IN SO YAKI NE CHAPTER 17 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

IN SO YAKI NE CHAPTER 17

IN SO YAKI NE CHAPTER 17

- - Post a Comment
IN SO YAKI NE CHAPTER 17


  Gaban wani tafkeken gida ya tsaya ba tare da b'ata lokaci ba ya zare seatbelt nashi ya fita, wasu lambobi ya danna daga gefen gate ɗin kamar kyafta ido gate ɗin ya buɗe, daga nan ya koma mota ya kutsa da motar zuwa cikin gidan. Laylah de kawai kallon sa take duk da cewa tana da tambaya taƙi furta wa saboda she's not in a state to even ask him where they are at the moment. Tsarin gidan tsari ne k'ayatacce na gaske, Mansion ne na gani na faɗa kuma ga dukkan alamu sabon gini ne, hasken wutar da ta baibaye harabar gidan da kuma yanayin maghrib da sassanyar iskar dake kad'awa yasa Laylah lumshe ido, a lokacin da ta fito daga motar bayan yayi parking ji tayi da ma wannan yanayin ya zauna a haka na tsawon lokaci. Tayi nisa a tunanin bata ma san Suraj na magana ba saida yayi snapping fingers d'in shi a fuskar ta hakan yasa ta buɗe ido a firgice, ganin shi ne a gabanta sai ta sauk'e nannauyan ajiyar zuci.+ "Zaki shigo ne ko kuma mu bar ki a nan?" Kai ta gyad'a masa sannan ta bi bayan shi suna shiga ya danna wani button k'ofar ta koma ta rufe, Nan take taji tamkar ba a Nigeria take ba tsabar kayatuwar wajen, gida ne wanda aka gina shi tamkar Mansions d'in da muka saba gani a Tv serials, luxury iya luxury, nan take ni'imar wajen yasa duk jikin ta ya mutu ta ji wani kasala, shi kanshi Suraj ji yayi ya gaji yana buƙatar hutu, amma yasan yaran nan da ita kanta Laylah suna buƙatar abinci, kuma dole ya fita koda nearby restaurant ne ya samo musu, don haka ya dubeta yace "Ki je upstairs akwai bedrooms koma wanne ku shiga, freshen up kafin nan zan je in dawo, ki kula da yaran ga dayan phone d'ina if you need anything just gimme a call". Ya gama maganar yana kissing Boboh, haka kawai taji tsoron ya fita ya barsu cikin makeken gidan da sauri ta bi bayan shi rungume da Iman kamar zata yi kuka, she really wanted to stop him but she couldn't. "Me ma zan ce?" Ta tambayi kanta duk da cewa bata bar bin shi ba haka ma yaran biyu (Boboh da Tasleem) Yana jin steps d'in ta sarai, karaf d'aya ya tsinci kanshi da sakar Murmushi kafin ya tsaya chak ya juyo yana kallon ta, turus tayi itama da sauri ta duk'ad da kai tana dunk'ule hannunta ɗaya jikin rigar Iman tamkar bazata yi magana se kuma ta buɗe baki in a mumbling tone tace "M...mme..yasa zaka fita? I'm scared idan kuma Sa'eed ya zo nan fa? Zamu bi ka mu tafi tare" Dariya yayi kafin yace "Sa'eed bai san nan gidan ba infact bazai iya zuwa nan ba saboda haka ki kwantar da hankalin ki ,take care of the kids yanzun nan zan dawo i will be back before you even realised i'm gone" A hankali ta gyad'a kai shi kuma ya saki murmushi ya juya ya fice, sauk'e numfashi tayi ta d'aga kai tana ƙare wa falon kallo, tsabar girman shi yasa aka kasa shi ɓangare huɗu banda dining section dake chan wata duniyar, bangaren da suke tsakiya ne yana ɗauke da fararen royal lounges masu adon ruwan gold, daga chan baya kuma ash wallpaper ne da tafkeken cuved Tv a manne inda aka zagaye shi da black leather cushions B'angaren da ya fi ɗaukar hankalin ta bangare ne da aka keb'e shi da glass duk da cewa babu girma sosai amma ya yi mugun k'ayatuwa, rufe yake da turquoise and white labule. Wajen ta nufa a nutse ra tura k'ofar glass d'in ta shiga, komai na ciki blue ne da fari. Ɓangare guda kuwa tafkeken glass ne da yayi displaying harabar gidan daga inda take tsaye tana iya kallon kyawawan fitilun da suka ɗauke mata hankali lokacin shigowar su gidan ga furanni masu ɗaukar hankali dake kad'a wa, kujerun ciki a tsakiya suke. Daga chan dungu kuma treadmill ne na motsa jiki da keke,. Iya kayatuwa wajen ya kayatu don ko gidan Muhseen iyakaci, kukan iman ne yasa ta fito da sauri, da alama yunwa take ji, haka ta dinga rarrashin ta da kyar tayi shiru sannan ta k'ira su zuwa upstairs inda tayi musu wanka gashi babu kayan sawa haka ta barsu da towel ita ma ta shiga bathroom don watsa ruwa. Fitarsa bai tsaya ko ina ba se wani nearest boutique dake kusa da unguwar, da alama sabon waje ne aka buɗe, ko da ya shiga ya ɗauki lokaci kafin ya fito wani ma'aikacin wurin yana biye dashi ɗauke da kaya nik'i-nik'i ya sa masa a mota, daga nan kuma ya ƙara gaba inda ya tsaya a wani restaurant ya sai musu abinci da drinks sannan ya kama hanyar gida. Ko da ya shigo abincin kawai ya ajiye downstairs kayan kuma ya haura sama da su, bai ma san d'akin da suke ba, har zai wuce ya ji hayaniyar su Boboh don haka ya tura k'ofar da sallamar sa ya shiga, suna ganin shi kuwa da murna suka yi hugging nashi. Da murmushi ya ja su zuwa gado inda Iman ke barci, ya jibge kayan dake hannun sa yana stretching hannuwan shi a kasalance kafin ya dubi yaran yace "Where's your Super-mommy?" Dariya suka fara jin kalmar Super-mommy da ya ce, Tasleem ta ce "momma tana wanka". Kai ya gyad'a ya janyo ɗaya daga cikin shopping bags d'in ya ciro kaya ya mik'a wa Tasleem, riga ne pink tee da jeans da tsalle ta karb'a tana maimaita "thank you Daddy i love you" kumatun ta ya sumbata yana murmushi sannan yace "and Daddy loves you more princess". Had'e rai Boboh yayi yace "Ni ina nawa?. "Ohhh........ Babban mutum bana son rigima I'm not even done... Ga naka nan zo in shirya ka." Da sauri ya matso yana washe baki Suraj ya zare towel d'in ya saka masa wandon da rigar, sai ya kalli Iman dake barci shi kanshi ya tabbata barcin wahala ne, like a pro ya sa mata diaper sannan ya saka mata y'ar rigar da ya siyo though ta so tayi kaɗan ma de amma ya fi babu. Shiru ya ɗan yi yana sauraraon ƙaran zuban ruwa daga bathroom na ɗan wani lokaci idanuwan shi a lumshe yana jin yanda jikin shi ke masa ciwo shi kanshi ya san wankan ne kaɗai zai magance masa uban gajiyan nan da kasala, don tun wayewar gari jiya rabonsa da barci..... STORY CONTINUES BELOW Tun lokacin da ya shigo ta jiyo Muryar shi tare da yaran, duk da cewa ta gama wankan haka ta kunna ruwa a kanta tana tsaye tana tana jira taji fitar sa, saboda babu wani mayafi ko hijabi tattare da ita bata son ya ganta da wannan ɗan figigin towel d'in. Jin yayi shiru tayi tunanin ya fita don haka ta kashe ruwan ta gyara towel d'in wanda da kaɗan ya wuce cinyoyin ta. Daidai lokacin da ta sa k'afa lokacin yayi daidai da dagowar Suraj, tun daga kyawawan ƙafafun ta har zuwa fuskar ta dake d'igan ruwa haka ya bita da kallo bai san lokacin da ya haɗiye miyau ba yaji jikin sa yayi la'asar. A lokacin da ta tabbatar cewa shi ɗin ne zaune ba gizo yake mata ba, babu shiri ta juya da gudu ta koma bathroom tana dafe goshi cike da kunya shikam k'ofar ya bi da kallo baki a hangame. Saida Tasleem ta saki ƙara saboda zafin da hannun ta yayi tana ƙoƙarin saka rigar, da sauri ya maida hankalin sa gareta ya taimaka mata ta saka rigar yana rarrashin ta. "Who wants some french fries! And yoghurt???!" "Me! Me! Daddy i want some! French fries are my favorite!!". Cewar Boboh. Ɗaukan shi yayi sannan ya kama hannun Tasleem suka fita, a dining ya bar su sannan ya koma d'akin inda ya bar wayar shi, yana buɗe k'ofa ita kuma ta lek'o, karaf suka haɗa ido da sauri ta mayar da kanta tana dariya, shima dariyar yake yi daga bisani ya ɗauki kayan da ya siyo mata ya miƙa mata, da sauri ta sa hannu ta amshe sannan ta rufe k'ofar. "Idan kin gama ki sauko ki ci abinci" Shirun ta ma amsa ce a gareshi tunda ya san taji me yace sarai don haka ya juya ya fice, saida ta shirya tsaf ta d'aura alwala, abaya ce fara plain rufaffiya me kyau da mayafin ta, rigar ta so tayi mata tsayi sai tattare wa take, mayafin ta rufa ta gabatar da sallolin ta na maghrib da isha'i sannan ta fita........... 1 ____________ Hankali kwance yake zaune ya rufe idanu yana wasa da ƙaramar pistol dake hannun shi, duk wani motsin su yana ji, a tunanin shi yaran sa ne suka dawo tare da su Laylah bai san cewa zagaye yake da Armed forces ba, ba tare da ya d'ago ba ko buɗe idanuwan shi ya saki murmushi yace "Weldone boys!......... Take them back inside i will deal with them later". Ji yayi ba wanda ya motsa kafin wata murya da bai taɓa ji ba ta doki kunnuwan shi "Kafin nan we will have to deal with you first Sa'eed!!" Firgigit Sa'eed yayi ya mik'e idanuwan sa suka fara sauk'a kan yaran nasa dake gurfane a ƙasa sannan ya maida duban sa ga Captain Rasheed da inspector Victor dake tsaye daga gefe Habeeb ya nade hannuwan shi a kirji, a lokacin ne ya lura cewa zagaye yake babu hanyar fita, nan take ya tabbatar da cewa his shit don dry 😂 Wani narkakken gumi ne ya karyo masa lokaci guda yaga komai ya koma masa duhu. Ya fara tuna irin months ɗin da ya shafe yana shiri ace dare ɗaya komai ya rushe... All his plans were chopped off. Juyo wa yayi idanuwan sa cikin na Habeeb yayi imani cewa tausayin sa ƙarara ya bayyana a fuskar Habeeb ɗin, shi kanshi ya san ta ƙare mishi bashi da dabara, wannan shi ake cewa _99 days for the thief one day for the owner_ Daf da Sa'eed Habeeb ya k'arasa babu fargaba a tattare da shi yace1 "Sa'eed listen..... it's over now, come out of your illusions and face the reality.... This is life nothing in life goes the way we want it! The path you took is a part of self destruction and nothing else. Surrender yourself! It's not too late to repent and seek