy to stay away from her for five good minutes, dan haka na tafi ku sai kuji da Sufyan". Nan take Habeeb ma ya mik'e yana gyara riga kafin yace "Aa...m kasan miye Ameer? I think you are right! Na san Khadija zata yi kewa na zuwa yanzu, jira ni mu tafi!". Dariya kawai Suraj yayi sannan ya gyara zaman shi yana dannan wayar sa, ji yayi kamar mutum a kan shi hakan yasa ya d'ago kai Sufyan da Muhseen ne tsaye ko wannen su da glass a hannu suna murmushi......

Post a Comment for "IN SO YAKI NE CHAPTER 2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...