forgiveness from the Almighty for he is Al-Gafoor kuma shi mai Rahama ne (S.W.T)." Wani irin kad'awa idanuwan shi suka yi ya girgiza kai hannun shi ɗaya bisa kafad'ar Habeeb yace "I know it's over now, i know I've lost this battle tunda Laylah tayi outsmarting d'ina, not only did she escape but also she sent you here in full force, i have hurt so many people for her, i have killed for her! And i will do so even today if i get the opportunity.... Because my love for her is real and true, i have already reached the point of no return a soyayyar Laylah. One truth is that i can never live without her! Da in rasa Laylah na gwammace in rasa raina, go tell her this Habeeb! Today i have failed! But mace irin Laylah thousands of men like me will be after her because she is one of a kind ka faɗa ma Suraj ya killace ta in ba haka ba akwai waɗanda suka zarce Sa'eed Ahmad hauka a soyayya".... Yana rufe baki ya hankad'a Habeeb baya ya daga pistol d'in hannun shi ya dasa a kanshi, without a second taught ya harbe kanshi cikin abunda bai fi dak'ik'a ko seconds biyu ba ya aikata hakan basu ankara ba sai ganin mutum suka yi a ƙasa warwas. Idan da za'a tsaga jikin Habeeb babu digon jini dake gudana a jikin shi, ji yayi yawun bakin shi ya kafe ya nemi na had'iya ma ya rasa, kanshi yayi nauyi k'afafun sa suka kasa supporting jikin shi ya zuba gwiwa a ƙasa yana hawaye, wannan shine karo na farko da ya taɓa ganin suicide ido da ido, he was shocked and scared yanda Sa'eed ya harbe kansa da hannun sa ba tare da tunanin me zai tarar ba a chan...... Kafad'ar shi Captain Rasheed ya dafa yace "pull yourself together Habeeb.... I think we have to inform Suraj abunda ake ciki. Da sauri Habeeb ya d'ago ya girgiza kai yace "No..... Not now! No body should know this, for now, they have gone through alot already, and Suraj is not in good health, Sa'eed might be a bad person but for both of us he is still our brother.... They will be shocked ba shi ɗin ne Bama so ba halinsa ne bama so." Kai Captain ya jinjina kawai bai yi magana ba, inspector Victor yayi waya cikin kankanin lokaci aka kawo Ambulance wanda a ciki ne aka tafi da gawar Sa'eed, dole duk da sun yi witnessing lamarin sai an samu documentation ko written report akan mutuwar sa. Jiki babu kwari Habeeb ya shiga motar, saida suka sauk'e shi a gida sannan suka tafi........... 1 _________ Ƙarshen alewa ƙasa..... We have seen the dramatic end of Sa'eed! He chose the path of destruction and look where it brings him! Allah yasa mu dace, ya raba mu da son zuciya. Ameen.. Tun daga k'ofa yake hango Ameer tsaye daga ganin shi hankalinsa baya jikinsa, yana hango Habeeb ya nufo shi da sauri har muryar sa na rawa yace "Habeeb......me ake ciki? Ina su Tasleem ina Laylah? And Suraj........ Why is he not here?. Wani irin yanayi Habeeb ya tsinci kansa mara misaltuwa da kyar ya iya furta maganar da ya faɗa "They are safe, dare yayi ne suna tare da Suraj, Sa'eed has been captured". Yana kai nan ya wuce ciki ya bar Ameer tsaye. Tun daga yanayin muryar sa Ameer yayi imani akwai abunda ke faruwa,ya fahimci Habeeb is trying his best to conceal something from him, amma shi labarin yayi masa daɗi tunda yaji Suraj, Laylah da yaran suna lafiya, jan numfashi yayi yana k'are ma taurarin dake sararin samaniya kallo, Allah kaɗai yasan dalilin restlessness d'in shi, ya dauki lokaci a haka kafin ya koma cikin gida. Lokacin ƙarfe tara ma ya wuce dama chan da kyar ya samu ya lallab'a Mubeenah ta samu barci, ya tsaya kanta yana kallon yanda take barcin a galabaice , zama yayi gefen ta ya sa hannu yana shafa fuskar ta "it's over now........komai ya wuce insha Allah, our baby is safe and in good hands" kamar tana jin shi ta gyara kwanciyar ta tana rungume hannun nashi tamkar wani teddy haka kawai ya tsinci kanshi da sakar murmushi ya miƙa hannu ya kashe wutar d'akin amma ya kasa barci da ya kwanta sai juyi yake yi......+ Yana buɗe k'ofar ta d'ago kai tana kallon shi bata jira ya ƙaraso ba ta nufo shi da sauri ta rungume, shi kanshi Habeeb saida ya samu natsuwa kafin ya sake ta don gaba-daya jikinsa a sanyaye yake idanuwan sa yana taro mishi yanda Sa'eed ya harbe kanshi ya kuma tuna kalaman sa na ƙarshe. "How can someone take his own life just like that? What kind of a woman is Laylah da har dalilin ta wani zai iya rasa ransa?what kind of love is this?" Da sauri ya kawar da tunanin da yake yi domin ya san bashi da amsoshin tambayoyin nasa. Ya kama hannun Khadijah zuwa gado ya zaunar da ita shima ya zauna ya fuskance ta "It's over Habibty...... Our children are safe and sound, suna tare da Suraj, in ba don Laylah ba da ban san irin abunda Sa'eed zai aikata ba, she risked her life to protect them, mu gode ma Allah domin babu wanda yaji rauni, dare yayi kuma duk a gajiye suke, they will be back home tomorrow morning insha Allah, so relax and have a good night sleep" Nan take ta nemi kukan ta rasa cike da murna tace "zan iya magana da su? Please Abban Suraj lemme talk to my son only then i will have a peace of mind" Waya Habeeb ya ciro yayi dialing numbar Suraj, ya d'auki lokaci kafin ya amsa. Kasancewar video call yayi yasa Suraj ya mik'e zaune daga kwanciyar da yake "Suraj , Khadija ta damu sosai, she wants to speak with Boboh" Murmushi Suraj yayi ya miƙa wa Boboh wayar. Da sauri ya ajiye yoghurt d'in da yake sha ya amshi wayar "MOMMY!!" Ya k'ira ta gana washe baki, nan ya shiga zarar zance yana bata labarin bravery d'in Super-mommy yayinda tayi shiru cike da emotions tana jin sa , ji take kamar su kwana a haka yana bata labarin, share hawayen ta tayi tace "Give the phone to your Super-mommy" Shiru yayi yana juye juye kafin yace "Super-mommy is upstairs" kai ta jinjina tace "ok what of Tasleem?" Kamar jira take da sauri ta matso tana dariya ta amshi wayar, sun jima suna magana kafin suka maida wayar wajen Suraj suka koma cin abincin su, shima Habeeb ya sanar da shi yanda ya faɗa wa Ameer bai fad'i komai game da mutuwar Sa'eed ba,duk da haka Suraj yaji a jikin shi cewa akwai abunda Habeeb ke b'oye wa, sallama sukayi ya kashe wayar sannan ya maida hankalin shi kan yaran yana kallon su suna cin abinci. Ta gefen idon sa ya hango giftawar ta, da sauri ya dago yana kallon ta, tuni yaji shi a wata duniyar ta daban. Bai san dalili ba but kowacce rana soyayyar ta ƙara ratsa zuciyarsa take yi, salon ta,her innocent face, her smile, infact everything about her is special, wani murmushi ya sub'uce masa da sauri ya duk'ad da kansa ya miƙa hannu ya ɗauki glass na ruwa ya kurb'a. Daga chan gefe ta nemi waje ta zauna tana wasa da yatsun ta, kanta a ƙasa yake amma tana ji a jikin ta kallon ta yake. A hankali ta d'ago kai idanuwan su suka haɗu ga mamakin ta sai taga bai ɗauke ido ba hakan yasa ta rasa sukuni domin kallon shi kallo ne mai ratsa jiki, shock d'in da taji a lokacin yasa tayi saurin kawar da nata idon haɗe da gyaran murya kafin ta mik'e ta dawo inda yaran suke a ƙasa ta zauna. Ruwan da ya ajiye ta ɗauka, bata ma san shi ya sha ba ita de taji wuyanta ya bushe tana buƙatar ruwa don haka ta kai baki ta kurb'a. Take away Tasleem ta Mik'a mata dama chan yunwa take ji sai ma da ta buɗe abincin taji cikin ta ya ɗauki ruri kamar wanda tayi sati bata ci komai ba, pasta noodles ne ya sha veggies duk da ba cimar ta bane don in haka kawai za'a bata bazata kalle shi bama se gashi kuma ko kula fork bata yi ba ta sa hannu tana ci, dariya ta so ta bashi don kar ya kufce masa ya gyara murya ya ɗauki glass ya zuba juice ya mik'a mata, saida ta ɗan jinkirta tana kallon sa, murmushin fuskar sa bata gama b'ace wa ba. Karb'a tayi ta kurb'a ta ajiye sannan tacigaba da cin abincin a hankali. Bayan ta kallama ya taya ta suka kwashe wajen da duk jagwalgwalen yaran tsaf ta zubar da na zubar wa ta ajiye na ajiye wa a kitchen ta wanke hannun ta sannan ta dawo. "Mommy barci nake ji" Tasleem tayi maganar a gigin barci daman Boboh kam ya yi barci don haka ta mik'e ta ɗauki Boboh ta d'aura a kafad'ar ta, da sauri Suraj ya sa hannu ya amshe shi yace "don't worry zan kai shi d'akin ke ki ɗauko wancan ledan, madaran Iman ne I'm sure bazata iya barci on empty stomach ba in case ko zata tashi.... Ba musu ta ɗauki ledan ta bi bayan shi Tasleem kam har ta isa dakin ma shima da ya shigo kawai kwanciyar su ya gyara musu ya fita a lokacin Iman ta farka da kukan ta, bai jima ba ya dawo ɗauke da water bottles guda biyu ya dire su kan bedside drawer. A gigice Laylah take shaking madaran shi kuma sai jijjiga Iman yake amma idonta ya rufe, da sauri ta amshe ta ta kafa mata glass ɗin a baki tsit kake ji kamar ba itace ke kukan ba se shan madaran take, bayan ta sha ne ta shiga bathroom ta wanke mata jiki ta goya ta, saida tayi barci sannan ta kwantar da ita, shide Suraj kallonta kawai yake tana activities d'in ta. Daga bisani yayi sallam da ita ya fita ita ma ta kashe wuta tayi addu'a ta kwanta.... STORY CONTINUES BELOW Yana fita ya ɗauki watar sa kira numbar Meenah, kamar jira take ringing d'aya ta d'aga bata ko bashi damar magana ba ta dinga surutai shidai qala bai ce mata ba don bai son tashin hankali ballantana ma yasan she has every right to be mad at him, he wasn't by her side at her happy moment duka da shima ba hakan ya so ba, but ko da ace yayi mata bayani ba ɗauka zata yi ba, kuma yanzu ma surutan da take yi zai iya cutar da ita domin jiya aka yi mata aiki. don haka ya kashe wayar with a simple reply "I'm sorry" Tun daga nan ma ya kasa barci yanda yaga rana haka yaga dare sai bayan ya gabatar da sallar asuba ne wani mahaukacin barci yayi awon gaba da shi, haka Laylah daga ita har yaran barci suke basu tashi farkawa ba sai past nine. Har tayi musu wanka suka fito basu ga alamar Suraj ba, waje ta lek'o taga motar shi ajiye yanda ya barta jiya, wanib sigh of relief ta sauk'e sannan ta koma upstairs don ta duba shi, yawanci flats d'in a rufe suke sai guda ɗaya, a hankali ta tura k'ofar wanda ya sada ta da wani k'ayataccen living room wanda ya kasance komai na ciki traditional Arabian ne kama daga decor har furnitures wata k'ofa ta hango half opened without a second taught ta nufi kofar ta tura a hankali ta kutsa kai ciki, kamar an mintsile shi ya buɗe ido,karaf suka haɗa ido ta dubeshi daga sama har ƙasa nan take taji tamkar ta nutse don kunya, da gudu ta fita daga d'akin. Babu riga a jikin shi sai shorts kadai wanda suka dasa aya a cinya, dariya yayi ya mike da sauri yana miƙa.... Saida yayi wanka ya shirya tsaf sannan ya fito, lokacin ita ta koma wajen yaran. Daga nan ya ɗebe su suka koma gida....... _________ Sosai Mutuwar Sa'eed ta taɓa su musamman Ameer, duk da cewa abunda Sa'eed ya aikata mai muni ne but that bond between them lokacin suna yara keeps haunting him, he can't believe how his brother turn into a cruel human being ya san dama chan mahaifiyar su ta sangartar da shi kuma har shi kanshi Ameer ma ya so ya yi falling victim amma ya gyara halayen she, he realized so soon that he was on the wrong! Why did Sa'eed failed to do the same? Bayan alhakin mutane da ya kwasa ga zunubin kisan kanshi da kanshi?" Mai martaba kuwa ba don an saka baki ba cewa yayi ko da a k'ofar sa ake jana'izar Sa'eed bazashi ba da kyar aka rok'e shi yayi controlling anger d'in shi ya taho Abuja, ranshi a b'ace yana takaicin yanda karshen ɗan nasa ya kasance, sannan yana masa addu'a Allah ya masa gafara. Dad ma da yake Cairo yau ya iso don dama tun ranar da Suraj ya k'ira shi yake son zuwa yagan shi. Duk da b'acin ran mai martaba yasan cewa naka_naka ne duk rintsi kuma komai lalacewar sa. Don haka ya yafe ma Sa'eed. Ɓangaren Meenah kuwa satin ta guda a asibitin, saboda yanayin gidan kowa is not in a good state of mind babu wani shagali da aka yi, Suraj ya maida wa baby sunan Mom RAZIA Y'ar kwarya_kwaryar walima de suka yi inda Suraj ya gayyaci close friends da ma'aikatan sa na Company don taya shi murna hakan ma saida Ameer ya matsa masa domin kar ya zamana Meenah taji haushi afterall this is her first baby. Ita ma Meenah bata nuna damuwa ba, kamar de Suraj close friends and families kawai ta gayyato domin taya ta murna. Mai martaba a ranar ma ya koma Dad ya raka shi airport tare da Habeeb saida jirgin su ya tashi sannan suka komo gida........ _________ Tun safe ta tashi ta yi wanka sannan ta gyara d'akin ta fito ko akwai wani aikin da zata yi, a falo ta iske su suna ta hira gaba-daya harda su Dad. Gaida su tayi suka amsa da fara'a, Dad ya kasa d'aga idonsa daga kanta yana tuna abubuwan da suka faru a baya, ita de kanta a ƙasa ta nemi waje chan gefe ta zauna. Ummin Habeeb ta dubeta tace "Laylah Please kije d'akin Meenah ki taho da babyn za'a mata wanka, ta haɗa miki da kit nata."daɗin hakan taji, da sauri ta mik'e domin ta rasa abun da zata yi a falon duk sun fahimci hakan. Da sauri ta juya ta nufi d'akin Meenah duk da cewa ta san me zata riska amma ta yaƙi zuciyar ta tayi na maza ta shiga da sallamar ta, Meenah da kawarta Sadiyah suna zaune, Sadiyah ce ta amsa sallamar, Meenah kam wani mahaukacin kallo ta watsa mata wanda yasa taji duk jikin ta yayi sanyi. "Me ya kawo ki daki na??" Ta tambaya a gadarance . "Ummi tace ki bani Baby za'a mata wanka " Kamar wanda aka zungura Meenah ta mik'e ta fisgi hannun Laylah ja jata suka fita daga d'akin har downstairs, duk k'ok'arin Laylah na kwacewa ta kasa saboda bata son ta sa ƙarfi Meenah taji ciwo "Meenah miye haka kike yi?ki kyale ni!......... What's wrong with you? Me nayi miki? Leave me alone ki sakar min hannu na don Allah". Muryar Laylah ce tasa kowa ya maida Hankalin sa zuwa ga stairs, nan take duk suka mik'e da mamakin abunda Meenah ke aikatawa. Da wani force ta hankad'a Laylah ta yanda ba don sapna ta riƙe ta ba da tuni ta fad'i ƙasa. "MEENAH!!!!" Suraj ya daka mata tsawa har jikin sa na rawa, ita ma a fusace ta juyo idanuwan sa cikin nashi tace "What? Kaji haushin actions d'ina ne? Idan bakwa son haka ya dinga kasancewa just kindly tell her to stay away from me and my baby! Ku kaɗai ma kun isa ba sai wata outsider ta shigo cikin lamura na ba. I hate and despise the fact that i am living under the same roof with this cunning woman! What good did she bring to us tunda ta shigo rayuwar mu? Nothing but pain and suffering! Na rayu da Suraj duk da babu soyayya ta a zuciyar shi but we led a peaceful life amma tunda ta zo daga wannan se wancan it's either Muhseen or Sa'eed! Ban damu ba idan zata dawwama a gidan nan but she should stay away from my baby and I." Gaba ɗaya jikin su yayi sanyi musamman Suraj da ya rasa kalmar da zata fito daga bakin shi, ya rasa fitting answer da zai bayar wa Meenah ya samu gamsuwa , haka Meenah ta juya ta koma ciki.. duk abunda Meenah tayi Sadiya tana kallon ta domin itama tayi k'ok'arin hana ta amma ta ture ta gefe ta fisgi Laylah............. Ta dad'e bata yi experiencing disappointment ba kamar na yau, kukan ma bata san lokacin da ta fara shi ba, ji tayi tamkar an kwarara mata ƙanƙara, tamkar babu jini dake gudana a jikin ta , kasa tsaya wa tayi a wajen ta ruga da gudu zuwa d'aki, duk jefa k'afar ta da tayi ji take kamar tana aza su bisa shimfidar garwashi .... Su Kahdijah suka bi bayan ta da sauri dimin pacifying d'in ta. Tana shiga d'akin bata tsaya wata wata ba ta buɗe wardrobe, wani luggage ta ɗauka karami ta buɗe shi bisa gado sannan ta fara ciro kaya daga hanger tana watsa su ciki, kwata kwata kayan basu fi kala biyar ba se inner wears. Lokacin da take ƙoƙarin rufe luggage d'in taji an rik'e hannun ta. "What are you doing??" Mubeenah ta tambaya damuwa ƙarara a fuskar ta. "ina kuma zaki je? Ya naga kina packing? Please sit! Let's sort this out". Kai Laylah ta girgiza tace "No Mubeenah.........ina ganin abunda yafi shine in kawo ƙarshen matsalar Meenah da kaina!, Besides duk abunda ta faɗa gaskiya ne it's about time i go away from here. I don't want to make Meenahs life miserable. Daman nazo nan ne a matsayin mara lafiya,kuma Alhamdulillah na warke, idan na cigaba da zama a nan i will only bring difficulties to both Suraj and Meenah bana son auren su ya samu matsala saboda ni"+ Khadijah ta dafa Laylah sannan tace "idan kin tafi what about Suraj? Kin yi tunanin halin da zai shiga? He still loves you!! Laylah he wants only you! Meenah bata sani bane cewa Suraj is only doing her a favor..... Idan har kika tafi Suraj zai koma gidan jiya ne. I have seen him Fall and rise i have seen him cry and smile but babu abunda ya sauya na daga kaunar da yake miki Laylah he needs you fiye da yanda kike tsammani, just think about halin da zai shiga idan kika tafi. Think about the future of our kids Tasleem in particular!" Duk maganganun babu wanda ƙwaƙwalwar Laylah zata iya ɗauka a lokacin don ta tabbata idan ta zauna itace zata wahala don haka ta gyara mayafin ta sannan ta k'arasa rufe luggage d'in ta ja zuwa hanyar fita. "Laylah why can't you listen! This is not the solution to this problem! You can't just leave.......ki tsaya! Laylah Please listen!!!". Da sauri ya d'aga kai ya kalli inda maganganun su Khadijah ke fitowa bai san lokacin da ya mik'e tsaye ba. Ba don hayaniyar maganganun su Mubeenah ba, yayi imani sai duk sun ji ƙarar bugun zuciyarsa, nan take numfashin sa ya fara ɗauke wa. Turus tayi ta tsaya ba shiri saboda yanda ya tare ta sannan ya kafeta da idanuwan shi masu ɗauke da alamar tambaya. Kawar da jajayen idanuwan ta tayi daga kansa tana ƙoƙarin shanye hawayen hawayen da ke neman zubowa. "Miye ma'anar hakan da kike shirin yi?" Ya tambaya da sassanyar murya "Tafiya zan yi". Ta bashi amsa a tak'aice. "Idan kin tafi ina zaki? This is your only home!". Runtse idanuwan ta tayi wannan karon hawayen da tayi k'ok'arin riƙe wa suka zubo kafin tace "Duniyar nan tana da fad'i Suraj....i......i will manage" Wani dariyan takaici ne ya kufce masa ya matsa daf da ita yace "Let me ask you this Laylah!.....why is it that i am the only one who suffers? Why??? Seven years ago you turned your back on me! You left me shattered and broken! I managed to pull myself together when i finally met you again......and now? You are making the same sin! The same mistake! What have i done to deserve this? Kin sani cewa i love you more than my own life! Nayi zaton komai ya wuce we will begin a new life together as a family. And now...... Here you are trying to give up on me just like that. Just because of a trivial mattee!" Rik'e kafad'un ta yayi yana jijjiga ta "For once Laylah......for once be selfish and live for yourself not for others"3 Zame jikinta tayi daga hannun shi ta ja luggage d'in zata fita. Cikin fushi da b'acin rai Suraj ya fisgi luggage d'in yayi wurgi da shi. Hakan ba ƙaramin tsoro ya bata ba saida numfashin ta ya tsaya na wasu dak'ik'u. STORY CONTINUES BELOW "Kin san me!? I refuse to let you go!! Idan kin ga dama ki mutu....illa iyaka nima na rasa raina amma idan kinga na barki kin tafi toh Lallai bana numfashi" Dakewa tayi tace f "Suraj why are you doing this?" Da yatsa ya nuna ta yace "I should be the one asking you this!! I refuse to suffer the way i did seven years ago." Bai jira me zata ce ba ya fisgo hannun ta ya fara janta zuwa upstairs, tun k'arfin ta take kwacewa amma abun yaci tura "Suraj please let me go...... please Suraj ka shika min hannu!!" Bai saurari kukan ta ba kuma bai damu ba. Koma me zai faru, hankad'a ta yayi cikin d'akin shi ya ja k'ofar ya rufe ta a ciki "Stay here until you come back to your senses" ya juya ya bar wajen yana sa key ɗin cikin aljihun shi, yana ji tana bubbuga k'ofar amma ya basar. Kukan ta kuwa har ranshi yake ji amma ba zai bari taurin kanta yayi winning ba. Falon ya koma inda ya iske su kowa yayi jugum jugum ya dubi Sapna yace "Take the luggage back to Laylah's room" Yana kai nan ya fice ma gaba ɗaya daga gidan......... __________ Duk abunda ya faru kawar Meenah Sadiya tayi witnessing sosai ranta ya ɓaci da abunda Meenah ta aikata, haka kawai taji ya kamata tayi wa Meenah magana inda ta iske ta a bakin gado tayi tagumi ita kanta alamun ta san ta aikata ba daidai ba. "You disappointed me today Meenah! Ji nayi tamkar ba Meenah da na sani bace since childhood! Ban tab'a sanin baki da wayo ba se yau cikin ɗan kankanin lokaci kin ruguza image d'in ki a gaban familyn ki, kin ruguza darajar da kike da shi a idon Suraj!... What were you thinking Meenah? Why did you failed to see the favours she has done you? Kina tunanin ke kaɗai kika iya soyayya ne? Kin san amount of pain da ta shanye? Ko kin manta kafin ki mallaki Suraj ita ce matar sa? Matar da ya kasa daina kaunar ta tsawon shekaru bakwai what makes you think he will stop loving her da wannan attitude d'in naki? I know exactly how you feel I Know it hurts deep down. But kin yi tunanin yanda ita take ji duk lokacin da ta ganku tare da Suraj knowing that few years back he used to be all her's? If she can swallow her pain why can't you? She always has a smile on because of that you failed to see how she is suffering because you are too cruel and selfish. Ke ma fa mace ce....... Miye duniyar ma? Daga ita har ke babu mai tabbacin nan gaba waye life zai yi favoring. Think about what i just told you Meenah..... soyayyar da baki samu ba tsawon shekaru uku zaki same ta ne kawai ta dalilin Laylah, she was your only ticket to gain Suraj's love unfortunately you have lost it because of your actions! And lemme ask you? A tunanin ki wanne cutarwa kike tsammanin zata yi wa baby Razia? In case kin manta barin tuna miki kafin ki zama uwa.... Da shekaru bakwai Laylah was already a mother! It will be best if you go and apologize to both Suraj and Laylah domin da ita wata ce da tuni ta fisge ki daga matsayin ki ta koma gurbin ta amma se gashi bata aikata hakan ba. You know why? Because she respects you Meenah!" Sadiya tana k'arashe maganar ta fita ta bar Meenah a wajen tana kuka babu kalma ɗaya da Sadiya ta faɗa akan Laylah da ya kasance k'arya, nan take haushin kanta ya kamata......... __________ Tun tana kukan da sauti har ta daina ta jingina bayan ta da k'ofa a nan barci ya kamata, yanda take a takure haka ta sulale ta kwanta a ƙasa. Suraj kuwa da fitar sa office ya wuce ya ɗan yi wasu ayyukan sannan ya fito kasancewar weekend ne babu kowa a wajen se masu gadi don ya rasa sukuni sam. Ko da ya dawo gida ba wanda ya masa magana don suna san a cike yake. Ya jima a k'ofa yana tsaye yana tariyo abunda ya faru d'azu, daga bisani ya sa key ya buɗe kofar ba don ya riƙe k'ofar ba da yayi tuntube da ita sosai ya tausaya mata yayi regretting yanda ya rufe ta, ya kuma san ko breakfast bata yi ba gashi har lokacin lunch ya gabato, durkusa wa yayi a hankali ya ɗauke ta daga ƙasa ya shimfida ta bisa gado sannan yaja blanket zai rufa mata. Tamkar wanda aka watsa mata ruwa haka tayi firgigit ta buɗe ido suna haɗa ido ta fad'a jikin shi, yanayin rungumar da tayi masa ji yayi tamkar wani na neman kwace ta ne don tun k'arfinta ta riƙe shi, ta kifa fuskar ta cikin K'irjin shi, it was sudden and unexpected, suraj ya kasa controlling yanayin da ya shiga, he just couldnt stop himself! Bai san lokacin da yayi wrapping dinta da hannuwan shi ba yana sauraron rapid heartbeat d'in ta. A hakan da dashashshiyar murya tace "Suraj I'm sorry! I love you Suraj i didn't know what i was thinking please don't be angry with me i wasn't thinking straight". Bai san lokacin da wani murmushi ya kubuce masa ba ya runtse idanun sa yana sauraron ta a hankali cikin ransa kuwa yace "So this is it??? All i need to make you mine is a little anger?? Had i known i would have done that tun kafin yau" Ya ɗan haɗe rai ya janye jikin sa daga nata yace "Shush....... it's okay stop crying. I'm sorry for what i did earlier. You have to promise me this! Daga rana irin ta yau, ba Meenah ba koma waye yai miki laifi bazaki sake yunk'urin bari na ba, Laylah! I need you badly..... I really do!! I can't afford to lose you again Babe!" Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi tana dariyar kalmar "Babe" A tsare ya kalleta yace "what? Aren't you my Babe?" Murmushi tayi tace1 "You know Suraj My life has been a mystery since i was born, i was abandoned alone far away from my mother, then Baba took me in, he nutured, and treated me like his own daughter, a wancan lokacin everything seems perfect my life was moving on a smooth path! Then suddenly you came into my life Suraj i was happy.......no! It felt like i was the happiest woman on Earth. It was love at first sight it was unexpected, then you proposed despite knowing the consequences. You know Suraj that your Dad is against you mingling with even the middle class people while i came from a lower class family, i know nothing apart from rearing from dusk till dawn yet you still wanted only me! We have to lie to your father and conceal my identity, in doing so we faced uncountable obstacles from Dad to Ameer _ Ameer to Sa'eed! In the end Mai martaba made his decision he gave us new hope, i still remember how injured you were when you left belel, i was scared I'd loose you but then mai martaba again did the magic! I was brought to Abuja we spent quite memorable moments together we were so happy and in love, i still remember the laughter, the kisses and thousands of hugs we share, i still remember the joy on your face when you find out about my pregnancy, i was naive and stubborn sometimes you find it hard to pacify me, and i love the way i troubled you back then.... Little that we know danger is lurking around us from every corner! SA'EED......... He came back into our lives with his own style, we both were shocked. When he left we both taught it's over! We never knew that "when a lion takes a step back.. it's not because he is afraid rather he is adjusting to find a clear target"............ Laylah tayi shiru tana kallon sa idanuwan su cikin na juna......... Suraj ya runtse ido na ɗan wasu seconds yace "And then i recieved the news that shook me to the core!...... Mai martaba.... My only backbone! The only man who understands and love me dearly! He passed away........... It was the beginning of the end to our marriage! Belel! We went to Belel for his funeral not knowing it was also a funeral to our marriage. Baba was killed, we both are shocked I couldn't control you, you were under the impression that my brother Ameer was behind the murder little we all know that Rasuwar Baba will cost us a lot! It cost us Seven years..... SEVEN YEARS! In those seven years your absence turned me savage, i lost control of my self, my emotions it was the hardest times of my life, i die every single day because of your absence, i suffered a lot, i also hurt my brothers in the process but despite all that they choose to stay by my side to support me! Three years ago i lost Mom! My life turned upside down it felt like i have no purpose in life, I felt miserable that i wanted to die then one day you appeared......like a rainbow i taught it was a dream! Only for me to find out that you are married! Not only that.....i had a lovely cute daughter! Daga wannan ranar na ji a jiki na cewa you are back to me! And then Sa'eed came back again! Revealing the secrets of seven years! We came to know that he was behind everything! He tried his best to hurt me, my family and you but in the end he ended up dead! Laylah idan kika duba we have been in this mess because of one thing only! LOVE!!! Idan kuma zan shafe shekaru bakwai da kaunar ki ba tare da ya ragu ba ta yaya kike tsammanin zan bari ki yi nesa da ni? You will stay in this house you will be mine forever! I don't care what Meenah thinks!" Yana kai nan ya mik'e ya ce "Zan je in kawo miki abinci... I know you haven't eaten" Ita ma mik'ewan tayi tsaye tace "A'a Suraj ka barshi zan je in kawo da kaina it's not like i couldn't walk.." bai kula ta ba yayi murmushi ya fita.........

Post a Comment for "IN SO YAKI NE CHAPTER 17"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...